Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fadin 'karya nake maganar da nayi ya ce." Tokar don Allah ki daina haddasa fitina a tsakaninsu, da Ali da Jamila duk naki ne, mai zai sanya kina goyan bayansa yana cin zarafin yarinyar nan, bana jin dadin wannan al'amarin ko kadan wallahi."
Girgiza kanta tayi da cewar" 'Karya take duk maganar da ta fada muku sharri tayi masa ita da bakinta tayi furucin itace ajalinsa."
Baba Hama mahaifiyarsa ta ce." Nima na ji da kunne na saboda haka dole hukuma ta shiga cikin al'amarin nan wallahi." Kawu Sammani ya buga mata tsawa tare da cewa" Rufe mini baki shashashar banza da wofi duk waye ya 'bata yaron idan bake ba." Shiru tayi ranta a 'bace ta bar gurin. Ya kalleshi fuskarsa a murtuke! ya ce." Ka bata hakuri a gabana ko kuma ranka ya 'baci! ba zan lamunci wannan rashin kirkin ba."

Jin furucin mahaifinsa sai hankalinsa ya tashi! hak'uri yana nufin shi zai bata hakuri? to me ya yi mata wanda har za a k'askantar dashi irin haka! lokaci guda ya burkice! 'kwayoyin idanuwansa sukayi jawur! wani abu mai nauyi ya tokare masa a wuya! yana tsaye! kamar wanda aka dasa a gurin ya gagara bin umarnin mahaifin nasa, wanda ni kuma a lokacin ji nake kamar na taka rawa saboda farinciki, gaskiya naji dadin hukuncin da Kawu Sammani ya yanke masa.
Tsawa! mai karfi ya buga masa da fadin" Ba za ka yi abinda na umarce ka ba?"
Tokar ta ce" Sammani kabi a hankali mana, wai shin da Jamila da Ali waye babba ne?"
Ya ce." Duk ba wannan maganar ba Tokar ina sane da irin rashin arzikin da yaron nan yake yi, ya addabi yarinyar nan, ya hana ta sakat! ke kuma kina daure masa gindi saboda yana siyo miki nama da kifi! ita kuwa Jamila duk hidimar da take miki ba ki duba ba, kiyi hakuri da furuci na Tokar dole ki gyara idan ba haka ba, Allah zai tuhume ki ranar lahira domin dai Jamila amana ce a hannunki."
Jikinta ne ya yi sanyi sai ta sunkuyar da kanta tana cigaba da tsotsar k'ashin hannunta!
Kallonsa ya yi a karo na uku ya ce." Ban isa ba ko?" Kansa ya girgiza yana huci! ya ce." Kiyi hakuri!" da saurin gaske ya bar gurin don har sai da ya taka mini kafa da kambos din dake 'kafasa.

Ranar kwanan farinciki nayi dalilin abinda ya faru! kuma na samu sau'ki daga gurin Tokar ban sani ba ko nasihar Kawu Sammani ce take d'awainiya da ita domin yini tayi jikinta a sanyaye sai hannunka mai sanda take yi mini akan abubuwan da suke faruwa tsakanina dashi, na ce" Tokar wallahi babu ruwana da Bahago mutu'kar bai shiga hurumi na ba, ya yi rayuwarsa nayi tawa tunda babu wanda ya isa ya kori wani a tsakaninmu."
Ta ce."Ai jini daya ba wasa bane Jamila, Ali dan uwanki ne, kuma komai abinki ya girme ki tunda ya riga ki shakar iskar duniya, saboda haka ko yaya ne ki bashi girmansa.
Dariya maganar ta bani, na bude baki kenan zanyi magana ya shigo gidan cikin shigar 'kananun kaya kamar koda yaushe rigar data matse masa jiki da wando iya gwiwa mai tarin aljihunai. f-cap a kansa kafarsa sanye da kambos mai igiyoyi sai wasu shegun sarkoki a wuyansa al'amarin nasa dai sai gyaran Allah kamar ba dan musulmai ba.
Hanci na toshe saboda na tsani warin sigari ita ce kuma a hannunsa yana busawa! babu ruwansa a gaban kowa sha yake saboda rashin tarbiya.
Ta ce" Tun safe nake cigiyarka ina ka shiga ne?" Hayakin dake bakinsa ya feso mini a fuskata! ya kuma tsira mini jajayen idanuwansa masu girman gaske! kallonta nayi raina a masifar 'bace! Ta ce." Yi hakuri akan wanda ki ke yi." Ta kalleshi da fadin." Mai yasa kake neman tashin hankali ne?" shiru ya yi mata hankalinsa gabad'aya yana kaina, tunda naga haka sai nayi niyyar barin dakin, na san ba alheri ne ya shigo dashi ba, tashi nayi domin fita babu zato! ya sanya mini k'afarsa na fad'i a jikinsa! ya hankad'e ni na zube a kasa kafin ma na yun'kura! ya cimma ni, ya fara hauri na da takalmin kafarsa yana kaiwa fuskata duka! Tokar ta rarrafo tana rike 'kafarsa tare da fashewa da kuka! " Ali wace irin zuciya gare ka ne? na d'auka jiya akayi muku sulhu mai zai sanya kuma kazo kana dukanta."
Na ce" Tokar ki 'kyaleshi ya kashe ni mana ai d'an-daba ne d'an-ta'adda." Bakina ya kaiwa duka! da kafarsa a take kuwa jini ya fara zuba can naji turmin ha'kori na yana girgid'i! kukan kura nayi na tashi tsaye na kai hannu zan zabgawa fuskarsa mari! ya murd'e ni! bango ya matse ni ya cigaba da bugu na! kuka nake sosai ina zagin sa tare da kokarin kwace kaina. "Jama'a wai menene yake faruwa ne tun daga soro nake ji ihu! da kururuwa! Anti Hamida ce take wannan maganar lokacin da ta shigo dakin, nan taga abinda yake faruwa, salati tayi cikin tashin hankali tazo tana k'wace ni daga hannunsa da fadin." Idan ka kasheta wallahi sai munyi shari'a da kai! mara mutunci kawai!" Ya fita daga dakin yana numfarfashi! sai yanzu ya samu sassauci a zuciyarsa dalili jiya kwanan zaune ya yi in banda haya'ki babu abinda yake busawa! ya ji takaici abinda mahaifinsa ya yi masa shiyasa ya yanke shawarar ladabar da ita domin bata kai matsayin da zai 'kaskanta da kansa ba.

Rungume ta nayi sosai ina wani irin kuka! Na ce."Anti Hamida rayuwata yake nema! baya 'kaunata kullum kokarinsa ya za'ayi ya sabauta ni, bani da inda yafi nan, amma ina ganin dole zan tattara kaya na na tafi can gurin mahaifiyata domin na gaji da wannan lamari Bahago rayuwata yake nema!" cikin gurshe'ken kuka ta kai karshen maganar. Tokar ta dinga share hawaye! da alama itama abin ya girgizata, wai shin wannan wace irin k'iyayya ce yaran sukewa junansu?
Anti Hamida murya na rawa ta ce." Babu inda zakije Jamila, kamar yanda ki ka fada cewa baki da inda yafi nan hakane mune 'yan uwanki kuma gatanki dole ayi wa tufkar hanci domin ba zamu zuba ido wannan al'amari yana faruwa ba"

