Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk sanda nazo Nigeria na kanji tamkar na taɓa rayuwa a cikin ta amman na rasa gani komai a daren jiya nayi mafarki da wata yarinya ta kasance MAI CIKI CE!!!











Tana ambaton suna na da na tsaya ga yarana na tsaya a cikin wanan yanayin wasu abubuwan suka fara min yawo a kaina da safe bayan na shirya nazo plaza domin gabatar da wasu ayyuka na yanki tikiti na zanje Borno domin neman wanan MAI CIKI CE dake kira na tana nunamin wasu da cewa ahalina .








Kwatsam na taimaka mata da magana aka bata turare ina juyawa naji tana ambaton abinda nakiji kuma naki gani a barchi na cewa don Allah na tsaya lokacin da ta tsaya da ZALFAT a gaba na nan duk wane tunanin na ya dawo normal daga lokacin da Zayyan ya rungume ne naji duk duniya ba abinda naki marari tamkar ahali na da na bari tsawon shekaru goma sha takwas shin ina Khadija"?..




















Shuru duka sukayi sai hawaye musamman matan ZALFAT ce ta matso ta dafa sa suna haɗa ido ta faɗa jikin sa suka ƙanƙame juna ta fashe da wane matsanancin kuka duk an gaza mai rarrashi su chan HABLAT taga abun bana ƙarewa ba ne ta wuce ɗaki nan ta fito da wani leader mai tambarin asibiti fridge ta buɗe ta ɗauki goran ruwa mai ɗan sanyi ba dewa ba ta iso











"Kinga ZALFAT kin fa takurawa Daddy ga maganin ke yau daman baki sha ba na lura dake bakison magani kuma kinsan ke MAI CIKI CE. " duk ganin ta sukayi ganin ƙarfin hali irrin nata hannu tasa ta janyo ta kaɗan " ki daina kuka Mama na bukatar adu'a ke idan tana raye Allah ya bayyana ta tamkar yanda ya bayyana mana wanda muku da tabbacin mutuwar sa to ina ga wanda ta fita tayi tafiyarta ba'aji labarin mutuwar ba duk ku kwantar da hankalin ku "











" Matso ƴa ta matso" cewar Daddy nan ya dafa kafaɗarta "Allah ya miki Albarka haƙiƙa duk wanda sukayi sillar haifa ki duniya bazasui nadama ba ko ƙunci saidai su kasance masu farinciki da wadatar zuciya Allah ya miki Albarka"











"Amin "ta amsa da murmurshi a fuskarta "yauwa yanzu kam don Allah kowa yayi farinciki a samu sallama a zuciya" murmurshi Hafeez yayi "to sarkin magana kin kawo wa ZALFAT maganin ta ina da tabbacin kema baki sha naki ba "hararra ta watsamai "na rantse da gemun kaka na nasha haba ai na warke ma me sai nasha wani magani ZALFAT ce ya kamata tana shan magani not me














"Duk dariya sukayi kafin nan sai ga Amrat da leader " ga maganin ta nan Commender rabon da tasha maganin nan tun da muka zo wanan gidan ," to kinga daughter maza maza kisha maganin ke bakiga ke MAI CIKI CE ba"





Cewar Abba amsa tayi tana ya mutsa fuska haka duk su biyu nin suka sha maganin su sosai dadday da Abba suka samu farin ciki burin sa kawai bai wuce yaga Zee ba don ya barta tun tana ƙarama Abba ne yayi gyaran murya " wai ZALFAT yaushe kika fara magana ne " kai ta sosa " ummmm Abba wato wato" .

















Duk dariya sukayi " wato wato me " nan Daddy yayi murmurshi ciki da kewar ƴar sa da tausayi halin da ta tsinci kanta a cikin duk yana gani laifin sa ne "Abba ne yaga taƙi magana yaga HABLAT kamar " da magana a bakin ke daughter gayyamin yaushe ta fara magana "








Ita ma zaro ido tayi " wato Abba maganar gaskiya tsakani na da Allah muna barin Borno ta warke ta fara magana kuma ko yanzu tace ta tsani wanchan garin ko sunan sa bata son ji "subhanallahi suka haɗa baki ƙuncewa shikkinan zan kira Hajiya Hauwa ta zo da Zee nan nin sanan kuma ya kamata na sanar da doctor Isa Labaran shima ya taho da nasa iyalan gidan nan dukka lallai zakaga Zee kamar ZALFAT taki ba wane banbanci ai "










16 \ Nov \ 2023


********************************************








Bayan kwana biyu tun daga wanan abunda ya faru hankalin sir Yazid ya kasa kwanciya ganin irrin wulaƙanchin da Kboy ya aikatawa yarinya 'yar shikkaru goma sha tara a rayuwar ta domin yaga vedio sai dai yana tunanin kawai ya bar case nin ganin ƴar babban mutum ne wataƙila sun rufe zancen ne don kar maganganu mutane suyi yawa akan su kansa ya kifa ya rintsi idon sa ya tafe dogon tunani





.( kamar dai yanda naki muku dogon typing 🤣)















Da farko sunana Yazid mahaifina ya kasance tsohon ɗan sanda mai adalci da son zaman lafiya yakan tsaftace gari ta hanyar hana shigo da kayan maye musamman dokokin ƙwayar da aki safaran su ta ɓarauniyar hanya , kwatsam watarana cikin dare wasu mutane ƴan fashi suka kutsa gidan mu daki nan cikin Kano da haɗin bakin wasu ƴan sanda suka shigo da makamai akan cewa lallai Lallai mahaifina ya basu wasu muhimman bayanai na wasu takardun.














Shi kuma ya nuna taurin kai a wanan lokacin ina da shekaru ashirin chiff a rayuwa ta sai Abdul dake da goma Ikram shikaran ta ɗaya haihuwar ta ne sillar mutuwar mahaifiyar mu Ina da ƙani biyu Abdul da Ikram da fara isar su mahaifin na ya nema ya kira waya amman sun datse network na gidan gabaɗaya anan ya bani wani bakar jaka cewa na fita na bar gidan da ƙani na bansaniba amman na matsamai lallai ya taho mu tafe tare sai dai hakan ya chutura nan muka bar gidan muka nufa gidan amininsa sai dai tunanin maganganu na mahaifina cewa kar na yarda da kowa na bada document nan yasa na samu kiɓantanci fili na ɓoye takardun nan.














Safiya nayi aka sanar da mutuwar mahaifin mu an kashi shi da bindiga har cikin gida shikkaru biyu akayi ana bincike wanan takardun a gidan basu damu da bincike mutuwar sa ba sai wanan document nin daganin hakan na ƙara ajiye su nasha alwashin zan zamu ɗan sanda na kwacewa mahaifina hakkin sa kwatsam watarana naji tasha anan na tsinci wata mata a kan hanya tayi accedent da gudu na ɗauki ta mukayi asibiti anan akace ta samu matsalar taɓin ƙwaƙwalwa sosai na kula da ita ashe ba ne na tsinci ta ba ita ce ta tsinci ne.














Aunty Khadija ta kasance wacce ta chigaba da bamu taribya irrin wacce uwa zata bawa yaran ta daga baya da ta warke nayi juyin duniya ta samu tayi aure saidai ta nuna rashin amincewa ta hakan yasa nasa ta kuma makaranta har ta zama babban likita kuma ta chigaba da kulla da mu ,











Bayan na girma na gani dalilin da yasa aka kashi min mahaifina nayi tsayawar daka har ta kaiga ga na datse duk wata ta shigowar kayan maye a ruwa a jahar Kano a nan aka ƙaramin matsayi zuwa assistance Commitioner a kamin transfer zuwa Borno sai dai Aunty batason hakan ba itama na mata transfer zuwa Borno muka fara aiki wata daya kinan saiga had'uwa ta da Zee a kan hanya .













"Yazid! Yazid!! Yazid!!! zabura yayi "oh sorry Aunty " murmurshi tayi ta zauna tana miƙa misa ƙaramin cup dake kunshi da coffee mai zafi " Aunty yau da kanki baki aiko Ikram ba"? "umm a'a gwanda nazo naganka na ganka bakaji hausawa suka ce zuwa dakai yafi ɗan sako ba "











" To da alama akaiw zance ko"? gyara zama tayi "da farko Yazid kamin komai ban nema komai na rasa ba amman gashi yau inaji ina gani kana cikin matsala da damuwa ka kasa gayyamun banssn yaushi ka sauya ba , ohh my God aunty nifa ba komai i already tell you "





Murmurshi tayi " idan tayi tsami har ɗaki na zakazo ka sanarmin ne ɗan uwa bare kawai naje ", " to Aunty na nagode da kullawa ba komai ma ummmm " haka suka sallami juna ciki da nuna kulawa da lafiyar juna ....














Sharhin ƙanwat ta sis Ma'u





Waiyo Allah uktty Alhaji Imam ya dawo ga Sahibar sa Hajiya Khadija Soyayya sabuwa ga kuma ɗiyar su harda ƙarin ciki sai masha Allah.





