Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a tsorace nake da shi, saboda dakin da duhu! ga Tokar tana bacci, tsoro nake kada ya yi mini iskanci! tunda dama hakan halinsa ne.
Ya ce." Magani na kawo miki amma ki yi hakuri nayi dare ban kawo miki da wuri ba."
Tsaki Na ja tare da cewa" Bana bu'kata." Na koma na kwanta ina rufe kafafuna.
Yasa hannu ya cire zanin dake jikina, kafar ya janyo yana haskawa da fitilar wayarsa.
"Wai meye haka ne?'' Na fada da karfi da kuma fargaba! don ganin yanda yake shafa mini dunduniya 'kafa!

Tokar cikin bacci ta ambaci sunana "Jamila menene?" Fashewa na yi da kuka na cire dankwalin kaina na jefar dashi sannan nayi saurin zuge zif din rigata na sa'bule wuyan k'irjina ya fito dama bana sa rigar nono idan zan kwanta, cikin kururuwa! Na ce." Bahago ne ya shigo yana tatta'ba mini jiki har ya cire mini riga."
Zumbur ya tashi daga kusa da ni ya matsa can gefe, Tokar ta kunna fitilarta mai hasken gaske! duk gaggawar da ya yi gurin fita daga dakin sai da ta ga gilmawarsa.

Fargaba na ga ni a tare da ita sai haska ni take da fitilar hannunta, jikina na makyarkyata Ta ce." Be yi miki komai ba?"

Ina gyara wuyan rigata Na ce." Ya tatta'ba ni, sosai kuma dama ba wannan ne karo na farko ba ya jima yana yi mini." Ta rarrafo kusa da ni "Don Allah ki rufa masa asiri d'an uwanki ne, idan ki ka tozarta shi kamar kin tozarta kanki ne, kuma zuri'ata za ta shiga bakin duniya, ki yi mana suttura kada ki fadawa kowa mu kashe mu binne."
Dariya ta kusa kufce mini ganin yanda take 'kaskantar mini da kai, cikin zuciyata Na ce."Ashe akwai abinda zai firgita matar nan.

"A a wallahi, ni ba zan iya shiru ba domin wannan lamarin dole manya su sani, ayi wa tufkar hanci, haka kawai ba zan zauna ya cutar da ni ba, tunda dai idonki ya nuna miki gaskiya ai ba za ki ce anyi masa sharri ba, gashi iskancin nasa har cikin gida ya zo ya cire mini riga yana taba mini kirjina, gaskiya sai na fadawa Kawu Sammani ko kuma na gudu gurin Mahaifiyata."

Kuka ta fashe dashi, ta rike hannuna a lokacin ina jin yanda jikinta yake karkawa! majina na zurara! Ta ce." Jamila kada kiyi mini haka ki rufa mini asiri don Allah, kada ki fadawa kowa maganar nan, kuma kada ki gudu ki bar ni, ai idona ya nuna mini komai, kuma na yarda ba'ayi masa sharri ba, Ki yi hakuri In sha Allah zan ja masa kunne."
Ganin yanda duk ta fita daga hayyacinta yasa Na ce." Shikkenan na ha'kura amma ki ja masa kunne wannan ya zama na farko kuma na k'arshe, idan ya sake kwatantawa to sai na fad'a kowa ya san abinda yake."

Da sauri ta ce." In sha Allahu Rabbi, Zan ja masa kunne. Na ce" Ki koma ki kwanta sai da safe." "A'a bari na kwanta kusa dake tsoro nake kada ya dawo ya haike miki."
Dariya maganar ta bani, cikin zuciyata Na ce." Shikkenan kwanta." Aikuwa ta raku'be jikin shimfid'ata! har da dora hannunta akan cinyata, tausayinta ya rufe ni, ashe tana 'kaunata, tunda take gudun abinda zai cutar da ni. Sai kawai na ji hawaye sun kufce mini, nasa hannu na rugumeta sosai, haka bacci ya kwashe mu ma'kale da juna.
[6/22, 4:15 PM] bintaumarabbale: 10
Washe gari da safe muna karya kummalo ta dinga ro'kona akan na yi shiru da maganar ka da na fadawa kowa domin idan na rufa masa asiri kamar kaina na rufawa, kuma in sha Allahu za ta tsawatarsa masa, Ni har ga Allah na manta da abinda ya faru, to ganin yanda duk ta tayar da hankalinta ya sa na yi mata alkawarin babu wanda zai ji maganar, zan rufa masa asiri kamar yanda ta bu'kata.

Muna gama karyawa na had'a kwanuka da kofunan da mu ka yi amfani na kai gurin wanke-wanke. Ina k'okarin janyo ruwan da zan yi amfani dashi na ji motsi a bandaki, daga kaina na yi muka had'a ido ya fito da bokitin wanka a hannunsa saurin dauke kaina na yi ina mamakin yawan wankan da yake da sassafe, ban ce masa komai ba na matsa masa hanya don ya wuce, sai ya ajiye mini singilet dinsa da hankici gudu biyu wai na wanke masa. ko kallonsa ban yi ba na cigaba da jan ruwa a rijiya.

Cikin masifa kamar Ubana Ya ce." Ko ba kya ji ne?" Fuska a turbune! Na ce." Gaskiya ba zan iya wanke wannan singiletin ba don wani irin wari take, ga daud'a kamar ba daga jikin mutum ba.''

''Ke Ni ne kazami?" Ya fada yana tsatssare ni da manyan idanuwansa da suke kullum a lumshe! Shiru na yi masa na fara wanke-wanke na, bana tsammanin zan iya ta'ba singiletin domin tunda ya ajiye ta a gurin take tsami!
Gurin ya bari minti biyu ya dawo da wasu kayan a hannunsa, ya zuba ruwa a bokiti ya zuba kayan a ciki ya zazzaga kilin, Ya kalle ni, "Ki wanke mini su duka zan baki dari biyu."
Dariya ya ba ni, Na ce."Ko dubu biyu za ka ba ni, ba zan ta'ba najasa ba." ido ya tsira mini yana kallona, gabana ya fara bugawa don na riga na san halinsa da saurin hannu zai iya buge ni a gurin, aikuwa kafin na yi aune na ji saukar hannunsa a jikina, ihu! na kurma! na kwashi ruwan kumfa da dattin abinci na watsa masa a jikinsa. "Ba zan wanke ba din, kai aikin me ka ke yi da zaka ce lallai sai na yi maka wanki."
Matan gidan suka firfito, Tokar ma ta leko daga dakinta tana fadin." Bahago kada ka sake dukanta ranka zai 'baci kuma kazo ina so na yi magana da kai kafin ka fita."
Mari ya kai wa fuskata nayi saurin gocewa! Mahaifiyarsa ta janyeshi daga gurin, Baba Iyami ta rike hannuna tana rarrashina domin a lokacin Ni ma na fara rarume-rarumen makamin da zan dauka don na kwaci kaina, fadi take "Ki bar ganinki gansamemiya Bahago ya fi karfinki ba tun yau ba kin kasa fahimta duk lokacin da rigima ta hada ku, ba kya samun nasara, ki daina biye masa idan ba so ki ke ya k'arasa zubar miki da sauran ha'koran dake bakinki ba.''
Kuka sosai na ke yi, Na ce" Baba Iyami na tsane shi wallahi, bana so na bude idona na gan shi, ina ganin zan gudu can dangin Mamana na huta da wannan masifar."
"A'a ba za'a yi haka ba, addu'a za ki tsananta Allah ya kawo miki mijin aure shikkenan ki huta, amma Ni kaina bana sha'awar irin rayuwar da ki ke yi, a gidan nan." Rungumeta na yi a jikina ina jin wani irin kaunarta, ita ce kawai mai rarrashina a gidan sai Anti Hamida da itama take iyakar bakin kokarinta.
Tokar ta rarrafo har bakin kofar dakin Baba Iyami ta dinga zazzaga mata rashin mutumci, wai ta meye ruwanta da shiga sabgar dangi ita da aka auro shine zata sa ni a daki tana zuga ni, Baba Iyami dai ta yi mata shiru, har ta k'araci cin mutuncinta ba tace mata komai ba.

Ko da na shiga dakin ban saki fuskata ba dan ganinsa a zaune suna magana da Tokar d'in, tsallake su na yi na je na kwanta tare da fashewa da kuka mai karfin gaske!

Ita da shi duk suka zuba mini ido Tokar jikinta ya fara karkarwa ita dai tsoronta kada na tonawa d'an lelenta asiri! Ashar! ya lailaiyo! mini jikinsa na rawa! yake fadin." Ni za ki yi wa sharri don Uwarki!" Zumbur na tashi zaune tare da cewa; Ba dai uwata ba, kuma kai baka isa na yi maka sharri ba, mazina ci fasiki Allah ya kare ni daga sharrinka."
Ya dinga kallona yana ciccije bakinsa, Ya sake lailayo wani ashar din Ya ce." Menene abin sha'awa a tattare dake da har zan biyo dare na yi miki wani abu, ko da nake neman mata masu irin suffarki ba sa ba ni sha'awa, 'Yar iska mummuna ai da wuya ki samu mashinshini!" Maganganunsa kaf a kunnan Kawu Sammani. Ya fitar da hannu ya dinga gaura masa mari! Ita kuwa Tokar sai kuka take da majina a dakalin hancinta, fadi take shikkenan kuma zuri'ata zata shiga bakin duniya ya rasulu kazo da kanka ba sako ba.'' Duk da halin da nake ciki na damuwa sai da dariya ta kusa kufce mini ganin abinda Tokar ta ke yi na sambatu.
Kawu Sammani ya kalle shi da jan ido Ya ce" Kul! hawainiyarka ta kiyayi ramata wallahi, idan zakayi zinar ka je can waje ka yi domin ni tuntuni na cire ka daga cikin zuri'ata na sallamawa duniya kai, duk abinda kake ganin shine daidai da rayuwarka ka je ka yi, amma kada ka kuskura ka ke ta mini alfarmar yarinya idan ka kuskura sai na tsine maka ka lalace."

Lokacin da yake wannan furucin sai da tsigar jikina ta tashi, sai na fara nadamar abinda na yi gabadaya hasashe da zargi mu ke yi domin dai babu wanda ya ta'ba gani da idonsa ga yarinyar da ya lalata, sai dai muna jin labari a gari, da kuma irin alamomin da yake nunawa.

Tokar kuka kawai take tana fadin." Sammani bana son irin wannan munanan kalaman naka, wai shin da me yaron nan zai ji ne? kullum cikin aibata shi ka ke yi, ka tsane shi kamar ba kai ka haife shi sam baka ganin irin wahalar da yake maka, yana fita ya nemi kudi rana ruwa da iska tare da hargitsa bola da shiga kudiddifi domin ya sami rufin asiri ya kawo maka cikin gida amma ba ka gani, kullum mugun fata ka ke masa, ka da ka sake aibata shi mutukar kana so kaga farinciki na a gidan nan."

Kawu Sammani Ya kama hanya ya fita daga dakin ransa na wani irin zugi! Yaron nan gashi ya fada da bakinsa yana neman mata ashe da gaske ne ba karya akayi masa ba, Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! A zuriar Malam Zangina mai al'majirai aka samu wannan zakkar, lallai Allah ya jarabce shi, dole ya nemo masa matar aure domin gujewa abinda zai je ya dawo.
***
Wannan ya wuce da wasu kwanaki, wani al'amari bai sake giftawa ba a tsakaninmu, sabgarsa yake ina sabgata, ko kallona ba ya yi, sai dai ni idan ya shigo gurin Tokar na kan yi ta satar kallonsa, ganin ya yi shar-shar! a lokacin ya sauya sabbin tufafi, dama baya tu'ammali da manyan kaya, ya fi amfani da kananu kasancewar yana da suffah mai kyau sai kayan suke masa kyau a jikinsa, to cikin kwanakin nan ina ganin ya samu kudi ne domin ya sauya komai harda takalma da sabbin f-cap da dai sauran kayan gayu! matsalata dashi 'kazanta dakinsa idan mutum ya shiga yawu ba zai iya hadiya ba saboda wari! da tsamin hammata! tsaf zaka gan shi yana kamshin turare amma makwancinsa ba za'a a rasa kudin cizo ba da sauran 'kwarika.

Yau ma cikin sabbin kaya ya shigo dakin ya yi kyau sosai! wanda har na kasa dau'ke idona daga kansa ya ritsa ni ina kallonsa, 'bata fuskarsa ya yi, Ya ce." Idan ke mayya ce sai dai ki ci kanki." Uffan ban ce masa ba, na kawar da kaina ina yamutse fuska, Tokar Ta ce." Ka da ku yi don Allah ku rufa Mini asiri."
Da sauri Ya ce." Ni ina ruwana da ita, kawai na ritsa ta ne tana kallona kamar za ta cinye ni, kuma 'kwalelanta." Ya fada yana dauko babbar wayarsa dake aljihunsa.

Can kasan ma'koshi Na ce." Me zan yi da kai, ko na rasa Miji ba zan aure ka ba gwara na zauna a haka har rayuwata ta 'kare."
Tokar ta kyalkyale da dariya tana kallona Ta ce." Ki dai yi addu'a Allah ya ba ki miji kamarsa, mai zuciyar neman halal, jarumi, wanda bai yarda da roko da maula ba." Shiru na yi ban tanka mata ba.

Ya ce." Tokar na fara neman aure fa." Guda ta rangad'a! baki a washe ta ce." Alhamdullhi, amma na ji dadin wannan labari." Yana dariya Ya ce." Yarinyar ma ai ba 'boyayyiya ba ce, 'Yar gidan Alhaji Lawan ce.'' Bakinta ta rike da cewa; Ashe 'yar babban gida ce to yanzu maganar ta yi nisa ne? ina nufin iyayenka sun san halin da ake ciki."
Girgiza kansa Ya yi, Ya ce." Ina so dai na sami Kawu 'Danlami da maganar sai a san yanda za'ayi." Ta ce." To hakan ya yi Allah ya tabbatar da alheri, lallai idan al'amarin nan ya tabbata zamu sha ka'bakin arziki daga gidan Alhaji Lawan domin dai attajirin gaske ne." Shiru ya yi mata yana cigaba da latsa wayarsa

Ni kuwa tunani na shiga yi na yarinyar da yake so ya aura, na san 'yan matan gidan su biyu ne kacal, Sakina da Shafa, to shafar da ita kadai nake shiri, ita Sakinar girman kai ne da ita shiyasa sam jininmu bai hadu ba saboda tana da jiji dai ganin babanta yana da farcen susa!

"Tokar kin ga hotonta." Ya fada yana nuna mata hoton a wayarsa, kawai sai na tsinci kaina da lek'awa domin a lokacin gabana fad'uwa kawai yake haka kawai bana so ace Sakina ce, domin haushinta na ke ji.
Gaggawar janye wayarsa ya yi tare da cewa; Ke nake nunawa da zaki wani zuro kai don munafurci." Kunya ce ta kama ni, jiki a sanyaye na janye jikina, ya cigaba da nuna mata yana murmushi, ita kuma sai fara'a take tana fadin." Aikuwa kyakykyawa da ita, caras-cas! daidai da kai, Allah ya kaimu lokacin."
Wani irin kuttun ba'kinciki ya tsaya mini a wuya, kwanciya na yi tare da juya musu baya takaici kamar ya kashe ni.
[6/23, 10:49 AM] bintaumarabbale: 11
Ina kwance ina jin suna ta tattaunawa akan maganar, yana 'kara tabbatar mata da cewa; da gaske aure zai yi, domin har ya fara tanadi duba da cewar yarinyar 'yar masu hannu da shuni ce. Bai fita daga dakin ba sai da Tokar d'in ta tabbatar masa da cewa; Za ta sanar da mahaifinsa halin da ake ciki sannan ya yi mata sallama ya fita.
Yini nayi a kwance ina birgima, daga zarar na tuna da al'amarin sai gabana ya yanke fad'i, wani yanayi na shiga wanda ni kaina na gaza gane abinda yake damuna, abinda dai ya fi tsaya mini a raina yanda Bahago zai yi aure ya bar ni, dama kuma ya sha fada cewa; Ba zan ta'ba aure ba, to sai gashi maganarsa tana nema ta tabbata, tunda har yanzu babu wanda ya ta'ba zuwa soron gidanmu da niyyar ya zo zance gurina, yau shekaruna ashirin da hud'u a duniya, babban tashin hankalina Bahago ya yi aure ni ina zaune babu wani labari.

Da 'kyar na ci abincin dare na koma na kwanta ina sa'ka wasi'kar jaki, ga wani abu mai bala'in nauyi ya zo ya tsaya mini a wuya na rasa yanda zan yi da rayuwata, kawai sai na cusa kaina cikin hijabi na fara zubar da hawaye, domin kukan ka'dai zan yi na samu sassauci.
Shigowar Kawu Sammani ya sa nayi shiru tare da nutsuwa domin maganar da suke da Tokar din ta dauki hankalina. Jin furucinsa a kan lamarin ya sa zuciyata ta dan yi sanyi, ina ganin tunda bai amince ba dole shima Bahago din ya ha'kura da yarinyar ya nemi wata. Ita kuma Tokar ta ce lallai fa sai an je an nemi auran idan iyayan yarinyar sun ce ba za su ba shi ba to sai ya ha'kura. Kawu Sammani ya amince da maganarta ba dan ransa ya so ba, a jikinsa kawai yake jin kamar al'amarin ba zai yuwu ba, tunda babu wanda bai san Alhaji Lawan ba a unguwar Attajirin mai kud'i ne, mai izzah da k'yamar talaka.

To abinda ya biyo bayan al'amarin bai yi wa kowa dadi ba, domin ko da su Babana su ka je gidan da maganar auran, Alhaji Lawan ya nuna shi sam bai san da maganar ba, kuma ko zai aurar da 'yarsa ba zai bawa wanda ba shi da sana'a ba, a ganinsa sana'ar jari bola (Gwan-gwan) ba sana'a ba ce, a cewarsa ma duk ta wannan hanyar yara suke lalacewa da sata da kuma shaye-shaye! to saboda haka shi ba zai aurar da 'yarsa a gurin da bai cancanta ba. Babana ya fusata sosai! domin gaza ha'kuri ya yi a lokacin shi da Alhaji Lawan din suka dinga musayar yawu, Alhaji Lawan ya kira 'Yansanda suka tafi da Babana a cewarsa ya yi masa 'kazafi akan dukiyarsa da yake nema ta hanyar halal.
Kawu D'anjuma ya dinga ba shi hakuri ya janye maganar rashin fahimta ne duk ya janyo hakan, amma Alhaji Lawan ya rufe idonsa ruf, sai da ya tozarta Babana hankalinsa ya kwanta, kuma bai sa an fito da shi ba sai can da daddare.
Aikuwa a daran babu wanda ya sani, Bahago ya fita ransa ya mugun 'bace! gidan Alhaji Lawan din ya nufa, ya sa akayi sallama da shi, koda ya fito ya gan shi sai ya nufin komawa cikin gidan, da sauri ya tari gabansa ido a rufe ya fara yi masa tijara irin ta kangararrun marasa kunya, a fakaice ya dinga cin mutuncinsa da dukiyar tasa, kuma ya sha alwashi cewa sai ya yi sanadin da 'yarsa ta gagare shi.
Alhaji Lawan hankalinsa ya yi masifar ta shi ya fito da waya zai kira jami'an tsaro, a lokacin Bahago d'in ya fito da wata karamar bindiga daga aljihunsa ya nuna shi da ita tare da fadin Ni zan zama ajalinka, kuma sai na yi sanadin da dukiyarka ta lalace tsohon banza tsohon wofi! sosai Alhaji Lawan ya tsorata, kuma bai ta'ba tunanin kangarewar yaron har ta kai haka ba, shi duk kudinsa har yanzu bai mallaki bindiga ba, amma ga ta a hannun k'aramin yaro yana yi masa barazana! jikinsa ya dinga rawa ya nemi su yi sulhu, shi kuma Bahagon yaki yarda sai da ya gama tsoratar da shi tukkuna ya mayar da bindigar aljihunsa ya bar gurin zuciyarsa fes bai ga d'an iskan da zai ta'ba martabar iyayensa ya hak'ura ba, mussaman Kawunsa 'Danlami wanda ya sadaukar da rayuwarsa a kansa, shine yau aka wulakanta aka tozarta shi aka rufe shi a cell, don haka sai ya kudiri wani abu a ransa domin ya kara k'untatawa Alhaji Lawan din.

Tun da na samu labari rushewar auran hankalina ya kwanta, sai dai na ji ciwon tozarcin da akayi wa mahaifina dan har kuka na yi a lokacin da ya shigo gidan, jikinsa duk 'kura da cizon sauro, ya yi zuru-zuru saboda fargaba da tashin hankali, babu abinda yake nanatawa sai Innalillahi! Tokar kuwa sai tsine-tsine take yi tana aibata zuriyar Alhaji Lawan din.

Alhaji Lawan jiki na rawa ya shiga gida, kai tsaye dakin yaran ya nufa lokacin duk sun yi bacci, ya tashi Sakinar, yana tsaye a kanta har ta wartsake! ganinsa ya sanya hankalinta ya ta shi, dama ta yi tunanin haka zata faru, tunda Bahago din ya fad'a mata iyayensa za su zo neman auranta take cikin alhini da damuwa saboda sanin halin Babansu. Fada ya rufe ta da shi, ya kuma jaddada mata cewa; tun wuri ta rabu da yaron idan ba haka ba to za ta fuskanci bacin rai mai tsanani!

Kwanan kuka ta yi da sassafe muna karya kummalo sai ga ta a cikin gidanmu fuska a kumbure ido ya yi luhu-luhu! Tokar ta kalle ta da fadin." Wacece wannan za ki shigo mana gida katsaham babu sallama." Ta zube gaban Tokar din tana rusa ihu! Ni kam d'auke kaina na yi ina cigaba da kurbar kunu na.
"Don Allah ku yi hakuri, wallahi ina sonsa ba laifina ba ne abinda ya faru, rayuwata tana cikin garari idan ban mallake shi ba."
Tokar ta ri'ke hannunta tare da cewa" Daga ina ki ke ko dai kin yi 'batan kai ne?" Kallonta na yi ba tare da wata damuwa ba na ce." Tokar kada dai baki gane ta ba? Sakina ce budurwa Bahago 'Yar gidan Alhaji Lawan." Sai ta sha kunu! ta zabga mata harara da cewa; 'Yar nan ai ko ke kadai ki ka rage a duniya Bahago ba zai aure ki ba, mai za'ayi da irinku marasa kirki masu girman kai da tozarci, ki daina zubar da hawayenki a banza Bahago ba zai aure ki ba."
Hawaye wani-na-bin wani, ta ce" Wallahi muna son juna lefin na Babanmu ne, kuma ni zan aure shi a haka ko da ba shi da sana'a zan iya zama da shi, domin mun riga mun tsara rayuwar auranmu, don Allah ku yi hakuri."

Yanda take kuka da magiya akan Namiji abin ya ba ni tausayi da dariya na dinga kallonta ina mamaki! ko ina jiji da kan ya ta fi? yarinyar 'yar girman kai ce da izzah! yau ga ta a gabana tana gursheken kuka! gaskiya a gaishe da soyayya!

Tokar Fadi take ''Wannan jaraba har ina yarinya kin zo kin dame ni da koke-koke da safiyar Allah ta'alah, ke Jamila je ki d'akinsa ki kira shi domin bana tsammanin ma ya ta shi daga bacci, ki je ki tashe shi, ya zo ya raba ni da wannan mayyar yarinyar "

Cikin zuciyata Na ce." Tokar ba'a ci miki bashi, ba ayi miki ba kin amayar ballantana an ta'ba ki.

Domin na ga ya zata kasance da sauri na tashi na nufi dakin nasa dake soron gidan zuciyata fes na ji dadin ganin yanda Sakina ke kuka wiwi! kuma ina addu'ar Allah yasa shima Uban gayyar ya yi mata rashin mutunci tunda halinsa ne.
Tashinsa kenan daga bacci na shiga d'akin, yanayin da yake ciki ya sa na yi saurin kawar da kaina gabana yana fad'uwa, fuska ya 'bata tare da cewa" Menene?" Ba tare da na kalle shi ba Na ce." Tokar ce take kiran ka."
"Wani sharrin ki ka 'kulla mini da ake nema da sassafe?"
Girgiza kaina na yi Na ce." Budurwar ka ce ta zo tun d'azu ta hana mu sakat sai kuka ta ke yi."
Ya yi jim yana kallona kafin Ya ce." Wai kina nufin Sakina?" Na ce."Eh mana."
Da sauri Ya ce."Ubanta zan yi mata dan Uwarta.'' Cikin zuciyata Na ce." An zo gurin.
"Dallah Malama Fita ki ba ni guri munafuka kawai." Ya fada yana kokarin mik'ewa! da sauri na juya domin fita daga dakin da fadin." Sai ka ce wani dakin kirki da har ake korar mutum.

Ko da ya fito bai saurareta ba sai da ya yi wanka ya kimtsa jikinsa sannnan ya shigo dakin fuskarsa a murtuke! ba zato ba tsammani mu ka ga ta tashi da sauri ta rungume shi tare da fashewa da sabon kuka!
Tokar ta dinga tafa hannu tana sallalami, Ni Kuwa ido kawai na zuba musu ina kallon ikon Allah yayin da yake kokarin cire ta daga jikinsa tana 'kara manne masa.
Da 'kyar ta sake shi, amma ta ri'ke hannunsa gam! ruwan hawaye yana ta karakaina a kumatunta, sosai ta ba ni tausayi a lokacin, kuma na tabbatar da cewa; soyayyar da take masa ba ta wasa ba ce.
Rarrashinta ya dinga yi har ta yi shiru, ya ja hannnta suka fita daga gidan, inda Allah ya taimaka ma Iyayenmu Maza duk sun fita, Mahafiyarsa kuma na can gurinta tana aiki, ita kuma Baba Iyami ta tafi makaranta da yake tana koyarwa a wata firamare shiyasa akayi aka gama wani abu bai gifta ba.
Bayan fitarsu daga dakin. Tokar ta dinga fadin." Yarinyar nan 'Yar iska ce Tana so ta lalata mini yaro, ta rungume shi sai gogo masa nononta ta ke yi, shi kuma jikinsa duk ya yi sanyi idanuwansa har sun sauya kala, Jamila

Please Login or Register in order to submit comment