Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta gyara ne, amma babu abun da ta wani gyara, shara ce tayi , sharar ma bata yi ba, dan chan da datti chan share, chan datti haka sharar tayi.



Da sauri tazo gareshi, ta rungumeshi tana shafa kirjinshi, wata uwar tsawa ya daka mata, tare da cewa "zaki matsa min anan ko sai na babbalaki", ya fada yana tureta a jikinshi , cikin tsoro ta matsa, dan tunda takw dashu bai taɓa mata fada ba, sai taga fuskarshi ta koma kamar ta kumurci, da sauri ta nufi hanyar ficewa "Stupid girl", ya fada yana jaan tsaki, dan yanzu yaji ta fita ranshi kwata² baya son ganinta.


yana gama shiryawa, ya fice abinshi, driver yazo da sauri zai bude mishi mota, saurin dakatar dashi ya yi, tare da shigewa ya bata wuta, direct gidan Addarshi ya nufa, tun daga nesa yake burkaka horn kafin ya ƙaraso tuni get man din ya bude mishi get,shigewa ya yi ciki, ko dai²ta parking baiyi ba ya fice zuwa cikin gidan.


Tura ƙofar shiga palon ya yi, yana saka ƙafarshi ciki yaji ance "Oyoyo Uncle! Oyoyo Uncle", wata Yarinya da ba zata wuce 3years ba ta faɗa yana rungumeshi, daga Yarinyar sama , dan murmushi ya saki tare da sakar mata kiss a forever dinta, yana cewa "Baby ina Mom naki?", ya fada yana dafa kanta.


gyaran murya yaji anyi, da sauri ya kalli inda yaji anyi gyara muryar, ware idanunshi ya yi, yana binsu da kallo, nima bin inda yake kallon nayi da kallo, wasu Hamshaƙan mata huɗu na gani, zaune farare tar² kamar jini zaiyi tsartuwa a jikinsu, suna masifar kama dashi, ƙara ware idanunshi ya yi, tare da cewa "surprise", ya fada da murna fal ranshi, da sauri ya nufesu , rungumesu duka ya yi, yana jin yarda wani sanyi yaƙe ratsa zuciyarshi, duk kuma wani baƙin cikinshi na tafiya, kallonsu ya yi, suma shi suke kallo suna mishi dariya, dan duk ya ruɗe da ganinsu, ko dan sun dan jima basu haɗu duka ba, sannan babu wanda ya faɗamishi zai zo a cikinsu.


washe bakinshi ya ƙarayi tare da cewa "wai ni shin meeting aka haɗa ne ko ya?", ya fada yana daura baby akan cinyarshi, dariya duk sukayi kafin Adda Nabila tace "meeting din mai fa Auta", cuno baki ya yi tare da cewa "Yo duka na ganku lafiya dai ko, kuma babu wani dan kira", ya fada yana kallon Haleesa ya kalla da take ta game da waya , ko kallonshi ma batayi ba.


"kawai mun dawo ganin gida ne", Adda Nafisa ta fada tana ajiye mishi robar ruwa da cup a gabanshi, tare da tray din yankkakun kayan marmari, "aikam dai kum shammace ni, dan banyi tunanin zuwanku ba yanzu", ya fada yana kai cup din ruwan da Adda Zainab ta zuba mishi, Adda Zainab ce tace "dama ko baka zo ba muna da shirin muje gidanka gobe, sai kuna gaka kazo,"jinjina kanshi ya yi, kafin yace "Ke..! Auta lafiyarki kuwa", ya fada yana daka mata tsawa, da sauri ta zube ƙasa ta ce "Sannu da zuwa Auta ban lura bane game ta dauke min hankali, ina Anty Sadiyya?", ta fada cikin tsoro, dan tasan karamin aikinshi ne ya mangareta.


banza ya mata yaci gaba da fira da Yan uwanshi, sai wajen 10 kafin ya wuce gida, a palo ya tarar da Sadiyya da Jamseey, da sauri Sadiyya ta mike, tana mishi sannu da zuwa, gudun kar ya yarfata sai ya amsa, amma a zahirin gaskiya har lokacin fushi yake da ita, cikin yanga da ƙissa da ƙisisina irin ta yan bariki, Jamseey tace "Barka da Zuwa Yallaɓai", ko kallonta baiyi ba ya shige ciki, bin bayanshi Sadiyya tayi, Jamseey kuwa, wani makirin Murmushi ta saki tare da ce wa "Ooooh Allah ka kai damo ga harawa ko baici ba yay ɓarna, kai yama ci", ta fada tana lumshe ido tare da lashe lips dinta.



tare suka shiga cikin bedroom din, sai da suka shiga kafin yace "Wace waccan a palo?", ya fada cikin tuhuma, dan shi kallo daya yawa Jamseey ya gane goggiyar yar bariki ce, "Au Jamsy ai Ƙawata ce", ta fada cikin share zance, ganin tayi fatali da zancen yasa ya share shima, bathroom ta jufa, ruwan wanka ta haɗa mishi mai dan ragwamen zafi kafin ta fito, kallonshi tayi tare da cewa "ga ruwan wanka", tana fada ta fice , girgiza kanshi ya yi, kafin ya shige cikin bathroom.




```Washe gari```


Kamar yarda su Adda Zainab suka fada, hakan ce ta faru guraren 1pm sai gasu, su da Yaransu kusan su goma, har da Haleesa, da Sallama suka shiga cikin palon, shiru babu wanda ya amsa, ƙara sallamar sukayi still ba bu wanda ya amsa , ƙarasa shiga sukayi ciki , guri suka samu suka zazzauna,suna bin palon da kallo , farin tayis amma ya koma ruwan ƙasa saboda rashin tsafta, kallon Adda Nafisa tayi tare da cewa "Tooo! Ikon Allah wai ni kaɗai naga abun da na gani ko kuma kun gani?", ta fada tana tsaresu da idanu.



Kallonta Adda Nabila tayi tare da cewa "nima na gani,amma dai ina jin ba lafiya ba, tunda kika ga gidan nan haka, killan ko bata jin dadi ne, Auta shiga ki gano ko tana nan ma", ta fada tana Kallon Haleesa, mikewa tayi da Ƴar Adda Zainab Ihsan ta nufi hanyar ɗakin Sadiyya, tun daga Ƙofar shiga ta jiyo shewar Sadiyya da Jamseey, da mamaki ta ƙarasa cikin bedroom din, zaune ta gansu suna fira kowa da waya a hannunshi,duk binta da kallo sukayi, dan kimtsa fuskarta tayi tare da cewa "Anty Sadiyya baki ji zuwan mu bane?", ta fada tana kallonta.



dan taɓe baki tayi, Jamseey ce tace "Wace ce wannan?", buɗar bakin Sadiyya sai tace "Dangin Miji mana dangin tsiya", da sauri Haleesa ta kalleta,,tana maimaita dangin tsiya, dan murmushi tayi tare da cewa "Ayya lallai kam dangin tsiya mana, tunda anzo cikin Arziki anyi male² an manta da tsiyar da ta liƙewa tsoho a jiki, in kin gama shashancin sai ki fito palo ana son ganinki", ta fada tana jaan tsaki tare da ficewa.


zare ido Sadiyya tayi tana nin bayan Haleesa da kallo, dan ita sam batayi tunanin Haleesa zata iya mayar mata da magana irin haka ba, "tab lallai sai kin dauki mataki akan wannan Yarinyar"Jamseey ta fada cikin zuga, kwafa Sadiyya tayi tare da cewa "barta dan buhun Ubanta,,zata gane kurenta ne", ta fada rana mikewa, kallonta Jamseey tayi tare da cewa "ina zaki?", ta fada tana rikr hannunta, dan janye hannun tayi tare da cewa,"zanje naga waye yazo", "kar kije dallah ki barsu, in sun gaji sun tafi", ta fada tana mata kallon ƙasan ido.



zama tayi, tana cewa "to ai shi kena", ta fada tana daukar wayarta, Jamseey kuwa dariya tayi a ƙasan ranta tare da cewa "shashasha haka zanta miki rijiya kina fadawa, tunda ke baki da wayau", ta fada tana yar dariya a fili.



rai ɓace Haleesa ta fito daga ɗakin ,zama tayi gefen Adda Zainab , kallonta tayo tare da ce wa "lafiya? ina Sadiyyar?", ta fada tana kallonta, taɓe baki tayi tare da cewa "tana zuwa", zama suka ci gaba dayi, suna Yar fira tsakaninsu, kusan 1hour suna gurin, kallonsu Adda Zainab tayi tare da cewa "ni dai bari na shiga na dubo Ƴar nan, shiru har yanzu bata fito ba", ta fada tana yin hanyar sashen Sadiyya.



Dan murmushi ne ya suɓecewa Haleesa, dan tasan Adda Zainab bata daukar raini, dan ko Hameed din baya kawo mata wargi , tana tafe tana mamakin kiɗan da take ji yana tashi, daga cikin bedroom din Sadiyya, alamar tana nan kuma lafiya,dan da bata da lafiya da ba zata ji kiɗa ba, kuma tana da tabbacin Haleesa ta sanar da ita zuwansu.



tura ƙofar bedroom din tayi, da masifa Sadiyya ta juyo, dan ta dauka Haleesa ce ta sauƙe mata kwandon bala'inta, ido biyu tayi da Adda Zainab, tuni masifa da bala'inta, suka koma ciki dan wani kwarji da ta gani akan fuskar Adda Zainab din yasa ta haɗiye duk abun da yake bakinta.


dan murmushin da baikai ciki ba tayi tare da cewa "Sannu da zuwa Adda", kallo ta ƙare mata tare da cewa "Sadiyya..!", cikim kama kai ta ce "Na'am Adda!".


"ba kiji zuwan mu bane?", ta fada tana ƙara tsareta da ido, shiru ta danyi kafin tace "ban ji ba", jinjina kanta tayi tare da cewa "Haleesa bata shigo ta fada miki ba?", dan sosa kai tayi tare da cewa "ta shigo amma na dauka wasa take ba da gaske ba", ta fada tana dan tura baki.


"Sadiyya ya akayi kika koma haka?", ta fada tana haɗe ranta, shiru Sadiyya tayi bata ce komai ba, tsawa ta daka mata tare da cewa "kin zama Aura! kin zama ballagaza!! kin zama jakka, ki duba ki gani yanzu nan wai gurin kwanan bawa ne, shin wai da da kina gidanku haka kikeyi ne?, ko kuwa raini ne da iskanci yasa kike yin haka anan?, baki san komai na gidanki ba, ina da tabbacin ko girki dakyar in kin iya, tun da dai har kina zaune da ranki da lafiyarki, amma ba zaki iya kula da gidanki ba, ko sai an kawo wata kafin ki ringa hauka kina ƙururuwar , tare da cewa an cuceki, to wallahi ki zauna da hankalinki in ba haka ba uhmmmm", ta fada tana sakin wani kill smile irin na you will see.



rai ɓace itama ta fito, kallonsu tayi tare da cewa "Muje", ta fada tana nufar ƙofa, "lafiya Adda?", Adda Nafisa ta fada tana kallonta, bata ko kulata ba ta fice, mikewa dukkansu sukayi suka fice babu wanda ya ƙara bi ta kan Sadiyya, Motocinsu suka shiga tare da ficewa a gidan.




gidan Hajiya suka koma, a zaune suka tarar da ita tana jaan casbaha, zama sukayi gefenta tare da gaisheta, amsawa tayi, kafin su fara fira, Adda Zainab dai na zaune abun duniya ya Addabi ranta, jin tayi shiru yasa Hajiya kallonta tace "kina Lafiya kuwa Zainab?", firgigit ta juyo ta kalli Mahaifiyar tasu, rausayar da kanta tayi tare da cewa "Hajiya Aure nake tunanin in da zan nemar wa Autanki", ta fada tana gyara zama.


duk kallonta sukayi cike da mamaki, "Aure kuma?", Hajiya ta fada tana ƙare mata kallo, da son gasgata abun da take fada, jinjina kanta tayi Alamar tabbas, "Hajiya duba da yarda Hameed yake gudanar da rayuwarshi da da yanzu ba daya ba, tun daga haka yaci ace kun gane yana cikin matsala, bashi da wani kwanciyar hankali, kullum sai zuƙewa yake, shi yasa nakeson ya ƙara aure", ta fada tana kimtse fuskarta, dan ma kar wanda ya kawo mata wargi cikin ƙannen nata.




"to da kika je gidan kin fahimci wani abu ne?", dan murmushib taƙaici tayi tare da cewa, "ah'ah kawai", "to ke yanzu wa kike ganin za'a aura mishi a tunaninki?", Hajiya ta fada tana kallonta, shiru tayi tare da cewa "Yarinya Ƙarama wadda ba zata wuce 10 to 11 years ba, dan yanzu ba zai ƙara aurar Babbar mace ba, dan Aurensu da matsala", zare ido Haleesa tayi tare da cewa "Adda mai 10years ai ko sa'ata bata kai ba, wannan ai rainonta zaiyi", ta fada tana kallonta, wani kallo ta aika mata kafin tace "Eyyi na sani, kuma na yanke magana, dan haka bana bukatar wani ƙarin bayani", Shiru Hajiya tayi dan tasan Adda Zainab bata magana biyu, har in tayi magana to ta zauba kamar yankan wuƙa shi yasa babu mai mata musu in tayi magana tayi.



"To Allah ya tabbatar da Alkhairi", dan murmushi tayi tare da cewa "Ameen!, sai dai ina son ko anyi Auren ya zamo na Sirri pls, bana son a fadawa Auta", Adda Nabila ce tace "me ne ne Fa'idar mishi Aure bai sani ga, ni a ganina gaskiya hakan bai yi ba, ya kamata ace da saninshi", duk sauran suka ce "Eh gaskiya Adda a fada mishi", karo na farko da ta bar maganarta tabi tasu, jinjina kanta tayi, ta ce "to shi kenan, za'ayi hakan", murmushi Hajiya tayi tare da sa musu Albarrka.



suna zaune kira ya shigo wayarta, mika mata Haleesa tayi, karɓa tayi, tare da ƙarawa a kunnenta, "Masha Allah Malam Arabi , Allah ya sanya Alkhairi, insha Allah zamu halarta baki dayan mu", ta fada tana dan murmushi, sallama sukayi ta kashe wayar.



kallonsu tayi tare da cewa "gobe akwai sauka da za'ayi da Walima a makarantar da muka buɗe chan Ƙofar Marusa, dukkan ku ku shirya tare zamu tafi", ta fada tana ci gaba da tasbihin ta , Amsa mata sukayi tare da ficewa kowa ya shige ɗakinshi.



******************

```Washe gari```


Tun da sassafe Nazlah ta fita daga gidan Iya zuwa gidansu, da yake gaba da na Iya kaɗan, tafiya take cikin natsuwa tana karanta Arzikar din safe a hankali cikin ɗaɗɗar muryarta, a wannan lokacin in ka ganta zaka rantse da Allah babu ruwanta da duniya.



"Nazilatu Masifatu!", taji an faɗa a bayanta, a fusace ta saki Azikar din da takeyi ta juyo bayanta, harara ta dalla mata tare da cewa "ke! Hasina ki fita a harkata ko naci kutuumar Ubanki tam", ta fada tana juyawa.






07033371851




```Daga Taskar Yar lelen royal star````
[12/21, 12:10 PM] YAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♂️🧚‍♂️: ☘️☘️ *NAZLAH*☘️☘️





*DAGA AL[]ALAMIN*




SALMAJI/[]AR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️






*WANNAN LITTAFIN DAGA FARKONSHI HAR KARSHENSHI, SADAUKARWAR NE GA YAYATAH (MARYAM YUSUF) WANNAN LITTAFIN WAKE NA RUBUTASHI, KIYI YADDA KIKESO DASHI, ALLAH YA RAYA MIKI ZURI'ARKI, YA KUMA K'ARA RUFA ASIRI DUNIYA DA LAHEERAH...*



*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*






15-16.





""""""""""""""""""Jaawo Hijab dinta taji anyi, dunƙule hannunta tayi tana juyowa ta bugarwa Hasina baki, da sauri ta sakar mata hijab din, tana tarba gaba daya hannunwata a bakinta, ihu ta fasa lokacin da taga jini na fitowa daga cikin bakin, wani abu taji ya faɗo guda biyu, tana ciro hannun ta duba sai ta ga haƙoranta guda biyu a hannunta.


cikin mugu²n ta shin hankali ta laluba, zaro idanunta tayi jin haƙora gaba babu su, kuma ta tabbatar da cewa sune suka fita, ihu ta kwada tare da cewa "Wayyo na shiga ukku ta ciremin Haƙora da sanyi safiya", ta fada tana daura hannayenta bibiyu aka.


Wata muguwar dariya Nazlah ta kwashe da ita tare da cewa, "ai ba haka na so ba, so nayi gaba daya haƙoran su zube, Allah ne ya soki, amma gaba ki ƙara tara ta ki ga ikon Allah", ta fada tana ci gaba da tafiyarta.



baki washe take tafiya, tana cikin tafiyar taji ta ci tuntuɓe, dan tsayawa tayi ta duƙa, kusan 2 minutes sai kuma ta mike ta ci gaba da tafiya fuska a haɗe kamar an aiko mata da sakon mutuwa haka ta ringa tafiya har ta ƙaraso gida, ba ko Sallama ta sanya kai cikin gidan, Ummu ta tarar zaune tana kiciniyar haɗa wuta, bata ko kalleta ba ta shige chan ciki ta samu guri ta zauna, tare da haɗa kai da guiwa ta fara gunjin kuka mai ban tsoro da tayar da hankali.


a tsorace kuma cike da mamaki Ummu take kallonta, kamar daga sama Abba ya yakice labulan Dakin Umma ya fito da dorinarshi, yana cewa "wani sabon iskancin ne kika zo dashi yanzu da sassafen nan?, " ya fada yana ware bulalar, shiru tayi ta ci gaba da kukanta, da kana jinshi kasan ba nata bane, "Yau zaki ci ubanki, zan gyara miki zama, tunda baki san mutunci ba", ya fada yana daga bulalar zai zula mata.



idanunta da suka rine suka koma jaaazir kamar jini ta watsa mishi, tare da ce wa"doke ni to", ta fada tana kallon cikin idanunshi abun da tunda take bata taɓa yi ba kenan, tun daga nan ya sha jinin jikinshi, "nace ka duke ni", ta fada cikin tsawa, sauke bulalar ya yi, tare da cewa "Allah ya soki kinyi magana yau da kinci ƙaniyarki", ya fada yana jura takalminshi, bai ko tsaya ba ya fice da sauri.



Yah Haleem ne ya fito daga ɗaki, kallon inda take ya yi, kallo daya yay mata ya daka mata tsawa, ɗagowa tayi ta kalleshi, suna haɗa idanu tayo maza ta sauke idanunta ƙasa, "zo nan..!", ya fada tana ya fitota, ba musu ta mike izuwa gareshi, tana zuwa gareshi ta zube ƙasa , riƙe kanta ya yi, tare da cewa "mai ya kawoki yanzu da sassafe lau?", ya fada cikin sigar tambaya, cikin kuka tace "tabo mu akayi," ta fada tana kara dukar da kanta ƙasa, jinjina kanshi ya yi, tare da cewa "to kuyi haƙuri ku tafi", ya fada yana sakar mata kan.



babu musu ta girgiza kanta alamar to, kafin ta yi mika a hankali da wata sanyayiyar hamma, sai kuma ta fara bin gidan da kallo, inda ta tashi ta koma batawa kowa magana ba, tana kuma zama sai ga Mamar Hasina da Hasina sum shigo Haƙora a hannu, sai zazzaga ruwan masifa suke.



Haƙuri Ummu ta fars bawa Maman hasina ,amma kamar ana ƙarawa wuta fetur, sai kaucewa take zata kamo Nazlah, ita kuwa tana inda ta tashi fuska a turɓune in kasar da take gurin ta tanka itama ta tanka,gajiya Ummu tayi da bawa Maman Hasina Haƙuri tayi, ta ce "ga tanan yi mata duk abun da kike jim zaki mata tunda ba zakiyi haƙuri ba",,ta fada tana komawa gefe ta ci gaba da yunƙurin haɗa wutarta a murhu.



Mamar hasina kuwakan Nazlah tayi gadan², kafin ta ƙarasa gareta taci tuntunɓe , kafin tayi wani yunƙuri, an yi sama² da ita an bata fettt a ƙasa, tare da fara mulmulata a gurin kai da ganin aikin ƙasan ba ƙaramin ɓata rai ba akayi a gurin, haka Mamar Hasina ta ringa mulmula tana ihu dakyar aka samu ta tsaya, sai da Ummu tayi ta bawa Nazlar haƙuri , Hasina kuwa tuni ta ari na kare, dan tun ɗaga Ummanta tayi waje, bata tsaya ba sai da ta kai gida tana haki, Nazlah kuwa bata ko taɓa Maman Hasina ba Hasalima tana zaune daga inda take ko kallon Maman hasina batayi ba da ta shigo..



dakyar Maman hasina ta mike tare da taimakon Ummu ta fita tana kuka tare da jaan ƙafa, sai da Maman Hasina ta fita kafin ta mike ta shige banɗaki wanka ta sheƙo da ruwan sanyi ta fito , ɗaki ta shiga ta shirya cikin sabbin kayan Makarantar Islamiyya da suka mugun karɓi jikinta suka mata kyau sosai, naɗe gashin kanta tayi,ta mishi kamar acuci maza, fitowa tayi daga ɗakin tana dai-daita sanyin hijab dinta.



da tsananin Mamaki Ummu take kallon Nazlah dan ita a iya saninta basu chanja mata Uniform ba kuma bata ga ta shigo dasu ba, kallonta tayi tare da ce wa "Ke..! ina kika samu wannan kayan?", ta fada tana tsura mata idanu cikin wata murya da take nuni da cewa basu tafi ba tace "tambaya ko neman sani?", tunda Ummu taji haka sai ta jaa bakinta tayi shiru.



miƙa mata dan gutun koko da ko rabin cup baiyi ba ta ce "Ungo", kallon cikin kofin tayi, dan murmushi tayi tare da ƙarma, matsaw tayi ta jaa kujera, kafa cup din tayi a bakinta , kusan 3 minutes ta sauke cup din tare da sakin sanyyayiyar gyatsa, ajiye cup din tayi, kallon cikin cup din Umma tayi tare da kallonta, jinjina kanta tayi cikin tarin mamaki ganin yarda ta bata kokon haka ta ajiyeshi gashi kuma wai har da gyatsa tayi, mikewa tayi sai da ta kusa ƙofar tace "mun taf..!", tana fadar haka ta fice , tana fita Ummu ta sauke numfashi tare da cewa "Allah gamu gareka..!", kafin ta dauki sauran kokon ta shige ɗaki dashi.



A hankali take tafiya, cikin wata natsuwa da ta shigeta Yau din, haka har ta isa Islamiyyarsu da yan tsurarun mutane suka zo Yau din, dan kowa tsoro yake ji, da Bissimillah ta taka cikin Makarantar, batawa kowa magana ba har ta shiga cikin Ajinsu da babu kowa a jiki, layin gaba da shine layinta ita daya ta zauna.



Cikin natsuwa tayi Bissimillah tare da fara rero karatuj Al-qur'ani mai girma cikin bawa ko wane harafi haƙƙinsa, bata bari ta shiga haƙƙin ko wane, haka ta ringa rerowa wanda da,kaki zakasan Allah ya mata baiwa bayan baiwar tata kuma akwai taimakon wasu mutaman daban.



tana cikin Karatun Yan ajinsu suka fara shigowa, nayi mamaki na ganinsu, dan manya² ne yan Ajin nasu, dan wasu ko hasu haifeta ba, to sun girme mata nesa ba kusa ba, zama sukayi tare da fara labarinsu suna shewa da dariya, tsayar da karatun nata tayi tare da cewa "Amma nasan kunji da kunnanku karatu muke ko?", ta fada cikin sanyin murya, Hauwa'u ce tace "to sai me dan karatu kike, kinsan dai ba zaki hanamu labarin Saukarmu ba ko k...", idanunta ne suka fara ƙaƙƙafewa maganar da ta fara ta kasa karasawa, wata kumfa ta fara fitowa daga bakinta, da sauri duk yan ajin suka fice suna ihun neman taimako, ita,kuwa Oganninyar Zamanta ta gyara tare da ci gaba da karatunta, cikin suratul ```BAQARA``` dan har ta,kusa kaiwa karshen shafin karshe.



Malam Abbakar da ya,kasance shine Malamin Ajin mai koyar dasu Al-qur'ani ne ya shigo cikin ajin, yana kallon yarda Hauwa'u ta kaƙƙafe yasa aikin Nazlah ne da yake sun mishi bayanin abun da ya faru, kuna shi yasan Nazlah na da mutanan Boye tun ba yanzu ba, duba da yarda yake musu karatu ta dauke a jikin biyawar farko gashi in zata bashi hadda har sai ta ƙaranta inda bai musu ba, wannan kwazon nata yasa aka daukota daga ajin da take aka dawo da ita wannan ajin dan tafi Ɗaliban ajin karatu da mayar da hankali, har mamaki take bawa Malamai gurin karatu dan har gyara take cinsu.




" bana son haka, Saketa...!", ya fada yana zama

Please Login or Register in order to submit comment