Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar suyi magana sunyi lutsu-lutsu acikin jini kamar nama amiya.
Hannu tasaka tatsamo tare da nunawa Kulu tana dariya kamar tana da tabbacin shidinne.
kar6a tayi sannan suka fita suna masu jin dad’in Allah yanunamusu batare da sunsha wuyaba.
Sun gwada bud’ewa amma duk sunqi se ana biyun qarshe kawai seya bud’e.

******
Mahaukacin wari ne yabigisu mai d’aga hankali inda suka gama shiga d’akin fitilun ciki suka kunna inda d’akin yahad’e yayi jajur dashi kamar me.
”Wato Abba ba qaramin matsafi bane ba kenan, fitilun d’akima na tsafine, Astagfirullah.... ”,
Hafsace ke fad’i azuciyarta batasan yafito filiba.
”Lallai ke yarinyar nan kina wasa nifa dakika ganni nan yanzu babu abinda zai girgizani na saba ganin case wanda sukafi wannan hargitsi dan haka ai ragowane”Kulu tafad’a tare da kunna fitilar wayarta dan bazata juri ganin wannan jan hasken ba.

**********

Babu komai ad’akin banda sassan jikin mutane kowane iri wasu gasunan mutane amma bazaka gane waye ba saboda zakaga ancire idanuwa, kunnuwa, hancina, farcina, wani kaga anbud’e kansa and’auki wani abin, wanikuma cikinsa afarke gasunan dai duk bazaka ta6a gane wani acikiba sedai ma kaji tsoro. Haka sukaita ganin abubuwa daban-daban wanda mara imanin ubansu ya aikata.....

Sai da suka gama ganin komai suka fito ransu a6ace kowa ransa ba dad’i. Hauwa ce ta kalli Hafsa tace mata.....

”Hafsa maza kishiga ki d’aukomana hijabi kizo mui sauri mudawo”
Kallonta tayi tare da alamun tanaso tai magana tai maza ta dakatar da ita da fad’in....
”Kinga Hafsa banason wata magana kiyi yadda nace kinsan dai baki fini sanin aikina ba ”,
Batai musu ba taihanyar d’akinsu hartana tinti6e.

***********

”Zonan Hafsa!”
Abinda Hajja tafad’a kenan sanda taji shigowar Hafsa sad’af-sad’af batason aganta.
A birkice ta juyo tare da tsugunawa gaban Hajja tace.
”Hajjajunmu tsowuwa mai ran qarfe,kinganmu munacan muna shawara,kinsan yau NURA zaizo shine Hauwa tace zatayo siyayya awaje tanason tamai kayan shan ruwa yace yau yana azumi,to shinefa bazan barta tafita itakad’ai ba senace zanrakata”
Kallonta Hajja tayi tayi murmushi tare da fad’in.....
”Yauwa yarinyar kirki kinkyauta ainasha kinacan kuna shirme,to sekun dawo Allah yatsaremin ku”
Ta fad’a tare da tashi itama ta zagaya.
Cike da murnar tayadda da qaryar datayimata tafito dauke da hijab da mayafi,tana zuwa tamiqowa Hauwa mayafin itakuma tafara qoqarin saka hijab.
Hauwa ce ta zabura tafige tajefar da mayafin qasa tana fad’in”Lallaima yarinyar nan kin rainani nizaki bawa mayafi kisa hijab”,Tafad’a tana saka hijabin .........







’YAR GATAN MAMA✍️.
🏡A WANI GIDA🏡




LABARI /RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
(’YAR GATAN MAMA)





_________________________



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*


🏡🏡END🏡🏡
_________________________


Kainuwa✍️✍️✍️✍️✍️
Kainuwa✍️✍️✍️✍️✍️
Kainuwa dashen Allah ba dashen mutum ba,,, Eh💃
Writers Association yau muna ba,,,,, Eh💃
Sake fadamusu, Qara fadamusu gad’an zaki yayi girma🗣️
Inkaji wane to wane ne baizoba💃💃💃💃💃.


🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

🅿️2️⃣8️⃣.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡


Bayan tasakane kawai taiwucewarta batare data kula Hafsanba,ganin haka yasa Hafsa dariya tare da yafa mayafin tabi bayanta.

********

”Ka dan Allah Momy yazakice haka bayan zamanmu agidannan baikawo mana wata matsalaba?,kuma Momy ni aganina komawarmu gida kamar tonawa kanmu asiri zamuyi saboda kinsan labarin Abbansu Kulu ba inda baizagayeba,amma Momy na barki kiyi tinani”
Ayshace ke magana inda ta sunkuyar da kanta tana mai kallon yatsun hannunta tare dayima mahaifiyarta wadda takira da Momy magana,Momy ce ta kalleta aharzuqe tare da cewa.
”Uhumm,,,,,Aysha ke yarinya ce shiyasa bazaku gane abinda nake nufi ba,ni habaici da zund’e duk bazasu d’agamin hankali kamar yadda halin d’an uwana yarabani da shiba,zamana agidannan gani nake kamar nima aikata abinda yayi nakeyi saboda duka banyarda da gidanba gani nake zamanmu acikin gidanma yarigada ya haramta”
Haka dai sukaita tattaunawa tsakaninsu kafin su tsayarda magana d’aya akan gobe zasu kkoma garinsu.

******
Tunfitarsu Hafsa ke tambayar Hauwa ina zasuje amma tayimata shiru kamar bada ita take magana ba.

”Kai Aunty Hauwa kikulani mana”,Ta fad’a tare da kwantar dakai ita adole setaji inda zasuje....
”Malama Kin isheni fa da tambaya,yau ko sedaki zanyi se haka,to ba wani guri zamujeba gidan Malam Liman zamuje mutawo dashi”,ai kafin Hafsa tasake wata magana ma tini sun iso qofar gidan,da sallama suka shiga gidan suka gaggaisa sannan akayimusu iso turakar Liman.

”Assalamu alaikum”
Suka had’a baki wajan yin sallama inda Liman ya amsa musu da ”Amin waalaikumussalamu ”.
”Sannunku da zuwa ’yan biyu kyautar Allah”
Murmushi sukayi tare da zama suna fuskantar Liman,Hauwa ce ta kalli Hafsa sannan tamaida dubanta ga Liman tafara cewa.......
”Malam sannu da qoqari, Malam dama ba wani abune yakawomuba illa zancen dakasani watannin baya akan d’akin sirrin mahaifinmu......
Aibatakai inda takeson tsayawaba ya dakatar da ita da fad’in...... ”Dakin yabud’ene?, kuma me kuka gani acikinsa?


*******

Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, abinda bakunansu keta maimaitawa kenan sanda Aunty Safiyya ta sanar dasu Hauwa ta bud’e d’akin sirrin Abba kuma sunshiga itada Hafsa, Hajjo jikinta se 6ari yakeyi tarasa ina zatasaka kanta duk tabi tagama rud’ewa sai surutai takeyi tana shassheqar kuka tana fad’in.....
”Wannan rashin imani dayawa yake, Shikuwa Abba Hasafi ina zaikai zunubi ranar gobe qiyama?, mai zaicewa mahaliccinsa?, Innalillahi wa’inna ilaihi rajiun, ace bawa bazai tina mutuwarsaba yaugashi yamutu yabar duk wata dukiya daya tara kuma bata amfaneshi da komai ba setarin nadama, Ni HAUWA’U naga tashin hankali yau yanzu acikin qasusuwan dake d’akinsa bazaarasa na yarinyata AMINA ba, Allah ya isa tsakaninmu da wannan azzalumin yaro....... ”
Haka taita surutai barkatai kamar wadda tafara samun matsalar qwaqwalwa ba ita tayi shiru ba harseda su Momyn Aysha suka rufa akanta suna tausarta sannan tadaina surutai amma duk da haka bata daina kukaba.

