Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ita, bata dad’eba sai gata ta fito sanye da baqaqen kaya fuskarta lullu6e da baqin qalle hannunta d’auke da qwarya baka ganin qafarta saboda kayan jikinta sun lullu6e qafar harjan qasa sukeyi wuf tayi tafice daga d’akin tad’au hanyar KOGON SARAUNIYA...........

Fitarta da komai akan idon Aunty Safiyya, Aysha da Fatima........


Aunty Safiyya ce tafara fita ta take mata baya tanason binta tayi hanyar kenan tajuyo ihun neman agaji can hanyar bayan gidan gudu-gudu sauri-sauri haka tajuyo tayi hanyar datakejin ihun........

JARUMA CE Fitarta kenan yauma tahad’u da Fatima tafito leqen asiri, batare da 6ata lokaci ba tai mata yadda taiwa Suwaiba jiya tabarta anan ba ihun da batai ba amma ba mataimaki........

Sanda Aunty Safiyya ta isa tini mefaruwa ta faru ga Fatima haka tariqeta ajikinta tana wani irin kuka wanda ya qunshi abubuwa daban-daban........





🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡


Tinda Kulu ta shiga cikin Kogo mamaki ya cikata sakamakon............















’YAR GATAN MAMA✍️.
*🏡A WANI GIDA🏡*

*LABARI/ RUBUTAWA*
*KHADIJA S. SAMINU*
*(YAR GATAN MAMA)*



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*


Assalamu alaikum ina miqo gaisuwata agareku tare da fatan alkairi😘😘.


🅿️🔟.


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Tinda Kulu ta shiga cikin kogo mamaki ya cikata saboda kalaman da taji suna fitowa daga bakin mai bayani kamar haka...
”SARAUNIYA TANA GODIYA TARE DA JINJINA GAREKI JARUMA..... Lallai awannan karan kina aikin daya dace SARAUNIYA tace afad’amiki jinin jiya ya qayatar da ita ”Ai kafin mai maganar ya rufe baki tini JARUMA ta matsa kusa da SARAUNIYAR tasu wadda ganintama abin tsoro ne, itadai na farko ba mutum bace ayadda idonka zai gantama tabbas tafi qwarangwal saboda tana jiki matuqa amma kana ganinta kaga dodanniya mai matuqarmuni, tana da fuska maiban tsoro wanda baka ganin komai acikinta sai daqwa-daqwan idanunta masu munin gaske jajawurdasu..........

Matsawa tayi daf da dodon tsafinnasu ta d’aga qwaryar hannunta tayi gaba d’aya jikinta na rawa tasaita dai-dai wata babbar qofa wadda ta firgita Kulu dan gaba d’aya dodanniyar abar tsoro ce tana tsaka da tinani taga JARUMA tana juye wannan jinin a wannan qofar wanda sai sannan ta lura ashe bakin SARAUNIYAR ne ahaka...........

Bayan ta gama juyewa ne tadurqusa gaban SARAUNIYA ta had’e hannayenta biyu tare da yin qasa da kanta alamar girmamawa sannan ta fara magana kamar haka........

”SARAUNIYA Ina cikin tashin hankali matuqa....
SARAUNIYA gaba d’aya tinanina ya qwace.....
SARAUNIYA Ina neman alfarma tare da roqonki akan kisa abincikomin SARQATA.......... Domin da wannan SARQAR nake iya duk wani siddabaru da nakeyi..... Haka kuma kin tabbatar min indai SARQAR nan tabar hannuna to na gama yawo ni kuma banason asirina ya tonu saboda bangama cika burikana ba..... ”

Cikin Kulu ne yabada wata qara sakamakon jin abinda JARUMA take fad’i ”To wai wacece wannan JARUMAR.......?
Tambayar da Kulu kewa kanta kenan bayan tasan bata da bata amsa, tana cikin duniyar tinani bata ankaraba sai ji tayi........

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Kuka Aunty Hafsa takeyi tamkar ranta zai fita , tana ta jijjiga FATIMA ko zata tashi amma ina tini rayuwar Fatima ta qare sai dai labari ......
Tana tsaka da kukanta take tinanin to tayaya zata d’auke Fatima daga nan.......
Ba zato ba tsammani kawai saijin mutum tayi akanta ana magana......
”Dubunki ta cika dan haka kawai kimiqa kanki”
Jin maganar tayi tamkar amafarki, sake bud’e idonta tayi sosai danta tabbatar da gaskene abinda take gani ko ko qarya ne?
Mama Luba ce akanta riqe da qugu tana kallonta sama da qasa......
Cikin hanzari Aunty Hafsa ta qarasa miqewa tare da nufo inda mama luba take tana fad’in......
”Yauwa Mama dan Allah kizo mu temaki Fatima yauma kinga ankashe mana ita ........... ta fad’a tare da nufo Mama tana yunqurin ta rungumeta....... bata ankara ba sai jitayi mama tasa hannu ta hankad’ata baya tana fad’in..........

”Wallahi Hafsa yau kin gama yawo, Allah ya toni asirinki nakamaki dumu-dumu kina zuqe jinin baiwar Allah , Ashe daman ke ce kike kashemana mutane agidannan..... to wallahi yau kam kinbani danni da kaina zan tona miki asiri kuma sai an hukuntaki dai-dai da abinda kikayi, gwandama akashemana ke mu rabu da annoba gaba d’aya”

Tana gama fad’in haka tasakai taijuyawarta 6angarenta.......

Innalillahi wa’inna ilaihi rajiun..... Allahumma ajirny fi musibati wa aklufni kairan minha...... innalillahi wa’inna ilaihi rajiun.........

Abinda Aunty Safiyya taita maimatawa kenan cikin matsanancin tashin hankali, alokaci d’aya Nadama, danasani, kaico gaba d’aya suka dirar mata saboda yanda taji laifin kisa zai dawo kanta batajiba bata gani ba....... Ganin zama anan bazai fishshetaba hakan yasa taduba wayarta tana neman number BALA maigadinsu bai d’aga ba harsaida tayi kira uku sannan ya d’aga, akid’ime take gayamai inda take, nan yake cemata baya gidan yaje ganin gida d’azu haka dan dole tashiga 6angarensu ta nemo LAMI mai aikinsu suka kama Fatima suka tafi da ita d’akinsu, Sa’ilin Su Hafsa da Aysha sunyi baccinsu hakan yasa basu tashi ba......

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

”Lallai JARUMA kin tafka babban kuskure dakikai sakacin da kika rabu da SARQAR TSARONKI dan haka kizauna acikin shiri dan asirinki yana daf da tonuwa acikin wannan gidan...........
Kinfi kowa sanin yadda kika wahala kafin kisami wannan sarqar amma kika bari ta salwanta dan haka...........




’YAR GATAN MAMA✍️



PLSSS KUYIMIN HAQURI HAIHUWA AKAIMINI SHIYASA 👏
*🏡A WANI GIDA🏡*

*LABARI/ RUBUTAWA*
*KHADIJA S. SAMINU*
*(YAR GATAN MAMA)*



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



🅿️1️⃣1️⃣.

Kinfi kowa sanin yadda kikasha wahala lafin kidamu wannan sarqar amma kika bari ta salwata dan haka.... mu yanzu babu abinda zamu iya miki akai.....
”DARAUNIYA Atemaki baiwa me nema aqarqashin uban gidanta, ni baiwa ce awannan gida se yadda akayi dani dan haka atemakeni duk rintsi duk wahala zanyi qoqari, afad’amin kome zanyi nikuma zanyishi indai sarqata zata dawo nibanason sabuwa tawa nake so.......
Jaruma ta fad’a cikin tashin hankali mara misaltuwa......

tana tsaye ta rasa meke mata dad’i kawai saiji tayi ana bata umarni wanda seda jikinta yad’au rawa tsabar tsoron d taji ya dirar mata lokaci d’aya......

’SARAUNIYA tana buqatar ki kawo mata jinin mutane kamar haka......
Hauwa kulu, Haneef Sannan Abba matuqar kika kawo jininsu to matsalarki takau sedai kiji wani yana kuka amma bake ba.......

gyara tsayuwa tayi sannan tafara magana kamar haka......
”Matuqar asirina, zai rufu to ko jinin waye zankawo dan haka abani lokaci....
Suna gama tattaunawa sukasha jini masu buqatu aka biyamusu sannan suka tafi saboda kusantowar asubahi........

Ta hanyoyi mabanbanta suka koma d’akunansu....
Tinda Kulu ta turo qofa tayi hud’u da Fatima wadda tad’ashe tayi fari fat yanda ko bakasan mutuwa ba zakagane wannan sedai haquri...... tina kayan dake jikinta yasa tad’an tsaya sannan tasako kai ta shiga gabadayanta...... cikin sauri tacire kayanta sannan sannan taja ta kwanta idonta nakan Fatima babu damar tayi magana......
Aunty Safiyya ce tabud’e qofa tafito daga band’aki fuskarnan tayi jawur ido yayi luwu-luwu kana ganinta kasan taci kuka ta qoshi, tana fitowa inda kulu take ta nufa, tsugunnawa tayi gaban kulu zata mata magana sai kuma saikuma ta fashe da kuka...

’Aunty Safiyya menene? menene yafaru kike kuka? baki bacci ba idonki yayi haka”ajere tayo mata tambayoyin me makon ta amsa itama saita mayo mata da tambaya......

”Hauwa kitemakemu kifad’i gaskiya, Hauwa ina kike zuwa cikin dare kuma mekikeyi?
Hauwa mene alaqarki da kayan sa kikasa jiya?
Hauwa wane yakashe Suwaiba kuma wane yakashe Fatima jiya?........

Batare da wani firgici ko tsoro ba Kulu ta gyara zamanta sannan itama tabata amsa kamar haka.......

”Haba Aunty Safiyya wannan wane irin tambayoyi ne haka kike yimin kamar kina zargina da kisan da akeyi agidannan..... gsky ni banason irin haka dan haka bansan komai ba”
Hauwa tafad’a tana miqewa tsaye niyyarta ta fice daga d’akin gaba d’aya..... Ruqota aunty Safiyya tayi tare da fad’in..........

”Hauwa ni ba zarginki nake ba na tambayeki ne saboda nasan kinsan komai akai, fad’amin gaskiya shine zai ku6utr dake daga zargi 6oyemin kuma shine zaisa kema azargeki, kisani alhakin kisan Fatima yahau kains kuma zankar6a har Allah yabayyana gaskiyarsa.....
tana gama fad’in haka tao shigewarta band’aki inda tayo wanka had’eda alwalasannan tafito.......


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Tinda mama luba takoma d’aki farin ciki yacikata dankasa komawa bacci tayi tsabar murna tanason safiya tayi asirin Aunty Safiyya ya tonu.... ahaka kuwa tai zamnta harsaida gari yawaye tana kullewa da kwancewa.......


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Rabon da gidan ya hargitse irin haka kowa ya manta... sai dai dake ance(idan maye yaci ya manta uwar ya bata mantaba) kowa arud’e daka masu kuka sai masu kurari kowa yana d’aukan alwashi kala-kala..... Abbama kansa hankalinsa yayi matsanancin tashi yarasa inda zaisa kansa ..... Aysha kam tinda akafara sabgar tanemi waje d’aya tazauna tana tinanin ta hanyar dazata fallasa sirrin data riqe tin daren jiya zuwa yau.....


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Yau kwana biyu da rasuwar Fatima ba zato ba tsammani wasu daga cikin gida sukaji sammaci ......daga cikinsu akwai....Hauwa kulu,Aunty Safiyya,Hajiya Nafi,Mama Luba da kuma shi abban kansa....

