Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

danna belt dib da yake jikin kofar.



da Sassarfa ta karasa zuwa gurin ƙofar, tana budewa ya fada jikinta, tare da sauke numfashi mai nauyi, cikin siririyar muryarshi mai amsa amo yace "Miss you so much Maa", shafa kanshi tayi, tare da sakar mishi wami ni'imtaccen Murmushi wanda a fuskar Mahaifiya ne kawai ake samushi , ta sakar mishi , tare da cewa "ya hanya ?", kanshi ya daura akan kafadarshi, tare da cewa "Alhamdulillah", jaan hannunshi tayi suka fara takawa izuwa cikin palon gidan, zaunar dashi tayi akan kujera, tare da zama gefenshi tana kallon.




cike da mamakin ramar da ya yi, tace "Muhammad", a hankali ya Amsa mata cikin sanyin murya, taɓa kashin wuyanshi tayi tare da cewa "me ne ne wannan, ciwo kayi ne", ta fada tana zazzaro idanu.




Siririn Murmushi ya saki , tare da cewa "Qlau nake Maa, kawai yana yin aiki ne ba hutu", jinjina kanta tayi bawai dan ta yarda da cewa aiki ne ya sanyashi rame ba ,haka sai dai in wani abu, amma da yake bata son sanya wani abu tsakaninsu yasa tayi shiru.





Shafa cikinshi da yake mishi kuka , ya yi tare da kallonta yana kwaɓe fuska, alama ta mishu da ido alamar me ne ne , cikin muryar Shagwaɓa da Sakalci yace "I'm feel hungry", fa fada yana yamutsa fuska.




kama hannunshi tayi suka nufi dinning room , tare da cewa , "ai dama komai an gama kai ake jira, " ta fada tana jaa mishi kujara, zama ya yi, yana kallon coolers din da aka jajjera akan dining din, zama tayi kusa dashi, tare da bude wata babbar cooler , haɗɗaɗiyar fried rice ce ta bayyana, wadda kallo daya zaka mata kasan ta hadu saboda yarda take daukar ido da yarda tayi kyau, tasha kayan haɗi sosai.



zuba mishi tayi kafin ta kara bude wata cooler farfesun kifi ne ya bayyana a ciki sai kamshin kayan kamshi yake, ya yi kyau shima, cikin dan bowl ta zuba mishi, tare da kara bude wata cooler tuƙƙaƙen tuwon Shinkafa ne , ya bayyana, zare ido ya yi , ganin zata zuba mishi.



kwaɓe fuska ya yi, tare da cewa "ni da wa?", harararshi tayi, tare da cewa "kai da wanda ka gani a kusa" ta fada tana ƙoƙarin zuba mishi, da sauri ya rike hannunta tare da cewa,"wannan ma is okay ", ya fada yana sanya spoon s ciki, cikin natsuwa ya fara ci da Bissimillah dauke a bakinshi.




tun da ya fara ci, baiyi magana ba, har ya tsame spoon din daga cikin Abincin tare da furta "Alhamdulillah", kallon shi tayi da mamaki ƙarara akan fuskarta, "mai kake nufi?", ta fada tana kallonshi.




kwaɓe fuska ya yi, tare da cewa "Allah kuwa na ƙoshi", ya fada yana kwantar da kanshi akan kafadarta, "Baka cin Abinci shi yasa ka rame ka lalace haka, to ba zan lamunta ba, maza² dauka kaci kafin na ɓata maka rai", ta fada tana haɗe fuska, shiru ya yi, dan baisan kuma mai zai kara cewa ba, dan ya mugun ƙoshi.



ganin ya yi shiru, yasa ta dauki Spoon, ta dibi abin cin ta fara bashi, bai mata musu ba ya bude baki, baifi 3 spoon ba ya fara kakarin amai, a dan tsorace ta jaan ye hannunta, daga kan spoon din, mikewa ya yi, da sauri ya nufi toilet din dake cikin dinning room din.



kafin ya ƙarasa shiga, aman ya taho mishi, da sauri ya duƙa ƙasa, ya fara kwarara amai, a dan tsorace ta biyu bayanshi, duƙawa tayi kusa dashi, tana shafa bayanshi, tun yana aman cikin hayyacinshi, har ya fita a hayyacinshi, aman ma har ya koma babu komai cikinshi, sai kakari da wahala.




dakyar aman ya tsaya, wanke mishi bakinshi, tayi ta kamashi suka fito palo, zaunar dashi tayi akan kujera, tare da zama, kanshi ya daura akan cinyarta ,yana sauke numfashi, ganin yarda yake yasa Nadama saukar mata, tasan tun yana Karami in har yaci Abin ci da yawa to karshenshi sai dai ya Amayar dashi, bacci ne ya dan daukeshi, baiyi ko 3 minutes yana baccin ba ya farka , a hankali ya fara bude idanunshu, har ya budesu tarrr akan fuskar Hajiya , da sauri tace "Sannu ya jikin naka", ta fada cikin tausayawa.



murmushi ya yi, tare sa cewa "ni babu abun da yake damuna", ya fada yana mikewa zaune, hamdallah tayi, kalle² ya fara yi cikin palon, kafin ya kalleta yace "Hajiya ni banga Auta ba", ya fada yana kara jujjuyawa.




Yar dariya tayi, tare da cewa "kaga ta tafi gidan Addarta ", da mamaki ya kalleta , tare da cewa "Wace Addar bayan duk basa Ƙasar", zare ido tayi, kafin tace "Aisha Man , ai sun dawo kusan two weeks da dawowarsu, "ta fada tana kallonshi, taɓe baki ya yi, tare da cewa "Lallai Yayah, ashe ta dawo shine bata fada min ba, ta kyauta ai", ya fada yana mikewa.




kallonshi tayi, tare da cewa "ina zuwa haka?", dan tsayawa ya yi, tare da cewa "gida zanje Hajiya, zuwa Anjima zan dawo", ya fada yana yin gaba, fatan sauka lafiya ta mishi, kafin ya fice.



Yana fita ya tarar da Yaranahi, zazzaune suna cin Abinci, suna ganinshi suka zabura suka mike gaba dayansu, suna sara mishi, kowa gurin mota ya nufa, murmushi ya musu, kafin yace "ku zauna ku gama cin Abin cin, in kun gama ku shiga da kayan ciki, ni zan tafi gida, in yaso in kuka gama kwa taho", ya fada yana wucewa.



Abbas ne ya yi, saurin bude mishi mota ya shiga, shima shiga ya yi mazaunin driver, tare da kunna motar, tafiya ya fara yi, tun kafin ya karaso bakin get aka bude musu, yana zuwa ya fice, kan titi ya hau, kasantuwar Unguwar kusan gaba dayanta titi ne, dan Unguwar Sarakai ce , da manyan Yan siyasa, basu wata tafiya sosai ba suka ƙaraso Barhim .




Tunda suka tun karo Unguwar zuwansu , ya isar da Yan Unguwar, hakan yasa kowa ya shiga taitayinshi, dan baya wasa da mutum, in ka mishi iskanci ko ka nemi yiwa wani to taka maka wuya zaiyi ba abun da yasha mishi kai, Suna karasowa getman din ya wangale musu get din gidan suka shige.



sai da Abbas din ya dai-daita parkinga kafim ua fito, yana shaƙar daddar iskar da take kaɗawa, cikin izza ya fara takawa cikin gidan, bai ko damu da Sojojin da suke sara mishi ba, yana zuwa jikin kofar ta bude da kanta, ƙafarshi na taka shiga cikin palon yaci karo da Plate a ƙofar shigowa palon.



da mugun Mamaki yake kallon cikin palon, ganin komai a hargitse, da alama ɓa tunda ya tafi babu abun da aka gyara cikin gidan, da Sallama ya shiga cikin palon, da sauri Sadiyya ta mike tana kallonshi, fuskarta ta bayyana tsantsar farin cikin ganinshi.


gurinshi ta nufi tana washe baki, cikin muryarta mai dadi tace "barka da zuwa, saukar yaushe?", ta fada tana karɓar brief case din da yake hannunshi, sakat mata ya yi, ya shige ba tare da yace mata komai ba.





*********



"Ke! Nazlah tashi kizo ki shirya, ki tafi Makaranta dan su Salamatu tun dazun naga sun wuce Amma ke baki da Niyyar mikewa ki tafi", tura baki Nazlah tayi, tare da cewa "to kema Umma mi Wallahi na gaji", ta fada tana , ci gaba da yanka kyallayen da suke gabanta.



Haleem ne da ya shigo yanzu, ya daka mata tsawa, tare da cewa "Zaki tashi ko sai na tattakaki Sakarar Yarinya, " ya fada kamar zai duketa, da sauri ta mike tana diddira ƙafafunta ta shige ɗaki, ta kusa Minti goma da shiga amma bata fito ba, "zaki fito wai ko sai na shigo ɗakin", Haleem ya fada cikin muryarshi mai dadi da kuma Amo, a hankali ta bude labulen ɗakin ta fito tana share hawaye, fuskarta tayi jargwab da hawaye, gabanshi ta tsaya tana cuno dan karamin bakinta.



kallo ya ƙare mata tare da cewa, "shige ji tafi, kuma Wallahi na fito na gsnki a hanya kina wasa ko kin tsaya sai na ɓallaki", ya fada yana dungure mata kai, kuka ta fasa tare da ficewa, tana kukan ita an tsaneta komai sai ace dole tayi, a haka ta kama hanyar zuwa Makarantar , babu nisa sosai daga gidansu zuwa Makarantar sai dai, sai an tsallaka titi, tana cikin tafiya ta haɗu da wani Yaro dan Unguwarsu mai suna Idi, ganin tana kuka yasa ya fara mata dariya.



da sauri ta ɗago kanta tana kallonshi, cikin hasala da jin haushi, kan Yaron tayi da gudu, tana zuwa ta cukwikuyeshi
, ta hadashi da bango, tare da fara gwara kanshi, tana zazzaga mishi ruwan masifa, yakushinta Yaron ya fara yi yana neman hanyar guduwa.




damkarshi tayi, tare da kafa mishi cizo a wuyanshi, ta rike ta cije , taƙi saki, ihu Yaron ya saki, yana son ta sakeshi, amma ta gama duƙunƙuneshi, mutane ne suka fara taruwa, suna son rabasu, amma taƙi rabuwa dashi, taƙi sakin Yaron ga wuyanshi har ya fara jini , wani Mutum ne, yazo ya fisgeta daga jikin Yaron tare da dalla mata mari.



Tsautsayi yasa Yatsan hannun mutumin ya fada cikin bakinta, wani wahalalan cizo, mai ratsa kwanya , wsnda yake bi ta cikin jijiyoyin jiki ta sakar mishi, wanda yasa mutumin, ba shiri ya saki ihun azaba, tana ganin idanun mutane sun fara yo kanta, ta saki hannun mutumin da gudu, kamar iska haka ta tsallake titi zuwa Islamiyarsu.



Tana cikin gudun ta haɗu da wani tsoho Daga mata hannu ya yi, itama ta daga mishi, cikin kwala murya yace "ki kula ana Taro Makarantarku, kar ki bari a duke ki, ki gudu", ya fada yana juya baya.



babu wanda ya lura da lokacin da ta shige ciki, ruɗewa Mutumin ya yi, yana cewa "Aljana! Wallahi Aljana ce kun gani ta ɓace ɓat", ya fada cikin ruɗu da tashin hankali, wani Matashi ne yace "Wallahi Alhaji ba Aljana bace, mutum ce, Allah dai ya shirya, dan fitinar Yarinyar nan tayi yawa", ya fada yana jinjina kanshi.





itana shiga cikin Islamiyyar tasu ta tarar da Malam Arabi na dukan latti, tsuru² tayi da ita, ba abin ta koma waje ba tasan boom din da ta haɗa, gashi bata kaunar bulala ko kaɗan dan har in aka mata to ranar bata kwana lafiya, take dubura ta faɗo mata, ana dukan wata ta mike, tabi bayanta, kasantuwar suna da yawa wanda aka duƙa, ba lallai ne a iya ganeta ba, har ta gota Malamin wata Yarinya tace "Malam Arabi ga Nazlah chan ta ruga baka bigeta ba", da hanzarinshi ya juyo, tare da kwalala mata manya²n idanunshi masu kama dana Nufawa.



"Ke! Uban wa yace ki tashi ban dukeki ba ki gudu?", ya fada yana zazzare mata idanunshi, cikin jin haushi tace "Malam Arabi ka daina zagar min Uba kaga dai babu abun da ya maka", ta fada tana dalla mishi harara dan arayuwar ta tsani zagi, "Ke! dan Ubanki ni kike cewa haka?, Nace Uban wa yace ki tashi ki tafi?", cikin dakiya da nuna rashin tsoro, ta kawar da kanta tare da cewa "Ubanka ne", ta fada tana karkaɗa kanta.



Ware idanunshi ya yi, da mugun Mamaki, cikin Azama ya damki wuyan hijab dinta tare da cewa "Kutumar Uba, dan Ubanki ni kike zagi?, Ashe Yau zan ci Ubanki kuwa", ya fada yana zuba mata bulala a gadon bayanta.



ihu mai karfi ta saki, tare da cewa, "ba kaine kace Uban wa ya sani guduwa ba, kuma ai Ubanka na haɗu dashi yace min in naga ana taron Makara na gudu, kuma dan na fada maka shine zaka duke ni", ta fada tana ƙoƙarin kwacewa, zuba mata bulalar ya kara yi a tsakiyar kanta, wadda ta zago har fuskarta, tuni shatin bulalar ya tsaga fuskarta ya yi, wani jaaa lokaci daya abunka da farar mace.



jin yarda bulalar ta ratsa mata cikin jikinta, da kwanyarta har tana barazanar illata mata jinta da ganinta yasa ta faɗi kasa, yana ƙoƙarin riketa, ya mikar da ita, ta shige cikin rigarshi Yar shara,Makalewa tayi tana gunjin kuka, ƙoƙarin fiddota ya shiga yi, amma ta manne.


gefen Mararshi ta samu, ta gasa mishi wani Lalataccen cizo, mai illata yan hanjin ciki, riƙe gurin tayu kam taƙi sakinshi, zufa ce ta fara karyo mishi, cikin jikinshi, ba abin ya yi, ihu ba ace Malam na kuka, gashi kuma ya kasa cirota daga cikin jikinshi, haka ta ringa bi tana mammana mishi cizo duk inda ta samu, yakushi kuwa, babu inda bata ya kusa ba, ƙoƙarin cire rigar ya fara yi, amma ta rike kam taki sakin rigar, taki kuma daina cizonshi.




ganin Yana niyyar kashe kanshi, yasa ya saki ihu tare da cewa "Wayyo Jama'a ku kawo dauki, wannan shegiyar Ƴar zata kashe ni, wayyo Marata wayyo", ya fada yana ƙoƙarin guduwa, hardewa ya yi, ya fadi cikin filin makarantar.



birgima ya fara, yana kokarin cireta, amma abu yaci tura, hakan yasa yaci gaba da zunduma ihu, tuni Malaman Makarantar sunzo sun zagayesu, dakyar da jibin goshi, suka samu suka fito da ita daga jikin Malam Arabi, ana fitar da ita ya fice daga makarantar da gudu, yana haki,bai tsaya ko ina ba sai da yaje gida, zubewa ya yi a tsakar gida yana haki, Matarshi ce ta kalleshi, tare da cewa "Lafiya Malam", girgiza kanshi ya fara yi, alamar ba lafiya, sai dai ya kasa yin magana.




ruwa ta kawo mishi, dakyar ya sha, yana sha ya fara cewa "Wallahi ba Mutum bace! ba mutum bace!! nace miki Aljana ce", ya fada yana zazzare idanu tare da leƙen hanyar waje, ita kuwa ta kasa gane maganar da yake yi, sai binshi da kallon mamaki take, ganin sahun cizo na haƙora raɗo² akan fatar cikinshi, fa yakushi har kan kirji.



sai lokacin ta lura da babu komai jikinshi sai gajeran wando, "Malam ina rigarka?", ta fada tana mishi kallon tuhuma, "na fada miki ba mutum bace", cikin tsawa tace "kai Malam yimin shiru, ashe halin da ka koma kenan, kwartanci ka fara, shine har da zuwamin ba riga, to ai na gani basai ka karamin wata magana ba, maci Amana kawai, kuma Wallahi naji dadi da aka maka haka, naso ma da sun gurguntar da kai, kaga kwartanci ya yi rana", ta fads tana mikewa daga gurin ta shige ɗaki abinta.



************


Bulali Malaman suka sanya aka cicciro musu, suka sanya Nazlah Office, zasu duketa, hankalinta in ya yi, dubu ya tashi da ganin irin bulalan da aka zagayeta dasu, Faɗuwa tayi a gurin , jikinta na wani kyarma, daga baya kuma ya saki bata ko motsi, daya daga cikin Malaman ne ga zabga mata bulala, akan ƙafafunta, tare da cewa "tashi Munafuƙa yau sai kin gane kurenki, na abubuwan da kike yi, dama dama muke jira, yau kuma gata ta samu, ba Aljannu ba, ko Uban Aljannu ne yau sai mun ci ubansu", ya fada yana yin ball da ƙafafunta.



wani Uban ihu ta kwarara, tare da fara wani Yare wanda duk cikinsu, babu wanda ya iya gane mai take cewa, Malamin ne ya dagota tare da haɗata da bango, ya dago bulala zai zabga mata, wani Wulaƙantaccen kallo ta watsa mishi, tare da sanya hannunta dauki wata bulala da take kusa da ita, ta zabga mishi akan sankonshi , a ruɗe ya saki bulalar hannunshi, yana dafe kanshi da yaji kamar an sauke mishi shi, kafin ya yi wani yunkuri, ta kara zabga mishi a gadon bayanshi, gantsarewa ya yi, tare da sakin ihun azaba,
ganin tana dukanshi, yasa gaba daya Malaman suka yo kanta, tama cikinsu tayi, tana dukanshi suka dukanta, abun ka da Jinnu , karfi ba daya ba, tuni ta haɗa musu jini da Majina, cewa take "Uban waye yace ku taɓa mana Goɗiya, yau sai kun gane baku da wayau, dama ku Bil Adam dinan baku da mutunci, bakusan kawaici ba, kuma baku da kunya, daga Yau ko wani ne yace ku kara taɓa ta zaku ga abin da zai faru da ku, marasu kunyan Wooofi kawai", wata murya da sam batayi kama da tata ba ta fada, tana zazzare musu idanu, karatu suka haɗa baki gurin yi mata.



dariya ta sheƙe, da ita, tare da karasa musu karshen Ayar da suka dauko, haka suka dunga yi, tana dukansu suna karatu tana karasa musu, duk surar da suka dauko ita take karasa musu.



da gudu, suka bude office din suka fice, ita kuwa Hamma ta buga tare da sulalewa a gurin Summamiya, Malamai kowa ya kama gabanshi, Ɗaliban ma ganin Gwagwarmayar da akeyi yasa kowa warewa, dan babu mai zama anan wannan badaqalar............



Ga duk mai so, zai iya min magana ta number na kamar haka👇

07033371851



```DAGA TASKAR SALMAJI / ƳAR LELEN ROYAL/ SARAUNIYAR YAƘIN MARUBUTA```
[12/21, 12:10 PM] YAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♂️🧚‍♂️: ☘️☘️ *NAZLAH*☘️☘️





*DAGA AL[]ALAMIN*




SALMAJI/[]AR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️






*WANNAN LITTAFIN DAGA FARKONSHI HAR KARSHENSHI, SADAUKARWAR NE GA YAYATAH (MARYAM YUSUF) WANNAN LITTAFIN WAKE NA RUBUTASHI, KIYI YADDA KIKESO DASHI, ALLAH YA RAYA MIKI ZURI'ARKI, YA KUMA K'ARA RUFA ASIRI DUNIYA DA LAHEERAH...*



*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*




13-14




""""""""""""""Babu wanda ya kula da Nazlah kowa ta kanshi ya yi, babu kuma wanda ya yi tunanin zuws gidansu ya faɗi halin da take ciki.



Ummu tana ta jiranta, dan an kawo mata kashedinta har gida, hakan yasa take jiranta taji ba'asin Abun da ya faru, kafin ta dauki mataki a kanta, shiru² Nazlah bata dawo ba har gabanin Magrib, hakan yasa hankalinta ya tashi, ta kasa zaune ta ƙasa tsaye, tana cikin Safa da marwa, Yah Haleem ya shigo, kallonta ya yi tare da cewa "Ummu Lafiya kuwa?", ya fada yana kallonta, da sauri ta juyo gareshi tare da cewa "Nazlah ce bata dawo ba, tun ɗazun da ta fita Islamiyya, gashi Abbanku baya nan, kuma ya hanani fita in baya nan, ko zaka je ka duba min ita ?", ta fada tana kallonshi, "to Ummu bari naje na duba", ya fada yana juyawa.


cikin sauri yake tafiya zuwa Makarantar tasu Nazlah dan duhu har ya fara rufawa, cikin sa'a ko da yaje makarantar a bude take, sai dai ba kowa a ciki, hankalinshi ya fara tashi, cikin daƙiya ya fara dudduba Ajujuwan Makarantar, sai dai ba kowa a ciki, kuma duk a bubude, cike da tsananin mamaki yake kallon Ofishin Malaman da yake a bude , kuma makarantar ba kowa, hankalinshi ne ya kaiga wani waren takalmi da ya gani yashe a ƙasa kusa da Ofishin, tafiya ya fara yi zuwa ofishin, da sauri ya shiga yana furta "Innalillahi Nazlah! Nazlah!! Nazlah!!!", ya fada yana jijjigata.


A hankali ta fara bude idanunta, da suka mata nauyi, "Yah Haleem..! ta fada tana shigewa jikinshi", mikewa ya yi, da ita jikinshi ya nufi hanyar waje, da ita rungume a jikinshi, hanyar gida ya nufo da ita, yana cikin tafiya yaji an kwala mishi kira, da sauri ya juya yana kallon Iya da take nufoshi, da sauri ta ƙaraso gareshi tare da cewa "kaga Nazlan?", Nuna mata ita ya yi, tare da cewa "gata bacci na tarar da ita tana yi, babu kowa a makarantar sai ita daya", ya fada yana direta ƙasa, ganin yarda take ta mutsu² da son ya sauketa.



Yana sauketa, ta Afka kan Iya tare da cewa, "Iya goyani bacci nake ji", ta fada tana riketa, da mamakina babu ko kunya Iya ta duƙa Nazlah ta haye bayanta, zaro ido Yah Haleem ya yi, tare da cewa "Iya dama har yanzu baki daina goyata ba,kar ta je ta karyaki fa", ya fada yana yunƙurin dauke Nazlah daga bayan Iya.


kaɓe hannunshi Iya, tayi tare da cewa "mai yasha ruwanka da harkarmu, baka ji tace bacci take ji ba, " ta fada tana zare dan kwallinta, kyakyawan dogon gashinta mai kyau ne ya bayyana, wanda duk da tsufar da tayi amma yananan sumul sai dai furfurar da ba'a rasa ba akan tsoffafi.



dakyar take takawa da Nazlah akan bayanta amma haka take tafiya, Yah Haleem ya yi, ya yi ta sauko da ita amma taƙi, sai ma kara kankameta da Nazlah tayi ta rumtse idanunta.




*************



Da sauri ta bi bayanshi, tana shiga ta tarar dashi zaune gefen bed dinshi, ya buga uban tagumi, zama tayi kusa dashi, tare da cewa "lafiya kuwa My Solder?", ta fada tana dafa kafaɗarshi.


dago idanunshi ya yi, ya watsasu cikin nata , Cikin faɗa ya ce"wai ke ba zaki chanja halinki ba, duk abun da ake fada miki va zakiji ba, bayan rashin kula da ni , hanzu kuma har wani sabon salo kika koya ba rashin tsafta, duba wai nan ɗakin Mijinki ne, amma kacha² ba gyara ba komai, yanzu wannan rayuwar da kika daukarwa kanki kina tunanin mai daurewa ce, ?" ya fada yana kallonta.


cuno baki tayi gaba, tare da daura kanta akan kirjinshi, "to ba yanzu , zan tashi na gyara ba", ta fada tana mikewa, bathroom dinshi ta fara wankewa, wanka ya shiga, kafin ta fito har ta gyara mishi bedroom, kallon Bedroom din ya yi, jinjina kanshi ya yi, tare da cewa " tab da matsala kuwa", ya fada yana kara kallon bedroom din , dan kawai sunan ta gyara ne, amma babu abun da ta wani gyara, shara ce tayi , sharar ma bata yi ba, dan chan da datti chan share, chan datti haka sharar tayi. , kallon Bedroom din ya yi, jinjina kanshi ya yi, tare da cewa " tab da matsala kuwa", ya fada yana kara kallon bedroom din , dan kawai sunan

Please Login or Register in order to submit comment