Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yagama kullewa saboda sam batai tinanin hakan ga Hajiyaba...

”To dama abinda Hauwa tagani kenan ta aikoni?
Lallai dole tace ta tanadi hujjoji game da wannan shari’ar........
Haka Hafsa taita zancen zuci har Hajiya Nafi tafito ta isa inda take....
”Shin ina Safiyya tashiga bata zauna daniba sai ke?
Tinanin me kikeyi haka kintsaya kallona?
”Ummm Hajiya ba komai, Aunty Safiyya bata da lafiya itama shiyasa bata zaunaba..... Tinani kuma ina tinanin yadda za’a rabani da ’yar uwata abar k’aunata wadda itakad’ai nake da awannan lokacin sabida wani son zuciyanata..... Hafsa ta fad’a tana share hawayen dakebin kundu-kukin ra matuqar zafi cikin qasan zuciyarta babau dad’i kwata-kwata duk takaici yayimata katutu.
Wani kallon banza Hajiya Nafi tabita dashi sannan ta zauna tana fad’in...
”Uhumm aidama qarrshen qasa duk inda kakai da qarya watarana se anriqeka........
Hafsa najinta amma taimata shiru tamkar bata d’akin.....


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Yau babu wanda baizoba dukansu sun iso da wuri saboda kowa yagaji da wannan shari, ar dataqi ci taqi cinyewa...

Barister Hashim ne ya fito d’auke da sarqarnan ahannunsa yad’agata sama tare da fad’in. shinwaye ya yarda sarqarsa?
Tinda Hajiya Nafi ga ganta jikinta yad’auki rawa tinaninta baki d’aya ya d’auke hankalinta atashe take fad’in..... ”Nikam yau tawa taqare”
bata idda tinanin da takeba saijitai Hauwa kulu na cewa.....
”Tabbas wannan sarqar tawace fad’uwa tai ahanyata tashigowa wannan kotu”

Ai bata ida zancenta ba seganin Hajiya Nafi akai tatashi tana ”K’arya kikeyi munafuka annamimiya makira sark’a tawace mallakina ce”

Sororo akayi ana kallonta kafin alk’ali yabukaci afito da ita domin tayi bayani yadda kowa zai gane......
Aikafin ace tafito tini tafito tayi gun B. Hashim cike da k’warin gwiwa tanason kar6a, cikin hanzari yai maza yayi baya da hannunsa , bayan kanta akashigar da ita domin ta amsa tambayoyin dazaai mata.
Fafur Hajiya Nafi tak’i amsa kowace tambaya ba abinda take fad’i sai..... ”Ni bansan komai ba, amma sark’a tawace”
Duk tambayar d akai mata abinda take cewa kenan daga haka bata kuma cewa komai saitakama bakinta ta rufe.
Kamar daga sama taji B. Hashim yace ”JARUMA kibud’e baki kiyimana bayanin wacece ke sannan kifad’amana dalilanki na kashe wad’annan bayin Allah”
Cike da firgici da tsoro tai saurin juyowa ta kalle shi , maimakon tabada amsar tambayar da akai mata kawai secewa rayi....
”Wallahi Hafsa senaga bayanki wato seda kikabi sirrina kikazo kika bankad’ashi ko?
Wallahi Hafsa yadda Abba yaga bayan Hajiya AMEENA to wallahi nima ni zanga bayanku tinda kuma bayana kukeson gani........

Maganar duniyar nan anyiwa H. Nafi kan tayi shiru tadaina hayaniya amma taqi ita k’ok’arin fitowa ta dank’i wuyan Hafsama takeyi amma jami’an tsaro sun hanata fita aikam se zuba mata ido da kunnuwa akayi domin aji me takeson isarwa.....
Fahimtar hakan yasa tayi shiru amma bata fasa dannawa B. Hafsa ashar da munanan kalamai ba....
Tambayar B. Hafsa akayi ko tana da abincewa game da zarginta da H. Nafisa takeyi?
Batare da 6ata lokaciba B. Hafsa ta buk’aci ahad’a wayarta da TV tanason jama’a su kalli sheda d’aya tak da zata bayar wadda zata tabbatarwa da kotu cewa H. Nafi itace JARUMA kuma itace wadda duk wani k’ulle-k’ulle a6oye ba tare da wani ya zargeta ba.
Kamar yadda tace haka akayi aka jona aikuwa sega H. Nafi acikin d’aki se zagaye takeyi tana surutai wanda kai baka isa kagane abinda take fad’aba, tintanayi ahankali harta fara d’aga murya ahaka kawai seganinta akayi jikinta yakoma gaba d’aya gashi kanta kawai kakegani kagane mutumce ahaka taita tsalle tana dira kan abubuwan amfanin d’akin wasu su fashe wasu kuma basu bashefa, tad’auki lokaci ahaka kafin daga baya tafara dawowa suffarta wadda kowa ke iya ganinta ayanzu ana zuwa nan ya d’auke....... Aikuwa ba wanda yakula da H. Nafi tini tayi kururuwa tanufo inda B. Hafsa take niyyarta ta danneta bazata sakeba setaga bayanta ana riqeta tana fad’in......
”Wallahi senaga bayanku munafukai, menayi muku kukebibiyar sirrina, idan fansa zaku d’auka akan mahaifinku yakamata ku d’auka tinda shine ya kashe muku mahaifiya bani ba, nikaina badan nashiga k’ungiyaba se yaga bayana, yau dole allura ta tono garma acikin gidannan, nidai nasan tawa tarigada ta k’are..........

More comment more typing✍️
*🏡A WANI GIDA🏡*

*LABARI/ RUBUTAWA*
*KHADIJA S. SAMINU*
*(YAR GATAN MAMA)*



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*.


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
🅿️1️⃣6️⃣
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡


Yau dole allura saita tono garma acikin gidannan,nidai nasan tawa tarigada taqare ........Bak’in cikina d’aya bangama d’aukar fansata ba asirina yatonu naso sena k’arar da danginka baki d’ayansu sannan natonawa kaina asiri nima akasheni idan yaso..........

Jin surutan nata sunyi yawa ne yasa aka dakatar da ita amma ina itafa yau seta fad’i komai idan yaso duk mai lefi ya kar6i hukuncinsa............
Ganin abinnata yaci tura ne yasa alk’ali ya buk’aci alalla6ata tafad’i komai batare da ansamu matsalaba,hakan kuwa akayi cikin lalla6i da laluma aka jata inda zata fad’i komai daki-daki........


Tashin hankali,fargaba,tsoro,razani,rud’ani,gigita sune bayyana afuskar Abba wanda bai bari ank’arasa da itaba yatashi cikin kid’ima yana fad’in.........

” Kubarta! Kubarta!! Kubarta!!!.......
Nafisa kada ki fad’i wani abu bari nizan fad’a da kaina,zangad’a da kaina........

Gaba d’aya su Aunty Safiyya hankalinsu yakai k’ololuwa wajan tashi duk sunrasa yadda zasuyi kowacce innalillahi takeja acikin zuciyarta saboda neman d’aukin ubangiji yabasu juriya da dauriya bisa wannan bak’on al’amari daya zomusu basui zatoba.
Bayadda suka iya haka sukabarshi yafad’i duk abinda yakeson fad’i.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
Saida Abba yayi gyaran murya sannan yatsaya sosai tare da fuskantar kowa ya fara fad’in......

”Ina mai neman afuwarku iyalina baki d’ayanku,sannan ina nemn yafiyarku agareni komai kukaji kuyi hak’uri ku yafemini kusa aranku hakan yanacikin k’addarar ku,sannan ina barar adduarku gareni bayan raina hakan zaisa nasamu sassauci”
Ya idar da maganarsa tare dasa hannunsa yagoge k’wallar data zubomasa sannan yafara bada ainihin labarin rayuwar gidannnasa.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

”Ni Sunana MUSTAPHA ADAM wanda mafi yawancin mutane sukafi sanina da ABBA sanadin tindagakan iyayena harzuwa k’annena duka da Abba suke kirana saboda sunan mahaifin mamana naci dan haka Abba yabini.............
Farkon rayuwata kowa yasanni mutumin kirkine wanda baruwana da kowa rayuwatace kawai agabana,muntaso mu hud’une maza acikin yaran mamarmu kuma dukanmu mungirma,duk sunrigani yin aure ciki harda yake bina saboda ni na tsaya nasaka buri araina lallai bazanyi aureba harsai nazama attajirin gaske wanda duk duniya zata sanni ,haka kuwa akayi iyayena sunsha zama suzaunar dani suyimin fad’a akan nanemo matar aure kokuma su sunemamin idan nakasa, koyaushe nunamusu nake lokacine baiyiba amma idan lokaci yayi za’ayi nikam harcikin raina bawani lokaci danake jira illa lokacin dazanyi arzik’i adinga kwatance dani ana fad’in alhaji Mustapha Adam multi millonier ,haka naitayi tsakanin ’yan uwa da abokai idannashiga cikinsu banda hira seta kud’i mafarkina kud’i komai nawa yazama kud’i......Kai tafi-tafi dai hartakai da inaneman inda zansamu kud’i kota halin k’ak’a fuskantar hakan da wani abokina BASHIR yayi seyagayyaceni gidansa da daddare,aikuwa cikin murna da farin ciki nashirya na tafi saboda nasan irin manyan kud’ad’en daya mallaka kuma yanzu idannaje zai iya yimin kyautar da saina girgiza........
Zuwana keda wuya yasa aka kawomin kayan abinci kala-kala masu dad’in gaske tare da abubuwan sha masu ratsa zuciya,bayan naci nasha ne yazo yazauna mukafira hira.....
”Uhummmm....Nikam Abba zuwa yanzu wane cigaba kasamu akasuwancika”
”Kaidai bari Bashir niduk l amurana sungama dagulewa wallahi komai bayatafimin dai-dai,ni zuwa yanzuma na yanke shawarar zuwazanyi nasamu babban malamin da zaimin aikin da zanyi arzik’i farat d’aya sannan akullen bakin ’yan bani na k’iya wanda basa gani saisun tanka danninagaji dazaman jiran arzik’i gashi kamarma guduna yakeyi......
Dafa kafad’arsa Bashir yayi sannan yace”Haba...abokina kai kamar ba wayayyeba kaita zama cikin duhu?
Abba aiyanzu kan mage ya waye kowa shiga harka yakeyi adama dashi,kai badaban kana da tsoro ba aida na gayyaceka kashigo k’ungiyarmu kaida tsiya har abada........☺️

Cikin zumud’i had’eda farin ciki mara misaltuwa haka namiqe naita masa godiya tare da jaddadamai na amince ko yanzu yakaini..........
Haka kuwa akayi ba’ad’uki wani lokaci ba Bashir ya gabatar dani ak’unyarsu aikwanaga tarba mai kyau kuma tin aranar akacikamin jikina da kud’ad’e masu tarin yawa...
Nanda nan na yunk’ura gyaran gidanmu inda yake buk’atar gyara,nazama banda abinyi sai kyauta nan da nan kafin kacemai tini sunana yafara yawo acikin unguwa duk majalisar daka zauna zancen ABBA HASAFI akeyi saboda harwasu sunfara canzan suna saboda indai kahad’u dani to ranar ka wanke baki kashiga madafar nama saboda kud’i mai yawa zanbaka wanda saika bawa wani......
Haka naita rayuwa alokacin,agidanmu babu wanda ke tambayata a ina nake samun kad’ad’e haka,kowa burinshi nabashi ’yan uwana basu da abin alfahari saini,burinsu suji ance ABBA HASAFI d’an gidansu ne.....
Bayan kud’i sun zaunane nafara siyen kadarori ina ajjewa har Allah yasa nasamu wani babban fili wanda tsayinsa badai kazagayeshi da k’afarkaba dole sekahau abin hawa,girman wajannan nawa idan zaai misali anayine da gidan wani babban malami kuma hamshaqin mai kud’i wanda yake zaune agarin kano wato Isyaka Rabi’u shine akace daga gidansa zuwa masallacinsa akwai nisa toni girman nawa yayi ukun nasa,gini aka farayimin nazuwa kallo wanda saida akayi 6angare-6angare sannan aka yanki wani 6angare me girma akayimin babban gidan gona wanda aka zuba nau’i daban-daban na ababen kiwo and’au lokaci ana ginin gidana kafin agamashi......
Bayan naga komai ya kankama ne sannan nafara neman auren ’yar wani malami anan unguwarmu me AMINATU ba’a wani 6ata lokaci wajan binkiceba aka bani aurenta saboda kowa yasan iyayena mutanen kirkine kuma nima haka bawanda yasan wannan sirrinnawa sai abokina wanda shikuma ko mutuwa zaigani bazai tonaba,bawani lokaci me tsawo aka saba akayi aurena da ita saboda yadda nake juya ’yan canji...........











’YAR GATAN MAMA✍️.




More comment more typing✍️.

Sisina ina miqo gaisuwata agareki 🥰
Hayaty rai shi dad’e✊.
Aunty Fauxy ayi karatu qalau😘.
*🏡A WANI GIDA🏡*

*LABARI/ RUBUTAWA*
*KHADIJA S. SAMINU*
*(YAR GATAN MAMA)*



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

🅿️1️⃣7️⃣

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡


”Ba wani lokaci mai tsawo aka sakaba akayi aurena da ita saboda inajuya ’yan canji.......
Munyi aure cikin So da k’aunar juna ba k’ananun kyaututtuka ’yan k’ungiyarmu sukayiminba sunyimin bajinta sosai da sosai hakan yasa nak’arajin k’aunarsu acikin zuciyata,saida nad’auki hutun mako guda bana zuwa k’ungiya saboda nayi amarya,to wannan hutun dana d’auka seyafara canzan tinani saboda naga kwana biyu banje na kar6o kudiba,Ameena nada wata d’aya agidana tasamu cikin yara biyu kuma dukansu mata dagani har ita babu wanda yasani acikinmu kasancewar ita bamai wahalallen laulayinnan bace ba,nima nasanine lokacin danaje k’ungiya ake cemin ansamu rabo agidana danhaka ana buqatar jinin yaran dukansu,nikuma jinhaka saina d’auki dukkan wata soyayyata na dora akansu nazaka araina kozan rasa raina bazan iya badasuba saboda yadda nakeson kallon yara biyu ahoto balle kuma agaske,agaskenma kuma wai agidana,anyi fad’a sosai dani ak’ungiya kafin su canza akalar buk’atrsu zuwakan d’an uwana wanda nafi k’auna aka bani za6i naza6a yarana koshi? haka badan nasoba nabada shi sewayar gari akai yamutu,haka naita rayuwa acikin k’ungiya kullum cikin bada jinin mutane nake tindaga kan jarirai harzuwa tsoffi duk wanda aka nema sena samoshi hakanne yasa akeji dani acikin lamarin....
Tafi-tafi rayuwa na tafiya har ameena tahaife yarana guda biyu dukansu mata,maimakon adinga kiransu da Hassana da Husaina sena sakamusu d’aya sunan mahaifiyata d’aya sunan babar Ameena,Hassana ake kiranta da Hauwa kulu,Husaina kuma Hafsa,yarane masu matuqar kyau da saurin shiga rai idan kagansu kamarsu d’aya danseka musu farin sani zaka banbance tsakaninsu,Hanya d’ayace zaka iya gane Hafsa wajan fara’a domin tana da sakin fuska koda bata sankaba,Hauwa kuwa akwai miskilanci matuk’a gaya dan ita batafiye son hayaniya ba ga rashin yaddar bala’i kai kace ’yar gidan yare☺️Haka suka taso gwanin sha’awa kodayaushe Dodon tsafi cikin son yasha jininsu yake amma abin yaci tura saboda yadda yaran suka iya adduoi kala daban-daban koyaushe uwar cikin koyamusu adduoi take da karatun kur,ani mai girma dan haka tin dodon tsafi nacewa nabada jininsu harya haqura yabarsu.....
Basu wani girma ba Ameena tasamu wani cikin saboda kwanika takeyi nan da nan ta haihu amma inda aka samu matsala mata duk take haifa,alokacin se zuciyata ta bujuromin dason nahaifi yaro namiji aikam abinka damai shi banwani d’au lokaciba nafara neman auren Hajiya Nafisa wadda itama ’yar wani attajirine bbu dadewa na aureta,lokacin da Nafi tasamu cikine ake fadan namijine acikinta nannasa soyayyar duniya akan yaron amma da aka haifeshi sai dodon tsafi yai rantsuwar matuqar ban bada shiba za’a qwace duk wata dukiya da akabani kuma nida arziqi har abada,jin hakan yasa hankalina yatashi badan inasoba nabada wannan yaron ga qungiya,mutuwar yaron tadaki kowa saboda yadda kowa yad’au k’auna yad’orawa yaron amma haka akayi haqurin rashinshi,wasa-wasa saida Hajiya Nafi ta haifi yara maza hud’u ina bada jininsu ganin haka hankalinta yatashi tafara tinanin kodai matsalar daga itane seta haihu lafiya awayi gari babu yaro?
Dan tarage zafin rashin yara ’yan uwanta suka yanke shawarar bata kyautar ’yar yayarta data rasu kuma asannan ma yarinyar tafara girma hakan kuwa ba qaramin dad’i yayi mataba nanta riqe yarinyarnan kamar ita ta haifeta......
Kwatsam babu zato babu tsammani dodon tsafi ya buqaci jinin mahifiyata da mahaifina abin ya girgizani dan haka naso na daga qarshedai aka bani za6i na bada d’aya daga cikinsu shaquwar dake tsakanin uwa da d’anta tasa nakasa bada mahaifiyata saina bada mahaifina shima bandad’e da badashiba akasake buqatar jinin mahaifiyata bansha wahala ba wajan bada jininta saboda zuwa sannan zuciyata tagama qeqashewa alokacinne nakejin zan iya bada jinin kowaye tinda har na bada ran mahaifana da wasu daga cikin ’yan uwa harma da yarana na cikina...........
Wata rana matata Nafisa tayi wata rashin lafiya kamar bazata kaiba sai mahaifiyarta tazo dubata sharrin shed’an shiyayi tasiri acikin zuciyata haryakaini naji inason shan jinin sirikata banyi wani tinaniba haka nashanye jininta acikina saigani akai ta mutu Nafi mutuwar mahaifiyarta agidanta ya rud’ata dan saida ta fita daga hayyacinta matuqa da gaske haka akakira wayar danginsu makusantansu na kusa dana nesa suka fara tawowa ban daddaraba haka acikin shaqiqanta saida nabada jinin guda biyu mace da namiji sannan nadakata dar kar asirina yatonu.....
Sai da aka d’auki shekara biyu bayan haka kwatsam se Dodon tsafi yabuqaci na kawomai jinin d’aya daga cikin matana nikuma ganin irin ta6argazar danayiwa Nafi hakan yasa naqi bada jininta bawai dannafi sonta akan Ameena ba Aa sedan tunowa da abubuwan dana mata, haka nad’au Ameena nakaiwa Dodon tsafi ita saboda tahakane zamuqara samun wasu maqudan kud’ad’e suqara shigowa qungiyarmu.....
Bayan bada ran Ameena har saida nakwanta rashin lafiya saboda son da nakewa Ameena gashi yanzu nabada jininta bazan sake ganinta sedai yaranta guda biyar data mutu ta bari Kulu, Hafsa da qannensu guda uku ciki harda namiji d’aya wanda shima yafara wayau, ahaka da kad’an-kad’an saida nabada ragowar yara ukun suka rage saisu biyu kawai saikuma yarinyar wajan Nafi Safiyya.........
Bayan nabada jinin Ameena ne Dodon tsafi yayi rantsuwar shan jinin Hafsa da Kulu amma me duk ranar da nahimmatu nazuqe jininsu sainaga sunzamemin macizai suna qoqarin sarana dana gayawa ’yan qungiya abinda nakegani inzansha jininsu sai sukace qarya nake nan akabawa wani daga cikin qungiya aikin kawo jininsu memakon yakawo jini sewayar gari akayi ya mutu, aka sake bawa wani akaro nabiyu shima yamutu daga nanne aka haqura dajininsu gaba d’aya........
Arayuwata banson rayuwa da mace d’aya dan haka na himmatu zan qara aure, haka nashiga neman aure wannan karon seda nabar gari naje nasamo LUBABATU wadda yarana suke kiranta da Mama nikuma nake cemata Luba..........
Tinda na auri Luba gidana yasauya daga yadda akasanshi bansan daliliba amma kusan kullum cikin dare sekaji iface-iface agidana masu ban tsoro, nayi iya bincikena amma bangane ba..........
Sai da Luba tad’auki lokaci sannan tahaifi yaro guda d’aya wato HANEEF wanda seda kowa yafiddarai sannan ta haihu to nidai sena cemuku tinbayan haihuwar wannan yaron bankuma samun kwanciyar hankaliba saboda tsoro yaron yake bani duksanda muka had’u dashi seya dinga tambayata abubuwan baya wanda ni namanta dawasuma, hankalina yana tashi matuqa saboda nasan wasu abubuwan ko mahaifiyarsa batasaniba balle shi, amma shikuma yasani, ganin haka yasa nafara qoqarin bada jininsa amma yaqi samuwa dandole nazubamai ido.......
Ban kuma tsorata ba saida Kulu fara karatun lawyer itada ’yar uwarta bayan sungamane kullum suna hanyar shari’a hartakai ga nakama Kulu na bibiyar takuna tana neman wasu daga cikin sirrikana, sanda nafuskanci hakan hankalina yayi mugun tashi amma sam banyi zaton abin zaikai ga haka ba.............



’YAR GATAN MAMA✍️.
takawarki lafiya 6auna mai tafiyar qasaita, wahainiyar mai canza launi,Haziqah mai saurin fahimta, Kyakkkyawa mai kyakkyawar zuciya,Kina Sona baki so kiga na doshi baqi kullum fari kike nuna mini, jinjina taban girma nakemiki maiso domin Allah, Ina sonki da dukka zuciyata❤️.

Ummuna dake nake😘😘.





Sis Sady ina miqo gaisuwa tare jinjinar ban girma👍👍.




















More comment more typing✍️.
*🏡A WANI GIDA🏡*

*LABARI/ RUBUTAWA*
*KHADIJA S. SAMINU*
*(YAR GATAN MAMA)*



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

🅿️1️⃣8️⃣

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

”Sansa na fuskanci Kulu na binciken sirrina hankalina ba qaramin tashi yayiba amma sam banyi zaton abin zaikai haka ba.......
Gaba d’aya tinanina ya tsaya akan tinda nayi iqirarin tsinemata to rabar maganar ashe itace zataga bayana......”Abba yagama fad’a tare da dafe kansa da dukan hannuwansa.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Kowa dake cikin kotunnan ya girgiza da lamarin Abba saboda kowa yaji yadda Abba yaringa kisankai batare da imani yayi tasiri azuciyarsa ba,haka akaita qananun surutai kotu duk tabi tahargitse kowa albarkacin bakinsa yake fad’i .........

Tinda Labari yayi nisa Barister Hafsa batasan inda kanta yakeba,tinda ta sunkuyar da kanta bata d’agoba,Kulu kam tarasa abinyi saibin kowa da ido takeyi daga kan wannan ta sauke akan wannan haka taitayi har Allah yakai idonta kan ’yar uwarta masoyiyarta abar alfaharinta d’aya tamkar da dubu BaristerHafsa,wata razananniyar qara tasaki tare da miqewa tsaye dafad’in ” ’YAR UWATA!!!
Hankalin kowa ne yadawo kanta inda basui qasa agwiwaba suka nufi inda Hafsa takifa kanta,d’agota suka farayi aikuwa ta koma luuuuu......
Hankalin mutanene yatashi kowa ya hargitse yana fad’in abinda yazo bakinsa,Kulu kam takasa barin inda take burinta kawai taga qanwarta sahibarta ta tashj tazo inda take,batare datayi zatoba saijitayi wata mata na fad’in......
”Kunga kudena wahalar da kanki wajan ganin tamiqe,wannan ta6argaza da ubansu yayi ai ya isa yasa zuciyarta tabuga ta had’iyi zuciya tamutu lahira,aini naga qarfin halin ’yar uwarta dake tsaye damm ba’abinda ya gigitata...............

Ba wanda yalura awajan kawai saijin fad’uwar Kulu akayi aqasa timmmm.....
Aunty Safiyyace ta sake rushewa da matsanancin kuka tare da dawowa inda Kulu take tana jijjigata,iya yinsu sunzubamusu ruwa amma ba wadda ta tashi acikinsu ganin haka yasa aka d’aukesu sai asibiti....
Anshafe awanni kafin asamu numfashin Hafsa yadawo dai-dai,Hauwa kulu kuwa likitoci sun rufa akanta bayadda take haka akasakamata naurar numfashi saboda duk wasu gwaje-gwaje anmata amma shiru jikin bayadda yake ganin hakane yasa jikin likitocin gaba d’aya yayi sanyi suka barwa Allah ikonsa.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
Acan kotu kuwa Alk’ali cewa yayi acigaba da shari’a ba amfanin ace sai sunji sauk’i za’a cigaba,Haka kotu ta tilastawa Aunty Safiyya zama domin agama agabanta idan yaso saji yadda aka k’arke daga baya.

Abbama duru-duru yafara sanda akafita dasu Kulu yana ik’irarin saiya bisu masu tsaronsa suka hanashi,wasuma harsun fara zubarmai da habaici suna suma binsu zakayi kakashesu?..........

Ganin lokaci na k’urewa aka bawa Hajiya Nafi dama tafad’i duk abinda zata fad’a game da dalilin shigarta k’ungiya dakuma dalilinta na kashe wanda basu jiba basu ganiba.........

Gyara tsayuwa tayi tafara da cewa........

”Randa aka kawoni gidan Alhaji Mustapha Adam wato Abba nasamu kyakkyawar tarba daga wajan matarsa Ameena domin kaf dangina saida suka tafi suna fad’in kyawawan halayenta,Sanda dangina suka tafi itama tatako tazo har inda aka ajjeni wato d’akina,da sallama ta shigomin sannan tayimin sannu da zuwa taimana fatan zama lafiya,dukda inajin kunyarta hakan bai hanani satar kallontaba saboda inason na tabbatar da kishiyatace takemin wannan maganganun cikin tausasa lafazi da lallashi kamar wata yayata?
Fuskantar ina satar kallonta yasa tasaka hannu tare da sauke lullu6in fuskata muka kalli juna,murmushi ta sakarmin tare da fatan alkairi taimini sallama tafita.....
Tinda tafita nake zaune harna fara gyangyad’i batare da ango yashigo ba,kai tin inajiran ango har bacci ya d’aukeni saida nasamu bacci mai yawan gaske sannan nafarka waiko zanga angona yashigo amma shiru,kallon agogo nayi naga dare yayi sosai tsorone ya kamani sanadin bamsaba kwana ni d’aya agidaba,haka nafito dukda bansan 6angaren Ameena ba,can nafara jiyo kukan jaririyarta wadda take goyo sannan fahimtar inda kukan yake naimaza nadoshi inda naji kukan ,saida nabuga k’ofar d’akin sannan tazo tatambayi wanene shin lfiya?maimakon nabata amsa kawai sena fashe da matsanancinkuka,jin kuka yasa tabud’e da sauri tana riqoni da tambayata lafiya.....
Ban iya magana ba haka tashigar dani har cikin d’akinta takaini bakin gado sannan ta ajje yaron hannunta tadawo kusa dani ta zauna,kasa kallonta nayi saboda kunyarta nakeji amma haka tad’ago fuskata cikin sigar lallashi tana bani baki kannayi haquri nasamu bacci saboda gajiyar biki,kallonta nayi da mamakin yadda sauqinta yake dayawa haka,kallona tayi idonta taf da qwallah tagirgizamin kai tare da sakin murmushi alokaci d’aya tacemin”Dan Allah Nafisa kiyi Haquri ki kwantar da hankalinki bawani abu,nima randa aka kawoni ni kad’ai nakwana agidannan danshi yace atsarinsa bazaizo gun amaryarsa ba saitayi bacci ta sauke gajiyar biki dan haka kiyi haquriki baccinki segobe zaki ganshi”
Tafad’a tare da d’an bugun kafad’ata tanamin murmushi,nikuwa ban iya magana ba saboda dukna takura kunyarta ta dabaibayeni,yaronta ma d’auka danaji yana kuka amma tayimasa shiru tana qoqarind’aukomin bargo,saida ta kawomin sannan tafita.....
Tinanina ne yatafi akan to ina zataje da tsohon darenann?........
Saida ta jima sosai harna fara tinanin kodai ba lafiya,ina tsaka da tinani naji sallamarta d’ago kan dazanyi muka had’a ido da ita hannunta d’auke da faranti da lemo......
”Amshi kici.......Nasan kinajin yunwa dan amare basa zama suci abincin kirki”
Mamakine yacikani nakalli abincin,nan da nan kuwa naji kamar bakomai acikina sanadin qamshin daya bigeni mai matuqar dad’i,had’ad’d’iyar taliyace wadda taji lafiyayyen kifi da albasa sai qamshi ke tashi dukda kunyarta danake i seda nasake saboda yadda ta dage idan bazanciba zata bani jinhakan yasa nahauci banbariba seda naji cikina yayi dam....Ina gamawa nasha ruwa da lemo sannan naje nayo alwala zankwanta kamar daga sama naji tana fad’in ”Yauwa aunty amarya kozaki iya muyi sallah raka’a biyu domin neman zaman lafiya?.......
Banyi musuba haka muka idar mukayi adduoi sosai sannan na kwanta,itakuwa ragowar abincina tacinye abinka damai goyo sannan itama ta kwanta......
Tinda nakwanta nake tinanin yadda zanyi domin naga nafarantawa Ameena fiyeda yadda tayimin azamanmu danni tini tinanin ango yabarni nakoma tinanin rayuwata da abokiyar zaman arziqi ahaka har bacci mai nauyi da dad’i ya d’aukeni.
Tom na tak’aice muku ahaka muka zauna nida Ameena cikin girmama juna da mutunta junanmu baruwanmu da maganar bak’i domin mu ’yan gulma basu sami qofa awajanmuba,saboda dukanmu awaje d’aya muke zama har baqonmu ya tafi.
Ban ta6a d’arsa mugunta ko makamancin haka azuciyata ba,banta6a zaton Abba shiyake kashe yarana ba harsai ranar dana kamashi dumu-dumu yana shan jinin abokiyarr zamana wato Ameena............


’YAR GATAN MAMA✍️.
*🏡A WANI GIDA🏡*

*LABARI/ RUBUTAWA*
*KHADIJA S. SAMINU*
*(YAR GATAN MAMA)*



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*.


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

🅿️1️⃣9️⃣

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡


...... A wannan ranar hankalina ba qaramin tashi yayi ba, rsshin nutsuwa, fargaba, tsoro, razani gaba d’ayansu seda suka ziyarceni awannan lokaci nagigita matuqa, inatsaye jikin tagar d’akinnata na hangoshi tsaye akanta yarufemata fuska da farin qalle sai mutsu mutsu takeyi ahaka shikuma yashanye jininta tsaf hannuna nasaka tare da toshe bakina saboda ihun danake jinzai kufcemin saboda yadda abin yakid’imani wanda ko, a mafarki banta6a tinanin hakan daga gareshiba .
Innalillahi wa’inna ilaihi raji, un...... Kalmar datake tayawo kenan akan le66ana ziciyatace tadake na yunqura domin shiga d’akin shigata keda wuya naje natarar baya d’akin itakuma tini rai yayi halinsa, kuka nake kamar raina zai fita sabod yadda nakejin zuciyata tana rad’ad’i da zugi na rashin abokiyar zamana, alokacin yadda Abba yazama bazaka ta6a tinanin shine yai wannan ta, asarba dukya susuce yafita daga hayyacinsa baidawo dai daiba harseda akagama zaman makokin Ameena, tindaga wannan lokaci najaye jikina daga gareshi sam bana shiga harkarsa lokaci d’aya nai canzawar daba wanda zaiyi tinanin watarana zanyita dan

2 Comments On A WANI GIDA
avatar
fatima-9-7-8

1 year ago

Reply

Masha allah

avatar
fatima-9-7-8

1 year ago

Reply

Yayi dadi allah yakara basira

Please Login or Register in order to submit comment