Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Me yasa wai mutane suke haka ne? ni tunda nake ma ban ta'ba amfani da daddawa a miya ba me za'ayi da kayan wari kuma ma ko bukatar daddawar nake me zanyi data hannuniki."

Idanuwa na suka ciko da hawaye kafin ma nayi wani yunkuri su kwace suka shiga sauka a saman fuskarta. Murya Innah naji tana fadin." Hajia Kuturta ce dani da ba zaki bukaci abin hannuna ba a zato na wanda yayi ki shine yayi ni kuma babu wani wanda ya fifita akanmu sai wanda yafi bauta masa."

Hannu ta daga mata a fusace tace." Kinga Habiba dama kin saba mayar min da magana yanzu me ya kawo ku gidana."?


Innah ta girgiza kai cikin takaici tace." Hajia kin san hausawa suka ce yaba kyauta tukwici idan baki manta ba duk lokacin da yaron ki yayi mana abin alkairi Malam yakan turo ni nazo nayi muku godiya to wannan karon ma godiyar muke tafe da ita."


Tsaki taja da fadin." Da kun sani kunyi zamanku wallahi domin wannan zuwan naku ya janyo min bacin rai duk wani abu da Babangida yake muku yin kansa ne shi yayi
Niyya sabida haka ku dai na zuwa kuna damuna don Allah.

Innah tace."To ai shikkenan Hajia tunda bakya bukatar mu zamu daina zuwa inda kike dama kuma saboda karamci da mutunci yasa muke zuwa inda kike amma insha Allahu daga yau mun daina zuwa gidanki.

Tabe bakinta tayi ta dauke kanta daga kan mu. A sanyaye nace." Innah tashi mu tafi." Ta yunkura ta mike tsaye tana gyara yafan mayafinta tace."To Allah ya bamu alkairi." Inda muke bata kalla ba ballantana mu samu amsa. Jiki a mace muka fita daga gidan.



*MAR'ATUS-SALIHA*
_(Itace Cikakkiyar Mace)_

*Saboda yawan Tambayoyi gami da neman shawarwari daga 'Yan uwana mata ya sanya ni bude Group na mussaman domin wayar da kan 'Yan uwana mata akan abubuwan da suka damesu Mussaman A gidajen auransu👫 Matan aure da masu shirin aure su na amince suyi rigstar domin samun damar sauraran abubuwan da za'a gabatar a cikin Group din. Bayan haka akwai Magunguna na hausa masu kyau da Inganci!*
1- Maganin Sanyin mara
2-Maganin Sanyi mai sa budewar gaba
3-Maganin Sanyi mai sa warin gaba da fitar da ruwa
4-Maganin Sanyi mai sa bushewar gaba
5- Maganin Sanyi mai hana Sha'awa
6-Maganin Sanyi mai hana haihuwa
7- Maganin Sanyi mai sa zafi gurin saduwar aure (sex)
8-Maganin Basir mai tsiro
9-Maganin Basir mai kulle ciki
10-Maganin Karfin Maza(Gurin Sex)
*11- Maganin Karin Ni'ima
12- Maganin K'iba mai kyau
13- Maganin Cikar Nono (Breast)
14- Maganin Hips
15-Maganin kurajen fata da hadin sabulai masu kyau da inganci!
16- Maganin Matsi mai kyau
17-Maganin Sanyi mai sa budewar gaba
18-Maganin kara karfin sha'awa da dade wa gurin (Sex)
19-Maganin Basir mai sa yunkuri da budewar gaba


*_Duk Zaku samu wannan magungunan Cikin farashi mai sauki Kuma babu algus da almundahana a ciki sai da mukayi binkice muka tantance sannan Kada kiyi kokwanto ko shakka akan ingantattun magungunan mu Insha Allahu idan kin gwada sai kin neme mu Hausawa suka ce siyan nagari mai da kudi gida Ga masu bukatar suyi rigstar da Group na MAR'ATUS-SALIHA sai suyi min magana ta WhatsApp da wannan number._*
*07084653262*
*1k Rigstar da Group din MAR'ATUS-SALIHA*
Accont.....0542382124.....Binta Umar gtbank....Idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.
*07084653262*


Ko a hanya da muna tafiya kasa tsayar da hawayen idona nayi saboda tsabar bakin ciki me za'ayi da wasu masu kudin kwata-kwata Hajia Sabuwa ba ta san meye mutunci ba ai arziki na Allah ne sai yaso yake bawa wanda yaso ya kuma hana wanda yaso ba wai dan ba ya sonsa ba tunda iyayena suka haife ni ban ta'ba tsintar kaina cikin halin k'unci da damuwa irin na yau. Na tsani aci mutuncin iyayena ko kadan amma babu komai rayuwa ce.

Tana kokarin bude kofar gidan tace."Ai sai kiyi shiru haka ni ai wulakancin Hajia Sabuwa ba sabo bane a guri na."

Nasa hannu na goge fuskarta a sanyaye nace."Wallahi ji nake tamkar zuciya ta za ta fashe banta'ba tsammanin rashin mutuncin matar ya kai haka ba. ko da yake Inna kema kina da laifi tunda sai da nace miki ki ajiye daddawar nan amma kikayi fir kinga kin janyo mana cin mutunci.

Girgiza kanta tayi tace."Surayya ko da daddawa ko babu dama hajia Sabuwa 'yar cin mutunci ce saboda haka wannan al'amarin ya daina 'bata miki rai kiyi hakuri saboda d'anta Nuraddin.


Ajiyar zuciya na sauke nace."Shikkenan Inna Allah yayi mana maganin abinda ya dame mu." Ta amsa da "Ameeen ya Allah haka nake so ki kasance mai mayar da al'amuran ki ga Allah.


To koda wasa da Malam ya dawo ba mu fada masa abinda ya faru ba gudun bacin ransa duk dai shi ya kasance mutum ne mai saukin kai da mayar da komai ba komai ba amma dai tilas yaji irin cin zarafin da matar tayi mana ransa ba zai masa dadi ba.



Washe garin ranar da yake Juma'a ce sai nayi ado sosai nace." Innah don Allah zanje gidansu Samira.

Ta kalleni da fadin." Surayya nifa bana san yawo ina ce shekaran jiya kike je gidansu ita me yasa bata zuwa sai ke."?

A sanyaye nace."Innah kin san suna aikin awara shiyasa babarsu bata barin ta fita." Tace."Ayyo kece kenan mara aiki to babu inda zaki ki nemi guri ki zauna."

"Innah don Allah ki bari naje wallahi ba zan dade ba." Shuru tayi min ta cigaba da sabgarta na cigaba da yi mata magiya tace." Kije amma kada ki dade kinji abinda na fada miki ko."?

Da sauri nace."Eh insha Allahu zan dawo da wuri tace." To a gaishe da mutan gidan." Ina 'kokarin fita na amsa da zasuji."

Lokacin dana isa gidansu Samira suna shiryawa ita da Ummiyo za suje gidan bikin 'yar kanwar babarsu Nace." Samira idan ba zaku kai dare ba zanje." Tace." Eh to ya danganta da lokacin amma idan ana DJ zamu zauna muyi kallo. "

Nace." Ina ne gurin bikin."? Tace?" Rijiyar zaki ne." shuru nayi inaso naje amma kuma bana so na b'ata ran iyayena

Tace."Surayya ki daina tunani kawai idan zaki je baki da matsala damu idan magariba tayi kawai sai mu dawo."

Nace." To shikkenan muje." Ummiyo ta gama shiryawa tana sanye da wani material anyi mata wani irin dinki na banza fuskarta taci mai tayi gau! ta lafta hoda da bakin jan baki(daba-daba) kanta cunkus da attecement tayi daurin ture kaga tsiya kai kana ganin Ummiyo kasan idonta a bude yake.

Tana fesa turere ta kallemu da fadin." Idan kun shirya ku sameni a waje.'' Samira tace." Kaya na kawai zan sanya fa."Ummiyo na kokarin fita tace." Nace dai ku same ni a waje.'' Samira ta bita da harara bayan fitar ta tace.'' Mutsiyaciya kawai dama haka take duk sanda tayi kwaliyya sai ta fita ta zauna a waje tana nunawa maza."

Murmushi kawai nayi ina mamakin al'amarin Gidansu Samira sam babu tarbiya kowa abinda ya ga dama shi yake.

Atampa ta sanya riga da siket itama sun matse ta amma ba kamar na Ummiyo ba ta dauki karamin gyale tasa nace."Ke kuwa Samira ki sauya mayafi mana." Tabe baki tayi tace.'' Meye illar wannan din."?

Nace."Duba fa mazaunanki a waje ga siket din ya matse ki.'' Tace."Aikuwa wallahi ba zan sauya gyale ba domin shine mahadin kayan."

Girgixa kaina kurrum nayi na mike tare da gyara hijabin jikina ta kalle ni da fadin."Kema ai ya kamata kisa mayafi ki cire hijabin jikin ki tunda gidan biki zamuje"

Girgiza kai nayi nace."Samira kyale ni da hijabi na." Ba tare da damuwa ba ta dauki turare tana fesa wa ni kuma na fita daga dakin na tsaya ina kalle-kalle a tsakar gidan nace."Samira babarku bata nan ne.''? Tana kokarin fitowa tace."Eh itama taje gidan bikin amma na manya." Nace."Ayya shiyasa tunda na shigo gidan ban ji motsinta ba"

To koda muka fito sai kawai muka samu Ummiyo ita da wasu maza sai cafkewa suke sun sanyata a tsakiya sai hira suke tana kyalkyala dariya gashi mutane masu wuce wa domun tafiya massalacin Juma'a sai kallonsu sukeyi ni kaina al'amarin beyi min dadi ba Gabadaya Ummiyo bata da tarbiya da kamun kai.


Bakin titi muka fito domin samun abun hawa muna tsaye mu uku a jere muka ji horn a bayanmu da sauri muka juya...........Sai da fitsari ya kusa kufce min ganinshi yana sauke gilashin motarsa yana mana wani irin kallo mussaman Ummiyo da yake ji tamkar ya fito daga motar yaci mutuncinta.........A sanyaye na sunkuyar da kaina kasa gabana na wani irin fad'uwa mummunan kallon da yake mana shine ya kashe min jiki. mayar da gilashin motarsa yayi ya bar gurin. na sauke zazzafar ajiyar zuciya tare da tsirawa kasan gurin kallo.

Ummiyo taja tsaki da fadin."Wannan guy fa dan rainin hankali ne wallahi duba don Allah sai kace wanda yaga tumakai sai kallon banza yake mana."

Samira Murmushi kawai tayi tace."Ni kuwa guy birgeni yake wallahi kuma insha Allah ya kusa zama mijin kawata."

Ummiyo ta watsa mata wani irin kallo tace."A gidan uwarki ko an fad'a miki irin wad'annan mazan kowace irin mace suke aure."

Samira ta kyalkyale da dariya tace."Wallahi Ummiyo sai dai idan babu so amma idan so yana tasiri babu abinda za'a fasa.

Tace."Shashanci banza da wofi wannan ko wacece ta had'a kanta da wahala dan wannan guy da yake da masifar girman kan tsiya ba zai aureta ba."

Samira ta kalleni da fadin." Surayya kinji maganar da Ummiyo take ko.''? A sanyaye na daga kai gabadaya ni hankalina na kansa fuskarsa tana tayi min gizo da alama massalaci zai tafi dan yana sanye da farar shadda hade da farar hula da farin gilashinsa na qa'ida. yayi min kyau sosai sai dai yanayin fuskarsa shine kadai ke sanyayar min da gwiwa.


Wani mai babur ne yayi parking a gabanmu Ummiyo ta fada masa inda za muje ya fad'a mata abinda za'a bashi ba tare da 'bata lokaci ba ta bashi kudin muka shiga babur yaja muka dauki hanyar rijiyar zaki inda ake gabatar da shagalin bikin.




_*GA MASU BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP #400 VIP #600 ACCONT.......0542382124....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZA'A TURO AYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBERS ZAN FA'DI YANDA ZA'AYI*_
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*

*_MUTANAN NIJAR IDAN KUNA BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP DALA DARI VIP GROUP JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO ORANGE KU NEMI WANNAN NUMBER......._*
*22790899076*
*HAJIA FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
[9/25, 3:47 PM] Jamila Yushau: *MATSALAR MU A YAU!*
_(Labarin Surayya)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION🤝🏻*
____________________________

*SADAUKARWA NE GA:*
_(Surayya dee🥰)_

FreePege
*17&18*
Ina jin su Samira suna hira a tsakaninsu amma na kasa sa musu baki hankalina gabad'aya yana kansa da tunanin irin rayuwar da zamu gudanar idan munyi aure
" Surayya ki daina tsawwala wa kanki shi fa aure nufin Allah ne kuma mafi a kasari abinda kake so baya zama alkairi a gare ka" Zuciyata ce ke tunasar dani. Sai kawai zuciya ta ta karye hawaye suka zubo min da sauri na goge ashe Ummiyo ta gani tace."Ke kuma lafiya kike kuka."?

Da sauri nace."Ba kuka nake ba wani abu ne ya shiga idona shine yake fitar da ruwa." Ummiyo ta yarda da magana ta amma banda Samira saboda tafi kowa sanin halin da nake ciki.

To a gurin bikin ma bani da walwala ina kallo ana ta gudanar da shagulgula Ummiyo da Samira sai rawa sukeyi a tsakiyar Mai DJ sai manna musu kudi ake saboda Ummiyo ta iya rawa ta shaid'anci. Al'amarin ya dinga bani mamaki da kunya dan ganin yanda ta dage take karye-karye nononta sai tsalle yake sabida tsabar rawa.

Ta kusa dani na tambaya lokaci wayarta ta fito dashi ta duba ta kalle ni da fadin." Tara da rabi." Zumbur na mike tsaye gabana na faduwa.........Kutsawa nayi gurin me DJ din na kamo Samira nasa bakina a kunnenta murya na rawa na fada mata lokaci....Cikin shau'ki tana girgiza jiki tace."Ai Surayya sai dai ki tafi ke kadai dan wallahi ba zan tafi ba sai lokacin da me DJ d'in nan ya tashi kina kallo dai yanzu ne ma yake sanya wakoki masu dadi.

Murya na rawa nace."Samira haka zaki min ko."? Tace."Surayya dama ai sai da na fada miki ban munafurce ki ba kinga bani da laifi." Tana gama maganarta ta bar ni a gurun.

Cikin tsananin fargaba da damuwa na fito bakin titi gashi babu ko kwabo a hannuna hawaye suka wanke min fuska babu shakka duk wanda bai ji maganar na gaba dashi ba yana tare da matsala.

Wani mai babur ne ya tsaya a gabana yana tambaya ta nace." Goran dutse zaka kai ni." Yace."To kudin ki dari biyu." Babur din na shiga da fadin." Muje." yaja da sauri muka bar gurin.......Rintse idanuwana nayi na cigaba da addua akan Allah ya sassauta zuciyar Innah na san tana can cikin bacin rai uwa uba Malam da baya son nayi dare a waje.

"Hajia mun zo" Muryar direban ce ta dawo dani hankali na nace."To dan Allah ka shiga dani ciki ka ajiye ni a kofar gidanmu sai na baka kudin."

Yace."Ai ba haka muka yi dake ba ni ba zan shiga wannan lokon ba kawai ki fito ki bani kudina.....Muryata na rawa nace."Don Allah ka taimaka min ni wallahi yanzu babu ko kwabo a hannuna dama sai ka ajiye ni a gida sai na baka kudin.

Zagi ya kurma! yana wani irin fito! ya fito daga babur din ya tsaya a kaina yana fadin." Wallahi zanyi miki rashin mutunci a gurin nan mutukar baki bani kudi na ba ni zaki rainawa hankali."

Nace."Haba dan uwana ka kar'bi uzuri na wallahi babu kudi a hannuna." Cikin hayaniya yace." Me yasa tun farko baki fada min ba ni ba zan kar'bi Uzurin ki ba kawai ki bani hakki na."

Magana zanyi kawai ya fara kokarin janyo hijabi na a fusace! nace."Dallah Malami sakar min hijabi." Yace." Ba zan saki ba sai kin biya ni kudi na wall.........."Wai me yake faruwa ne." Wani mai siyar da fetur a gurin yake wannan maganar. ba tare da bata lokaci ba ya shiga fada masa yanda mukayi


Fitowa nayi daga babur din ina kalle-kalle a gurin wai har jama'a sun taru saboda tsabar sa'ido

Yace."Ke ya akayi kika shigar masa babur baki da kudi." ? Rashin abin cewa yasa na fashe da kuka babban takaici na jama'ar da sukayi dafifi a kaina suna kallona............................K'amshin turaransa ya tabbatar min da cewa yana gurin. gabana na faduwa na dago kaina muka had'a ido dashi suna magana da direban yana fada masa abinda ya faru.

Dari biyar ya bashi ya kalle ni da fuska tamkar ta zaki Yace." Wuce muje." Da saurin gaske nabi bayansa zanin jikina na kokarin yar dani.

Bayan motar na zauna ya tayar muka bar gurin.....Kaina a sunkuye naji sautin muryarsa." Yace." Ina kuka je ke da wad'ancan 'yan iskan yaran."?

Shuru nayi bakina yayi min masifar nauyi! "Surayya ba dake nake magana ba."?

Murya na rawa nace." Gidan biki." Yace."Wace."Unguwa ne."? "Can rijiyar zaki." Girgiza kansa yayi yace."Lokacin da zaki fita daga gidanku mahaifiyarki ta sani."? da sauri nace."Eh na fada mata." Ta mirror ya watsa mata wani irin kallo ya girgiza kansa da fadin." Kin raina iyayenki ko kina basu wahala saboda kawai kina ganin ke kadai suka haifa shiyasa kike yin duk abinda kike so sai kiyi musu karya ki tafi yawo kisa hankalinsu ya tashi sabida baki da mutumci to wallahi wannan shine na farko kuma shine na karshe kada na sake ganin ki da wa'innan yaran marasa tarbiya ni ba zanyi miki da sauki ba sai naci mutuncin ki."

Cikin kuka nace."Uncle dan Allah kayi hakuri kaji." Tsaki yaja yana gyara parking yace."Duba dan Allah haka kawai kin tashi hankalin bawan Allah saboda kawai kinga yana sonki."

Da sauri na kalli gurun Malam yana zaune kan kekensa kana ganinsa kasan hankalinsa a tashe yake......Nace."Uncle don Allah kace yayi hakuri sannan ka shiga gidan ka bawa Innah hakuri wallahi ba zan kara ba.

Yace." Ni na zama dan aiken ki kenan."? Da sauri nace."Aa ba haka nake nufi ba.'' Yace." To maza fice min a mota shashasha kawai." Da sauri na bude motar ina jin takaicin kira na da shashasha da yayi.



*MAR'ATUS-SALIHA*
_(Itace Cikakkiyar Mace)_

*Saboda yawan Tambayoyi gami da neman shawarwari daga 'Yan uwana mata ya sanya ni bude Group na mussaman domin wayar da kan 'Yan uwana mata akan abubuwan da suka damesu Mussaman A gidajen auransu👫 Matan aure da masu shirin aure su na amince suyi rigstar domin samun damar sauraran abubuwan da za'a gabatar a cikin Group din. Bayan haka akwai Magunguna na hausa masu kyau da Inganci!*
1- Maganin Sanyin mara
2-Maganin Sanyi mai sa budewar gaba
3-Maganin Sanyi mai sa warin gaba da fitar da ruwa
4-Maganin Sanyi mai sa bushewar gaba
5- Maganin Sanyi mai hana Sha'awa
6-Maganin Sanyi mai hana haihuwa
7- Maganin Sanyi mai sa zafi gurin saduwar aure (sex)
8-Maganin Basir mai tsiro
9-Maganin Basir mai kulle ciki
10-Maganin Karfin Maza(Gurin Sex)
*11- Maganin Karin Ni'ima
12- Maganin K'iba mai kyau
13- Maganin Cikar Nono (Breast)
14- Maganin Hips
15-Maganin kurajen fata da hadin sabulai masu kyau da inganci!
16- Maganin Matsi mai kyau
17-Maganin Sanyi mai sa budewar gaba
18-Maganin kara karfin sha'awa da dade wa gurin (Sex)
19-Maganin Basir mai sa yunkuri da budewar gaba


*_Duk Zaku samu wannan magungunan Cikin farashi mai sauki Kuma babu algus da almundahana a ciki sai da mukayi binkice muka tantance sannan Kada kiyi kokwanto ko shakka akan ingantattun magungunan mu Insha Allahu idan kin gwada sai kin neme mu Hausawa suka ce siyan nagari mai da kudi gida Ga masu bukatar suyi rigstar da Group na MAR'ATUS-SALIHA sai suyi min magana ta WhatsApp da wannan number._*
*07084653262*
*1k Rigstar da Group din MAR'ATUS-SALIHA*
Accont.....0542382124.....Binta Umar gtbank....Idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp



Har na isa inda yake idonsa na kaina. sai kawai na zube a gabansa na rike hannunsa hawaye na ambaliya a fuskarta nace."Malam don Allah kayi hakuri wallahi ban san dare yayi ba.

Shuru yayi kawai yana kallona, na rintse hannunsa da fadin." Malam kada kayi fushi dani tsautsayi ne." Girgiza kansa yayi yace."Surayya me yasa kike tayar min da hankali na." Nace."Malam kayi hakuri tsautsayi ne." Yace."Kin yaudari mahaifiyarki kan cewa zaki je gidansu 'kawarki ashe yawo kika tafi." Shuru nayi domin bani da abin fada.

Yace."Wannan yaron Nuraddin babu abinda zan ce dashi alkairinsa nada yawa a gare ni tun bayan La'asar dashi ake neman inda kike sai daga baya muka samu labari cewa kun je gidan biki keda wa'innan yaran masu soye-soye a waje me yasa kike so ki zubar min da mutumci na."

Shuru nayi hawaye na cigaba da gudana a saman fuskata Yace."To mutukar kina son farin ciki na ki dinga jin magana kuma ki daina k'arya a cikin al'amuranki sannan kuma Nuraddin din ya yanke hukunci a kanki ya raba ki da Samira tunda ita take koya miki rashin kamun kai."

Nace."To Malam naji insha Allahu zan kiyaye." Shuru yayi min ya fara kokarim tura kekensa na mike da sauri na taimaka masa muka shiga cikin gidan.


Innah ta cika tayi fam! nace."Innah kiyi hakuri kinji.'' ko kallo na ba tayi ba." Malam daki ya shiga ya kwanta Sunanta na kira tayi min banza, a sanyaye na mike na shiga daki domin cire kayan jiki na.

Babu zato naji duka da wayar redio a fatar baya na wani irin gantsarewa nayi ina ihu! ina kokarin rike wayar tana fizgewa da fadin.'' Ai tunda na rantse to sai na dake ki ni ba shashashar uwa bace da zaki dinga raina min hankali."

Zabga min wayar take ta ko'ina ina kwarma ihu tare da so na kwace wayar amma tayi mata rikon tsauri gaskiya ban ta'ba tsammamin haka Innah take da karfi ba........"Habiba ki kyale yarinyar nan kada kiyi mata rauni dukan ya isa haka." Shuru tayi masa ta cigaba da labta ta kawai sai na fad'i a gurin ina turjiya kamar me aljanu. hakan da nayi shi ya taimaka min sai ta yar da wayar ta fita daga dakin tana numfarfashi.

Laga-laga na kwanta a kasan dakin na dinga kuka yaushe rabon da Innah ta dake ni sai yau gaskiya banyi wa kaina a dalci ba domin nasan komai ya faru ni na janyowa kaina...

Sai dana sha panadol na kwanta bacci mara dadi ya dauke ni da safe da kyar ta amsa gaisuwa ta Malam kafin ya fita sai ya sake min fada da nasiha akan abinda ya faru.

Bayan kwana biyu sai ga Samira tazo tana washe min baki tana bani labarin irin shagalin da akayi bayan tafiya ta naja tsaki da fadin." Malama ya isa haka ni ba zan sake zuwa sabgar ku ba."

Tace."Saboda me."? Murya na rawa nace."Naci duka a gurin Innah sannan Uncle ya farfad'a min bakar magana.'' A sanyaye tace." Kiyi hakuri 'kawata wallahi ban san haka zata faru ba." Shuru nayi mata. Tace."Amma dai ranar litinin zaki je makaranta."?

Girgiza mata kai nayi nace."Uncle ya mayar dani makarantarsa dake KABUGA da sauri ta kalle ni da fadin." Yaushe hakan ta faru babu labari."?


Duk yanda al'amarin ya kasance na fada mata a sanyaye tace." Wallahi nima da zai dauke ni da naji dadi." Nace." Nima zanso hakan dan har na yanke shawarar fadawa Malam ya nema miki alfarma sai wannan matsalar ta faru wai yace kada ma na sake Mu'amula dake.

Tace."Saboda dame wani mugun abu nayi."? Shuru nayi tace." Na san dai Laifin Ummiyo ne ya shafe ni amma ni kowa ya sheda bana iskanci nida Ummiyo ciki daya muka fito amma kuma halin kowa daban."

Nace."Ki rabu dashi Samira bana jin zan daina Aminta dake domin kina bani shawarwari masu amfani dan haka ki kwantar da hankalinki."

Tace."Shikkenan Surayya ni zan tafi amma nima zan samu babanmu nace masa ya nema nin alfarma a gurun Uncle din domin ya kaini makarantar sa." Nace."To hakan yayi Samira Allah yasa a dace."

Koda muka fito daga dakin.... da sauri Innah ta dauke kanta. Samira tace." Innah na tafi." a dakile ta amsa jiki a sanyaye na rakata soro na dawo cikin gidan babu kuzari a jikina.



*Please a ayi shearing*


_*GA MASU BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP #400 VIP #600 ACCONT.......0542382124....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZA'A TURO AYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBERS ZAN FA'DI YANDA ZA'AYI*_
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*

*_MUTANAN NIJAR IDAN KUNA BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP DALA DARI VIP GROUP JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO ORANGE KU NEMI WANNAN NUMBER......._*
*22790899076*
*HAJIA FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
[9/25, 3:47 PM] Jamila Yushau: *MATSALAR MU A YAU!*
_(Labarin Surayya)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION🤝🏻*
____________________________

*SADAUKARWA NE GA:*
_(Surayya dee🥰)_

FreePege

*19&20*
Ranar litinin tsaf na shirya cikin kayan makaranta na fito domin tafiya Malam ya dauko dari biyu ya bani yace nayi kudin mota sauran kuma na sayi wani abun.

A marairace na kalleshi da fadin." Malam dari biyu tayi kadan ka kara min hamsin kai." Innah dake kokarin fitowa daga daki tace."Haba Surayya har nawa ne kudin mota daga nan zuwa kabuga Naira Hamsin zuwa haka dawowa sai ki sayi wani abu da sauran kudin........Nace."Wallahi Innah baki san yanda ake jin yunwa a makaranta ba Allah naira dari tayi min kadan.

Tace."To ai kowa da sandar hannunsa yake kai duka mahaifinki talaka ne daidai gwargwado yayi miki kokari ina laifi." A marairace nace."Dan Allah Innah ki kara min hamsin." Wata uwar harara ta watsa min..Malam yayi murmushi hade da gyara zaman sa hannu yasa a aljihu ya dauko naira hamsin ya miko min da sauri na kar'ba ina dariya. Innah ta girgiza kai da fadin." Wallahi Malam ka daina sangartar yarinyar nan da kudi yanzu ce naira dari bata isheta ba.

Yace."Habiba bana so yarinyar nan ta shiga damuwa acikin 'yan uwanta idan ina da iko to zan bata abinda yafi haka saboda haka ki daina maganar

Please Login or Register in order to submit comment