Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ga halin da Inmal yake ciki sai ya dubi Dakarun aljanunsa ya daka musu tsawa ya ce, "Me kuke jira ne,maza ku kaiwa Inmal dauki..
Nan take wadansu aljanu guda biyu suka kaiwa Inmal dauki suka cafoshi tare da keken dokin suka yi saman ramin, sannan suka kawosu gaban sarki Maharaz suka saukesu a hankali.
Kamar hadin baki sai sarki Maharaz da Hibru suka risina suka yi sujjada ga jarumi Inmal. Koda ganin haka sai gaba dayan dakarun tawagar ma suka yi jinjina a gareshi.
Ita kuwa gimbiva. Mulaifa tana fitowa
daga cikin keken dokin sai ta rungume inmal ta fashe da kukan farin ciki. Al'amarin da ya sa gaba dayan jama'ar da kè wajen suka hau rafka tafi. Dajin gaba daya ya cika da tafin yana amsa kuwa.
Bayan Mulaifa ta janye jikinta daga cikin na Inmal ta koma gefe daya ta tsaya sai sarki Maharaz ya zo gaban Inmal ya tsaya yana murmushi ya dafa kafadarsa ya ce, "Ya kai jarumin jarumai, kuma gwarzon zamani,hakika a yau na tsinke da al'amarinka bisa ganin wannan gagarumar bajinta da ka yi, in ba don kai ba, bamu san yadda zamu yi da wannan katon dodo ba, domin koda zamu kashe shi sai da yawanmu sun hallaka. Bugu da kari gashi a gaban idanuna ka ceci rayuwar 'yata a lokacin da babu abin da zan iya yi ma ta tun da ina can wani wuri dabam. Tsananin karfin gudunka da karfin jarumtakarka ne ya sa ka sami nasarar ceto rayuwarta. Ya kai Inmal nayi maka alkawari lallai zan yi maka sakaiya da lada irin wanda ban taba baiwa wani ba".
Koda jin haka sai Inmal yai murmushi kuma ya yi godiya.
Nan dai sarki ya bada umarni aka shiga debo mutane da aljanu wadanda suka mutu da wadanda suka raunana aka binne na binnewa,wadanda za a yiwa magani aka yi musu magani.
Sai da aka kwana a wajen sanann da sassafe aka tashi aka kimtsa aka ci gaba da tafiya.
Wannan karon sai su sarki Maharaz suka ga tafiyar tasu ta kara sauri ainun, domin dawakansu da rakumansu suna yin wani irin azababben gudu na ban mamaki.
Suna gifta dazuzzuka tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya. A cikin kwanaki goma sha bakwai suka hango tekun bahar Sufiya daga can nesa.
Tun daga nesan suka ga wadansu Kwari kanana bakake sun cika sararin samaniya da kan tekun tamkar babu komai a wajen sai su.
Koda Inmal ya hango wadannan Kwari sai ya cika da mamaki ya dubi Hibru ya ce, "Ya kai Abbana wai shin wadancan tsuntsayen wadanne iri ne? Belbelu ne ko Tsattsewala?".
Kafin Hibru ya budi baki ya ce wani abu sai sarki Maharaz ya tari numfashinsa ya dubi
Inmal ya ce, "Ai wadanda abubuwan da kake hangowa sun cika sama da kasa ba tsuntsaye bane, rudunar abokan gabarmu ce, yanzu haka suna kan laluben inda takobin SAIFUL LUJARA take ne a cikin kogin".
Koda jin wannan batu sai Inmal ya cika da tsananin mamaki kuma yaji tsoro ya darsu a cikin zuciyarsa bisa ganin yawan abokan gabar wanda idan bai ninka tasu rundunar sau uku ba, zai gaza sau biyu ba.
Cikin matukar damuwa Inmal ya ce, "To yanzu ta ya ya muma zamu iya laluben takobin a cikin wannan teku?"
Sarki Maharaz ya ce, "Ta hanyar afkawa abokan gabar tamu da yaki, idan muka kawar da su sai mu shiga laluben takobin a cikin kwanciyar hankali".
Koda gama fadin haka sai sarki Maharaz ya yi shiru bai kara cewa komai ba, a sannan ne suka fara shaida dandazon abokan gabar tasu suma su sarki Dujalu suka ankara da tasu tahowar.
Wohoho! Bala'i ba a sa masa rana. Idan masife ta durfafo, to fe babu abin da ya isa ya tsaide ita face yar uwarta masifa.
Koda sarki Dujalu ya dago kai ya hango su sarki Maharaz sai ya kwarara uban ihu ya dakawa dakarunsa tsawa yuna mai basu umarnin su tafi su tari abokan gaba tun gabannin su Karaso bakin tekum.
Da jin wannan umarni sai dakarun aljanu suka bude fuka-fukansu guka nufi dandazon su Maharaz suna mugun ihu rike da muggan makamai. Ihu nc wanda ka iya sabautar da bil'adama su zauce domin gaba dayan tsuntsayen da ke wajen ma wadanda ke shawagi a sama sai suku kama fadowa kasa matattu. Halittun da ke cikin ruwa kuwa sai gani aka yi gawarwakinsu na tasowa sama saboda masifar wennan inu na aljanu.



Su kansu jama'ar sarki Maharaz in ba don shi saki Maharaz din ya taresu da Karfin sihirinsa ba da nan take gaba dayansu za su kurmance ko su haukace ko kuma duk su zube kasa matattu.


Lokacin da sarki Maharaz ya ga dakarun aljanu na sarki Dujalu sun durfafo inda suke sai shima ya baiwa nasa dakarun aljanun umamin su taresu. Ai kuwa suma sai suka yi sama suka ruga kansu tamkar an cilla kibiyoyi.
Kafin kiftawar ido rundunar biyu sun hade a sararin samaniya sun kacame da fitinannen yaki wanda ya fi gaban mai tunani ya tunano bare mai misali ya misalta. Nan fa suma dakarum biladama da ke kasa na kowanne 6angare suka falfalo da matsannicin gudu ana kokarin a hadu.
Kaico! Inda ace mutum na nan a lokacin da wadannen runduna biyu ta yunkura za a hadu ya ga irin tsanonin yawansu sai ya yì tsammemin cewa gaba dayan mutanen duniya ne za su hade da gaba dayan daboobin dunya.Ai kuwa bangare biyun na haduwa a tsakiya aka ruguntsue da azababban yaki mai dugunzumoa hankali da tafasa kwakwalwa.


Saboda jijjigar da kasa tayi a wannán ràna sai da gaba dayan tekunan duniya suka hausine guka kana ambahiyar ruwa saboda tekun bahar Sufiya ne no babbar cibiya na dukkanin tekunan duniya.
Wohohol A wannan rana an yi gumurzu, dauki ba dadi, artabu, turnuku, ruguntsuni da fafatawa irin wacce ba a taba yin kamanta ba a duniye, kuma ba za a taba yi ba.
Sai da aka kwana aka yini ana ragargazar
mazajen aljanu da na biladama aka rinka asarar rayuka amma komai kwarin idon mutum da iya kallon Kurillarsa bai isa ya iya tantance 6angaren da ke samun nasara ba.
A duk sa'adda sarki Dujalu ya durfafi wurin sai dai ka ga fili, duk inda ya sa gabansa sai ka ga maza na zubcwa tamkar guguwar annoba ce ta fado daga sama. Haka ma a 6angaren su sarki Maharaz duk inda sadauki Inmal ya durfafa sai dai ga yana banke mutane da kirjinsa, hannaycnsa da kafafunsa suna zubewa kasa tamkar ana sassabe a gona,an rasa wanda zai iya tsayar da shi.


Sarki Maharaz kuwa yana amfani da karfin sihirinsa ne kawai domin duk inda yai numi da sandarsa ta tsafi sai dai ka ga kawunan bil'adama na gutsurewa suna faduwa kasa.Sadauki Hibri ma ba a barshi a baya ba domin shima ragargazar maza yake yana ta yin ta'adi. A bangaren serki Dujalu ma akwai wadansu zakwakuran mayakansa guda biyu wadanda ake kira Matinu da Ratiju wadanda summa sun addabi jama'ar sarki Maharaz, don duk inda suka sa gabansu sai dai kaga maza na ratattakewa.
Lokacin da Mutinu da Ratiju suka hango irin mummunar barnar da sarki Maharaz da Hibru ke yiwa jama'arsu sai suka yi KUKAN KURA suka ruga garesu aka ruguntsume da wani masifaffen yakin. Matinu ya tari sarki Maharaz shi kuwa Ratiju sai ya tari Hibru.Wani abin mamaki shi ne Matinu yana takama da a
karfin tsafi ne zalla ba wai jaruntaka ba shi kuwa Ratiju tsagwaron jarumtaka ce da shi kawai sai gashi duk su biyun sun tari dai-dai da su don haka sai fadan nasu ya zama abin sha'awa kuma abin tsoro domin komai zai iya faruwa babu wanda yake da tabbacin samun nasara akan abokim gwaminsa saboda karfi yazo daya.
Lokacin da sarki Maharaz ya ga karfin sihirinsa ya zo dai-dai da na Matinu sai ya cika da tsananin mamaki domin shi a zatonsa babu mai iya karawa da shi a fagen yaki face sarki Dujalu amma sai gashi daya daga cikiin yaran Dujalu ya bashi mamaki.
Abin da sarki Maharez bai sani ba shi ne,Sarki Dujalu ya boiwa Matinu gabe dayan Karfin sihirinsa ne yanzu yana wannan yaki ne da zallar karfin damtsensa.



Kamar yadda Inmal ya addabi dakarun Dujalu ya rinka ratsawa ta cikinsa ta kowanne bangare yana ragargazarsu haka shima sarki Dujalu ya addabi jama'ar sarki Maharaz tamkar an auna barnar da suke yi tazo dai-dai.Ana cikin haka ne sarki Dujalu ya hango irin mummunar barnar da Inmal ke yi sai hankalinsa ya dugunzuma kuma ya cika da tsananin mamakin yadda Karamin yaro ya sami irin wannan gagarumin karfi haka.
Cikin tsananin fusata sarki Maharaz ya tarwatsa mazajen da ke gabansa ya falfala da gudun tsiya tamkar ana shara da tsintsiya ya durfafi inda Inmal yakc. Ai kuwa sai Inmal ya dago kai ya hango tahowarsa. Nan take shima Inmal ya tarwatsa mazajen da suka lullu6eshi ya falfala da matsanaicin gudu yana banke mutane da dawakai, rakuma da alfadarai da ke gabansa ya nufi sarki Dujalu cikin dacin rai da kunar zuci gami da mugun nufi domin su hadu. Ai kuwa suna haduwa suka kacame da mugun yaki na ban tsoro da ban al'ajabi.Tamkar jikinsu ba na jini da tsoka bane haka suka rinka kaiwa juna sara da suka cikin tsananin juriya, zafin nama da bajinta. Sai
gashi tsohon kashi ya hadu da sabon kashi,naci da naci, zuciya da zuciya, kowannensu yaki yake yi iya karfinsa tamkar ba za su taba dainawa ba facc an tashi duniyar gaba daya.Haka dai aka ci gaba da wannan masifaffen yaki, har sai da rana ta fadi, gari ya soma duhu. Kai saboda bala'in artabun da ake yi a sama da kasa, wato aljanu nayi, mutane nayi sai da wata irin gagarumar tsawa da walkiya suka addabi kowa, tartsatsin wuta kuwa ya rinka fantsama yana haddasa gobara har a cikin tekun. Babu wani bangare da ke shirin ja da baya a yakin. Mutane da aljanu suka rinka zabga gumi, yunwa da kishirwa ta addabi kowa. Gashi dai an zo da guzurin abincin kuma ga ruwan teku ana gani amma sai ci da sha ya gagari kowa saboda bala'in da ake ciki da mugun tashin hankalin da ake fuskanta. Ba shiri dan dole kowanne bangare suka busa kahon janye yakin domin tsananin duhu da hayakin wuta ya sa ba a shaida juna ha ta kai cewa idanu sun rufe mutane sun fara yakar 'yan uwansu ma basu sani ba.
Koda jin sautin kahon na kowanne bangare sai duk aka ja da baya aka daina yakin
tamkar daukewar ruwan sama a lokaci guda. A sannan ne matsafa suka samar da hasken tsafi kowa ya iya ganin komai.
Kaico! Hakika yaki masifa.Da baiyanar wannan haske sai ga gawarwakin mutane da aljanu zube a kas ko ina rututu, babu inda mutum zai iya takawa da kafarsa face ya taka gawa. Kai har akan ruwan tekun gawarwaki ne barjik babu adadi kuma ba kyan gani. Jini kuwa gashi nan yana ta gudu da malala akan kasa har ya jirkita ruwan tekun gaba daya yana neman rineshi. Komai kallon Kurillar mutum bai isa ya iya tantance 6angaren da aka fi yiwa barna ba. A gaba dayan mazajen da ke filin wannan yaki walau na mutane ko na aljanu babu mahalukin da bashi da raunuka a jikinsa,hatta manyan baraden kuwa, wato su sarki Dujalu da su Inmal.
Bayan kowanne bangare sun ja da baya nesa da juna sai aka shiga aikin binne gawarwaki, masu kuka nayi, masu bakin ciki nayi, kuma a sanann ne kowa ya rinka neman ruwan sha da abinci, sannan kuma aka rinka sanya magani a raunika. Masu karaya aka rinka gyarasu suna ihu bisa jin radadi da zogin
gyara.


Manyan mazaje kuwa, za ka ga sun yi shiru ko motsi basa yi. In ba don albarkacin mata ba wadanda aka taho da su wannan yaki da ba za a sami masu dawaniyar kula da lafiyar mutane ba domin gaba dayan mazajen babu wanda bai jigata ba ainun, wasu ma kamar ba za su rayu ba wasu kuwa sun gama zama nakasassu ba zama su iya ci gaba da yaki ba.
A 6angaren su sarki Maharaz kuwa,bayan an kafa tantuna sai sarki Maharaz, Hibru da Inmal suka taru a cikin tantin sarki Maharaz kuyangi na sa musu magani a jikin raunikan jikinsu, gimbiya Mulaifa ce da kanta take sawa Inmal magani a jikinsa bata yarda wata kuyanga ta taba shi ba.
Bayan an tsaida jinin da ke zuba a jikinsu kuma sun ci abinci sun sha ruwa sun sami 'yar nutsuwa sai sarki Maharaz ya ja dogon numfashi sannan ya dubi sarkin yaki Hibru ya ce, "Ya kai abokina yanzu a hangenka me kake ganin zai faru idan aka ci gaba da wannan yaki?"
Koda jin wannan tambaya sai shima
Hibru yai ajiyar zuciya sannan ya dubi sarki Maharaz ya cc, "Ya shugabana ni dai a ganina a Karshen yakin nan RAGAS za a yi kowa da komai sai ya mutu, ka ga ke nan babu bangaren da zai iya mallakar wannan takobi ta Saiful Lujara da ke karkashin tekun nan tun da gashi muna kallon tekun da idanuwanmu amma shiga cikinta ma ya gagaremu bare ayi laluben inda takobin take."


Koda jin wannan batu sai Inmal ya yi murmushi saman ya dubi Hibru ya ce, "Haba ya Abbana saboda me za ka yi waman batu, ai har abada mutum ba ya fidda rai ga samun rabo muddin yana numfashi a doron Kasa. Ni a rayuwata zuciyata ba ta taba karaya ba bisa samun abin da zuciyata ke so. Na yi imani da hakan dari bisa dari saboda haka na Kudurce a raina idan kowa da komai zai hallaka a bakin wamnan tekun ya zamana saura ni kadai jal lallai sai na lalubo takobin saiful Lujara a karkashin wannan teku kodakuwa zan hallaka a kokarin hakan. Ai rai ba a bakin komai yake ba muddin akwai biyan bukata".
Koda jin haka sai sarki Maharaz ya yi murmushi ya cc, "Da kyau jarumin jarumai,
tauraron zamani, ka ci gaba da jajirccwa bisa wannan Kuduri naka koda kuwa gaba dayan jama'ata zamu karc ya zamana saura kai kadai jal. Ka sani ccwa idan har ka sami nasarar mallskar wannan takobi ta Saiful Lujara sannan ka mallaki mashin Galilil Haras da hular Lamsara ka ajiye abin tarihin da babu wani mahalukin da ya taбa ajiyewa a duniya,kuma sai ka sami daukaka wacce babu wanda zai samu. Ya kai abin alfaharina kuma mafarkina na gobe kayi iya yinka don ganin ka cimma buri ka sani cewa rayuwarmu gaba daya a yanzu ta dogara da iyakar kokarinka domin karfin sihirinmu da karfin damtsenmu ba za su iya yin komai ba face kawai kara maka Kwarin guiwa."


Sa'adda sarki Maharaz ya zo nan a zancensa sai Inmal ya cika da tsananin mamaki ya dubeshi ya ce, "Ya shugabana ya ya ni da nake yaro kankani a cikinku za ka ce rayuwarku ta dogara a hannuna? Ka yi sani cewa ni kaina na tsorata da al'amarin sarki Dujalu a lokacin da muka fara fafata yaki ni da shi, domin ban taбa ganin mutum mai tsananin karfin dantse kamar sa ba, gami da zafin nama.
Sannan yana da matukar juriya da naci fiye da yadda nake da su. Duk da cewar zuciyata bata taбa karaya ba akan dukkan al'amari amma a wannan karon akwai darsuwar kokwanto a cikinta".
Sa'adda sarki Maharaz yaji wamnan batu na Inmal sai ya bushc da dariya sannan ya dubi 'yarsa Mulaifa kuma ya dubi Inmal ya ce, "Ai kuwa idan har nayi tsawon rai a waman yaki sadakin aurenka na 'yata Mulaifa shi ne samun nasararka akan dauko takobin Saiful Lujara a cikin Karkashin wannan teku. Idan har ka kasa dauko wannan takobi to har abada ba za ka auri 'yata ba".
Koda gama wannan jawabi sai sarki Maharaz ya kishingida bisa shimfidar da yake zaune ya lummshe idanunsa. Shima Hibru sai ya yi koyi da abin da sarki Maharaz ya yi.Gimbiya Mulaifa da Inmal kuwa sai suka Kurawa jumansu idanu cikin tsananin tashin hankali da fargaba. Nan take hawaye ya zubowa Mulaifa ta rungume iNmal tana mai yi masa rada a kunne ta ce, "Idan har kaunar da kake yi mini ta gaskiya ce duk yadda za ka yi ka tabbatar da cewa ka dauko wannan takobi ta
Saiful Lujara. Idan kuwa ka kasa bana tsammanin ccwa zan ci gaba da rayuwa a duniya".


Koda jin wannan batu sai idanun Inmal suka zazzaro yaji hankalinsa ya yi mummunan tashi, bai san sa'adda jikinsa ya kama tsuma ba yaji kamar ya tashi ya ruga da gudu ya dauki kahon yaki ya busa domin a ci gaba da wannan masifaffen yaki.
Wannan shi nc abin da ya faru ga su Inmal bayan an fafata azababben yaki tsakanin ruodunarsu da rundunar sarki Dujalu a karo na farko a bakin tekun bahar Sufiya.


A CAN BANGAREN kuwa, bayan sun binne na su
su sarki Dujalu
gawarwakin kuma an kafa tantuna an duba
marasa lafiya kowa ya dawo cikin haiyacinsa
kuma an kafa tantuna sai sarki Dujalu ya
kadaita da 'yar uwarsa Hursiya a cikin tantinsa
inda ta rinka sa masa magani a jikin raunikan
da ke jikinsa. Koda ta ga raunikan sun kai guda
bakwai kuma duk masu zurfi ne, wasu ma sai
da ta dinke masa fatar sai zuciyarta ta karaya
bata san sa'adda ta fashe da kuka ba. Cikin matukar mamaki sarki Dujalu ya dubi Hursiya ya ce, "Ya ke 'yar uwata ina dalilin wannan kuka naki?"
Hursiya ta dago kai ta dubi sarki Dujalu cikin tsananin damuwa ta ce, "Ya kai dan uwana ka sani cewa a duniya bani da kowa face kai. Zuciyata ta karaya bisa ganin wadannan manyan raunika na jikinka har ina ganin cewa abu ne mawuyaci mu sami nasarar wannan yaki. Yanzu idan babu kai ya ya zan yi rayuwa a diniya?".
Sa'adda Hursiya ta zo nan a zancenta sai sarki Dujalu ya kamu da tsananin tausayinta har idanunsa suka ciko da Kwalla sannan ya ce,"Ya ke 'yar uwata kiyi sani cewa duk irin gumu da bala'in da za a yi a wannan yaki a ba zan taba mutuwa ba ammma bincike ya nuna mini cewa zan shiga mugun yanayi kamar zan mutu da ni da babban jarumi na cikin abokan gabarmu, wato wannan yaro Inmal dan sadauki Hibru.
Ni da shi duk ba zamu mutu ba amma duk irin yanayin da na shiga sai shima ya shiga.A cikin binciken nawa na gani cewa mutum hudu
ne kacal za su tsira da rayuwarsu a wannan yaki amma na kasa gano ko su waye, ragowar mutum biyun bayan ni da Inmal. Abin da nake so da ke shi ne, kafin a ci gaba da wannan yaki a karo na biyu ki sulale ki bar wajen nan gaba daya ki koma can nahiyarmu ki ci gaba da mulkin Kasarmu ta Hawarul din in da muka baro mata, yara da tsofaffi, domin idan har baki koma ba gaba dayan jama'armu za su shafe a doron kasa a manta damu har abada.Idan har Inmal ya rigani dauko takobin Saiful Lujara, ki sani cewa hadimina aljani Baizurul Aufan na can a baya cikin dajin Saurul yana jiranki domin tuntuni na shirya hakan.' Lallai za ku yi wannan tafiya lafiya har ki isa gida babu wani tsautsayi da zai sameki."
Sa'adda sarki Dujalu ya zo nan a zancensa sai Hursiya ta sake fashewa da matsanaicin kuka kuma ta rungumeshi ta ce, "Ta ya ya kake tsammanin zan iya tafiya na barka anan ana wannan masifaffen yaki? Lallai ba zanje ko ina ba in ba tare da kai ba, sai dai nima ajalina ya riskeni anan din. Ai sadauki Hibru ya yi bayanin gaskiya da ya ce rayuwa ba ta da amfani idan babu masoyi. Ka sani cewa mulki
da dukiya ba za su taba haifar da kwanciyar hankali ba a rayuwata muddin babu kai a kusa da ni. Ka tuna cewa tun da na taso ban san uwata ba kuma ban san ubana ba sai kai.


Babu wanda na shaku da shi a duniya sama da kai.
Babu irin jin dadin da baka bani ba a kullum kana riritani baka son koda kuda ya sauka a jikina. Waye zai iya yi mini irin wannan gata da ka yi mini?
Waye zai iya kare lafiyata kamar yadda ka kare kuma waye zai soni kamar yadda ka soni? Na ka-na ka ne har abada ba zan taba samun madadinka ba. Ina tabbatar maka da cewa idan zai zamo ni kadai ce na rayu a filin yakin nan kuma na sami ikon mallakar takobin Saiful Lujara, ba zan koma gida ba na ci gaba da rayuwa sai dai na binne kaina a kusa da kabarinka domin mutuwa ce kadai za ta iya kawar mini da bakin cikin rashinka."
Lokacin da Hursiya tazo nan a zancenta sai shima sarki Dujalu ya fashe da matsanaicin kuka kuma ya kankameta a kirjinsa yana mai cewa,"Hakika abin da ke shirin faruwa a gareni yana neman ya zama dai-dai da yarda
rayuwar sadauki Shaddadu na birnin Kufa ta
kasance."
Koda jin wannan batu sai Hursiya tayi wuf ta janye jikinta daga cikin na sarki Dujalu suka fuskanci juna sannan ta ce, "Mene na ya faru ga rayuwar sadauki Shadaddu?".
Sarki Dujalu ya sunkui da kansa kas ya yi ajiyar zuciya sannan ya fara ba ta labari kamar haka.
AWANI ZAMANI can baya, wanda
ya zo dai dai da zamanin sadauki
Hantaru na bimin Kisra,an yi wani azzalumin sarki a birnin Kufa wanda ake kira da suna
Lafaru ibini Hurdas.

Sarki Lafaru ya mallaki dukiya mai tsananin yawan gaske, kuma sai da ya shekara arba'in a duniya bai taбa yin aure ba kuma bai taba yin rashin lafiya ba koda kuwa ciwon kai na tsawon dakika daya.
Sarki Lafaru ya kasance sadaukin sadaukai mai dakawa maza gumba a hannu domin a tarihin rayuwarsa ya ziyarci yakoki guda dari da ashirin yana samun nasara kuma
ko karce jikinsa ba a taбa yi ba a wajen yaki.Saboda tsananin jarumtakarsa, zafin namansa da kuma tsagwaron sa'a.
A rayuwar sarki Lafaru bai taba yin tsafi ba, kuma tsafi baya cinsa, baya dogara da komai face tsagwaron karfin damtse. A kasarsa gaba daya ba a yin addini ko wanne iri, idan kuwa aka kama mutum yana wani addini koda a 6oyene sai an kashe shi.
Sarki Lafaru na da wata muguwar al'ada ta yiwa mata fyade, domin a duk sa'adda ya ga kyakkyawar mace in dai ya yi sha'awarta ko matar wa ce sai ya mangareta ta sume sannan ya biya bukatarsa da ita. Daga wannan rana sai ya sa a tsare wamnan mace har tsawon wata shida sai an tabbatar da cewa bata sami ciki da shi ba sanann zai sa a saketa.

Idan kuwa ta sami ciki ta ke zai sa a hallakata. Dalili kuwa shi ne, ko kadan sarki Lafaru baya son ya sami magaji a duniya saboda jarumtakarsa ta gado ce iyaye da kakanni, ma'ana babansa ya kasance, shima kakansa haka yake kuma abin ya biyo salsala tun sarkin kufa na farko.
Lokacin da sarki Lafaru ya sami tarihin wannan al'amari a cikin kundin tarihin sarauta
na gidansu sai ya kudurce a zuciyarsa cewa shi ne zai zamo sarki na karshe mai wannan baiwa ta jarumtaka da karfin lafiya, don haka ba zai taba yarda ya haifi magajinsa ba.
Wani abin mamaki dangane da rayuwar sarki Lafaru shi ne a duk shekara sau daya yake sawa a nemo masa budurwa wacce babu kamarta a fagen kyawu a kasarsa. Ana kawota sai ya sumar da ita ya biya bukatarsa da ita.Sai da ya shekara ashirin akan karagar mulki yana wannan muguwar dabi'a. A cikin shekara ta ashirin da daya ne al'amura suka zo da sauyi domin a wannan shekarar ne aka kawo masa wata tsaleliyar budurwa mai suna Sharlis wacce tsananin kyawunta ya fi gaban kwatance.
Da la'asar sakaliya sarki Lafaru na zaune a fadarsa an kewayeshai ana fadanci sai ga Sharlis an shigo da ita. Nan take gaba dayan mutanen da ke fadar suka rude suka dimauce bisa ganin tsananin kyawun Sharlis. Shi kansa sarki Lafaru bai san sa'adda ya mike tsaye ba jikinsa ya kama tsuma ya taka kafafunsa ya nufi inda Sharlis ke tsaye sabanin yadda ya saba yi a duk shekara, sai dai akai budur war
har gabansa.
Sarki Lafaru ya iso daf da Sharlis ya tsaya yana mai kura ma ta idanu a lokacin da gaba dayan jikinta ke karkarwa saboda tsoro kuma hawaye na zuba a idanunta. Sarki Lafaru ya daga hannunsa da nufin ya make Sharlis domin ta suma ya biya bukatarsa da ita amma sai ya kasa dukanta. Al'amarin da ya matukar baiwa kowa mamaki ke nan

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment