Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels



*LOKACI NE*
(Gajeran Labari)

Daga Alƙalamin
Maryam Abdul'aziz
(Mai_Ƙosai)

Godiya: Ga Allah subhanahu wata'ala da ya ba ni dama da ikon fara rubuta wannan ɗan gajeran Labarin. Tsira da aminci su tabbata ga shugaban rahma Annabi Muhammad (S.W.A) da sahabbansa da ahlayensa da duka mabiyansa.

Gargaɗi: Ban yarda wani ko wata su sauya min Labarina ba, yin hakan ya saɓa da doka, kuma lallai tabbas ba makawa za a ɗau tsattsauran hukunci ga duk wanda ya yi hakan domin Labarin da rubutun duka haƙƙin Marubuciyar ne, dan haka a kiyaye.

Ɗaya
Sannu a hankali take bin kowanne sassan ɗakin da kallo, lokaci guda ƙwaƙwalwarta ta soma dawo mata da muhawararta da mahaifiyartana san auren dolen da take shirin yi mata, kuma wai ba da kowa ba sai da mutumin da ya so keta mata haddinta, mashayi ɗan caca. ko da yake ba wannan ce tsagwarar damuwarta ba illah kawai ta ga ta yi aure ta huta da gorin da ake mata, amma ya ta iya da samarin kakarta lokaci ne kuma ba shakka zai keto ta kanta.
Ta sauke hucin iskar da ta futar daga bakinta. Gaba ɗaya ƙwaƙwalwarta a cunkushe take ,ji take yi kantana mugun sara mata ta yiyuwu ma madaki ne ake dukanta ta shi wanda za a iya ta'allaƙashi da rodi ko guduma. Tsakiyar kanta ce ke tsananin san tarwatsewa saboda tsabar sarawar da kan nata ya ke yi.
Rinannun jajayen idanuwanta da suka kaɗa suka yi jazur da su wanda sun jima da sauya launi ta ɗaga tana mai kallon agogon da ke maƙale jikin bangon ɗakin. tana ji zuciyartana kuma bugawa da sauri da sauri kamar tarago, yadda ko wanne sakanni ke kaɗawa tare da tafiyar tsinken jikin agogon.
Matashiyar budurwa ce mai kimanin shekaru ashirin da biyu wankan tarwaɗa ,tana da yalwar ga shi wanda zaka gane hakan ta yadda gashin ya zubo mata har gadan baya ,sai matasan idanuwanta da ba za ka saka su a matsayin manya ba ko ƙanana, sai laɓɓanta biyu masukalar ruwan hoda, ba ta da wani kakkauran jiki sai dai tana da yalwar tsayi.
A hankali ta ranƙwafa ta miƙe tsaye jikintana wani irin kakkarwa, daidai da jirin da ya kwasheta ta tafi taga-taga za ta faɗi, cikin sauri ta koma ta zauna da ƙyar ta iya ya fito kalmar "Hasbunallahu wani'imal wakil" ta yafa a bakinta. Cikin hukuncin Allah wasu zafafan ruwan hawaye masu ɗumi suka shiga kwaranyo mata a kan kyawawan kumatunta.
Karo na biyu da ta kuma yinƙurawa ta miƙe cikin dauriya da san nuna jarumta , hannunta ta saka a kan kanta ta dafe kan da ke tsananin sara mata hawaye na daɗa kwarara daga cikin kogin idanuwanta.
Dukkan abin da Ubangijj buwayi gagara misali ya hukunta lallai ba shakka ko ana muzuru ana shaho sai lamarin ya kasance. Mutane da dama kan nazarci wasu abubuwan daban ta fuskoki mabambanta. Duk da kallon hadarin ka jin da wasu ke yiwa abun cikin rashin sanin ingantacciyar mafaka, har ila yau abubuwa ke kuma cunkushewa a cikin ƙwaƙwalensu in da take musu tufka da warwara cikin wasu daƙiƙu kuma sai su zartar da abin da zai saka zuƙatansu tararradi.

***
Jingine ya ke jikin wata dallaleliyar kyakkyawar mota wanda a ƙiyasi ba za a iya ƙiyasto adadin kuɗin da a ka saka a ka siyota ba. Ya fi mintuna masu ɗan tsawo a wajen jefi-jefi ya kan duba agogon dake ɗaure a saman tsintsiyar hannunsa tare da jan tsaki. "Mitsss!" Karo na uku ke nan da ya kuma jan wani tsakin wanda in ka na daga nesa ma za ka iya jiyo shi muddin tazarar ba ta wuce taku ashirin ba.
"Abbas har yanzu ba ka wuce ba.?"
A ka jefo masa tambayar da ta saka shi kallon in da sautin maganar ta fito. Kauda kansa ya yi gefe tare da taɓe baki kafin ya ce,
" Ban tafi ba, ina nan dai tsaye kamar bishiyar da aka dasa."
"Ni kam sai na ke ganin kamar zai fi maka ka kyau ka san na yi." A ka kuma furtawa.
"Ba na tunanin sanyawa icen da ya tanƙware mayen ƙarfe zai saka ya dawo yadda ya ke."
Abbas ya yi furucin ya na mai sake taɓe bakinsa.
"Shi ke nan tunda haka ka zaɓa, amma kamar zai fi maka kyau ka bazawa bujan bujejen burmemen wandonka iska ka arci na kare wala Allah ka sami sa'ada."
Matashin saurayin ya ƙarasa faɗa da sakin wani guntun gajeran murmurshi. A shekaru da tsayi za su iya yin kai ɗaya da Abbas ɗin duk da cewa Abbas ya fi shi nuna jikin girma da hutu.
Abbas bai tanka masa ba, domin ji yake zuciyarsa na matuƙar tafarfasa a halin yanzu, kuma muddin in har ya buɗe baki ya yi magana to zai iya gasa masa maganar da zai kwana ya yini ya na jinta cikin ƙahon zuciyarsa kuma ƙwaƙwalwarsa ba za ta taɓa mantawa da maganar ba za ta kasance kullum abar tunaninsa.
Shi ma ganin haka ya sa ya kama gaban shi ba tare da ya sake furtawa Abbas ɗin komai ba.
Duk abin da ya ke faruwa kan idanuwan wata kyakkyawar matashiyar yarinya mai kimanin shekara goma sha tara zuwa ashirin. Laɓe take jikin wata katanga tana hangensu duk da ba ta ji me suke tattaunawa ba amma ya nayin fuskar Abbas ya nuna mata lallai ba magana mai daɗi ci ta wanzu tsakaninsu ba.
Ya tsina baki ta yi tana mai furta, "Wahalalle, ai sai ka daskare a wajen." ta juya daga inda take tana mai komawa cikin gidan.
"Har kin dawo? Ya tafi ne?" A ka watso mata mabambanta tambayoyin, wanda ba kowa ba ce fa ce mahaifiyarta Mama.
Turo baki ta yi tana mai ɗan ƙunƙuni ta ce, "A'a ni ko ƙarasawa ma ban yi ba wajensa. Mama kawai ni fa ba na jin zan iya jin zantukan kalamansa a cikin amsa kuwwar kunnuwana."
"Iye! Lallai kin girma kin zama riƙaƙƙiyar kuɓewa, kin ta fasa kin zama talge shiyasa." Mama ta yi furucin.
"Ni Mama wai mene ne laifina a ciki ? Ba fa a yin so dole." Ta ce.
"Ba a yi. Amma dai ki yi a hankali wallahi ina jiye miki gaba." Mama ta ce.
Ba ta kuma sauraran lafuzan Mama ba ta wuce ɗaki a bin ta tana mai ƙara turo baki gaba, balle ma ta san cewa wani ɓoyayyen saƙo Mama ke san isar mata. Mama kam ƙwafa ta yi ta cigaba da sabgoginta.
Sabon salo ,sabon kafce.
Mai_ƙosai

*LOKACI NE*

Mai_Ƙosai

FCWA

Biyu.
Wasu ruwan hawaye ne suka kuma kwaranyowa a kan fuskarta, maganar Mama da rayuwarta ta baya suka so dawo mata sababbi dal! Ta lallaɓa a hankali ta isa bakin ƙofar ɗakin da ta ke ciki, kallon ko ina ta ke yi kantana kuma sarawa.
"Har kin farka?"
A ka jefo mata tambaya, gyaɗa kai kawai ta yi dan ba za ta iya furta wani furucin ba a halin da ta ke ciki a yanzu.
"Sannu, muje na nuna miki bayi ki yi alawa ki zo ki yi sallah, dan lokacin sallah har ya gota sosai."
Matar ta kuma yin furucin a karo na biyu. Duk da cewa ta zarar ta su ba ta da wani yawa a ƙirar jiki sai dai kawai matar ta nuna mata diri.
Har banɗakin ta raka ta tare da kunna mata fanfo ta nuna mata komai sannan ta barta a ciki.
Ta ɗau tsawon mintuna goma a ciki kafin ta fito tana mai ya tsina fuska game da yarfar da hannu.
A hankali matar ta kama hannunta ta isa da ita izuwa kan sallayar da ta shimfiɗa mata.
"Dan Allah ki yi sallar, tunani ba zai amfanar dake komai ba."
Ba ta tanka mata ba ta tada iƙama kamar yadda itama ba ta sa ran jin amsa daga gare ta ba.
Ficewa ta yi daga ɗakin ta barta dan ta samu damar gabatar da ibadarta yadda ya ka mata.
Kifa kanta ta yi kan guiwoyinta biyu bayan ta idar da sallar tana mai kuma jin zuciyarta babu daɗi ga wani ɗaci wanda ya zarce na farasitamol da ya gauraye duk ilahirin bakinta.
Ta fi mintina uku a haka kafin ta zame jikinta a hankali kamar mara laka ta kwanta kan dardumar sai ka ce mage, wani sanyi na ratsa dukka ilahirin sassan jikinta fiye da sanyin ƙanƙara. Kalaman Mamanta suka kuma dawo mata sababbi dal cikin kwanyar kanta.
"Ki dai yi a hankali, ina ji ye miki gaba." Ta saka hannunta ta goge ruwan hawayen da suka kuma zubo mata a karo na ba adadi.
Sallama matar ta yi bayan ta ƙarasa shigowa ɗakin, hannunta ɗauke da ƙaramin faranti ɗauke da abinci. Ta isa gabanta gami da furta,
"Ta shi ki sakawa cikin ki wani abun."
Tana jinta amma sam ba za ta iya furta mata ko da ƙala ba, gaba ɗaya ji ta ke yi bakinta ya matanauyi sam maganar ba za ta iya fita ba.
"Ki ta shi ki sakawa cikin ki abinci." Ta kuma sake furta hakan a karo na biyu.
Kuma har a lokacin ba ta jin za ta iya yi mata magana.
"Dan Allah ki ajjiye duk wani tunani ki dawo cikin nutsuwarki, ki kuma daure ki ci abincin nan. Yau kwanan ki biyu ba ki ci komai ba sai ruwa da ki ke sha shi ma ba zai wuce sau biyu zuwa uku ba." Ta tsagaita da maganar tana mai kallon cikin idanta.
Runtse idanuwanta ta yi sosai ,a ranta tana mai jin damuwar da take ciki ba za ta taɓa bari ta iya cin komai ba.
"Ba na jin zan iya sakawa cikina komai a yanzu." Ta yi maganar kamar wacca a ka yiwa dole.
"Na haɗa ki da girman Allah ki ta shi badan ni ba ki ci abincin nan." Matar ta ce.
Ba dan ranta ya so ba ta miƙe zaune a hankali, sai dan dai kawai matsawar da matar da ta mata kuma ciki harda haɗata da girman zatin Allah da ta yi.
Loma ɗaya ta saka mata a baki ta ji ba za ta iya haɗiyewa ba , tari ne ya soma sarƙafeta ta soma yin ƙurin amai. ganin haka ya saka matar miƙewa ta fice daga ɗakin. Mintina uku ta dawo ɗauke da kofi na shayi mai kauri a hankali ta shiga ba ta a baki da kaɗan-kaɗan.Cikin ikon Allah ta sha fiye da rabi.Ta sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya mai ƙarfi. Kunnuwanta suka sake shiga yi mata amsa kuwwar kalmar da take sake sakata cikin matuƙar baƙin ciki, kalmar da take jin ƙyanƙyamin kanta a duk sanda aka yarfa mata ita.
"Mai baƙin jinin da ta rasa masoyi."
Tana jin zafin kalmar sosai a ranta, to baƙin jinin me kuma? Bayan ta san tunda take ba ta taɓa rasa masoya ba. I! mana ba ta taɓa rasawa ba tunda dai Mamantana santa ,kuma haka zalika ta taɓa tsayawa da wani a matsayin masoyinta. Amma mene ne dalilin da zai saka mutane jifanta da kalmar gami da liƙa mata wannan mummunar kalmar, kuma ba su tsaya a nan ba harda aro kalmar Shegantaka su jefa mata ita.
Me ya sa mutane ba sa gane cewa; komai na duniyar nan da duk abin da ya ke faruwa cikinta muƙaddari ne daga Lillahi wahadahu sarkin sarakuna? Me ya sa ba za su gane cewa ko wanne maƙasudin abu da lokacinsa? Haka zalika ko wanne ɗan adam da irin tasa ƙaddarar.
"Tunanin ne dai.?" Ta jiyo tashin sautin muryar matar na tambayarta.
Kallo ta bita da shi, dan ba ta jin za ta iya ba ta amsa. Ta zame jikinta a hankali ta kwanta kan daddumar .
Ganin hakan bai sa ta hanata ba, ta san kome za ta ce mata ba za ta kuma tankawa ba hasalima ba za ta samu kowacce irin amsa daga gareta ba balle kuma ta motsa gaɓoɓinta. kawai sai itama ta miƙe ta hau tattara kwanukan ta fice daga ɗakin ta barta dan ta kuma samun hutu.
Wani ɗaki ta shiga daban da wanda ta fito daga cikinsa. Kallon ɗakin take yi tana mai sake nazartarsa kamar yau ta soma ganinsa. Zama ta yi gefen gadon dake ɗakin tare da saka hannunta ɗaya saman kan kuncinta.
Daidai da shigowar wani kyakkyawan saurayi dogo, fari,mai yalwar suma, mai matsakaicin hanci da baki, da kyawawan idanuwansa masu shaf irin na ƙwai, mai shekara talatin da biyu. Ganinta zaune ta yi ta gumi da duka hannayenta ga kuma alamun bata ma san ya shigo ba ya saka shi furta,
"Aunty na meke faruwa ne?" Bai ba ta damar magana ba duk da cewa sai a lokacin ta dawo daga kogin tunanin da ta faɗa ya ɗora da faɗin,
" Kin san yawan ta gumi na haifar da hauhawar jini."
Ƴar ƙaramar dariya ta yi ,tana mai kallonsa.
" Da ɗina da kai tsantsan tsagwaran sharri, a ina aka faɗi hakan.?" Ta jefo masa ayar tambaya.
Shi ma murmusawar ya yi ka na ya ce,
" Ko dai ba a faɗa ba ni na faɗa, kuma dai tagumi babu kyau. Dan Allah ki daina ni ba na so na ganki kin yi wani jugum kamar marainiya."
Yaƙe ta yi wanda ya fi kuka ciwo.
"Ba na samun wata damar da zan iya tunano abubuwan da suka riga suka shuɗe min sai a irin wannan yanayin shiyasa ba zan iya dai nawa ba."
"Duk da haka dai Aunty ki ajjiye shi dan Allah, abin da ya jima da wuce ba zai taɓa dawo wa ba."
Ya ƙarasa faɗa yana mai zame mata hannun da har yanzu ba ta sauke su daga kan kuncin na ta ba. Ba ta ce masa komai ba sai ma miƙewa da ta yi tsaye.
"Ta farka kuwa.?" ya jefa mata tambaya.
"Ta ta shi ,harma ta samu ta ɗan sha shayi. Amma yanzu dai ta koma."
Ta ba shi amsar a gajerce.
"Shayi kuma Aunty? Mai ya sa ba ki ba ta abinci ba ?" Ya kuma jefo mata wata tambayar.
"To ni ma ba na ce ba, dan kuwa tabbas banso hakan ta kasance ba, amma ba ni da ikon da zan tursasa mata a kan hakan." Ta ce.
Gyaɗa kansa ya yi kamar ƙadangare. " Bari na ɗan leƙa na ga ni."
"A'a Musbahu, ka barta ta sake samun barcin." Ta katse hanzarinsa da sauri.
Bai mu sa mata ba, kawai sai ya saka kai ya fice daga ɗakin. Bin shi ta yi da kallo, ƙwaƙwalwartana tuna mata da wasu abubuwa, a kullum ta kalli fuskarsa sai ta ji zuciyartana bugawa da sauri da sauri ,tana kuma tuno mata da abubuwa ma su ɗumbin yawa.

Mai_ƙosai

*LOKACI NE*

Mai_Ƙosai

FCWA

Uku.

"Ya Ilahi"
Ta furta a hankali. Ficewa ta yi daga ɗakin ta kuma leƙawa ɗakin da take kwancan. Har a yanzu tana kwance tana barci cike da tausaya mata ta koma ɗakinta itama ta kwanta tare da lumshe idanuwanta, suka soma hasko mata abin da in ta tsinci kanta a irin yanayin ta ke ganowa.
Haɗaɗɗen Saurayi ne mai shekaru talatin da bakwai, fari dogo, mai siririn hanci, sai dara-daran idanuwa, da laɓɓa madaidaita. Tsaye ya ke sai faman zuba yalwataccen murmushi ya ke yi.
Daidai lokacin da wata yarinya ta iso gare shi duk da cewa tana da shekaru wanda za sukai Ashirin da takwas. Fuskarta ɗauke da kyakkyawan murmushi, cikin shagwaɓa ta ce,
"Yayana sannu da zuwa."
"Yawwa shaleleta, da har ina cewa bari na wuce tunda ba za a kula ni ba, kin san nifa har yanzu tsoron matana ke yi." Ya ƙarasa cikin sigar tsokana.
" A duk lokacin da ka ke irin wannan zancan sai na ji zuciyatana dakan gunba, idaniyata ta cika taf da ruwan hawaye, ka ji kuwa yadda ƙirjina ya ke bugawa dalilin fitar kalmomin." Ta ƙarasa kamar za ta yi kuka.
"Tuba na ke shalelena, ni na isa na saka gimbiyata ta rarradi, lallai yau kam sai na amshi tsattsauran hukunci." Ya faɗa ya na mai durƙusawa ƙasa.
Rufe idanuwanta ta yi da tafukan hannayenta biyu. " Ni ba ka yi min komai ba hasalima ni ce na yi maka, dan Allah ka ta shi dan kuwa ni ce na fi cancanta da a hukunta."
Cikin shauƙin so ya ce, "Ke kam kin cika wayo, shiyasa kullum na ke ƙara jin sanki cikin zuciyata."
Ta ɗan yi far da idanuwanta, "Ni kam kullum ƙara narkewa ka ke yi cikin rai na." Ta ce cikin dariya.
Dariya sosai ya yi har sai da ya gaji dan kansa ya tsagaita, ita kam tamkar ta sami majigi ta kafeshi da dara-daran manyan idanuwanta."
"An ya wannan son da ki ke masa ba zai ja maki wata illar ba Khausar.?"
Lokaci guda idanuwanta suka kuma hasko mata muƙabularta da ƙawarta da suke maƙotan tazara, kunnuwanta suka shiga tariyo mata sautukan zantawar ta su. Ita ce kaɗai wacca ta ke iya raɓarta ba tare da firgici da tsoro ba, itama kuma ta ke mu'amala da ita ba tare da ta yi mata ƙyanƙyami ba ko kallon wani abu daban. Saɓanin yadda sauran mutanen da suke kewaye da da su suke mata tsantsan-tsagawarar ƙyara.
"Ba na jin son da na kewa Abbas zai haifar min da da wata illa cikin zuciyata, shi ne mutumin da ya so ni a lokacin da kowa ya ke guduna ciki kuwa har da iyaye na da suka haifeni. Koma dai hakan ta faru ni a wajena shahadace ,kuma har abada ba zan taɓa rage wani kaso na daga cikin son shi da na ke yi ba."
Ta ba ta amsa daidai gwargwado.
"Ni kam ina jiye miki gaba ne, ka da ki sakarwa wani ragamar zuciyarki daga baya ya juya miki baya kwatan-kwacin abin da ya faru, daga ƙarshe ya zame miki baƙin ƙadangaren bakin tulu ya barki da tsantsar wahala, duk da cewa ina masa kyakkyawan zato."
"Dan Allah in ba za ki faɗi alheri ba to ki yi shiru." Ta faɗa ranta a matuƙar ɓace.
Ta dawo daga duniyar mafarkinta, tare da sauke ajjiyar zuciya da saka hannayenta saman ƙirjinta tana mai jin yadda ya ke harbawa fat-fat da sauri.
"Har a bada kai na daban ne masoyina."
Ta furta hakan cikin sanyayyiyar murya tana mai share hawayen da suka daɗe da yi mata shimfiɗa a kan fuskarta.

***
Dattijuwar mata ce ta fito daga ɗaki fuskarta babu walwala balle annuri a tattare da ita. Kai ka ce an mata albishir da saƙon mutuwa.Taɓarmar da ke hannunta ta shimfiɗa a tsakar gidan, ta kuma maida kanta cikin ɗakin. Mintina ƙalilan ta kuma fitowa ɗauke da maficin kaba a hannunta da kwanan sha mai ɗauke da zallan nono ,duk da iskar da ke yalwace a tsakar gidan amma hakan bai hanata samarwa da kanta iska daga jikin maficin ba.
Ba ta jima da zama ba wata mata ta shigo tare da kwaɗa sallama. Amsawa ta yi daga zaunen da take bata ko motsa ba, itama waje ta samu ta zauna ba tare da ta nemi izinin matar da ke zaune ba.
"Wai har yanzu shiru, sai ka ce an aiki shirwa ko?"
Kamar ba za ta tanka mata ba, can kuma ta ce.
"Duk yadda a ka yi ta yi nisan kiwo ne, domin kuwa na jima da sanin lallai jiran gawon shanu na ke yi."
"A'a Asabe ka da ki ce haka, ai ba a cire rai ga rahmar ubangiji, Allah yana tare damu, kuma in sha Allahu komai zai wuce kamar yadda walƙiya ta ke giftawa." Ta faɗa cikin san kwantar mata da hankali.
"Kayya dai da kamar wuya, wai ɓarawo a hannun mata." Asabe ta ce.
"To Allah ya kyauta dai, ni bari in wuce, daman na zo ne na ji ko kin sami wani labari ne a kanta.?" Ta ida zancan tana mai miƙewa tsaye.
"Sai anjima Asabe, Allah ya kyauta lamarin." ta sake furtawa.
"A sauka lafiya, na gode." Asabe ta yi furucin. Har lokacin ba ta motsa daga in da take a zaunen ba.

****
Kakarin aman da ta jiyo daga ɗakin ne ya dawo da ita daga nahiyar tunanin da ta jima da lulawa.Cikin sauri ta iske ɗakin ta isa gareta tare da faɗin,
"Lafiya? Me ya faru.?"
Ba ta iya bata amsa ba illa ma ci gaba da aman da take yi. A daidai lokacin ne Musbahu ya yiwa gidan dirar mikiya, ganin abin da ya ke wakana ya sa shi saurin faɗin,
"Aunty mai zai hana mu je asibiti, na ga jikin nata kamar ba sauƙi."
Ba tare da ta kalleshi ba ta ce,
"Ina ga abin da za ayi ke nan, dan ni ma naga alamun haka, ma za jeka fito da mota mu wuce."
Juyawa ya yi ba tare da ya ba ta amsa ba ya wuce aikata abin da ta umarce shi.
Ka mata ta yi da nufin su wuce.
"A'a Aunty ki barni a hakana domin kuwa a yanzu ba abin da na fi ƙauna irin na ga na bar duniyar dan Allah."
Ta furta hakan cikin galabaita tare da ƙoƙarin komawa ta zauna.
"Ba ki da ikon yankewa kan ki wani hukunci cikin ƙaddarar da Allah ya iya kanta miki, ina so ki sa ni duk wani ɗan Adam da irin ta sa gwagwarmayar, ban san me ya faru da ke ba amma sai na ke jin matsalarki mai sauƙi ce a kan ta wasu. Ki yi haƙuri muje asibitin koma mene ne daga baya kya yi shi in dai har zai samawa zuciyarki da ruhinki salama."

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

1 Comments On LOKACI NE
avatar
khamilu

1 year ago

Reply

Mashallah

Please Login or Register in order to submit comment