Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kumatunta dayai jawur saboda yadda yafara sabawa da zubar ruwa.

Malam yajuyo tare da gyaran murya yace....

”Uhumm,kowane bawa da ubangijiya halitta akwai kalar jarrabawar da yake yimai,wani yacinye wani kuma yafad’a rami,yanzudai ita tafi buqatar muimata addu’ar Allah yasa ta cinye tata jarrabawar......A yadda yanayinta ya nuna tayi gamo da jinnu masu matuqar hatsari ga mutum dansu basu da buri sesu cutar dashi,amma cikin izinin Allah idan tadage da addu’a Allah zairabasu,dan ba wani abu da suka isa suyi idanba bada izininsa ba,zan aiko da rubutun da za’a ringa bata tana sha,Allah yabata lafiya”.

Haka Malam yaimusu sallama ya tafi da alqawarin zemusu aike idan yakoma gida.

Haka sukacigaba da kula da Hauwa cikin izinin ubangiji tafara samun sauqi saboda yadda aka dagemata ruwan rubutun yazama ruwan shanta gashi idan zata kwanta shi Hafsa take shafamata aduka cikinta,wuya ba dad’i zuwa yanzu zafin ciwo haryasa Hauwa tayi duhu-duhu jikinnan dukya fara baya idan ka kalleta se idanuwa wanda sune basui qasaba,amma ahakan jiki Alhamdulillahi dan sam ba wani dazai nuna akwai aljanu atare da ita.

Yau sati biyu rabonta da Haneef saboda shima bashi da lafiyar tin ranar dasuka yi damben neman ran juna,Hafsa ce yau zaune Hauwa na kwance ta d’ora kanta acinyar Hafsan suna hira gwanin ban shaawa ganin hira tayi dad’ine yasa Hafsa sakowa Hauwa hirar lafiyarta kamar haka.....

”Nikam Kulu na tambayeki,yanzu yakikejin jikinki kuma meyasa bakyason ganin Haneef yanzu....?

”Uhumm,’yar uwa kenan,zuwa yanzu hankalina yadawo jikina nasamu lafiya sosai, Haneef kuma nima bansaniba nidai tinda abinnan yafaru idannaganshi nakanji kawai idan banga yamutuba bazanji dad’iba,kuma shima na fuskanci hakanne anasa 6angaren ko.....

Hafsa ce tasake kallonta tare damata wata tambayar kamar haka.....

”Nifa Kulu kinsan abinda yake d’auremin kai,kullum tinanina idan nazauna shine,yaushe kika gamu da Aljanu?”

Itama kallonta tayi tare da sakar mata wani qayataccen murmushi wanda rabonda tayishi tin lokacin su Abba na raye tace....

” Hafsa kenan,nidama kinsan tincan baya da dad’ewa kinsan Hajiya Nafi ta ta6a cewa ina da Aljanu,kuma nima nasan haka saboda yanayin yadda nake jina,abayane basu bayyana ba yanzunma tsananin tashin hankali da damuwa ne suka tashi lokaci d’aya”

Haka dai sukaita hira tsakaninsu har fuskar Hauwa tafara canzawa tafara had’e-had’en rai,ganin haka kuwa yasa Hafsa tabar zancen ta d’auko wani zancen kamar haka....

”Nikam Hauwa ya maganar Nura,Allah sa dai abinda yafaru baisa yagudu ba.....
Tafad’a da alamun damuwa afuskarta taci gaba da fad’in......Ni kinga na kirashi tsakanin jiya da yau se d’azu yakirani yacimun mutunci yaimin gori wai shi bazai auri ’yar matsafi ba”
ta qarasa fad’a tana sakin kuka maicin rai,Kulu ce ta tashi zaune tariqe hannunta gam sannan takalleta tace....

”Haba Hafsa mezai dameki kuma?
Ki godewa Allah mahaifinki ne kad’ai bana gari ba mahafiyarki nagartacciyar macece wadda abokiyar zamanta ma tayi alfahari da ita,kiji dad’i baki d’auki mugun halin mahaifinki ba,kiji dad’i da ubangiji yabaki lafiyar da zaki yiwa iyayenki addu’a,kiji dad’i kinmallaki zuciyarki bakya aikata alfasha abayan qasa”

Farin ciki ne ya bayyana akan fuskar Hafsa dan kasa magana tayi sam kawai se rungume Hauwa tayi tana fad’in.....