*******

”Aa malam ba d’akinne yabud’e da kansaba, adaren jiya nakwana banajin dad’in jikina sannan ban iya wani baccin arziqiba, ba abinda nake sai razana da firgita ga fad’uwar gaba, acikin wannan yanayi bacci mai nauyi ya d’aukeni, banjima ina baccinba senayi mafarki da Abbanmu.........
Tana zuwa nan kawa seta fashe da kuka mai tsuma zuciya tare da kifa kanta kafad’ar Hafsa, idan hankalin Hafsa yayi dubu to babu wanda baitashi ba acikinsu dn gaba d’aya tsorone yasake shigarta lokaci guda saboda tasan kukan Kulu ba lafiya baneba, dan idan harkaga Hauwa na kuka ti tabbas abu yakai Innalillahi.......
Malam ne yayi gyaran murya tare da cewa.....
”Allah yana tare da masu gaskiya, dan haka kinutsu kiyimana bayanin meke faruwa ”
Dagowa tayi ta kallesu duk da muryarta tafara disashewa haka taci gaba....
”Allah shigafarta malam, abin yamatuqar d’agamin hankali, Abbanmu da yake fari kyakkyawa amma shina gani amummunar kama, Farko naje hucewa takusa dawani kogo inacikin shiga ta alfarma kawai saiji nayi ana qwalamin kira da sunan da Abbana ke kirana wato HASSANA, juyawa nayi afirgice saboda nasan yarigada yarasu amma dukda tinanin danayi bai hanani juyawa gareshi ba, juyawar danayi itace tai sanadin ganinsa acikin suffar ban tsoro, gaba d’aya Abba yajuye daga kamanninsa yakoma baqiqqirin kamar gawayi babu wani abu dayake fari ajikinsa hatta ratsin farin dake cikin idon mutum banganiba a idonsa danshi suffarsama bazakace ta mutum bace ba.
Bud’ar bakinsa secewa yayi......
”Hasana ina neman yafiyarku kuma ina neman adduarku gareni sannan ayanzu inason duk yadda zaayi ayi kozan samu salama, Hasana tinda nabar rayuwa nake cikin wahala da azaba da danasani wanda bazasu amfaniba, bani da wani abinci kosha se ruwan qurji me matuqar wari wanda kafin nashashi warinsa seya bugaddani nafad’i na suma, sannan idan nafarfad’o haka zansake d’agashi saboda tsananin yunwa da qishirwa Hasana bazan iya fad’amiki azabobin danake sha awajannan ba, yanzuma Allah ne yasoni da rahama dahar yahad’ani dake na nemi yafiyarki dannasan koke kad’ai kika yafeni zan samu sassauci duk da nikaina bansan iya adadin wanda na zaluntaba amma kuma sannan zanbaki saqo........! ”
”Malam Anan yatsayamin dan yana fad’in abinda yakesonfad’amin kawai bazato ba tsammani sejin wani sauti mukayi wanda yake saka kunne cikin rud’ani, wasu manya-manyan duwatsu ne na wuta wanda banta6a ganin irinsu ba, daga inda nake inajiyo wuci da zafin wutar dake jikin dutsen tana zuwa inda nake, tsoronane yaqaru sanda naga Abba yakurma wani ihu wanda duka wajan seda ya amsa sanda duwatsu suka iso daf dashi suka sakashi atsakiya shikuma se kurma ihu yakeyi dawahalalliyar murya wadda kanaji kasan me ita yanacikin mawuyacin hali, haka yaita rusa ihu har muryarsa tadena fita inda kuma wucin wutarnan ke ratsa sassan jikinsa kafin ka ankara tini iya wucin wutarnan yagama janye jikin Abba, ban ankaraba segani nayi tundaga kan fatarsa har zuwa naman jikinsa haka yake zuba aqasa kamar anacire naman rago, tsoro da razani ne suka shigeni inda lokaci d’aya imanina ya hauhawa nakuma gasgata Allah sarkin sarakuna, kafin qiftawar ido tini Abba yazama labari se qasusuwa dasuka zube aqasa, dukda haka suma baarabu dasuba nan duwatsun suka gangara kansu inda komai yazama ba komai ba, jirine yafara d’ibana nan n riqe kaina wanda yake sarawa tare da kiran sunan Allah, juyawa nayi da niyyar naga mezan gani abayana kawai senaganni ad’akinmu wanda hakanne ya tabbatarmin dana farka daga mafarkin danakeyi, nan natashi afirgice kaina kamar yacire saboda na tsorata da abinda nagani amafarkina akan Abbanmu....... Allah gafarta malam kaji abinda yasani nadage seda nabud’e d’akin surrin Abba saboda inason komai yazo ”

”Innalillahi wa’inna ilaihi rajiun, abinda malam yaita maimaitawa kenan kafin yatashi yafita daga zauren........

Fitowa yayi inda mutanen gidan suke zaune tare da fad’in......
”Am,,,, Ina IBRAHIM Yake?, kuma AUWALU yadawo? ”
Wani matashin saurayi ne ya amsa masa da cewa....
”Allah gafarta malam,,,, Ibrahim yana nan qwar gida shida masu d’aukar darasi, shikuma Auwalu yaje anguwa yana dawowa”
Jin haka yasa malam yace yataso zasuje wani waje sudawo sannan yatura yace akirawo su Hauwa su tafi.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Suna shiga gidan suka iske tashin hankali wanda ba’a samasa rana, 6angaren Hajiya Nafine gaba d’ayanshi yakama dawuta kamar anasaka mata makamashi haka take ruruwa alhalin kasheta akeyi, nan Malam yasa su Ibrahim suje akashe wutar amma taqi mutuwa sam saima qaruwa datakeyi .
Ibrahim ne yakalli malam tare da cewa.....
”Ranka shi dade baranakira su Auwalu su qaraso ”
Gyad’a masa kai kawai malam yayi batare dayace komai ba.
Haka kuwa akayi su Auwalu sukazo kowa yad’auki iya inda zai iya daga ciki alqur’ani mau girma inda kafin kace me sukafara karatun sauka baji ba gani.

******

Abikice ya shigo cikin gidan kamar anhankad’oshi, kai daga ganinsa zaka tabbatar da cewa wannan ba kowa bane se mahaukacin daya dad’e yana hauka, kowa shi yake kallo saboda ayanayin daya shigo dole mutum yafirgita saboda gaba d’aya babu alamar nutsuwa tattare dashi, ganin wasu daga ciki masu karatu suntsaya kallonshi yasa malam yayi gyaran murya kowa yaci gaba.

**********

”NINE QAURA NAMIJIN MAZAJE, NAMIJIN MAZAJE SHEGEN DAJI, BANSAN TAUSAYIBA BALLE NA TAUSAYAWA WANINA, BANSON SABO BA BALLE NA TINA TARAYYARMU DA WANI NI QAURA WAZAIJA DANI”

Haka mahaukacin yadage yaita surfawa kansa kirari tare dazagaye wajan yana gudu yana cigaba da surutansa.

Haneef ne kwance akan tabarma kusa da malm Aunty safiyya tana shafamasa ruwan rubutu ajikinsa yafarka arazane inda malam yayi hanzarin tofa masa addu’a takoma ya kwanta kamar wani mamaci.

Hajjoce ta kalli Qaura tare da cewa...
”Bawan Allah daga ina haka kayimana magana”
Bushewa yayi da mahaukaciyar dariya tare da fad’in ”INA LUBA.....!!? ”
saida gidan ya amsa kafin Hajjo tayimasa bayanin yadda akayi gabad’aya dama yadda akayi Luba tamutu mutuwar hulaqanci, jikinsa ne yayi sanyi inda yayi ragwaf yazauna kawai ba zato ba tsammani akaga yarushe da kuka, nan shima yabasu labarin shine QAURA mai yiwa Luba aiki kuma shine yaturowa Haneef Mugayen Aljanu masu cutarwa wanda tinkafin ahaifeshi har yagirma basu rabu dashi ba. Hajjoce cikin 6acin rai tadubi QAURA sannan tadubi sauran mutanen dake wajan tace........
”Yanzunnan base anjima ba, inason akamamin wannan azzalumin akaishi ga hukuma aganamasa azaba harsai ya kwance qullin dayayiwa jikana sannan ayankemasa hukunci.... ”.
Hankalinsane yatashi lokacin dayaga gadan-gadan qatti sunnufoshi zasu damqeshi nan da nan beyi wata-wata ba yamiqe yana d’agamusu hannu alamar tare da alamar su tsaya base sun kamashi ba.
Daga murya yai yakama cewa suyi haquri yanzu zai kwance duk abinda yaiwa Haneef.
Haka kuwa akayi cikin izinin ubangiji yayi duk abinda zaiyi nan kuwa Haneef yakama kyarma harseda yayi bacci, Haneef nayin Bacci Jikin QAURA yafara rawa nan yakama ihu tare dayin sashen d’akin abba da gudu yana kurma ihu kamar ransa zaifita yaicikin sashen Abba cikin yanayi mara dad’i mara dad’in fad’i, shigarsa keda wuya wajan gaba d’aya yakama da wuta kowa yanajin ihunsa amma haka malam yace arabu dashi wannan duk ikon Allah ne sunajin haka masu sauka sukacigaba da karatunsu.

Wannan kenan........

**********

Kafin agama karatu tini Hauwa tasa masu aikinsu sunyi had’ad’d’en girki wanda kaji suka wadata aciki, nan aka shiga rabo gida yazama kamar taron biki sannan malama yayi gyaran murya yafara magana kamar haka.
”Da sunan Allah mai rahama mai jin qai, Bayada duba da yadda ALHAJI MUSTAPHA ADAM(ABBA HASAFI)ya tsara rayuwarsa gaba d’aya bai tsarata bisa qa’ida ba, idan muka duba duka wani abu da aka mallaka awannan gida an mallakeshine bata hanya maikyauba, antarasu da jinin mutane mabanbanta. Idan aqa’ida zamubi zaman gidannan ma ya haramta agareku baki d’ayanku amma saboda wani dalili bazakubar gidanba idan akayi duba da yadda kuka taso, Mahaifinku tinkafin yayi aure yashiga qungiyar danasani kuma dukkan dukiyarsa ta haram ce sannan ku dakuke iyalansa kun rayu acikin haram tindaga abincinku suturarku ilimjnku duk da bada kud’in halak kukayiba, kuma rayuwar dakukayi cikin kud’in haram bazaisa hakan bazaisa atuhumeku ba balle ayimuku azaba akan hakan saboda ku baku sani ba, sanda kuka sani kuma kunsani aqurarren lokaci kuma gashi bakuda wani arziqi wnda bana mahaifinku ba, da ace kuna da wani matsuguni wanda badaga hannunsa yafitoba daseku koma can da zama to amma lamarinku yazama lalura dan haka zaku iya zama acikin gidannan harsanda allah zai budamuku kuma kumallaki naku na halak.
Hakadai Malam yaita musu bayani tare da nasiha mai ratsa zuciya ahaka haryai musu sallama aka tafi aka barsu.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Haka suka cigaba da gudanar da gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da nutsuwa batare da fargabar komai ba kowa yanajin dad’in rayuwa acikinsu, inda Hafsa ita tatafi qaro karatu hauwa kuma nazaune itada Hajjo a6angarensu dan yanzu 6angare d’aya suka d’auka yazama nasu, Aunty Safiyyama tasami d’aya daga cikin mutanen Malam Liman ta aura dake talakane Hajjo tace sud’auki 6angare d’aya su zauna aciki da mijinta.
Haka itama 6angaren Hafsa acan qasar dataje Allah yahad’ata da wani Babban Alhaji wanda kowa yaimasa shedar arziqi dan dafarko qin yaddatayi wai ita yanzu tsoron masu kud’i takeyi tindaga kan mahaifinta dan haka itama antsaida ranar auranta rana d’aya da Hauwa kulu saboda itama anan shirin biki suke da NURADDEN d’inta masoyin amana wanda wani abu baira6a sawa yaji zai rabu da itaba dan haka haryanzu suna tare bakamar saurayin Hafsaba wanda dayaji halin ubansu yarabu da ita dukda masifar sonsa datakeyi amma yanzu Allah ya musanya mata da mafi alkairinsa.
Haka kuwa akayi bayan watannin dasuka shud’e Hafsa tadawo Malam liman yazama wakilinsu yabada auransu inda shima aka d’aura nasa auran da Hajjo saboda asake qullah zumunci.

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Hafsa ce ta kalli Hauwa cikin zolaya takama cewa.....
”Uhumm,,,,,, nikam Hauwa dan Allah mekike cine agidannan naga kullum se qara kyau kikeyi kamar..... ”
Aibata rufe baki ba taji kamar daga sama Nura na fad’in.....
”Ba abinda takeci sai ladabi biyayya, kuma tazauna dakowa da zuciya d’aya, sannan bata kwana da wani aranta, kuma sam bata bari lokacin sallah yafita batayiba, bugu da qari tariqe Azkar hannu bibbiyu bata da ambato idan ba Allah ba, duk sanda kikaganta cikin nishad’i salatin maaiki takeyi tana ayyano kyakkyawar sufarsa”


Cike dajin dad’in kalamansa Hauwa tatashi tare dayimai jinjina tace......
”Madalla dakai kyakkyawan mijina maisona nagode da wannan sheda da kayimin nagode Allah yatsaremin kai yaqarama lafiya”
Nan duk suka amsa ameen kafin Itama tace.....
”Nima Allah yakaren mijina yatsareshi dukkan sharri harzuwa ranar sakamako”
Ameen suka sake amsawa da ita kafin suci gaba da hira cikin nishad’i da farin cikin dukansu kowa na dariya kai bazakace sun ta6a shiga damuwaba arayuwarsu gaba d’aya.

Kallon juna sukayi sannan suka had’a baku wajan fad’in......



ALLAH MUNGODEMAKA BISA BAIWAR DA KAYIMANA, ALLAH KAQARAWA ANNABI DARAJA KAQARAMANA QAUNARSA DASHI DA IYALAN GIDANSA BAKI DAYA AMEEN👏


Suka shafa inda nima nashafa nace ameen. 👏💞💞..



🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Allahduk wani abu danai dai-dai Allah ina roqanka kasa nad’ore akan haka👏Avindanayi akasinsa Allah kabawa masu karantawa damar gyaramin nikuma kabani ikon gyarawa.
الحمدلله💖💖💖
Allah nagode maka💖💖💖

🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡


ALLAH KAJIQAN IYAYENMU DA MALAMANMU BAKI DAYA.KA DAUKAKA QUNGIYARMU DAMU DAMUKE CIKINTA AMEEN💖


Sai mun had’u asabon littafina mai taken.......... 🤭


’YAR GATAN MAMA✍️.


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


2 Comments On A WANI GIDA
avatar
fatima-9-7-8

1 year ago

Reply

Masha allah

avatar
fatima-9-7-8

1 year ago

Reply

Yayi dadi allah yakara basira

Please Login or Register in order to submit comment