Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutane Manya da ƙanana, kowa ka gani fuska washe dan an wadata kowa da komai abin ci da lemuka har ba'a magana.



bayan an gama daurin auren Hannu Yah Haleem ya mikawa Hameed cikin yar fara'a yace "ina taya ka murna, Allah ya sanya Alkhairi", dan murmushin da bai kai ciki ba Hameed ya yi, tare da ce wa "Na gode, uhmmm Haleem ko , Yayan Nazlah?", gyaɗa kanshi Yah Haleem ya yi, murmushi ya ƙara sakar mishi, kafin su zauna cikin Abokan Hameed din ,hannunshi kuma na rike da na Yah Haleem,sai da kowa ya watse Hameed ya rage daga Hameed sai Abokansa ,Adda Zainab ta fito daga cikin gidan, suna haɗa ido ya dan kauda kanshi.



Yar dariya tayi tare da ce wa "Ango kasha kamshi..!", Yar harararta ya yi, tare da dauke kanshi, dan matsawa kusa da shi tayi, tare da cewa "Allah in baka saki fuskar nan ba sai na ɓata maka rai" ta fada cikin raɗa.



kamar zai yi kuka haka yawa fuskarshi, dan wani kalar yanayi yake ji, shi dai ba zaice farin cikin Auren yake ji ba,kuma ba zai ce Yana jin baƙin ciki ba, kawai dai yana yi yake ji , shi ba sama ba shi ba ƙasa ba, gadai shinan.




riƙe hannunshi tayi tare da cewa "Muje ciki ka gaiyar da mutane", ta fada tana fara takawa, bin bayanta suka yi duka da Abokanshi, sai baza kamshi suke, har ƙasa suka ɗuƙa suka gaisar da mutanan dake cikin gidan kafin su shiga ɗakin Ummu, itama har ƙasa suka gaisheta, Adda Zainab ce ta kalli Ummu tare da nuna mata Hameed tace "Wannan ne Hameed din", "Hameed wannan ita ce Ummun Nazlah", bai ɗago kanshi ba, sai dai zuciyarshi tayi wani mugun bugawa, Ummu kuwa dan murmushi tayi bata ce komai ba, yar dariya Adda Zainab tayi dan tasan kunyarshi Ummu take ji, sai dai ita ta tabbatar wata rana sai ta daina jin kunyarshi dan duk ranar da Ya fara son Nazlah sai ta bani da rashin kunyarshi , dan baya iya boye abun da yake so.



mikewa sukayi zasu fice , Ummu ce tace "Zainab...!", juyowa Adda Zainab tayi ta dawo baya tace "Na'am Ummu..!", "a raka su gidan su Iya", ta fada tana dan kallonta, murmushi tayi tare da cewa "Yanzu kuwa ai ni zan rakasu ma",,ta fada tana ficewa.




tana fitowa Khalil yace "Adda wai ina Amaryar ne?, naga ban ganta ba", ya fada yana dan murmushi, "kai kuwa Khalil mai kake ci na baka na zuba, yanzu zan raka ku gidan Kakarta tana chan ai" ta fada tana yin gaba, duk bin bayanta sukayi, anan suka bar motocinsu suka bi bayanta.




Da sallama Adda ta kutsa kai cikin gidan , Iya da take tsakar gida ta Amsa mata, tare da cewa "Zainabu ce? shigo mana...!", ta fada tana kara buɗe taburmar da take kai, jin ance Zainab yasa Haleesa dan leqowa ganin Adda Zainab ce yasa ta fito.


Gaisawa da Iya tayi kafin tace "Iya da Anguna muke tafe", yar harararta tayi kafin tace "shine kika barsu a waje, ke Haleesa jeki ki shigo dasu, bari na karo taburma", ta fada tana mikewa, Haleesa kuwa tayi waje, ison shigowa ta musu, kafin ta juyo .



kafin su shigo Iya ta shimfiɗa musu Taburma, Adda Zainab kuwa ta shige cikin ɗaki Gurin Nazlah, zama sukayi kan taburmar tare da gaishe da Iya Amsa musu tayi da fara'a,kafin tace "ina Angon nawa yake?", ta fada tana kallonsu.



Khalil ne ya nuna Hameed da hannu tare da cewa "gashi nan Mama", murmushi tayi tare da cewa " , kar ka yarda a baka nunar rana, a bar ni, dan wannan dan fari²n duk rana ce ta duketa, ni kuwa ka gani fess da ni , gani dakwau ," ta fada cikin yar tsokanar jika da kaka, Dan murmushi Hameed ya yi, tare da cewa "Haba Iya ai sabuwa ake so mai jini a jika", ya fada yana yar dariya.




Bangaren Adda Zainab kuwa, tana shiga ta nufi Nazlah da take fitar da numfashi sama², sosai zazzaɓin ya yi zafi, matsawa tayi gareta ta sanya hannunta akan wuyanta, da sauri ta cire saboda wani mugun zafi da ya daki fatar hannunta, "Nazlah!", ta dan furta da ruɗu, idanunta da suka mata nauyi ta bude tana kallon Adda Zainab bata iya Amsa kiran da ta mata ba.



ganin tana jin jiki sosai, yasa ta fito tare da cewa "Iya zazzaɓi ne sosai a jikinta, akwai magani a bata kafin a tafi da ita Asibiti",,ta fada cikin yar damuwa, shi kuwa gogan taɓe baki ya yi.



"Maganin ya ƙare dama shi kenan ta ƙarasa shanyeshi ɗazun, ban san mai yasa wannan zazzaɓin nata ya ke yawan taƙura mataba kwana biyu ga,zafi ga naci ",ta fada cikin tausayawa Nazlah.



Kallon Hameed Adda Zainab tayi tare da cewa "taso ka dauketa mu tafi hospital dan jikin ya yi zafi sosai har na fara jin tsoro", ta fada tana kallonshi, shi kuwa shiru ya yi kuma bai tashi daga in da yake zaune ba.



"Wai ni kam ba da,Hameed nake magana bane?," ta fada cikin yar tsawa, mikewa yay, yana jin Adda ta fara shiga haƙƙinshi da yawa.



bin bayanta ya yi suka shiga ɗakin, sai da suka shiga tsakiyar ɗakin kafin yace "ina take?", ya fada yana dan duddubawa , nuna mishi Nazlah da take kakkafewa tayi, ido ya fitar waje kafin yace "Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un, wannan Ƴar Abar Adda mai yasa zakimin haka ne?, yanzu wannan ni ba abin kunya bane na nunata a matsayin mata, lallai da sakyal dan kuwa anyi bonono rufin ɗaki da Ɓarawo, dan wlh wannan ko bata mutu ba, zata sha wuya, kaji abu kamar mage, ji yarda,ta wani lafe tana futar da numfashi kamar,zata mutu k.......




07033371851



```DAGA TASKAR ƳAR LELEN ROYAL STAR```



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment