Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sangarci."

Girgiza kai kawai tayi ta shige daki. Na kalleshi cike da kauna nace."Malam sai na dawo kayi min addua.'' Cikin kulawa yace."Surayya Allah ya tsare Allah ya baki ilimi mai amfani." Ina kokarin daure igiyar takalmina na amsa da ameeen ameeen Malam.



Daga can nesa na hangi Samira cikin Uniform irin na jikina sai abin ya bani mamaki tun kafin na karasa inda take take washe min baki. Na kalleta da fadin." Samira ya haka."? tana dariya tace."Ai dama na fada miki nima sai na san yanda nayi na samu shiga makarantar nan.

Muna tafiya take bani labarin yanda al'amarin ya faru Babarsu ce taje ta gurfana gaban Hajiya Sabuwa tayi mata kirari da bambadanci ta roki alfarma a gurin ta to dama ita Hajia Sabuwa macace mai Izzah! ganin yanda Zuwaira ta gurfana a gabanta kamar me neman gafara sai kawai tace ta kwantar da hankalinta zata san yanda tayi 'yarta ta samu shiga makarantar.......Uncle kuwa ba da san ransa ba ya amince da al'amarin domin sam baya bukatar marasa tarbiya a cikin makarantarsa dan dai kawai Umarni ne na iyaye babu yanda zaiyi.

Nace."Amma naji dadi wallahi dama ina jin rashin dadi a zuciyata Allah yasa a kai mu aji daya." Cike da farin ciki ta amsa da "Ameeen. Bakin titi muka fito muna neman abin hawa sai ga Mansur saurayin Samira yayi parking a gaban mu yana murmushi yace." 'Yan mata kun canza skull ne."?

Samira na firirita tace."Eh wallahi dama muna neman adaidaita sahu makarantar a can Kabuga take." Yace." Ayya gashi mashing din yayi muku kad'an da na dauke ku."

Da sauri tace."Haba babu wani kad'an ai sai mu hade jikinmu dama Surayya bata da qiba.'' Da sauri na kalleta na kalli mashing din.

Yace."Surayya kin ji shawarar kawarki kada ku makara kawai kuyi goyo na dauke ku dama hanyar zanyi sai kawai na sauke ku."

A sanyaye nace."Samira duba mana time idan da sauran lokaci sai mu tsaya jiran abin hawa. Ta fito da wayarta ta duba. da sauri tace." Takwas da rabi ta kusa.'' A sanyaye nace." Kuma karfe takwas ake rufe gate dan na karanta dokokin makarantar." Tace." To kin gani kawai mu hau Mansur ya rage mana hanya.

Nace."Shikkenan sai ki hau.'' Mansur da sauri ya gyara mata mashing din ta hau nima na dafa kafadarta na hau ya figa da gudun gaske.............

Tunda muka doshi bakin gate din makarantar gabana ke fad'uwa! a bude yake motoci na shiga wasu na fitowa da alama direbobi ne.....Da sauri nace."Mansur ba sai ka shiga damu ciki ba sauke mu." ai ko saurarata beyi ba ya fige mashing din cikin makarantar.

Daga can saman baranda ya hangi shigowarsu ya mike tsaye da saurin gaske. karfen barandar ya rike yana so ya tantance su waye.

Securities ne suka zo inda muke duk munyi tsuru-tsuru ganin yanda malamai da dalibai suke bin mu da wani irin kallo sai kus-kus ne yake tashi a gurin.

"Kai me yasa zaka karya mana doka ka wani fafaro mashing da alama dai farin shiga ne." Daya daga cikin securities ne yake wannan maganar.

Mansur murya na rawa yace."Ranka ya dade ayi min afuwa ban san dokar makarantar ba domin yau na fara kawo dalibai."

Yace."Okey to anyi maka uzuri amma kada ka kuskura ka qara yi mana goyon biyu doka ce mai karfi daga shugaban makarantar."

Mansur yana kokarin magana ya 'karaso gurin hannunsa goye a bayansa. gabad'aya kowa ya sunkuyar da kansa. Ya kalli Mansur rai a 'bace yace."Kai bakasan sharia ba ko."?

Mansur yayi shuru yace."Kai a matsayin ka na musulmi abinda kayi a yanzu shine daidai ka goya mata biyu a bayan mashing d'inka alhalin duk ba muharaman ka ba.

Mansur a sanyaye yace."Ranka ya dade nayi kuskure a gafarce ni." Tsaki yaja yace."Kada ka sake kwatantawa idan na kara ganin ka shigo min makaranta da goyon biyu sai nayi sharia da kai.'' Da sauri yace." Insha Allah ba zan sake ba.

A wulakance ya kallemu yace." Dube su shashashai kawai marasa sanin ciwon kansu." Gabadaya idanun dalibai da malamai ya dawo kan mu Muka muzanta kwalla ta cika kwarmin idona.

Yace."Duk sanda kuka sake aikata wannan abu sai nayi muku hukunci mai tsaurin gaske." Murya na rawa nace."Uncle kayi hakuri wallah........"Rufe min baki.''? Cikin tsawa ya katse ni.'' sai na sake muzanta tuni hawayen da nake makalewa suka k'wace sharara suka dinga zuba.

Ya kalli gate Man da fadin." Ka rufe kofar nan kada ka sake bari kowa ya shigo." da sauri ya amsa ya bar gurin.....Cikin zafin nama ya juya da fadin." Ku same ni a ofis.'' Simi-simi muka bi bayansa gwiwa a sanyaye.


Yana tafiya muna biye da bayansa yayin da malamai da dalibai ke ratse masa hanya suna gaisheshi......Daf da bakin ofis din ya juyo da sauri muka sunkuyar da kan mu ya kira sunan wata malama da sauri tazo inda yake Ya kalleta da fadin." Wad'annan yaran sabbi ne ki kai su Ss1 amma kada ki had'a su guri daya." Ta amsa da "To ranka ya dade." Ofis din ya shiga ba tare da ya kallemu ba.

Ta kallemu fuska babu walwala tace."Ku biyo bayana." Da sauri muka rufa mata baya giwar mu a sanyaye a gaskiya makarantar tana da tsanani hatta da malamai tsoronsa suke gudun kada suyi laifi.


Ni Class A Samira Class B hakan yayi mana dadi tunda muna kusa da juna......Koda aka fito break guri guda muka samu muna mayar da magana Nace."Samira al'amarin guy nan ya soma bani tsoro ki duba kiga irin rashin mutumcin da yayi mana a gaban jama'a."

Samira ta fashe da dariya da fadin." Ni wallahi Mansur ne ma ya bani dariya ya tsorota sai zare ido yake yana gudun kada a k'wace masa mashing d'insa.

Murmushi nayi nace."Ai Uncle din ne yake da mugun kwarjinin tsiya ni wallahi idan yana kusa dani gwiwata sanyi take."

Samira tace."Na lura Surayya soyayya ce ta kawo ki makarantar nan gashi kuma wallahi da za mu tsaya muyi wa kan mu gata da zamu samu karatu a makarantar sosai."

Murmushin takaici nayi nace."Samira soyayyar Uncle ba zata bari na fahimci komai ba." Tace." To yanzu ke a wane matsayi kike Surayya mutumin nan fa da wuya ya aure ki wahalar da kanki kawai kike."


Murya na rawa nace."Samira ba zan iya hakura da Uncle ba zan kara zage dantse idan rabona ne zan aureshi.

Dariyar takaici tayi tace."Surayya mun rubuta masa wasika sama da biyar babu amsa yanzu wace dubara za'ayi masa kuma." Shuru nayi ina tunani akan al'amarin.

Tace."Idan kuma zaki same shi gaba da gaba ki fada masa manufarki hakan yafi.'' Kallonta nayi ina Mamakin maganarta.

Tace."Wannan shawarar itace daidai.'' Girgiza kai nayi nace."Samira ba zan iya ba wani irin kwarjini yake min za dai mu cigaba da rubuta masa wasika akwai numbers d'inshi a jikin form na makaranta zamu dauka muyi amfani da wayarki gurin tura masa text na soyayya.

Tace."To shikkenan Allah yasa a dace." a sanyaye na amsa da ameee ya Allah. Muna nan a zaune muna saka wasikar jaki aka kad'a kararrawa hakanan muka shiga aji ba tare da mun sayi wani abu mun ci ba.........


*Please a taimaka da Sharing*






_*GA MASU BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP #400 VIP #600 ACCONT.......0542382124....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZA'A TURO AYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBERS ZAN FA'DI YANDA ZA'AYI*_
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*

*_MUTANAN NIJAR IDAN KUNA BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP DALA DARI VIP GROUP JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO ORANGE KU NEMI WANNAN NUMBER......._*
*22790899076*
*HAJIA FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
[9/25, 3:47 PM] Jamila Yushau: *MATSALAR MU A YAU!*
_(Labarin Surayya)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION🤝🏻*
____________________________

*SADAUKARWA NE GA:*
_(Surayya dee🥰)_

FreePege
*27&28*
Diriricewa nayi na fara inda-inda! ya buga min razananniyar tsawar da ta kusa sa fitsari ya kufce min murya na rawa nace."Uncle ka dube ni da kyau wallahi bana shafa man bleaching ni tun asali haka kalar fatata take.

Ya tsira min ido da bacin rai a fuskarsa yace." Don Ubanki! makoho zaki mayar dani kome."? Jin zagin daya kurma min yasa jikina ya mutu sai na sunkuyar da kaina hawaye na nema ya 'kwace min.....Ya cigaba da cewa." Kin raina Allah har kike rantsewa dashi ko."? Uffan ban ce ba sai kokarin mayar da hawaye nake. Yace."Zaki fada min wanda yake siya miki man bleaching ko kuwa."?

Murya na rawa nace." Babu kowa ni haka skin d'ina yake." Da azama! ya mike nayi saurin kallonsa gabana na faduwa naga ya dauko bulalar Uncle Bash. Da sauri na mike Tsaye ina zazzare ido jikin bango na makure Jikina hawaye kuwa kamar an kwance famfo murya na rawa nake bashi hakuri.

Rai a bace yace." Zaki fad'a min ko kuwa."? Hanci na shaqa cikin inda-inda nace."Saurayina ne sunansa Shahid." Ido ya tsira min. Nace."Wallahi da gaske nake shine yake siyo min kayan kwalliya." Babu sukuni yace."Ashe har kinyi girman da zakiyi samari."? shuru nai tare da sunkuyar da kaina ya girgiza kai cike da takaici yace."Babu mamaki tunda kina tare da wad'annan yaran marasa kunya zakiyi abinda yafi haka to wannan shine na farko shine kuma na k'arshe kada ki kuskura ki kara shafa man bleaching ki bar hallitar da Allah yayi miki komai ba'ki da muninki ba zaki rasa mai auranki ba rashin wayo da dubara shine yake cutarku kuyi ta shafe-shafe saboda wai ku samu mazajen aure to wannan ba dabara bace saboda haka ki kiyaye ni wallahi daga yau kada ki sake shafa man karin haske idan kuma kika sa'bawa umarnina sai nayi miki mummunan hukunci."

Cikin mutuwar jiki gami da dana sani nace."Uncle kayi hakuri don Allah insha Allah ba zan kara shafawa ba."

Hanya ya nuna min da hannu alamar na tafi....Da sauri na sanya takalmana nayi gaggawar fita daga ofis din.

Can bakin band'akuna na hangosu a gurfane hannu a sama fuskokinsu a idon rana da saurin gaske nayi nufin sanja Hanya wata 'yar ajinsu Samira ta gan ni ta nunawa Uncle sunana ya kira na dawo da baya yace."Zo don ubanki ki shiga cikin 'yan uwanki." Tamkar na kurma ihu! saboda bakin ciki naje nasa gwiwata a kasa tare da daga hannuwa sama kamar yanda sauran sukayi.


Ranar nan mun galabaita mutuka mutum kusan bakwai suka tada aljanu Uncle Bash ya rabu dasu sukayi suka gama suka tashi Sai da aka tashi sannan Uncle Bash ya kyalemu muka tafi gida tun daga ranar kowa ya kiyaye saboda Uncle ya tsananta da yawa ya hana bleaching ya hana zuwa da waya bayan haka ya kafa dokoki masu tsauri yanzu karatu muke sosai babu wasa dan idan ka sake aka samu wani kuskure ta gurinka to kashin ka ya Bushe gurin Uncle Bash.

****
Muna daf da zana jarrabawar Nyco Shahid yazo min da wata magana raina a bace nace."Kaga Shahid ni don Allah ka kyale ni naji da abinda ya dame ni jarrabawa ce a gabana kai kuma kazo kana min wata magana nifa ko nayi Candy ba aure zanyi ba karatu zan cigaba dashi.

A sanyaye yace."Haba Surayya ya zaki karya alkawari kuma. Kada fa ki manta shekara guda mukayi dake a kancewa kina gama secondary za'ayi maganar aure amma yanzu sai ki sanja magana.

D'auke kaina nayi ina kallon hanya ni sam ba wannan damuwar ce a gabana ba burina kawai Uncle yace ya sona da aure. Yace."Surayya kinyi shuru baki ce komai ba alamu ya nuna kin amince na turo da sadaki na.

Wani banzan kallo na watsa masa da fadin " Aa ni kada ka turo kowa na fada maka ba yanzu zanyi aure ba sai nayi degree. "

Murmushin takaici yayi yace."Surayya kenan kin san wahalhalun karatu kuwa? ko kina da wanda zai tsaya miki."?

Cikin Izzah! Nace."Eh Ina dashi ba kowa bane face Uncle Nura." Shahid ransa ya 'baci kishi ya rufe masa ido yace."Nasan zai tsaya miki kiyi karatu tunda shine Ubangidanki ai ina da labarin duk irin hidimar da yake muku to ina rokon Allah yasa karatu kawai zai tsaya miki kada yace zai aure ki."

Naji kamar ya soka min wuka a makoshi ido jawur nace."To idan yazo zai aure ni don Allah ka hana aikin banza kawai."

Ya fusata mutuka yace."Ni kike zagi Surayya ashe dama baki da kunya To wallahi sai na rama abinda kikayi min kuma sai kun biya ni hidimar da nayi muku.

Nace."Shahid duk abunda kayi mana babu wanda ya saka kai kayi niyya don haka babu wani abu da zamu biya." Girgiza kai yayi yana hura hanci ya dauko wayarsa daga aljihu yana danne-danne.................Malam ne ya karaso gurin akan kekensa ganinsu a tsaye cikin 'bacin rai yasa yace."Ina fata dai lafiya."? Hawayen fuskata nagoge na shige gida ba tare da nace komai ba. Ya kalli Shahid din da fadin." Me yake faruwa ne."? Shahid na hura hanci yace." Malam ina ganin girma da mutuncin ka amma yarinyar nan tana so ta janyo maka bacin rai." Malam yace."Kayi hakuri kayi min bayanin abinda yake faruwa.

Shahid ya sauke ajiyar zuciya yace............Tsaf ya kwashe duk abinda yake faruwa ya fada masa. Malam ransa ya b'aci yace."Kayi hakuri kaji ko Surayya bata isa ta mayar dani 'karamin mutum ba kamar yanda mukayi magana da ita shekara daya data wuce ta tabbatar min da cewa kai ta za'ba a matsayin abokin rayuwarta to alkawari yana nan babu gudu babu ja da baya kaje ka cigaba da shirye-shirye." Shahid cike da farin yace."Nagode sosai Malamai Allah ya kara girma.'' Malam ya amsa da ameeen ameen ya tura kekensa domin shiga cikin gida.....Shahid kuwa cike da karsashi da kuzari ya bar gurun.


Ban ta'ba ganin bacin ran Malam ba sai yau yana shigowa gidan ya rufe ni da fad'a ta inda yake shiga ba tanan yake fita. Ya cigaba da cewa"To baki isa ki mayar dani k'aramin mutum ba wannan yaro ke kika amince da auransa muka zauna da mahaifinsa mukayi magana sai yanzu kuma da aski yazo gaban goshi sannan zaki bijire to baki isa ba wannan aure sai an anyi shi."

Cikin kuka nace."Ni wallahi bashi nake so ba Malam kada kayi min auran dole." Innah ta bude baki tana kallona tace."Yanzu ke baki ji kunyar fadar wannan maganar ba."?

Hanci na shaqa cikin dashewar murya nace."Innah ai kema kin san gaskiya a cikin al'amarin nan ina Shahid yaga sana'ar da zai iya aurena bashi da aiki sai buge-buge yak........Gwa'be min baki tayi tace."Ashe kin san bashi da sana'a amma idan ya kawo miki abin duniya kike kar'ba kina washe baki a gidan uban wa yake samo kudin."

Malam yace."Duk abinda zakiyi sai dai kiyi ba zaki mayar dani k'aramin mutum ba."

Da sauri na mike na shige daki na fad'a saman gado ina kuka Wallahi ba zan ta'ba amincewa da wannan al'amarin ba ta yaya ma za'ayi nayi rayuwar aure da wani namiji ba Uncle ba na riga na sanyawa raina auransa insha Allahu sai Allah ya cika min burina.


Washe gari a makaranta na zayyanewa Samira duk abinda yake faruwa jikinta yayi sanyi tace."Surayya da zakiyi hakuri ki auri Shahid din watakila shine alkairi a tare dake tunda dai kinga duk wannan abun da kike akan Uncle be san ki nayi ba."

Cikin 'bacin rai nace."Samira kada ki 'bata min rai don Allah wannan wace irin banzar magana ce nifa na fad'a miki koda Allah bai bani nasarar auran Uncle ba to wallahi ba zan auri Shahid ba saboda haka kima daina wannan maganar."

Tace."To shikkenan Allah ya za'ba miki abinda yafi alkairi." Na amsa da ameeen da fadin." Ina fatan kinzo da wayar ki."

Tace."Nazo da ita amma ki bari a fita break sai mu samu gurin da babu kowa muyi abinda za muyi." Nace."Ni don Allah bani wayar na shiga karkashin tevur nayi abinda zanyi."

Tace."Surayya kin san yanzu Malamar English zata shigo kuma kin san halinta bata da mutunci."

Tsaki naja da fadin." Kinga Samira idan zaki bani waya ki bani wallahi kwana biyu da ban ji muryarsa ba duk wani iri nake ji."

Girgiza kai kurrum tayi ta dauko wayar a 'boye ta bani ni kuma na fakaici idon 'yan ajin da sauri na shiga karkashin tevur............Number shi nasa ina kokarin kira Malama Sa'adiyya ta shigo a maimakon na fito sai na cigaba da abin da nake.............Muryarsa ce ta doki kunnune yana sallama had'e da kiran sunana."

Shuru nayi ina lumshe ido wani irin a zababben feelings ne yake taso min........"Assalamu alaikum Surayya ko ba da ita nake magana ba."? A firgice! na d'ago kaina sai kawai na hangi wucewarsa ta window sai da wayar ta kusa fad'uwa daga hannuna saboda tsabar razana! Kafin ma nayi wani yunkuri ya shigo ajin.......Gabadaya kowa yayi tsit! babu mai kwakkwaran motsi. Har yanzu wayar na mak'ale a kunnansa yana magana idonsa tsaye a gurin zaman ta. Ganin babu ita a gurin sai ya gazgata zarginsa. cikin nutsuwa ya cire wayar daga kunnansa ya fara tafiya zuwa gurin......Samira tamkar ta saki fitsari a wando saboda fargaba da tsoro ni kuwa ta tsakankani nake hango zuwan shi sai kawai nayi saurin sa wayar a cikin breziyya ta nayi kwance a 'kasan gurin ina rike ciki had'e da birgima a gurin..........


*A taimaka da Shearing👏🏾*



*MAR'ATUS-SALIHA*
_(Itace Cikakkiyar Mace)_

*Saboda yawan Tambayoyi gami da neman shawarwari daga 'Yan uwana mata ya sanya ni bude Group na mussaman domin wayar da kan 'Yan uwana mata akan abubuwan da suka damesu Mussaman A gidajen auransu👫 Matan aure da masu shirin aure su na amince suyi rigstar domin samun damar sauraran abubuwan da za'a gabatar a cikin Group din. Bayan haka akwai Magunguna na hausa masu kyau da Inganci!*
1- Maganin Sanyin mara
2-Maganin Sanyi mai sa budewar gaba
3-Maganin Sanyi mai sa warin gaba da fitar da ruwa
4-Maganin Sanyi mai sa bushewar gaba
5- Maganin Sanyi mai hana Sha'awa
6-Maganin Sanyi mai hana haihuwa
7- Maganin Sanyi mai sa zafi gurin saduwar aure (sex)
8-Maganin Basir mai tsiro
9-Maganin Basir mai kulle ciki
10-Maganin Karfin Maza(Gurin Sex)
*11- Maganin Karin Ni'ima
12- Maganin K'iba mai kyau
13- Maganin Cikar Nono (Breast)
14- Maganin Hips
15-Maganin kurajen fata da hadin sabulai masu kyau da inganci!
16- Maganin Matsi mai kyau
17-Maganin Sanyi mai sa budewar gaba
18-Maganin kara karfin sha'awa da dade wa gurin (Sex)
19-Maganin Basir mai sa yunkuri da budewar gaba


*_Duk Zaku samu wannan magungunan Cikin farashi mai sauki Kuma babu algus da almundahana a ciki sai da mukayi binkice muka tantance sannan Kada kiyi kokwanto ko shakka akan ingantattun magungunan mu Insha Allahu idan kin gwada sai kin neme mu Hausawa suka ce siyan nagari mai da kudi gida Ga masu bukatar suyi rigstar da Group na MAR'ATUS-SALIHA sai suyi min magana ta WhatsApp da wannan number._*
*07084653262*
*1k Rigstar da Group din MAR'ATUS-SALIHA*
Accont.....0542382124.....Binta Umar gtbank....Idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp




_*GA MASU BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP #400 VIP #600 ACCONT.......0542382124....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZA'A TURO AYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBERS ZAN FA'DI YANDA ZA'AYI*_
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*

*_MUTANAN NIJAR IDAN KUNA BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP DALA DARI VIP GROUP JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO ORANGE KU NEMI WANNAN NUMBER......._*
*22790899076*
*HAJIA FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
[9/25, 3:47 PM] Jamila Yushau: *MATSALAR MU A YAU!*
_(Labarin Surayya)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION🤝🏻*
____________________________

*SADAUKARWA NE GA:*
_(Surayya dee🥰)_

FreePege
*21&22*
Washe gari da wuri muka fito bakin titi domin samun abun hawa jin horn a bayan mu yasa da sauri muka juya motarsa ce ke kokarin fitowa daga ciki sai muka matsa gefe muna rige-rigen gaishe shi. Cikin nutsuwa ya sauke gilashin motar da hannu yayi mana alamar mu shiga......Ba tare da 'bata lokaci ba Samira ta bude motar ta shiga na zauna a kusa da ita yace."Ku rufe motar sosai." Da sauri na rufe motar ina sake gyara zamana....... Sanyi da kamshin motar ne suka saukar min da wata irin kasala na dinga satar kallonshi yana draving cikin nutsuwa komai nasa babu baragada da shirme a cikinsa gefan fuskarsa na tsirawa ido babu ko kiftawa hakika ina mutukar kaunar Namiji mai saje da gemu daidai misali Uncle yana da wani irin saje mai kyau wanda ya qayata masa fuskarsa kalar fatarsa kuwa irin me wahalar samu ce yana da wani irin kyau wanda sai ka tsira masa ido sannan zaka tantance.

Duk irin kallon kurrulan da take masa yana kallonta da gefan idonsa sai al'amarin ya dinga bashi mamaki yana nazari da tunani akan kallon da take masa................Zazzafar ajiyar zuciya na sauke wanda yayi daidai da lokacin da ya kunna karatun al'kur'ani a cikin motar....Zuciyata ta sake narkewa sai kawai naji hawaye na kokarin kufce min hakika Allah ya jarrabe ni da abinda yafi karfina.


Tun daga bakin gate ake gaishe shi har muka shiga cikin makarantar a gurin parking ma Malamai da dalibai masu mu'kami sunyi dafifi a gurin suna jiran ya fito.

Ya kallemu babu walwala a fuskarsa yace."Kuje aji.'' Da sauri na bude motar aikuwa idanu yayi caaaa! a kanmu a take naga sauyin yanayi a fuskokin wasu malamai mata da daliban makaranar...... gurin muka bari da sauri kamar yanda ya umarce mu.


Tunda na zauna kan kujera na kifa kaina kasa ban kara sanin abinda ake gudanarwa a class din ba....Tunani na gabadaya ya tafi gurin ganin hanyar da zan samu muradin zuciyata....Malamai uku suka shigo sukayi abinda za suyi suka fita ban gane komai ba Allah-Allah nake a fita break mu zauna da Samira.


A sanyaye nace."Samira guy nan kamar kara masa kyau ake wallahi dazu a cikin motarsa ji nayi kamar naje na sumbaci gefan fuskarsa ina tsananin kaunar namiji mai gemu da saje.

Samira na kallona tace."Surayya kin makance gaskiya wallahi ina tausayi miki wani abu." Rai a bace nace."Samira kada ki 'bata min rai don Allah wallahi ni ji nake kamar na aureshi na gama sam yanzu bana jin tsoron na furta masa kalmar so.

Tace."Kamar gaske wallahi ba zaki iya ba abinda kina ganinsa jikinki yake mutuwa ina kallonki fa dazu a motarsa kina goge hawaye." Girgiza kaina nayi nace."Samira ni kaina ban san sanda hawayen ke fitowa ba shiyasa nace miki Allah ya jarrabe ni."

Tace."To yanzu dai ga waya kuma akwai kudi ina fatan kin dauki number." Wayar na kar'ba daga hannunta nasa number. Cike da mamaki tace."Lallai har kin haddace number sa a kanki."

Murmushin takaici nayi nace."Meye number waya Samira shi kansa na haddace shi dan idan na rintse idona shi kadai nake gani.

Girgiza kanta kawai tayi tace."To yau kuma wasu irin kalamai zamu tsara masa." kallonta nayi da fadin.'' Kalaman soyayya masu zafi amma fara kiranshi muryarsa kawai nake so naji.

Baki bude take kallona nace."Idan kin kira shuru za muyi kawai inaso naji muryarsa.....Samira ba tare da shakka ba ta fara kiran number.

Tana kokarin katsewa ya d'aga muryarsa mai cike da amo da sauti ta bayyana.......da sauri na kar'bi wayar na bude hands free nasa wayar a kunnena ina lumshe idona "Salamu alaikum wake magana." Na lumshe ido tare da sauke wani irin nishi!!!!

Da saurin gaske ya cire wayar daga kunnanshi yana duba number Nishin! da yake fita daga wayar shine ya bashi mamaki! wayar ya mayar kunnanshi cikin tsawa! yace."Waye akan layi."?

Hannu na rawa na kashe wayar! muka tsirawa juna ido ni da ita........'bangaran shi kuwa shuru yayi da wayar a hannunsa yana mamakin al'amarin wace 'yar iskar yarinya ce ta kira shi a waya take masa nishi!!!!

Please Login or Register in order to submit comment