Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

komai a duniya.Sai dai kash! Baka sami nasarar cika mini burina ba kuma baka da laifi ko kadan,murmushin da ka ga nayi maka dazu shi ne murmushin karshe tsakanina da kai, kuma shi ne na bankwana. Lallai ban ga amfanin zamana a duniya ba tun da na kasa cika alkawarin mahaifiyata wanda na yi rantsuwa da soyayyata a gareta a akansa. Kayi hakuri ya kai masoyina kuma ka gafarta min bisa tafiyar da zan yi na barka, ka sani cewa idan ma na zauna ba zan yi nisan kwana ba domin ciwon zuciya ne zai kasheni.
Da wannan furuci nake maka bankwana na karshe. Idan har akwai wata rayuwar bayan ta duniya ina fatan mu sake saduwa".
Koda gama fadin hakan sai gimbiya Larziya ta fito da hannayenta daga bayanta sai ga wata sharbebiyar wuka a hannunta. Koda
Hantaru ya hango wannan wuka sai ya falfalo da matsanaicin gudu domin ya hanata aikata abin da take nufi. Amma da yake bakin alkalami ya riga ya bushe kafin ya iso gareta da tazarar taku uku kacal, tuni ta soka wannan wuka a cikinta, kawai sai ta sulale kasa matacciya.
Hantaru ya fada kan gawar Larziya ya fashe da kuka, ko kadan ba a jin sautinsa kuma wanda babu hawaye.
Bayan Hantaru ya dade yana kuka sai ya zare wannan wuka daga cikin Larziya ya hau cakawa jikinsa. Abirka da jikin tsohon sadauki mai tarin sihirin tsafi sai wukar ta kasa hudashi. Nan fa Hantaru ya zama kamar mahaukaci ya rinka wawuro komai yana makawa a jikinsa don ya kashe kansa ya huta da bakin ciki amma duk abin da ya caka a cikin nasa sai ya ki tasiri.
A wannan lokacin babu kowa a gidan sarki domin gaba dayan mutanen gidan sun tafi gidan Shurem don yin gaisuwar mutuwar Salimat.
Nan take Hantaru ya dauki gawar Larziya ya koma da ita gidan Shurem inda ya iske
Sarki da sauran jama'ar gari,
Koda sarki ya hango Hantaru dauke da gawar Larziya sai ya fashe da matsanaicin kuka kuma nan take Kwakwalwarsa ta tabu ya kama surutai irin na mahaukata. Gaba dayan jama'ar da ke wajen sai da suka afshe da matsanaicin kuka saboda tsananin tausayin Hantaru da Sarki.
Sannu a hankali Hantaru yazo da gawar gimbiya Larziya kusa da kabarin mahaifiyarsa Salimat ya ajiye gawar. Kawai sai ya mike tsaye yaje inda dokinsa ke daure ya dauko takobin Saiful Lujara. Koda jama'a suka ga ya zare takobin daga cikin kufenta sai suka firgice suka kama guje-guje da iface-iface.Kawai sai Hantaru ya dubi jama'a ya yi wani dan guntun murmushi sannan ya caka takobin takobin ta lume ta faso gadon bayansa. Hantaru ya tafi kasa luu! Ya durkusa bisa guiwoyinsa ba tare da ya fadi kasa ba ya zama gawa. Amma har a wannan lokacin murmushi na fuskarsa bai guseh ba.
Faruwar hakan ke da wuya sai takobin Saiful Lujara ta zare kanta daga cikin Hantaru ta yi sama ta luluka izuwa cikin gajimare ta
6ace 6at! A sannan ne kuma gaba dayan jikin
Hantaru ya sandare ya zamo gunki.
Har yau, har kwanan gobe idan mutum yaje birnin Darul Mahabul ya ziyarci gidan Shurem zai ga sadauki Hantaru cikin siffar gunki ya durkusa a gaban kabarin Salimat da kabarin matarsa gimbiya Larziya da murmushi a fuskarsa..."
LOKACIN DA SARKI DUJALU ya zo nan a labarinsa sai ya ga idanuun
Hursiya sun cika sharkaf da hawaye saboda
tsananin tausayi.
Tsawon yan dakiku daya daga cikinsu bai ce uffan ba. Daga can sai Sarki Dujalu ya dubeta ya ce, "Ya ke 'yar uwata yanzu me kika fahimta a cikin wannan labari na Hantaru,kuma wane irin darasi kika samu?".
Koda jin wannan tambaya sai Hursiya tayi ajiyar zuciya ta ce, "Hakika na fahimci cewa a duniya babu wani abu mai hadarin gaske sama da soyayya, domin za ta iya sa mutum ya aikata abin da bai dace ba kamar yadda sarki Kusaidu ya hadiyi zuciya ya mutu saboda
ganin an kashe matarsa Zarifa da yadda Salimat ta sha guba ta mutu saboda mijinta Sarki Kusaidu ya mutu da kuma yadda sadauki Rabbasu ya murdewa kansa wuya ya mutu saboda ya fuskanci cewa ba zai taba samun masoyiyarsa ba Larziya. Uwa uba kuma shi ne,Hantaru wanda ya sallama rayuwarsa don kyautata wa masoyiyarsa amma sai gashi a banza ya kashe kansa bayan ya sha bakar wahala kuma ya sami daukakar da babu wanda ya sami kamarta a wannan zamani amma kuma daukakar bata amfane shi da komai ba.
Na yi koyi darusa da dama a cikin wannan labari, musamman akan, duk abin da mutum zai so to ya soshi saisa-saisa kada ya zurfafa.'Abu na biyu kada mutum ya bari zuciyarsa ta kawatu da son kudi ko matsayi da yawa domin.zai iya hallaka kowa domin ya sameta ko da kuwa dan uwansa na jinine kamar yadda Zarifa da Marifa suka taso a cikin kiyayyar juna alhalin sun kasance 'yan uwan juna na jini uwa daya uba daya.
Abu na uku mafi muhimmanci shi ne,daukar alkawari bisa abin da mutum bashi da tabbacin zai iya cikawa. Tun da farko inda
Hantaru bai dauki alkawarin zai yi duk abin da Larziya za ta umarceshi da yi ba da ba zai je birnin Kisra ba har yai aikin da zai zo yai nadamarsa ba, amma saboda idanunsa sun rufe akan soyayyarta sai ya amsa dukkan muradinta.
Ya kai dan uwana kayi sani cewa idan zan ci gaba da lissafo maka darasin da ke cikin wannan labari sai gari ya waye ban kare ba."
Koda jin wannan batu sai sarki Dujalu ya bushe da dariya ya ce, "Ai wadannan darussan ma kadan ne akan wanda ke cikin labarin sadauki Shaddadu na birnin Kufa da kuma labarin sadauki Hulkas na birnin Romaniya".
Koda jin wannan batu sai Hursiya ta goge hawayen idanunta da sauri ta dubi Sarki Dujalu cikin murmushi ta ce, "Ina rokonka da ka bani labarin sadauki Shaddadu na birnin Kufa domin na ji irin abubuwan al'ajabin da ke cikin tasa rayuwar".
Koda jin wannan batu sai sarki Dujalu ya sake bushewa da dariya a karo na biyu ya ce,"Daga kanki sama ki duba ki gani, mene ne wancan?".
Cikin sauri Hursiya ta daga kanta sama
sai ta ga ashc har alfijir ya keto. Al'amarin da ya matukar ba ta mamaki ke nan bisa yaddaa aka yi suka shafe sa'o'i masu yawa haka a zaune tana sauraron labari ba tare da ta gaji ba ko kuma barci ya dauketa ba."
Koda sarki Dujalu ya fahimci cewa Hursiya tayi mamaki matuka bisa tsawon lokacin da suka shafe yana ba ta labarin Hantaru, sai ya mike tsaye ya ce, "Ya ke 'yar uwata ki sani cewa labarin sadauki Shaddadu ya ninka na sadauki Hantaru yawa sau biyu,sai dai kawai na gajarce miki shi saboda haka sai mun sami isasshen lokaci anan gaba. Yanzu sai ki tashi da sauri ki koma can tantinki domin kiyi wanka kiyi kalaci nan da dan lokaci kadan wannan runduna tamu za ta ci gaba da tafiya domin mu isa tekun Bahar Sufiya akan lokaci".
Gama fadin hakan ke da wuya sai sarki Dujalu ya juya ya nufi inda tantinsa yake.Cikin sauri itama Hursiya ta mike tsaye ta ruga izuwa na ta tantin.
Ko rabin sa'a ba a yi ba gaba dayan rundunar su sarki Dujalu suka gama kimtsawa,aljanu suka kwashi mutane da dukkanin kayayyakinsu suka bude fuka-fukansu suka
Maza MIAUAVTIN ATIAT
tashi sama suka fara tsala matsanaicin gudu suna masu tunkarar tekun bahar Sufiya.
Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin sarki Dujalu da yar uwarsa "Hursiya bayan ya gama bata labarin sadauki Hantaru sun kuma kintsawa sun ci gaba da tafiya sun tunkari kogin bahar Sufiya don dauko takobin SAIFUL LUJARA.
SARKI MAHARAZ
AL'AMARIN RUNDUNAR Sarki
Maharaz kuwa, lokacin da suka baro
birnin Darul Mahabul sai suka wanzu suna
wata tafiya ta ban al'ajabi, wacce ta baiwa
kowa mamaki, dalili kuwa shi ne, saurin
tafiyar ya wuce misali, domin gani suke yi
kamar suna shafe tafiyar kwana guda a cikin
abin da bai kai rabin sa'a ba.
Shi kansa sarki Maharaz yana mamakin al'amarin amma da ya tuno da jawabin da ubangijinsa Darbuza ya yi masa cewar zai gajarce musu nisan wannan tafiya sai ya daina mamakin komai, hankalinsa ya kwanta.
Sadauki Inmal ko yaushe yana daf da keken dokin da Mulaifa ke ciki, baya yarda a
sami wata tazara a tsakaninsu don tabbatar da tsaron lafiyarta. Duk bayan 'yan dakiku kadan sai Mulaifa ta yaye labulen keken dokin ta leko wajen sun hada ido da Inmal gami da yiwa juna murmushi.
Haka dai aka ci gaba da wannan tafiya ba sassauci face idan dare ya yi a yada zango.Wani lokacin ma in dai akwai hasken farin wata ba a yada zango sai dai a ci gaba da tafiya.
Hakika masu iya magana sun yi gaskiya da suke cewa, "Idan ka ga ki gudu, to sa gudu ne bai zo ba'. Kai tsaye wannan runduna ta su Sarki.Maharaz ta rinka ratsa dazuzzuka tana wucewa, komai yawan 'yan fashi ko muggan dabbobin daji ko muggan aljanu da zarar sun jiyo takun sawun wannan runduna wacce ke haddasa karamar girgizar kasa saboda tsananin yawansu sai ka ga wadannan muggan halittu sun falfala da gudu sun nemi ramuka sun shige sun 6uya domin sun san cewa GABA DA GABANTA, aljani ya taka wuta.
Lokacin da wannan runduna ta iso cikin dajin Sauratul Auzur dama sarkin yaki Hibru da sarki Maharaz ne akan gaba, don haka sai
sarki Maharaz ya ja linzamin dokinsa ya tsaya cak. Nan take kuwa kowa ya yi koyi da shi,aka yi tsit tamkar babu mai numfashi a wajen.
Sarki Maharaz ya shaki numfashi sannan ya dubi gabas da yamma, kudu da arewa sannan ya daga kansa sama ya sauke ya dubi kasa. Kawai sai ya yi ajiyar zuciya ya ce,"Tabbas abokan gaban gabarmu sun wuce ta cikin wnanan daji kimanin kwanaki biyu rak!da suka wuce, kuma sun fafata kazamin yaki da daya daga cikin irin mugayen halittun da ke cikinsa.
Ya ku jama'ata kuyi sani cewa masifi da ke cikin wannan daji sun fi gaban tunanin bil'adama ko aljan, don haka ba lallai bane yawanmu, jarumtakarmu da karfin sihirinmu ya Kwace mu, amma tun da har abokan gabarmu suka samu nasarar wuce lallai ina sa ran cewa muna zamu iya wucewa,sai dai bai zamo lallai ba dukkaninmu mu iya wucewa ba a raye, don haka sai kowa ya gyara damararsa kuma ya yi iya kokarinsa domin ceton rayuwarsa".
Koda gama fadin haka sai sarki Maharaz ya dubi sarki yaki Hibru ya ce, "Ya kai
abokina ai sai ka wuce kan gaba domin a wannan dajin babu batun karfin sihiri sai dai amfani da tsagwaron karfin damtse da hikima gami da basira".
Da jin wannan batu sai Hibru ya yi murmushi sannan ya Kwalawa Inmal kira.Inmal ya zaburi dokinsa ya rufa inda Hibru da sarki ke tsaye. Hibru ya dubi Inmal ya ce, "Ina son ka kasance kusa da ni." Inmal ya gigirza kai alamar cewa ya bi umarni. Nan take Hibru ya sakarwa dokinsa linzami ya wuce gaba,cikin sauri Hibru ya take masa baya sannan sarki da sauran jama'a.
Koda fara wannan tafiya a cikin dajin Sauratul Auzur sai kowa hankalinsa ya tashi ganin irin yanayin dajin yadda komai a cikinsa ya kasance a cikin siffar ban tsoro, sannan kuma tunda suka fara tafiya a cikin dajin ba su ga halitta ko daya ba koda kuwa kananan Kwari da tsuntsaye, kuma basa jin sautin komai face sautin takun sawun dawakansu da rakumansu.
Sai da aka shafe sa'a guda ana tafiya ba a ga komai ba, kwatsam! Sai aka yi kicibus da gawar katuwar halittar nan wacce ta danne
sarki Dujalu aka rasa yadda za a yi a zaroshi daga karkashinta har sai da tsoho Shurkaib ya zo da shawarar yadda za a iya kubutar da shi.
Koda ganin wannan halitta sai aka yi cirko-cirko ana kallonta cikin tsananin al'ajabi bisa ganin tsananin girmanta da siffarta. Nan take sarki Maharaz ya sauka daga kan dokinsa ya zo gaban halittar ya tsaya, kawai sai ya dafa gawar halittar da hannunsa na hagu sannan ya rintse idanunsa. Nan fa ya rinka ganin duk abubuwan da suka faru tsakanin halittar da rundunar su sarki Dujalu tun daga lokacin da suka fara artabu da halittar har izuwa lokacin da sarki Dujalu ya sami nasarra kasheta ta danneshi kawo izuwa sa'ar da aka zaroshi daga karkashin dabbar da Kyar.
Gama ganin wannan al'amari ke da wuya sai sarki Maharaz ya bude idanunsa ya dubi Hibru ya ce,"Anan gaba kadan zamu iya haduwa da wata muguwar halittar mai kama da wannan. Idan har muka sami nasarar hallakata ba zamu sake haduwa da komai ba har mu fita daga cikin wannan daji".
Koda jin wannan batu sai Hibru ya girgiza kai sannan ya zare takobinsa. Da ganin haka
sai shima Inmal ya zare tasa. Ganin aka ne ya sa gaba dayan sauran Dakarun suka kama zare takubbansu. Karar zare takubban nasu ya cika dajin gaba daya ya amsa kuwwa. Ba tare da 6ata lokaci ba aka ci gaba da ratsa dajin.
A wannan lokaci kowa ka dubaa sai ka ga ba a cikin nutsuwa yake ba saboda fargaba da tsoron abin da za a iya haduwa da shi. Sai da aka sake shafe sa'a guda ana tafiyar sannan kwatsam aka yi arba da wani garkeken dodo mai tsananin tsawo, fadi da kauri. Saboda tsawon dodon ya kere gaba dayan bishiyoyi,duwatsu da tsaunikan da ke dajin.
Dodon na da Kwala-Kwalan idanuwa jajaye kamar an gasa dan buda a cikin wuta,kúma girmansa ya kai na kwan jimina. Yana da wawakeken hanci tamkar an bude kofar gari. Fadin bakinsa kuwa da zurfinsa tamkar rijiya hakar mutanen farko. Saboda fadin dodon ya cika hanyar gaba daya babu ta inda za a iya wuce face ta karkashin kafafunsa da ya dan warasu.
Gaba dayan jikin dodon a murde yake,kuma kwarin fatar jikinsa tamkar da dutse aka yi ta. Jikin nasa duka a lullube yake da gashi,
-
kuma wani irin gashi ne mai tsawo da tsini tamkar allurai aka lillika.
Koda dodon ya yi wani irin gurnani sai gaba dayan mutane da aljanun rundunar suka firgice suka dimauce. Da yawansu basu san sa'adda suka saki makamansu kasa ba suka juya da baya da gudu. Kai ba ma su ba, hatta dawakai da rakuma firgicewa suka yi suka tarwatse suka kama gudu a cikin dajin.
Wasu a garin gudun ne ma suka rinka fadawa cikin mugayen ramuka suna hallaka,wasu suka rinka fadawa kan kayoyi da itatuwa suna cakewa. Wadanda kuwa basu sami damar guduwa ba sai suka rinka zubewa kasa sumammu.
Sarki Maharaz,Hibru da Inmal ne kadai basu firgice ba amma suma sun tsorata da ganin wannan dodo kuma sai aka rasa wanda zai karasa inda dodon yake.
Lokacin da dodon ya ga mutum uku rak!A gabansa tamkar an ajiye kadangaru a gaban mikiya, sai shi kansa ya cika da mamakin su Hibru, kawai sai ya tsaya yana kallonsu suma suna kallonsa jikinsu na tsuma.
Gimbiya Mulaifa kuwa, lokacin da jama'a
suka firgice, sai dawakan keken dokinta suka juya da baya da gudu a dimauce suka nufi wani rami mai zurfin gaske. Mulaifa ta rinka Kwala ihu tana neman a taimaka mata, amma da yake iface-iface ya yi yawa a wajen babu wanda ya tuna da al'amarinta tun da nafsi-nafsi ake yi. Ai kuwa sai dawakan suka fada cikin wannan rami, karshen keken dokin ne ya makale a jikin wani dutse mai gwafa daga sama ya kama reto. Tuni a wannan lokaci gimbiya Mulaifa ta suma a cikin keken dokin da ke reto a sama sakamakon tsananin razanar da tayi bisa ganin wannan rami mai zurfi da ta fada.
Tsawon 'yan dakiku ana kallon-kallo tsakanin wannan dodo da su Hibru,amma sun rasa abin da ya kamata su yi. Daga can sai Hibru ya yi ta maza ya rugo da gudu izuwa kan dodon. Dodon ya kawo masa mangari da hannunsa guda. Cikin zafin nama Hibru ya sunkuya kuma ya yi alkafira a kasa a karkashin Kafafun dodon, a lokacin da hannun dodon ya bugi iska ya tafi ya share wadansu manyan bishiyoyi guda bakwai da ke tsaye a jerc. Gaba dayan bishiyoyin sai da suka
tun6uko daga cikin Kasa har jijiyoyinsu suka zube kasa saboda tsananin karfin dantsen dodon. Kafin dodon ya juya bayansa inda Hibru yake sai Hibru ya dankara masa sara,take tartsatsin wuta ya tashi sakamakon haduwar takobin da gashin jikin dodon. Kawai sai Hibru ya ga hayaki na tashi a gaba dayan jikin takobin tasa, kuma ko ina a jikin takobin ya huje saboda tsinin gashin dodon ne ya caccaketa.
Koda dodon ya juya bayansa ya yi arba da Hibru sai ya kai masa cafka. Hibru ya yunkura domin ya goce, amma sai dodon ya sami nasarar dankarsa kawai sai ya dagoshi sama ya wangame bakinsa zai jefashi ciki ya lankwame.
Koda Inmal ya hango abin da ke shirin faruwa ga mahaifinsa sai ya falfala da matsanaicin gudu irin wanda bai taba yi ba a rayuwarsa kuma ya daka wawan tsalle ya dira akan cinyar dodon ya kama kafarsa ya dinga hawa samansa tamkar kadangare na hawa bango.
Kafin dodon ya jefa Hibru a cikin bakinsa tuni Inmal ya isa kan kafadar dodon ya caka
masa takobin a cikin katuwar Kwayar idonsa.B& shuri dodon ya saki Hibru ya fado kasa kuma yá kurma ihu irin nasu na dodanni a lokacin da Kwayar idon nasa ta fashe ruwan jini ya balle tamkar an bude IDANTYAR RUWA®
Nan fa dodon ya haukace ya rinka kai naushi, bugu da taku da hannaycnsa da Karafinsa ya zamana ccwa yana tarwatsa bishiyoyi da duwatsun dajin suna fashewa da ratattakewa. Duk inda dodon ya kai takau da kafarsa sai ka ga kasa ta rufta tayi rami zururu.In ba don Inmal na da matukar zafin nama ba da tuni dodon ya tattakeshi shi da Hibru amma sai Inmal ya suri Hibru tamkar ya suri dan yaro ya goyashi a bayansa ya falfala da mzteznaicin gudu suka kasa tsere da dodon.Dama:tmi shima sarki Maharaz ya cika wandonsa da iska ya tashi sama da karfin sihiri ya ruga izuwa cikin daji.
Inmal ya ci gaba da gudu iya karfinsa amma da ya waigo sai ya ga wannan dodo daf da shi. Babban abin da ya fi tayarwa da Inmal hankali shi ne, takun kafafun dodon bisa kasa yana haifar da girgizar kasa a dajin gaba daya,
kafin Inmal ya isa wurin ma sai ya ga kaser gabansa ta zabtarc tayi rami, sai ya daka wawan tsalle ya tsallake ramin.
Shi kuwa dodon komai zurfin rami da fadinsa da ya daga kafarsa daya sai ya shallakeshi.
Lokacin da Inmal ya fara wannan gudu ne ya lura da halin da jama'arsu suka shiga,kawai sai gimbiya Mulaifa ta fado masa a rai, nan take Inmal yaji dukkan tsoro ya gushe dage zuciyarse,kawai sai ya ga wamman gudun da yake yi bashi da wani amfani gwara ma ya tsaya ayi dik abunm da za a yi.
Koda gema aiyana hakan sai Inmal ya yiwa kafaraa birki ya tsuginna kasa ba zato.Ai kuwa sai wannan dodo ya shallakeshi bai sani ba. Cikin tsananin zafm nama Inmal ya yi jifa da Hibru can gefe daya samnan ya sake daka tsalle ya haye kan dodon ya rinka gudu a kansz kamar yadda ya yi dazu domin ya iss kan kafadarsa.
Koda dodon ya fahimci nufinse sai ya rinka kai masa wawan duka da hanaunsa,shi kuwa Inmal ya ringa tsalle yana gocewa da kauccwa yana ta tsallc-tsalle a kansa. Abin da
ya baiwa Inmal mamaki shi ne, yadda wannan gashi na jikin dodon mai tsini kamar kayoyi bai sossokeshi ba.
Abin da Inmal bai sani ba shi ne, akwai tsumin maganin kaifi da tsini a jikinsa, kuma tun yana jarir mahaifinsa Hibru ya rinka shayar da shi wannan tsumi.
Hibru na zaune a kasa dirshan yana kallon wannan gumurzu da ake yi tsakanin dodo da Inmal. Al'amarin da ya matukar bashi mamaki ke nan, domin ya san cewa shi kansa ba zai iya wannan bajinta ba wacce Inmal ke yi domin zafin namansa ya wuce gaban kwatance.
A dai-dai waman lokaci ne sarki Maharaz ya baiyana daf da Hibru shima ya zauna kusa da shi yana kallon abin da ke faruwa.
Sai da aka shafe sa'a uku ana bakin gumurzu tsakanin wannan dodo da Inmal,babu irin kokarin da dodon bai yi ba akan ya make Inmal ko ya damkeshi da hannu amma sai ya kasa saboda tsalle-tsallen da Inmal ya dinga yi a kansa tamkar dan biri akan bishiya.
Sai da Inmal ya galabaitar da dodon sosai sannan ya sami nasarar sake soke daya idon ya fashe. Wannan karon da dodon ya wangame
bakinsa ya kwarara ihu sai da gaba dayan bishiyoyin dajin suka kakkarye suka zube Kasa. Kuma wani irin feshin wuta ne ya rinka fita daga bakinsa yana haddasa gobara.Al'amarin da ya dugunzuma hankalin su sarki Maharaz ke nan sai da sarki Maharaz ya yi amfani da karfin sihiri wajen kashe wutar.
Lokacin da wannan dodo ya zama makaho wato duk idanun nasa biyu Inmal ya fasa su sai ya kara haukacewa ya rinka duka da fatali da komai, wato kan mai uwa da wa bi.Bai Kyale duwatsu da bishiyoyin da suka farfado bama. Nan da nan ya hautsina dajiin gaba daya. Ba shiri sarki Maharaz, Hibru da Inmal suka falfala da gudu suka bar inda dodon yake suna gudu suna waigen halin da dodon yake ciki. Sai da suka yi dan nisa daga inda yake sannan suka tsaya suna hangensa..
Dodon bai daina tagagi da walagigi ba har sai bayan sa'a guda sannan ya yanke jiki ya fadi kasa rikica! Kamar katon tsauni ya fada cikin teku domin sai da dajin gaba daya ya yi girgiza.
Da ganin abin da ya faru sai sarkin yaki Hibru ya cire kambun sarautarsa na sarkin yaki
ya mikawa Inmal ya ce, "Ya kai dana hakika kaine ka cancanci da wannan kambu, amma ba ni ba".
Cikin matukar mamaki Inmal ya dubi Hibru ya ce, "Haba ya kai Abbana ya za a yi na daura kambunka alhalin kana raye a doron kasa? Ba zan iya ba"
Da jin haka sai sarki Maharaz ya karbi kambun daga hannun Hibru ya daurawa Inmal da kansa a damtsen hannunsa ya dubeshi cikin murmushi ya ce. Tabbas mahaifinka ya yi gaskiya, kaine kafi cancanta da wannan kambu. Ya kai Inmal ka yi sani cewa ko a cikin tarihin sadaukan da zamaninsu ya gushe ba a taba samun sadauki mai karancin shekaru irin naka da ya yi irin wannan bajinta ba.".
Gama fadin hakan ke da wuya sai ga wadansu dakarun sarki sun rugo garesu da gudu a kasa suna haki. Da isowarsu sai suka zube kasa, dayansu ya bude baki da kyar ta ambaci sunan gimbiya Mulaifa yana mai nuni da hannunsa izuwa ga hanyar da suka fito..!
Kafin kowa ya ce wani abu tuni Inmal ya falfala da azababben gudu ya bi hanyar da aka nuna masa. Yana cikin gudun ne ya hango keken dokin gimbiya Mulaifa a saman wannan rami mai zurfi, keken dokin na reto saura kiris ya subuce zuwa kasa.
A wannan lokaci Mulaifa ta farfado daga dogon suman da tayi, ta rinka kwala ihu.Koda Inmal ya jiyo ihun Mulaifa sai ya kara karfin gudunsa har ma yana daka tsalle yana kara dira gaba. A dai-dai lokacin da ya yi tsallen karshe kafarsa ta dira akan bakin ramin, kuma a sannan ne keken dokin ya subuce ya yi kasa zai nutse izuwa karshen ramin. Nan take Inmal ya sake daka tatsalle ya ruko keken dokin da hannu daya sanann ya ruko dutsen da ke saman ramin da daya hannun nasa sai gashi keken dokin na reto,shima Inmal yana reto a sama a lokacin da Kwanjin hannunsa ya kumbura, jijiyoyin jikinsa gaba daya suka tashi suka yi burdun-burdun. A dai-dai wannan lokaci ne gimbiya Mulaifa ta daina ihu.' Tana daga cikin keken dokin sai ta kurawa Inmal idanu kawai ta ta kame kuma ta kasa yin magana saboda tsananin mamakin irin wannan" gagarumar bajinta da ya yi.
Kwatsam! Sai ga su sarki Maharaz sun iso
wajen da gudu, sannan sai ga sauran gaba dayan jama'ar rundunar. Duk wanda ya iso ya ga Inmal a sama yana reto kuma yana rike da keken doki da hannu daya sai ya kame kamar gunki saboda tsananin al'ajabi. Abin mamakin shi ne, wai shin wane irin karfi ne da Inmal har da ya iya rike keken doki da hannu daya alhalin dawakai uku ne a jikin keken dokin,nauyinsu ma kadai ya isheshi bare bare kuma ga nauyin shi kansa keken dokin wanda aka yi shi da karafa masu nauyi.
Koda isowar sarki Maharaz ya

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment