Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta'ba nunawa ba sai ranar.
Baba Hama hankalina ya tashi, da gudu ta nufi gurin Tokar domin ta sheda mata abinda yake faruwa, Ni da Anti Hamida muka dinga kuka ganin irin abinda Mamana take yi a kwance wanda ba mu ta ta'ba gani ba.
Tokar ta tsorata sosai domin idan akwai abinda take jin tsoro a duniya bai wuce Aljani ba, da saurin gaske ta yafa mayafi ta fita jikinta sai karkarwa yake.

Tare suka shigo gidan da Babana da Malam Iliya duk hankalinsu a tashe! Ni kuwa ina rungume da ita a jikina ina ta kuka don lokacin ban yi tunanin yi mata addua ba, da kyar Anti Hamida ta ja ni muka fita daga dakin, Tokar da Baba Hama suna tsaye sun yi tsuru-tsuru! Mussaman Tokar kafafunta sai rawa suke, Bahago ya shigo gidan ya riski abinda yake faruwa, dariya ya 'kyalkyale da ita kawai ya d'auki buhun da yake yawon gwangwan d'insa ya fita daga gidan yana wa'ke-wa'ke, tabbacin abin bai dame shi ba, hakan da ya yi sai ya kara mini tsanarsa a cikin zuciyata.

Malam Iliya ya samu nasarar yin magana da iskar dake kan Mamana inda suka yi gargadi da jan kunne akan abunda yake faruwa a gidan, yana da kyau tun wuri ayiwa tufkar hanci, domin sun gaji da ganin god'iyarsu cikin damuwa da tashin hankali, kasancewarsu musulmai ba zai hana su d'auki mataki ba akan abinda akayi mata saboda tunda aka haife ta suke tare da ita kuma basu ta'ba nuna kansu ba sai a wannan lokacin dan ganin abin ya yi yawa, wannan ya zama na farko kuma ya zama na k'arshe ka da wanda ya sake muzanta Hansatu da 'yarta Jamila."
Malam Iliya ya ba su hakuri sannan kuma ya gargad'e su akan su ji tsoron Allah kada su cutar da kowa, muddin akan wannan lamarin suka zo to hakan ba zai sake faruwa ba.
Sun yi alkawarin babu wanda za su cuta! amma wannan ya zama na farko da 'karshe!

Sai da ta kwana uku a kwance tana jinyya sannan ta dawo hayyancinta, Tokar har da zuwa duba ta, wanda tunda ta zo gidan Tokar din bata ta'ba shiga dakinta ba saboda irin k'iyayyar da take mata. Ita kanta Baba Hama sai da ta shiga har cikin dakinta ta nemi afuwar ta domin Umarni ne daga gurin Kawu Sammani ya ce duk lokacin da ta sake kwatanta irin haka to sai ranta ya yi mummunan 'baci!
[6/14, 8:42 AM] bintaumarabbale: 8
Mun samu rangwame ta 'bangaran Tokar da Baba Hama, Damuwar mu a yanzu Bahago domin ya matsanta mini kullum sai ya sa ni kuka! a makaranta da yake ajinmu d'aya muna aji shida a sakandire jarrabawar fita muke shirin yi, To haka zai ta duka na saboda yana matsayin monitor (shugaban aji) ban yi lefin komai ba zai kirkira k'arya ya fitar dani cikin rana, ko kuma ya sanya ni tsallan kwad'o, idan ya yi ra'ayi kuma sai ya rubuta sunana cikin jerin masu laifi, ya kai ni gaban Shugaban Makaranta duk malamin da ya zo ya gan ni a zaune sai ya d'auki bulala ya zane ni, gabad'aya Malaman makarantar sun tsane ni sakamakon sharrin da yake mini a gurinsu, Kuma wani abin haushi da takaici! shi a 'bangaransa ya yarda ya doke ni, ya ci mutunci na, amma bai yarda wani acikin ajinmu ko a Makarantar ya ta'ba ni ba, duk ranar da hakan ta faru! cikin aji da Makarantar sai ran kowa ya 'baci! To hakan da yake ni sam ba ya burgeni domin duk abinda za'ayi mini a makarantar shine ya bada k'ofa, ko da yaushe cikin 'bacin rai nake komawa gida watarana ma da kuka nake shiga gidan, Mamana ta koya mini dabarun fad'a amma ba na iyawa domin Ya fi ni 'karfi nesa ba kusa ba, A duk lokacin da ya yi mini abu nayi yunk'urin ramawa murd'e mini hannu yake sai ya kusa karyewa yake saki Targad'e kuwa wanda ya yi mini ba zai lissafu ba.