”Madallah dake ’yar uwa tagari me nusar da ’yar uwarta,Hauwa rashinki ayanzu cikin rayuwata bansan yazan kasance ba......

Bata qarasa magana ba Kulu ta tareta da cewa......

”Zaki kasance kamar yadda Allah yatsara miki rayuwa cikin aminci.....
Zaki kasance cikin godiya ga mahaliccinki dan ba akanki akafara rasa d’an uwa ba.......
Zaki zamo wadda zai dingajin kunyarki kuma zai dinga biyamiki buqatunki ma’ana zai shiga cikin duka lamuranki saboda yasan baki da wani mataimaki sai shi kad’ai kinrasa kowa naki asanda kike buqatarsu,Hafsa matuqar kin dogara ga Allah ya isarmiki dan haka kimiqa duk lamiranki gareshi.....
Hafsa babu wani mai yi sai Rabbil izzati komai da nufinsa yake kasancewa,Hafsa kisa aranki koda yaushe zaki rasamu gabad’ayanmu kuma kisawa ranki haquri da juriya kiyimana addu’a.Hawayene suka zubowa Hauwa tasa hannu tagoge sannan taci gaba da fad’in....Hafsa dan Allah naroqeki kiyafemin kiyafemin duk wani abu danai miki wanda nasani dama wanda bansaniba,Hafsa inaji ajikina bazan tsawon rai ba mutuwa zanyi,Hafsa munzo duniya rana d’aya amma kowa da ranar komawarsa,zanso ace nidake rana d’aya zamu koma ga mahaliccinmu muna riqe da hannun juna.....

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.....Hafsa kiduba fa duk qaunar da mukewa junanmu bazamu tafi tareba idanma muntafi tare bazamu ta6a zama tareba kowa cikin qabarinsa daban za’asakashi shikad’ai dagashi sai halinsa zaiyi rayuwa,Hafsa rayuwarmu tafara tafiya mungirma munmallaki hankalin kanmu,Hafsa yanzu lokaci ne wanda da sonmune muna gidan mazajenmu amma kuma ubangijiyatsara mana rayuwa ahaka dan haka mugodemasa mu tsarkake zuciyoyinmu muyi aiki nagari 😭😭.

Kuka ne yaci qarfinta tayi shiru,nan kuwa suka had’u sukaita kukansu babu me rarrashin wani acikinsu.

Tin Hajjo nasa ran ganinsu hartagaji ta tashi domin tabi sawu,shigarta keda wuya ta taddasu riqe da juna se kukansu suke hankali kwance...........






’YAR GATAN MAMA✍️.
🏡A WANI GIDA 🏡



LABARI/RUBUTAWA
KHADIJA S. SAMINU
(’YAR GATAN MAMA)




*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*


Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga ubangijin halittu baki d’aya,wanda shiya halicci dukkan komai mai rai damara rai baki d’ayansu,shine mai girma wanda bashi da abokin tarayya bai haifaba kuma ba’a haifeshi ba ya gagara yacika ya bunqasa yazarce dukkan wani tinani nazari akansa sai dai imani.
Tsira da aminci su tabbata ga shugaban mutane da aljannu,tsatson larabci mai dad’ad’an kalamai,mai zazzaqar murya,wanda yatake zalunci ya shimfid’a adalci badanshiba damukai yanzuba,darajar sa da ita muke tunqawo arayuwarmu badan arziqinsa ba da tini anshafemu kamar yadda aka shafe wasu kafin mu.Allah kaqara masa girma dan girmanka,Allah kasakamana soyayyarsa dan soyayyar dakake masa,Allah kasa mudawo gareka muna masu ambatonsa SAW💖RANAR RASULILLAHI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM💖.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

🅿️2️⃣4️⃣.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Ganinsu ahaka ne yasake harzuqata ta shigar da niyar ta balbale Hafsa da fad’a dan tasan itace tazo tasata agaba suke koke koken banza da wofi,shigarta keda wuya ta tadda Hauwa ce kawai ke kukan dan ita Hafsama ahaka har bacci yasaceta.

Tausayinsu ne yakamata ganinsu ahaka sai abubuwa da dama suka fad’omata memakon takama fad’an kamar yadda tayi niya kawai seta nemi kusa da Hauwan tazauna tare da ta6ota dan batasan tai magana Hafsa ta tashi,ilekuwa juyowar da Hauwa zatayi Hafsa tai firgigit ta tashi tare da kallon Hajjo sannan ta maida kallonta ga sanyin idaniyarta Hauwa,tattausan murmushi Hauwa ta sakarmata tare da sake damqe hannunta cikin nata suna kallon juna.
Hajjo gajiya tayi da wannan kallon soyayyar da sukeyiwa juna kamar anfad’awa d’aya mutuwar d’aya tace.....

”Uhumm....Masoya wai me kuke saqawa ne haka har yasaku kuka?,kedai Kulu nasan kina da hankali ba kamar Hafsa ba itace tazo tasaki kuka ko?...

Kulu ce tai saurin kallonta tare da had’e fuska tace.....

”Haba Hajjo ’yar uwartawa kike cewa bata da hankali?
Ni ba ita tasani kuka ba kawai muntune watarana dole mutuwa zata iya rabamu ne dan haka mukafara zubar da hawayen sabo amma mu ba kuka muka zauna munayiba......ta fad’a tare da kallon Hafsa tana mata alamun shine dalilin ko?....itama d’aga kai tayi alamun wannan ne gaskiyar magana,kallonsu Hajjo tayi akaro na ba adadi sannan tace.....

”Nidai ba wani abu nakeso kugane ba illah kusa aranku ubangiji yasan daku kuma yasan halin da kuke ciki,bawai ya manta dakubane A,a yanasane wannan ma duk cikin ikonsa ne dan shine mai iko akan dukkan komai,ba akanku aka fara maraici ba balle kuce baku da kowa,idan baku mantaba Shugaban halitta gaba d’aya maraya ne kuma shi tin yana ciki d’an wata biyu mahaifinsa yabar duniya sannan mahaifiyarsama baiwani dad’e da itaba itama tabar duniya,amma me betabajin wani abu dangane da hakan ba dan yasan wannan shirin mahaliccinsa ne dan haka ku ajje maganar rashin iyayenku agefe kud’aura d’ambar yimusu addu’a badare ba rana itakad’aice soyayyar da zaku nuna musu,kai bama sukad’aiba har mariqiyarku NAFISA da abokiyat zamanta LUBABATU.......
Haka taita musu nasiha mai ratsa zuciya har lokacin sallar la’asar yayi suka tashi domin sallah,kasancewar bayi zataiba seta d’auro alwala tazauna tare d’aukar carbi tana istigfari domin tinawa da tayi da matayen zamanin Annabinmu Muhammad SAW taji ance acikinsu akwai wad’anda idan lokacin al’adarsu yayi suke kuka kamar ransu zaifita saboda suna ganin yanzu basu da ikon sallah balle suroqi ubangijibuqatarsu,basu bar baqin ciki ba har sai lokacin da aka sami mai daraja SAW da maganar nan yake cemusu subar takaici da baqin ciki bisa ga wannan lamari su sani wannan wata hanyace da ubangijiya tsaramusu domin lafiyarsu kuma yanajin kunyarsu alokacin da basu da ikon sukai goshinsu qasa suroqeshi dan haka ne yajanye hijabi tsakaninsa dasu duk wadda tad’aga hannu tayi imani dashine ke biyamata buqata bawani ba to saiji kukanta kuma zai share mata hawayenta.
Tunawa da hakanne yasa Hauwa tazauna taita miqa kukanta gareshi dantayi imani zaijita kuma zai sharemata hawayenta.
Ba ita ta tashiba harsai bayan magrib sannan ta tashi da nufin taje taga jikin Aunty Hafsa dan yau kimanin kwana uku kenan bata da lafiya.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Haneef ne zaune jikin gadon da Aunty Safiyya ke kwance dan gama shan magungunanta kenan tad’an kwanta domin tad’an matse,tashi yayi ya shiga band’aki danshi bayi sallah ba saiyanzu.

Aunty Safiyyace ta amsa sallamar dasu Kulu sukayi sannan suka shigo,taji dad’in ganinsu dan haka tatashi zaune cikin sakin fuska suka gaisa suka shiga hira gwanin ban shaawa,sun dad’e sannan sega Haneef yafito daga band’aki riqe da rigarsa ahannu yanafad’in.....
”Aunty Safiyya zafi nakeji nawatsa ruwa kibani kayan baccina nasaka”
Rufe bakinsa keda wuya suka had’a ido da Hauwa take tasakarmasa wani qayataccen murmushi saboda kwana biyu bata ganshi ba ,bata idda tinanin datake ba taji ya sakar mata wani wawan naushi wanda saida kowa ya razana jin yadda yake kaimata duka kafin suyi wani yunquri tinin Hauwa ta sume awajan....

Hankali tashe su Hajjo suka shigo Hajjo na kuka kamar ranta zai fita tana wallahi yau se anfita da Haneef.......

Tana kuka haka aka kwashi Hauwa kulu
akai asibiti da ita cikin rashin hayyaci Su Hafsa se kuka sukeyi kamar ransu zai fita,lokaci d’ya Hafsa taji wata sabuwar tsanar Haneef ta dirar mata wadda takejin ba abinda bazata iyayimasaba.

Shima Haneef yana cikin asibitin saboda ana qwatarta ahannunsa yafadi shima yasuma awajan dan haka shima akatawo dashi.

Seda Hauwa tai sati cur anakula da ita sannan akadan samu kanta.....
🏡 A WANI GIDA🏡


LABARI /RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
(’YAR GATAN MAMA)


________________________


*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*


________________________


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
🅿️2️⃣5️⃣

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Bayan sundawo gidane ciwo yadawo sabo fil wanda seda akafara kiran masu magani suna zuwa suna duba Hauwa da Haneef saboda anasan sanin mene sanadin wannan baqar gabartasu....

Wani malami Aysha tasamo wanda anan garin yake kuma yana zuwa ya ajje kayansa duka yasa aka shimfid’a mishj tafkeken buzu yabaza kayansa akai,abubuwane mabanbanta wanda kaidaga gani kasan bakayan aikin Allah bane naneman duniya ne,wata tafkekiyar qwarya ce wadda akayi rubuce-rubuce mabanbanta acikinta can gefenta kuma wasu manya-manyan layune zube dayawa sannan agefensu suma akwai gwangwani wanda akazuba wani abu acikinsa damamme kamar koko amma shi kalarsa ba fari bane yayi duhu danyafi kunun kanwa duhu ataqaice dai bawanda yasan miye aciki sai wanda ya ajjesh,agabansa kuma wani tafkeken abune maikama da sili wanda qasa ce akansa inda gefen qasar wata qwayarce batakai waccan girmaba amma itakuma ruwa ne acikinta garau-garau kamar kasha.

Bayan yagama ajje komai ne ya buqaci azo da mara lafiyar,Hauwa kulu akafara kawo masa inda zamanta kenan yafara zuba kamar antambayeshi,surutai barkatai yahau yi wanda ya dagula musu lissafi.

” SAINI ZAKI MAI TARWATSA NAMUN DAJI,NINE NAMIJI WANDA SAURAN MAZA KE TSORO,KO AQINI KO ASONI NINE SARKI,BABU MAI RAINANI SEMO RABON SHAN DUKA....!

Haka yaitaiwa kansa kirari sannan ya kalli kulu yabushe da dariya sannan yace....

”Hhhhhh.....Wannan yarinya akwai tsawon rai akwai qarfin zuciya,maija da ita saiya shirya amma badan hakaba da tini saidai labarin wata ba itaba,Shed’anun dake kanta ba qananun mugaye bane domin ta had’a ruwa biyu ne baqaqen shaid’anu da fararensu.
Suna sone su hallata baki d’ayanta kune tintini baku fahimtaba amma tadad’e tare dasu yanzuma daliline ya tasosu lokaci guda batare da sanin kowaba,dan haka wannan se anyi akanta sosai.......

Ba wata qulalliyar tsana dake tsakaninta da wannan yaron,to ai abinda nakeso kugane ma ba wani abu baneba sedai inaso kusani wannan yaron da kuka 6oye ba cikakken mutum bane yanada ji6i da shaid’anu wad’anda sukayi qungiya ajikinsa kuma runduna guda wanda harsunfi qarfin kansa gashi sunyimai illah saboda sunason sujuyashi yakoma cikinsu....
Akwai wani sirri atattare dashi kuma sirrin bazai fad’u yanzuba dan haka senafara magana da wannan mara lafiyar....


Kulu ya kalla ya d’auki wani magani ya watsa agarwashi sannan ya saita hancin Kulu dashi,Shaqar qamshinnan da tayi keda wuya ta zabura ta miqe tsaye kamar wadda aka zungureta,ganin hakane yadaka mata tsawa wadda bata shiryaba tadawo inda take ta zauna,sake d’iban maganin yayi yazuba awutar sannan ya kalleta yace da ita......

”Shin wanene kai?
kuma daga ina kake?
Sannan meyasa kake zaune ajikinta?

Kafin yagama magana tini Hauwa tafara magana kamar haka.....

”Hhhhhhh.....Na raina tinaninka da kakeson kaja dani,kuma saina hukuntaka sanadin shiga gonata da kayi”

”Shin wacece gonar taka?
Shima ya tareshi azafafe kamar zai kaimasa duka....
”Kulu ce Gona ta mana,itace matar danakeso kuma nake da burin aura yanzu haka akwai sa ranata akanta,Kuma karkayi yunqurin rabani da ita domin bazakaci riba ba,shima wancan wawan dayake sonta sainaga bayanshi bazan qyaleshiba dannaga yafara tinanin yacini da yaqi toyagane sam ba haka bane ba nabashi damane kuma dazarar ta qare daga ranar yagama yawo,yafad’a yana nuna Haneef da yatsa.

Haka yaita masa tambayoyi yana amsawa kafin daga bisani
🏡 A WANI GIDA🏡



LABARI /RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
(’YAR GATAN MAMA)




*__________________

___________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*.



DUBUN GAISUWATA AGAREKU ’YAN QUNGIYAR KAINUWAR WRITERS ASSOCIATION,ALLAH YADADA DAUKAKA YAQARA ARZIQI💖💞💞.


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

🅿️2️⃣6️⃣.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡


Haka yaitayimasa tambayoyi kafin daga bisani yasake kallonsa yabushe da wata mahaukaciyar dariya ya kalli su Hajjo yace dasu su matso suga wani abu.
Wannan qwaryar ya d’auko wadda ruwane acikinta ana ganinsa garau ba wani abu ko datti acikinsa,matso da qwaryar yayi inda Hauwa take azaune ya saita qwaryar dai-dai fuskarta sannan ya buqaci su kalli cikin qwaryar........

Hajjo ce tafara ja da baya da sauri tana fad’in....

” Hasbunallahu waniimal wakil ,d’an magori me nake gani wannan...?”
Bushewa yayi da razannanniyar dariya sannan yace sunutsu suji bayanin dazai musu.......

”Wannan fuskar da kuka gani ta razanaku to itace fuskar da yaronku Haneef yake gani aduk sanda suka had’u,kuma itama abinda take gani kenan,kowanne yanayiwa kowa kallon yazone ya cutar dashi to hakan da suke ganine yakesa suke neman ran junansu....
Haka yaitamusu bayani kafin ya had’a kayan aikinsa yatafi yabasu magunguna tare da sharad’in idan anga wani abu nanda kwana uku asanar dashi da wuri tinkafin abin yayi nisa.
Sunyi masa alkarai masu yawa kafin yatafi sunata godiya akakwashi Hauwa akayi d’akinsu da ita saboda bata cikin hayyacinta gaba d’aya.

Yau duk cikin yanayi mara dad’i suka kwana
saboda duk lamarin Hauwa ya dagula musu lissafi yau tinda suka kwanta taketa mafarkai masu saka surutai kuma da alamu arazane take gabad’aya dan alamun tsoro duka sun bayyana afuskarta, daga bisani ne sukaga takoma kamar tana fad’a tana ciccijewa da had’e fuska tare da dunqule hannu kamar mekaiwa wani naushj yaudai ahaka ta kwana awahalce babu wani dad’i acikin baccinnata nayau.

Hafsa tinda suka idar da sallah take zaune tana kuka tana kaiwa Allah kukanta tare da roqonsa yasa wannan lamari yazo qarshe kosayi ibadarsu cikin nutsuwa.