Tokar na fyace! hanci ta ce." Hamida anya kuwa yara nan ba jifansu akayi ba? wannan abun yana bani tsoro wallahi, kiga irin dukan da yake mata kamar wanda aka aiko shi.
Ta ce."Tokar kema fa kina da hannu a cikin faruwar wannan lamari, domin icce tun yana danye ake tankwara shi, ke kuma tun fil'azal ba kya k'aunar 'bacin ran yaron nan komai ya yi daidai ne a gurinki, ya lalace ya zama d'an iska baya jin maganar kowa ya zama baragurbi a cikinmu saboda haka ni da kaina zan shigewa yarinyar nan gaba domin a kwatar mata hakkinta kada kuma a k'ure hak'urin Kawu 'Danlami abin ya yi yawa gaskiya."
Ta ce." To dai kada ki manta da Ali da Jamila duk babu bare a cikinsu, kuma idan salsala za'a bi Ali ne makusancinki domin ke kika saki nono ki ka bashi don haka ki bi komai a hankali."
Ranta a 'bace Ta ce." Yo ai ni gwara Jamila sau dubu a gurina tunda duk rintsi tana jin maganata tana kuma jin maganar iyayenta, shi kuwa fa ai na riga na sallamashi tunda babu wanda ya isa ya fada masa ya ji."
Ta ce." Itama fa tana yi masa abubuwa marasa kyau! tana kiransa da mazinaci dan shaye-shaye d'andaba! da dai sauran kalmomin da ba su dace ba."
Cikin takaici ta ce." Ai ba 'karya tayi ba Tokar Bahago bashi da kirki duk abinda Jamila ta lissafo a kansa yana aikatawa idan hakan ke b'ata masa rai sai ya gyara!
Tokar ta kama kuka tana tana ta goge majinar da take ta tsiyayowa a dakalin hancinta. Ita dai ta tsani a jingina masa mugun abu bayan kuma ta san duk abinda aka fad'a a kansa gaskiya ne.

"Jamila ki yi hakuri kinji ko ki tashi ki shirya kayanki mu je can gidana ki huta kafin mu san ya za'ay....Kafin ta karasa maganar Tokar ta katse ta da fad'in." Hamida baki isa ba kinyi kad'an!" duk muka zuba mata ido muna kallonta.
Ta cigaba da cewa" Aure ne kawai zai raba ni da Jamila ko mutuwa ke baki isa ba saboda haka ba zataje ko'ina ba ni bana son munafurci da neman gindin zama."
Anti Hamida tayi dariya tana kallonta ta ce." To ai kisan kai naga za'ayi a gabanki baki dauki mataki ba, shiyasa na yanke shawarar dauketa daga gidan, idan ya daina ganinta shikkenan sai ku sakata ku wala!"

Tsaki! mai tsawo taja ta ce." Ni dai na fada miki baki isa ba, idan kuma kina so ran mahaifinki ya 'baci akan wannan lamari shikkenan ki tafi da ita d'in."
Ta ce." Ba zan so hakan ba gani nayi lamarin yana kara tsananta shiyasa na yanke wannan hukuncin amma don Allah ku d'auki mataki akan wannan abu idan ba so akeyi yarinyar nan ta hadu da larura ba"

Ta ce." Ke dai baki isa ki shiga tsakaninsu ba duk gulma da munafurcinki don haka sahun ki a likkafa ki tashi ki tafi gidanki bana son neman guri."
Na ce."Anti Hamida yi mata shiru don Allah! kar ki sake magana, in sha Allahu cikin satin nan zan zo na kwana biyu a gidanki."
Ta ce." To godiya nake k'anwata bari na tashi na tafi dama gidan biki zan je na ce bari na shigo na gaisa da Tokar sai kuma na riski wannan tashin hankalin."
Na ce" Bikin Humaira ko ? ai tun sassafe Baba Hama ta tafi ita kuma Baba Iyami ta tafi aiki shiyasa ki ka ji gidan shiru, nima abinyi nake nema wallahi domin na gaji da zaman banza." Tana kokarin tashi tsaye Ta ce." Kada ki damu idan na dauki adashin da nake zan baki dubu goma sai kiyi shawarar sana'ar da zakiyi."
Cikin farinciki na rungume ta ina ta godiya Tokar sai ta'be bakinta take yi tana hararar mu.

Dubu biyu ta d:auko cikin jakarta ta ajiye mata a gabanta da fadin " Tokar gashin ki sayi goro." Abin mamaki! sai ta fara washe baki, tayi sauri ta dauki kudin tasa a k'arkashin fillo. Muka kalli junanmu dariya ta kufce mini da sauri na dauki hijab na fita tsakar gida ina dariya da mamakin abinda ya faru, itafa Tokar duk mai bata kudi ko wani abun duniya shine mutum a gurinta, kuma yanzu nan za'ayi magana da ita ta gaskiya amma anjima kad'an sai ta ce 'karya ne, mussaman idan kana yi mata ihsani to bata da gwani wanda ya kai ka.
[5/29, 8:30 PM] Binta Umar Abbale: 4
Tare muka fito daga gidan muna dariya A'lamarin Tokar. Na kalleta da fadin." Anti Hamida bari na raka ki bakin titi ki samu abin hawa ko." da sauran dariyar a tare da ita ta ce."Ai da tun zamana kin shirya da kin raka ni gidan bikin duk da dai ke ba kya son shiga cikin mutane."
Na ce."Anti ba wai bana son shiga cikin mutane bane kawai kallo ne bana so wallahi, shiyasa nake boye kaina, dan akwai wani taro da na raka Baba Iyami wallahi a kunnena na ji suna gulmata wai na fitta zakka a cikinku ni kad'ai ce ba'ka! abin ya yi mini ciwo sosai."
Anti Hamida tayi dariya sosai ta ce." To ai Jamila idan zaki biyewa maganar mutane ranki ne zai 'baci! kawai kiyi sabgar gabanki ki daina damuwa da surutu."
Shiru kawai nayi ina murmushi, cikin danginmu Anti Hamida tana da matsayi mai girma a gurina domin tana damuwa da damuwata.

Can muka hange shi zaune a kofar gidansu Abokinsa Shamsu yara sun kewaye shi kowanne da buhu a hannunsa cike da tarkace irin na gwan-gwan! da yake sana'arsa kenan tun yana yaro dan shekara bakwai yake harkar har kawo yanzu da ya tsaya da k'afarsa ya had'a gwiwa da wani kamfani a legos dake sarrafa k'arafuna da robobi.

D'auke kansa ya yi kamar bai san mu ba, Shamsu ya fito daga gidansu, shima dai sai addua kamar abokin nasa babu sutturar arziki a jikinsa ga wani shegen aski a kansa lebansa 'bakikirin da alama bayan sigari yana d'an taba ganye da sauran kayan maye, wanda shi Bahago sigarin kawai yake busawa.

Da fara'arsa ya ce." Anti Hamida ina kwana ya yara?" fuskarta a sake ta amsa "Lafiya lou Shamsu ya Mamanka don Allah idan ka shiga gida ka gaishe mini da ita" Ya ce." In sha Allahu zataji." Sosa kansa ya dan yi, ya saci kallona da fadin." Gimbiya babu gaisuwa?" kallonsa nayi da mamakin sunan da ya kira ni wai Gimbiya, na gyara fuskata da cewa" Ya kake?" da sauri ya ce."Lafiya lou." yanda yake fara'a hakan ya tabbatar mini da cewa; ya ji dadin yanda na saurareshi dama ba kulashi nake ba saboda haushin abokinsa, ko gidanmu ya shigo haka zai ta jana da magana nayi masa banza.

Ya kalli Anti Hamida da cewa" Anti Zan zo gidanki domin akwai maganar da nake so mu tattauna."
Ta ce."To Allah ya kawo ka amma ban amince kazo mini da irin wannan shigar ta jikinka ba" 'Yar dariya ya yi tare da cewa" Ai a kamili zanzo miki Anti." Ta ce " Shikkenan Allah ya kawo ka." ya amsa da amin amin ina kallonsa yana ta satar kallona.
Tsaki na ja da sauri na yi gaba ina mamakin kallon munafurcin da yake mini.

Ya zauna kusa da abokin nasa sai fara'a yake kamar wanda akayi wa albishir da samun aljanna. Bahago kuwa ji yake kamar ya kai masa naushi! saboda takaici! ko kallonsa bai yi ba ya cigaba da dudduba tarkacan da yaran suka kawo masa, ya yi musu kudi sannan ya salleme su tare da umartar d'aya daga cikinsu ya kai masa takarcan kangon da yake adanawa.

Kafad'arsa ya dafa tare da cewa" Abokina kasan akwai wani babban al'amari dana jima ina b'oye shi a cikin raina."

Babu yabo babu fallasa ya ce." Wane irin al'amari ne wannan da bani da labarinsa meye abin 'boyewa mutuk'ar ka yarda da amintar dake tsakaninmu sai ka fayyace mini komai."

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya ce." Yarinyar nan Jamila mana." Sai kuma ya yi shiru bai karasa maganar ba. yayin da nasa 'bangaran gabansa ke wani irin bugawa jin ya ambaci Jamila duk da dai bai tabbatar da wacce yake nufi ba.
Ya zuba masa manya idanuwansa da suka fara canza launi, fatan goshinsa ta tattare tare da tofowar gumi!

Ya cigaba da cewa" Wallahi Allah ne kad'ai ya san iya adadin 'kaunar da nake mata a cikin zuciyata amma yanda na fahimta kamar bata ra'ayi na."
Ya jima yana kallonsa tare da 'ko'karin ganin ya danne abinda ke taso masa, ya ce." Kai yanzu Shamsu dan girman Allah mai zakayi da Jamila? yarinya babu fasali! mummuna! irin wannan ka ajiyeta a gida kamar horo! ga 'baki kamar bayan tukunya! ka je ka nemi farar mace malam yanda kake ba'kar fata sai ka surka amma meye abin so da kauna a tare da Jamila sai kace god'iyar doki (matar doki)

Shamsu ya ji haushi sosai ya ce." Amma wallahi ka bani mamaki! kuma na raina wayonka da wayewarka! wai har kana bude baki ka cewa babu abin bu'kata a tare da Jamila. Lallai Bahogo towo ya rufe maka ido! to bari kaji gaskiyar magana wallahi Jamila tana daya daga cikin matan da suke wahalar samu! kana maganar muni! to ni banganshi ba sai tarin abubuwan dana hango a tare da ita wanda zan mora na ji dadi tare da farinciki. kafafun Jamila da cikar dunduniyarta su kad'ai sun isa bayyana maka wacece ita mutukar kasan mace kafin aje ga surar jiki, babu ruwana da farar fata ni ina duba mafita ne kawai! kuma bari kaji wata magana irinsu Jamila ne ba a iya rabuwa dasu mutukar mutum ya d'and'ana zumanrsu Alhaji ai ba'kar mace duniya ce kai zaka bawa wani labari."

Ransa ya dugunzuma! jin zantukan da Shamsun yake yi, tsaki ya ja zuciyarsa a k'untacce ya ce." Koda nake neman mata ban ta'ba kwanciya da ba'kar mace ba, kuma bana ra'ayinsu, kai ni gaba'daya ma suffar yarinyar nan ba ta yi mini ba, kai dai da kake ganin tayi daidai da ra'ayinka sai ka mayar da hankali."
Da saurin gaske ya ce." Aikuwa sai naga abinda ya turewa buzu nad'i domin wallahi na gama kwad'aituwa da ita, kuma auranta nake so nayi don Allah ka shige mini gaba akan lamarin."
Muguwar dariya ya yi yana kallonsa ya girgiza kansa da cewa" Muddin ni zan shige maka gaba akan wannan lamarin zaka fad'i wanwar! wallahi babu ni a wannan harkar ka je kafa gwamnatinka." Yana gama maganarsa ya tashi daga gurin, sai Shamsun ya bishi da kallon mamaki da tunani akan furucinsa.

Bakin 'kofar kangon dake jikin gidanmu wanda anan yake ajiye kayan gwangwan! dinsa na same shi tare da yara irin wad'anda ke kawo masa kwalabe yana ta rarraba musu kud'i da alama irin wad'anda suke binsa bashi ne kafin tafiyarsa. d'auke kaina nayi da sauri nayi nufin shiga cikin gidan bisa tsautsayi nayi gaba da wani mataccen langa-langa da duk ya yi tsatsa! aikuwa ya yanke mini k'afa! jini ya fara zuba!
Rintse ido nayi jin wani irin zafi na janye k'afata tare da tsugunawa ina duba gurin, sosai makamin ya yi mini rauni.
"Laa! Anti Jamila ciwo ki ka ji naga jini a kafarki." Daya daga cikin yaran ne ke magana cike da alhini yasa hannu ya janye langa-langan da yake kan hanya wanda ya fahimci cewa shine sanadi.
Maganar da yaron ya yi ta d'auki hankalinsa ya le'ko soron domin ganin abinda yake faruwa. tsigar jikinsa ce ta tashi ganin yanda jini yake ta tsiyaya!
Da sauri yaron ya ce." Wannan langa-langan ne ya ji mata ciwo.'' Babu walwala a fuskarsa ya ce." Kai waye yace ka ajiye akan hanya kasan abin yana da illah! a koda yaushe ina gargadinku da hakan saboda faruwar matsala irin wannan."
Yaron ya yi shiru duk jikinsa ya yi sanyi. ganin haka yasa na tashi tare da jan 'kafata na shiga gidan cikin zuciyata in banda Allah ya isa babu abinda nake masa.

Na samu Tokar a tsakar gida ta rarrafo ta fito tana ta garzar goro bakinta duk ya yi dagaje-dagaje! cikin damuwa ta ce." Tuntu'be ki ka yi ne naga kina jan kafa ka jini yana diga."
Na ce "Yaran Bahago ne suka ajiye Makami akan hanya ya yi mini rauni."
Ta ce." Ashsha! aikuwa sai yazo ya siyo miki magani ko ya kai ki chamis." Shiru kawai nayi domin ni kadai na san zafin da gurin yake mini fatar yatsan ta d'ago tare da farce na, jinin kuma bai daina zuba ba.
Ta ce." Ki samo kalanzir ki zuba a gurin jinin zai daskare." Nan ma ban tanka mata ba. sai gashi ya shigo gidan hankalinsa yana gurin da nake zaune. d'auke kaina nayi tare da jan tsaki! a duniya bani da babban makiyi kamarsa.
Ya zo ya tsaya a kaina tare da tsurawa 'kafata ido. da biyu yake kallon 'kafar yana so ya ga abinda Shamsu yake fada masa, shi dai bai ga komai ba sai cikar dunduniya kuma tun daga tafin 'kafar har zuwa idan sawu a cike yatsun ma irin masu kaurin nan ne. Ajiyar zuciya ya sauke yana sake hade fuskarsa ya ciro farin hankici daga aljihunsa biyu ya raba shi ya tsuguna gabana tare da janyo min kafa. da sauri na janye ina hararsa! Tokar ta ce"Ashe abinda ya faru kenan?" kansa ya 'daga da fad'in." Yara ne suka ajiye a kan hanya." Ta ce." Wannan ai dole sai kun je chamis ko?" ya ce." Sai da daddare tukkuna."
Ya sake janyo mini kafa a karo na biyu na janye tare da fadin." Kyale ni mana.
Wani irin kallo ya yi mini kafin ya k'ara kai hannu 'kafata a karo na uku kafin ma na janye ya rike da kyau! ya sanya abinda yake hannunsa ya d'aure sosai! jinin ya tsaya sai dai ya matse mini yatsa sosai! sai zugi yake mini.
Kwanciya nayi gefen tabarma aikuwa zazzabi ya rufe ni ba komai ne dalili ba sai raunin da nayi.
Sai bayan la'asar na tashi jikina yana ta karkarwa na daddafa a haka nayi wanka nayi sallah. ta kalle ni da cewa'' Yau haka zamu zauna bamu ci komai ba duka matan gidan basa nan. shiyasa fa na ce a raba tukunya saboda azabtar dani suke da yunwa".
Kafin nayi magana ya shigo gidan da karan sigari a hannunsa yana busawa! toshe hancina nayi cikin zuciyata ina Ala wadai da wannan muguwar dabi'a. Ta ce." Bahago yunwa muke ji fa tun safe babu komai a cikinmu matan gidan haka suka fita suka bar mu da yunwa."
Kallonta nayi ina mamakin 'karyar data shirga tsakani da Allah za a fad'a! Baba Iyami har d'umamen towo ta kawo mata, kuma Babana ya aiko mana da indomee da 'kwai, amma shine zatayi musu sharri."
Ya ce." Me kuke so ku ci yanzu?" Da sauri ta ce." wannan gurasar da kake siyo mini da tsire ke Jamila mai kike so?" ta fada tana kallona. Na ce." Bana bukatar komai'' Ba tare da ya yi magana ba ya kama hanya ya fita still da sigarin a hannunsa yana zuk'a.

Minti goma sha biyar sai gashi da k'atuwar leda ya ajiye mata har da yogurt roba uku masu Sanyi ta dinga shi masa albarka tare da yi masa addua akan sana'arsa, ni kaina na tabbatar da nagartarsa da tausayinsa ta wannan b'angaran muddin yana gari to ya dinga yi mana facaka kenan, duk abinda Tokar take so sai ya siya mata, nima har na shiga ciki, amma bana nuna kwa'dayi na a gabansa saboda na riga na san halinsa sai baya gurin nake zagewa na cika cikina wani sa'in ma har na fi Tokar din ci tunda ba ha'kora ne da ita ba tana jimawa kafin ta cinye na bakinta, to wannan dalilin ne yasa a duk lokacin da wani sa'bani ya gifta a tsakanina dashi Tokar sai tayi mini gori akan hidimar da yake yi wanda nima nake shiga cikin inuwarsa.
[6/6, 3:39 PM] bintaumarabbale: 5
Asalin Labari.
Gombe nan ne asalinmu muna zaune ne cikin garin dukku. Asalinmu fulani ne usul wanda ni Jamila ko da wasa ban d'auko kammani da asalin gidanmu ba, ni kad'ai nayi daban a cikin zuria'armu. Kakanmu Malam Zangina malamin addinin musulunci ne sosai yana da almajirai masu d'aukar darasu a gurinsa, a yanda muka sami labari cewa shi d'in mutum ne mai gudun duniya da kiyaye dokokin Ubangiji domin har ya kwanta dama bai ta'ba kwanciya kan katifa ba saboda tsananin gudun duniya da 'kin rashin sakankacewa! kullum maganarsa d'aya ce duniya ba gidan zama bane guri ne na bautar Ubangiji domin samun rabo a ranar 'kiyama! kuma Malam Zangina har ya k'are rayuwarsa a duniya bai 'ba ta sauya wani tufafi ba face farin yadi kuma dashi aka lullube shi bayan Allah ya 'karbi rayuwarsa
Matarsa d'aya Mariya wacce 'yan-uwanta suke kiranta da Tokar dalilin rashin ha'kurinta a zamanin tana da k'uruciya da kuma yanzu da ta tsufa halinta yana nan sai abinda ya yi gaba. tana da kirki muddin ka iya zama da ita amma butsuwa ce sam bata da mu'amula mai kyau! ita ce ta yi masa takaba kuma ta cigaba da d'awainiya da yaranta uku duk maza wanda suka haifa tare da mijinta Malam Zangina.

Tokar ta sha wuya sosai da yaranta kafin su girma su kai minzali kuma duk babu fitinnane a cikinsu kansu a had'e! yake suna fita neman kudi domin samun abinda asirinsu sai ya rufu, sai dai abinda mahaifiyarsu ke musu bai kamata ba, wasu lokatan ita ce take haddasa rikici da samun matsala a tsakaninsu, domin dabi'arta ce gulma da d'aya daga cikinsu idan Sammani babban d'anta ya

Please Login or Register in order to submit comment