Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

MAZAN JIYA
BOOK 2 - Abdulaziz Sani Madakin Gini
Typing by Shuraih Usman 99%
Post and Published at Taskarnovels - 2023

KASHE GARI da sassafe rundunar su Sarki Dujalu suka mike suka ci gaba da tafiya, bayan kowa ya kimtsa cikinsa. Tun da aka fara tafiyar sai sarki Dujalu ya lura da cewa 'yar uwarsa Hursiya bata da sukuni.

A duk sa'adda ya dubeta sai ya ga alamomin damuwa cike a fuskarta kawai sai ya yi murmushi domin shi kadai ne ya san abin da ke damunta.

Abin da ya bashi mamaki shi ne, mene ne ya hanata ta baiyana masa abin da ke damunta, ba wani abu bane ya ke damun Hursiya ba face tsananin son jin ci gaban labarin sadauki Hantaru.

Haka dai aka ci gaba da wannan tafiya har tsawon kwana uku, Duk sa'adda aka yada zango sai Hursiyya ta lallaba sarki Dujalu domin ya ci gaba da bata labarin.

Da zarar ya fuskanci abin da take so, sai ya kama gyan-gyadin karya, bisa dole Hursiya ta hakura itama ta kwanta har barci ya saceta bata sani ba.

Da yammacin kwana na uku ne wannan runduna ta su sarki Dujalu ta iso wani katon daji mai ban tsoro wanda ake yiwa lakabi da Sauratul Auzur.

Duk da tsananin yawan wannan runduna ta aljanu da mutane da kuma gagarumin shirinsu sai da kowa yaji tsoro ya shigeshi, bisa tsintar kansu a cikin dajin Sauratul Auzur, sarki Dujalu ne kadai bai girgiza ba.

Shi dai dajin Sauratul Auzur babu komai a cikinsa face manya-manyan bishiyoyi da manyan duwatsu masu ban mamaki.

Babu inda mutum zai je a duniya ya ga irinsu, sannan siffofin bishiyoyin da duwatsun ma ababan tsoro ne. Sau tari sai mutum ya ga suna motsi da rangaji tamkar za su haifar da girgizar kasa a dajin gaba daya.

Daga dajin Sauratul Auzur zuwa tekun bahar Sufiya tafiya ce ta wata hudu kacal, kuma a cikin dajin Sauratul Auzur mutum zai yi ta tafiya ta tsawon wata hudu.

Da isowar su sarki Dujalu farkon dajin Sauratul Auzur, sai sarki Dujalu ya bada umarnin a tsaya.

Nan take kuwa na kan dawakai suka dakatar da dawakansu, aljanun da ke tafiya a sararin sama kuwa suka saki fuka-fukansu suka sauko kasa.

Nan fa kowa yai ladaf aka yi tsit tamkar babu mai numfashi a wajen. Sarki Dujalu yai gyaran murya sannan ya ce,

"Ya ku jama'ata kuyi sani cewa mun iso dajin Sauratul Auzur. Daga nan zuwa tekun bahar Sufiya inda takobin Saiful Lujara take tafiyar wata hudu ce kacal. Ku yi sani cewa masifu da bala'in da ke cikin wannan daji sun wuce tunani don baka sai kowa ya gyara damararsa, domin komai zai iya faruwa.
Ko shakka bana yi da yawa daga cikinmu za su iya rasa rayuwarsu acikin wannan daji. Wadanda duk suka kai izuwa karshen wannan daji araye a cikin koshin lafiya sun cika mazajan kwarai ababan yabo da jinjina." ai Koda gama fadin haka sai sarki Dujalu ya dubi Hursiyq ya ce,

"Komai wuya da tsanani ki tabbatar da cewa a ko yaushe kina tare da ni. Hursiya ta gyada kai tana mai nuna nun cewa lallai za ta kiyaye. A Nan take sarki Dujalu ya zunguri cikin aljanin da ke dauke da su shi da Hursiy, suka fara wucewa kan gaba, sannan kowa ya bi bayansu a cikin yanayin tsoro da dari-dari. Sai da aka shafe sa'a guda ana tafiya a cikin dajin ba a hadu da komai ba kuma ba a ga wani mugun abu ba.

Al'amarin da ya jefa kowa cikin tsananin mamaki ke nan domin in banda kukan kananan tantsaye da kwari babu wani sauti da ke ratsa kunnuwa. Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai kawai aka hango wata jibgegiyar halitta a can gaba ta cika hanya tun daga sama har kasa tamkar za ta tokare da hadari.

Babu ta inda za a bi a wuce face ta cikin halittar. Ita dai wannan halitta tana kama da bil'adama, aljan da kuma dodo, Kuma gaba dayan jikinna ta ne yake da siffofi ukun. Ma'ana fuskarta da gangar jikinta da hannayenta.

Koda aka yi arba da wannan halitta sai gaba dayan dakarun sarki dujalu suka firgice suka tsaya cak A waje dqya Aljanin da ke dauke da dauke da sarki Dujalu wanda ake kira Rauzuf sai ya fara kaɗa fuka-fukansa a hankali alamar shima ya tsorata amma bai fasa tunkarar haittar ba saboda gudun fishin sarki Dujalu, ammna gaba dayan jiinsa karkarwa yake tamkar wanda ya kamu da Zazza6i mai zafi."

Koda sari Dujalu ya fahimci halin da aljani Rauzuf ke cilki sai ya daka masa tsawa ya ce, "Ya kai Rauzuf a kul ka kuskura ka ja da baya ko kuma ka tsaya ga ci gaba da tafiya idan kuwa ka tsaya ni da kaina zan zare maka ruhin numfashi". Koda jin wannan batu sai aljani Rauzuf ya kara karfin tafiyarsa ya tunkari wannan katuwar halitta kai tsaye.

Sai da suka iso daf da halittar ya ZAmana cewa tazarar da ke tsakaninsu ba ta wuce kamu uku ba sai haittar ta wangame katon bakinta mai kama da kofar gari ya buso wata irin iska mai karfin gaske tamkAr guguwa. Take aljani Rauzuf ya fado kasa tim! Sarki Dujalu da Hursiya suka tuntsuro kasa daga kansa suka baje a kas. Hatta sauran dakarun da ke bayansu sai da iskar ta tarwatsasu, na sama suka rikito kasa na kasa kuwa suka baje.

Daga can sai katuwar halittar ta bushe da mahauknciyar dariya mai tsananin ban tsoro wacce ta sa kowa da kowa ya sume face sarki Dujalu Gaba dayan dajin ya hautsine ya kama rangaji. wuta ta kama bishiyoyi. Babu abun da ya rage a tsaye bisa duga-digansa face sarki Dujalu.

A wannan lokaci ne shirgegiyar halittar ta bude idanuwanta kwala-kwala masu kama da girman rana ta dubi Dujalu cikin tsananin mamaki. Fiye da shekaru dubu da doriya wannar halitta ke tsare wannan hanya, duk abin da ya zo gabantan in dai tayi wannan dariya sai abin ya fadi Kasa sumamme amma yau ga wani takadarin bil'adama guda daya a tsaye cak a gabanta ko girgiza bai yi ba.

Cikin wata irin kakkausar murya halittar ta dubi aljani Dujalu ta daka masa tsawa Duk da cewa sarki Dujalu gwarzon namiji ne wanda bai san tsoro ba sai da hantar cikinsa ta kada shi kuwa aljani RauZuf take ya kara sumewa a karo na biyu.

Halittar ta dubi Dujalu cilkin nutsuwa ta ce, ya kai wannan hatsabibin bil'adama wane ne kal kuma wane tsautsayi ne ya shigo da ku cikin Wannan daji na Sauratul Auzur alhali kun sani cewa ba a taba ratsowa ta cikinsa ba?" Sa'adda sarki Dujalu yaji wannan tambaya sai ya bushe da dariya sannan ya murtuke fuskarsa kamar wanda aka aikowa da sakon mnutuwa ya ce, "Ni ne sarki Dujalu mai mulkar kasar Hawarul din.

Ya kai wannan babbar halitta ka sani cewWa na yarda da kaina domin ni ne DODON MAZA a wannan ZAmani, magajin MAZAN JIYA. Duk bala'in da ke cikin wanann daji na san da shi kuma sai na ketare ta cikinsa domin na isa tekun bahar Sufiya don na dauko takobin Saiful Lujara."

Koda sarki Dujalu yazo nan a zancensa sai katuwar halittar ta sake bushewa da dariya a karo na biyu sannan ta ce, "Sama da mutum dubu dari ire-irenku wato masu irin wannan buri naka sun hallaka bisa wannan tafarki wadanda duk abin da kake takama da shi sun fika. Babu wanda ya taba haye bala'in bare har ya shafe sauran tafiyar da ke cikin dannan daji na Sauratul Auzur ya ketare sauran masifun da ke cikinsa ya isa bakin tekun Bahar Sufiya.

Ina mai shawartarka da ka juya da baya kai da jama'arka domin kada ka janyo asarar miliyoyin rayuka a banza." Sariki Dujalu ya yi murmushi mai nuna yarda da kai, sannan ya ce, "Ko mutum daya daga cikin jama'ata ba zai rasa rayuwarsa ba. Ni kadai zan samar mana da hanya mu wuce gaba saboda haka ina mai shawartarka da ka kauce daga kan hanyarmu idan har kana son ka tsira da rayuwarka don ban ga abin da ya isa ya hanani ratsawa ta cikin wannan daji ba." Kafin sarki Dujalu ya gama rufe bakinsa tuni katuwar halittar ta mike tsaye. Alamarin da ya sa gaba daya dajin ya yi lumshi tamkar rana ta faɗi ashe da can a zAune take ba a tsaye ba. A sannan ne sarki Dujalu ya daga kansa sama ya dubi halittar Nan take halittar ta sake buso iska ga sarki Dujalu,


Wannan karon sai iskar ta dagashi sama ta fara gwarashi a jikin manyan bishiyoyin dake dajin. A dai-dai wannan lokacin ne Hursiya da sauran Dakarun gaba daya suka farfado daga dogon suman da suka yi suka ga abin da ke faruwa.

Koda suka ga sarki Dujalu a sama ana gwarashi a jikin bishiyoyi har ya fara galabaita sai bankalinsu ya dugunzuma ainun suka karaya lta kuwa Hursiya sai ta fashe da kuka domin ta tabbatar da cewa shi ke nan ta rasa dan uwanta. Gaba dayan dakarun dai sai suka cika da mamaki saboda a yadda suka san sadaukantakar sarkinsu da karfin sihirinsa amma sai gashi duk sun zamo banza ya kasa ceton kansa ma bare suma ya cecesu.


Nan fa wasu daga cilkinsu suka fara tunanin su ja da baya don kada Wannan halitta ta gama da sarki dujalu sannan ta dawo kansu . Kafin su yanke hukunci ne wani abin mamaki ya faru, kawai sai gani suka yi shima sarki Dujalu ya yi nuni da hannunsa izuwa ga wannan iska mai karfi da take wujijigashi take wata irin iska ta fito daga cikin haAnnun nasa ta kama đaya iskar mai wahalar da shi suka kamna gumurzu, Nan fa kallo ya koma kan iskokin biyu suka rinka tsiri a sama suna fitar da wata irin tsawa da kugi mai razanarwa.


Wani lokacin idan iskokin suka yi sama sai ka ji sun fado kasa fat! Tamkar giwa ta fadi. Katuwar halittar da sarki Dujalu sai sulka zuba idanu kawai suna kallon gumurzun da iskokin ke yi. Nan fa dajin ya kara ruguntsumewa domin a duk sa'adda iskokin suka hada jiki sai ka ga wuta na feshi da tartsatsi. Al'amarin da ya sa gaba dayan dakarun suka dimauce ke nan suka kama guje-guje a cikin dajin suna neman ma6oya. Kafin a jima filin wajen ya dade babu kowa face sariki Dujalu sai aljaninsa Rauzuf da kuma Hursiya wadda jikinsu ke makyarkyata saboda tsananin tsoro, shi aljani Rauzuf ma bai san sa'adda ya fara sakin fitsari ba, amma bisa mamaki sai ya ga wannan feshin wuta da tartsatsin basa zuwa inda suke shi da Hursiya sai dai su zuba a gefensa.


A duk sa'adda iskokin biyu suka fađo kasa kuwa, sai gaba dayan dajin ya kama tambal tamkar jirgin ruwa akan kogi sa'adda ruwa ta kada. Haka dai aka ci gaba da wannan dauki ba dadi har tsawon sa'a guda.

Daga karshe ne iskokin biyu suka kankame juna suka kama da wuta sulka kone kurmus suka zama toka. Koda faruwar hakan sai aka fara kallon-kallo tsakanin sarki Dujalu da katuwar halittar a ya yin da ta sauko da dogon kanta kasa tamkar zal6e ya leko da wuyansa waje daga cikin tagar daki.

Koda sarki Dujalu ya yi arba da mummunar fuskar halitar sai yaji zuciyarsa ta buga da karfin gaske. Wannan shi ne karo ne farko da sarki Dujalu yaji tsoro ya shigeshi a rayuwarsa. Bisa dole Dujalu ya ja da baya taku uku, amma saboda yana da dakakkiyar zuciya sai ya ki gudu ya tsaya ya zare takobi, kuma ya gyara tsayuwa akan aljani Rauzuf.

Ya yin da babbar halittar ta ga abin da Dujalu ya yi sai ta bude hannayenta biyu ta dagasu sama kai kace Lagwayen tsaunikane ke yawo a samaniya sannan Sai ta wangame katon bakinta ta kwarara uban ihu wanda ya zamo sanadin sake ruguntsumewar dajın fiye da ko yaushe. Shi kansa Dujalu bai san sa'adda ya kara ja da baya ba. Ita kuwa Hursiya sai ta kankame Dujalu ta baya ta fashe da kuka.

Cikin kwarin zuciya Dujalu ya 6an6areta daga jikinsa ya zaunar da ita kasa bisa kan aljani Rauzuf sannan sai ya tashi sama kamar tsuntsu ya juyo ya dubi aljani Rauzuf ya ce, "Ku dan ja da baya kadan ku zuba ido ku ga abin da zai faru. Idan na sami nasarar hallaka wannan halitta sai mu ci gaba da tafiya idan kuma ta hallakani ku koma da baya ku nemi sauran abokan tafiya domin ku koma can birnin Hawarul din, gimbiya Hursiya ta gaji karagata".

Koda gama fadin haka sai sarki Dujahu ya yunkura da dukkan karfinsa ya tasarmma katuwar halittar ya kai ma ta wawan sara a hannunta na hagu." Koda takobin Dujalu ta sari hannun sai tartsatsin wuta ya tashi gami da wata irin kara tamkar karfe da karfe. Halittar ta yi girgiza tamkar susa aka yi ma ta. Dujalu yaja da baya kadan, koda ya dubi kaifin takobinsa sai ya ga ta dakushe. Al'amarin da ya matukar girgizZa hankalinsa kenan ya gamsu cewa lallai yau ya gamu da gamonsa.

Dujalu ya kurawa halittar idanu yana tunanin irin dabarar da ya kamata ya yi don ganin ya kawar da ita. Abu na farko dai shi ne, ya tabbatar da cewa in dai batun karfin damtse ne ba zai iya da ita ba, don ko ba a gwadaba linzami yafi karfin bakin kaZa. Haka kuma idan batun karfin Sihiri ne nan ma ya san babu nasara tun da an gwada an yi RAGAS. To wai shin mene ne zai kwaceshi a hannun wannan halitta? Ai babu mafita face sa'a, Kafin sarki Dujalu ya gama aiyana wannan furuci a bakinsa sai halittar ta yi masa wawan mangari da hannunta guda a fuska saboda karfin dukan sai da sarki Dujalu ya ga taurarin wahala a idanunsa numfashinsa ya sarke a lokacin da yi sama tamkar an janyeshi da kugiya Dujalu ya gwaru da bishiya har keyarsa ta tsage ya fado kasa a cilkin wani irin mugun hali mai kama da rabin suma.

Koda jibgegiyar halittar ta ga ta sami wannan nasara sai ta bushe da mahaukaciyar dariya. Koda gama fadin haka sai Hursiya ta kwarara uban ihu ta fashe da kuka, domin zuciyarta ta gama karaya ta sallama cewa dan uwanta ya gama halaka, Shi kuwa aljani Rauzuf sai ya yunkura da nufin ya bude fuka-fukanssa ya gudu.

Ai kuwa shima sai ji ya yi an fyadeshi ya baje a kas, sai ga jini na zuba ta cikin hancinsa da bakinsa, ko motsi bai yi ba tamkar gawa. A dai-dai wannan lokaci ne katuwar halittar ta fara tako kafafunta ta nufo inda sarki Dujalu ke kwance da kafuta, da nufin ta mitsttsikeshi sannan ta halaka Hursiya.

Cikin karfin hali Hursiya ta ruga kan Dujalu ta fara kokarin janyeshi daga inda yake kwance, don kada halittar ta cimma nufinta. Hursiya na cikin jan sarki Dujalu sai kawai taji ya cije. Nan take ya bude idanunsa ya dubeta ya ce, "Ma za ki mike ki ruga izuwa baya, yanzu za mu fara gagarumin yaki ni da wannan halitta wanda zai iya janyo hallakar duk wani abu mai rai da ke cilkin dajin nan saboda haka kiyi ta gudu iyakar iyawarki har sai inda kuzarinki ya kare, kar ki damu dani, nai miki alkawari lallai zan riskeki a duk inda kike kuma a raye."


Koda jin wannan batu sai Hursiya ta mike zumbur ta falfala da gudun tsiya. A dai-dai wannan lokaci ne halittar tayi taku đaya jal, ta isa daf da Dujalu ta daga kafarta guda sama za ta mitsttsikeshi.


Yadda Dujalu ya ga fadin kafar halittar tamkar katon tsauni ne zai danneshi cikin tsananin zafin nama sarki Dujalu ya daka tsalle ya haye kan saman kafar halittar ya kama azababben gudu akanta, yabi ta kan kansakalin kafar ya bi ta cinya tamkar kadangare na hawa bango. Koda halittar taji Dujalu na tafiya a jikinta sai ta rinka kawo masa duk da tafin hannunta. Da ZArar ta kawo dukan ya goce sai ka ji wata irin kara fau tamkar an buga tambura, wani irin gagarumar iska na tashi.


A haka ne Dujalu ya samu ya isa kan kafadar halittar, sai da ya yi gudun rabin sa'a uku akan kafadar sannan ya iso inda fuskar take ya sake daka tsalle sama ya saita ha6ar halittar da takobinsa. Sautin karar haduwar Rarfe da karfe ne ya tashi kawai. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin Dujalu ke nan domin shi a zatonsa halittar Za ta ji sara a fuska. Nan fa aka fara sabon gumurzu a tsakaninsu ya zAMana cewa Dujalu na ta tsalle-tsalle akan halittar tamkar mai yawo a cikin katon daji. Ita kuwa halittar ta rinka kai masa duka da cafka, aka rasa wanda zai sami nasara a cikinsu. Sai da aka shafe sa'a tara ana Wannan gumurzu. A sannan ne sarki Dujalu ya gaji ainun, ita kuwa halittar ko kadan babu alanar gajiya a tare da ita tamkar ma a sannan aka fara artabu. Koda sarki Dujau ya fahimci cewa idan fa aka ci gaba da wannan gumurzu a haka izuwa tsawon sa'a daya jal zai sare ya kasa komai, halittar ta sami nasarar hallakashi sai hankalinsa ya dugunzuma ya fara tunanin abin da zai fissheshi. Tsawon rabin sa'a Dujalu bai yi tunanin mafita ba. dai-dai wannan lokaci ne halittar ta A shammaci Dujalu ta mangareshi ta baya ya rikito kasa daga kan kafadarta. Koda ganin haka sai halittar tayi shiri tana jira kawai Dujalu ya fado kan turba ta murkusheshi da guiwarta yadda za ta talitseshi. Saboda nisan da ke tsakanin kafar helittar zuwa kasa sai da Dujalu ya shafe dakika đari shida da sittin yana saukowa kasa. Sa'adda Dujalu yaji kafafunsa sun dira bisa turba sai ya yunkura ya kara daka tsalle sama tamkar akan sifirin ya dira, a lokacin ne kuma halittar ta tsugunno kasa da nufin ta talitseshi da guiwarta amma sai taji guiwarta ta bugi kasa ta nutse cikin kasar ta haifar da katon rami mai zurfin kamu dubu.

Kafin halittar ta zare guiwarta daga cikin karkashin kasa tuni Dujalu ya sake isa kan kafadarta. Kafafunsq na dira akan kafadar sai ya sake daka tsalle yai sama ya isa dai-dai fuskarta sai kawai ya soka takobinsa izuwa cikin hancinta guda. Ai kuwa sai halittar ta kwarara uban ihu bisa tsananin zafin da zogin da taji tayi taga-taga da baya. Tuni takobin Dujalu ta makale cikin hancin halittar, shi kuwa sai ya rike takobin da hannaycnsa biyu yana reto a sama kuma ya ci gaba da kokarin Zare takobin amma sai ya kasa.

A duk sa'adda ya girgiza takobin sai halittar ta kwarara ihu ta kawo masa mangari amma sai ya wurkila kafafunsa ya goce. Shi kansa Dujalu ya yi mamakin yadda ya kasa Zare takobin duk da cewa gaba dayan nauyinsa a kanta yake. Daga can sai Dujalu ya yi amfani da dukkan karfinsa ya finciko takobin ya zarota daga cikin hancin halittar.

Takobin na zarewa sai ga jini na shatata tamkar teku ta 6alle. Dujalu ya rikito izuwa kasa, itama halittar sai ta taho kasa a sandare. Dujalu da halittar suka taba turba a lokaci guda. Kafin Dujalu ya goce wuyan halittar ya fadi a tsakiyar cikinsa, amma sai ya yi gwafa bai ta6a jikinsa ba, amma ya rufeshi yadda ba zai iya fitar da kansa ba.


Halittar dai ko motsi bata sake yi ba, domin ta zama gawa. Har a sannan kuma jini na malala daga cikinta yana kwarara a dajin, tamkar ruwan Samansa ake yi. Dujalu dai bai san sa'adda ya bushe da dariyar farin ciki ba, bisa ganin wannan gagarumnar nasara da ya samu ta hallaka halittar, amma da ya dago kai ya dubi wuyan halittar Wanda yai gwafa a kansa ya tokareshi sai hankalinsa ya yi mummunan tashi domin bai san yadda zai iya ture gawar halittar ba ya fito, saboda jikin halittar ba zai saruba da takobi bare ya Sareshi. Dujalu na cikin wannan tunani ne ya hango yar uwarsa Hursiya ta rugo gareshi da gudu ita kedai tana murmushin farin ciki. A

sannan ne kuma aljani Rauzuf ya farka daga dogon suman da ya yi, ba zato kuma sai ga sauran dakaru suna dawowa đai-đai daga wuraren da suka buya suna rugowa wajen Dujalu suna ihu bayan hari. Duk wanda yazo ya ga wannan katuwar halitta kwance a kas a mace sai ya cika da tsananin mamaki. Nan fa dakaru suka kama shewa da murna suna yiwa Dujalu jinjina.


Duk wannan abu da ke faruwa zuciyar Dujalu tafarfasa take kamar za ta kone saboda tashin hankalin da yake ciki na ganin kansa a karkashin gawar halittar bisa sanin ćewa ba zai iya fitowa ba. Daga can sai Hursiya ta lura da fuskar Dujatu ta fahimci cewa lallai a cikin tsananin damuwa yake. Cikin firgici Hursiya ta dubeshi ta ce, "Ya kai đan uwana ina dalilin wannan matsanaiciyar damuwa a gareka?". Koda jin wannan tambaya sai sarki Dujalu yai ajiyar zuciya cikin karaya ya ce, "Ya ke 'yar uwata kiyi sani cewa wannan murna da kuke yi bisa samun nasarata dai-dai take da farin ciki da Zuwan mutuwata. Ki dubi yadda na kasance a Karkashin gawar wannan halitta, yanzu ta ya ya za ku iya Zaroni daga karkashinta, shin a cikinku Wane ne ya yi tunanin wannan hali da
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment