Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga gaisheta sai ta zaunar dashi da maganganu marasa dadi a kan 'Danjuma d'anta na biyu kenan ta dinga sukarsa akan baya yi mata alheri alhalin yana aiki a kamfani, watarana yini take da yunwa! to sai hakan sai ya fusata! Sammani ya samu D'anjuma da maganar cikin hayaniya, sai kuma rigima ta kaure a tsakaninsu domin dai D'anjuma ya san yana iyakar bakin 'kokarinsa! idan taga suna fad'a da zagin junansu sai ta fashe! da kuka! ta samu 'Danjuma a gefe d'aya ta ce"Ita fa 'karya Sammani ya yi mata kawai yana yi masa hassada ne don ya ga Allah ya rufa masa asiri." 'Danjuma sai ya ajiye hakan a cikin ransa yana kallon Sammani a matsayin mai masa hassada! D'anlami 'karamin cikinsu da yake yana da nutsuwa sosai kuma kamar ya fi su tunani! shine ya zaunar dasu ya yi musu sulhu tare da jaddada musu cewa hakan da suke ba daidai ba ne, kuma duk wasu maganganu da mahaifiyarsu zata fad'a a tsakaninsu kada su yarda hakan ya zama sanadiyar lalacewar zumuncinsu! shine ya kara tunasar dasu Halayyar mahaifiyarsu tun zamanin kuruciya kawo yanzu da girma ya baibayeta! kawai addua ya kamata suyi mata Allah yasa ta gama lafiya.
Wannan azancin na 'Danlami ya sanya sun nutsu sun kuma yi sulhu a tsakaninsu, sun kuma fahimci mahaifiyarsu ita ce ke haddasa duk wani tashin hankali a gidan. haka suka cigaba da yi mata biyyaya tare da 'kokarin faranta mata da kuma nusar da ita cikin lisilama ba tare da hakan ya sosa ranta ba.

Haka rayuwarsu ta cigaba da tafiya yau fari gobe ba'ki, sun had'e kansu tunda sun gane halin mahaifiyarsu sai suke hakurin zama da ita tare da yi mata adduar shiriya, kuma ba su sake barin wata 'baraka ta shiga tsakaninsu ba.

Kawu Sammani ya kammala komai da ya danganci aure har gurin da zai zauna da iyalinsa ya gyara tunda gidan babba ne, sai dai fafur! Tokar ta'ki aminta da matar da zai aura a cewarta yarinyar bata da tarbiya kuma mahaifinta karamin mutum ne, Sammani ya shiga halin damuwa! ya rasa yanda zai yi da rayuwarsa kawai sai ya tattara lamarin auran ya ajiye a gefe ya cigaba da neman kud'insa, rana tsaka ta tara su duk su ukun, ta kallesu da cewa; Sammami da 'Danjuma Allah ya rufa muku asiri tunda kuna da abin yi. saboda haka na za'ba muku matan da zaku aura. Kai Sammani zaka auri Hama 'yar gidan Lantana 'kawata. kai kuma 'Danjuma ka je gurin Sailuba 'yar gidan 'Kanwata Larai sai ku daidaita kanku domin bana so a ja dogon lokaci." Cike da bada umarni ta kai karshen maganar.

Gabadaya jikinsu ya yi sanyi! babu yanda suka iya da lamarinta haka suka amsa ba don ransu ya so hakan ba, kawai sun bi umarninta ne.

Yanda yanda ta bukata ba a ja dogon lokaci ba akayi komai a kammala amare suka tare a cikin gidan. kowanne da 'kofarsa. sati d'aya da faruwar al'amarin zamantakewar gidan ta lalace! domin dambe da fad'a! ne ya dinga faruwa tsakanin Hama da Sailuba, kuma ba kowane sanadi ba sai Uwar mijinsu ita ce take haddasa rikicin! a duk lokacin da wata daga cikinsu ta shiga da niyyar gaisheta anan take had'a gurmin! a'lamarin dai ya tsananta! wanda ya janyo har mazajensu suka san da abinda yake faruwa! suka zaunar dasu domin sulhu! Tokar tana daga cikin daki tana jinsu ba ta ce uffan ba. Kawu Sammani ya leka dakin ya ce mata ta fito tayi musu fada akan abinda sukeyi. bud'ar bakinta sai ta ce." Ni ma ba jin maganata suke ba sun raina ni, domin idan suna fadan watarana har zagi na sukeyi."

Wannan maganar ta sake dugunzuma! zuciyoyin mazan! suka ce kowacce ta tattara kayanta ta tafi gidansu tunda abin na su ya kai kan mahaifiyarsu. Jin irin hukuncin da suka yanke yasa da sauri ta fito tana fadin.'' A'a ba za'ayi haka ba, kowacce ta koma d'akinta ta zauna sai dai idan ba su daina fad'a ba, to sai kuyi musu kishiyoyi watakila sai gyara halinsu."

Tun daga ranar Hama da Sailuba suka shiga taitayinsu suka fahimci cewa; lallai Tokar ba surukar arziki ba ce, kuma ita ce take haddasa rikici a tsakaninsu amma shine take cewa ayi musu kishiya bayan sharrin da tayi musu, sai kowacce ta shiga hankalinta suka fahimci juna tsakaninsu mutunci ne da girmama juna.
Hakan bai yi wa Tokar dad'i ba, domin gabadaya ware ta sukayi a gidan, suka daina shiga huruminta idan sun gaishe ta sun kai mata abinci shikkenan babu wani abu da yake k'ara shiga tsakaninsu sai idan gari ya kuma waye wa.

Tokar ta zauna da yaranta tana kuka tare da sheda mata irin cin kashin da matansu suke mata, sun mayar da ita saniyar ware a gidan, babu mai kula ta abinci ma don dai ya zama dole ne suke ba ta.
To da yake sun san halin mahaifiyarsu sai suka rarrasheta tare da jaddada mata cewa; Za su ja wa matan nasu kunne akan abinda suke yi.

Wannan ya wuce da wasu watanni, sai kuma ta fara tashin hankali a gidan cewa; ita fa ta ga ji da jiran gawan shanu! suna zaune d'irka-d'irka da su sai da su ci-su sha sannan su wanke goma su tsoma biyar! don haka ita fa tana bukatar ganin jikokinta, a yanda haihuwar yanzu ta zama ya kamata a ce sun haihu ko kuma a gansu suna cire 'kara da 'kyar! ma'ana haihuwa ko yau ko gobe! amma shiru malam ya ci shirwa gashi yau wata goma cif da auransu.
[6/9, 3:58 PM] bintaumarabbale: 6
To a she a lokacin da ta tayar da wannan rikicin Hama Matar Kawu Sammani na d'auke da ciki na sati hud'u wanda itama bata tabbatar da shi ba sai da ta ji shiru a watan ba ta yi al'ada ba, sannan ta fara zargin wani faruwar wani abu tunda dama tun kafin zuwan lokacin tana rashin lafiya mussaman zazza'bi da kasala da tashin zuciya, To ko da suka je asibiti aka duba ta likita ya tabbatarwa da Kawu Sammani ciki na sati hudu wata d'aya kenan, cikin farinciki suka dawo gida da kyakykyawan albishir, Tokar ta rangad'a bud'a! farinciki take sosai da samuwar cikin, sai ta shiga lallaba Hama! bata san ba'cin ranta ko d'an! ta dinga bin hanyoyi marasa kyau tana cuzgunawa! Sailuba kullum cikin gori! da ba'kar magana, yanda Tokar take gallazawa Sailuba kamar ba 'yar 'kanwatar ba, domin shi kansa Kawu 'Danjuma abin yana damunsa don dai babu yanda zai yi ne, ya riga ya san haihuwa Allah ne yake bayarwa ba. Sailuba duk dare kafin ta yi bacci sai tayi kuka saboda tsabar bakin ciki da takaici! ga shi duk wahalar da take yi ba'a gani, dawainiyar gidan duk ita take dauka girkin safe na rana da kuma na dare sam bata da lokacin kanta dalili Tokar ta d'aurewa Hama gindi wai ciki ne da ita ba za ta yi aikin wahala ba, Kawu 'Danjuma ya so ya raba tukunyar gidan saboda a ransa ya san ana zalintar matarsa, ko da ya tunkari Mahaifiyarsa da maganar sai ta buga tsalle ta ce bata amince da wannan tsarin ba, Sailuba ita za cigaba da kula da hidimar gida har sai lokacin da Hama ta haihu tunda dai ita juya ce bata haihuwa to aikinta girki da wanke-wanke da shara!
Kawu 'Danjuma ya janye maganar duk domin samun zaman lafiya a gidan, 'bangaran Sailuba kuwa da abin ya yi mata yawa kawai sai ta tattara kayanta ta gudu gidansu tana kuka ta shedawa babarta duk irin gallazawar da Tokar ta ke yi mata.
Zulai Ta fusata! sosai ganin yanda 'yarta ta rame ta kojale! yarinyarta mai garin jiki amma duk ta lalace! gaskiya ba zata lamunta ba dole ta yi wa tufkar hanci.


"Kin ga Zulai ba za ki zo har cikin gidana cikin dakina ki zage ni ba, da kaina na bu'kaci! Danjuma ya auri Sailuba, sai dai kuma yanzu gabadaya auran ya fice mini daga raina domin kuwa babu riba, aure shekara guda amma babu wani labari duk sa'oin auransu sun haihu ita kuma shiru sai da ta ci- ta sha! ta shiga bandaki, to ba zai yuwu ba ina bukatar ganin jikoki a gabana."

Zulai ta ce" To In ban da abinki Tokar har yaushe akayi auran da za ki fara 'korafi duka duka fa wata goma sha biyu yanzu ina wadanda suke shekara goma ba su haihu ba ai wani jinkirin alheri ne."

"Yo ina wani alheri a jinkiri? gaskiya 'Danjuma ba d'an wahala ba ne da zai dinga nemowa yana kawowa 'yarki tana cinyewa amma ta kasa d'aukar 'kwan haihuwa a mahaifarta gaskiya da sake."

Zulai ta fusata! ta ce" To yanzu wai ya ki ke so ayi ne? Kin san dai Allah shine yake bada haihuwa ba wani mahalu'ki ba." Ta ce." To gaskiyar magana zan fada miki Zulai 'Danjuma zai 'kara aure domin dai Allah ya yassare masa zai iya rike mace hud'u saboda haka ba za'a tauye masa hakki ba."
Zulai ranta ya 'baci ta ce." Tokar yanzu abinda zakiyi mini kenan? kada ki manta fa Sailuba 'yarki ce kamar 'Danjuma shine zaki rufe ido ki ci mini mutunci wato ke baki san Allah ba ko?"

"Kada ki zage ni Zulai domin kuwa ranki zai 'baci wallahi! ko yanzu na yi ra'ayi zan Umarci Danjuma ya rabu da Sailuba domin dama tilas na yi masa baya sonta, saboda haka aure D'anjuma zai 'kara domin ya samu haihuwa."

Zulai idonta ya ciko da ruwan hawaye! ta mike tsaye cikin fushi! Ta ce." Ba ki cika 'yar halak ba sai kin sanya 'Danjuma ya saki Sailuba sannan zan san cewa; baki da mutunci." Wannan maganar a kunnen 'Danjuma a lokacin da yake kokarin shigowa dakin, kawai sai ta fashe da kuka tare da cewa" Zulai ni ki ke zagi har kina kira na da mara mutunci!" Kuka wurjajan! ta ke yi har da majina! Zulai ba ta sake wata magana ba ta fita daga gidan cikin tsananin 'bacin rai!
To a lokacin ta zaunar da 'Danjuma ta shirya masa 'karya da gaskiya! ta kuma ce lallai ya rubuta takardar saki uku ya aikawa da Sailuba domin kuwa wannan ne kadai matakin da za ta d'auka akan irin cin mutuncin da Zulai ta zo har gidanta ta yi mata.
Kawu 'Danjuma ya dinga nusar da ita illar abinda ta sanya shi, Allah da kansa ya hallata saki amma ba ya jin dadi a duk lokacin da a ka yi shi, gaskiya ba ya jin zai iya sakin matarsa tunda yana sonta iya zaman da ya yi da ita bata ta'ba munana masa ba!
Ganin yana so ya bijirwa Umarninta ya sa hankalinta ya ta shi, wato Zulai ta shiga ta fita tana nema ta sanya d'an cikinta ya bijerewa Umarinta, kawai sai ta hau cin mutuncinsa ta in da take shiga ba ta nan take fita ba, ta ce muddin bai saki Sailuba to sai ta tsine masa albarka.
Ganin yanda ta fusata! ya sanya ya yanke shawara a cikin zuciyarsa, ya riga ya san wacece Tokar tsaf za ta iya yi masa baki ko kuma ta tsine masa kamar yanda ta kud'irta a zuciyarta!
Kawai sai ya furta da bakinsa cewa; Ni 'Danjuma na saki Mata ta Sailuba saki d'aya. Hakan bai yi mata ba ta ce saki uku take buk'ata! jikinsa ji'ke da gumi ya ce." Tokar d'ayan ma ya wadatar don Allah ki yi hakuri idan tunda ba kya bukatar zamana da Sailuba wallahi na hakura da ita har abada."
Ta ja tsaki da cewa'' Yo me za'ayi da auran irinsu ai babu riba, kuma kamar yanda ka fada babu kai babu ita har abada idan na ji labarin ka je gidansu biko sai na tsine maka albarka." Ya ce." Hakan ba za ta faru ba in sha Allahu." Takalmansa yasa ya fita daga gidan hankalinsa a tashe.
Ita kuwa Tokar a daran ranar ta lulluba mayafi ta nufi gidan Zulai da takardar sakin Sailuba.

Cin mutunci ta zuba a gidan i ya son ranta kafin ta jefar da takardar sakin ta kama hanya ta fita tana cigaba da surutai irin na rashin arziki! Zulai da Sailuba kwanar kuka da Takaici Sukayi. hakika Tokar ta basu mamaki! ganin irin hallancin da sukayi mata a lokacin da ta bu'kaci had'a auran akwai maganar wani amma suka ture mahaifin Sailuba ya kar'bi maganar hannu biyu acewarsa gida bai k'oshi ba ba za'a kai dawa ba. Ashe bacin rai ne zai biyo bayan al'amarin.

To da yake Allah yana duba zuciya cikin ikon Allah Sailuba na gama iddah tsohon saurayinta ya dawo kuma da niyyar auranta tunda shi Gaskiya yana sonta har yanzu. aikuwa ba a ja dogon lokaci ba akayi aka gama amarya ta tare a sabon gidanta ginin zamani gashi komai na budurwa angonta ya yi mata lallai wani hanin ga Allah baiwa ne. Tokar hankalinta ya tashi ainun! ta bud'ewa 'Danjuma wuta lallai ya nemo matar da zai aura idan ba haka ba to za ta nemo masa.
Jin haka ya sa babu shiri ya fara neman matar aure. lokacin Hama matar Kawu Sammani ta haihu yarinyar ta yi wayo sunan Tokar ne da ita sai ake kiranta da Hamida. Kawu 'Danjuma ya nemo matar aure wacce yake ganin zai samu daidato da zaman lafiya da ita amma kafin tabbatuwar al'amarin ya sheda mata halin mahaifiyarsa ita kuma ta ce babu komai ai tsofaffi sai da rarrashi! aka kammala komai cikin walwala da farinciki domin ba a samu wani tasgaro daga 'bangaran Tokar ba, Amarya ta tare a d'akinta!
To tafiya na tafiya amarya Atika har ta yi wata shida babu wani labari, sai narka uwar 'kiba take yi, Tokar ta fara habaice-habaice tana yar da magana wanda Atika ta fara fahimtar da ita take.
Tun tana daurewa har ta ga ji ta fara mayar da martani! domin gaskiya ba za ta iya jurewa ba, anan Tokar ta fara ikirarin idan ba ta daina yi mata rashin kunya ba to za ta sa 'Danjuma ya sake ta ko kuma ya 'kara aure! Atika ta mayar mata da magana mai zafi! wanda ya sanya a ranar ta yini tana kuka da fyace! hanci! Ita dai Hama matar Kawu Sammani 'yar kallo ta zama tana godewa Allah da ya 'kwace ta.

A na tsaka da wannan dambawar 'Danlami wato auta ya rakito aure kuma Bayerabiya irin masu tallan magani a cikin kasuwa! turkashi! An sha badakala kafin Tokar ta amince da lamarin acewarta ba za a gur'bata mata zuri'a da wata 'kabila ba, da 'kyar Malam Iliyasu abokin mijinta mai rasuwa ya rarrasheta tare da kawo mata hadisai da ayoyin al'akurani mai girma wato yin hakan ba Haram ba ne, sannan fa ta amince al'amarin ya yiwu Amarya Hansatu ta tare a d'akinta! Har lokacin Tokar ba ta 'kyale Atika ba kullum cikin ba'kar magana da gori iri-iri!
Itama Hansatu da ta zo daga baya sai da ta fahimci wani abu Hama matar Sammani ita ce Mowa a gidan su kam sun zama bayi 'ya'yan wahala! ba su da hutu a gidan kullum cikin aiki da d'awainiya kuma ba a ga ni, kawai sai ta yanke shawara a zuciyarta, mijinta yana dawo wa daga gurin sana'arsa ta siyar da shayi ta ce" Ita kam ba za ta iya zaman bauta ba duk ta kwashe abinda yake faruwa a gidan ta fad'a masa, bai yi jayya da ita ba domin ya san abinda ya fi haka ma zai faru, ya rarrashe ta da cewa; Za a raba tukunya ta dinga yin girkinta hakan shine maslaha idan ya so idan ta gama abincin sai ta zubawa Tokar din a kwano ta kai mata.
Wannan tsarin bai yi wa Tokar dad'i ba kawai dai ta ha'kura ne jin surutai da k'ananun maganganu na yawo a gari na irin gallazawar da takewa surukanta wannan dalilin ya sa ta rage wasu abubuwan ta 'kyalesu suna cin gashin kansu, sai dai duk wacce ta kai mata abinci a cikinsu sai ta kushe! ko ta kira almajiri ta ba shi, abincin Hama kawai take ci babu tsagu-na-guni!
[6/11, 7:03 PM] bintaumarabbale: 7
Wani Ikon Allah auran Sailuba wato tsohuwar matar 'Danjuma ya yi albarka domin tana shiga ta samu ciki. Jin wannan labarin sai ya d'aga hankalin Tokar ta sake zage damtse gurin ganin ta cuzgunawa Atika mussaman da ta tabbatar da cewar Hansatu ta samu ciki dan kusan a tare suka samu da Hama matar Sammani suke ta laulayi a lokaci guda. Hakan ya tashin hankalin Atika dan Tokar ta hana ta shan ruwa a gidan, Aiki kamar ya kasheta ga kuma kyara da tsangwama iri-iri! Babu shiri ta tattara kayanta ta gudu gidansu dama haka Tokar din take buk'ata! 'Danjuma ya yi yun'kurin zuwa ya yi bikon matarsa ta ce ba da yawunta ba, idan ya je sai ta d'aga masa nono ma'ana ta tsine masa albarka muddin bai rubuta takardar saki ya aika mata ba.
Wannan karon har sai da ya zubar da hawaye saboda tsananin tashin hankali da damuwa! 'Yan uwansa sune suka dinga rarrashinsa ya yi hakuri ya yi mata biyayya kamar yanda ta bu'kata! 'Danjuma yana zubar da hawayen ba'kinciki ya rubuta takardar saki ya je har gida ya kai mata yana ta bata hakuri! Atika ta ji ciwon abin sosai! sai ta barwa Allah mussaman da ta tabbatar da cewa ba laifinsa ba ne, Mahaifiyarsa ce ta tursasa shi, tabbas Allah zai maye mata gurbi da wanda ya fi shi, 'Danjuma kuwa ya 'kudure a ransa cewa; Sai ya huta tukkuna zai sake wani auran domin baya so jama'a su dinga yi masa kallon Namiji mai auri saki.
***
Cikin hukuncin Ubangiji nak'uda ta kama Hama da Hansatu a rana d'aya, Hama ta haihu da safe misalin takawas da rabi, ita kuma Hansatu ta haihu daf da magariba. Tokar ta ji haushin sosai ganin Hansatu ta haifi 'ya mace! sam bata nuna gand'oki akan jaririyar ba, tana can gurin Hama wacce ta haifi santalelen d'anta Namiji wanda ya dauko siffar mijinta Malam Zangina, ta d'auki son duniya ta d'ora masa, kuma ko da wasa bata je ta ga abinda 'Danlami ya haifa ba saboda tana zaune labari ya iske ta cewa; 'Ya mace aka haifa ba'ka mummuna kamar uwarta, a lokacin ta fara zargi da was-wasi! domin dama abinda take gudu kenan a gur'ba mata zuri'a.
Bayan anyi suna da sati uku. 'Danlami rungume da 'yarsa Jamila ya nufi gurin Mahaifiyarsa da ita dan ya ga ji da abunda ake masa a gidan dashi da matarsa.
Ya yi sallama ya shiga ya zauna rungume da yarinyar a jikinsa. wani irin kallo take masa dashi da yarinyar, ta amsa gaisuwarsa kamar bataso, ya danne damuwarsa ya ce." Na kawo miki Jamila ne ku gaisa ga tanan tayi wayo." Da yake tana da san girma tayi gwa'bi kamar anyi kwana ar'bain da haihuwar.
Ta ce." Danlami ni fa wannan yarinyar kamar ba jini na ba." Gabansa ne ya fad'i jin abin abinda take fad'a. Muryarsa na rawa ya ce." Tokar wace irin magana ce wannan? don Allah kada zafin 'kiyayyar da ki ke wa uwarta ya sa ki sheganta jininki."
Bakinta ta ta'be Ta ce." Ai abin ne da mamaki wallahi! duba jikinta ko'ina dulum! babu haske sai na 'kwayar idonta kuma sam ba ta d'auko kammaninka ba ko ta yatsu! can ta kwaso kammanin Uwarta kafirai!"
Girgiza kansa ya yi ya numfasa ya ce." Tokar na sha fada miki cewa; Kasancewar Hansatu Bayerabiya ba zai sanya ta cikin jerin kafurai ita da ahalinta ba, dukkaninsu musulmai ne masu riko da addin Allah, don na ganta a kasuwa akan sana'arta na aureta ba laifi ba ne, shari'a ta hallata mini auran karuwa mutukar ta tuba ga Allah ta yi istubura'i zan iya auranta mu raya sunnah! kuma mu haifi 'ya'ya masu albarka, to balle Hansatu da a gaban iyayenta na aure ta kuma na samu budurci a tare da ita, wannan dalilin ya sa bana kokwanto akan wannan yarinyar dake hannuna domin kuwa ni ne Ubanta, saboda haka don girman Allah da Annabi ki cire son zuciya ki rungumi wannan yarinyar a matsayin jininki kada wani ya ji wannan maganar daga bakinki."

Jikinta ne ya yi sanyi da jin kalamansa, sai ta dinga satar kallon yarinyar dake hannunsa tana ayyana abubuwa da yawa a cikin ranta, ita dai haka kawai jaririyar bata kwanta mata a rai ba, zuciyarta ta fi gazgata mata cewa; Hamida da Aliyu 'ya'yan Sammani sune jinin ta.

Tun ina yarinya na fahimci irin 'kiyayyar da Tokar take yi mini, dalilin da ya sanya kenan tsakaninta da Mamana babu jituwa kusan kullum cikin rikici suke domin yanzu ko kad'an Mamana ta daina rangwanta mata! Idan ta fad'a mata magana a gurin take mayar mata da martani! tana ganin hakan shine daidai don bahaushe ya ce idan Babba ya zubar da girmansa sai 'karami ya hau ya taka.
Nima ganin irin 'Kiyayyar da take nuna mana ya sanya ko gurinta bana zuwa kullum ina 'bangaran mu, kuma idan ta aikeni wani gurin bana zuwa guduwa nake yi, sai ta kai 'kara ta gurin Babana wai ina zaginta kuma idan ta aikeni bana zuwa rashin kunya nake mata, A ranar na ci duka sosai! na yi ta kuka ina bashi hakuri ba zan sake ba, Mamana ta ji ciwon abin amma bata tanka masa ba har ya 'karaci fad'ansa ya fita daga gidan.
Bahago ya dinga le'kowa yana tsokana ta yana yi mini dariya, hakan ya 'kara tunzuwa mini zuciya dama kuma bama shiri ko da yaushe cikin fada muke muddin zamu had'u sai mun raba gari a makaranta ma haka Malamai suke shan fama da mu tare da mamakin irin 'kiyayyar da mukewa junanmu.
Ganin har yanzu bai daina yi mini dariya ba yasa na tashi a fusace! na bi bayansa da gudu! sai ya yi hanyar fita waje yana fad'in" Ki fito wallahi sai na ci Ubanki." Jin yana zagar mini Uba yasa na sake harzu'ka!na d'auki dutse! da gudu na bi shi, ashe ya la'be a bayan 'kyaure ina fita ya tad'e ni na fad'i a kasa! bakina ya fashe ya fara zubar da jini, ya cigaba da dariya tare da fadin." Mai rubabben baki 'kazama! kawai." Kuka ne ya 'kwace mini! Na yun'kura domin na tashi yasa kafarsa ya take mini yatsun hannu! Ihu! na kurma! ina zaginsa! ko a jikinsa ya yi tafiyarsa yana ta dariya!
Zuciyata a 'kuntace na tashi har yanzu bakina na d'igar da jini! ina kuka na samu Babarsa na fad'a mata, ko kallona ba ta yi ba ta cigaba da aikinta, sai na nufi gurin Tokar duk da na san ba wani mataki zata dauka ba tunda ba wannan ne farko ba.
Ta kalle ni tare da Cewa" Tsokanarsa ki ka yi dan na san halinki da rashin kunya Iyayenki ma baki bari ba, saboda haka ki wuce ki bani guri."
Na ce." Allah ya isa ban yafe ba." Da sauri Ta ce."Jamila Ni ki ke wa Allah ya isa to ni me nayi miki?" Banza na yi mata na fita daga dakin hawaye masu zafi na karakaina a saman fuskata.

Wannan karon Mamana kasa jurewa ta yi, domin dai wannan cin zalin ya yi yawa! don haka a fusace! ta Nufi gurin Baba Hama domin ta jawa danta kunne! fad'a ne ya kaure a tsakaninsu, Baba Hama sai sakin maganganu take yi har da fad'in.'' 'Yar taki da har yanzu ake kokwanto a kanta shine har ki ke wani tayar da jijiyar wuya to duk abinda yake faruwa muna da labari."
Mamana a lokacin ta yanke jiki ta fad'i! Ashe tana da iskokai! wanda basu

Please Login or Register in order to submit comment