Kai HABLAT ke nin duniya ce sillar ke family sun dawo ke har a mafarki kina zuwa congratulations barka kinsha magani.....










Lallai Sir Yazid rayuwar ku taban tausayi Allah ya shiryar da mutane masu maye da masu saffarar kayan maye..








Ya za'ayi nan gaba idan Hajiya Hauwa taga one family akaiw ƙura , Uktty Allah ƙara basira gaskiya kinsha fama da labarin nan ya haɗu.












Masha Allah dake da masu zuba Sharhi ina matuƙar godiya 🥰🙏💓








AL'KALAMIN NARNAH ƘANWAR SOJA 🖋️💞🤰🤰🤰🤰🤰🤰🤰












MAI CIKI CE
💘❤️💘❤️💘❤️💘❤️
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️ 💞







Facebook page : Narnah ƙanwar soja
Wattsppt numb: 08101235739



















PART 2
PAGE 43& 44



The comedian sweet love story with full of sympathy.💔🔥😭









❤اللَّهُمَّ عَافِـني فِي بَدَنِي، اللَّهُمَّ عَافِـنِي فِي سَمْعِي، اللَّهُمَّ عَافِنِي فِي بَصَرِي، لَا إِلَهَ إلاَّ أَنْتَ. اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُبِكَ مِنَ الْكُفْر، وَالفَقْرِ، وَأَعُوذُبِكَ مِنْ عَذَابِ الْقَبْرِ ، لَا إلَهَ إلاَّ أَنْتَ🥺🙏





LAST PAGE


18\ Nov \ 2023.











KANO





**********************************************



A hankali ya sauko daga motan cikin shigar kamala da ƙarfin sa fararren kaya ne a jikin sa wanda ya sha zubin aiki kalar ƙasa Afra ce ta fito tareda Zee wani kallo sukiye wa gidan juyuwa tayi "Mommy nan ma gidan Daddy ne "?














Murmurshi tayi mata " banda abunki haya daman zai kama lokacin kuna yara munzo gidan kawai dai an ƙara mata gyara ne amman ita Amrat tasan gidan tunda anan Kano taki karatu daman ,








Hajiya Talatu ne gabanta ya fad'i rass ta dafe Hajiya Hauwa " kinji abinda nakiji kuwa "abin ba ni kaɗai bane bansan dalilin da yasa Alhaji ya gayyaci mu nan nin cikin gaggawa ba " duk shiga sukayi kicibus Hajiya Hauwa tayi da ANBAR nan suka fara kallo kallo ciki da tuhuma ta tunkaro ta





Ke uban mi kikiye a gidan nan daman baku watsi ba "murmurshi tayi mata "maraba da zuwa cikin dangi Hajiya Hauwa "baki ta buɗe" ne da gidan miji na zaki min maraba wai ke wacce irrin "bata gama magana ba Latu ta iso tare da buɗi mayafinta" Salma "cewar Hajiya Talatu "daman kicce kina raye "daga jin an ambaci Salma Alhaji Isa ne ya matso duk ganin juna sukiye tamkar yau suka san juna.














HABLAT ce ta turu cikin ta ta fito rigi da plate da na qwara da yasha ɗanyin albasa da yaji "maraba da zuwa wanan gidan mai Albarka " bata gama magana ba Afra ta watsa mata harara da ganin ta sam ba kwanta mata a rai ba ita ma hararrar ta watsamai ta da cewa "ina fatan duk wacce ta kasance batajin magana zata ajiye a bakin ƙofa domin akaiw aljannu a wanan gidan masu bala'in "!








Inna ce da fara'a ta fito "a'a HABLATU ya akabar baƙin a tsaye maraba ku da zuwa maraba" fuuuu Hajiya Hauwa ta wucce ɗakin sama duk kallo suka bita dashi Zee ce ta nufa wani ɗakin tana cewa " mutum da gidan uban sa amma duk an tara wasu agawki marasa kunya talakawa " da ido HABLAT tabi Zee dashi da ɗaga murya











"Allahu Akbar muje aya nagaba" sam abinda su Mommy sukayi baiwa Amrat daɗi ba musamman ma Zee da zagin da ta zunduma ZALFAT ce da ta ɓoya HABLAT ta ganta kama hanun ta tayi "su kuma wanan suwaye kinan'" nan ta kwashi komai tagayamata lallai akaiw ƙaramin yaƙi a gidan nan don wallahi idan akamin abu sai na rama "















" Subhanallahi kiye haƙuri wallahi masifafune bansan magana kinji ki barsu kawai halin su ne a hakan" tura abinchin nata tayi bakin da " to wallahi ko Abban Majhat ne yamin ba dai dai ba sai na rama balle ma wanan ƙwarin " oh sorry ƴar uwar ke ma ko"











Dariya tayi " ke na gayyamiki wanibabban sirrin "da sauri ta ajiye plate ɗin ta kura ruwa ta matso da kunnen ta "gayyamin mana ƴar uwa kar kuwa ma yaji " dariya ta mata duk inda gurmi yaki anan kike ko HABLAT ? to Zee fa tana son Doctor Zayyan kishi takiye dani bare kuma kigani da idon ke "











" Kan bu" da sauri ta toshi bakin ta "don Allah karkiye zagi ashar ba kyau bugi hannun ta tayi " don Allah saki ne shiyasa ma na tsani ta ashe ballagaza ce ko mijin ke takiso munafuka tana tafiya kamar wata sabuwar amarya wacce mijinta yamata shigar ƙarfe da wani bakinta kamar na "








"Oh my God kar muyi hakan dake kamar ya bangani maganar ke ba "shiru HABLAT tayi " no kawai rai na ne ya ɓace kuma naga tafiyar ta kamar da matsala "dariya ZALFAT tayi ko dai kin tsorata ne " nan matsowa tayi to ita kuma wanchan ƴar kyakyawar budurwar mai lankwasa hanci wacecce ita "









" Ita sunan ta Afra yarinayr wanan babban mutum da kigani ya bi matar sa ƙatuwar nan waje sunga Latu sun rikici to itace mahaifiyarta yawancin hallayar su ɗaya da Zee banbanci su kaɗan ne ita Afra idan taga dama tana kwantar da kanta amman ta tsani talaka kuma uwar ta ma asalin ta talakawa ne" ganin Anbar tana shigowa gunsu ne suka nitsu "






"HABLAT tunda naga ku anan gulma kukiye ko "? ZALFAT ce zataye magana ta kwaɓi hanun ta " no kawai muna tsara kalar tarbar da zamuwa baƙin mu ne" zama tayi alright nima aye dani kafin su Abba su dawo ko " girgiza kai tayi da cewa " Aunty ANBAR nikam da safe da na fito naganki da Abba kamar kuna magana wai zancen mi kukiye ne "? pillow ta hurga mata wanda hakan yayi dai dai da shigowar Hafeez da Zayyan " A'a ban shiga ukku ba meke faruwa da dukkan matata "duk dariya sukayi nan suka hallara suna hirar su ,














23 \ Nov \ 2023


BAYAN WATA BIYU



"Abban Majhat wai ina zaka fita sai sauri kakiye" murmurshi yayi mai kyau ya ɗauri takalmin da "wato ke HABLAT idan mutum baison magana lokacin kikiso banda neman magana irrin naki ga uniform a jikina still you are asking me ina zanje "turo baki tayi "oh Allah ya baka ha'kuri daga tambaya sai ya zama masifa" baki ya bude " wallahi banda time naki yau rigimar ke kiyewa su Inna idan kinje part nasu ko in kun haɗu a babban perlour"














Yana magana yana fita da sauri ta ɗaga murya "waiyoo Allah "cikin azama ya juyu don tabbatar da lafiyarta " Abban Majhat ka taimaka ka samin talakalim muje perlour duk ƙafan ta kumbura kamar ba a jikina naki jiba sam " da kallon tausayi ya bita dashi takalmin yadirgusa ya sanya mata tare da kama hannun ta ta tashi hankali suka fito sai nishi taki lokachin da Ta zauna a kan kujerar babban perlour sallamar ta yayi ya gaida Inna da Mallam wanda aka basu part nasu na musamman daga ciki madaidaiciyar parlour da ɗaki har biyu sai kitchen da toilet a kowane ɗaki haka wasu part suka kasance a wanan gidan,

















Tafiyar Hafeez da minti talatin HABLAT ta tsunduma wane azazzababin ihu daga kan kujerar ta faɗo a ƙasa "Waiyo Inna waiyo Baffa waiyo Mallam shikkinan ƙafata ya fitta daga ganganr jikina "da sauri ANBAR da ta taso daga kan gado ta fito "subhanallahi HABLAT ko haihuwar ce" ina ko jinta batayi sai runtuma ihu takiye da gudu PAYAM ya fito cikin uniform na makaranta wanda ya mishi kyau da sauri ya yar da jakan hakan ya buɗe wani ƙofa daga perlour yaki tsunduma musu kira














" Doctor kamar fa ana kiran ka kuma like inajin ihu " mirginawa yayi ya kama hannun ta yasa hannun sa akan tumbin ta " kedai yau kuma salon da zaki tashi ne a barchi kinan don na fitta da wuri ko " kafin ya kamalla muryar PAYAM ta duke dodon kunne sa da gudu ya fito wanda ZALFAT ta taso a hankali da tunbin cikin ta a waje haihuwa ko yau ko gobe kafin ta iso babban ɗakin nasu tuni da taimakon Zayyan san ɗauki HABLAT zuwa asibitin ARFAT Kano special hospital kano domin bata agajin gaggawa na masu haihuwa.

















Isowa su yayi dai dai da ƙarasowar Hafeez a ɗimauce duk ihun ta ya karaɗi layin masu labour room doctor me ya kama hanun sa" look soja maza basa shiga" hararra ya dallla mai ya wuce nurse ce ta waworo zagi zata buga mai ganin sa a tsaye zololoo kamar bishiya cikin kakin soja ta rufe bakin ta don ko murmurshi bai mata ba da sauri ɗaya ta zungure ƴar uwar ta '














" Kinga ko ashe masifar Rabi kam na rainin waiyo ne tawa soja mana kuma da alamar matar sace gashi ta tsinka mata mari har biyu Allah ya sama ita kaɗai ke labour da yaga matan mutane ta faɗa cikin raɗa " kedai bare sis da ta zagisa da taga ruwan bala'i yau mai ƙwatan ta sai ya shirya" basuji fitar ta ba sai motsin ƙofar sukagani











"Waiyo Allah Abban Majhat na mutu ka taimaka wa rayuwa ta nagama yawo ka karɓi cikin ka namaka al'kawarin bazan saki kwana da kai ba bare ma nayi ciki kaje ka aure mata ukku kai na baka lasisi huɗu ma kayi yo hauka naki waiyyyyyoooo " da sauri ya ƙanƙame hanunta sai hawaye yana











"Sorry my HABLAT ke daure kinje kifa matar soja ce ko ke daina ihu nan haka" what !!! ta faɗa da ƙarfi hanun ta tasa ta sharara mai mari " nabi matar soja da gudu kai na yaga barrack nin nasa a kundon bola bazan daina ihun ba ka cuci ne ka cuci rayuwata Allah ya isa tsakanin na dakai mugu azzalumi bazan ye shirin ba '"











Inna da ta iso takama baki da sallati "haba mai sunan larabawa adu'a zakiye kinje kin kusa ma suka ce " wallahi Inna yaron ke ya cuci ne daman haka haihuwar take Allah ya isa mun sunan turawa ne wallahi mutuwa zanyi nabi uwata munyi barchi wanan zalunchi ne "








ZALFAT da suka iso leqawa tayi ganin irrin kururuwa da HABLAT taki saida zuciyar ta ta buga ido ta walwallo waje sam doctor baisan ma ta zo hospital nin ba dasu Hajiya Hauwa da Amrat sai Zee suka hau mota suka iso , zufa ce ke malalowa "wai Abban Majhat wanan gadon shine ake cewa gadon azaba duniya duk mace da ta hau to tashiga aljanna ta fito duk zunubanta ma ai za_a kogee ko ?"








" HABLAT haka ne "lahaula lahaula lahaula wane azabbabin ihu ta buga nan doctor Khadijja ta iso da facemask a fuskar ta da wasu nur'ses " sorry fa Madam push ganin Hafeez tayi " oga kayi ha'kuri kujeramu a waje" ko bai mata gardama ba sam ya fitta sai Inna dake gun " doctor ce ko ko aljanna ce ke duba min zan mutu ko don Allah idan na mutu kice ina da ƙanjamau kar yaya Hafeez ya ƙara aure shikkinan wahalar ta ta tafe a banza kinan"











ZALFAT ce ta rigi mararta da bayan ta sai ga wani uban nishi da amai sai nan Zayyan ya ganta" ZALFAT are you fine "innalillahi wa ina iallhin raji'oun doctor zan mutu "!!!! sosai ya tsorata da sauri aka shigar da ita ɗakin HABLAT kusa da gado aka duba ta akace labour ne ta tsinki but bazata jima ha

1 Comments On MAI CIKI CE
avatar
anas-muhammad

1 year ago

Reply

Good novel

Please Login or Register in order to submit comment