Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya dinga bin number da kallo yana jimanta al'amarin.

Samira ta fashe da dariya tana kallona tace."Gaskiya Surayya kina da matsala duba don Allah yanda idanuwanki sukayi jawur! shin wai soyayya ce ko jaraba."? Cikin wani irin yanayi nace." Samira nima ban sani ba kawai ina jin wani irin feelings ne a duk lokacin da zanji muryarsa.

Tace."Lallai to Allah dai ya cika miki burinki.'' Cikin farin ciki na amsa da ameeen 'kawata nagode sosai yanzu sai mu fara rubuta masa text din.

_Assalamu alaikum_
_Ya farin cikin zuciyata ina rokon Allah ya mallaka min kai a matsayin mijina uban 'ya'yana hakika na san na samu gwarzon namiji wanda ko wace mace take muradi.....Wallahi na kan gigice na d'imauce a duk lokacin da zanyi tozali da kai kana sanya ni cikin wani irin hali na bukatuwa ban ta'ba sha'awar d'a Namiji ba sai kai kullum sai nayi mafarkinka da tunaninka nake kwana dashi nake tashi Masoyi na ina tunanin kaunarka ce ajali na amma zan tsananta da addua akan Allah ya mallaka min kai domin na more rayuwar duniya Gwarzon maza D'aya tamkar da dubu jarumin jarumai Allah ya nuna min ranar da zan mallake ka mu kasance a cikin bargo daya a ranar babu wanda ya kaini farin ciki.......Na barka lafiya Habibi Allah ya tsare min kai a duk inda kake_
*DAGA S-R-Y*

Na jima ina karanta text din nace" Samira komai yayi daidai kawai a tura masa." Tace."To shikkenan." sai da text din yaje ta nuna min wayar da fadin." Gashinan ya tafi." Ajiyar zuciya na sauke da fadin." Tashi muje mu samu wani abu mu siya kafin a kada kararrawa." Ta mike tana kokarin mayar da wayarta cikin jaka.......Ikilima 'yar ajinsu ta karaso gurin tana kallonta tace."Ke Samira wallahi ki daina zuwa da wayarki idan ba haka ba za'a kwace miki

Nace."Ikilima kwacen waya aka a makarantar."? Tace."Eh mana ai ba'a zuwa da waya da kayan siyarwa saboda haka sai ku kiyaye.'' Tana gama maganarta ta bar gurin.


P-A d'insa ne ya shiga ofis din da ledar take away a hannunsa suka gaisa cikin mutunci ya ajiye masa abincin ya fita sai da ya kammala ayyukan dake gabansa tukkuna ya sauka daga kujerar kan wata katuwar kujera dake girke a ofis din ya zauna ya bude abincin yana ci yana duba wayarsa......Text din ne ya shigo sai ya fara dubawa......Number dai itace ta dazu wacce aka kira shi ana Nishi!! Ya dinga nanata karanta text din yana mamaki.........SRY Wannnan harufan sune suka fi daukar hankalinsa yayi - yayi ya had'a sunan ya kasa gabadaya kwakwalwarsa ta toshe babu shakka yarinyar nan ce data jima tana tura masa da wasikar soyayya ta hanyar Haruna maigadi yanzu ta samu number wayarsa Murmushin takaici yayi yana girgiza kansa lallai babu shakka duk ranar da ya gane ko wacece sai ta gane kuranta kamar shi da baya shiga sabgar ko wace 'Yar iska za'a kawo masa wannan shirman babban abinda yake 'bata masa rai shine duk cikin text d'in sai tayi maganar had'a shimfida da shiga bargo d'aya gaskiya yana mamakin tsagerancin yarinyar..


*****
Yau Juma'a ce da wuri aka tashi daga makaranta Cikin adaidaita sahu ta kalleni da fadin." Wallahi Surayya kada ki cutar da kanki kina ganin alkairi kina gudu jiya da muka had'u da Shahid yace yana so yazo gidanku amma yana jin tsoro kada ki wulakantashi.

Ta'be baki nayi nace."Samira idan kina min maganar Shahid wallahi haushi kike bani ni me zanyi da Shahid." Tace."Ai ba cewa nayi ki aureshi ba kawai muci kudinsa." shuru kawai nayi mata tace."Idan kuma kina jin tsoron yazo gidanku to kawai kizo gidanmu sai ku hadu." Girgixa kai nayi nace."Kawai kice masa yazo gidanmu." Tace."To shikkenan yanzu bari na kira wayarsa na fada masa.

Ina ji suna waya Shahid sai murna yake sai ya bani tausayi saboda na san shima Allah ya jarrabeshi da irin abinda ya jarrabeni son maso wani.

Tana dariya tace." Kina jin yanda yake murna ko.'' Nace."Ni wallahi tausayi ma yake bani Samira babu kyau yaudara." Tace."Ai shi yasa kansa ba wani ne ya aikoshi ba duk abinda ya baki ki kar'ba shi yasa kansa." Kaina kawai na girgiza da fadin." To Allah yasa yazo da alkairi."


Bayan Isha'i gabadayanmu muna zaune a tsakar gida har Malam muna cin abinci yaro yayi sallama da fadin." Wai ana sallama da Surayya a waje." Da sauri Innah ta kalleni na sunkuyar da kaina kasa. Malam yace."Je kace wanene."? yaron ya juya ya fita minti biyu ya dawo da fadin." Wai inji Shahid na gidan Malam Ado." Malam yayi murmushi da fadin.'' Jeka kace gatanan zuwa." da sauri yaron ya juya fita.

Ya kalleni da murmushi a fuskarsa yace."Tuntuni na fahimci yaron nan yana sonki Surayya ba zanyi miki dole ba idan kina sonsa kina iya zuwa ki saurareshi domun na fahimci yaron yayi hankali ba kamar yanda na sanshi ba gashi ubansa mutumin Kirki ne za'a iya had'a mu'amula ta aure dashi.

Ba tare da nace komai ba na mike simi-simi na shiga daki nasa hijabi na fito Innah ta dinga bina da kallo har na fita daga gidan.....Ta kalli mijin nata da fadin." Malam ni kam gabadaya wannan al'amari beyi min dadi ba saboda na san halin mahaifiyar yaron nan Mariya bata hakuri gashi surukanta suna kuka da ita bayan haka kuma yaron nan bashi da sana'a."

Yace."Duk wannan abu ne mai sauki Habiba shi aure albarka gareshi rashin sana'ar yaron ba zata hana abinda Allah ya hukunta ba addua kawai zamu tsananta akan Allah ya za'ba abinda yafi alkairi." Tace."To Malam Allah ya za'ba mana abinda yafi alkairi ya amsa da ameeen ya Allah.


Tunda muka gaisa na sunkuyar da kaina sai dai gabadaya hankalina yana kan katuwar ledar da yazo da ita sai magana yake banda E da Aa babu abinda nake iya fad'a.

Yace."Surayya tun kina yarinya Allah ya jarabce ni da Kaunarki dan Allah kada ki watsa min kasa a ido ki aminci na turo iyayena a tsayar da magana.

Kallonsa nayi tare da kokarin saisaita fuskata nace."Shahid ka kwantar da hankalinka nima ina sonka idan Allah ya kaddara aure a Tsakaninmu za muyi amma ba yanzu nake so ka turo iyayenka ba tunda kaga ban gama makaranta ba da sauran lokaci."

Yace."Surayya bana so wani yayi min shigar sauri ne shiyasa nake so iyaye su shiga maganar."......Girgiza kai nayi nace."Kada ka damu Shahid mahaifina ba zaiyi min aure dole ba sai da wanda nake so dan haka ka daina damuwa."

Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Shikkenan Surayya nagode sosai ni zan tafi." Ina murmushi nace."To Shahid nima nagode." Ya miko min katuwar ledar dake shaqe da kaya Yace."Ga wannan babu yawa." Ina murmushi nasa hannu na kar'ba da fadin." Shahid kenan harda wata hidima to nagode." Yace."Babu komai Surayya babu abinda ba zan miki ba." Dariya nayi ina kallonsa yace."Na tafi insha Allah zan siya miki waya koda kypad ce sai mu dinga gaisawa." Nace."Eh hakan yana da kyau Allah ya yassare." Ya amsa da ameeen yana kokarin tafiya. na daga masa Hannu da fadin." Sai anjima a gaishe da mutan gida." Ya amsa da zasuji insha Allahu." Cike da murna da farin ciki na shiga cikin gida hannuna rike da ledar sauri nake na bude naga abinda yake ciki..


*A taimaka da Sharing👏🏾*




_*GA MASU BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP #400 VIP #600 ACCONT.......0542382124....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZA'A TURO AYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBERS ZAN FA'DI YANDA ZA'AYI*_
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*

*_MUTANAN NIJAR IDAN KUNA BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP DALA DARI VIP GROUP JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO ORANGE KU NEMI WANNAN NUMBER......._*
*22790899076*
*HAJIA FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
[9/25, 3:47 PM] Jamila Yushau: *MATSALAR MU A YAU!*
_(Labarin Surayya)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION🤝🏻*
____________________________

*SADAUKARWA NE GA:*
_(Surayya dee🥰)_

FreePege
*23&24*
Kusa da ita na zauna da ledar a hannuna, cikin rashin walwala tace."Menene acikin ledar ne."? Babu karfin gwiwa nace."Nima ban sani ba yanzu dai zan bude naga ni." Girgiza kai tayi tace."Surayya bana son shiga sabgar Mariya shiyasa kwata-kwata wannan alaqar dake tsakaninki da yaron ta bana so." Shuru nayi mata ina firfito da kayan dake cikin ledar.....Tace."Ko a gidan uban wa ya sami kudi da har yayi miki wannan siyayyar nasan dai uwarsa bata sani ba domin da ta sani ba zata barshi ba."

Nace."Innah don Allah kiyi shuru da maganar nan haka nifa bani nace yayi min hidima ba shine yayi ra'ayi.

Tace."To duk kulafucin ki babu abinda zakiyi amfani dashi a cikin kayan nan tunda nasan dai ba sonsa kike ba babu amfani kici abinsa.

Murya na rawa nace."Haba Innah har guda nawa kayan suke duk rabi fa kayan kwalliya ne sai mayafai da takalmi amma kuma kice ba zanyi amfani dashi ba.

Tace."Ni dai na fada miki ki mayar da kayan cikin leda ki daure." Kuka nasa ina kallonta bakina sai rawa yake saboda tsabar takaici.

Malam ya mike zaune da alamun bacci a maganarsa yace."Menene kuma naji ana kuka."? Da sauri tace."Ai gwara daka tashi idonka ya gane maka ka duba kaga uban kayan da yaron nan ya kawo mata bayan babu wata tsayayyar magana a tsakaninsu."


Malam ya haska kayan da torchlight d'inshi yana dubawa. Kai ya girgiza yace."Surayya nima ban goyi da bayan kiyi amfani da kayan nan ba ki bari insha Allahu zan samu mahaifinsa mu tattauna maganar

Da sauri nace."Aa ni dai kada kuyi wata magana yanzu sai na gama makaranta tunda nace shi nake so to akan me za'a ce ba zanyi amfani da kayansa ba."

Da sauri ta zaburo kamar zata kai min duka tace."Don Ubanki rashin kunya zaki mana."? Girgiza kaina nayi ina bata hakuri. Malam yace."To shikkenan tunda kince haka Habiba ki zama sheda kada daga baya tazo ta sauya magana.

Cike da takaici tace."Malam wannan al'amarin babu sanya hannuna a ciki dan gabadaya maganar bata gamsar dani ba tunda kun amince ai shikkenan.

Kallona yayi yace."Ki shiga da kayan daki kiyi amfani dasu tunda dai kin za'bi Shahid a matsayin abokin rayuwarki to kada ki kuskura daga baya ki sauya magana.

Ba tare da tunanin wani abu ba nace."Eh insha Allahu babu abinda zai faru." Ajiyar zuciya ya sauke ya koma ya kwanta ni kuma cike da farin ciki na dauki ledar kayan na shiga daki ina murna na samu mayukan da zasu sanya ni fari dama na tsani naga fuskata tana maiko duk da baki na ba mai muni bane amma ina sha'awar fuskar Ummiyo saboda man da take shafawa yayi mata kyau.


Da sassafe sai ga Samira...Innah da kyar ta amsa gaisuwarta ta shiga daki ta same ni jikinta duk a sanyaye tace."Surayya na lura Innah bata so nake zuwa gurinki."

Da sauri nace."Wai Samira me yasa har yanzu kika kasa sabawa da halin Innah ne itafa wata iri ce mai wuyar sha'ani nima hakuri nake da ita sam bata da fara'a."

Tace."Ai ni idan naga tana shan kunu tana min wani irin kallo duk sai na zargi kaina." Nace."Nima da ta haife ni haka take min.

Dariya tayi tace."Ya kukayi da Shahid kuwa."? Hannu na bata muka tafa nace."Samira wallahi da babu Uncle a zuciyata da zan iya auran Shahid saboda ni a rayuwata ina masifar so naga namiji na masifar sona baki ga uwar hidimar da yayi min ba.

Tace."Ai na fada miki dama Shahid ne masoyinki na hakika amma kin tsaya kina 'bata wa kanki lokaci.''

Rai na 'bata ina watsa mata wani irin kallo tayi murmushi da fadin.'' Allah ya baki hakuri yanzu dai dauko min kayan na gani."

Girgixa kai na kawai nayi na janyo mata ledar kayan ta zazzage a gurin tana dubawa sai murna da tsalle take da fadin ta samu mai."

Nace."Ki dauki k'aramin sai ki bar min babban turaran ma ki dauki kwali daya sabulu ma ki dauki kwali daya." Tace."To mayafin fa." ? Nace."Ki dauki daya dan dama ni mayafi bai dame ni ba nafi son hijab.

Ta dauki takalmi guda tana dubawa nace."Kin san dai duk cikin takalman nan babu wanda zaiyi miki saboda haka sai ki hakura." Tace."Ai shiyasa na dauka ina dubawa ke kam k'aramar kafa ce dake.'' Nace."Nima nayi mamaki da har ya gane sizi d'ina Yace ma zai siya min waya." Sai kawai ta rangwada guda ta wani rungume ni tana kyalkyala dariya." Innah ta leko dakin tana fadin." Kuna da hankali kuke wannan shashanci ko kuwa a gidan biki kuke."?

Shuru mukayi taja tsaki tare da sakin labulan dakin ta bar gurin....Nace."Samira yau akwai Isilamiyya fa." Tace."Ni wallahi ko uniform din ban wanke ba na manta.'' Nace."Ai dama kin saba asha ruwan tsintsaye yau kije gobe ki zauna yana da kyau kije ki wanke kayan kafin zuwan lokacin.

Ta mike da sauri da fadin."Bani leda nasa kayan nan a ciki yau nima na zama me 'yanci Ummiyo zata daina hura min hanci." Dariya nasa da fadin."Hajia Ummiyo kenan." bakar leda na dauko mata tasa kayan a ciki.

Har waje na rakata ina sake jadadda mata cewa ta wanke inform d'inta kada lokaci yayi.


Yau Innah wake 'kulu da man gyada tayi mana abinda na tsana kenan a rayuwata da kyar naci ina ya tsine fuska ........Tana kallona uffan ba tace min ba sai da na mike domun wanko hannuna tace."Wallahi Surayya kiyi sabo da cin komai kada anan gaba kisha wahala domin baki san inda zaki je ba.


Ina kokarin sanya hijabi a wuya na nace."Innah ashe bakya min fatan auran mai kudi." Ta'be baki tayi tace."Yo ai juma'ar da za tayi kyau tun daga laraba ake gane ta Shahid ne fa d'an gidan Mariya matar da take takurawa surukanta."

Nace."Ni wallahi Innah babu wata suruka da ta isa ta takura min ai ba ita nake aure ba." Kallona tayi tana girgiza kai tace."To maganin ayi kada a fara ki hakura da yaron nan Shahid dan mahaifiyarsa masifaffiya ce."

Nace."Innah addua zaki cigaba dayi min." Tace."To Allah ya zaba miki abinda yafi alkairi." Na amsa da ameeen Innah ni zan tafi makaranta." fatan alkairi tayi min tare da adduar dawowa gida lafiya.


Abin mamaki koda na biyawa Samira makaranta tana zaune durshan suna hira da 'yan gidansu. Na kalleta rai a bace."Nace."Samira meye haka na dauka kafin nazo kin shirya amma dube ki a zaune ko wanka baki ba."

Tace."Surayya kalli igiya ki gani wallahi yanzu na wanke kayan dan ina dawowa daga gidanku bacci ya dauke ni sai yanzu na tashi." Igiyar nabi da kallo Uniform d'inta jagab da ruwa. Tsabar takaici yasa na juya ba tare da na sake wata magana ba na fita daga gidan.......A gaskiya su Samira ba suyi sa'ar uwa ba Zuwaira shashasha ce duk abinda 'ya'yanta sukayi daidai ne shiyasa gashinan Ummiyo ta lalace.



Biyar da rabi na yamma muke tashi a makaranta tun a hanya nake addua akan Allah yasa ya fito tunda dama duk weakened yake zaman karatu a bakin gate na gidansu.......Ajiyar zuciya mai sanyi na sauke ganinshi zaune a kujera da tarin littafai a gabanshi. Kafin na ankara naji abokanan tafiya ta suna maganarsa ko wacce sai gyara tafiya take. raina ya 'baci naji kamar na buge musu baki a ganina duk me zaiyi dasu da har suke wani sanja tafiya saboda shi.......Har muka wuce k'ungiyar mu guda bai dago kai ya kallemu ba hankalinsa na kan littafin hannunsa....Ni dai jikina a masifar sanyaye na isa gida na zube kan tabarma tare da cusa fuskata cikin hijabi kuka ya kwace min da alama 'yan matan dake son Uncle suna da yawa 'ya'yan masu kudi manya mata kyawawa masu kwarjini ni kuwa 'yar musaki takala nakasashe na san ko gasa ya yasa nice zan fad'i tunda bani da kyau bani da kudi babana talaka mai nakasa gani baka dole na kasance koma baya.

Maganarta naji a kaina." Surayya menene kin shigo babu sallama kawai kinsa kai cikin hijabi kina kuka."

Cikin dauriya nace. " Innah ba kuka nake ba kaina ne yake ciwo.'' Tace "Ai ni ba yarinya bace da zaki raina min hankali yana da kyau ki koyi hakuri da juriya komai akai miki sai ki dinga kuka wannan ba rayuwa bace."


Nace."Nifa Innah ba kuka nake ba." Girgiza kai kawai tayi ta bar gurin ni kuma na tashi jiki babu kwari na shiga daki domin cire uniform din jikina.


*Bayan sati uku*
Na dage da shafa man caro white wanda Shahid ya kawo min a maimakon ya sani fari sai wasu irin irin kuraje suka fito min fuskata ta sake baki hankalina ya tashi sai na ajiye man na daina shafawa ita kuwa Samira man ya kar'beta fuskarta tayi luwai tayi haske mai kyau kullum nayi ta sha'awar fuskarta yanzu dai na siyar mata da nawa man ta bani kudin mun shirya zuwa kasuwa domin siyan wani ko za'a dace.


Ranar litinin gurin Assembly aka firfito da masu bleacing aka ware su a gefe cikinsu harda Samira duk sun muzanta ko wacce sai zare ido take sosai na tausaya musu muna kallo a ka tasa keyarsu zuwa ofis din mai gayya mai aiki.


Uncle fad'a da nasiha yayi musu sosai ya nuna musu illar abinda suke ya kuma ce hakan ba zai hana ayi musu hukunci ba ya had'asu da dispelling master yace yaje dasu ya basu horo mai tsanani Uncle Bash dama abinda yake jira kenan ba tare da 'bata lokaci ba ya sauka dasu 'kasa can bakin band'akuna inda rana ta k'walle yace susa gwiwarsu a kasa su d'aga hannu sama kuma su kalli fuskar rana babu kiftawa so yake fuskokinsu su 'kone da da zafi rana inda nan gaba fuskar ba zata dauki mai ba.

Ya nemi kujera ya zauna yana kallonsu..........Kuka wiwi suke suna bashi hakuri azaba ta ishesu fuskarsu sai k'aikaiyi take tana maiko babu damar sosawa dan Uncle Bash mugu ne daga sunyi motsi zai zabga musu bulula sai da ya tabbatar sun galabaita sannan ya basu umarnin mi'kewa aikuwa a lokacin wata daga cikinsu ta yanke jiki ta fad'i iskokai suka tashi Uncle Bash ko a jikinsu ya bar gurin....Malamai mata sune suka taimakawa yarinyar ta dawo daidai sai kuka takeyi......Koda Uncle ya samu labarin abinda yake faruwa yace."Maza a kira direbansu a waya yazo ya dauketa ya kaita gida.

Tun daga ranar da wannan al'amari ya faru kowa ya tsorata masu shafa man bleating suka daina masu shirin farawa suk daina nima dana siyo nawa na ajiye ina jin tsoron shafawa.



*****
"Babangida naga kamar sauri kake ka zauna akwai maganar da nake so mu tattauna da kai."Hajia Sabuwa mahaifiyarsa itake wannan maganar.

Agogon dake daure a hannunsa ya duba a nutse yace."Hajia duk Uzurin da nake dashi ai dole na saurari naki.''

Tayi murmushin jin dadi tace."Babangida shiyasa nake alfahari da kai domin kuwa kana min ladabi da biyayya akan komai." Murmushi ya gyara zamansa da fadin." Ina sauraranki."

Tace."Ina fatan ka fahimci Munufar yarinyar nan Fadila akan ka."? Ya kalleta yana neman karin baya ni.'' Ta gyara zama fuskarta babu walwala tace."Fadila dai sonka take kuma ta jima da fad'a min sanin halin ka yasa ban nema ka da maganar ba sai yau naga ya dace na fad'a maka hukuncin dana yanke akan ku Hausawa suna cewa gida bai koshi ba to kuwa ba za a kaiwa dawa ba saboda haka ga Fadila nan itace macan da na za'ba maka a matsayin matar da zaka aura."
Cikin wani irin yanayi ya dago kansa yana kallonta Yace...........


*A taimaka da Shearing*





_*GA MASU BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP #400 VIP #600 ACCONT.......0542382124....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZA'A TURO AYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBERS ZAN FA'DI YANDA ZA'AYI*_
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*

*_MUTANAN NIJAR IDAN KUNA BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP DALA DARI VIP GROUP JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO ORANGE KU NEMI WANNAN NUMBER......._*
*22790899076*
*HAJIA FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
[9/25, 3:47 PM] Jamila Yushau: *MATSALAR MU A YAU!*
_(Labarin Surayya)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION🤝🏻*
____________________________

*SADAUKARWA NE GA:*
_(Surayya dee🥰)_

FreePege
*25&26*
"Hajia Babu Fadila kwata-kwata a cikin tsarin rayuwata bana sha'awar auran zumunci dan Allah ki janye wannan kudirin naki." 'Bata fuska tayi tace."Babangida kaifa yanzu ba yaro bane ka kai matakin aure har ka wuce shekaru talatin da biyar ba kadan bane duk sa'onin ka sunyi aure amma kai kana zaune ko sha'awar auran ma ba kayi wai shin ko dai baka da lafiya ne."?

Girgiza kanshi yayi cike da damuwa yace."Hajia shi aure lokaci ne ki daina damuwa sannan ni lafiyata lau kawai lokaci ne beyi ba amma tunda kinyi magana yanzu zan fara duba matar aure amma inaso ki janye maganar Fadila dan kwata-kwata bana sha'awar auranta.

Tace."To shikkenan tunda kace haka yanzu zuwa wane lokaci zaka kawo min matar auran naka." Shuru yayi yana nazari tace."Kayi shuru kai nake saurare.'' Yace."Ki bani lokaci zan duba." Murmushin takaici tayi tace."Babangida wannan itace damarka ta karshe idan baka kawo min matar aure ba to babu shakka Fadila ce uwar 'ya'yanka."

Mikewa yayi babu walwala a tare dashi yayi mata sallama ya fita ta bishi da kallo tana girgiza kai tabbas idan ba tayi masa da gaske ba to haka zai ta zama babu aure duk ga abokanansa da 'ya'ya amma shi yana zaune.

Koda Maigidan ya dawo ta sheda masa hukuncin data yanke sai ya nuna farin cikinsa yace."Fadila yarinya ce mai tarbiya da nutsuwa kuma 'yar uwarsa ce akan ya fita ya dauko wata to gwara ya aureta.'' Cike da farin ciki tace."Nima abinda nayi tunani kenan sannan kuma zumuncinmu da 'yar uwata zai kara karfi." Alhaji Sabo yace."Kwarai kuwa Allah ya tabbatar da alkairi.'' Ta amsa da ameeen ya Allah.


*BAYAN WATA BIYU*
Shahid ya siya min waya kamar yanda ya fad'a kuma duk abinda ya samu yana rawar jiki zai kawo min hidima babu irin wacce ba yayi min Innah ta dinga bala'i tana fadin ita ta gaji da wannan shashancin bata neman fitina sai kawai na yanke shawarar a duk lokacin da Shahid ya kawo min wani abu bana shiga dashi gidan gidansu Samira nake 'boyewa wasu muyi amfani dashi wasu kuma mu siyar mu kar'bi kudin mu kashe.....Magulmata sukaje suka kai wa mahaifiyarsa gulma da irin facakar da yake min da kudi.

Iya Mari ta fusata ta kumbura yana shiga gidan ta rufeshi da fad'a ta inda take shiga ba tanan take fita ba yace." Iya Mari kiyi hakuri ki daina wannan fad'an maganar aure tsakanina da Surayya tayi nisa domin Baba ya sani kuma sun tsayar da magana da Babanta yanzu ana jira nan da shekara daya lokacin za tayi Candy sai a daura aure.

Ajiyar zuciya ta sauke tace."To yanzu naji magana ai na dauka babu wata tsayayyar magana a tsakaninku kake kashe mata kudi a banza.

Girgiza kansa yayi yace."Akwai magana mai karfi a tsakaninmu.'' Tace."To Allah ya sanya alkairi yanzu sai ka tsagaita dayi mata hidima ka fara kokarin gyara gurin da zaku zauna.

Yace."Inna Mari da inaso na fita na kama haya ne." A fusace! tace."Ashe baka da hankali Shahid yanzu duk girman gidan nan ka rasa gurin zama a cikinsa babu inda zakaje a cikin gidan nan zaka zauna kamar 'yan uwanka." Yace."To shikkenan Innah haka za'ayi." Abinci ta bashi ta zauna sai fada take masa shi dai abincinsa kawai yake ci yana gyada kansa inda sabo ya saba da masifarta.

****
Ganin yanda wasu da cikin 'yan ajinmu suka manta da abinda ya faru yasa nima na dauko White scret d'in dana siyo na

Please Login or Register in order to submit comment