Tinda saqo ya isa wajan Abba yaketa sababi yana mita...
Hajiya Nafi kuwa ko ajikinta cikin dariya danuna ko ajikinta ta kar6a....
Hauwa kulu kuwa tinda ta kar6a tashiga farin ciki mara misaltuwa tare da murnar tarkonta yakama wadanda ta d’anawa.....
Aunty Safiyya cikin jimami ta kar6a tace Allah yabayyana gaskiya...
Sanda mama luba taji ankaiwa su safiyyamurna takamata saboda tanasob lallai saitaga bayan safiyya,amma kuma saigashi itama ankawo mata aikam ba qaramin rud’ani ne yaziyarceta ba saida tayi da gaske sannan ta daidaita kanta......
wannan kenan..... 🤮

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡


Gobe sadakar uku kuma gobe za’a shiga kotu domin aqwatowa Fatima da Suwaiba haqqinsu na kashesu da akayi basujiba basu gani ba....

Kowa a6angarensa shirye-shirye yakeyi nashiga kotu kuma kowa yana burin shine zaiyi nasara.......

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Lokaci yayi hakan yasa kowa ya hallara akotu dukda dukansu daban-daban sukaje saboda kowa baisan ganin kowa.... Hafsa ce kawai suka tafi itada Hauwa kulu dukda itama hafsan batasan me Hauwan take shiryawaba........



✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️.


HASASHE...........


Shin wanene zaiyi nasara acikin wannan shari,ar?

Dawa-dawa ne zasu fad’a rami idan angama shari,a?

Shin me kulu take shiryawa ne aqasan zuciyarta?

Shin mene ya had’a hajiya Nafisa da wannan shari,ar?


Shin wane sirrine Aysha take dashi ahannunta..?

Mene yasa akasaka Abba awannan shari,ar?

Shin mene abinda mama luba take shiryawa?


shin mene ’yar gatan mama take shirin rubutawa😜?????



amsa kawai zaka bada........ayi comment dayawa ayi shari,a dayawa..........
*🏡A WANI GIDA🏡*

*LABARI/ RUBUTAWA*
*KHADIJA S. SAMINU*
*(YAR GATAN MAMA)*



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*🅿️1️⃣2️⃣.


Lokaci yayi, hakan yasa kowa ya hallara akotu dukda dukansu daban-daban sukazo dan kowa baisan ganin kowa.... Hafsa da Hauwa kulu ne kawai sukazo tare dukda itama Hafsan batasan me Hauwan take shiryawaba.... Itadai abinda tasani ’yar uwarta bazata iya kisan kaiba balle har mutum biyu......

Kallon-kallo akeyi atsakinsu kowa ta ciki na ciki ne kawai.......

Kallo ne yakoma sama lokacin da Abba yashigo yana d’agawa kowa hannu, ganin kowa ya hallara hakan yasa kowa ya nutsu domin fara shari’a......

Barister Hashim shine mai kare Mama Luba....

Barister Khalid Shine mai kare Abba.....

Barister Hafsa Itace mai kare Aunty Safiyya.....

Barister Fauzah itace mai kare Hauwa Kulu......

Gaba d’ayansu duk suntashi sun gabatar da kansu kafin ashiga rikitacciyar shari’a ka’in da Na’in........

Mai kare masu qarane yamiqe domin yafad’o duk abinda akazauna dominshi....

Assalamu alaikum waeahmatullahi wabarakatuhu.... Nidai Sunana Barister IBRAHIM KHALIL BELLO tare dani akwai d’an uwa abokin aiki wato AHMAD AMINU JIBRIL... Yan uwa Assalamu alaikum.. shima yamiqo sallama tare da komawa ya zauna.....

Alqaline yabashi umarnin yafad’i duk abinda yakeson fad’a.....

”Uhummm”
Yayi gyaran murya kafin yafara magana kamar haka...
”Da farko dai kowa dake wajannan yadan menene yataramu anan... amma bari na maimaitamuku... A WANI GIDA mai cike da qalubale wanda ya tattara iyali masu yawa anwayi gari anyi kisan kai kuma acikin wad’anda ake zargi sun had’a da mutanen biyar d’innan dake tsaye agabana wanda hujjoji da qwaqqwaran bincike shi zai tabbatar da ainihin wanda yayi kisan acikinsu......
Yanzu dai kotu tana buqatar amatso da Safiyya kusa domin ta amsa tambayoyin da za, a mata....

”Kotu ta bada dama”

Antambayi Aunty Safiyya sunanta tabada kamar haka....
”Tom, da farko dai Ni sunana SAFIYYATU MUSTAPHA ADAM ”

”munji sunanki Hajiya Safiyyatu.... Safiyyatu ana zarginki da kisan Fatima Sadiq mezaki fad’i akai”

Barister Ibrahimkhalil ya tambayeta.....

Kuka Aunty Safiyya ta saka kafin tad’ago ta kalli kowa sannan ta bud’i baki tace......

”Eh....Yamai girma mai shari’a inamai roqonka ayimin adalci aimin hukunci dai-dai da abinda nayi... na amsa laifina tabbas NI NAKASHE FATIMA.....”

Rige-rigen kallonta akafarayi kowa kansa yayi dumm....wani irin malalacin kallo Hauwa kulu tabi Aunty Safiyya dashi inda acikin ranta hakan yayi mata dad’i saboda hakan alamune na zasuci nasara......

”Me girma me shari’a wadda ake zargi bata wahalar da shari,a ba wajan fad’in gaskiya dan haka ina roqon wannan kotu mai albarka data sa ayankemata hukunci dai-dai da abinda tayi.......

Haka akacigaba da shari’adaki-daki inda da akazo tuhumar Hauwa kulu ta tibire tace tana zargin Mama Luba ita takashe Fatima,nan dai wuri ya hargitse kowa na fad’in albarkacin bakinsa ganin hakan yasa mai shari’a ya tsayar da ita sai 12/6/2021 zaacigaba da shari’a dan haka anbawa kowa daman yaje yasake shiri sannan masu bincike suci gaba da qoqari....nan dai shari’a ta tashi sai lokaci yacika.

Haka dukansu suka tafi gida...
Hafsa ce ta matso kusa da Aunty Safiyya tare da fad’in...
”Aunty Safiyya aikinki yayi kyau tabbas wannan itace hanyar dazamubi wajan dagulawa mara gaskiya lissafi....Inason kisa aranki babu abinda zai sameki saboda ni na tabbatar da kulu ba qaraminshiri tayiwa wannan shari’ar ba”

”Hafsa wallahi har cikin raina bana zargin Hauwa dayin kisannan kuma ita kanta Mama Luban bana tinanin ita tayi kisan kawai dai wani 6oyayyen al,amari ne wanda sai ubangiji zai bayyana shi dan haka yau bazamu rintsaba dole mu dage da roqon Allah munsan bazai kunyatamuba”
Haka sukaita tattaunawa atsakaninsu kafin Kulu ta shigo suka d’ora....
Hauwa ta kalli Aunty Safiyya tare da cewa....

”Aunty Safiyya akwai wani bincike da nayi kuma yabani sakamako yadda banyi zatoba,amma dukda haka namiqa lamarina ga Allah...Aunty Safiyya na roqeki gobe idan ance anje kotu zakiji abinda kanki bazai d’aukaba amma dan Allah inason kikwantar da hankalinki badanniba ”
Ta fad’a tana had’a hannuwanta alamar roqo tare da sakar mata murmushi wanda yafito da zallar kyawunta mai d’aukar hankali.......
Hafsa ce takalli Hauwa tare bugunta tana fad’in ”Hhhhhh...Wallahi Kulu naso ni ake zargi nasan kinfini qwarewa aharkar kuma shari’a dake bata tsawo nan d nan gaskiya take halinta....amma yanzuma ke zaki aikin ni taimako kawai zanyi ....ta fad’a tare da kashewa Hauwan ido,Itadai Hauwa murmushi kawai take tare da tashi saboda lokacin sallar isha’i yayi.


Yauma dare yayi masu shiri sun shirya domin tafiya ibadar da babu lada acikinta.....

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

”SARAUNIYA yau nashiga rud’ani saboda sammaci har da ni babban tashin hankalina bai wuce sarqar nanba SARAUNIYA ki temakeni saboda kar asirina ya tonu....ni ba tonuwar asirin nake tsoroba tsorona bangama d’aukar fansa ba.......

”JARUMA kin rigada kinyi kuskure tinda har kika had’a baki da wata kikeson ku yaqi SARAUNIYA saboda kinason kihau babban kujera dan haka yau ta qaremiki.....
Aka bata ba yadda tai tsammaniba cike da zafin nama da tashin hankali ta miqe tare da bankad’e qallen fuskarta hawaye nabin fuskarta takama cewa.....

”Dama duk wanda ya kaucewa hanyar Allah yasan me yayi kuma nima badan san raina nashiga wannan qungiyaba saidan mijina...Kuma shima baisan inacikiba amma tinda abin hakane nagode.......
Indai na amsa sunana na JARUMA to wallahi nida kaina zanwargatsa wannan qungiya tamu... ”

Tana gama fad’in haka taificewarta ita tama manta bata rufe fuskarba sai bayan ta fita sannan talura da hakan......


Hauwa Kulu ba qaramin girgiza tayi ba sakamakon ganin wadda batayi zato ba amatsayin JARUMA, Haka taita tinani har aka sallami kowa suka fito..... Farin ciki yagama cigata saboda tagama samun hujjojin da a iya gobe kad’ai sai gaskiya tayi halinta..... Cike da murna tashiga d’akinsu yau bata wani cire kayan jikinta ba saboda Hafsa da Aunty Safiyya ne kad’ai su kuma sunsan abinda ttakeyi, ahaka suka kwana suna tattaunawa har Allah yawayi garinsa.


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡



RANA BATA QARYA SAIDAI UWAR D’IYA TAJI KUNYA.....

Yau kam kotu tacika maqil babu masaka tsinke kowa ya hallara amma duk da haka saida akad’auki lokaci ana jiran zuwan kulu batazoba qarshema se fara shari, ar akayi batanan....







’YAR GATAN MAMA✍️
*🏡A WANI GIDA🏡*

*LABARI/ RUBUTAWA*
*KHADIJA S. SAMINU*
*(YAR GATAN MAMA)*



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



🅿️1️⃣3️⃣.


Shari’a tasa kawunan mutane sun kulle saboda kowa yakasa gane mai gaskiya damai qarya, kotu ta wanke Hajiya Nafi bisa zargin da ake mata ta wanke Mama Luba.... Ahalin yanzu ba wadda kotu ke jira ta yankewa hukunci sai Hauwa Kulu saboda duk shaidu sun bayyana Kulu ce ta aikata laifin kisa......

Ansamu shaidu awajan Aysha ’yar uwar Suwiba da Fatima..... Tq tabbatarwa da kotu hotunan da tayiwa Hauwa kulu lokacin da zata fita kafin kisan Fatima....
Iya shaidun da bada da kuma wanda Barister Hafsa tabayar kawai suka isa su tabbatar da laifi akan Kulu saboda Hafsa ta tabbatarwa da kotu batasan me Hauwa kulu ke shiryawa ba kuma itama taganta da kayan kuma tasha tambayarta tana 6oye mata abinda take aikatawa asanda Hafsa ke bayani harda fashewa da kuka saboda takaicin halin da ’yar uwarta tasaka kanta......

Hauwa kulu ba ita tazoba harsaida aka fara tinanin kodai nemota za’ayi saboda tinaninsu taqi zuwane saboda tasan yau dubunta ta isa ba zato ba tsammani saijin sallamarta akayi tare da ita akwai wata dattijuwa wadda kana ganinta kaga wadda hutu ya ratsata tasaka farin glass wanda ya qara fito da ainihin kyawunta dad’i da qari macece mai matuqar kwarjini, kallone ya koma sama sanda sukaga Hauwa Kulu ta shigo hankalinta kwance kai bazakace gidansu yana cikin tashin hankaliba, ba wata kwalliya tayi afuskaba saboda ita Allah yayi mata halitta kyawu kuwa saidai masha Allah tayi kyau iya kyau dukda ita ba maabociyar saka matsattsun kaya baceba, wani had’ad’d’en yadi ne ajikinta wanda akayi mata d’inkin abaya yazauna ajikinta ta nannad’e kanta da mayafin kayan sannan ta saqala jaka, hannunta wata babbar leda ce wadda kowa yaqagu yaga mene acikinta......