Akwai ranar da ya kama wani a makarantar ya dinga dukansa kamar zai kai shi Lahira wai akan ya ja mini hijibi, Ya juyo kaina Nima ya dinga gaura mini mari yana tambayata wai lallai sai na fad'a masa gaskiya ko yaron ya ta'ba mini nono ko d'uwawu! duk da akwai kuruciya a lokacin sai da na tsorata da ganin yanayinsa idanunsa sunyi jajawur! fatar goshinsa ta tattare! na tsorata sosai! na dinga rantsewa da Allah kan cewa; babu gurin da ya ta'ba a jikina tunda lokacin ma ban jima da fara 'kirgar dangi ba amma sun fito sosai dama kwankwaso ba'a magana akwai shi! To a takaice dai sai da ya sumar da Yaron nan sannan hankalinsa ya kwanta ya dinga wani irin huci! yana numfarfashi!

Sai dai abinda ya biyo bayan al'amarin beyi wa kowa dadi ba, domin kwana ya yi a ofis din 'yansanda! dalili iyayen yaron sun ce ba za su yarda ba sai hukuma ta dauki mataki a kan lamari.

Tokar ta dinga kuka tana fyace! hanci ta dauki mayafi ta yafa wai lallai sai ta je ofis din 'yansanda ta ba su hakuri kada su kashe mata yaro, yanda ta tayar da Hankalinta iyayansa basu tayar ba, A karo na uku Babana ya sake komawa ofis din 'yansandan tare da kudi dubu ashirin da biyar wanda ya d'auka a cikin jarinsa! don a lokacin ana shirye-shiryen tafiya dashi kotu, da 'kyar suka bada belinsa akan kudi dubu goma sha biyar, sauran dubu goman kuma aka bawa iyayen yaron domin su yi masa magani, saboda ya yi masa rauni a wasu guraran na jikinsa.
A ka fito da shi daga cell din jikinsa duk shatin bulala da cizon sauro! abinka da farin mutum! idanuwansa duk sun zurma gefen bakinsa ya dan kumbura da alamar duka!
Ganin yanda kammaninsa suka sauya ya ba ni tausayi, 'kwalla ta cika kwarmin idanuwa na amma ban bari ta zubo ba, Babana ya ce; na yi sauri na d'ora masa ruwan zafi domin ya yi wanka ya gargasa jikinsa, A sanyaye na kunna wutar ina ta tunanin al'amarin, gefe guda kuma ina sauraran maganarsu da Tokar yana fada yanda lamarin ya faru sai ciccije bakinsa yake, ita kuma tana 'kara ingiza shi a maimakon ta nuna masa kuskuran abinda ya aikata. A sanyaye na kalle shi da fad'in." Ni fa babu wani abu da ya ta'ba had'a ni da shi, kuma gefen hijabi na kawai ya rike, bai ta'ba wani abu na jiki na ba." Ya zabura! yana huci ya lailayo ashar! "Ni za ki fad'awa haka? a kan idona ki ke tafiyar banza ki na murgud'a mazaunanki! ba dole 'yan iskan maza su dinga bin ki suna ta'ba ki ba, to wallahi sai na ci " Uwarki duk lokacin da na kara ganin kin yi magana da wani Namiji a cikin makaranta.
Can kasan makoshi na ce" Ba dai uwata ba wallahi." Jikinsa na tsuma! ya mike ya zo ya tsaya a kaina! gabana ya dinga bugawa! Na ce" To yanzu kuma me na yi maka?" Da yatsansa ya nuna ni tare cewa; Kin ji gargadin da nayi miki ko sai jikinki ya fada miki." Da sauri Na ce." Na ji." Tokar ta janye shi daga kaina, ya koma ya zauna gabanta yana cigaba da zage-zage! kamar d'an maguzawa!

A cikin satin da al'amarin ya faru sai ga shi ya kawo mini wasu zurma-zurman kayan Makaranta wando da rigar manya haka ma hijabin har 'kasa! Ya dinga jaddadawa Mamana cewe; Wasan banza na ke yi a makarantar da maza har wani ya samu nasarar shiga rigar mutuncina, saboda haka lallai wannan kayan su zan dinga sanyawa idan zan tafi.
Kawai kallonsa muke da mamakin! 'Karfa-Karfa! da kuma Umarnin da yake ba mu kamar wanda ya ajiye mu a gidan, saboda samun zaman lafiya yasa ta kar'bi kayan daga hannunsa tana yi masa godiya ya kama hanya ya fita daga yana ta wani cin magani.
To can 'bangaran Hama kuma jin labarin ya yi mini sabbi kayan makaranta sai ta dinga yi masa fad'a lallai sai ya fada mata a ina ya samu kud'i, Kai tsaye Ya ce.'' Kud'insa ne na gurin Abokinsa Shamsu da suka hada guiwa suke sana'ar gwangwan! (Ina da kwalabe) tare. Ta rufe shi da fada akan me zai dinga yi mini wahala bayan shima da wuya yake samun kud'in, Ya bata amsa da cewa; Duk abinda yake yana da dalili." Bai saurari jin wani abu daga gare ta ba ya sanya kai ya fita daga gidan.
Ka'ida dama idan an ta shi daga makaranta ya dawo gida ya ci abinci fita yake yi sana'arsa domin bana tsammanin ya tsayar da sallah duk da cewa mun kai munzali na balaga a lokacin shakara goma sha bakwai amma ibadah ba ta zauna a zuciyarsa da gangar jikinsa ba, ya fi bawa neman kudi muhimmanci, makarantar Allo kuwa baya zuwa babu irin dukan da Kawu Sammani beyi masa ba don har a sasari! ya d'aure shi! Tokar ta ce ya yi gaggwar kwance shi hakan ba shine mafita ba, Abin sai ya zama kamar tiri, yana kwance shi daga sararin al'amuransa suka dagule! ya fara busa sugari da yawace-yawancen dare, haka yake dawowa gida tsakiyar dare! Hankalin iyayen mu ya tashi, sai suka shiga ro'kon Allah da sadaka akan Allah ya ta'kaita masa al'amarin ya tsaya a kuruciya! amma duk sun d'auki laifin kacokan sun d'ora akan Tokar ita ce Silar jefa rayuwarsa cikin garari.
Don akwai ranar da ya kwance mata akoyoyi daga turke, rago turkeke da tunkiya wanda a lokacin kud'insu suka kai kimanin dubu tamanin, tsakiyar dare ya fita da su aka wayi gari da tashin hankali. Kawu Sammani bai dora zarginsa akan kowa ba sai akan yaron nasa saboda dama ya san yana d'auke-d'auke! mutukar akayi wasarere! da abu to zai sanya hannu ya d'auka, a matsayinsu na Iyayensa, ya yi musu hakan da dama, kawai dai sunyi shiru ne domin alkairi ake yayatawa! ba sharri ba.
A ka dinga neman dabbobin tare da shi domin ko da wasa bai nuna wata alama ba, Tokar ta dinga tsine-tsine a gidan tana zubar da hawaye! Yini guda ta firgice! ta kasa cin abinci. Kawu Sammani ya dakatar da ita da Cewa" Tokar wannan satar da akayi miki na jikinki ne don haka tsine-tsinen da ki ke babu amfani, bana zargin kowa sai Ali, shine ya bi dare ya sace miki dabbobi."

Ta ce." Ban yarda ba Sammani ban amince cewa Bahago zai kwance mini dabbobi ba, kana ganin fa tun safe ya kasa zama da shi ake nema Lunguna-lunguna To ni babu b'arawo a cikin zuri'ata, kuma Bahago ba zai cutar da ni ba."
Haushi da takaici yasa bai sake wata magana ba ya kama hanya ya fita daga gidan ya na yi wa yaron nasa adduar shiriya, to 'karshe dai kudin dabbobin da ita aka cinye domin duk daran duniya sai ya kawo mata nama mai yawa a takarda tare da lemo mai sanyi.
A daddafe muka kammala secondary shi ya samu nasarar tafiya babbar makaranta wato University tunda yana buge-buge! yana samun kud'i sai ya yi wa kansa komai da ake bu'kata, Ni ma da yake takarduna sunyi kyau! Babana ya fara kokarin sama mini gurbin karatu, Aikuwa ya bi dare da rana ya zuga shi kan cewa; Idan na je University zan lalace! gwara kawai ya yi mini aure domin shine cikar kamalar duk wata 'ya mace. Wannan hud'ubar ta karya kudirin dake zuciyar mahaifina kawai sai ya ajiye maganar a gefe guda ya cigaba da sabgogin gabansa, Jin shiru babu wani wata magana daga gare shi yasa Ni da Mamana muka tuntube shi da maganar, alokacin ya fad'a mana hukuncin da ya yanke cewar ba zan cigaba da karatu ba kawai na tsayar da mijin aure, Mamana ta tunga nusar da shi muhimmancin Ilimi a gurin 'Ya mace, Ya ce shi dai ya sauya shawara kawai aure zai yi mini. Sai da mu ka yi binkice muka gane cewa Bahago ne duk ya rusa mana shiri, Aikuwa raina ya 'baci sosai! Na same shi a d'akinsa tare da abokinsa Shamsu da suke shed'anci su tare, Na dinga zazzaga masa rashin mutunci duk da na san hakan ba zai haifar mini da alheri ba, amma ba zan yi masa shiru ba dole sai na amayar da kuttun takaicin da ya jima yana kuntuka mini! Ya tashi ya je ya rufe kofar dakin da mukkuli, belt dinsa dake rataye ya ciro daya ya yo kaina zai zabga mini, Shamsu ya rike belt din tare da fad'in" Meye haka Abokina? ka doke ta ka ce ka daki wa?"
Ya cije bakinsa da cewa" Na doki banza mana ko kana tsammanin tana da galihu ne?" Ya fizge blet din hannunsa da fadin" Amma ka ba ni mamaki Wallahi, Ai duk maganarta akan gaskiya take, ina ruwanka da rayuwarta da kullum ka ke cin dunduniyarta."
Ya zabura! Ya fizge madokin tare da sake kai mini duka da shi da sauri na kauce ya daki iska, Na ce" Shamsu ka rabu da shi mana ya doke ni, yana maganar ba ni da galihu ko? to wallahi yau ka ta'ba lafiyata sai kayi kwanan kurkuku!.''
Wawan Naushi! ya kai wa bakina a take ya fashe! jini ya cika mini baki nasa hannu na taro jinin tare da ha'kora na biyu da suka zube!
A lokacin na kad'u sosai! ganin irin jinin da yake zuba! ga kuma ha'kora na biyu a hannuna, jikina ya dinga karkarwa! na kama hanya na fita daga dakin ina wani irin kuka mai cin rai!"
[6/18, 11:57 AM] bintaumarabbale: 9
Tokar da Mahaifiyarsa na zaune a tsakar gida suna hira na zo na shige ina kuka ga jini na zuba amma babu wacce ta tambaye Ni dalili hirarsu suka cigaba da yi tabbacin ba su damu da halin da nake ciki ba.

Cikin karayar zuciya da nadamar fitowa daga alhalin gidan na zube jikinta a lokacin tana tankad'e garin masara domin d'ora mana abinci, jinin dake zuba daga bakina ya 'bata mata gaban rigarta, jikinta ya dinga karkarwa! ta mi'kar da ni tsaye! hannuna ta ri'ke muka nufi cikin gidan, wanda har lokacin suna zaune suna Hira shi kuma Bahago din yana jan ruwa a rijiya yana zubawa a bokiti da alama wanka zai shiga, Cikin tsananin 'bacin rai da tashin hankali ta kalli Tokar tare da cewa" Yau dai ina so a nuna mini a bolar da na tsinto yarinyar nan, Domin na ga ji da wannan masifa na ga ji, abinda Bahago ya ke ya wuce gona da iri, to yau zan kawo 'karshen al'amarin nan, wallahi jinin 'Yata ba zai zuba a banza ba."
Mahaifiyarsa ba ta ce Uffan ba ta kama hanya bar gurin, hakan ya 'kara 'kona zuciyar Ummana, itama Tokar din tsaki ta ja sai ta fara kokarin jan jikinta za ta shiga d'akinta, al'amarin da ya fusata Ummana kenan, kawai ta shiga sakin maganganu irin bacin rai! Ni kuka Ita kuka, wanda hakan ya karya alkadarinsa ya zo yana bata hakuri! ba ta saurare shi ba ta cigaba da gaggayawa Tokar maganar da duk ta zo bakinta! Tokar din ta fashe da kuka! tare da cewa; Hansatu abin har da zagi ? kada fa ki d'auka tsoronki na ke ji shiyasa nayi miki shiru, kawai ina tsoro kada iskarki ta ta tashi akan wannan 'kan'kanin lamari, kuma duk wannan maganganun da ki ke yi baki isa ki raba yaran nan ba, jininsu d'aya don Bahago ya hukunta Jamila akan wani dalili ai ba laifi ba ne."
Cikin tsawa! dan har lokacin jikinta rawa yake ''Ban yarda da maganarki ba Tokar, ba kya 'kaunata shiyasa ba kya kaunar Jamila, sau nawa kina aibata ta, kin ce kina kokwanto ko a waje nayi cikinta na kawo muku cikin gida, to wannan sharrin da ku ka yi mini sai Allah ya bi mini hakkina, kuma wallahi na gama zama daku har abada! domin auran irinku jaraba ne da kaddara."
Wannan maganar a kunne Babana lokacin da ya shigo gidan, aikuwa ransa a 'bace! ya wanke fuskarta da mari! sam bai duba halin da muke ciki ba, ganin haka sai Tokar ta sake rushewa da kuka! ta cigaba da za'kulo magana wacce akayi da wacce ba a yi ba.
Ya fusata! sosai ya nuna ta da hannu "Ki tattara ke da 'yar taki ku fice mana daga gida.
Rushewa na yi da kuka na rike kafafunsa ina rokonsa ya janye 'kudirinsa! ''Ka yi hakuri Baba ka janye maganarka don Allah kada ka raba ni da Mahaifiyata." Bahago ya zo gurin yana ba shi hakuri! ban san lokacin da nayi kukan kura na cakumi wuyansa ba, da yake abin ya zo masa a bazata! sai ya fad'i wanwar a gurin, na haye ruwan cikinsa na dinga kai masa naushi! a ko'ina na jikinsa, kuka nake sosai tare da yi masa Allah ya isa tsine masa nake ina kai duka da yakushi a fuskarsa, ya dinga kokarin ture ni daga jikinsa ya kasa, domin a lokacin ni kaina nayi mamakin k'arfina, 'kokari kawai nake Ni ma naga na zubar masa da ha'kora kamar yanda ya zubar mini, Tokar fadi take ku janye ta kada ta kashe shi, 'yar gadon aljanu, mai kirar samudawa! wannan dai da alama ba ita kadai ba ce tana da masu taimaka mata, saukar icce! na ji a gadon baya na, hakan yasa na gantsare! sai ya bashi damar ture ni daga jikinsa ya ta shi da saurin gaske ya kama hanyar fita.
Babana ya dinga 'ko'karin sake dukana da iccen dake hannunsa Ummana tana kare ni, al'amarin da ya janyo musu musayar yawu kenan! tana fad'a yana fad'a! ita kuma Tokar dake gefe tana kara zuga shi, 'karshe dai shaidan ya samu Nasara ya furta mata kalmar saki! jin haka yasa na kurma Ihu! tare da fadin." Shikkenan na shiga Uku na lalace rayuwata ta shiga garari!" Ta rumgume ni ." Rayuwarki bata lalace ba muddin ina raye, sannan kuma ba zan tafi na barki a wannan gidan ba." Jin haka yasa Tokar Magantuwa." Baki isa ba Hansatu! kinyi kad'an zuri'ata tayi agolanci a wani guri, ke kadai ki ka zo, ke kadai za ki tafi, Jamila nan ne asalinta."
Ta ce." A'a ku dai bar mini ita na kai ta gurin Ubanta na Asali, ai kun jima kuna sheganta ta." Wannan furucin ya yi wa Babana zafi sosai! don haka ya ja tunga a tsakar gidan har ta gama had'a mana kayanmu cikin akwati muka fito yana tsaye! tsawa! ya buga mini akan na koma cikin gidan na turje! fita ya yi ya kira Bahago ya shigo gidan, nan ya Umarce shi da ya yi mini rikon tsauri! kafin ma nayi wani yunu'kuri! ya kama ni! ya dinga jana ina turjewa tare da kai masa duka kokawa sosai muka dinga yi, lokacin Mama na ta fita daga gidan tana kuka na tashin hankali da fargabar halin da zan shiga.

Wannan shine sanadiyar mutuwar auran Mamana, Na yi kuka sosai don har sai da na kwanta jinyya ta kwanaki, Ganin mawuyacin halin da na shiga Kawu Sammani ya dinga fad'a, yana nunawa Babana kuskuran abinda aikaita wanda shima a lokacin ya shiga Nadama tare da dana sani, dama Annabi Ya ce." Kada ku yanke hukunci cikin fushi, hakan zai janyo muku Nadama! Kawu Sammani da Dan-Uwansa 'Danjuma suka dinga kokarin ganin sun daidaita al'amarin, amma Mamana fafur taki amincewa da dawowa gidan, Iyayenta kuma ba su matsanta mata ba, domin bahaushe Ya ce." Mai daki shi ya san inda yake masa oyoyo! don haka sai kawai suka goyawa 'Yarsu baya, kuma bata yi wani jinkiri ba tayi wani auran, wanda hakan ya 'kuntata! zuciyar Tokar, ta dinga tursasa Babana lallai shima sai ya yi aure wai kada ayi masa dariya, sai kawai ya ce mata ba shi da kudin aure sai ya tara tukkuna. Hakan da ya fada mata sai ya samu salama, domin dama duk cikinsu shine mai karamin karfi.

Haka na cigaba da Rayuwa a gidan cikin rashin 'Yanci! sai da Kawu Danjuma ya yi aure tukkuna na d'an samu sauki, domin matarsa Iyami tana da kirki, sosai ta ja ni a jikinta ko da yaushe ina 'bangaranta muna hira kuma duk abinda ta girka za ta zuba mini a kwano na ci na 'koshi.
Tokar ta d'ora mata karan tsana! amma Ita Iyamin bata ta'ba nuna 'bacin ranta ba, tunda dama kafin ta shigo gidan tana da labarin komai, haka ta dinga hakuri tana kawar da kanta akan abunda Tokar take mata na cin mutunci, Baba Iyami bata samu Sauki ba sai da Allah ya bata ciki tukkuna Tokar ta saurara mata, kuma wani abu na Allah haihuwar sai ta bud'e domin auranta da shekara hud'u har ta ajiye 'ya'ya uku kuma duk maza! sai ta rufe bakin tsantsa, Tokar ba ta sake yi mata gorin haihuwa ba, sai dai wani abu daban da take yi a gidan wanda ya riga ya zama dabi'arta kowa hakuri yake da ita.

'Bangaran Bahago kuwa al'amarin sai addua domin tun da ya fara zuwa University idanuwansa suka kara bud'ewa! sai karatun ma ya zama asha ruwan tsuntsaye! neman mata ya fi yawa, yana kashewa 'yan mata kud'i sosai, suma kuma 'yan matan suna bibiyarsa har gida suke zuwa nemansa kuma wani abin mamaki! da yawa daga cikinsu sun wuce ajinsa haka suke ta turereniya a kansa wasu ma sun girme shi, duk abinda yake aikatawa Iyayanmu suna da labari, Tokar dai ta 'karyata ta ce sharri akayi masa saboda an ga yana da nasibi, Mahaifinsa kuwa tsine masa ne kawai beyi ba, amma fushi yake da shi sosai, babu wanda yake mu'amular arziki a gidan sai da Babana domin shi kad'ai ne zai fada masa magana ya tsaya ya saurare shi kuma ya yi aiki da maganarsa, Ni kuwa dama sama-sama muke magana dan sai mu yi wata biyu ko uku maganar arziki bata hada mu ba, rikici ya fi yawa a tsakaninmu, kuma kallonsa nake domin duk na san abinda yake aikatawa tunda wani lokacin cikin dare a kan idona yake dawowa daga yawonsa idan na fito fitsari na ga ya cika ruwa a bokiti ya shiga wanka, tun ban fahimci komai ba har dai na gazgata zargina domin kusan kullum idan ya dawo daga barikinsa a gidan yake wanke najasar da ya d'auko! 'kyamarsa nake sosai ko kusa da ni bana so ya zauna ballanatana wata magana ta had'a mu.

A haka a daddafe ya samu N.C.E tunda ya kar'bi takardunsa ya ajiye su sai ya fantsama! tafiye-tafiye mussaman kudu k'asashen arna! a can yake harkar gwangwan! (Kwalabe) Allah kuma yasa masa Nasibi ya had'u da wani mutum duk da kirista ne, shi ya kai shi wani kamfanin sarrafa k'arafuna a legos suka had'a guiwa suke harkokinsu a tare.

Zan yi shedarsa ta fanni kula da Iyaye! domin yana hidimta musu sosai, idan baya garin duk wata yake yi musu aike, kusan ragamar gidan tana hannunsa, ba shi da ganin ido sannan ba shi da mugunta, idan ya samu kud'i sai cimar gidanmu ta sauya, hakan yana 'kona zuciyar Baba Hama don dai babu yanda za ta yi dashi tunda halinsa kyauta da rashin ganin 'kyashi.


WANNAN SHINE ABINDA YA SHUDE.

Cikin bacci na ji maganarsa a kusa da ni yana tashi na ta hanyar jan 'kafata wacce ta yi tsami! sosai sakamakon yankewar da na yi. Zaune na mi'ke na janye jikina ganin yanda ya kusance ni, "Meye haka?" Na fada gabana yana faduwa don har ga Allah

Please Login or Register in order to submit comment