Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi magana shi ya rigata cikin fitar hayyaci yake fada masa wai iskanci nake da maza ya ga ni da idonsa wani gardi ya kawo ni a babur na tattare masa zanina yana haska jikina da wayarsa."

Ina kuka Na ce." Ka ji tsoron ALLAH yanzu Uncle Sadiq din ne gardi? YA ZA'AYI na yi iskanci da mijin 'yar uwata, wannan sharri ne kake kokarin yi mini."

Ya fara rantsuwa da k'arya yana kara tabbatarwa da Kawu D'anjuma maganar. Sai kawai na dinga kallonsa ina mamakin sharrinsa 'kiri-'kiri ya lauya maganar, amma na san ko daga bacci ya ta shi zai sheda fuskar mijin 'yar uwarsa.

Kawu 'Danjuma Ya ce." Bari na kira Sadiq din na ji komai daga gare shi." Ya fito da wayarsa daga cikin aljihu yana ta gwada kiransa sai ace masa wayar a kashe take.

Ya ce." Kawu Yanzu ka gazgata maganata ko?" ai ba yaro ba ne ni, kuma na san Sadiq sosai, wannan dogo ne baki, shi kuma mijin Anti Hamida gajere na mai kiba kuma fari, don haka duk cikin maganata babu sharri ko 'kage!"

Kawu ya waiwayo kaina fuskarsa ya murtuke Ya ce." Jamila abinda za ki yi mana kenan?" Shiru kawai na yi hawaye na bin kumatuna, bakina ya mutu murus! na rasa a wane mizani zan ajiye wannan al'amari, kiri-kiri ana kokarin kulla mini sharri.

Gabadaya haka muka kwana da bakinciki da damuwa, dan Babana ma da ya dawo daga gurin sana'arsa ya samu labari bai d'ora laifin akan kowa ba sai akaina, Kawu Sammani ne kawai yace shi bai yarda da zargin da ake mini ba dole sai ya bibiyi al'amarin.
Washe gari da kansa ya nufi gidan Anti Hamidan domin jin karin bayani daga gare ta.
Sosai ta ji takaicin abinda Bahagon din ya aikata wato iskancin nasa ya wuce kanta ya koma kan mijinta, sharri zai yi masa, haba shiyasa ta ga ya dawo gidan fuskarsa babu walwala ashe abinda ya faru kenan.

Da Kawu ya dawo gidan ya sanar da 'Yan Uwansa gaskiya lamari, Kawu Danjuma ya yarda kuma ya ji haushin hakan a cikin ransa, amma Babana bai nuna yardarsa ba, a cewarsa wai ba'a shedar mutum tunda na kai munzalin aure shekara ashirin da biyar to komai zai iya faruwa, kafin na d'auko musu abin kunya zai yi k'o'karin aurar da ni, wannan maganar ta daga mini hankali sosai! na shiga damuwa mai tsanan da adduar Allah ya kawo mini mafita a rayuwata.

Na shiga zullumi! babu wanda ya damu da damuwata sai Baba Iyami, ita ce ke dan kwantar mini da hankali a duk lokacin da na shiga gurinta, amma Tokar da Baba Hama yanda na fahimta kamar suna farinciki da halin da nake ciki.
Sai na yanke shawarar zuwa gurin Mamana domin samun sassauci. na nemi izini a gurin Tokar ta ce na tambayi Babana ita bata da hurumin bari na fita tunda ga irin abubuwan dana fara.
Na kalleta ina jin wani abu mai nauyi a makogwarona Na ce."Tokar har yanzu zuciyarki tana zargina ko? a gabanki fa na rayu kin fi kowa sanin halina ashe za ki iya yarda da wannan sharrin? wallahi Allah ne daya ban aikata komai ba Bahago 'kage ya yi mini."

Jikinta a sanyaye ta ce." Jamila ba'a shaidar mutumin yau kamar yanda babanki ya fada kin kai kin kawo, gaki nan tubarkallah nono cike a kirjinki, a yanzu babu abinda ki ke bukata sai namiji don haka ni ba zan amince da maganarki ba."

Girgiza kai na yi tare da cewa; Wannan ba hujja ba ce Tokar, kada ranar lahira Allah ya tsayar daku domin ku nuna masa shaida akan abinda kuke zargina da aikatawa wallahi ban ta'ba sanin wani da namiji ba tunda nake, kuma kin san sharrin zina yana da muni! wallahi ban aikata ba, ku daina zargi na sharri ya yi mini.

Shiru ta yi tana kallona da alamun rusuna a tare da ita.
Na ce." Kiyi hakuri ki tambayar mini Babana ya bar ni na je kin ga na kwana biyu ban je ba."

Shiru ta yi ba ta ce komai ba ta dauko goronta tana gurzawa.
Da asuba ina kwance ya shigo dakin kamar yanda ya saba suka gaisa, na ta shi zaune na gaishe shi, ya amsa ba tare da nuna kulawa ba.
Sai na koma na kwanta jikina duk a mace, wato Babana ya fi kaunar Bahago da ni, tunda ya kasa fahimtar matsalata.

Ina jin Tokar tana rokar mini shi ya bar ni zuwa gurin Mamana yana turjewa tare da kawo hojjoji. wai dole idan ina so na je sai dai Bahago ya kai ni, don ba zai lamunci tafiyata ni kadai ba.
Tokar din ta nuna yardar ta akan hujjarsa.
Bayan fitarsa take sake jadadda mini maganar. Na ce." To shikkenan sai mu je tare da shi din, idan ya shigo sai ki fada masa.

Muna karya kummalo ya shigo dakin yana tambayarta ruwan zafi zai yi wanka. Ina jin tana tambayarsa wankan me zai yi da sassafe! sai ya rufe ta da fad'a wai mai yasa take masa kutse a cikin al'amuransa.
Da yake tana jin tsoron b'acin ransa ta 'dauko fulas dinta da ruwan zafi a ciki ta mika masa ya kar'ba ya fita daga dakin.

Bayan minti talatin ya sake shigowa cikin gayu sai kamshin turare yake mai sanyi, saurin dauke kaina na yi daga gurin da yake tsaye don tunda al'amarin ya faru wata magana bata sake shiga tsakaninmu ba sai dai kallo.
Ta ce." Ka yi kyau sai dai bana son wannan sarkokin na wuyanka ka da fa ka manta kakanka babban Malami ne a cikin garin nan."
Ya ce." Ni ma malami ne, sanya sarkoki ba shi ne yake nuna zahirin mutum ba, tsoron Allah a zuciya yake."
Sai ta girgiza kanta da cewa; Dama Babanku Danlami ne ya ce wai za ka kai Jamila gidan Babarta saboda yana jin tsoron faruwar wani abu.

Ya ce." Hakan ya yi, amma sai da daddare don yanzu ina da uzuri." Da sauri ta ce " To shikkenan Allah ya kaimu lafiya."
Hanya fita ya nufa yana taje tarin sumar dake kansa da mataji.

To tun yamma na yi wanka na kimtsa jikina, na kalleta da cewa." Tokar ko na tafi da kayana kala biyu sai na kwana a can."
Kai ta girgiza lokaci guda ta murtuke fuska, "Ina lefi ma ku gaisa ki dawo gida, zaman me za ki yi a gidan mutane."
Ganin yanda ta cukune! fuska yasa na bar maganar ban sake cewa komai ba, har akayi isha'i bai shigo ba.
Sai wajan tara shaura sai ga shi wai na fito mu tafi, Tokar ta ce" Anya kuwa dare bai yi ba?"
Ya ce." Babu wani dare ai motar abokina za mu je."
Ta ce." Da sauki tunda a motar gida ne.

Ba tare da ya kalle ni ba Ya ce." Ki fito mu tafi." Ya fada bai saurari wata magana ba ya fita daga dakin.
Turare na fesa a hijab dina nasa ya sauka har kasa, na daura nikab a fuskata nayi mata sallama na fito, nan na ga sabuwar mota Peugeot mai kyau a fake a can gefe, cikin raina nake raya cewa; Yaushe ya iya tuka mota? kawai dan dai ina bukatar ganin Mamana ya sa na amince da tafiya da shi, amma na san Bahago yana sawun farko gurin ma'kiya na.

Yana zaune gurin driving na bude kofar baya zan shiga. Ya ce." Malama waye direbanki?" Na bude kusa da shi na zauna tare da rufe kofar. ya kwanto jikina yana jan murfin motar tare da cewa; 'Yar kauye kawai kada ki bar mana mota a bud'e." Sai da ya tabbatar da cewa murfin ya rufu sannan ya ja motar ya kama hanyar fita daga layin domin hawa babban titi.
[7/8, 9:35 AM] bintaumarabbale: 15
Yana tsaka da tu'kin motar ya zaro sigari daga aljihunsa ya soka a bakinsa tare da kunna mata wuta, lokaci guda wari ya cika motar da haya'kin tabar dalili duk gilashin motar a rufe suke, tashin hankali na shiga domin a rayuwata na tsani warin taba, tari ne ya sarke ni, babu shiri na d'age niqab din fuskata na toshe hancina zuciyata na wani irin tashi.
Ganin halin da na shiga ya sa ya kashe sigarin, amma ko sannu bai yi mini ba har tarin da nake ya lafa, miyau! ya cika mini baki, kawai sai na tofar dashi a kasan site, kaina na wani irin juyawa.

"Ke wace irin 'kazanta ce wannan zaki zubar mana da miyau a mota." Yana hararata yake maganar.

Ko kallonsa ban yi ba na kawar da kaina ina ya mutse fuska.

Shiru na 'yan mintina kafin Ya ce.'' Me ki ke ganin za mu kai wa Ummanki na tsaraba, bai dace mu shiga gidan a haka ba."
Mamakin maganarsa ya kama ni, amma ban ce masa uffan ba.
Na ji yana fadin.'' Ke nifa ban iya gaba ba, idan ma saboda na ji shaushi ki ke yi to kin yi a banza wallahi, kuma duk lokacin da na sake ganin kin hau babur din wani gardi kina jin d'uminsa yana jin d'uminki to ranar sai na illataki."

Kallonsa na yi fuska a tamke Na ce." Idan na yi aure mijina zai juya ni yanda ransa yake so, zai yi wasa da sassan jikina, zan kula da shi sosai zan mallaka masa kaina cikin so da 'kauna."

Tsayar da motar ya yi yana yi mini wani irin kallo, gabadaya ya burkice idanuwansa sun yi jawur!
Sai na fara nadamar furucina, don ganin yanda kammaninsa suka sauya.
Ya ce." Maimaitama maganar da ki ka yi."

Cikin fargaba Na ce.'' Ba sai na maimaita ba, na san ka ji abinda na fada, aure ne zai raba ni da masifarka, kuma In sha Allahu rabbi na kusa shakar iskar 'yanci, na je na yi rayuwata cikin nutsuwa"

"Waye wanda za ki aura?" Yanda ya yi mini tambayar a kufule, shi ya tabbatar mini da cewa a kusa yake domun muryarsa har wani rawa take.
Sai kawai na share maganar ban ba shi amsa ba sanin da na yi ba ni da wanda zan aura ya sa na 'dauke kaina daga barin kallon masifar da yake mini.

Ya fizgo fuskata muka kalli juna, jikinsa na kyarma Ya ce." Ko waye sai na kashe shi!" Ya fada cikin wani irin yanayi gashi ya tsatstsare ni da jajayen idanuwansa.

Gabana na faduwa Na ce." Kisa fa ka ce?" Ya gyada kansa da sake tabbatar mini da maganarsa, rigarsa ya daga ya zura hannunsa cikin gajeran wandonsa ya fito da wata karamar bindiga!
Sai na ji fitsari yana kokarin kufce mini, gabana ya dinga dukan uku-uku! ga wani uban gumi na tashin hankali da ya yi mini dabaibayi, tunani nake a raina a ina ya samu bindiga?

"Da wannan zan kashe shi." Ya fada kamar wani taba'bbe! yana ta gyara bindigar.
Na yi namijin kokarin yi masa magana duk da a lokacin ina cikin tsananin tashin hankali Na ce.'' A Ina k..Samu bindiga waye ya baka lasisi?"
Shiru ya yi mini ya mayar da ita jikinsa ya kalle ni, lokacin gabadaya tunanina yana kansa Ya ce." Wallahi na ji maganar a bakin wani sai na sabauta miki rayuwarki.''
Furucinsa ya sa wasu zafafan hawaye kwaranya a fuskata! Murya na rawa Na ce." Rayuwar daka za'bawa kanka kenan? Ka tuna daga zuri'ar daka fito kakanmu babban Malami ne wanda ya yi shuru a duniya da riko da addini da al'kur'ani mai girma, Malam Zangina bai cancanci wannan sakamakon ba, don Allah ka tausayawa iyayenmu."

Ya jima yana kallona a lokacin da nake ta sharbar kuka! tsabar tashin hankalin ganinsa da bindiga,duk da ina jin haushinsa amma ina tausaya masa mutukar hukuma ta kama shi da irin wannan kayan ta'adin, tabbas ba shi kadai ba, mu kan mu, mun shiga bala'i.''

"Ni dai na fada miki duk wanda ki ka fadawa a cikin gidanmu to rayuwarki tana gagari, Bindiga kuma saboda Ke nake ajiyeta da ita, babu wani mahalukin da zai aure ki muddin ina raye."

Maganarsa ta jefa ni cikin tunani, kawai sai na tsinci kaina da fadin." Idan baka bari an aure ni ba kai zaka aure ni?" Idona a tsaye a kansa na yi masa tambayar.

Yasa hankici ya goge gumin goshinsa, ba tare da ya kalle ni ba Ya ce." Ni me zan yi dake ba kya cikin jerin matan da nake da burin aure, kawai dai bana ra'ayin wani Matsiyaci ya aure ki."

Wani kuttun takaici ya tsaya mini a wuya, ido na zuba masa ina wani tunani a kansa, da sauri na rike hannuwasa da yake driving, Na ce."Ka tsayar da motar idan ba haka ba sai na yi sanadiyar da duk muka rasa rayuwarmu."

Cigaba ya yi da tukar mota bai kalle ni ba 'karfina duka na tattara! na shaki wuyansa! sitiyarin motar ya kufce daga hannunsa motar ta fara tangal-tangal! a hanya.

Ihu! yake kurmawa yana kiran Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! kokari yake ya tsayar da motar abin ya gagara, saboda na turmushe shi! ga hannuwana shake da wuyansa! dukansa kawai nake ina fadin." Mutuwar mu ta fi akan wannan rayuwar da muke, ka zame mini masifa, bana bukatar wannan rayuwar gwara duka mu mutu! sai mun mutu! za mu mutu!"
Sambatun da nake kenan ina naushinsa ta ko'ina, hawaye da majina sai tsiyaya suke, shi kuma sai kokarin tsayar da motar yake har dai ta gangara wata hanya, Allah ya tsayar da ita, Ya dinga nanata Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!.

Kafin ki ce kwabo jama'a sun baibaye motar. Na yi saurin sauka da jikinsa ina goge fuskata, niqab dina na d'aura, shi kuma ya bude motar ya fita yana magana da mutune, ganin haka yasa ba tare da ya lura ba na bude motar na fita, hanya na mika na fara tafiya ina tikar kuka gwara na shiga duniya akan rayuwata a gida daya da Bahago!

Bayana ya biyo yana ta magana na yi masa banza, ya tare gaba na, "Wai ba zaki tsaya ba." Ya fada da alamun tashin hankali a tare da shi. Ture shi na yi zan wuce ya gaura mini mari a kumatu! yana wani irin nishi!
Kawai sai na kama shi da kokawa! dukansa nake ta ko'ina kamar mahaukaciya duka da cizo!
Ya zube kasan 'kafata, ya rike da kyau! jikinsa sai wani irin rawa yake, kafafuna ya rike sosai! nayi nayi na kwace kafata na kasa saboda rikon tsauri ya yi mini.

"Allah Ya baki hakuri." Kalmar da ta daki kunnena kenan. Abinda bai ta'ba faruwa ba a tsakaninmu, duk lefin da zai yi mini baya bani ha'kuri! sai jikina ya yi sanyi, jin yanda jikinsa yake rawa kalmar hakuri kuma ya fadi ya fi sau biyar.
Murya a dashe Na ce." 'Karya ka ke, kwanaki a gidan Anti Hamida haka ka yi, sabida haka ka kyale ni na shiga duniya rayuwa a tare da kai masifa ne."

Sosai ya rungume kafafuna" Ba zan iya barin ki ba, kin ga amana na dauko ki, mai ki ke so ya faru idan na koma gida babu ke, ina tausayawa Babanmu Danlami, idan akan maganar da na yi ki ke wannan abu to na janye babu ruwana da mijin da za ki aura."
Shiru na yi masa ban ce komai ba.
Ya ta shi tsaye yana kallona. A raunane Ya ce." Wuce mu tafi kada mu zama abin kallo a hanya, ga dare ya yi."
Dauke kaina na yi don har yanzu haushinsa nake ji.
"Jamila."
Sunana da ya kira yasa na kalle shi, nan na hango taruwar ruwan hawaye a cikin gidanuwansa.

Ya ce." Mai ki ka ga ni a tare da ni?"
Shiru na yi masa, Sai ya rike hannuna yana ja na haka muka shiga mota, ya kunna a hankali ya hau titin muka d'auki hanya.

Mun yi nisa sosai da tafiya ya dan kalle ni tare da cewa; Jamila ashe ba ki da hankali waye ya fada miki na shirya mutuwa yanzu? wato ke daga an yi miki abu sai ki ce za ki kashe kanki, shin kin san hukuncin wanda ya kashe kansa a gurin Allah kuwa?"
Cikin wani irin yanayi ya kai karshen maganar. Kuma tunda nake da shi bai ta'ba yi mini magana cikin kalami mai dadi ba sai yanzu.

Jin na yi shiru ban ba shi amsa ba Ya ce." Ka da ki sake irin wannan gangancin, ba don kowa sai don mahaifinki."
Na ce." Kai ma kada ka sake shiga rayuwata banza d'an-iska kawai d'an-ta'addah."

Na d'auka zai yi mini wani abu kawai sai na ga ya yi murmushi bai sake wata magana ba har muka isa gidan Mamana dake Unguwar Bolari. Ya samu guri ya yi parking, ba tare da na ce masa komai ba na bude motar da sauri na fita na shiga gidan ban saurari maganar da yake mini ba.

Ga mamakina kawai sai na ga ya shiga gidan babu neman iso har suna wasa da dariya da maigidan. sai na shiga tunani har yaushe suka san juna da sabo ya shiga tsakaninsu.

Da fara'a da girmamawa Mamana ta shimfida masa dadduma fuskarta a washe suka gaisa har tana tambayarsa bayan rabuwa.
Wai ashe yana zuwa gaisheta idan ya bushi iska amma bai ta'ba nuna mana ba.
Ya ce." Wallahi ayyuka ne sukayi yawa, k'arfin zaman nawa yana legos, yanzu ma hutu na zo shine Na ce." Bari na shigo mu gaisa, Babanmu Danlami ya ce na kawo miki Jamila ta gaisheki."
Yanda yake magana cikin kaskantar da kai da girmamawa shine abinda ya fi ba ni mamaki! a gaban idonta yana girmamata, amma a bayan idonta yana zaginta, sai na ji duk guiwa ta tayi sanyi duk wasu maganganun dana k'ullo domin na fada mata ina da tabbacin ba zata yarda ba duba da yanda na ga ya samu shiga a gurinta sai hira suke ni ina zaune kamar almajira"
Ya dan gyara tare da zira hannu cikin aljihu ya fito da kudi masu yawa ya ajiye mata a gabanta.
Ta dinga fadin." Ali wai baka gajiya da wahala ne? duk zuwa da hidimarka to Allah ya yi maka albarka."
Ya amsa da "Ameen yana sinne kansa Ya ce." Ina jiranki a waje idan kun gaisa sai ki fito mu tafi"

Kukan da nake dannewa ya kufce! Cikin zafin zuciya Na ce." Babu inda zan je, na riga na dawo hannun Mahaifiyata! munafiki macuci azzalimi!"
Sai ya sunkuyar da kansa da alamar damuwa a tare da shi.
Ita kuwa Mamana rufe ni tayi da fada! sai na rungumeta ina rusa kuka tare da fadin." Ba ki san halin da nake ciki ba ne shiyasa ki ke kokarin tura ni mahallaka! wannan da yake tsaye a gabanki rayuwata yake nema."
Ta ture ni daga jikinta tare da cewa; Ni ba zan yarda da maganarki ba tunda ga shi a gabana kin kuna mini zahiri, da Ali shine yake nuna miki k'iyayya sabida halin kuruciya, amma yanzu shi yake kula dake da d'awainiya dake, ni babu abinda zan masa sai addu'a, saboda haka dole ki koma domin nan ki ke da madafa.''

A sanyaye kamar wani mumini, Ya ce." Wallahi haka muke fama da ita a gida, taurin kai ne da ita, jar hanzu kiyayya take nuna mini, abubuwan da suka faru a baya ni a ganina duk kuruciya ce, Jamila 'Yar-uwata ce sai inda karfina ya kare a kanta."
Ta ce." Je ka waje yanzu za ta fito ku tafi kada ka damu, na san ai lefin duk nata ne."
Ya dan rusuna da cewa" To shikkenan Mama Allah ya bamu alheri."
Yana fita ta rufe ni da fad'a har tana kokarin yi mini baki abinda ya tsorata ni kenan, na shiga bata hakuri tare da yi mata alkawari In sha Allah zan yi yanda take so, haka na tashi jikina duk a salube ina kara jadadda makircin Bahago a cikin zuciyata, Wato ya bi dare da rana ya siye iyayena, ni kuma yana azabtar da ni, ban san ya rayuwata zata kasance anan gaba ba.''

Leda viva ta ba ni cike da kayayyaki na karba na yi godiya na fito na sake riskar maigidan suna hira da shi, har kasa na tsuguna na yi masa sallama ya dauki dubu biyu ya ba ni, jiki ba kuzari na shiga mota na zauna kaina na wani irin sarawa!

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment