Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a koma kan masoyan Marifa domin suma su amsa tasu gasar.
Nan take, aka umarci Marifa ta mike tsaye domin ta gabatar da ta ta tambayoyin ga jaruman gasarta mutum hudu kacal. Marifa ta dubi saurayi na farko da ke tsaye akan sahun gaba wanda ya kasance kyakkyawan gaske mai Kuruciya domin shekarunsa ba za su haura ashirin ba yana sanye da tufafi irin na sarakai masu tsadar gaske, kai da ganinsa ka san dan sarki ne.
Cikin murmushi mai rikita zuciyar da namiji Marifa ta dubi kyakkyawan saurayin ta ce,"Tambaya ta farko a gareka ita ce, Wadanne abubuwa ne guda biyu a duniya wadanda suka kasance kishiyar juna kuma ba a taba ganin sun a hadu waje daya ba ? Tambaya ta biyu ita ce, Wane ruwa ne shi bai sauko daga sama ba kuma bai tsiro daga kasa ba?

Tambaya ta uku kuwa ita ce, Wadanne abubuwa ne guda uku wadanda mutane da aljanu basa iya tsallake sharrinsu?".

Koda Marifa ta gama furta wadannan tambayoyi guda uku sai gaba dayan jama'ar da ke cikin filin fadar suka shiga wasi-wasi da rudani gami da zancen zuci.
Shi kuwa wannan kyakkyawan saurayi na farko akan sahun layin masoya Marifa sai idanunsa suka zazzaro kuma suka ciko da Kwalla ya kasa amsa koda tambaya daya ya tsandara ihu ya fadi kasa yana birgima a cikin kasa saboda bakin ciki.
Cikin gaggawa Dakaru suka ruga suka daukeshi suka yi waje da shi. Mutum na biyu kuwa tun kafin azo kansa ya fashe da kauka ya fita daga kan sahu ya koma gefe daya.Mutum na uku wani tsohon boka ne, da aka zo kansa bai yi shakkar komai ba, kawai sai ya nutsu sannan yai
gyaran murya ya ce,"Ya ke wannan ma'abociyar kyau kiyi sani cewa game da tambayarki ta farko amsarta ita ce, 'Rana da wata, domin su ne kishiyar juna daya yana da matukar zafi, daya yana da matukar sanyi, kuma kullum ana ganinsu a duniya,amma ba a taba ganin ranar da suka hadu ba a waje daya.
Dangane da tambayarki ta biyu kuwa,amsarta ita ce, "Hawaye. Domin shi daga cikin ido yake zuba kuma ba a saman mutum yake ba kuma ba a kasansa yake ba.
Tambaya ta uku kuwa, amsarta ita ce, "Mata,dukiya da mulki. Komai karfin mutum kaifin tunaninsa wadannan abubuwa uku za su iya rikita masa.Kwakwalwa ko kuma su je fashi cikin hallaka.


Lokacin da wannan boka yazo nan a jawabinsa sai aka ga Marifa ta murtuke fuska kamar za ta fashe da kuka. Al'amarin da ya jefa bokan cikin tsananin farin ciki ke nan domin ya tabbatar da cewa ya ci wannan gasa. Dukkanin jama'ar da ke fadar ma sai jikinsu ya yi sanyi domin suna ganin cewa wannan tsohon boka ya tsinci dami akala. ba zato ba tsammani sai aka ga Marifa ta saki murmushi sannan sai ta ce, "Ya kai wannan dattijo hakika ka bani matukar tausayi domin kiris ya rage ka amsa wadannan tambayoyi
dai-dai.Ka sani cewa ka amsa tambayar farko da ta uku dai-dai, tambaya ta biyu ce ta gagareka,saboda haka sai ka kauce ka baiwa mutum na karshe wuri domin ya jarraba tashi sa'ar".
Kafin Marifa ta gama rufe bakinta sai aka ga wannan tsohon boka ya kama makyarkyata daga tsaye, kafin a ankara ya kife kasa sumamme.Da gudu Dakaru suka isa kansa suka yayyafa masa ruwa,ya farfado yana sambatu da kiran sunan Marifa.
Nan da nan aka daukeshi aka yi waje da shi.Koda sarki Darul Mahabul ya matso gaba domin ya amsa tambaya ta biyun sai fadar ta sake yin tsit tamkar babu wani abu mai numfashi a wajen.In ka dauke sautin numfashin jama'a da sautin kadawar iska babu abin da kunne ke ji.
Sarki yai gyaran murya sannan ya dubi Marifa cikin murmushi ya ce,"Amsar tarabayarki ta biyu ita ce, "Zufa, domin ita zufa tana fitowa ne daga ko ina a jikin a halitta, ba wai ta sama ko kasa ba."
Da jin haka sai Marifa ta ruga da gudu izuwa ga inda sarki ke tsaye ta rungumeshi cikin tsananin farin ciki tana mai cewa,. "Kai ne mijina, hakika kaine mijina!".

Nan take fadar ta sake rudewa da kade-kade da bushe-bushe gami da raye-raye.
Sai da aka kwana bakwai ana ta shagalin biki na auren sarki Kusaidu da Zarifa da kuma Sarkin Darul Mahabul da Marifa sannan aka kare. A ranar da Sarki zai dauki amaryarsa ya tafi daita birninsa na Darul Mahabul ne ya ga idanun Marifa sun ciko da Kwalla, nan da nan hawaye ya fara sartu a kumatunta. Da farko ya yi tsammanin cewa alhinin rabuwa da mahaifarta ne ya jefata a cikin wannan hali amma da ya ga ta yini tana kuka sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ya kadaita da ita ya ce, "Ya ke matata ina dalilin wannan kuka naki? Shin ba kya Kaunata ne a matsayin abokin rayuwarki ko kuwa wani abu nayi miki ya sosa miki zuciya?"
Sa'adda Marifa taji wannan tambaya sai ta share hawayenta,sannan ta ce, "Ya kai mijina kayi sani cewa ina Kaunarka dari bisa dari kamar yadda uwa ke son dan da ta haifa kuma ko kadan ba ka yi mini wani laifi ba. Ba wani abu bane ya sa ka ga ina wannan kuka face naji jikina cewa abu ne mawuyaci na zauna ture da kai har zuwa lokaci mai tsawo ba tare da ajali ya riskeni ba. Ma'ana ina kyautata zaton a ko yaushe zan iya kamuwa da rashin lafiya wacce za ta zamo sanadin ajalina.Tausayinka ne yasa ka ga ina wannan kuka domin kafin mu rabu na san za ka shaku da ni ainun kuma za ka yi bakin ciki irin wanda baka taba yi
ba a rayuwarka bayan mutuwata. Ina son ka yi mini alkawari guda biyu a yanzu. Alkawari na farko shi ne, a duk sa'adda na kwanta cutar ajali za ka zo har nan birnin Kisra ka kawowa 'yar uwata wata wasika daga gareni.
Alkawari na biyu shi ne, idan har na haihu da kai za ka kula da abin da na haifa ainun walau mace ko namiji."
Lacin da Marifa tazo nan a zancenta sai hankalin Sarki ya Kara dugunzume
yaushe cikin alamun rashin fahimta ya dubeta ya
ce, "Ya ke matata ina dalilin wannan furuci naki?
Ya ya aka yi kika san cewa ba za mu dade tare ba,
kuma wane ne ya gaya miki cewa za ki kamu da
ciwo har ki kwanta jinya?"
Marifa ta sa hannunta ta share hawayenta sannan ta ce, "Ya kai mijina ka yai sani cewa gaya maka wannan alamari ba shi da wani amfani domin ba zai haifar da komai ba a cikin rayuwar aurenmu face bakin ciki da rashin sukuni da kwanciyar hankali. Abin da nake so naji daga bakinka kawai shi ne, ka daukar mini alkawarin da na zaiyana maka".
Koda jin wannan batu sai Sarki ya yi shiru yana mai sunkui da kansa kas sannan ya ce, "Na yi alkawari lallai zan yi wadannan abubuwa biyu da kika bukata daga gareni".

Da jin haka sai Marifa ta rungume sarki ta fashe da kukan farin ciki, shi kuwa sai yaji ya kamu da tsananin tausayinta har kwalla ta cika masa idanu.
Ba tare da 6ata lokaci ba Sarki da amaryarsa,
boka Sulbaini da boka Zaharu suka yi bankwana
da Sarki Kusaidu, Sarki ya kama hannun
amaryarsa Marifa suka nufi keken doki za su
shiga, a wannan lokaci Sarki Kusaidu na rike da hannunun Zarifa ya na tsaye
Marifa ta dubi Sarki Kusaidu ta ce, "Ina son zan
gana da 'yar uwata".
Sarki Kusaidu ya ce, "Je ki ya ke matata".Marifa ta juyo da baya ta nufi inda sarki Kusaidu da Zarifa ke tsaye al'amarin da ya matukar baiwa Kusaidu da Zarifa mamaki ke nan domin basu san abin da za ta zo ta ce da su ba. Da isowarta daf da Zarifa sai ta tsaya cak ta kura ma ta idanu a lokacin da Kwalla ta zo ma ta sannan ta ce,"Ya ke 'yar uwata kin sani cewa tun muna yara da muka taso bamu taba kaunar juna ba har muka girma amma a halin yanzu da zamu yi rabuwa ta har abada sai naji ina Kaunarki fiye da komai a duniya saboda na san cewa bani da kowa a duniya face ke. Don haka bana kaunarki baya nufin cewa zan iya goge jininki a cikin nawa. Ina da wani babban sirri wanda ya shafi dukiyarmu wanda duk duniya
babu wanda ya san da shi sai ni kadai amma ba bayan mutuwata za ki ji wannan sirri ba a yanzu akwai wasika da zan baiwa mijina ya aiko miki da ita. Ina mai tayaki farin ciki da kika sami nasarar ganin bayana amma ina tabbatar miki da cewa nan gaba sai kin yi nadama bisa abin da kika yi mini.Da wannan furuci nake yi miki bankwana da sallamar karshe."
Koda gama fadin haka sai Marifa ta juya ta tafi wajen mijinta suka shiga cikin keken dokinsu suka yi gaba. Boka Sulbaini da boka Zaharu sukn tashi sama kamar tsuntsaye suna bin keken dokin daya a hannun hagu, daya kuma a hannun dama.
Tun da mahaifiyata Marifa ta dawo birnin Darul Mahabul ta ci gaba da rayuwa cikin nishadi,jin dadi da kwanciyar hankali tamkar wani abu bai ta6a zama matsala ba a rayuwarta.
A kwana a tashi sai mahaifiyarta ta sami juna biyu. Wata tara na cika sai ta haifi kyakkyawar 'ya ta gaban kwatance wadda tun a ranar da aka haifeta labari ya cika birnin Darul Mahubul gaba daya. Mutane suka rinka tururuwa daga birane da kauyuka suna zuwa ganin jaririyar suna bata kyaututtuka iri-iri. Kai har daga sauran makotan
ana zuwa a
yi yawa sai ya kafa dokar hana kowa ganin wannan jaririya face sarki kansa, mahaifiyarsa da kuma 'yan uwan sarki na jikinsa.Da ranar suna ta zagayo sai aka radawa yarinya suna gimbiya Larziya. Sai da aka kwana bakwai ana shagalin suna sannan aka kare. Tun daga ranar da aka kammala sunan Marifa ta kamu da tsananin rashin lafiya har ta kwanta jinya sai dai a kwantar a tayar bata iya yin komai da kanta. Koda ganin wannan hali da Marifa ta shiga sai hankalin Sarki ya dugunzuma ya tuno kalaman da ta yi masa tun a birnin Kisra cewar nan gaba ba za ta dade ba a duniya.
Kullum sarki baya zuwa ko ina sai dai ya zauna a gaban gadon Marifa yana kallonta kuma yana kallon jaririyarta yana zubar da hawaye.Magani babu irin wanda Sarki bai sa an nemo anyi ma ta ba amma a banza, daga nan yasa bokayensa Sulbaini da Zaharu suka dukufa akan bincike amma sai suka kasa gano ainahin abin da ke damun Marifa.
Bayan cikar watanni goma sha uku da dawowar Sarki tare da amaryarsa birnin Darul Mahabul sai ciwon Marifa ya yi tsanani. A daren wata na goma sha ukun ne ta dubi sarki cikin yanayin tausayi sa'adda hawaye ya gangaro daga cikin idanunta ya zuba bisa kumatunta sannan ta
budi baki da Kyar ta ce, "Ya kai mijina ka sani cewa a yau ina ji a jikina cewa zan mutu ba zan kai gobe ba, saboda haka ina mai yi maka tuni bisa alkawarin da ke tsakaninmu. Lallai ka kula da Larziya da kyau a bayan baya nan, sannan ka bude akwatin suturata za ka iske wasika wacce na barwa 'yar uwata Zarifa lallai ina son ka dauki wannan wasika ka bayar da ita ga amintaccen manzonka ya kaiwa Zarifa matar Sarki Kusaidu hannu da hannu.
Wasiya ta karshe da zan bar maka ita ce,wani babban sirri wanda nake son ka ajiyeshi a cikin zuciyarka kada kla gayawa kowa face 'yata Larziya idan ta girma. Kuma ina gargadinka da kada ka kuskura ka ce za ka dauki mataki bisa abin da zan gaya makan domin idan ka dauki matakin da kai da 'yarka duk mutuwa za ku yi. Ina son ka saurareni da kyau ka haddace duk abin da zan fada maka domin idan ka manta abu daya tamkar ka tarwatsa rayuwar 'yarka ce anan gaba".
Koda jin wannan batu sai Sarki ya kara nutsuwa ya Kurawa Marifa idanu, ita kuwa sai ta ci gaba da bayani tana mai cewa, "Ya kai mijina ina mai sanar da kai cewa wannan ciwo da ya kamani ya zama cutar ajali a gareni ba wani bane ya haddasa mini shi ba face 'yar uwata Zarifa matar Sarki Kusaidu".
Koda jin wannan batu sai idanun Sarki suka
Zazaro ya cika da tsananin mamaki.
Marifa ta ci gaba da cewa, "Zarifa tayi mini asiri ne a ranar da aka yi gasar neman aurenmu domin ta hallakani saboda ta gaji dukiyar da mahaifinmu ya mutu ya bari. Abin da bata sani ba shi ne,babu wanda zai iya shiga cikin wannan kogo da mahaifinmu ya boye,wannan dukiya har ya debeta face jarumin da ya iya dauko takobin Saiful Lujara a kogon Mazubatul Dulshal. Lallai bincike ya tabbatar da cewa nan gaba za a sami jarumin da zai dauko wanman takobi bayan an yi gasar neman auren Larziya anan birnin Darul Mahabul.
Wasiyar da nake son ka barwa Larziya ita ce,"Lallai ta umarci wannan jarami da ya dauko takobin Saiful Lujara da ya je birni Kisra ya kashe 'yar uwata Zarifa domin daukar fansar asirin da tayi min kuma yaje wamnan kogo wanda mahaifina ya boye wannan dukiya ya sa a debota kaf a dorota akan rakuma da dawakai komai yawanta a kawowa Larziya. Idan har wannan jarumi ya ki yarda da wannan bukata to lallai Larziya ta yanke Kauna tsakaninta da shi. Ma'ana kada ta yarda da shi ya santa 'ya mace idan kuma ya matsa ma ta ta kashe kanta idan har ta yarda cewa ni ce mahaifiyarta, kuma tana kishin cin
amanar da 'yar uwata tayi mini."
Sa'adda Marifa tazo nan a zancenta sai idanunta suka kafe komai na jikinta ya sandare ya daina motsi. Koda ganin haka sai Sarki ya fada kan gawar ya fashe da matsanaicin kuka.
Har aka binne Marifa a kabarinta sarki bai daina kuka ba. Kai karshe ma akan kabarin ya kwana yana kuka saboda tsananin bakin cikin rashin mahaifiyate sai da Sarki ya kwana arba'in baiyi magana da kowa ba kuma bai zauna a fada ba, kuma komai dadin abinci idan ya yi loma uku ya barshi ke nan domin tunanin Marifa ne zai fado masa ya fashe da kuka.
Daga wannan lokaci Sarki ya dauki son duniya ya dora akan jaririyar da Marifa ta bari ya zamana cewa ana kula da ita ainun ko kuda ba a bari ya sauka a jikinta.
Sannu-sannu yarinya ta rinka girma har ta cika budurwa bata san mahaifiyarta ba face wata kuyangar mahaifinta wacce ta shayar da ita kuma ta reneta.Sai da Larziya ta cika shekara goma sha bakwai sannan wata rana ta tambayi Sarki labarin mahaifiyarta domin tuntuni Sarki yana kaita kabarin mahaifiyar tata su tsugunna tare a gaban kabarin su yi addu'a sannan su tashi su shiga cikin gidan sarauta. Ko sau daya sarki bai taba baiwa Larziya labarin rayuwar mahaifiyarta ba da yadda
ajali ya risketa.
Lokacin da Sarki yaji Larziya ta tambayi labarin mahaifiyarta sai hankalinsa ya dugunzuma.Nan take idanunsa suka ciko da kwalla ya yi kamar ba zai iya gaya ma ta ba, amma da ya tuno da alkawarin da ya daukarwa Marifa sai ya kwashe labarin komai ya zaiyane mata har da batun wasiyar da mahaifiyar ta ta ta bar ma ta akan daukar fansa da debo dukiyar nan tasu.
Sa'adda Sarki ya gama bani wannan labari ni Larziya sai na fashe da matsanaicin kuka kuma na kamu da tsananin bakin ciki. Cikin tsananin fusata na dubi Sarki na ce, "Na rantse da darajar kabarin mahaifiyata lallai wannan wasiyya da ta bar mini sai na cikata, kuma lallai idan jarumin da ya ci gasar aurena yaki biya mini bukatar mahaifiyata sai na yanke kauna tsakanina da shi kuma har abada ba zai sanni 'ya mace ba kuma idan ya matsa mini zan kashe kaina don cika umamin mahaifiyata.
Ya kai Abbana yanzu abu daya nake so naji daga bakinka, shin wannan wasika da mahaifiyata ta bar maka ka aika da ita ga Zarifa matar sarki Kusaidu? Kuma wane irin sakone a cikin wasikar?".
Koda jin wannan tambaya sai sarki yai ajiyar zuciya sannan ya ce,"Ba komai bane a cikin
wannan wasika ba face bayanin cewa Marifa ta gane asirin da 'yar uwarta Zarifa tayi ma ta sannan tayi ma ta albishir da cewa wanann dukiya da take hankoron ci ita kadai har abada ba za ta iya cinta ba domin mahaifin nasu ya boyeta a cikin kogon Hurshal da ke can bayan gari.
Lokacin da manzona ya isar da wannan wasika ga Zarifa ta karantata sai hankalinta ya yi matukar dugunzuma ta rasa abin da ke ma ta dadi a duniya. Har yau har kwanan gobe a cikin binciken yadda za ta iya sawa a debo ma ta wannan dukiyar take amma ta kasa."
Lokacin da Sarki ya zo nan a zancensa sai fuskata ta fadada da mrumushin farin ciki, na dubeshi na ce, "Ai kuwa har abada ba za ta taba mallakar wannan dukiya ba, wani nata ma ba zai mallake ta ba, ni ce zan mallaki dukiyar".
Sa'adda Larziya tazo nan a labarintaa sai ta dubi Hantaru ta ga idanunsa sun cika sharkaf da hawaye don haka sai tayi tsammanin cewa tsananin tausayinta ne ya sa shi yin kuka.
Larziya ta ce,"Ya kai mijina wannan shi ne takaitaccen tarihin rayuwata da ta mahaifiyata kuma bisa wannan dalili ne tun kafin a yi gasar neman aurena na bukaci da ka daukar mini alkawari guda uku. Alkawari na farko shi ne, duk alfarmar da na nema a wajenka ba za ka ketare ba.
Alfarma ta biyu ita ce, komai tsanani ba za ka gujeni ba. Sannan alfarma ta uku ita ce, komai wuya ba za ka fita daga cikin gasar neman aurena ba.
Yanzu ka cika alkawari na farko tun da ka jure duk wahalar da ke cikin gasar neman aurena har ka sami nasara ka zamo zakara. Yanzu abin da ya rage shi ne ka shirya ka tafi izuwa birnin Kisra ka saro kan 'yan uwar mahaifiyata Zarifa ka kawo mini shi nan na gani da idanuna, sannan kuma ka je ka shiga kogon Hulshal ka debo mini wannan dukiya ta kakana. Alkawari na karshe shi ne, ka zauna tare da ni har izuwa karshen rayuwar daya daga cikinmu ya zamana cewa babu abin da zai rabamu face mutuwa. Idan kuma ka ki yarda da duk wadannan bukatu nawa lallai zan kashe kaina'.
Sa'adda Larziya tazo nan a jawabinta sai Hantaru ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa wanda ya firgita Larziya ta dimauce ta mike tsaye zumbur! Za ta ruga da gudu, amma sai ya ga Hantaru ya fashe da matsanaicin kuka, sai ta dawo ta tsugunna a gabansa ta kama kafadunsa ta rike ta ce, "Ya kai mijina ina dalilin wannan ihu a kuka naka?"
Koda Hantaru yaji wannan tambaya sai ta dago kai ya dubi Larziya a lokacin da hawaye ke
shatata daga bisa kan kimatunsa ya ce, "Ya ke abar kaunata, abar begena dare da rana,kiyi sani cewa Zarifa matar Sarki Kusaidu wacce kike son na je na saro miki kanta ita ce ainahin mahaifiyata,amma kuma boka Ardusa ne mahaifina ba Salimat ba, kuma a gidan sarki Kusaidu na taso a matsayin dan matarsa Salimat ta zamana cewa yana matukar kaunata fiye da komai a rayuwarsa."
Koda jin wannan batu sai Larziya ta cika da tsananin mamaki kawai sai ta rusa ihu kuma ta fashe da matsanaicin kuka, shima Hantaru sai ya ci gaba da kukan aka rasa wanda zai rarrashi wani 8 tsakaninsu.
Sai da rabin sa'a ta shude suna kukan kuma dayansu bai ce kala ba. Daga can sai Larziya ta mike tsaye ta juyawa Hantaru baya sannan ta budi baki ta ce, "Ya kai masoyina kayi sani cewa kaddara ta riga fata, ni kam har yanzu ina nan akan bakana domin matsayinka a wajen Zarifa ba zai sa na sauya ra'ayina ba na son cika burin mahaifiyata ba kuma ba zai sa na fasa zama da kai ba cikin soyayyar gaskiya da amana ba. Daga yau na baka wata shida kaje birnin Kisra ka dawo mini da kan Zarifa da kuma dukiyar mahaifiyata,idan ka dawo babu wadannan abubuwa biyu lallai aure ya haramta tsakanina da kai har abada".
Koda gama wannan furuci sai Larziya ta fice
daga cikin gidan gaba daya ta hau doki ta nufi
gidan Sarki a cikin wannan dare.
Shi kuwa Hantaru sai da ya jima zaune a kas dirshan yana tunani da kuka sannan shima ya mike tsaye ya fice daga cikin dakin ya nufi gidan Shurem kai tsaye.
A wannan lokaci dare ya raba sosai don haka Hantaru bai hadu da kowa ba akan hanyarsa face tsirarun kamnuka wadanda da zarar ya durfafesu suna jin kamshin jikinsa sai su watse domin sun san uban maza ne zakaran gas8.
Lokacin da Hantaru ya shigo cikin tsakar gidan Shurem sai ya kasa shiga cikin dakinse don haka sai ya zauna ya yi tagumi ya ci gaba da tunanin abin da ya fi kamata ya yi. Yana cikin wannan hali ne yaji an dafa kafadarsa ta baya.Cikin sauri ya juyo ya ga ashe Salima ce tsaye a kansa.
Cikin matukar mamaki Salimat ta dubi Hantaru ta ce, "Ya kai dana mene ne ya dawo da kai nan gida a cikin wannan dare? Ai yanzu kamata ya yi ace kana can tare da amaryarka kuna more amarcinku?".
Sa'adda Hantaru ya ji wannan tambaya dage bakin Salimat sai ya kasa bata amsa kawai sai ya rungumeta ya fashe da matsanaicin kuka.Al'amarin da ya matukar dugunzuma hankalinta
ke nan ta janye jikinta daga cikin na Hantaru suka fuskanci juna ta ce,"Wai shin mene ne yaa faru ne? Shin wani abu ne ya sami amaryar taka ko kuwa sabani kuka samu?'.
Hantaru ya sake yin shiru a karo na biyu ya kasa magana. Nan take ran Salimat ya 6aci, ta harzuka don haka sai ta dubeshi a lokacin da idanunta suka ciko da kwalla ta ce,"Hakika a yaune ka nuna mini cewa kai ba dan cikina bane!Yanzu ashe har ka manta da duk irin dawainiyar da nayi da kai ne tun kana jariri? Ni ce fa na shayar da kai kuma na ci fitsarinka da kashinka har ka girma ka zamo mutum. Akan wane dalili za ka 6oye mini wani abu da ke damunka? Ashe ba ni ce wadda ya kamata ta san dukkan sirrinka ba?Ashe ba ni ce wacce ya kamata ta baka shawara bisa al'amuranka ba?"
Koda Salimat tazo nan a zancenta sai ta fashe da kuka, sanann ta mike tsaye za ta juya da baya ta nufi dakinta. Koda ganin haka sai Hantaru ya mike zumbur! Ya ruko hannunta ta waigo ta dubeshi. Hantaru ya sa hannunsa ya share hawayen Salimat asnann ya ce, "Ki gafarceni ya ke mahaifiyata, ki yi sani cewa abin da zan gaya miki ne yana da nauyi, ina tsoron abin da zai biyi baya idan kika ji al'amarin".
Nan take Hantaru ya kwashe labarin duk abin
da ya faru tsakaninsa da gimbiya Larziya ya
zaiyane ma ta.
Ya yin da Salimat taji jawabin Hantaru sai gaba dayan jikinta ya kama karkarwa ta dinga layi daga tsaye kamar wacce ta sha giya ta bugu.Daga can ma sai ta yanke jiki ta fadi kasa sumammiya.Cikin firgici Hantaru ya kwala ihu ya tsugunna a kanta yana yi ma ta firfita.
A lokacin ne Shaulat da sauran mutanen gidan suka firfito a guje har suna dauko makamai domin a zatonsu barayi ne suka shigo, ko kuma abokan gaba ne suka kawo farmaki.
Koda suka ga ashe Hantaru ne a gaban Salimat yana yi ma ta firfita sai kowa ya cika da mamaki. Shaulat ta dafa kafadar Hantaru domin ta tambayeshi abin da ya faru, sai Salimat ta farfado.Kawai sai ta mike tsaye ta dubi Hantaru fuskarta a murtuke ta ce, "Daga yau babu sauran alaka ta uwa da da tsakanina da kai face kayi mini alkawarin cewar ba za ka bi umarnin da matarka ta baka bel"
Koda gama fadin hakan sai Salimat ta juya ta tafi izuwa cikin dakinta da sauri ta rufo kofa.
Hantaru ya ruga izuwa kofar dakin ya yi ta Kwankwasawa yana rokon Salimat da ta bude kofar amma sai ta ki. Al'amarin da ya baiwa Shaulat da sauran mutanen gidan mamaki ke nan.
Shaulat ta karasa kofar dakin Salimat itama ta rinka kiran sunarta domin ta bude kofar amma sai taki. Koda ganin haka sai Hantaru ya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment