Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amma badai a fada min ba, yanzu dai bani nasha" ,,dariya ta kara saki tare da cewa "ai ban baki labari ba yanzun nan mutuminki ya turamin #5000k kuma na gudu na kyaleshi da abunshi, ai daga yanzu na gama yarda ya kusance ni sai ya bani cash, cash dib ma in naga dama ko ya bani na gudu", ta fada tana wani juya kwanciya daga in da take...............







Dariya ta sheƙe da ita tare da cewa "Kai wannan abun yamin Suga, kici gaba da gasa mishi aya a hannu, bamce ki bashi ba sai kin gama lale dan Iska, ke ko dattin Aljihu bance ki barshi dashi ba",ta fada cikin maganar mata yan duniya,wanda suka san takan tsiya, dariya tayi tare da cewa "ai dadina dake kina da man kai, yo dama ta ina zan yarda ai ko zan yarda sai na tabbatar da ba samu rabona", haka suka ci gaba da surutansu wanda basu da kai balle gindi, sai shawarwarin banza take bata, ita kuwa sai dariya take tana kara hawa kan motar ƙaiƙai.................









Cikin mugun yanayin nan ya kwana, yana murkususu, sai yanzu yake nadamar Auren Sadiyya da ya yi, gashi bata mishi komai,,ko bakutarshi in yazo da ita bata sauke mishi, gashi a rayuwarshi bashi da tsarin yin Aure-Aure balle saki...............








*WASHE GARI*







Tun Asuba bai koma bacci ba, dan yana dawowa daga Masallaci gurin motsa jiki ya nufa, motsa jikinshi ya fara yi, kusan 2 hours yana abu daya, kafin ya nufi cikin gidan tana share zufar da take yanko mishi, zaune ya tarar da ita a palo, ta chaɓa Ado cikin wani tsantsareran lass mai kyan gaske, ba wata babba bace dan ba zata wuce 19 to 20 years ba, ba laifi tana da dan kyanta dai-dai gargwado...............





kallonshi nayi shima din dai ba zai wuce 27 to 28 ba sai dai yana da garin jiki sosai, dan in ba fada maka akayi ba bazaka taɓa dauka Asalin shekarunshi ba kennan, saboda yana da babban jiki, yana da tsawo sosai gashi da ƙiba sai dai ba irin ƙiba ba sosai dai-dai misali dan ba za'a kirashi mai ƙiba sosai ba sannan ba za'a kirashi ramamme ba, tsaka tsakiya ne, sai dai Allah ya zuba kyau ,dan kallo daya zaka mishi kasan cewa shi cikakken Bafulatani ne, dan fari ne tas yana da matsakaicin baki mai dauke da ƙananan lips masu dan kauri kaɗan , dogon hancinshi har baka, idanunshi dara-dara fsrare tar sai golden Eyes ball da yake da shi, gashin girarshi da na idanunshi gazar-gazar gwanin kyau , Fatabaraqallahu Ahsanun qalikin ,Masha Allah , na furta dan ya haɗu iya haduwa yakai karshe a gurin kyau..............








yana karasowa cikin palon tace "Good morning My Solder", ta fada tana dan mishi murmushi, wani kill smile ya saki tare da cewa "Morning how are you ?", "Alhamdulillah", jinjina kanshi ya yi tare da cewa "Good", yana fadar haka ya hayewarshi sama...............








Tana mugun Mamaki da shi duk abinda zata mishi vaya yin fushi, ko ya yi ina saurin saukowa da wuri, wayarta ta dauka da sauri ta danna kira , ring biyu aka dauka , daga chan ɓangaten aka ce "Ya akayi ne Ƙawata", dariya tayi tare da cewa, da dauri ta dakatar da ita tare da cewa "Yanzu My Solder ya dawo daga motsa jiki", dariya tayi tare da cewa, "ya akayi kikasan haka zan fada ?",,dariya tayi tare da cewa "Sharw kawai yanzu ya akayi, mai kika girka na aiko na Ansa",,dariya tayi tare da cewa, "Wallahi Doya da kwai kawai ba soya, ganinan ma zuwa gidan baasai kin aiko ba", ta fada tana kike................







Mayafinta kawai taja , sai da ta shiga kitchen ta haɗo kan komai kafin ta fice , abunta dan ko tambayarshi batayi ba...........







Yana shiga Wanka ya fads bathroom ya yi, yana fitowa yaji wayarshi na ringa, da sauri ya matsa gurin Wayar *Hajiya* ya gani rubuce akan screen din wayarshi, kashe kiran ya yi, tare da kira back, sai da ya ɗuƙar da kanshi Ƙasa kafin yace "Ina Kwana Hajiyata" murmushi tayi tare da cewa, "Alhamdulillahi Auta , wai nace kayi sauri kar dare ya mana a hanya, dan kasan bana son dare a hanya ko kaɗan", ta fada cikin so da kaunar Ɗan nata...............






Jinjina kanshi ya yi tare da cewa "To insha Allahu Hajiyata ganinan a hanya", "To sai kazo", suna fadar hakan ya kashe wayar, cikim sauri-sauri ya shirya cikin Shadda mai kyau sai maiko take taji aikin surfani wanda kana kallonshi zakasan kuɗi ya yi kuka gurin aikin , takalminshi da Agogonshi Gucci sai bakar Zanna da ya kafa a kanshi,baƙin gashin kanshi da ya kwanto bayan wayanshi, ya yi kyau sosai, turaruka ya fara fesawa sai da ya yi wanka dasu kafin, ya fara takawa cikin takun isa ya fito daga bedroom din, dayan bedroom din ya leqa tun da ya ga wayam yasan ta fice, gefen bed ya karasa raper na 1k ya ajiye mata kan bed din tare da fice abinshi........






Rantsatsiyar Motarshi mai kyau da tsari ya nufa, sai yanzu ma ni naga Sojojin da suke shawagi a gidan da Alama ma sune masu gadin gidan, nayi mamaki sosai dan lokacin da na shigo jiya banga wannan tulin mutanan ba, suna ganinshi suka fara sara mishi, wasu ukku ne suka rugo da gudu suja bude mishi bayan mota, daya ne ya shiga cikin motar, sauran kuwa suka shiga cikin wasu motoci guda biyu suka mara mishi ba, tsula gudu suke kan hanyar , duk wanda ya gansu gefe yake dan yau manya ne akan hanyar da jiniyarsu suke tafiya.............






**************





Wani daki na shiga da babu wani haske sosai cikin ɗaki, ina shiga na hangi Wata mata Durƙushi take akan guyayinta, tana jujjuya kai ga wata uwar zufa da take karyo mata, sai kace wadda ta haɗiyi kunama, murkususu take tana cije lips dinta, a hankali ta fara nishi mai sauti irin na wanda yake cikin fitar hayyaci, ta dade sosai tana cikin wannan halin, a hankali ta fara rarrafe har ta isa gadon bononta da yake cikin ɗakin..............




A hankali ta fara dan dukan gadon, tana nishi, a hankali ta fara furta "Mai gida! Mai gida!! Mai gida!!!", ta fada tana daura kanta jikin gadon bonon , wani wawan tsaki akaja kafin wata murya ta daki dodon kunnena, cikin faɗa yace "so nawa zan fada miki in ina bacci ki daina tashina mai yasa ke gaba daya, bakya da tunani ne, kamar Dabba haka kike Al-amuranki , Wai ya akayi ne ma," ya fada cikin fada-fada..............





Hawayen da suke maƙale a idanunta ne suka zubo, cikin rawar murya tace "Dan Allah kayi hakuri", tsaki ya kara jaa tare da cewa "to! da hakurin ya mutu Sadakar nawa kika bada Ke! Maryam Wallahi ki kiyaye ni, dan zanyi mugun saɓa miki Shashasha kawai", cije lips dinta tayi tare da cewa, "dan Allah ka taimakamin ina jin naƙuda ce nake", dariya ya sheƙe da ita tare da cewa "Au haba naƙudar ce, Uhmmmm lokacin da kikazo kikaji dadin ki wa ya hanaki , sai yanzu ne kike cewa kina wata naƙuda, to ki haife mutanen duniya ma mana ni ina ruwa, dan haka karki kara tashina ko kuma Wallahi ki gane kuranki ", ya fada yana juyawa...............





rasa yarda zatayi tayi, ga wani azababban ciwon baya da na mara da ƙafafu da ya sauko mata gaba daya, a hankali take rarrafawa har ta isa bakin kofar ɗakinta da ko siminti bata samu arzikinshi ba, kanta ta leqa tare da cewa "Haleem! Haleem!! Haleem!!!", ta fada cikin rashin fitar murya............





Wani Yaro da bazai wuce Shekara 9 zuwa 11 ba ya fito daga wani ɗaki da gudu tare da cewa, "Ummu gani", rike hannunshi tayi tana sauke numfarfashi tace , "Haleeem jeka ka kiramin Iya yi sauri", ta fada tana dafe mararta, "Ummu baki da lafiya ne ?", ya fada cikin muryar tsoro, jnjina kanta tayi , tare da cewa "yi sauri kaje", ta fada tana sakin hannunshi..............




da gudu ya fita daga gidan, minutes kaɗan sai gashi sun shigo da wata Yar Tsohuwar mata sai dai ba tsohuwa bace chan ta dai manyanta, da sauri ta karasa gareta, tare da dafa kanta da tan jinginar a jikin ginin ɗakin tana hawaye ga wani kyarma da jikinta yakeyi, naman jikinta har wani rawa-rawa yake, cikin tausayawa tace "Maryama! Maryama Assha naƙudar ce, sannu tashi mu shiga ciki", ta fada tana riketa, dakyar ta yunƙura, da taimakon Iya suka shiga cikin ɗakin..................





tsakiyar dakin suka tsaya, kallon kan gadon da Lawan ke kwance tayi, cikin fada tace "Kai Amma Lawan anyi ɗan iskan Yaro ashe dama haka kake, yanzu matarka tana naƙuda amma kana nan kwance, amma kayi Asara wallahi, k......" dafata tayi tare da cewa "Iya bai sani bane, kuma...", ɗaga mata hannu tayi tare da cewa "..............





*Wannan littafin na kuɗi ne #200 ne kuɗinshi, ki daure ki biya kisha karatunki cikin kwanciyar hankali*






~DAGA TASKAR SALMAJI / ƳAR LELEN ROYAL STAR CE~🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️
[11/27, 10:42 PM] Sarauniyar Yaƙin Marubuta: ☘️☘️NAZLAH☘️☘️




*DAGA ALƘALAMIN*


SARAUNIYAR YAƘIN MARUBUTA / ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️.



*WANNAN LITTAFIN GABA DAYA SADAUKARWA NE GA YAYATAH (MARYAM YUSUF)WANNAN LITFAFIN WAKE NA RUBUTASHI, KI YI YARDA KIKESO DASHI, ALLAH YA RAYA MIKI ZURI'ARKI , YA KUMA KARA RUFA ASIRI , DUNIYA DA LAHEERA........*










بسم الله الرحمن الرحيم






7-8.





"""""""""""""Yana tafiya Jamseey ta tattaro kayanta gaba daya ita da Ƙanwarta Jasmin suka dawo gidan, tunda suka dawo komai a gidan sukeyi, basa ko dan zuwa gidansu su zauna, sai dai su ɗibi abin ci su bada akai,basa mata aikin komai, kwana biyu kawai gida ya fita daga hayyacinshi, mai aikin da take zuwa tana gyara palon ma Jamseey ta hanata zuwa, Sadiyya kuwa kamar wadda aka Asirce bata iya yin komai, kullum tana tule, duk abi da suka ce mata shi takeyi, bata son ganin bacin ransu ko kaɗan biyayya take musi kamar uwarsu...........





*********





Tsabar kukan, Ummu ko leqowa waje bata yi ba saboda kawar da kai ga Yaranta, haka Nazlah ta mike ta shiga ɗakin tana kuka, kan jikin Maryama ta zauna tana shasheƙar kuka , tare da nuna mata hannunta, hannun ta rike tana dubawa, bata san sanda hawaye ya zubo mata ba ganin hannun gaba daya ya tashi, sharw mata hawayen idanunta ta shigayi, ita kuma nata na zubowa, ganin Ummu na kuka yasa itama ta kara fashewa da kuka, dan duk da bata wuce shekara daya da rabi ba amma gaba daya batason ganin Mamarta na kuka..............




yakice Labulen dakin Lawan ya yi, tare da cewa "wane shege ne yakeson mayar min da gida filim mutuwa, kumin shiru ko na tattaka ku gaba dayanku", ya fada yana daka musu tsawa................





Shiru Ummu tayi, kanar ruwa ya cita, Nazlah kuwa kara fashewa tayi da kuka tana boyewa jikin Ummu dan gaba daya bata son ganin Lawan ko kaɗan dan kallon mugu take mishi, "dan Ubanki rufemin baki ko nazo na tattaka ki", ya fada yana shirin shigowa ɗakin ,da sauri Ummu ta sanya tafi hannunta ra rufe mata baki, (Allah Sarki Mahaifiya, bata son duk abunda zai faru ga Ɗanta, tana iya jure dawainiyar Yaro tun daga ciki har izuwa haihuwa da raino, kashinka futsarinka, da komai naka ita take gyarawa, ko dan ciwo kaɗan bataso kaji, balle ta kai ga wani yaci zalinka, sai dai kawai tayi kawaici ta kyale bawai dan bataji ciwo a ranta ba, kawai dan mutunci da zaman tare, Allah ka tsare mana Mahaifanmu ka shirya mana Mahaifanmu sannan kaji ƙansu, ka gafarta musu zunubansu, Alfarmar Annabi da Al-qur'ani , Ameeen).





sakin labulen ya yi, tare da ficewa yana banbamin bala'i, ganin ya fice da sauri ta dauki, Nazlar ta daurata akan gado tare da fara bincikar in da zataga maganin wuta, tasha wuya sosai kafin ta nemo maganin, tana kuka, Nazlah na kuka haka ta ciccire mata fatar da ta tashi, ta barbada mata maganin, bayan ta gama, feeding dinta ta fara yi tana shafa,mata kai tare da busa mata iska a hannunta, bacci mai nauyu sosai ya dauketa, ganin bacci ya yi awon gaba da ita yasa ta sauke numfashi da karfi, tunanin rayuwa ta fara yi, batayi aune ba taji ana kiran Magrib..............





Sallah tayi, lokacin da zata gama Haleem ya dawo daga aikin kanikancin da aka sanyashi, cikin murna ya matsa gareta tare da cewa "Ummu kalli, Oga na ya bani wannan", ya fada yana nuna mata wata sabuwar naira Ashirin da ya fitar a Aljihunshi, murmushi tayi tare da cewa "Allah ya mata Albarka, kaima Allah ya maka Albarka dama Ƴar uwarka," ta fada tana shafa kanshi, "Ameeen Ummu", ya fada yana jingina da jikinta..............






idanunshi ne ya hasko mishi ƙunar hannun Nazlah , da sauri ya mike ya nufeta , yana cewa "Ummu mai ya samu Nazlah", ya fada cikin rudu, yana kara kallon hannun, tuni kwalla ta cika mishi idanu dan bayason ganin ciwo ko ya yake a jikin Mahaifiyarshi ko Ƙanwarshi dan yana tsananin Ƙaunarsu fiye da komai, shafa kanshi tayi tare da cewa "Ƙonewa tayi dazun", girgiza kanshi ya yi, tare da cewa "kuma duka hannunwan Ummu ?", ya fada ya kara kallon hannun, "bana son surutu tunda dai ta ƙone ai shi kenan", ta fada tana kawar da kanta daga kallonshi, shiru ya yi bai kara cewa komai ba...............





Chan kuma yace "Ummu mai zamu ci da dare", shiru tayi sai kuma chan tace "ga goma chan dauka ka haɗa da kuɗin hannunka ka siyo muku garin kwaki na ashirin sugar ta goma sai kusha", ta fada tana nuna mishi kabet dinta , mikewa ya yi, yaje ya dauka ya fice, minutes kadan sai gashi ya dawo da duk abin da tace,karɓa tayi tare da jiƴa musu, kallonshi tayi tare da cewa "sha ka rage mata", suna cikin maganar ta bude idanunta da suka jaajir , idanunshi na kanta hakan yasa da sauri ya dauketa ya sanyata a jikinsa...........





fita ya yi da ita ya wanke mata baki, tare dawo da ita, garin ya fara bata,yana bata yana sha, surutu ta fara bashi tana cewa "Abbu! Abbu!! Abbu!!!", "shine ya ji miki ciwon", da sauri ta gyaɗa kanta ,shiru ya yi, dan shi tunda yaga ƙunar zarginshi ya ta'allaƙa ga Mahaifinsu, ganin Ummu bata son zance yasa bai kara magana ba............





ko rabin garin basu yi ba, Lawan ya shigo baaaga-baaaga, kwace kofin garin ya yi, tare da zama ya fara shaa, Nazlah na ganinshi kamar taga mala'ikan mutuwa, haka ta ringa ƙanƙame Haleem , taƙi yarda ko ido su haɗa.............




shafa kanta ya shigayi yana karanto mata Addu'ar neman tsari dan har wani firgita takeyi, Lawan na gama shan garin ya kwanta sai bacci, dama ya gama shaa ya bugu.............






~********~



Bayan shekara daya da rabi, a lokacin Nazlah na da shekara ukku chass, ta ƙara zama wata cute gal, tayi wayau sosai ga karatu a bakinta, hakan yasa Iya ta kaita Makarantar tayani gantali dake chan bayansu, ba wata shahararriyar makaranta ba ce, dan sai Yaro na da mugun ƙoƙari kafin ya iya gane abun da ake koyawa saboda cunkushewarsu da rashin Malaman koyarwa, sai dai duk da haka tana ganewa sosai dan bata zama sai layin gaba, sai dai ba halin nan an na kwaɗayi, dan in taga abu miyanta har zubowa yake, tana tanɗar baki, hakan yasa mutane da yawa suka tsaneta, dan da taga mutum na cin abu zata je ta sanyashi gaba tana kallo, ko ta mika mishi hannu.............





Umma na iyakacin bakin ƙoƙarinta na ganin ta hanata, amma abun ya faskara Haleem ma ya yi iya bakin ƙoƙarinshi, amma abun yaƙi ci yaƙi cinyewa hakan yasa suka barta...........





sai dai da taga Lawan ko mai tale take take komawa cikin hayyacinta, ana cikin haka aka sanyata wata Islamiyya chan gefen Unguwarsu, Islamiyya ce mai kyau, wadda Fisabillilah wani Bawan Allah ya ginata, domin Gajiyyayu da Marayu, hakan yasa aka kaita chan, Haleem na zuwa aikinshi Ummu ma tana zuwa wani gidan Masu kuɗi tana musu aikatau suna biyanta, sai dai ko kusa bata taɓa zuwa da Nazlah ba dan tasan duk ranar da ta kuskure taje da ita, to wallahi ranar ta tashi aiki, dan korarta zasuyi, dan Nazkah bata gani ta ƙyale ba kuma taga abu batayi kamar ta fada ba, hakan yasa suke iyakar ƙoƙarinsu na ganin sun siya mata abubuwan Makulashe duk san kar ta gani hannu Yara ta roƙa, sai dai ko akwai abu a hannunta da taga na wani sai ta mika mishi hannu, in taga Yaro ne in bai bata ba, ta kamashi ta duka, dan fada gareta sosai ko dage ya shafa matw lafiya a faɗa.............





Kamar Kullun Yau ma an tasosu daga Makarantar Boko , tana tafe tana karanta A B C D, tana gyada kai da taɓa hannu, idanunta ne suka hararo mata Wata Yarinya da Alale a hannunta tana ci, kamar Walƙiya baga ta kwasa a guje, gaban Yarinyar ta tsaya, tare da cewa "Kandala", ta fada tana murmushi tare da haɗiyar miyau.............





Harara ta dalla mata tare da cewa "lafiya zaki tsayamin aka", ta fada tana ci gaba da cin Alalenta, murmushi tayi tare da zama kusa da ita tana cewa "ai abun ba na fada bane, Ƙawata", ta fada tana dafa kafaɗarta, sauke hannunta tayi tare da cewa "wace ce Ƙawar taki?, yanzu ne kikasan da ni a matsayin Ƙawarki, yanzu da kika ga abun duniya ko, to wallahi ahirrr dinki, dan ko zaki mutu ba zakici Alalen nan ba", ta fada tana dauke kwanonta ta mayar gabanta, "ke Dalla ki ajiye muci nima anjima in na siyo abuna zan baki", ta fada tana mika hannunta cikin kwanon.................





kwaɓe hannunta tayi tare da cewa "Cire kin hannunki a cikin abuna", ta fada tana mikewa, cikin jin haushi tace "to wallahi sai na ci ko zaki mutu dan ma in binki cikin lalama", ta fada tana dalla mata harara.........




ta fada tana fige kwanon hannun Kandala, wawushewa tayi tare da turata baki duka, wani azababban Mari Kandala ta sakar mata, tare da riketa mata wuyan riga tace "Wallahi ko da wannan Uban naki dan caca kike yawo sai kin biyamin alalena", ta fada idanunta na tara hawaye...............





Tsalle Nazlah tayu tare da ƙifa mata wani wawan mari tare da cewa "ke dan Ubanki har kin isa ki zagi Ubana, naga ai tare da ubanki suke cacan dan haka babu kin ga ba sauran gori", ta fada tana dukan kirjinta tare da kama wuyan rigarta............






fada ne sosai ya kaure a tsakaninsu, gashi unguwar babu yawan mutanen da suke zirga - zirga hakan yasa babu wanda ya rabasu, Hannu Nazlah ta daura akan Kandala, Jelar gashin dokin da aka sanyawa Kandala ta kama, tare da ja cisgowa gashin dokin ya yi , tare da gashinta gaba daya, jini ne ya fara zuba, ganin haka yasa da sauri Nazlah ta saketa tana zare ido, shafo kanta Kandala tayi ganin jini yasa ta zaro idanunta...............





Sakin Nazlah tayi tare da dafe kaiiii, ganin ta saketa yasa ta falla da gudun tsiya ba inda ta tsaya sai gidan Iya dan tasan ta koma gida Ummu batanan kuma ko dafata za'ayi sai ayi a gama bata dawo ba, da gudu ta shiga gidan Iya, Iya da take bakin murhu tana ƙoƙarin hada wuta da sauri ta mike tana cewa "Kayya! Kayya!! me ne ne?", ta fada tana zare idanunta, sai da ta kai kofar dakin Iya kafih tace "Iya fada muka yi da Kandala har na cirw mata taura(jelar gashi) daya kuma wallahi ga jini na zuba " ta fada tana sakin futsari saboda tsoron da take ciki...............






"Mtswwwww wace Kandala, ita abun da takeyi a cikin garin nan ai sai a daure Ubanta, kema ranar ba ta duke ki ba, dama ai rama cuta ga macuci ibada ne, ni da in kai karar Ɗa gwara a akawo min kararshi, " bata rufe haki ba Delu Uwar Kandala tayi Sallama, da gudu Nazlah ta banka karkashin Gadon Iya ta shige tare da rike bakinta tayi lakur.............






Huci Delu ta fara yi tare da cewa "In wannan shegiyar Jikar taki take?",ta fada tana kallon Iya , cikin fada Iya tace "kul kar ki kara shegantamin Jika in ba haka ba zan nakaɗa miki tsinannan duka a cikin gidan nan", ta fada tana harararta, tula mata jelar gashin tayi tare da cewa "gashi nan

Please Login or Register in order to submit comment