Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kan kujera, dukar da kanta tayi dan tana tsananin jin kunyarshi da ganin mutuncinshi, cikib siririyar murya ta ce "in har bata dai na surutu ana karatu ba, wallahi ba zata ƙara magana ba har duniya ta naɗe", ta fads tana juya idanunta, sai ga Hauwa'u tana zazzzare ido an sakar mata maƙogwaro.



dan murmushi ya yi , tare da fara amsar karatun da zasu gurin Sauka, bai karɓi na Nazlah ba dan yasan bashi da matsala da ita, sai dai sai kallonta yake, dan yajin labarin abun da ya faru jiya da Malamai, sai dai bai yi wani jimami ba sai Allah kara da ya musu dan Malam, basa da,kirki babu abun da suka ajiye sai cutar Yara.


.
baya sun gama Karatu aka tattauba yarda abubuwan sauka zasu kasance a gobe, kafin a tashesu su fice, direct gida ta nufa cikin farin cikin da ta rasa ko na me ne ne.



tana zuwa ta faɗa jikin Ummu da take tunanib, yarda zatayo da su dan Yau basu da ko kwayar hatsi da zasu ci abin ci gashi tasan Nazlah da yunwa zata dawo firgigit ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi, kallonta tayi tare da cewa "har kin dawo..!?", gyads kanta tayi tare da cewa "Ummu Saukar mu fa gobe banga ana shirye² ba", ta fada tana kallon cikin gidan.


Dan murmushi da bai kai ciki ba tayi tare da cewa , "muna nan muna yi", ta fada tana shafa kanta, shiru tayi bata ce komai ba, haka suka ci gaba da zama shiru, sun ɗan jima haka kafin Ummu tace "tashi kije gidan Iya kice ina gaisheta", mikewa tayi tana murna da tsalle ta fice, bin bayanta da kallo tayi tana jinjina irin wannan Yarinta ta Nazlah shekara 10 cikin ta sha daya amma bata daina sakalci ba, tana tsoron ranar da zata faɗi (period) batayi hankali ba.



ba tayi 5mimutes da fita ba, ta shigo da kaya riƙi² a hannunta, har tana zubar da wasu da babbat kula, ajiyewa tayi a gaban Ummu tare da cewa "gashi...!", tana ajiyewa ta shige ɗaki, Ummu na magana amma bata tsaya ba, mikewa tayi ta bita ciki da niyyar tambayarta daga ina.



tana shiga ta nemeta sama ko ƙasa babu ita babu labarinta, duddubawa ta shiga yi har ƙasan gadonta amma batanan, gabanta taji ya faɗi , dandanan wani tunani taji ya darsu a ranta, hakan yasa ta fice tare da zarar gyalenta ,tayi gaba zuwa gidan Iya.



tana fita Abba ya shigo, ganin kaya zube a banza, sai ya kwashe ya fice, kai tsaye dandalin cacarsu ya nufa, yana zuwa ya tarar da wani ya sanya kuɗi duba biyar, kawai shima sai ya miƙa kayan, ya zauna aka fara bugawa dashi.




ko da ta ƙarasa gidan Iya zama tayi suka fara firarsu, suna dariya tare da wani gwaranci da su kaɗai suke iya gane kanshi ,ko ince mutanansu ne kawai suke iya gane kanshi, dan mutanan kan Iya sune suka koma kan Nazlah saboda kaunar da take mata.



cikin sauri Ummu ta tura kanta cikin gidan, ganinta zaune yasa ta ja burki tana sauke numfashi, cike da tsoro wace ce wacchan din?, ta tambayi kanta cikin ruɗu,shi ko mutanan Nazlar ne har suka chanja mata salo da haka?, kallonta Iya tayi tare da cewa "Ƙara so mana", girgiza kanta tayi, tare da ce wa "Iya bai san na fito ba", ta fada tana juyawa ta fice.



Ummu tana zuwa ta tarar babu kaya , iya tashin hankali ta shiga, tasan dai ba mutanan suka zo suka dauki kayan ba , sai dai in Abba ne zai shigo ya dauka, bata ko zauna ba sai gashi ya shigo, bashi ga tsuntsu bashu ga tarko, dan ya zuba kayan am cinyeshi, shi kuma bai cin komai ba ,kasa ta zube tare da gaishe shi , amsawa ya yi a yatsine cikin fusata, dukar da kanta tayi tare da cewa "Dan Allah ko kaga kaya ɗazun akan taburma?" ta fada kanta na karayin ƙasa.




wani banzan kallo ya watsa mata tare da ce wa "Eh na gani kuma na zuba su A caca, ko a kwai yarda za'ayi da ni," da bala'in sauri ta dago idanuta , sai dai bata iya cewa komai ba, bata san yarda zata fada mishi haɗarin kayan ba, bayan Sallah Isha Nazlah ta tattara komatsanta ta tafi gidansu.



``` Washe gari```



Tun Asuba Nazlah ta farka, tana ta yan tattare- tattarenta , bayan ta gama ta tashi Ummu dama Abba ba gidan ya kwana ba, bayan sunyi Sallah da Azkae din sade, tayi Karatun Al-qur'ani.


bayan ta gama ta kalli Ummu tace "Ummu ina Kayan Abin ci a daura kar lokaci ya kure mana?", shiru Ummu tayi bata ce komai ba, ƙara tambayarta tayi, juyowa tayi ta kalleta kafin tace "Babanki ya daukesu, a harzuƙe ta kalli Umma sai kuma ta fice, bata jima ba, Ummu taji ƙarar ɓuruntunta , tana fitowa ta tarae tana kiciniyar daura tukunya ga kanyan Abincin na zube a gabanta.



iya tashin hankali Ummu ta shiga, dan bata son Abubuwan ban su bude wa Nazlah ido, dama ta lafiyar kura balle kuma tayi hauka, tayata tayi suka daura, dandanan suka gama duk abun da ya dace, har wanka da sauransu.


bayan Nazlah tayi wanka Ummu rasa kaya da zata bata ta sanya tayi, dan bata mata Ankon Saukar ba, haka yasa ta kasa shiga ɗakin da ba tasan mai zata ce mata ba, tana tsaye ta fito cikin shigar Atamfa super da ta mata kyau kwarai da gaske kalar green da farar hijab dinta da takalminta, tayi kyau sosai sai walwali take, dan ma wai babu kitso balle lalle, dan mutananta bata so ko kaɗan.



Karo na farko da tayi Alfahari da mutanan Nazlah dan sun fitar da ita kunya, ko da ta shiga itama sabbin kaya ta gani ajiye, da ƙin sawa tayi, sai kuma wata zuciyar ta ce "Allah ne fa ya cida ki ki sa kawai" ,sawa tayi itama ta fito garau da ita, Yah Haleem ma cikin kyakyawar shiga ya shigo gidan da wasu Yara, su suka dauki Abincin suka tafi gurin Saukar.


cike damkam suka tarar da gurin dan saukar bata mutum daya bace ta kusan mutum Ashirin ce, ga kuma gayyar manya mutane, dakyar suka samu hanyar shiga cikin taron, Nazlah sai wangale baki take tana magana ita daya, nikam nace ```tab wannan taron ai dole ma da Gayyarki ciki```…




Guri suka samu suka zauna, ita kuwa gurin Ɗalibai Yan uwanta ta nufa, zama tayi kafin su gaggaisa, cikin Yar raha.




*********


tun da sassafe Hajiya ta kira Hameed ta shaida mishi batun Saukar da za'ayi, haka yasa ya turo da kyautarshi ta Malamai da wuri, tare da manyan kyatutuka da ya shirya domin bayarwa ga Daliban sa sukayi saukar , Duka yan Uwanshi suma sai da suka sanya gudumuwarsu a ciki, dan dama makarantar kusan haɗin guiwa ne dasu, sai dai kuɗinshi sun fi yawa a ciki , dan shi yake biyan Malam duk wata.




shi kuwa sai misalin 10am ya shigo cikin gidan da Sallamarshi sai baza kamshin turaren Giorgio Armani, yake cikin kwarjini da cikar haiba yake takawa zuwa cikin palon, inda suke zaune suna jiranshi, gaishesu ya yi Ƙanan suka gaisheshi, amsawa musu ya yi,yana zama kusa da Hajiya tare da daura kanshi a kafaɗarta, shafa kanshi tayi tare da cewa "Auta ka taushe hannu, kai kawai muke jira tun dazun", ta fada tana yunkurawa zata mike, kallon Adda Zainab ya yi, tare da ce wa "Adda ki ɗiba kin break fast mana",ya fada yana binsu da kallo.



kallonsu suk Adda Zainab tayi, suma suka kalleta kafin ta ce "To ina matar gidan? da ta bar mijinta da yunwa..!", shiru ya yi alama baya son zancen hakan ya tilasta mata yin shiru itama, sai da ta diɓar mishi kafin su fice, mota huɗu sukayi Adda Zainab da Hameed daya, Hajiya da Adda Nabila da Adda Nafisa daya, sai Haleesa da Yaran su Adda daya, sai dayar kuma Sojojin Hameed ne a ciki .



kai tsaye makaranta suka nufa , basu dau wani dogon lokaci ba suka ƙarasa dan tsakanin Unguwarsu Hajiya da Makarantar ba nisa sosai,suna shiga ciki aka basu hanya, suka shiga, ganinsu yasa gaba daya Malaman suka mike zuwa taryarsu, bayan gama gaishe-gaishe aka samu gurin da aka tanadar musu mai AC da Fanka, cikin rumfa, Nazlah tun da taji karar shigowar Motoci zuciyarta tayi wani mugun bugawa da karfi, hakan yasa ta dafe saitin.



bayan gama bude taro da Addu'a wanda Nazlah tayi , da gabatar da baƙi da Malam Abbakar ya yi, sai aka danyi drama ta larabci wanda shima har da Nazlah wadda ita take jaan ragamar drama ,bayan ta gama aka fara karatun sauka, wanda Nazlah aka fara kira ,,cikin natsuwa ta hau kan munbari, fuskarta a bude tar ta,karayin wani fari, sauran kuwa duk da niƙaf ita kuwa bata sanyawa dan numfashinta daukewa yake in ta sanya, cikin ƙira'arta mai dadi ra fara karatu wanda duk wanda yake gurin hankalinshi da idanunshi na kanta ,amma banda Hameed da kanshi na ƙasa saurararta kawai yake, har ta gama ba'a cita gyaran ko wasali daya ba,balle akai ga fidda kalkala dan tasan inda haƙƙoƙinsu suke, kuma tana kiyayesu .



bayan ta gana aka kikkira Abokan saukarta, suma sukayi, sai sai Yawan cinsu duk da akwai kura-kurai a cikin karatunsu, bayan sun gama aka basu kyauttuka, wanda Nazlah tafi kowa samun kyauta mai tsoka, bayan bada kyattutuka da bada shahada, aka kira Nazlah again domin gabatar da Nasiha ga mutane, cikin gajiyawa ta kara hawa munbarin, cikin wata murya mai dadi ta fara magana, muryar da ko baka kaunar Uwarka da Ubanka in ka jita sai ka kaunaci mai ita ta fara magana, wanda yasa Hameed ya dago idanunshi ya dubi inda ake maganar, sai da gabanshi ya faɗi, dan kamar ance su kalli juna su biyun, kusan 30 seconds idanunsu na cikin na juna kafin ta jaanye idanunta, shi kuwa bai iya daukewa ba dan zalar mamaki ya cika mishi zuciya ganin Yar Yarinyar da take raira wannan karatu da tafseer duk a lokaci daya gashi komai za'ayi sai an kirata.




bayan ta gama Adda Zainab da karɓi Laundspeaker ta jaaddada godiya ga Iyayen Yaran da sukayi Sauka da bada kyauttutukanta, da jaddada Albarka a gesu, duk a cikim harshen larabci, sai da ta gama kaf kafin ta kira sunan Nazlah Lawal, a hankali Nazlah ta dago da gajiyyayun idanunta ta kalleta, alama ta mata da tazo, mukewa tayo tazo har gabanta kafin ta sunkutar da kanta kasa alamar girnamawa.


Cheack din 2 millions ta damƙa mata a hannu, tare da kara sanya mata albarka, dan Yarinyar ta bala'in burgeta ta kuma shiga ranta, har ƙasa Nazlah ta duƙa tanawa Adda Zainab godiya...........





07033371851



```DAGA TASKAR ƳAR LELEN ROTAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️```
[12/21, 12:11 PM] YAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♂️🧚‍♂️: ☘️☘️ *NAZLAH*☘️☘️





*DAGA AL[]ALAMIN*




SALMAJI/[]AR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️






*WANNAN LITTAFIN DAGA FARKONSHI HAR KARSHENSHI, SADAUKARWAR NE GA YAYATAH (MARYAM YUSUF) WANNAN LITTAFIN WAKE NA RUBUTASHI, KIYI YADDA KIKESO DASHI, ALLAH YA RAYA MIKI ZURI'ARKI, YA KUMA K'ARA RUFA ASIRI DUNIYA DA LAHEERAH...*



*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*





17-18.



""""""""""Shafa kanta tayi, tare da girguza kanta alamar ta daina mata godiya haka.


sosai Nazlah tasha kyattutuka na ban mamaki, dan daga ko wane sashe kawo mata kyauta ake har mutananta sai da suka minmiko mata, su kansu su Adda Nabila Yarinyar ta burgesu, haka aka tashi kowa da mamakin Nazlah da burgeshi a cikin ranshi.



Su Nazlah kuwa haka suka dauki niƙi-niƙin kayyayakin kyauttutu kansu , suka tafi gida, sai dai Abun Mamaki bayan sun shiga gida suna shiga Ɗaki suka ci karo da kyauttutuka na ban mamaki ajiye tulugu guda, da kallo Ummu take bin kayan kafin ta kalli Yah Haleem tace "Haleem abun nan ya fara tsorata ni da yawa, mutanan nan so suke su kashe ni da tsoro, ɗiɓe kayan nan ka fice dasu", ta fada tana zama kan Yangwananniyar Katifar da take gefe.



Yah Haleem na kai hannu zai dauka, Nazlah ta rike hannunshi, ta re da cewa "Bandirawo dai na,,wannan kyauta ce ba'a mayar da hannun kyauta baya ,shaidan ne kawai yake mayar da kyauta in an mishi", ta fada kanta *ƘAASA*.



Cikin Hasala Ummu tace "zaki bari a fita da su ko sai na saɓa miki?", ta fada cikin bada umarni, kallon Ummu tayi kafin tace "Ummu kar a fitar da kayan nan kyauta ce aka kawo mata, in kuma aka fitar dasu to duk abun da ya biyo baya ba ruwana , domin wannan ba daga ni bane daga Sarki ne", ta fada tana komawa gefe ta zauna, kallon Ummu Yah Haleem ya yi, itama ta kalleshi , sai kuma suka kalli Nazlah da ta duƙar da kanta ƙasa tana kallon Kyauttutukan da suka shigo da su.



"A fita da su?", Yah Haleem ya fada yana kallon Ummu, girgiza kanta tayi, tare da cewa "ka barsu", kallon Ummun Nazlah tayi kafin ta mike ta fice daga ɗakin , tana fita tsakar gida ta cire dan kwalinta da hijab ta fada banɗaki,bayan Nazlah ta fita Ummu tace "Haleem ya za muuyi da kayan nan, kasan Mahaifinku da ya shigo zai tattarasu ya tafi da su chan ya salwantar dasu , mai shawara?", ta fada tana kallomshi.



jinjina kanshi ya yi, tare da cewa "to ko mu kai gidan Iya sai a ajiye ?, kin ga ba zai bi kayan chan ba", ya fada yana kallon uwayen kayan da suka kusan cika dakin, dan ɗakin ba wani mai girma bane sosai, jijjiga kai tayi tare da cewa "hakan kawai za'a y.....!!", bata ƙarasa ba suka ji Nazlah ta kwala ƙara.


da sauri jikimsu har mazari yake suka fito suna rige², turus Ummu tayi tana kallon Hijab da Dan kwallin Nazlah da yake yashe a gurin, Yah Haleem kuwa toiler din ya nufa dan daga ciki yake jiyo ihun ta.



yana shiga ya tarar da ita ƙasa yashe tana burgima da ihu, dakyar ta iya cicciɓarta ya fito da ita sa boda wani nauyi da tayi, ɗakin Ummu ya shiga da ita, tare da shimfiɗeta a ƙasa, "mai haka!", Yah Haleem ya fada cikin ɓacin rai, ganin yarda ya haɗe ranshi ya yi kicin²,yasa Nazlah cewa "Murna muka zo..!" , ta fada tana ci gaba da burgima.



tsawa ya daka mata tare da cewa " haka ake murnan?, kuma tun ɗazun mai yasa baku zo ba, lokacin da kowa yake taya murnar sai yanzu?, shin kunzo ne domin ku dagula mata lissafi ko kuwa kunzo ne domin ɓata mata ranar farin cikinta?", ya fada cikin ɓacin rai.


girgiza kai tayi tare da ce wa"bamu da ikon zuwa a wannan lokacin domin Sarkin Musulamai ne a gurin, ba muzo dan dagula mata lissafi ba, hasali ma murna muka zo tayata akan wata murnan, amma zamu tafi ", ta fada tana daga kai zata yi Atishawa, saurin dakatar da ita ya yi , ta hanyar daka mata tsawa, da sauri ta natsu, cikin kaushin murya yace "mai yasa kuka fara bayyana kan ku tun yanzu?,ko kuna son nakasa mata rayuwa ne?", ya ƙarasa fada cikin rauni.



shiru tayi kafin ta ce "lokacin bayyanar mu ne baiyi ba sai yanzu, da ya yi da tuntuni mum bayyana, ko da yake dama muna a laɓe gane mune kawai ba'ayi ba sai yanzu, kuma mu dan Allah kayi haƙuri kun tafu", tana kai wa nan tayi atishawa da karfi ba tare da ta bari ya ƙarayin wata magana ba.



shimfiɗeta ya yi, tare da fitowa, ajiyar Zuciya Ummu ta sauke tare da raɓawa gefe daya ta zauna, abun duniya ya mata yawa, kallonta Yah Haleem ya yu, tare da ce wa "kar ki sanya damuwa a ranki, ni bari na fita, na samu mana abun da zamu ci",ya fada yana yin gaba, da fatan Alkhairi ta bishi , yana fita Abba ya shigo yana washe baki, kallonta ya yi, tare da ce wa "Ummun su sannu da hutawa", dagowa tayi baki bude tana kallonshi, zama ya yi a gefenta tare da ce wa "ina chan ina buga caca naji wani abun Alkhairi da ya sauka, ni ban ma san zatayi sauka ba, wai waya ma sanyata makarantar, ina kayan suke", dan tsananin takaici da mamaki kasa magana tayi, sai ta tyna lokacin da ta fada mishi za'a sanya Yarinyar Makaranta ya je ya kaita, sai cewa ya yi "na kai wa? wannan shegiya?, ni fa bana kaunarta, in ma kika kaita kukayi Amfani da sunana Ban yafe ba", har ƙasa ta zuƙunna rana rokonshi yaƙi, sai dai Haleem ya kaita aka yi mata register da sunansa, amma yanzu sai gashi wai yazo a bashi abun da ta samu.



"bakya ji ina miki magana kika yi shiru?",,Abba ya daka mata tsawa, Iya da take shigowa tace "To Ubanka zata ce maka in baya yi shiru ba Wallahi Lawan ka kiyayeni , na ce ka fita a idona na rufe", ta fada tana shigowa cikin hasala, da ɓacin rai.




"to wai Iya mai yasa kike so ki shiga tsakanina da Iyalina ne, ba fa na son haka", ya fada cikin daga murya shima, "Eyyi dama in baka yi haka ba ai baka cika da Mu'azu ba, to bari na fada,maka sisi ba zaka samu ba a cikin abun da Yarinyar nan ta samu, dan bakasan komai na,karatunta ba", ta fada tana shigewa ciki.



kayan ta tattara cikin buhu ta dauka ta fice dasu waje , Yara ta dinga ɗiba tana ba mawa suna kai mata gida, har ta jide tsaf , Lawan kuwa yana zaune cike da baƙin ciki, dan wata caca zasu buga da wani Alhaji da ya sa 50k , shbe yazo ya kwashi abun da suka samo ya kai, dan ya zauna ayi c'ac'ar dashi.



```BAYAN KWANA BIYU```




Kullum Adda Zainab da Nazlah take kwana, take tashi da ita a cikin ranta, ga kuma abun Hameed kullum gani take yana ƙara ta'azzara.


kamar kullum suna zaune cikin palo, suna fira, Haleesa ce tace "Wai ni kam Adda , ya batun nemawa Auta Mata yar 10years kin fasa ne ko ya?, gaba baki ƙara maganar ba!,"numfashi ta sauke kafin ta ce "bawai na fasa ba har yanzu ina kan bakana" , da sauri Adda Nabila tace ",Ni kam Adda mu gwada sa'ar mu akan Yarinyar nan mana", duk kallonta suka yi kafin Adda Nafisa tace "wace Yarinya..!?", dan murmushi tayi kafin tace "Hafizar nan mana Nazlah", tsalle Haleesa ta buga tare da ce wa "Wallahi kuwa nima tunani nake a kanta, dan Allah Adda",,ta fada tana dan yi fuskar tausayi.



Jinjina kanta tayi, tare da cewa "nima ita nake tunani, amma bari na fadawa Hajiya in ta aminta da ita gobe ba sai muje ba", ta fada tana mikewa, duk bin bayanta sukayi, dan zuwa ɗakin mahaifiyarsu, zaune suka sameta tana karatun Al-qur'ani, zama sukayi a gefenta, suna saurarob Daddadar muryar Mahaifiyar tasu da ta ƙara dadi da tana karatun, sai da ta kai karshen page din da take, kafin ta tsaya tana kallonsu, ta cikin Eyesglass dinta, ganin yarda suka natsu yasa ta zare glass din , ta tattara gaba daya hankalinta garesu.



Adda Zainab ce ta matsa tare da riƙeta, Alamar magana mai muhimmanci zata fada mata, dan murmushi tayi kafin tace "ina sauraronki daga gani akwai magana mai muhimmamci a bakin ki", ta fada tana kallon sauran, duk murmushi sukayi , gyaran murya tayi tare da cewa "Hajiya akan Maganar Auran Autanki, mu mun ga dacewa da natsuwar Yarinyar nan Nazlah, kuma munyi sha'awar zamanta a cikin Ahalinmu, shine muka zo mu fada miki", tun da Adda Zainab ta fara magana Hajiya ta zuba mata idanunta, sai da ta kai karshen bayaninta ta sauke numfashi tare da cewa "Uhmm Zainab, lallai kam nima sai da na ayyana hakan a cikin raina, sai dai wannan Yarinyar tawa Auta Ƙanƙanta, ba zata iya dauke buƙatunshi ba, za'a iya cutar da ita, ke kanki kinsan Auta yana da buƙatuwa sosai, bakya ganin za'a tauyeta ,"shiru ta dan yi, kafin tace "Hajiya ina ji a raina Yarinyar nan ba zata cutu ba har an ta aureshi, sannan ina da yaƙin cewa zai kula da ita, kuma dama ai Miji shi yake koyawa Matarshi komai, in ma ragwanci ko Jarumta, dan haka ina ganin babu wata matsala, domin Yarinyar nan tana da ilimin Addini, ina da yaƙinin ba zata taɓa kauce hanya ba, kuma zata,kula dashi, dan tasan haƙƙin miji akan matarshi, idan kin Amince gobe muje gidansu", ta fada tana kara damke hannunta.



Numfashi ta sauke kafin tace "toshi kenan", fa fada tana ci gaba da karatunta, da murnarsu suka fito, bayan sun fito kuma Adda Zainab ta cewa Haleesa "An somin Wayar Hajiya na kira Malaminsu ", ta fada tana daukar wayarta.



da sauri Haleesa ta mike, ta karɓo mata, kiran Malam Arabi tayi akan gove zasu zo, cikin rawar jiki ya amsa musu, dan yasan suka zo zai kwashi damje gidanshi, dan basa zuwa su tafi basu dan lafa mishi wani abu ba, su kuwa firar Nazlah suka ci gaba da yi.




Washe gari guraren
4pm sukawa gidansu Nazlah Dirar mikiya da taimakon Malam Arabi da ya rakosu har gidan, bayan sun zo gidan ya tsaya a waje su kuma suka shiga ciki.



da Sallama suka shiga , suna shiga suka tarar da Nazlah na

Please Login or Register in order to submit comment