Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsugunna a kofar dakin ya yi ta rusa kuka kamar ba zai daina ba. Babu irin rarrashin da Shaulat bata yi masa ba amma sai ya ki yin shiru bare ta tambaye shi abin da ke faruwa.
Koda ganin haka sai Shaulat tayi tafiyarta izuwa cikin turakarta suma sauran mutanen gidan sai suka koma cikin dakunansu suka rufe kofofinsu.
Sai da alfijir ya keto Hantaru bai tashi daga bakin kofar Salimat ba kuma bai daina kuka da rokon ta bude masa kofar ba amma sai Salimat tayi biris da shi. Lokacin da Hantaru ya tabbatar da cewar Salimat ba za ta saurareshi ba sai ya mike tsaye ya shiga cikin dakinsa ya bude wata katuwar akwati ya dauko ajiyarsa ta takobin Saiful Lujara wacce ke lullube a cikin mayafi. Hantaru bai sake daukar komai ba a cikin dakin kawai sai ya fice daga cikin gidan ya kwanto doki guda daga cikin bargar dawakai ya hau kansa ya kama tafiya ba guzuri babu tanadin komai.
HANTARU YA NAUSA cikin daji ya rinka tafiya ba ji ba gani, dare da rana
ko yaushe takobin Saiful Lujara na rataye a bayansa.Duk sa'adda ya gaji sai ya yada zango a duk inda ya ga dama, idan kuma yaji yunwa sai ya yi farauta a cikin daji ya samo abin kalaci.
Haka dai Hantaru ya ci gaba da tafiya yana ratsawa ta cikin dazuzzukan masu mugun hadari,amma bisa mamaki sai Hantaru ta ga ko sau daya bai hadu da wata muguwar dabba da ta durfafeshi,kai ko aljanu idan suka hangoshi daga nesa sai su tarwatse su kama guje-guje suna neman maboya.Idan kuwa riskarsu ya yi tsulum sai su kama yi masa sujjada suna tuba da neman gafara tamkar sun ga mutum a gabansa. Al'amarin da yai matukar bashi mamaki ke nan.
Abin da bai sani ba shi ne, ba komai ne ya janyo hakan bs face wannan takobi ta Saiful Lujara ds ke rataye a bayansa.Sirrinta shi ne, in dai mutum na tare da ite duk irin halittar da ganshi sai ta ganshi firgice te razana ainun walau mutum ko dabba ko dodo.
Sannu-sannu darare na shudewa rana na wucewa har Hantaru ya shafe wata uku yana tafiya har ya iso birnin Kisra. Da shigarsa cikin garin sai ya sauko daga kan dokinsa ya daure dokin a jikin wata bishiya sannan ya cire takobin saiful Lujara daga cikin mafiyafinta kuma ya zareta daga cikin kufenta ya ruketa tsirara ya nufi gidan boka
Ardusa kai tsaye fuskarsa a murtuke har tana yatsina saboda fusata,kuma jikinsa na tsuma. Duk inda ya ratsa jama'a suka ganshi sai ka ga ana tashi ana rugawa izuwa cikin gida ana kulle kofofi saboda ganin Hantaru a cikin mugun yanayi, kuma ga babbar takobi mai daraja a hanannsa.
Boka Ardusa na kwance a cikin turakarsa yana faman shara barci abinsa, kawai sai yaji turakarsa ta cika da hayaniye. A firgice ya farka ya mife zaune domin wannen ne karo na farko arayuwarsa da ya taba jin hayaniya a turakarsa.Boka Ardusa na bude idanunnsa sai ya yi arba da dukkanin hadimansa na aljanu sun cika dakin jikinsu na kyarma kamar ace kyat! su tsure da gudawa.
Cijin fushi boka Ardusa ya daka musu tsawa ya ce, "Ina delilin shigowarku nan turakata ba tare da izinina ba? Lallai gaba dayanku sai kun dandana kudarku domin kun sa na farka a lokacin da na ke cikin yin barcina mai dadi".


Koda jin wannan batu sai shugaban hedimansa ya zube a Kasa gaban boka Ardusa ya ce, "Ya shugabana ai yau mu da kai duk muna cikin mummunan bala'i ne. Mun zo gareka ne domin ka gaggauta nemo mana wajen buya har kai kanka kuwa, ka sani cewa a halin yanzu ga jarumi Hantaru can ya durfafo wannan gida naka dauke da takobin Saiful Lujara. Kuma ya taho ne domin
ya hallakaka bisa cin amanar sarki da kayi ka
kwanta da matarsa aka sami cikinsa."
Koda jin wannan batu sai boka Ardusa ya daka tsalle sama ya tumu da kasa. Idanunsa suka zezzaro,kawai sai ya ruga da gudu izuwa cikin dakinsa na halwa domin ya duba wadansu ababan dogaronsa na tsafi. A wannan lokaci ne wadannan hadiman aljanu nasa da ya baro a turakarsa duk suka tarwatse suka tashi sama suka rinka tsala gudu cikin dimauta ba tare da sanin inda suka dosa ba.
Boka Ardusa ya yi sauri ya debo dukkanin guraye da layu na tsafinsa sannan ya dauko kayan yakinsa ya rugo waje da gudu daga cikin dakin da nuim shima ya tashi sama, kawai sai ya ga Hantaru tsulum! A gabansa.
Boka ardusa ya yunkura da nufin ya shafi weta laya da ke wuyansa, sai Hantaru ya sa takobin Saiful Lujara cikin zafin nama ya sare kan boka Ardusa. Kan yai tsalle sama ya rabu da gangar jikin, kawai sai hantaru ya daga daya hannun nasa ya cafo gashin kan Ardusa a lokacin da gangar jikin ta sulale kasa ta fadi.Kawai sai Hantaru ya juya juya ya fice daga cikin gidan ya durfafi gidan sarki Kusaidu.
Sarki Kusaidu na kwance bisa gado yana jinyar rashin lafiya, kawai sai wani hadiminsa ya
shigo cikin turakar da gudu yana haki, ya fadi Kasa ya ce, "Ya shugabana gari fa babu lafiye".
Cikin Karfin hali Sarki ya dubeshi ya ce Yaki ne ya taso mana yanzu-yanzu?". Hadimi ya ce, "Ai abin da ya taso yanzu yafi karfin yaki domin danka ne Hantaru ya dawo rike da takobin SAIFUL LUJARA, har ma yaje gidan boka Ardusa ya yanko kansa.
Kode jin wannan batu sai sarki Kusaidu ya mike zumbur! Cikin tsananin farin ciki tamkar bai tabe yin wani ciwo ba ya ruga waje da gudu yana mai bude hannayensa yana kwalawa Hantara kira A wannan lokaci gaba dayan Dakarun gidan sun dimauce sai guje-guje suke da iface-iface suna neman inda za su shiga su buya domin sun san cewa basu issa su tari Hantaru ba bare har su hana shì yìn abin da ya zo yi.
Shi kuwa sariki Kusaidu ko kadan bai damu da wannan hali da dakarunsa suka shiga ba kawai burinsa shi ne ya ga ta inda Hantaru zai 6ullo ya tareshi su rungume juna yaji dumninsa kirjinsa.
Sarki Kusaidu ya ci gaba da gudu a cikin gidan sarautar ya shiga wannan sako ya fita ya shiga wancan loko yana ta Kwalawa Hantaru kira,amma bai ganshi ba.
Shi kuwa Hantaru lokacin da ya shigo ciki
gidan sarautar sai ya ruga lzuwa cikin wani surfuki inda babu wanda zai yi zaton shigarsa wajen sannan ya rikide ya zama gashin dawisu ya nufi dakin gimbiya Zarifa


Duk wannan hayaniya da ke faruwa a cikin gidan sarauta Zarifa bata san da ita ba, domin tana can cikin kewayenta a cikin baho tana wanka a cikin ruwan kumfa mai kamshi.
Tana cikin wannan hali ne ta ga wani gashin dswisu mai kyau ya shigo cikin turakar. Koda ganin gashin dawisun sai ta tsaya cak ta kura masa idanu, daga can sai ta bushe da dariya ta ce, "Lale marhabun da dana na cikina wanda ya zo domin ya sare kaina ya kaiwa matarsa".
Kode jin wannan batu sai wannan gashin dawisu ye rikide ya zama Hantaru sai gashi tsaye a gabanta rike da kan boka Ardusa a hannun hagu jini na diga a jikin ken. A hannunsa na dama kuwa takobin Saiful Lujara ce sai sheki da walwali take ta haskake bandakin gaba dayansa tamkar an kunna fitilu a cikinsa guda dubu.
Cikin sanyin jiki da matukar mamaki Hantaru ya dubi Zarifa a lokacin da hawaye ye zubo masa ya ce, "Ya ke Ummina ina dalilin da ya sa kika ci amanar sarki Kusaidu kika sadu de bokansa aka samu cikina? ya ya aka yi kika ganeni a yanzu da na shigo cikin wannan kewaye a cikin
siffar gashin dawisu?"
Koda jin wadannan tambayoyi guda biyu sai Zarifa ta sake bushewa da dariya a karo na biyu sannan ta tsuke fuska ta ce, "Ya kai dana ina son ka sani cewa in dai don biyan bukatar rai, mutunci da dukiya ba a bakin komai suke ba, saboda bukatar cika burin zuciyata ne na ci amanar sarki na sadu da bokansa aka sami cikinka kuma na bashi kai a matsayiin dan cikinsa har ya soka fiye da komai a duniya.Tabbas burina ya cikan tun da na sami nasarar kawar da 'yar uwata Marifa domin na mallaki dukiyar da mahaifinmu ya bar mana ni kadai.Sai dai kash! Har yanzu ban mallaki dukiyar ba, bakin cikin hakan ne ya sa naji bana tsoron mutuwa don haka idan ka kasheni a yanzu zan kasance a cikin farin ciki tum da burina bai gama cika ba a duniya. Abin da zan sanar da kai shi ne, kaima baka isa ka shiga kogon da aka ajiye wannan dukiya ba domin ka debota ka kaiwa matarka Larziya domin a lokacin da na fahimci cewa ba zan iya mallakar dukiyar ba face na samo takobin Saiful Lujara sai hankalina ya dugunzuma na baza manzanni a duniya suka rinka ziyartar manyan bokaye
akan yadda zan iya kona wannan dukiya gaba dayanta yadda har abada babu wanda zai moreta. Sai da manzannina suka shekara goma sha biyar suna wannan aiki sannan suka samo mini sihirin da na sami damar kona dukkan wannan dukiya ta zama toka. Yanzu haka idan ka shiga inda dukiyar take za ka iske babu komai a ciki face toka.
Game da tambayarka ta biyu kuwa, ina son ka sani cewa komai sammakonka wani a tafe ya kwana. Saboda tsananin yawo na a cikin duniya wajen bokaye sai da na mallaki dukkan sihirin tsafi na duniya wanda ban samu ba kawai shi ne wanda ke jikin takobin Saiful Lujara. Ka ga ke nan a duk matsafan duniya yanzu babu wanda ya fini karfin sihiri face kai,don haka duk irin yanayin da mutum zai juye izuwa wata siffar da na kalleshi sai na ganshi a zahirin siffarsa ta gaskiya. Yanzu gashi a matsayinka na dan da na haifa a cikina baka kaunata ka tsaneni kamar yadda ka tsani mutuwarka. Dukiyar da na ke ta hankoron mallaka tafi karfina ina ji ina gani, mijina da yake mutuwar sona fiye da komai a duniya na ha'inceshi na ci amanarsa kuma ya san duk
abin da na aikata amma saboda tsananin son da yake yi mini ya danne komai a zuciyarsa ko a fuskarsa bai taбa nuna mini ba".
Sa'adda zarifa tazo nan a zancenta sai idanunta suka ciko da Kwalla hawaye ya fara zuba sannan ta ci gaba da kallon Hantaru tana mai cewa,"Ya kai dana yanzu mene ne amfanin zamana a duniya? Ina ribar da na samu tun da har yanzu abin da na shuka ban girbi komai ba? Hakika nayi nadama tun daga lokacin da 'yar uwata Marifa ta fada mini maganganun cewar za ta rabu da ni ba a son ranta ba duk da cewa bama son juna saboda ko babu komai ni jinin ta ce.
Duk sa'adda na tuno da kalamanta sai nayi kuka na zubar da hawaye, yanzu ne na gane cewa duniya ta rudeni na bi son zuciyata nayi biyu babu don haka yanzu bani da sauran buri a duniya wanda ya fi na bi 'yar uwata Marifa izuwa inda ta tafi. Ina tabbatar maka da cewa idan ma ka tafi yanzu baka kasheni ba sai na kashe kaina. Bakin cikina shi ne na ri ga na lalata maka taka rayuwar domin kaima ba za ka taba samun sukuni ba da kwanciyar hankali."
Lokacin da Zarifa ta zo nan a zancenta sai jikin Hantaru ya yi sanyi, yaji ba zai iya sare kanta ba, kawai sai ya fashe da kuka cikin tsananin bakin ciki.
Zarifa ta dubeshi ta ce, "Maza ka yi abin da ya kawoka domin wannan kukan ba zai fishsheka ba. Idan kuma ba za ka iya kashe ni ba to ni ka bani takobin Saiful Lujara na sare maka kai sannan na kashe kaina.'
Kafin Hantaru ya ce wani abu sai Zarifa ta fito daga cikin bahon wakan ta fisge takobin Saiful Lujara daga hannunsa ta daga sama za ta sare masa kai. Cikin zafin nama Hantaru ya cafki takobin ya Kwace takobin sannan ya datse ma ta wuta, sai ga kanta na lilo a hannunsa.
A dai-dai wannan lokacin ne sarki Kusaidu ya banko Kofar kewayen ya shigo. Da shigowarsa ya yi arba da kan Zarifa a hannun Hantaru jini na zuba sannan ya ga gangar jikinta kwance a Kasa faca-faca da jini. Koda ganin wannan al'amari sai sarki Kusaidu ya hadiyi zuciya nan take ya fadi kasa matacce.
Hantaru ya kwarara uban ihu ya fadi kan gawar sarki Kusaidu ya rungumeta kuma ya
fashe da matsanaicin kuka.
Sai da aka kwana goma sha bakwai ana kuka da bakin cikin mutuwar sarki Kusaidu a cikin birnin Kisra. Shi kuwa Hantaru saboda tsananin bakin ciki ma kasa zama ya yi ayi jana'izar Sarki da shi. A wannan rana ya shirya ya tafi kogon da mahaifin su Zarifa ya 6oye wannan dukiya.
Bisa tarihi tun bayan mutuwar mahaifin su Zarifa ba a taba samun wani mahaluki da ya shige shi ba walau mutum ko aljana, amma a wannan rana sai ga shi Hantaru ya sa takobin Saiful Lujars ya sare wata bakar kofa ta karfe a jikin kogon. Take kofar ta rufta ciki ta fadi Fasa.Duk da cewa kogon a can bayan gari yake sai da aka jiyo karar faduwar kofar a can cikin bimin Kisra, saboda girman kofar da nauyinta domin inda Kartin aljanu majiya karfi guda dubuc casa'in za su hada karfi ba za su iya banke kofar ba har su kaita kas. Kai sabods karfin sihirin da ke jikin kogon ko fara ce ta gifta ta kusa da kogon sai ta fado kasa matacciya bare mutum ko aljan.
Bayan Hantaru ya banke kofar ta fadi kasa sai ya kunna kai cikin kogon ba tare da
fargabar komai ba. Duk da cewa kogon na da tsananin duhu ko tafin hannu mutum ba ya iya gani amma da shigar Hataru cikin kogon sai ya haskake gaba daya albarkacin hasken takobin Saiful Lujara.Kawai sai ya ga babu komai a cikin kogon face bakar toka tuli a ko ina, sama da kasa. Koda ganin wannan al'amari sai Hantaru ya durkusa kasa bisa guiwoyinsa ya fashe da kukan bakin ciki. A sannan ne ya gasgata maganar Zarifa cewar ta gama kona dukiyar gaba dayanta amma a sa'adda ta gaya masa sam bai yarda ba.
Sai da Hantaru ya dade a durkushe a kasa yana kukan takaici da bakin ciki. Abin da ya fara fado masa a zuciya shi ne ya ya Larziya za ta karbeshi idan ya koma gareta babu wannan dukiya sai kan mahaifiyarsa Zarifa?"
Haka dai Hantaru ya ci gaba da tunani mai zurfi a zuciyarsa ya tuna cewa shi fa yanzu ya rasa babban masoyinsa a duniya wato sarki Kusaidu, wanda ya rage masa kawai mutum biyu ne, daga Salimat wacce ta shayar da shi ta reneshi a matsayin dan cikinta sai kuma matarsa Larziya wadda take kuma take &matsayin 'yar uwarsa ta jini ta hanyar haduwar
jini tsakanin mahaifiyarsa Zarifa da
mahaifiyarta Marifa.
Idan Salimat taji cewar Sarki Kusaidu ya mutu sakamakon ganin gawar Zarifa da wane matsayi za ta dubeshi? Kawai sai Hantaru ya aiyana a ransa ya ce, "Lallai ba zan baiyana ma ta gaskiyar al'amari ba har sai ta dawo birnin Kisra da kanta taji abin da ya faru".
Bayan Hantaru ya gama Kulle-Kulle a zuciyarsa sai ya mike tsaye cikin sanyin jiki da tsananin damuwa da bakin ciki ya fice daga cikin kogon gaba daya ba tare da bata wani lokaci ba ya hau dokinsa ya ci gaba da tafiya ba sassauci ya durfafi birnin Darul Mahabul.
KAMAR YADDA ya shafe watanni yana tafiya a lokacin zuwansa birnin Kisra haka ya sake shafe wadannan watanni ya dawo birnin Darul Mahabul, kuma a wannan karon ma takobinsa bata sha jini ba, domin babu wani abu da ya kawo masa farmaki walau mutum, aljan ko dabba har ya iso kofar birnin Darul Mahabul.
Da zuwansa bakin kofar birnin sai ya ja
linzamin dokinsa ya tsaya cak! Yana tunani.Abin da ya fara fado masa a rai, ina ya kamata ya fara zuwa? Shin wajen mahaifiyarsa Salimat zai je ko kuwa gidan sarki zai wuce domin ya ga masoyiyarsa abar begensa dare da rana wato matarsa kuma 'yar uwarsa Larziya?
Nan take Hantaru yaji zuciyarsa ta cika da tsananin farin ciki,domin ya san cewa a yau ne zai more amarcinsa da Larziya, amma da ya tuna cewa a cikin abubuwa guda biyun da Larziya ta ce ya zo ma ta da su guda daya kacal ya zo da shi, wato kan mahaifiyarsa Zarifa sai hankalinsa ya dugunzuma ainun yaji zuciyarsa ta fara bugawa da karfi kamar za ta tsage ta fado kasa ba don komai ba sai don tunanin cewa ba lallai bane Larziya ta amince da shi ba kuma za ta iya kashe kanta bisa bakin cikin rashin cika burin mahaifiyarta.
Hantaru ya tuno da batun Salimat, take yaji kirjin nasa ya ci gaba da daka da sauri da sauri duk da cewar ya yanke shawarar ba zai gaya ma ta ainahin gaskiyar al'amarin da ya faru ba.
Sai da Hantaru ya shafe rabin sa'a a tsaye akan dokinsa yana ta sakar zuci, fargaba da
tunanin abinda zai fishsheshi sannan daga karshe ya yanke shawarar ya fara zuwa gidan Shurem domin ya sadu da Salimat saboda ya san cewa ya tafi ya barta a cikin tsananin fishi da bakin ciki, bai san halin da take ciki ba yanzu. Lallai ya zamo wajibi a gareshi yaje gareta ya nemi gafararta kuma ba zai yarda te san da mummunan bamar da ya aikata ba a can birnin Kisra har reyuka uku suka salwanta.
Lokacin da Hantaru ya fara tafiya ya nufi hanyar de za ta kaishi gidan Shurem, sai ya tuna cewa ai yana dauke da kan mahaifiyarsa Zarifa a cikin jakara guzurinsa wanda ya zuba masa wani ruwan sihiri wanda ya hanashi rubewa. Nan take Hantaru ya ratse hanya ya shiga cikin daji ya isa har karkashin wani tsauni mai duhuwa ya saula daga kan dokinsaya tsaya cak! Ya dubi gabas da yamma,kudu da arewa bai ga kowa ba kuma bai ji motsin komai ba. Har tsawon lokaci yana tsaye a hakan. Koda ya tabbatar da cewa babu mai ganinsa sai ya haka rami a gaban wata siririyar bushiya ya binne wannan kai na Zarifa sannan ya koma da baya ya kau kana dokinsa ya durfafi gidan Shurem.
Tun dage nesa Hantaru ya hango kofar gidan Shurem a ciko makil da zuriarsu ta makera, jama'a na tsaitsaye sun yi tsit ba a jia muryar kowa face sautin numfashinsu.
Koda ganin haka sai zuciyar Hantaru ta buga da tsananin karfi irin bugawar da bai tafa ji ba a rayuwarsa. Cikin tsananin fargaba ya iso cikin taron, ai kuwa jama'a na hangoshi sai aka dare aka bashi banya ya kutsa ta tsakiyarsu bisa dokinsa ya iso tsakiyar harabar gidan. Koda ya yi arba da abin da aka shimfide a agabansa sai ya tsandara uban ihu ya fado kasa tim! Daga kan dokinsa ya fashe da mataanaicin kuka yana mai buga kansa a jikin dirkar gini, har kan nasa ya fashe jini ya ringa zuba. Cikin sauri wasu karti majiya karfi su uku suka kamashi suka rirrikeshi don kada ya ci gaba da buga kansa a jikin dirkar ginin wacce ita ma kanta ta fara tsattsagowa tana barazanar rugujewa.
Ba wani abu Hantaru ya yi arba da shi ba face gawar Salimat a shimfide idanunta a Kafe kamar za a yi ma ta magana ta amsa.
Hantaru ya ci gaba da rusa kuka da ihu tamkar mahaukaci sabon kamu har ya zamana

cewa gaba dayan jama'ar da ke wajen sun tsorata ainun sun fara watsewa don tsoron kada ya zare takobinsa ya hausu da sara.
Shaulat da ke tsaye a kansa tana ta faman zubar da hawaye ta kasa cewa da shi komai,sai ta sa hannunta cikin aljihu ta dauko wata guntuwar wasika ta mikawa Hantaru. Hannun Hantaru na karkarwa ya karbi wasikar ya budeta ya fara karantawa a fili, kamar haka;
Ya kai dana Hantaru,kayi sani cewa ka bani kunya, kuma ka bani mamaki, domin a zatona za ka janye mugun nufin da ka tafi da shi izuwa birin Kisra, amma sai gashi soyayya ta sa idanunka sun rufe ka manta da muhimmancina a rayuwarka
Ka tuna cewa babu wani mahaluki da nake so a wannan duniya sama da Sarki Kusaidu,gashi ka kashe matarsa Zarifa a dalilin ganin gawarta da ya yi shima ya hadiyi zuciya ya mutu.
Ka tuna cewa yanzu na rasa mijina, kuma na rasa kakana boka Sulbaini da mahaifina,wanda ya rage mini kawai ita ce mahaifiyata da kai,kuma yanzu na tsaneka kamar yadda na
tsani dukkan makiyana a duniya.Na san za ka yi mamaki bisa yadda aka yi na san duk abin da ka aikata a birnin Kisra, amma idan kayi tunani ba abin mamaki bane tun da matsafa basu kare ba a doron kasa. Tun daga ranar da ka bar nan birin ka tafi izuwa birnin Kisra har ka je ka kashe boka Ardusa, sannan ka je ke kashe Zarifa kawo izuwa barowarka birin Kisra duk na gani a cikn madubin tsafi.
Koda na gama ganin wannen al'amari sai na fashe de matsanancin kuka na kamu da Babban bakin ciki kuma nan take naji duniyar ta yi min kunci bani de bukater na ci gaba da rayuwa Bisa wannan delili ne na sha guba a ranar de ka iso nan birnin Kisra.


Wanann shi ne kelamaina na karshe a gareka ya kai dana. Ina mai yi maka bushara da cewe rayuwar duniya be ta da wani dadi idan har babu masoyi. Tabbas ka zame mini bakin takobi, kumna bakin kumurci mai mugun dafi. Ina mai shawartarka da ka bi rayuwar duniya a sańnu kuma ka sani cewa baka da babban makiyi a rayuwarka sama da zuciyarka tun da ba za ka iya sarrafata ba. Ka sani cewa a duniya bebu abin da ya fi soyayya karfi de
dadi, kuma babu abin da ya fita wahala da hadari. Har abada ba zan koma Kisra ba...."
Sa'adda Hantaru ya zo nan a karatun wasikarsa sai ya sake fashewa da matsanaicin kuka ya rungume gawar Salimat a kirjinsa ya yi ta kuka kamar ba zai taba dainawa ba. Da Kyar da sidin goshi kuma da rarrashi gami da lallami aka banbare gawar Salimat daga hannunsa, sannan aka haka kabari aka binneta.A bakin kabarin nata Hartaru ya kwana yana kuka har gari ya waye rana ta take. Saboda tsoron fushin Hantaru sai aka rasa wanda zai zo ya rarrasheshi. Hatta Shaulat ma kasa zuwa ta yi.
Lokacin da Hantaru ya gaji da kuka har ya zamana cewa ruwan hawayensa ya kafe kuma muryarsa ta dashe, kuma numfashinsa na sarkewa sai ya sulale kasa sumamme. Sai da Shaulat ta debo ruwa ta watsa masa sannan ta bashi a baki ya sha sannanj ya dawo cikin haiyacinsa.Koda ya nutsu sai ya mike tsaye ya fice daga cikin gidan Shurem ya durfafi gidan sarki kai tsaye,yana tafe yana tangadi kamar wanda ya sha giya ya bugu saboda tsananin
yunwa da kishirwar da ke jikinsa gami da
dumbin bakin ciki.
Da zuwan Hantaru kofar gidan Sarki sai ya ga kan mahaifiyarsa Zarifa a cake jikin itace. Al'amarin da ya matukar firgitashi ke nan ya cika da tsananin mamaki. Shi dai a saninsa ya binne wannan kai a can cikin daji a lokacin da babu wanda ya ganshi.
Abin tambaya anan shi ne, wane ne yaje ya tono kan ya kawoshi nan? kuma ya ya akayi aka san inda kan yake?
Ba zato ba tsammani, sai Hantaru ya hango gimbiya Larziya ta fito daga cikin gidan Sarki ita kadai tana sanye da wata farar doguwar riga mai shara-shara wacce ke baiyana gaba dayan kyakkyawar surar jikinta.Fuskarta a cike take da annuri kuma ta goya hannayenta a gadon bayanta.
Koda ganinta a cikin wannan hali sai Hantaru ya cika da tsananin farin ciki,ya yunkura zai ruga da gudu izuwa gareta kawai sai yaji ta daka masa tsawa ta ce, "Dakata!Anan inda kake ya kai masoyina".
Cikin matukar kaduwa da mamaki Hantaru ya tsaya cak a inda yake ba tare da ya
yi gardama ba. Kawai sai ya ga hawaye ya zubo daga cikin idanun gimbiya Larziya sannan ta dubeshi ta ce, "Ya kai masoyina abin begena dare da rana,kayi sani cewa na yaba da tsananin kokarinka bisa kokarin cika alkawarin da ka daukar mini kuma na tabbatar da cewa kana kaunata fiye da

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment