Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

MAZAN JIYA
littafi na biyu 2
Mujalladi na biyu 2
littafin Abdulaziz Sani Madakin Gini
Typing by Shuraihu Usman.

Zamu tashi daga inda muka tsaya a Mujalladi na ɗaya 1, idan ba a manta ba, amma kafinnan a sani wannan typing mallakin shafin Taskar Novels ne kadai ba'a yarda wasu shafuka su dau typing ɗinnan ba ta kowanne hali kuwa, idan kuwa suka dauka zasu hanyo DMCA ya hau kan shafinsu wanda hakan zai yi sanadiyar lalata shafin nasu ya taba musu SEO, DOMAIN da HOSTING. Saboda tuni munyi registan content na shafinmu da hukumar DMCA, Digital Millennium Copyright Act amma kuna iya karantawa anan kyauta ko ku downloading duka daga shafinmu idan kunyi subscription na shafin Taskar Novels.

kike ciki na sani kuma na zo ne domin na taimakeki na biya miki bukatarki".


Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Zarifa kuma ta cika da dumbin farin ciki. Ba tareda fargabar komai ba Zarifa ta zauna daf da boka Ardusa ta kura masa idanu tana mai sauraron abinda zai fada ma ta.

Boka Ardusa yai murmushi gami da gyaran murya sannan ya ce, "Ya ke ma'abociyar kyawu,tauraruwar kyawawa, ina son ki sani cewa na san baki da wani buri wanda ya fi ki daukaka a duniya fiye da dukkan sauran mata, kuma kina son kimallaki dukiyar da babu mai kamarta.

Tabbas idan kika yi abubuwan da zan umarceki sai bukatarki tabiya.


Yanzu nazo gareki a sirrance lallai ki rike sirrin kada ki kuskura ki gayawa wani wannan sirri na zuwana wajenki koda bukatarki ta biyane idan kuwa kika fadi sai dan da za ki haifa yazamo sanadin ajalinki".


Koda jin haka sai Zarifa ta ja dogon numfashi ta ce,"Ai kuwa ba zan taba gayawa wani wannan sirri ba".


Boka Ardusa ya ce,"Na san kin yi mamakin yadda aka yi na kawo kaina wajenki, to amma ba abin mamaki bane idan kika yi la'akari da matsayina a yanzu na bokan da yafi dukkan bokayen duniyar nan karfin sihiri, amma kuma ina



daga cikin talakawan bokayen. Yau shekarata ashirin da biyar ina bauta a karkashin wannan masarauta ta birnin Kisra kuma akwai alkawari mai nauyi tsakanina da dangin su Sarki Kusaidu cewar ba zan daina bauta a garesu ba sai bayan shekara hamsin, kin ga ke nan a gaba akwai shekaru ashirin da biyar.

A ka'idar wannan alkawari ban isa na yiwa wani aiki ba face su idankuwa na kuskura na yiwa wani aiki mutuwa zan yi domin an yi alkawarin ne a cikin sihirin tsafi bisa amincewar mahaifina da mahaifin sarki Kusaidu.

Yanzu na zo wajenki ba aiki zan yi miki ba kawai zan gaya miki abubuwan da za ki yi ne a kanki domin bukatarki ta biya, ladana a wajenki abubiyu ne rak.


Abu na farko,bayan bukatarki ta biya za kibani kanki na sanki 'ya mace domin a rayuwata nayi alkawarin ba zan ta6a kwanciya da wata 'yamace ba sai wadda take da tsananin kyawu nagaban kwatance, kuma wadda ta kasance 'yar attajirin da babu kamarsa a wannan nahiya gabadaya,gashi kuma na yi dace na sameki.


Ladana na biyu shi ne, za ki raba dukiyarki gida biyu ki bani rabi bayan mutuwar 'yar uwarki Marifa domin a sannan ne za a baki gaba dayan dukiyar da mahaifinki ya bari.
Idan kin amince da wannan sharadi yanzu
take zan gaya miki abubuwan da za ki yi ki samu cikar burinki.


Sa'adda boka Ardusa ya zo nan a zancensa sai hankalin Zarifa ya dugunzuma ainun ta rasa abin da ke ma ta dadi a duniya ta mike tsaye dagakan gadonta ta kama kaikawo da tunani bisa hukuncin da ya kamata ta yanke akan ta yarda dashi.


Abin da ya fara fado ma ta a rai shi ne ya za ayi ta bayar da wannan kyakkyawan jiki na ta ga boka Ardusa tsohon da ya kai sa'an ubanta alhalin tana takama da tsananin kyawun da babu mai tabata face babban Basarake ko mashahurin attajiri.


Abu na biyu da ya fado ma ta a rai shi ne, yaza a yi ta raba wannan dukiya ta ta mai tsananin yawa ta baiwa wani rabi, wacce ta ishi mutum rayuwa a duniya koda zai shekara dubu

Lokacin da boka Ardusa ya ga Zarifa ta shiga halin rudewa da wasi-wasi sai ya mike tsaye yadubeta ya ce, "Wai shin kin manta ne da abin da bokaye da dama suka gaya miki cewa babu mai iya biya miki bukatarki face ni.

Idan zuciyarki bata gamsu da al'amarina ba shi ke nan ni zan yi tafiyata na barki da wayonki".

Koda jin haka sai Zarifa ta yi sauri ta shagaban boka Ardusa ta ce, "Ya kai wannan sakin bokaye ka yi sani cewa jikina da dukiyata ba abakin komai suke ba muddin zan sami biyan bukata Lallai na amince da dukka wanann sharadi naka don haka kayi sauri ka sanar da ni abubuwanda zan yi domin bukata ta biya".


Koda jin haka sai boka Ardusa ya yi murmushi ya ce, "Kafin nayi miki bayanin abubuwan da za ki yi kuma kika yi su kika sami nasara sannan daga baya kika yi min butulci, ma'ana kika ki cika mini alkawari, lallai zaki mutu a cikin kwanaki talatin cicif bayan yin aurenki.

Haka kuma dole ne ki ci gaba da bani kanki a duk sa'adda na bukace ki, idan kuwa kikaki asirinki zai tonu kuma ki rasa abin da kika samu a rayuwa. Yanzu sai ki saurareni da kyau domin kiji duk abubuwan da zan gaya miki wadanda za kiyi su bukatarki ta biya.

Abu na farko da za ki yi shi ne, dole ne ki fada mini tambayoyi guda uku wadanda mahaifinki ya fada miki ki tambayi masu neman aurenki gami da amsoshinsu domin nasanar da sarki Kusaidu su ya sami damar aurenki.Kin ga idan kika auri sarki Kusaidu za ki sami damar da babu wata mace da ta samu a duniya domin shi ne sarkin da a tarihi sarakan duniya babu masarautar da ta fi tashi tsohon tarihi da daukaka da karfin mulki.

Duk sarkin da ya yi zamaninsa har bayan shudewarsa ba a mancewada shi da matansa domin har a fadar sarkin Aljanun duniya ana rubuta tarihinsu a ajiye, atakaice dai sai sunanki ya bazu ko ina a duniya kinga ke nan ko ta nan kin yiwa 'yar uwarki Marifa fintinkau.

Abu na biyu da za ki yi shi ne, ki samo kasko ki yi fitsari a cikinsa sannan ki diga digon jininki a ciki, sai ki kira sunan 'yar uwarki sau uku ki tofa a ciki sannan ki wanke idanunki da shi amma a ranar da za a yi gasar neman aurenku. Dazarar 'yar uwarki Marifa ta hada idanu da ke awannan rana ba za ta yi wata goma sha uku ba aduniya za ta mutu, idan kuwa baki hada idanu daita ba to kece za ki mutu a cikin wata goma sha ukun.


Wannan shi ne iyakar abin da za ki yi. dukkan burinki ya cika.Da wannan furuci nake miki sallama sai mun hadu a ranar gasa.”


Kafin Zarifa ta bude baki ta ce wani abu tuni boka Ardusa ya yi girgiza ya bace 6at. Al'amarinda ya matukar baiwa Zarifa mamaki ke anan domin ya tafi ba tare da ta fada masa wannan tambayoyi uku ba, wadanda zai sanar da sarki Kusaidu gamida amsoshinsu.

Zarifa ta koma kan gadonta zuciyarta cike da sake-sake da tunani bisa wannan abu da ya faru tsakaninta da boka Ardusa. Ba wani abu take tunani da wasi-wasi ba face hadarin da ke cikin aikin da boka Ardusa ya sa ta.

Koda takwanta akan gadonta domin ta mike kafafunta tayibarci sai kawai tayi arba da wata takarda akangadon. Al'amarin da ya matukar ba ta tsoro damamaki ke nan domin a saninta babu wata takarda& cikin turakar ta ta koda guda daya kuma babu yadda za a yi a shigo da wani abu ba tare da saninta ba.Hannun Zarifa na karkarwa ta sa hannayenta biyu ta dauki takardar wacce ta kasance fara kal babu zanen komai a kanta.Koda ta dubi takardar sai ga hoton fuskar boka Ardusa ta baiyana akai yana mai murmushi a gareta sannan ya ce,"Maza kifadi wadannan tambayoyi uku gami da amsoshinsu."
Koda jin haka sai Zarifa ta karanto tambayoyin gami da amsoshinsu.

Bisa mamaki sai Zarifa ta ga an rubuta duk abin da ta fada akan wannan takarda ba tare da ta ga mai rubutun ba ko alkalamin da ke yin rubutun.

Nan take takardar ta6ace 6at tamkar bata taba wanzuwa ba a wajen.

Koda ganin haka sai Zarifa tayi murmushi sannanta kwanta. Kwanciyarta ke da wuya sai barci yasace ta,bata sani ba.


Abin da bata sani ba shi ne, kafin boka Ardusa ya bace daga cikin turakar ya busa mata hodar banju ta shaka, shi ya sa nan da nan barci yakamata in ba don haka be da ba za ta iya barcin basaboda tunanin gagarumin aikin da ke gabanta dakuma sharadin da ke tsakaninta da boka Ardusa.

DA RANAR gasa tazo sai fadar birnin Kisra ta cika ta batse da mutane duk inda mutum ya duba gabas da yamma, kudu da arewa sai dai ya ga kawunan bil'adama fululu babu masakar tsinke.


A tsakiyar fadar ne jaruman gasa suka taru wadanda gaba dayansu sun kasance sarakai da attajirai da ma manyan bokaye daga kowanne bangare a kasashen da ke nahiyar.


Sarki Kusaidu da sarkin Darul Mahabul ne suka shigo a karshe,bokayensu na take musu baya.

Maimakon su sarki Kusaidu su tafi izuwa inda karagar mulki take sai suma suka shiga tsakiyar fadar inda sauran jaruman gasar suke.


Saboda shakkar wanman gasa gaba dayan jaruman da suka tsaya a tsakiyar fadar su goma ne kacal su sarki Kusaidu ne suka zamo cikon na shabiyun. Ba wani abu bane ya janyo hakan ba face sauran jama'ar da suke son su shiga gasar wadanda adadinsu ya fi dubu dari bokayensu sun tabbatarmusu da cewa 6ata lokacinsu za su yi ba za su iyacin nasara ba.


Shi kuwa Sarkin Darul Mahabul ana i gobe za ayi gasar ne ya sami f
kwarin guiwar fitow awanann gasar bayan boka Sulbaini da boka Zaharu sun hakura da kiyayyar da ke tsakaninsu sun hada karfi da karfe sun binciki amsar tambayar da za ayi masa ya iya amsawa. Kuma a binciken da suka yi sai suka kasa gano tambayoyin da Zarifa za ta yi sai na Marifa suka gani. Koda suka ga tambayoyin sai suka kasa fahimtar amsoshinsu har sai da suka tara gaba dayan hadiman aljanunsu suka bazamasu izuwa cikin duniya wajen tsofafin mutane da aljanu masana ilimin tarihi. Da Kyar da sidin goshi aljanun suka samo amsar tarabayoyi biyu. Amsar tambaya ta uku kuwa ba a sameta ba sai a lokacim da suka fito filin gasar sannan wani hadimin boka Sulbaimi yazo da ita. Ai kuwa cikin gaggawa ya radawa sarki amsar a kunnensa.Koda jin amsar sai sarki ya cika da farin ciki kuma ya sami nutsuwar shigar gasar.
Jim kadan de shigar su sarki Kusaidu cikin jaruman gasa sai ga Zarifa da Marifa suka shigo cikin filin fadar.Kowacce daga cikinsu ta caba ado na ban mamaki kuma na kure adaka,kuyanginta na biye da ita gaba da baya suna watsa furanni masu kamshi akan hanyar takawarta.
Kamshin turaren da su Zarifa suka sanya a jikinsu ne ya fara dukan hancin kowa a fadar.Koda jama'a suka ji wannan kamshi sai suka waigo suka dubi masu shigowar,wohoho! Nan fa maza suka rude suka dimauce, wasu suka kama
dalalar da yawu, basu sani ba wasu kuwa sai suka kama yanke jiki suna faduwa kasa sumammu saboda sun ga abin da kwakwalwarsu ba za ta iya dauka ba.Masu Karfin hali ne suka rinka kuka suna zubar de hawaye saboda takaici bisa sanin cewa ba za su taba mallakar wadannan kyawawan 'yan mata biyu.
Tun kafn su Zarifa su shigo cikin fadar sai Zarifa ta ga Marifa ta sha lullu6i kuma ta sunku da kanta kas idanunta basa kallon komai face kasa inda take takawa. Alamarin da ya dugunzuma hankalin Zarifa ke nan domin ta san cewa idan har basu hada ido ba ita da Marifa kashinta ya bushe kuma ba za ta taba cika burinta ba. Nan fa Zarifa ta fara tunanin abin de za ta yi domin ta tabbatar cewa ta hada idanu da Marifa. Inda matsalar take shi. ne akwai tazara tsakaninta da Marifa kuma akwai kuyangin Marifa a tsakaninsu. Koda Zarifa ta ga fuskar Marifa a rufe take sai itama ta janyo mayafinta tayi lullu6i kuma ta sunkui da kanta kas amma zuciyarta sai bugawa take da karfi cikin tsananin tsoro.
Zarifa da Marifa suka ci gaba da tafiya suka nufi inda aka tanadar musu su zauna amma Zarifa na daga kai tana satar kallon Marifa ko za ta ga itama ta dago kai domin su hada idanu, amma bata dago din ba. Zarifa na cikin wannan satar kallo ne
ta hada ido da boka Ardusa,nan take ya yi ma ta nuni da idanunsa cewa lallai tayi duk iyakar kokarinta ta hada idanu da Marifa kafin su isa inda kujerun zamansu suke. Koda ganin wannan inkiya sai hankalin Zarifa ya kara dugunzuma ta shiga tunanin abin da za ta yi ya zamana cewa lallai ta hada idanu da Marifa kafin su kai mazauninsu. Sai da ya rage saura baifi taku goma ba su isa mazaunin nasu sannan dabara ta fado ma ta. Kawai sai tayi kamar tayi tuntu6e, cikin shammace ta tafi taga-taga ta fadi a gaban Marifa.Cikin mamaki da kaduwa Marifa ta sunkuya ta dubi Zarifa suka hada idanu. Suna hada idon sai Marifa taji wani abu ya soketa a kirji tamker an tsira ma ta mashi. Saura kiris tayi ihu kuma ta fadi kasa, amma sai ta daure ta mike ta ci gaba da tafiya. A sannan ne ta ga Zarifa ta dubeta tayi ma ta wani irin murmushi na mugunta. Nan take Marifa ta tsergu da cewa tabbas 'yar uwarta Zarifa tayi ma ta wani mugun asirin.
Zarifa da Marifa sun dade suna yiwa junansu mugun jifa na sihiri amma sihirin yaki ya yi tasiri akan kowannensu kuma duk wajen bokan da suka je yana gaya musu cewa sai dai su yi hakuri babu wani sihiri da zai iya huda jikinsu a yanzu,domin mahaifinsu ya yi musu tsari na musamman babu wanda zai iya karya wannan sihirin face bokan da
ya yishi kuma ba wani bane face boka Ardusa.
Cikin tashin hankali da mamaki Marifa ta karasa zuwa kan kujerar da aka tanadar ma ta ta zauna,itama Zarifa sai taje ta zauna akan ta ta kujerar fuskarta cike da murmushi,zuciyarta ta cika makil da farin ciki. Zamansu ke da wuya sai Alkalan gasar suka fara zartar da aikinsu aka ware jaruman da ke son Marifa da wadanda ke son Zarifa.
A zaton sarki Kusaidu Sarkin Darul Mahabul zai shiga cikin sahun masu son Zarifa amma sai ya ga ya shiga cikin sahun masu son Marifa. Nan take Sarki Kusaidu ya hau kan layin masu son Zarife ya tsaya daga Kanhe. Masu son Zarifa mutum bakwai ne, masu son Marifa kuwa mutun uku ne,sarkin Darul Mahabul ya zamo na hudunsu. Saboda haka sarki Kusaidu ne na takwas a cikin sahun masu son Zarifa. Be wani abu bane ya sa masoyan Zarifa suka hi yawa ba face its Zurifa ta baiyana fuskarta an gani tun kafin a fara gasar don haka jaruman gasar sun dauka tafi 'yar uwarta kyau sai da Marifa ta yaye lullubinta gaba daya aka ga kyawunta de kyawun surar jikinta wanda har yafi na Zarifa sannan aka dimauce. Shi kuwa sarki Kusaidu ya zabi Zarifa ne saboda boka Ardusa ya gaya masa cewa na ta tambayoyin kadai ya sani amma bai san na Marifa ba.Wani abin mamaki shi
ne duk da cewa Marifa tafi Zarifa kyau sai sarki Kusaidu yaji yafi son Zarifa kuma nan take ya kamu da tsananin begenta a zuciyarsa.
Ba tare da 6ata lokaci ba Alkalan gasa suka umarci Zarifa da ta mike tsaye ta karanto tambayoyinta guda uku ga jaruman gasarta mutum takwas bisa sharadin cewa duk wanda ya amsa tambayar dai-dai shi ne zai zamo mijin da za ta aura.
Cikin mumushi gami da takama Zarifa ta mike tsaye ta fuskanci miliyoyin jama'ar da ke cikin fadar a lokacin da aka yi tsit! Tamkar mutuwa ta gifta. Zarifa ta bude baki cikin muryarta mai zaki tamkar sarewa ta ce tambayoyina gareku masoyana su ne kamar haka.
Tambaya ta farko, a duniya wane abu ne mafi tsananin karfi, karfin da yafi na radadiin mutuwa ciwo kuma yafi karfin wadatacciyar lafiya dadi a zuciyar bil'adama da aljanu?
Tambaya ta biyu ita ce, "Wacce halittace me rai tana ci kuma tana sha amma bata kashi da fitsari?.
Tambaya ta uku ita ce,"Wane abu ne wanda idan ya baiyana yana firgita mutane da aljanu a duk inda suke, idan (kuma kishiyarsa ya baiyana sai su sami nutsuwa da kwanciyar hankali?"
Sa'adda Zarifa ta gama fadin wadannan. tambayoyi guda uku sai ta zauna akan kujerarta takasa kunne tana sauraron amsae da jarumin farkozai bayar.Gaba dayan fadar sai ta sake yin tsit! Mutane suka shiga zancen zuci suna maimaita tambayoyin uku a cikin zukatansu suna kokarin amsawa. Nan take jarumin farko ya mike tsaye yace,"Amsar tambaya ta farko ita ce,soyayya,domin karfin so a cikin zuciya yafi komai tunda mutum ko aljan zai iya sallama rayuwarsa don yamallaki masoyinsa haka kuma idan mutum yamallaki masoyinsa yana jin tsananin farin ciki azuciyarsa fiye da a bashi komai na rayuwa.

Amsar tambaya ta biyu ita ce babu wata halitta wacce tana ci kuma tana sha amma bata fitsari da kashi face shuka, domin taki ne abincinta, kuma ana zuba ma ta ruwa ta tsotse.Har abada shuka ba ta fitar da takin da ta tsotse daga jikinta kuma ba ta fitar da ruwan da ta tsotse a matsayin bashi da amfani a jikinta.
Game da tambaya ta uku kuwa babu abin dake firgita mutane da aljanu idan ya baiyana face yaki, kishiyarsa kuwa shi ne zaman lafiya".
Ya yin da wannan jarumi na farko yazo nan ajawabinsa sai Zarifa tayi murmushi ta ce,"Ya kai wannan masoyi nawa hakika kayi matukar kokari domin ka amsa tambaya ta farko da ta biyu dai-dai amma tambaya ta uku ba daidai bace don haka sai

ka koma gefe daya ka baiwa wanda ke bayanka wuri ya jarraba sa'arsa ko zai iya amsa tambaya ta ukun".
Koda jin haka sai wannan jarumi ya kamu da tsananin bakin ciki, nan take zuciyarsa ta buga ya Sulale Kasa matacce. Cikin hanzari dakaru suke ruga suka dauke gawarsa aka yi wajen fadar da shi.

Jarumi na biyu ya matso gaba a lokacin da gaba dayan jikinsa ya kama karkarwa tamkar an tsamoshi a cikin ruwan Kankara a lokacin da ake hunturun sanyi. Jarumin ya yi shiru yana tunani da nazari a cikin Kwakwalwarsa ya tuna irin nisan tafiyar da ya sha daga garinsu zuwa wannan birni na Kisra da kuma ya tuno da miliyoyin darhaman da ya kashe kafin ya sami damar shiga wannan gasa.

Jarumin ya dada tunawa cewa shi fa dan sarkin garinsu ne kuma shi kadai ne da namiji a wajen ubansa mai gadon sarauta. Da ya tabbatar da cewa bai san amsar wannan tambaya ta ukun ba, sai ya koma gefe daya yana mai nuna alamar cewa ya gaza.

Nan take fadar ta rude da ihu har wasu ma na jifansa suna cewa ya yi abin kunya.
Sai da Dakaru suka yi tsawa sannan mutane suka daina jifan da ihun, sannan jaruman gasar suka ci gaba da amsa tambaya ta uku. Har aka zo kan jarumi na bakwai ba a sami wanda ya amsa
dai-dai ba.
Koda aka zo kan Sarki Küsäidu säi fadar ta sake rudewa da shewa da tafi gami da jinjina. Maroka suka kama yiwa sarki Kusaidu kirari,makada kuwa suka kama buga ganguna da tambura. Sai da Sarki yà tsaya a inda zai amsa tumbayar sannan fadar tayi tsit ya zamana ba a jin komai face numfashin jama'a. A wannan lokaci Zarifa ta murtuke fuskarta tana kallon sarki Küsäidu kuma ta kura masa idanu. Dama haka ta rinka yi duk sa'adda masu gasar ke amsa tambayoyin sai idan ta ga mutum ya amsa dai-dai sannan tayi murmushi tayi bayanin ko ya yi dai-dai.
Sarki Kusaidu ya yi gyaran murya sannan ya yi murmushi ya ce, "Amsar tambayarki ta uku ita ce, "Haske da duhu ba wai ya ki da zaman lafiya ba. Dalili kuwa shi ne, komai jarumtakar mutum ko aljan idan ya tsinci kansa a cikin matsanaicin duhu wanda baya iya ganin komai dole ne hankalinsa ya dugunzuma ya firgice domin bai san abin da zai faru gareshi ba. Haka kuma idan haske ya baiyana gareshi ya sami nutsuwa da kwanciyar hankali tun da zai iya ganin kowacce irin masifa da za ta tunkaroshi kuma zai yi tunanin hanyar da zai bullowa masifar ya iya tararta."
Koda sarki Kusaidu yazo nan a zancensa sai fuskar Zarifo ya fadada da murmaushi ta ce,"Tabbas kai ne mijina domin ka amsa wannan tamabaya dai-dai, haske da duhu su ne amsar tamabayata ba yaki da zaman lafiya ba. Dalili kuwa shi ne, yaki ba kowa ne ke tsoronsa ba don jarumin da ya yarda da kansa jarumtakarsa da Karfin sihirinsa baya tsoron kowanne irin yaki komai tsananinsa.Haka kuma akwai mutane da aljanu wadande suka tsani zaman lafiya ko yaushe ma sun fi so su ga ana cikin tashin hankali, da kansu ma suke kiran masifu da bala'in".

Zarifa na gama wannan jawabi sai fadar ta rude da shewa da tafi gami da bushe-bushe da kade-kade. Bayan 'yan dakiku sai aka ladaftar da jama'a suka yi shiru. Alkalan gasa suka tabbatar da cewa lallai sarki Kusaidu ne ya sami nasarar wannan gasa cikin masu son Zarifa da aure yanzu kuma za

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment