Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shara, Ummu na gefe tana duba Azkar, Sallamar su ce tasa Nazlah dago kanta tana dubansu,washe baki tayi tare da cewa "Ah'ah sannun ku da zuwa, maraba lalle, ku shigo", ta fada tana nuna musu hanya.



taburma ta shimfiɗa musu suka zauna, kafin ta gaishesucikin mutunci suka gaggaisa, Adda Zainab ce ta ce "Uhmm dama gaisuwa muka zo da rokon iri", cikin rashi fahimta Ummu tace "too gaisuwa da roƙon Iri kuma Hajiya?, ban gane mai kike nufi ba", ta fada tana gyara zamanta.



dan gutun murmushi tayi tare da cewa, "Ƴa muke so ki bamu",shiru Ummu tayi tare da cewa "anya kuwa nan gidan?, dan nan gidan babu wata Babbar Ƴa mace sai Nazlah, sai dai ko gidan gaba va nan ba", Yar dariya tayi tare da cewa "ita din nake nufi", rike baki Ummu tayi tare da cewa.


"to a gaskiya wannan ba magana ta bace, amma bari na aika a kira muku Iya sai kuyi magana da ita, ta fada tana kwalawa Nazlah da ta shige ɗaki da Ƴar Adda Zainab karama kira.



Amsa mata tayi kafin ta fito, goye da Yarinyar a bayanta, dan murmushi Ummu tayi, dan tasan Nazlah da mugun son Yara, ga son ta daukesu, sai dai fa har in ta miƙawa Yaro hannu ya mata ƙuya tofa ba,zata ji kunya ba, gsban uwar ɗa zata makeshi, in kuwa yazo ta ringa lelenshi kenan tana goyashi, da bashi abubuwan wasa da na ciye-ciye hakan yasa Ummu tai hamdalah lokacin da Ƴar Adda Zainab ta miƙawa Nazlah hannu bayan ta miko mata.



gaban Ummu ta zauna, tare da cewa "Ummu ga ni..!", kallonta tayi tare da ce wa "Iya zaki kira min, kice tazo Anyi Baƙi, suna son Magana da ita", kallon Ummu Adda Nabila tayi, kafin tace "to ki bari kawai sai muje chan din, kar a ƙatse mata wani aiki da take yi ", ta fada tana mikewa.


murmushi Ummu ta mata, dan dama ta rasa yarda zata ce su tafi chan din ne yasa tace a kirata, da tasan yanzu gab Abba yaje da dawowa daga gurin Cacarshi, mikewa sukayi Nazlah ta sanya Yan takalmanta Sino suka fice daga gidan.



tafiya suka fara yi zuwa gidan Iya, suna tafiya tana musu Yar fira da yake Nazlah ba dai labari ba, suna cikin tafiya suka haɗu da Hasina, harararta Nazlah tayi , kallonta Adda Zainab tayi tare da cewa "mai ta miki kika harareta ?", yar dariya tayi kafin tace "Bata jin Magana ne to ina dai-daita mata zama ne," ta fada dai-dai lokacin da suka shigo gidan Iya.



Da Sallama Nazlah ta fara kutsa kai cikin gidan, Iya da take zaune tana cin gujiya ta amsa musu, tare da cewa "Ƴar Halak kinki Ambato tun safe sai yanzu?", lokacin da ta kai karshen maganarta ne kuma ta hango su Adda zainab.



Washe baki tayu tare da cewa !Ah'ah Ashe da baƙi kuke tafe, Maraba lalle sannunku da zuwa", ta fada tana wangale musu taburmar da take zaune kai, zama sukayi suna gaisheta, da fara'a sosai a kan fuskarta ta amsa musu, Gujiyar gabanta ta mika musu tare da cewa "Bissimillan ku", Adda zainab ce tace "Aaaaaah Gujiya ai kam zamu ci, dan ni ha dade banci gujiya ba"ta fada tana daukar daya.



kara mika kwanon gujiyar tayi sosai gabanta, tare da cewa "ku ci dan Allah, ai gujiya abar marmari ce, nima na fita naganta shine na siyo na dafa " ,ta fads tana washe baki dan sam bata da rowar abun ta.



ci suka fara yi, Adda zainab ce ta kalleta tare da cewa "kar kuma mu cinyewa Yar tsohuwa abin ta", ta fada tana yar dariya, dan akwai ta da raha, "Ke..! Nazlatu dauki ki ƙaro musu ma cikin tukunya", ta fada tana kallonta, dauka tayi ta ƙaro , tare da dibo musu ita da Haleesa, kallonta tayi ta washe Yan ƙananan fararen haƙoranta masu kyau tace "Zo muci anan ki bar manya su ci nasu", ta fada tana ajiye musu.



matsawa tayi suka fara ci a tare, Su Adda kuwa suna ci suna yiwa Iya fira ana dariya, a lokacin in ka gansu sai kayi zaton sunyi irin 20years dinnan a tare , sa boda dukkansu, suna da fara'a, ga saurin sabo.



sai da suka gama ci tas, kafin nazlah ta jaa Haleesa da Yaran su Adda Nabila suka nufi ɗakin Iya, wasa suka fara yi Haleesa na biyesu duk da ta girme musu tana shan dariya.




Gyara zama Adda Zainab tayi, kafin ta kwashe duk abin da ya kawosu ta fadawa Iya, shiru Iya tayi tana sauraronsu, har suka kai ƙarshe , numfashi ta sauke tare da cewa "Uhmmmm Banƙi ta taki ba, amma dai Nazlatu Yarinya ce sosai, dan wallahi wannan kayan shiririta ne cike da kanta", ta fada tana kallonsu.



dan murmushi duk suka yi kafin tace "hakan nakeso domin nafi son wadda zai raina bawai ta raineshi ba , wadda zai dauka tun tana Yarinyarta ita de wadda ko mai za'a daurata akai ba zata ƙi ba kuma zata saba dashi ta tashi dashi, mu dai muna roƙo da ku bamu, sai dai in va muku ba kuma hankalinku bai kwanta da mu ba, kuma kuna jin bazaku iya haɗa zuri'a damu ba", ta fada tana dan kallon Iya.



"Iyeeeee kaji yar butar uwa, mu suwa ye da zamu ƙi haɗa zuri'a daku, ai babu wanda ba zai iya haɗa zuri'a daku ba, tunda kun dage na baku sai dai har sai kun gaji da shiriritarta , Allah ya sawa tarayyar albarka, amma kuma ni ba zan munafurce ku ba, Baban Yarinyar nan bashi da hali mai kyau , dan nasan ko ban faɗa muku ba za'a tareku a fada muku, domin wannan Alaqar Aure ce nasan dole a samu yan baƙin ciki da zasu shiga su fita, in kuwa na fada muku na fita ko ba sabulu", kallon juna suka yi .



Adda Nabila ce ta ce "to Iya zamu iya sanin Halin dan kar muji wai-wai a waje", dan murmushin takaici Iya tayi kafin tace "uhmmm halin yan zamani ya sawa kanshi, caca yake da shan sugari, sai dai na tabbata wata rana zai daina dan ba halinshi bane, daga bayan nan abun ya sameshi", ta fada tana kallonsu, da tsoron kar su fasa.



"Laaaaah Iya ai wannan ba komai bane, kaddara ce muna mishi fatan Allah ya shiryeshi, kuma hakan ba zaisa mu fasa Aure ba", Adda Nafisa ta fada tana dan murmushi.



jinjina kai Iya tayi kafin tace "to shi kenan mun gode da karamcinku garemu, yanzu yaushe kukeson Auren ya kai?, dan ina son na nuna muku na baku Ƴar kamar yarda kuka nuna kaunarku garemu", ta fada tana rike hannun Adda Zainab.



"Iya in ba damuwa nan da sati daya, domin zai tafi da ita ne chan gurin aikinshi da yake Soja ne to baya zama gida sai in yazo hutu, kuma bamu buƙatar komai naku domin komai da akwai shi kama daga kan, kayan ɗaki, kayan kitchen da sauransu", Adda Zainab ta fada tana murmushi, jijina kai Iya tayi kai Iya tayi tare da ce wa "to shi kenan mun gode sosai", Fira suka ci gaba da yi, cikin raha tana tsokanarsu suna tsokanarta, har guraren magrib kafin su wuce gida, cike da jin dadin karamcin Iyayen Nazlah gare su.




Bayan kwana biyu, suka ririɓo kayan sa biki suka kawo kama daga kan goro,biscuits , sweet , chew gum, da kuɗi na sa rana da sauransu, ranar da aka aiko ranar Abba ya sani, sai dai ya yi ko in kula da maganar da Ummu ta kara tuntuɓarshi ma sai cewa ya yi "ke..! ki ƙyale ni da maganar auren nan, ina ruwa na da wani auren ta, ku da kuka ruruɓo abun ku ku zakuyi, dan wallahi tsinke ba zan bayar ba", ys fada yana ficewarshi, haka Ummu ta zauna Cikin damuwa, da tunanin anya Abba zai chanja halinshi kuwa, tun da ta aureshi take fama dashi bata taɓa jin dadin aure ba a rayuwarta, kuma haka taƙe haƙuri da dauke kai, dan tasan abun da Iya ta mata A rayuwa har abada ba zata iya biyanta ba, shi yasa take yada kai bata taba daga kai ta kalleshi ba, in yana mata abu, kawai ta dauka ita ibada take, kuma mai ibada baya taɓa sarewa, domin Aljanna yake nema.



Yah Haleem kuwa da aka fads mishi, sai da ya nuna ƙin amincewarshi dan Yasan Nazlah Yarinya ce sosai , sai dai da Iya ta fatattakeshi ta nuna mishi da Yarda ake Aure sai ya haƙura badan ya so ba, haka akayi ta shirye-shirye, Oganninyar kuwa ita bata wani sani ba tadai ga ana ta ɗura mata abubuwa masu zaƙi ana mata shirye - shirye, amms kwaɗayi da wauta yasa ita duk abun da aka bata ba tambaya take shanyewa sa boda duk masu zaƙi ne.



maganin Infection kuwa shine akan gaba wanda ake bata(uhmmm Yan uwa, in har Yarki budurwa ce zatayi Aure, maganin Infection ya kamata ki fara bata, dan shine akan gaba, Maganin Mata babu abun da yake sai tatso ni'imarta ta tattaru guri daya, sannan yana kara dankarar da infection a jiki, in zaki siya maganin mata na dubu 5k to ki siya maganin Sanyi na 15k , domin yanzu ba babba ba Yaro, ba mai kuɗi na talaka, kowa yana fama da wannan ciwon sai dai na wani yafi na wani,infection babban matsala ne,domin yana hana jin dadin Auren, yana sakar da wasu ciwuwukan da dama, sai kiga anyi Aure wata daya, biyu, ukku, an fara samun matsala, Yarinya bata jin dadin aure, ko Mijin baya jin dadin Mu'amulla da matar, sai kiga kwana kaɗan da aure an fara kawo kiki ƙorafe-ƙorafe, shin mai yake kawo wannan matsalar ?, amsan infection, idan mai ba zaki mata maganinshi ba, to karki dura mata kayan mata, dan har gwara ki barta ba ki mata komai ba, dan zai kara yawan infection din a jikinta, sannan zai dakushe mata ni'imarta , kinga kuwa gwara a ki barta haka , Allah dai yasa mu dace, a kula maganin Sanyi shine gaba da na Mata).




Ana sauran kwana biyu biki da daddare, Hameed yazo gidan Hajiya, bayan sun gama gaggaisawa Adda Zainab ta jaashi bedroom dinta, kallonshi tayi tare da cewa "Auta...!", kallonta ya yi,yana son yaji mai zata ce.



gyara zamanta tayi da kyau tare da cewa "ni na maka katsalandan kuma ina fatan ba zaka bani kunya ba zaka rike zaɓina da hannu bibiyu?", kallonta ya yi cikin rashin fahimta, tare da cewa "katsallandan din mai Adda? ai babu wani katsalandan da zaki a cikin rayuwata, nasan komai zakiyi ba zaki taɓa yi dan ki cutar da ni ba",,murmushi tayi tare da cewa "to naji dadi da ka fahimci haka,kasan ba zan taɓa cutar da kai ba, " jinjina kanshi ya yi.


"toh Aure na nema maka, kuma an bamu , jibi daurin aure, sai dai kayi hkr nayi lattin gaya maka", idanunshi ya tsura mata cikin fargaba yace "Adda Aure fa?, duka yaushe nayi wanchan da zaki ce kuma wani aure yanzu?, " wani kallo ta mishi tare da cewa.



"ni na nemo kuma an bani ,bani da damuwa da yaushe kayi wanchan, kaje ka ci gaba da shirye-shirye ka dan bama buƙatar komai naka , in kuma ban isa da na zaɓa maka mata ba sai ka faɗa min", ta fada tana tsura mishi idanunta, masu matuƙar kaifi da kwarjini.




girgiza kanshi ya yi, tare da cewa "ni bana da sha'awar aure yanzu, hasali ma ni yanzu tsoron mata nake, duba da abubuwan da naga Sadiyya nayi, sai nake ganin kamar duk daya suke", dafa kafadarshi tayi tare da cewa.



"na tabbatar wannan ba zata maka abun da Sadiyya take yi ba , ya bawa da tarbiyarta da kamala tare da kwarjini yasa na nema maka ita, kuma kowa ya yi na'am da ita, sannan Yarinya ce danya shataf wadda kai zaka koya mata komai na rayuwa, ka zaka koya mata yarda zata yi kuma duk abun da ka koyar da ita tashi zata tashi", tura baki ya yi gaba tare da cewa "Yar raino zaku bani dai, wadda duk zan koyawa wannan ai sai yar 10 to 12,"ya fada yana kallonta.



Yar dariya tayi tare da cewa "to ka kaddara ma mai kamar wannan shekarun ce Yarinyar, " bude baki ya yi yana kallonta kafin yace "Adda 10 to 12 years, to a tatsi mage ko a kashe?,k




07033371851


```DAGA TASKAR ƳAR LELEN ROYAL STAR```
[12/21, 9:28 PM] YAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♂️🧚‍♂️: 19-20.



"""""""""""Harararshi tayi tare da cewa "duk ma yarda aka mata dai-dai ne, tunda tona min Asiri kake da niyyar yi", "uhmmmmm ba zaki gane bane Adda girman bukatata ta wuce na Yar 20years ma balle 15, kaya kawai zaku haɗani da shi", ya fada yana mikewa.


"ngd kuma ba sai ka gwadamin ban isa da kai ba", ta fada tana haɗe fuskarta alamar tayi fushi, matsawa ya yi kusa da ita, tare da riƙe hannunta yace "Adda na Amince..!", yana fadar haka ya fice daga bedroom din, cike da murna ta fito itama, haɗa baki suka yi gurin cewa "Adda ya amince?", wani kallo ta musu irin na wasa tare da cewa "ko yake jira sai kun amince", ta fada tana zama, dariya duk sukayi dan susan dole ma ne ya amince.



Washe gari gaba dayansu suka tafi Saloon , sai da suka je kafin Adda Zainab ta sa driver ya je ya taho da Nazlah , cikin minti kaɗan ya je gidan, kafin ya je ma Nazlah ta shirya dan sun kira Ummu ta Yar kwararraɓar wayarta sun sanar mata,cikin shiga mai kyau Nazlah ta fito sai kamshi take ,mota Driver ya bude mata, shiga tayi ta hakimce a baya, sai da ya rufe kafin ya koma mazaunin driver, ya kunna motae suka kama hanyar shagon saloon din.



15minutes ne ya sadasu da ƙawattacen shagon Saloon din da yake kan Hanyar Kano road , shago ne mai kyau da tsari , na masu kuɗi, bayan sun karasa ya bude mata motar ta fito, jagora ya mata har ciki, da Sallama ta shiga cikin shagon, duk juyowa sukayi da murmushi kan fuskarsu suka amsa mata, ƙarasawa tayi ta ɗuka har ƙasa ta gaishesu, Jaan ta Adda Zainab tayi jikinta ta rungumeta, tare da cewa "kina lafiya Ƙanwar Adda?", ta fada da murmushi kan fuskarta.



jinjina kanta tayi alamar lafiya lau, rungumeta suka shiga yi daya bayan daya suna tambayarta lafiyar ta, Haleesa da take mata murmushi tace "Sannu Amaryar Auta..!", dan murmushin yaƙe ta mata dan sam bata fahimci kan maganar ta ta ba, karɓar Ƴar Adda Zainab tayi ta zauna kusa da Haleesa tare da fara ma wasa.



Wata Yar siririyar Mata ce ta fito daga wata yar kofa tana cewa "Ayya kuyi hakuri na barku kuna jira na, yanzu me za'a fara muku kuma da wa za'a fara, "ta fada tana dan murmushi.


Nuna Nazlah Adda Zainab tayi tare da ce wa "ita zaki fara mawa gyaran jiki zaki mata da gyaran kai, sai ki wanke mata ƙafa , " kallon Nazlah tayi tace "kina son kitso?", da sauri ta girgiza kai alamar bata so, "mai yasa ba za'a miki ba? , zai fi fito da ke", dan kwaɓe fuska tayi tare da cewa "kaina namin ciwo in aka min", ta fada tana matsawa kusa da Mai gyaran jikin.



wankin ƙafa aka fara mata, duk da cewa ƙafarta tsaf take ga laushe da tsantsi, hakan yasa da aka wanken sai ta kara kyau da tsari, kumba ta gyara mata ƙafar tayi tarrr² har wani jaa² take kamar jini zai fito, wani ɗaki suka shiga anan aka mata dilka da halawa, komai binshi da ido Nazlah take, dan ita wannan abubuwan bata sansu ba, sai kallon jikinta take, tana mamakin wai ita ce ta koma haka, jikinta ya koma kalar na jarirai, sai shinning yake gwanin burgewa, bayan an gama turara mata jiki da turaren jiki mai kamshi da zama cikin jiki suka fito.



duk tsura mata idanu sukayi suna kallon zallar kyau irin na Nazlah dan haskenta ya kara fitowa sosai , dan in kai mata kallo daya ba lallai je ka iya gano daga wace ƙasar ta fito ba, dan kwata² batayi kala da Yan nigeria ba, zaunar da ita tayi gurin da zata wanke mata kai, dan kwallin kanta da tunda tazo bata cire ba Matar ta kama ta fara warwarewa, kyakyawan gashin kanta ne ya fara warwarewa daga gammon da ta mishi.



tana zare gammon gashin ya warware gaba dayanshi ya zubo akan bayanta, faɗowa Haleesa ta kusan yi sa boda tsananin mamakin irin yawan gashin kan Nazlah, duk da Ahalinsu na da gashi sosai Amma bata taɓa ganin mai yawan gashi da kyan gashi ba irin na Nazlah, matsawa tayi gurinta jikinta na rawa ta kama kasan gashin tace "Duk wannan naki ne..!?", gyaɗa kanta Nazlah tayi.



su Adda Dariya suka fara wa Haleesa dan sosai take zuba santin sama nata ne gashin, duk kuwa da cewa suma sun cika sa matsanancin mamakin yarda Yarinyar ta tara abubuwa da yawa, na daukar hankali.



gyaran gashin aka shiga yi mata, cikin kankanin lokaci aka gama, dan gashinta yana da taushi kamar na jarirai gashi da suɓi uwa-uba bashi da cunkushewar nan,a yaryare yake, duk kuwa da cewa yana da yawa amma bai cunkushe ba, bayan an gama Adda ta bada Ribbons guda huɗu aka daure mata kanta dasu.



izuwa lokacin idanun Nazlah sunyi jaa, dan gaba daya hankalinta ya fara tashi da yarda ake jaan gashin kan nata , dan bata son abun da zai taɓa kan, dan ma tana jin kunyar su Adda ne ba zata iya musu, musu ba da tuni ta mike .



lokacin kuma Yan taya mai shagon aiki suka zo, umarnin fara hakafarawa ta basu, hakan yasa suka farawa su Adda Zainab, Nazlah kuwa Abin ci Adda Zainab ta sa aka kawo mata , ta zauna chan bayansu suna ci ita da Yar Adda Zainab.



ba a dau wani lokacin mai yawa ba, aka gama musu dan nasu bai dauki lokaci kamar na Nazlah ba dan wankin kai ne kawai da wankin ƙafa, bayan sun gama, suka tafi gidan su Nazlah gaba daya, lokacin Yan Uwan Iya duk sun hallara gidan ana ta hada ², ana gyaran kayan miya da sauran kayan Abinci.




.



Tara ta mutunci aka musu , aka kawo musu Abin ci da Lemu wanda Iya ce ta bada aka karɓo musu, bayan sun gaisa suka bawa Ummu haƙurin kayan lefe da ba'a kawo ba, sai taje chan zasu bata kayanta, murmushi Iya tayi tare da ce wa "Ba komai ai gwara ma da baku kawo ba kuka barshi chan, dan wahala za'a sha sai an kawo kuma a mayar", basu wani jima ba sosai suka tayi suna godiyar karamci irin na Yan gidan.



Washe gari, Nazlah da rigama ta tashi,wanda hakan ya haddasa mata zazzaɓi , sai dai Iya ce ta dauketa zuwa gidanta, domin chan ne mai rangwamen hayaniya.



Tun 10 mutane suka fara daddala, zuwa gurin daurin Auren duk kuwa da cewa ba wata Gayya sukayi sosai ba, dan Bangaren su Nazlah Yan uwa kawai suka gayyata, Chan gidan Ango ne suka yo gayyatar mutane, 12 bata ƙarasa ba Adda Zainab da Haleesa da Hameed duka zo gidan .




lokacin da Hameed ya fito, ya yi mugun mamakin ganin Abokanshi a ƙodar gidan , dan shi kanshi jiya yaji zancen Auran, bai kuma fadawa kowa ba dan har Sadiyya bai faɗa mata ba, gurinshi duk suka tattaso suka zo, Khalil ne ya dan duku ƙafadarshi yace "Buddy ashe dama shirin shigewa kake daga ciki, amma ka bari ciwo zai kashe ka, amma wallahi ka shammace ni,kawai sai dai Invitation card naga yana yawo a media , na nemi wayarka kuma shiru ba'a samunka", dafe kanshi ya yi, tare da cewa "yi hkr pls kasan yana yin abun ne sai a hankali, dadin media din kenan ai, amma naji dadin ganin ka wallahi, na gode maka".




Ammar ne ya dan duki kafadarshi daga baya yace "mu da baka ji dadin ganin mu ba, ba komawa zamu yi ba ai", juyawa ta yi, yana dariya suka rungumi juna, fira suka ci gaba dayi irin ta Abokai, Adda Zainab da Haleesa kuwa tuni suka shige ciki.




Ko da suka shiga ciki ,cikin girmamawa ake gaishesu har ƙasa, har suka shiga Ɗakin Ummu da take cikin shiga mai kyau shar³ da ita sai murmushi take, nuna wa Adda Zainab kusa da ita tayi, zama tayo suka gaggaisa, fira suka shiga yi da dangin Iya, da yake duk fara'a garesu ga saurin sabo yasa, suke firarsu cikin jin dadi, da tattauna yarda zancen Auren yazo, Haleesa ce tace "Ummu ina Amaryar Auta,da Iya?, naga ban gansu ba", dan murmushi Ummu tayi tare da cewa "Suna gidan Iya ko asa a raka ki chan din ?".




dan gutun murmushi tayi tare da ce wa "Laaaah Ummu nasan gidan bari na je", ta fada tana mikewa, Amsar Yar Adda Zainab tayi ta fice da ita zuwa gidan Iya.




Da Misalin karfe 1pm na ranar Juma'ah , aka daura auren Hameed Abubakar da Nazlah Lawal akan sadaki naira dubu dari biyu, wanda Adda Zainab ce ta bada kuɗin sadakin, Daurin Auren sosai ya samu halarta

Please Login or Register in order to submit comment