Hakama Hajjo ba abinda takeyi sejan carbi tana addu’o’i tinda tasan babu abinda yafi addu’a.

Misalin bakwai na safe Su Hafsa na zaune inda suke kan sallaya batare dasun kula da tashin Hauwa ba Hauwan tafice daga d’akin, fitarta keda wuya tasa makulli ta kullesu ta waje sannan tayi gaba.......


Aunty Safiyyace ta tawo 6angarennasu domin taga ya Hauwa ta kwana kawai sukayi karo da ita abakin qofa tana kullewa ganinta datayi hakan yasa tasaki makullin qasa batare da ta saniba tabarta anan tayi wucewarta ganin haka sai Aunty Safiyya batai mata maganaba danta lura abirkice take, Shigatayi cikin d’akinnasu tatsaya abakin qofa danbatason Hauwa tafuskanci wani abu tana leqowa taga Hauwa tamiqe tayi sashen Abbansu gadan-gadan ganin haka yasa tabita ahankali tana 6uya yadda bazata ganta ba, makulli taga tasaka ta bud’e d’akin Abba kawai tasa kai ciki........

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Hafsa ce taji motsi alamun anshigo ko an fita saboda taji anbude qofa anrufe dan haka tamiqe dantaga waya shigo yakoma, Hajjo ce tabiyota tana tambayar shin lafiya?
Jin shiru yasa ta duba gado bataga Hauwa ba tashiga band’aki nanma batanan gashi Hafsa ma tafice dan haka kawai itama seta fito dantaga ina sukayi da sanyin safiyar nan haka......

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Tinda Kulu ta shiga kanta yake juyawa d’akin gaba d’aya juyamata yakeyi jitake kamar asama take ba’a qasaba amma haka takutsa har cikin d’akin baccin Abba wanda duk yayi qura saboda dad’ewa batare da mutum acikiba, saida tasha wahala wajan bud’e-bud’en lokoki amma bataga abinda take nema ba, gajiyatayi dan haka tad’an zauna tana hutawa kafin can kamar an mintsineta tamiqe da sauri tare da duba cikin kwabar Abba amma nanma bata ganiba dan haka kawai se tinaninta yabata ta d’aga katifar gadonsa ko zata gani, bata 6ata lokacibs wajan amfani da shawarar da zuciyarta ta bata nan da nan tad’ata cikin karsashi da dakewar zuciya.......

Ita kanta batasan sanda takama dariya ba sakamakon ganin abinda take nema, saka hannu tayi tad’auka tare da mayar da katifar tad’asu sama tana karkad’awa makulli d’ayane yacire daga jerin ’yan uwansa yafad’i qasa batare data luraba haka tafito da sauran na hannunta tayi bayan d’akunan duk batasan Aunty Safiyya da Hafsa suna biye da itaba......

Tsayawa tayi abakin qofar tana tinani tare da dafe kanta, maganar Abba ta tuno wadda bazata ta6a mantawa da itaba.......

”Kuma wannan maganar da mukayi dake yanzu ina mai tabbatarmiki idan kika bari wani yaji tom banyafe miki ba, nace ban yafemiki ba, Kulu inamai tabbatar miki da cewa zan iya yin komai haka zan iya aikata komai akan naga na6oye wannan 6oyayyen sirrin nawa, Haba Kulu kitina nifa mahaifinki idan baki rufamin asiri ba wazaki rufawa?, kowa dakike gani bayannine dan haka inamai roqonki kiduba Allah kibarwa cikinki, idan kuma ba hakaba ni zan iya cireki daga cikin ’ya’yana”

Dafe kanta sanadin jinda tayi ya sara mata kamar zai tsage, dafeshi ta sakeyi kafin taji wasu zafafan hawaye suna gangarowa kan kumatunta, maganganu takamayi ita d’aya tana cigaba da kukanta......

”Lallai Abba ka zaluncemu, kuma alqawarin danai maka yau zan karyashi danyau na quduri aniyar ko numfashina zai qare sena shiga wannan d’akin wanda har kake iqirarin zaka iya cireni acikin yaranka toyau nashiryawa koma miye dan ayau nakeson nakawo qarshen zaluncinka Abbana”

Tafad’a tare dasaka hannu ta toshe bakinta saboda kukan dataji zai qwace mata.....

Hafsace ta kalli Aunty Safiyya tare dacemata.....

”Aunty Safiyya farko nayi tinanin Hauwa ciwonta ne yatashi, amma yanzu na fuskanci garau take tashirya kawo qarshen tashin hankalin gidannan, ko bakiji kalamanta ba?
Aunty Safiyya dani aka fara wannan lamarin dan haka kitsaya ki kallo dani za, a qareshi.... ”

Tana gama magana bata jira amsar Aunty Safiyya ba tawuce inda Hauwa ke tsaye tana qoqarin bud’e d’akin sirrin Abba......
”Kulu kawo nabud’e da hannuna zuwa yanzu batsoro atare dani”
Kallonta Kulu tayi batare da tayimata maganaba ta girgiza mata kai tare da sakar mata murmushi tai bismillah sannan ta murd’a kubar d’akin........
Wani irin warine ya doki hancinansu gaba d’aya seda sukayi baya kafin su toshe hancinansu su danna kai ciki.......



Kuyi Haquri masoyana aski yazo gaban goshi dan haka kubiyoni......

Comment dinku suna sani nishad’i inajin dadi Allah yabar zumunci🥰💖💞💞.
Ummuna Allah yabaki lafiya tare daduk al,ummar musulmai baki d’aya👏💖💞💞.



















































’YAR GATAN MAMA✍️.
🏡 A WANI GIDA🏡



LABARI /RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
(’YAR GATAN MAMA)


_________________________


*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*


_________________________


Dan Allah kuyi haquri yadda kwana biyu kuka jini shiru hakan yafaru ne sanadin ciwon da Ummuna takeyi sam banda nutsuwar zama nayi Typing, amma zuwa yanzu jikinta Alhamdulillahi 👏.
Masu kirana suyimin yamai jiki da wanda ma basu kirani ba naga saqonku kuma nagode sosai Allah yabar zumunci 🤝🥰💞💞
Son So fisabilillahi❤️.

🅿️2️⃣7️⃣.



Kallon Hafsa tayi batare da tacemata komai ba tasakar mata murmushj sannan tayi Bismillah tamurd’a kubar d’akin, wani warine mai hawa kai wanda ke saurin saka ciwon kai shine yadoki k’ofofin hancinansu wanda sanadin hakan suka dawo da baya take, dawowarsu keda wuya sukaja d’ankwalayensu tare da toshe hancinansu suka danna kai cikin d’akin.
Wani matsanancin duwune yayiwa idanuwansu kwalli yadda ko tafin hannunsu basa iya gani saboda yadda d’akin yake baka iya ganin komai, Kuluce tasaka hannunta ciwon aljihun dake mak’ale ajikin rigarta tazaro tamfatsetsiyar wayarta tare da kunna fitila mai hasken gaske wanda yamamaye ilahirin d’akin yadda kana iya kallon abinda ido zai iya gani, Hafsa ce tarafa ganin inda makunnin yake nan da nan tayi wajen tare da kunna fitilar aikwa take haske yabayyana , se asannan Hauwa takashe fitilar wayarta tare da maidata aljihun ta kalli Hafsa tare dayimata alamun muyi abinda yakawomu.
Babban falone wanda girmansa yakai afad’eshi kuma ank’awatashi da manyan kujeru na alfarma ga tamfatsetsiyar talebijin amanne ajikin bangon kayan ado na falo babu wanda babu aciki, ba abinda su Hauwa keyi sebin falon da kallo kowa mamaki yarufeshi abinda suke tinani tomiye ke wari?, Hauwa ce takalli mukallayen hannunta tare da kallon d’akunan dake jere acikin falon wanda duk suke akulle gasunan guda hud’u reras sanin abinda ke cikine sai Allah.

********

Hauwa ce ta kalli Hafsa tare cemata,
”Yauwa, ’yar uwa yakike gani, mushiga duka tare ko kuma muraba nashiga d’aya kishiga d’aya? ”,
Kallonta itama tare da jijjiga kai tana fad’in,
”Aa gaskiya duk mushiga tare gudun karmu kasa hankulanmu ina ganin mushiga tare”
Ta bata amsa kamar yadda buqata, hakan kuwa akayi tasaka mukulli tabud’e qofar tare dayin Bismillah tatura qofar tasa kai ciki bakinta d’auke da ambaton ubangiji wanda a6angaren Hafsama abinda takeyi kenan addu’a.
Mamakine ya mamaye zuciyoyinsu lokaci guda sanda idanuwansu suka kai kan kud’ad’en dake barbaje ad’akin suncika wajan takansu kakebi k ana takawa dan duk ilahirin d’akin kud’ine wanda sai kanka yajuye saboda yawansu, Hauwa ce ta numfasa tare da girgiza kai tana qaremusu kallo.

”Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Hauwa duba saman d’akinnan kiga tanan kud’in ke zuba”

Hafsa ta fad’a jikinta yana rawa kamar mazari sabida yadda lamarin ya girgizata.
”Ke dalla matsoraciya, kikace yanzu baki da tsoro amma mene haka, kitina d’akuna hud’u zamu shiga dan haka kishirya ganin al’ajabai dannan baki ga komai ba malama.... ”, Hauwa tana fad’in haka tajuya tafice ad’akin inda itama bayadda zatayi haka tabiyota suka fita tare......
’Dakin kusa dashi tasake bud’wa suka shiga inda suka ga abinda yakuma kulle musu kai.

***********

Wani ramfatsetsen kafetne jajur dashi sai maiqo yakeyi inda dole sekabi takansa kafin katadda inda kayayyaki ke ajje acan qaeshen d’akin, Hauwa ce tafara saka qafarta akai inda tajita kamar tana taka ruwa bin qafafunsu tayi da kallo ga mamakinta setaga duk sunrine sunsha jini, se sannan suka lura ashe d’akin duk jini ne aciki, jikin bangon duk anzana qwarangwal idanuwansu da bakunansu jajaye komai jajayene aciki.
Hafsa ce tasa hannu tare dayin Bismillah tabud’e wata durowa dake jikin bango kawai sega qwarya tafad’o cike da jini yana zubowa, tsoro yagama kamasu amma duk da haka sunkasa fita seda suka gama ganin komai sannan suka nufi d’aki na uku.

***********

Suna shiga bakomai ne acikiba se wani qaton qwarangwal wanda aka ajjeshi sak Abbah wanda hakanne yai sanadin fitowar tsoronsu fili suka razana dan tinaninsu Abba ne yamusu fatalwa yashigo d’akin, sun tsorota matuqa amma dake akwai addu’o’i abakinsu kawai suka nemi qwarangwal suka rasa sama ko qasa bayanan haka sukacigaba da ambaton Allah har suka gama shiga d’akin.....
Bakomai ne aciki ba qasusuwan mutane gasunan abarbaje duk sunbushe raqayau kana takawa suna qara.
”Hauwa mu hanzarta muje wancan d’akin nafi tinanin acanne warin yake fitowa ”
Hafsa ta kalli Hauwa tana fad’i da iya gaskiyarta.
”Uhumm, kibi asannu zamu shiga, biiznillahi daga yau zamu kawo qarshen badaqalar gidannan karki damu”,
Itama Kulu tamayar mata kamar yadda tabuqata.

**********

Ba mukullin da basu gwadaba amma kowanne yaqi bud’e d’akin, cike da damuwa Hauwa ta kalli Hafsa tare dacewa.....
”Hafsa ina tinanin mukoma d’akin Abba muduba ko’ina munemoshi.... Haka suka koma ba abinda basu dubaba haka suka dawo cike da damuwa sannan suka fara lalubensa anan.
Basu sameshiba se ad’aki na uku inda suka tadda qasusuwa haka suka shiga bud’e-bud’e amma basu gani ba, Hafsace ta tawo da baya baya batare xata luraba kawai sukayi karo da wata ’yar qaramar qwarya wadda aka rufeta da wani jan yanki, seda takira Allah kafin tayaye yankin daga kai aikam ba zato ba tsammani kawai sega makullaye aciki

2 Comments On A WANI GIDA
avatar
fatima-9-7-8

1 year ago

Reply

Masha allah

avatar
fatima-9-7-8

1 year ago

Reply

Yayi dadi allah yakara basira

Please Login or Register in order to submit comment