Bayan sun shigone aka hanata zama akace saidai tayi bayan kanta domin ta amsa tambayoyin daza’amata.

Batare da damuwar komai ba tashige taja tatsaya tana kallon ’yan gidansu d’aya bayan d’aya, idontane ya sauka kan ’yar uwarta rabin ranta taga yadda kissa ta mayar da ita kalar tausayi da alamu taci kuka suna had’a ido Hauwa batasan sanda dariya takufce mata ba.....
Ganin lokaci na tafiya hakan yasa aka fara zayyanowa Hauwa kulu dukkan laifukan da ake zarginta dasu ciki harda tuhumarta dalilin dayasa tashiga qungiyar mafiya

Bud’ar bakin kulu secewa tayi ,”Tabbas ni ce nakashesu bama su kad’ai ba, kuma nan gaba ma akwai wad’anda nake shirin kashewa ”

Ta fad’a tana kallon kowa sekace ita ke tuhuma ba tuhumarta akeba......

Me tambaya ne yasake banko mata tambaya kamar haka....
”Menene dalilinki na kashesu, kuma suwaye zaki kashe yanzu, suma me sukai mikj......

”Bazance ina da daliliba saboda duk san raina ne yasa na kashesu, sai kuma wani quduri danayi wanda sam bai shafesuba, kuma bashi da amfani nazauna ina fad’insa anan,amma badan wannan dalilinba dana fad’a........Tana gama magana saikuma ta fashe da kuka mai cin rai”

Akayi-akayi tayi magana amma taqiyi tayi shiru taci gaba da kukanta kamar ranta zai fita.

Barister Hashim ne yashigo da wata had’ad’d’iyar silver sarqa mai matuqar d’aukar ido sai sheqi takeyi da walwali bazai yuwu kamata kallo d’ayaba dole saika qara........


Tana riqe ahannunsa sai sheqi takeyi yana cigaba da shigowa saitin inda mutane ke zazzaune yana d’agata sama yana kalla kamar me neman wani abu ajikinta.....

Tashin hankali, tsoro, fargabane suka taru alokaci d’aya suka dira acikin zuciyarta yayinda kanta yai wani irin sarawa jitayi bazata iya had’iyewa ba dole ta miqe tsaye tare dasa hannunta tana nuna sarqar hannun Barister Hashim, wani matsanancin nauyine yadira akan le66anta yadda ta kasa sarrafasu tayi magana, kafin ta ankare taji gabad’aya wurin najuyamata yadda bazata iya tilastawa qafafunta wajan tsayawaba, batare data shiryaba saijintayi kamar amfarki tayi qasa.......

Cikin tashin hankali Aunty Safiyya tamiqe ganin hajiyarsu tafad’i, kowa na wajan hankalinsa yatashi ganin fad’uwarta,cikin hanzari suka tafi gunta aka kinkimeta sai asibiti.... Hakanne ya tilastawa kotu d’aga shari’a harsai Hajiya Nafi tasamu lafiya.


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

”Haba Hauwa kinga kindagula mana shari’a munshirya ayau za’ayi komai agama amma kinzo da tsarinda shari, ar zatai tsawo ”
Hafsa ce ta fad’a tana yiwa kulu kallon bki kyautamini ba....

”Uhummm.... Hafsa kenan bazaki gane ba yazama dole muja shari, a tayi tsawo indai munason muyi nasara.... Kigane idan mukabi ahankali shine zamuci nasara cikin sauqi.... Abinda nakeso dake yanzu baiwuce kitafi 6angaren hajiya kidage ke zaki kwana da ita sannan kuma bana buqatar kiyi shegen baccinnan naki aiki nakeso kiyimin”
Hauwa ce ta fad’a tana kashewa Hafsa idanu .... Tafawa sukayi sannan sukacigaba da hira suna dariya.




🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

”Haba Aunty Safiyya yaza, ai keda kema bakyajin dad’i zakice zaki kwana da ita, amma bakomai saidai bansaniba ko baki d’aukeni ’yartaba shiyasa bazaki bari na kula da itaba kiyi haquri saida safe”
Hafsa ce take kallon Aunty Safiyya tana maganar sannan tasakai zatai ficewarta. Ruqota Aunty Safiyya tayi tana fadin....
”Haba... Hafsa yazakice haka kema yar hajiyace kamar ni dan haka kina iya zama da ita hartaji sauqi”

Ta fad’a tana kallon Hafsa tare da sakar mata murmushi tafita ta barta itada hajiya.

Aiki kan jiki kan qarfi haka Hafsa taita kula da Hajiya har kwana hud’u sannan Hajiya Nafi ta samu tad’anji dama-dama....... Tinda ta lura Hafsa ke jinyarta sai ranta bai mata dad’iba saboda...........











’YAR GATAN MAMA✍️.
*🏡A WANI GIDA🏡*

*LABARI/ RUBUTAWA*
*KHADIJA S. SAMINU*
*(YAR GATAN MAMA)*



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________~________~_____________



Ina miqo gaisuwata agareku masoyana, adduarku tana matuqar yimin dad’i sai dai nace Allah yabar zumunci 🤝🥰💞💞.

🅿️1️⃣4️⃣.


Aiki kan jiki kan ’karfi Hafsa taita kula da Hajiya Nafi harta samu tad’anji dama-dama........ Tinda ta lura Hafsa ke jinyarta sai ranta bai mata dad’iba saboda ba haka tasoba.

Hafsa ce ta kalleta ganin ta ’kuramata idanu tana kallonta da alama ma tinani ta tafi, sannan tace mata.......

”Hajiya sannu da jiki yakikejin jikinnaki yanzun?.........

Shirutayi ko kallon inda Hafsa take batai ba balle tasa ran zata amsa mata, haka sukaita zama bamai yiwa kowa magana acikinsu qarshema Hajiya Nafi tatashi zata shige d’akinta , ganin haka yasa Hafsa tasake cewa akaro na biyu.......

”Sannu Hajiya nataso narakaki bayin, kinga jikinki bai gama ’kwariba.......

Juyowa tayi tare da yimata kallon biyar ma tafiki sannan tayi shigewarta batare da tayiwa Hafsan maganar ba tasakai tayi shigewarta ciki.

Shigarta keda wuya Hafsa taji wani irin gurnani kamar na SA..... Hankalinta yabata lallai ba lafiya ba..... A hanzarce ta miqe tare da zuwa jikin tagar d’akin tana leqawa.....


Yau hankalinta idan yayi dubu to yatashj saboda abinda tagani yafirgitata matuqa da gaske, cike da tashin hankali ta danna wayar hannunta takama mata video batare data saniba, jikinta gaba d’aya rawa yakeyi saboda yadda ta razana, Hauwa kuluce ta fad’o saboda tasan da Kulu batare da fargabar komai ba zata d’auka..........

Tinda tagama d’auka ta zauna kanta ya kulle saboda gaba d’aya batai tinanin haka ba..............






Kuyi haquri wllh ina typing ina gyangyadi shiyasa amma gobe zan qarasa muku gobe two pages kenan😇😇😇
*🏡A WANI GIDA🏡*

*LABARI/ RUBUTAWA*
*KHADIJA S. SAMINU*
*(YAR GATAN MAMA)*



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*.




🅿️1️⃣5️⃣.


Tinda ta gama d’auka ta zauna gaba d’aya kanta

2 Comments On A WANI GIDA
avatar
fatima-9-7-8

1 year ago

Reply

Masha allah

avatar
fatima-9-7-8

1 year ago

Reply

Yayi dadi allah yakara basira

Please Login or Register in order to submit comment