Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko ba ki ga abinda ya faru ba ne?"
Na ce." Ga babban d'an-iska nan a cikin gidanki Tokar ki daina aibata yaran mutane bayan ga abu anan a tatttare dake, dama can sun saba rungume-rungume! to dan sun yi a gabanki kin ga ni ai ba wani abu ba ne, Bahago ne babban d'an-iska."
Ta 'bata rai sosai tare da cewa; Wato dai Jamila har yanzu ba za ki kyautatawa d'an-uwanki zato ba ko? ki daina yi masa 'kazafi!" Na ce" Zan daina amma sai ranar da kema ki ka yarda da cewa; Jikanki fasiki ne." Cikin b'acin rai da takaici na fadi maganar, kuma ban saurari jin wani abu daga bakinta ba na tashi na fita na zauna a tsakar gida zuciyata kamar ta tsage! saboda b'acin ran abinda ya faru tsakaninsa da yarinyar, duk abinda Tokar din ta fada Ni ma na gani, a jikinsa da canzawar launin idonsa, sai kawai zuciyata ta shiga zargin wani abu, zumbur! na tashi na kama hanyar d'akin nasa dake zauran gidan namu.
[6/25, 9:17 PM] bintaumarabbale: 12
Kwance a kan cinyarsa na same ta, shi kuma ya tallafo fuskarta yana share mata hawayen da take zubarwa. Cikin jajurcewa da k'o'karin danne abinda ke cikin raina Na ce." Meye haka wannan ai rashin arziki ne, salon kawai ka janyo mana abin magana a idon duniya." Kallo na Ya yi da jirkitattun idanuwansa, Ya ce." Me ki ka gani muna aikatawa?"
"Gashi nan kuwa ka rungumeta a jikin ka, ko hakan ba laifi ba ne a gurinka?" Kafin ya yi magana ta riga shi da cewa; Kin ga Jamila kada ki yi mana sharri dama na fahimci kamar ba kya k'aunar al'amarina dashi, to In sha Allahu sai mun yi aure, sai dai kiyi duk abinda za ki yi."
Murmushin takaici na yi Na ce." To meye abin ba'kinciki anan? mutumin k'warai shi akewa san barka, wannan kuma idan kin aure shi to ki rubuta ki ajiye cewa; Kin auri ajalinki wannan shine abinda zan iya fad'a miki."
Jiki a sanyaye take kallonsa, da alama furucina ya girgizata! tsaki! mai tsayi na ja tare da fad'in.'' Zan shedawa Kawu Sammani duk abinda ka aikata domin ba zan yarda ka janyo musu zagi ba"

Ganin yana yun'kurin tashi yasa da sauri na fita daga d'akin raina a mutuk'ar 'bace! tare da tunanin tsantsar soyayyarsa da na gani a cikin idon Sakina.

Tunda haka ta faru yake nan-nan da ni, idan ina magana ko ba da shi nake ba sai ya sanya bakinsa, na lura duk tsaurinsa yana jin tsoron fushin mahaifinsa, ba komai ne ya sa yake shiga sabgata ba sai don kada na fad'i halin da na gansu da budurwarsa, wanda ni tun a lokacin ma na watsar da maganar, mussaman dana lura da cewa; maganar da na yi musu a lokacin ta sanyayyar musu guiwa.
***
Anti Hamida ce ta zo gidan, muka zauna a d'akin Tokar muna ta hira, sosai ta kawo wa Tokar kayayyaki masu yawa harda kayan shayi madara da bombita, wannan yasa Tokar ba ta yi jayayya da abinda ta zo mata dashi, a take a lokacin ta amince da bukatarta, sai dai shigowar Bahago d'akin al'amarin ya lalace, don yana jin maganar da muke yi ya fara surutai yana 'ko'karin yi wa Anti Hamida rashin kunya duk ya wani tayar da hankalinsa wai babu inda zan je, Jin haka sai Tokar din ta biye masa wai idan na tafi waye zai dinga taimaka mata. Raina a b'ace Na ce." Wai ke aure na ka ke yi da zaka takura mini, to bari ka ji wallahi iyayena ne kawai za su hana ni abu na hanu, gwara ma ka daina damun kan ka."
Ashar ya fara d'ura mini yana 'kokarin kai mini duka Anti Hamida tana rik'e hannunsa, sai na ji wasu hawaye masu zafi sun cika idona, wai shin yaushe zan samu 'yancin kaina ne? sam ba ni da wani daraja da galihu a gidan, ba ni kuma da ra'ayin kaina, fita wannan sai ya sa mini ido bayan shi kullum yana waje, wallahi ba zan lamunta ba. Ganin yanda yake ta han'koro! wai dole sai ya dake ni, ya sanya na ta shi da sauri na d'auko wata sandar labule dake jingine a jikin kusurwa, na rike a hannuna, hawaye na zuba Na ce."Anti Hamida ki daina hana shi duka na don Allah, wallahi sai na rotsa masa kansa, ai ba Ubana ba ne, da zai gindaya mini sharad'i, kuma ba aurena yake ba.
Ganin abin ya ca'be ya sa Anti Hamida d'aukar wayarta tare da cewa; Bari na kira Babanmu a waya na sheda masa abinda kuke yi tunda ba kwa jin magana, dama laifin ba na kowa ba ne sai kai mara mutunci." Jin haka ya sa ya kama hanya ya fita daga gidan yana wani irin huci!

Yana fita na fara had'a kayana cikin akwati Tokar fad'i take "Jamila na fada miki ba inda za ki je, tunda dai Bahago ba ya so to sai ki hakura, kuma ai da gaskiyarsa idan kin tafi waye zai dinga taimaka mini, kina ganin halin da nake ciki na rashin k'afafu, ga tsufa." Uffan ban ce mata ba, domin a lokacin na riga na yanke hukunci, tsakanin su biyun babu wanda ya isa ya hana ni zuwa gidan Anti Hamida mutukar ba iyayena ba.
Hanyar fita na kama da akwatin kayana a hannuna Na ce." Anti Hamida ina jiran ki a waje."
Ban saurarin jin maganar Tokar ba, da sauri na fice daga dakin.
Can na hange shi zaune kan dakalin wani gida da sigari a hannunsa yana busawa, ga yara sun zageye shi, da sauri na d'auke kaina gabana na dukan uku-uku!.
Ganin shi yana 'kokarin zuwa gurin da nake ya sanya na fara addua a zuciyata, d'an akuya ne zai iya yi mini rashin mutunci a gurin, sai na yi saurin shiga soro na tsaya, ban fasa neman tsari da shi ba."
"Wato ba ki ji maganata ba ko?" Ya fad'a a lokacin da ya shigo soron.
D'auke kaina na yi daga kansa.
Sai ya fara k'okarin kwace akwatin dake hannuna tare da cewa; Babu inda za ki je na fad'a miki, Itama Anti Hamidar munafuka ce, ina zata ajiye ki a wannan tsukakken gidan nata? ga ki ke ba k'aramar hallita ba, ga kuma mijinta yana zurga-zurga! a gidan, to mu ba jahilai ba ne, muna da ilimin addani daidai gwargwado, ba zamu ga 'barna mu yi shiru ba.''

Cikin jin haushinsa Na ce." Wai to ina ruwanka ne? kai ka fi so na zauna kullum kana cuzguna mini, ba ka so na samu walwala, don Allah me na tsare maka a duniya?"

"Ba za dai ki je ba na riga na gama yanke hukunci." Cikin gadara yake maganar yana fizge akwatin hannuna, Na sa k'arfi na ture shi tare da matsawa gefe "Allah ya yi mini tsari da kai." Cikin rawar murya na yi maganar dan na rasa yanda zan yi da masifarsa.
Hannuna ya ri'ke yana jana wai sai na shiga gida, turjewa na dinga yi ina dukansa! Anti Hamida ta fito ta ga abinda mu ke yi, ture shi ta yi tana harararsa da fadin."Shashasha kawai dallah Malami ba ni hanya na wuce."
Ya ri'ke hannuna katamau! ya'ki saki, ido jawur! Ya ce." Ki k'wace ta daga hannuna idan kin isa, an fad'a miki ba za ta je ba, kin nace! wai a ina zaki ajiyeta a cikin wannan tsukakken gidan na ki, ki bari ki samu wadata tukkuna sai ki yi neman suna, yanzu dai baki da iko."

Anti Hamida ta nuna kirjinta "Ni ka ke wa cin mutunci." dauke kansa ya yi, yana jan tsaki tare da sake damke hannuna.

"Wannan masifa Allah ka yi mini maganinta." Cikin wani irin yanayi na furta maganar. Muka tsaya cirko-cirko! a soron domin Ni da Anti Hamida babu wanda yake da k'arfin da zai had'a 'kwanji da shi.
Ta kalle ni tare da cewa; Ki hakura ki koma gidan zan yi maganinsa." Da sauri Ya ce." Za mu yi maganin juna dai.'' Ko kallonsa ba ta yi ba ta kama hanyar fita ranta yana suya!. Kicubus sukayi da Kawu Sammani. Da sauri ta dawo cikon soron tana yi masa sannu da zuwa.

Bahago da sauri ya saki hannuna ya matsa gefe, Ni kuma a lokacin wani irin kuka ya k'wace mini na zube k'asan gurin tare da had'a kaina da guiwa! ina kiran Innalillahi-Wa'ina-Ilaihi rahi'un.'' Hankalinsa ya tashi ainun! sai ya dinga tambayar Anti Hamida abinda ya faru, domin tunda ya shigo ya fuskanci wani abu. aikuwa ba ta yi kasa a guiwa ba duk ta warware masa komai wanda a lokacin Bahagon d'in ya shige d'akinsa ya zura sakata.
Kawu Ya girgiza kansa cikin takaici Ya kalle ni, Yana rarrashina na tashi na goge fuskata muka fita daga gidan, shi kuma ya shige ciki ransa a bace! addua ita kad'ai zai lazumta domin ita ce makamin mumini, yana ro'kon Allah ya gajartawa yaron nasa wahala.
[7/5, 12:32 PM] bintaumarabbale: 13
Sati na biyu a gidan Anti Hamida zaman gidan ya gundure ni, saboda wasu halayen na mijinta kwata-kwata ba su kwanta mini ba, mutum ne shi mai kallon tsiya, kuma duk lokacin zan hada ido da shi sai na ritsa shi yana kallona to sai hakan ya fara damuna, na fara kiyaye haduwarmu, sannan kuma ga gida dan karami, duk lokacin da zan yi wani uzuri muddin yana gidan bana iya sakin jikina dalilin kallon kurrullan da yake mini, ita Anti Hamida sam bata fuskanci komai ba, ni kuma ina jin tsoron faruwar wani abu, sai kawai na yankewa shawarar tafiya gida. Ta tambaye ni dalili na hau dawurwura, kai tsaye dai ba zan iya furta mata cewa; Saboda mijinta na yanke wannan hukuncin ba.
Ganin ranta ya 'baci yasa na janye maganar tafiya, don gaskiya a duniya ina gudun fushinta kamar yanda take gudun nawa, sai dai ina taka tsan-tsan gurin gujewa wani abu da zai had'a ni da mijinta.

A can gida kuma Tokar ta tashi hankalin kowa lallai sai na dawo gida dalilin da ya sanya kenan ta turo Bahago da niyyar ya ta fi da ni.
Na ji dadin hakan, sai dai ban nuna a fuskata ba kawai dai na zuba masa ido ne a lokacin da ya zo gidan yana dogare a bakin 'kofa yana yi wa Anti Hamida Tijira, wanda har sai da idonta ya ciko da 'kwalla saboda jin zafin rashin mutumcin da yake mata, gabadaya ya raina ta baya ganin girmanta dan tana a matsayin sakuwarsa,

Ya kalle ni tare da cewe; Ki had'o kayanki mu tafi lada ya isa, kawai kin zo gidan mutane kin yi gososo! dake, ko kunya ba kya ji kina cinye musu abinci, me na sama ya ci ballantana ya bawa na 'kasa." Ya karasa maganar idonsa a tsaye a kaina.
Na ce."Ka je kawai zan dawo gida gobe."
Ya zabura! jikinsa har karkarwa yake Ya ce." Kina bukatar duka na ga alama, kin san bana son jayayya, don haka ki shiryo kayanki mu tafi ko na ci....Ya 'karasa maganar da zagin Uwata dama ita ce Marainiyar wayonsa.
Kallonsa na yi da cewa; Ni na san muhimmanci iyaye tare dana gaba da ni, ba zan mayar maka da martani ba, gida kuma ba zan tafi ba sai lokacin da na yi niyya, idan kana da 'kwanjin d'aukana aka bisimilla.
Ban yi aune ba kawai na ji ya cakume ni, kuma gabad'aya hannuwansa biyu a kirjina ya sauke su, yana k'okarin sa ni a kafad'a duk da girmana kuwa.
Na fara naushinsa a sassan jikinsa ina kokarin dira kasa yana kara cakumata! Anti Hamida da sauri ta zari igiyar guda ta fara zabga masa a bayansa, ko a jikinsa, sai da ya sa ni a kafad'a ya tallefe mazaunai na kawai ya kama hanyar fita.
Anti Hamida ta ruga a guje taje ta rufe gidan, fadi take "Wannan Yaro ban san irinsa ba wallahi, watakila dai ba shi kadai yake rayuwa ba.
Ni kuwa cizo na gartsa masa a kunnensa, ina kuka tare da dukansa! " Ka sauke ni d'an iska azzalimi."
Ya dire ni, a tsakiyar soron muka yi cirko-cirko! ya zura hannayensa cikin aljihun wandon dake jikinsa yana kallonmu.
Cikin tsantsar takaici da bakinciki Anti Hamida ta ce." Ali ka zo har cikin gidana kana zagi na ko?." Shiru ya yi bai ce komai ba.
Ta cigaba da cewa; Ko babu nasaba da danganta a tsakaninmu ban cancanci wannan cin zarafin ba, amma kai ba ka kunyar tozarta ni a ko'ina! wai shin mai yake damunka ne?"
Ya yi shiru har yanzu idonsa yana kaina ina ta rusa kukan ba'kinciki!

Na ce." Anti Hamida Ni fa zan iya shan fiya-fiya! ko kashin 'bera na mutu saboda wannan?" Na fad'a tare da nuna shi da hannuna.
Maganata ta ba su tsoro gabadaya. Ganin haka yasa na zabura! da gudu! nayi cikin gidan ina ihu! gadan-gadan rijiya na nufa!
Wani uban ihu! da ya kurma! sai da gidan ya amsa! yayo kaina a guje! igiyar gugan ta tad'e shi ya fad'i a gurin, ni kuma na bude rijiya na zura kafafuna biyu ciki.
Anti Hamida ta fashe da kuka! tana kiran Innalillahi'Wa'ina ilaihi rajiun! duk ta d'imauce!

Ina kuka da majina da hawaye sun ha'de Na ce." Anti Hamida ki yafe mini, sai mun hadu a darus-salam." kawai sai na saki murfin rijiyar, a lokacin ni kaina a kid'ime nake, na san idan na fada rijiya na mutu a wannan sanadin zan tashi a matsayin kafura! wannan dalilin yasa jikina karkarwa! hannuna d'aya ya zame duk jikina a cikin rijiyar, hannuna dake rike da dandamalin rijiyar ya ri'ke katamau!! ya zuro kansa jikinsa sai kyarma yake yana had'a zufa! Ya ce.

"Don zatin Allah kada ki fad'a, kada ki yi mana haka Jamila idan ni ne matsalarki na rantse da wanda raina yake a hannunsa na daina 'bata miki rai, ke idan ba kya son ganina ma gabad'aya zan tattara na tafi legos, amma kada ki yanke wannan hukuncin, zan shiga garari! sannan kuma Babanmu 'Danlami zai shiga damuwa, kada ki manta fa ke kadai ya haifa, ka da ki yi masa haka." Ya karasa maganar da wani irin rauni da sarewa! idanuwansa sunyi jajawur! Ya rike hannuna da dukkanin 'karfinsa!

Jikina ya yi sanyi, fargaba da tashin hankali suka dabaibayeni, na juya! na kalli nisan rijiyar dake cike da ruwa tunjim! na sake shiga tashin hankali, lokacin ne na fara nadama, na rike hannunsa katamau! ya rike nawa, kafafuna suna jale-jale! haka ya janyo ni wasu guraran na jikina duk sun dauje, ni da shi muke zube a bakin rijiyar muna mayar da numfashi wahala da tashin hankali!
Anti Hamida ta mi'kar da ni tsaye. Jikinta in ban da rawa babu abinda yake.
'Daki muka nufa ba mu san lokacin da ya fita daga gidan ba.

Anti Hamida ta jima tana jan kunne na akan abinda na aikata, wanda ni ma a lokacin nake cikin nadama mai tarin yawa, sai dai farincikin da nayi wanda na yi hakan domin sa ya tsorata dama ni babban burina kenan ya fita daga rayuwata.
Haka muka kwana sukuku babu mai kuzarin kirki a cikinmu, misalin karfe takwas da rabi na safe, Uncle Sadiq mijin Anti Hamida yana k'okarin fita da babur dinsa Babana Ya yi sallama a gidan, muna jin lokacin da suke gaisawa a soro kafin ya yi masa jagora.

Gabana na fad'uwa na gaishe shi, don har ga Allah na yi tunanin Bahago ya fad'a masa abinda na aikata, sai na ji sa'banin haka ne ya kawo shi. Bayan sun gaisa da Anti Hamida ya tambayi yaranta, sannan ya d'ora da fadin abinda ya kawo shi gidan wato Umarnin Tokar lallai na dawo gida yau.
Anti Hamida ta dinga kawo masa hojoji, ya'ki sauraranta.
Sai Uncle Sadiq din ne ya lallaba shi cewa; Ya yi hakuri in sha Allahu idan ya dawo da yamma zai kawo ni gida da kansa, sannan fa ya ha'kura ya tafi bayan ya bawa Yaran Anti Hamida d'ari biyar ya ce su raba.

Yanda na lura Anti Hamida sam bata son tafiyata, ni ma sai na dinga nuna alhini da damuwa, amma can kasan zuciyata murna nake da tafiyar saboda na tsani halin mijinta.

Daf da magariba na kalleta tana ta 'kokarin 'daura sanwar dare, Na ce." Anti Hamida kin ga Uncle bai dawo ba har yanzu, ko za ki ba ni kudin mota na tafi kada dare ya yi."
Ta ce." Yana kan hanya ai kin san wani lokacin ya na wuce magariba bai dawo ba." Shiru na yi ban ce mata komai ba, cikin zuciyata ba na 'kaunar wata alaka ta had'a ni da shi.
To har bayan isha'i babu labarinsa, na ci abinci na had'a kaya na shiru, duk na damu, ita kuma sabgar gabanta kawai take yi da yaranta. Kira ne ya shigo wayarta, ta d'auka duk da ba hands free tasa ba na gane da wanda take magana Bahago ne, Tana fad'a masa cewa; Mijinta ne zai kawo ni, ban ji amsar da ya bata ba, kawai sai na ga ta kashe wayar tana jan tsaki!

K'arar babur din Uncle din ta cika gidan alamar ya dawo kenan, Yusra da Yasir suka ruga a guje suna murna, Ajiyar zuciya na sauke tare da gyara hijab din wuyana. 'Dakin ya leko, sai kuma ya bud'e bakinsa da mamaki a fuskarsa yake kallona.
Anti Hamida na 'yar dariya ta yi masa sannu da zuwa ya amsa da cewa; Jamila tana nan ashe?"
Harara na zabga masa mugun haushinsa ya turnuke ni.
Ita kuma a maimakon ta nuna masa kuskuransa sai ta kama dariya tare da cewa; Kai ma Abban Yasir na lura baka son ta tafi shiyasa ba ka dawo gidan da wuri ba."
Sai ya kama wata dariya kamar shashasha! Ya ce." Wallahi kuwa kamar kin shiga zuciyata, sam ba na son Jamila ta tafi zamanta a gidan yana nufin abubuwa da yawa."

Maganarsa bai sa ta fahimci komai ba, Ta ce." Yanzu dai dare ya yi sai a bari sai gobe'' Agogon dake d'aure a hannunsa ya duba da cewa; Gaskiya kam tara saura sai mu bari gobe idan zan fita sai na ajiyeta."

Na kalleta a cunkushe Na ce." Anti Hamida Yau fa sai gida wallahi, ba na so a yi ta magana d'aya, mu girmama maganar magabatanmu don Allah idan ba zai kai ni ba, to ki ba ni kudin mota na kai kaina gida."
A sanyaye Ta ce."Dare fa ya yi Jamila ki bari sai gobe mana"
Ba tare da na ce mata komai ba na sunkuci kayana na kamar hanyar fita.
Ta kalle shi tare da cewa; Kana kallon yarinyar nan Abban Yasir wai sai ta tafi."
Wata munafukar dariyar ya yi Ya ce." Tunda ta dage sai ta tafi ai sai mu ha'kura bari na je na kai ta.
Bayana ya biyo rike da mukkulin babur din sa, Anti Hamida ta biyo mu har soron tana rarrashina, na taurare! ko sauraranta ban yi ba, yana burga babur din na tattare zanina na hau muka fita daga gidan fadi take "Kin kyauta Jamila a gaishe mini da mutan gidan kafin na zo." Na ce za su ji In sha Allahu rabbi.

'Yar 'karamar akwatin kayana na sanya a tsakiyarmu dalili ba na so jikina ya had'u da bayansa tunda Allah ya albarkace ni da kirji masu tudu da girma, to duk wannan dabarar da na yi sai da wasu guraran suka dinga had'uwa saboda gwajab-gwajab, haka dai muka isa gida yana ta yi mini hira, jin sa kawai nake babban burina na sauka daga babur din na huta rashin sabo ya sanya 'kafafuna duk sun yi tsami, cinyoyina sun sandare sai ciwo suke mini.
[7/6, 12:31 PM] bintaumarabbale: 14
Ganin ina ta cuku-cukun saukowa daga babur d'in ne yasa da sauri ya fara taimaka mini amma duk da hakan sai da salansar babur din ta k'ona ni a wajan 'kwaurin 'kafata, na sauko ina yamutsa fuska, shi kuma da sauri ya kafe babur din, hannunsa rike da akwatin kayana duba gurin dana 'kone d'in janyewa na dinga yi domin gabadaya haushinsa na ke ji ganin abinda yake wai lallai sai ya ga gurin, wayarsa ya kunna yana haskawa.

A daidai lokacin Bahago ya fito daga cikin gida ya riske mu a haka ina tsaye Uncle Sadiq din na gurfane a gabana ga zanina a tattare dalilin k'onewar da na yi yasa na tattare zanin.
Ganinsa ya sanya ni cikin fargaba, sai kuma na tuna alkawarin da ya yi mini cewa; Zai fita daga rayuwata har abada.
Yana zuwa bai yi wata-wata ba, yasa 'kafarsa dake cikin kambos ya buge hannun Uncle din katuwar wayarsa mai tsadar gaske ta yi tsalle ta fada cikin kwatar dake gefen mu.
Cike da mamaki Uncle din Ya kalle shi.

"Ali kan ka daya kuwa?" Ya fada yana kallonsa zuciyarsa cike da jin zafin abinda ya yi masa.

Tsaki ya ja mai tsayin ya kama hanya ya bar gurin cikin tsananin bacin ran dana gani a tare da shi. Ni ma ban yi wata magana ba na dauki akwatina na shige gida domin shi kansa Uncle Sadiq din haushi yake ba ni saboda abubuwan da yake aikatawa, ina zargin dai yana cin amanar Anti Hamida domin duk ga alamun rashin gaskiya nan ya bayyana a tare da shi.

Bahago kuwa wani matashin saurayi ya turo da wata kibiya mai tsinin gaske lokacin da Uncle din yake kokarin dauko wayarsa da ta tarwatse a cikin kwata, a sannan saurayin ya sanya kibiyar duk ya caccaka masa a tayar babur din, da sauri ya bar gurin bayan ya gama abinda aka sa shi, A takaice dai Uncle da turi ya je gida domin ko da ya fita titi masu faci sun tashi haka ya dinga tura babur din ransa idan ya yi dubu ya 'baci! Bahago ya janyo masa asara wayarsa dubu dari da tamanin ya saya amma ta tashi daga aiki, kawai don yana jin nauyi ne amma wallahi da sai ya hukunta yaron, haka ya shiga gidansa cikin k'unci da takaici mai tsananin gaske.

Ashe da sauran rina a kaba domin yana shigowa gidan, ya hargitse da hayaniya ganin yana 'kokarin ya yi mini sharri yasa Na ce.'' Wato ka 'dauka abinda ka ke aikatawa kowa ma haka yake, to Allah ya sawwak'e ya tsare ni da aikata zina, kaima ina rokon Allah ya shirye ka."

Duk da na kauce sai da dukan da ya kawo min ya same ni a gefen kafad'ata! na mike tsaye tare da rarumar wani kwanon sha mai nauyin gaske na jefa masa ya sauka a goshinsa. Tokar ta rushe da kuka tana kiran "Ya Wahidun Ahadun ka shiryi zuri'ar Malam Zangina mai 'yan makaranta, Ni 'yasu ya zanyi da rayuwata yara za su kashe kansu.'' Kuka take tukuru! Hawaye na zuba majina na dulala!

Ya tsallake kafarta ya nufo ni da zafinsa!
ganin idan na tsaya zai iya yi mini illah ya sanya na fara 'kokarin guduwa domin ceton rayuwata, amma sai da cimma mini, ya shak'e mini wuya ido jawur! yake magana. " Waye ya ce ki hau babur d'insa?"
Kamar mahaukaci haka ya zama ya tara zufa! jikinsa sai kyarma! yake.

Ido kawai na zuba masa babu halin magana tunda ya sha'ke mini wuya watakila kashe ni yake so ya yi, duk sambatun surutan da yake yi ba na fahimtar komai.

Sama-sama na ke jin maganar Kawu 'Danjuma shima Allah ne ya dawo da shi gidan a lokacin, da k'yar, ya kwace ni daga hannunsa.
Rungume shi nayi ina kuka tare da kiran Innalillihi wa'ina ilaihi raji'un.
Ya zaunar da ni a kusa da shi yana tambayata, na kasa yin magana tsoro da fargaba sun gama kashe mini jiki, gabadaya duniyar ta fice mini daga rai, cikin zuciyata nake raya cewa watakila Bahago shine ajalina.

Ya kalli Tokar dake ta koke-koke! sai surutai take marasa kan gado da ma'ana, Ya ce." Tokar kada ki yi sa'bo don Allah ki yi mini bayanin abinda ya faru."

Kafin Tokar din ta

Please Login or Register in order to submit comment