Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hajia Binta kuwa malamanta ta bawa aiki kan a hana Rahina aiwatar da kudirinta kan Omar da Iklas,dan haka da Umma Rahina ta tasarwa aikata sharrinta sai wani abun ya faru Wanda dole sai ta kasa aikatawa,abin ya dameta,ta rasa wai meke damunta,amma tunda hakane zata sa su Sadiya suyi komai,ai tana da jininta.

Omar bacci yake ji tuni ya fara baccinsa jikin Mama,Ummi kuwa tana can tana gyarewa Iklas kayanta tunda yanzu bata da wani lokaci,Gajia Mama tayi ta dauke kan Omar ta maidashi cinyar Iklas tace idan ya farka Ku koma part dinsa ta wuce Iklas... Tuni Iklas ta fara hawaye ita wai yanzu haka zatayi rayuwa duk ta gaji jikinta ciwo yakeyi,shike nan ita baza ta huta ba,kuma itama baccin takeji fa,ga shi an koma schl wayyo aikin Gomnatinta,

Omar sai baccinsa yakeyi hankali kwance,Sai daya tashi dan kansa ganinsa yayi kan cinyar Iklas,sai haushi yakeji ansashi aikata sabon Allah.ko kulashi Iklas batayi ba sabo da haushinsa takeji an takurata.
Kallo ya kare mata ke bakya damuwa wai hada jiki da mazan wasu?haushi ya kara turnuke Iklas bata San sanda ta kwanyawa Omar mintsini a cinya ba har cije baki takeyi dan mugunta,shakota Omar yayi ai kuwa Iklas dole me karfi yau baza ta kyaleshi ba,said suka fara kokawa tukuru suka kaure, shi Omar a hankali yakeyi da tsokana amma Iklas ita da gaske takeyi sai nishi takeyi wlh bazan dinga kyaleka ba na gaji ina ma Abu kana zagina.
Sosai Omar ke shan dariar Iklas ita dole fada takeyi,Iklas da kanta ta gajiyar da kanta kawai ta fashe da kuka nan take Hankalin Omar ya tashi baya son ganin kukan Iklas,

Bai San sanda ya rungume Iklas ba yana jijjiga ta tare da shafa bayanta,lakwas tayi tana goge idonta,cikin rada ya tambayeta kin gaji ne?kai ta daga masa wai eh,bacci ko?nan ma cike da shagwaba ta daga masa eh.to shine abin kuka kalli yanda kika farfasamin jiki da dukanki dama haka kike da karfi harda naushina fa kikayi ko dai kin taba zama a China ba a sani ba.
Fashewa da daria Iklas tayi da ta tuno haukar da tayi tana ta kokawa da Omar bayan ita ta wahalar da kanta,hannunta ya kama suka wuce Room dinsa cike da shauki,Iklas tasha mamaki ganin har an gyara ko ina neat yana kamshi,suna shiga Omar ya dauketa kamar baby ya daurata bisa bed maza kema yi baccin tunda naga adawa kike dani kina min bakin ciki nayi bacci ke bakiyi ba,akan Mama ta dorani kan cinyarki kike bakin ciki.murmushi tayi abinta ta juya masa baya sai bacci.

Shi kuwa a.c ya rage mata ya lullubeta da hadadden bargonsa ya shige toilet domin yin wanka gashi yau so yake Iklas ta rakashi masallacin juma'a sallah,ya Dade bai je ba.
Sai 1 Iklas ta farka Arba tayi da kyakyawar fuskar yana zaune kasan bed hannunsa kan cikin Iklas kansa bisa bed yana ta bacci shima.minti kadan ya bude idonsa ya dorasu ana Iklas wacce ta shagala wajen karewa halittarsa kallo.
Kunya taji ta mike tayi hanyar fita daga room din,pls ki shirya za muje masallaci yau.OK tace tare da komawa dakin Ummi.
Ummi sosai ta kara yiwa Iklas nasiha tare da nuna mata muhimmancin miji.shiryawa Iklas tayi cikin wata rantsatsiyar doguwar Riga baka me adon Golden,cikin akwati set 4 da Mama ta bata kafin a hada mata lefe.
Yana gyalen tayi a kanta,ta sa takalmi Golden da da jaka Golden masu tsadar gaske,kamar balarabiya haka ta fito.walwali kawai takeyi.
Ummi ta yiwa sallama ta wuce dakin Mama da fara'a Mama ta tareta ina zuwa haka?Mama ya Omar zan raka masallaci zaiyi sallar juma'a.
A dawo lfy a kula sosai kinji.to Mama insha'allah cewar Iklas.
Har room din Omar ta kara komawa sai taku dai dai takeyi,a jikin mudubi ta ganshi da gani kasan karfin hali kawai yakeyi,wata mashahuriyar danyar shadda ya sa ita ba fara ba ba kuma milk ba,yayi matukar kyau dan dagwas dashi,sumar nan taci kudi luf luf da ita,turaruka masu tsada ya fesa sannan ya kwashi wayoyinsa,Iklas an saki baki ana kallon zasu makara kawai hannunta ya rike suka fito cike da taku me birgewa.

Yaran Umma suna tsakar gidan sai gulma akeyi.wucesu sukayi Omar wata gangamemiyar mota fara Sol ya nufa driver ya ba key ya tukasu suna Kane bayan mota, har masallacin da Omar ke zuwa.
Bai fito daga mota ba sai da aka tayar sannan ya saki Iklas yaje yabi sahu,ana idarwa ya dawo cikin mota wajen ta,driver ya jasu ya fada Masa wani park yace can zasu je.shima wajen shakatawar manya ne,da Iklas dinsa ya fito.nama ya siya musu da abubuwan ciye ciye anan suka zauna cikin lafiyayyen wajen inda aka tanada saboda masu zama suci a wurin.

Kafarsa ya dauka daya tare da zare takalminsa ya dorata kan kafar Iklas gaba dayansu wani yanayi zazzafa suka tsinci Kansu ciki tare da son kasancewa da juna.cike da farin ciki a zukatansu suka dinga baje girki a cikinsu.

Sun mike zasu tafi sai ga Sultan da Raj suma tafawa sukayi suka fara yiwa Omar cakaki Jan Iklas yayi suka fara tafiya,kafin su karasa mota,dan saurayin da ya taba bige Iklas ya karaso wurinsu har wani kishi yake shifa bai yarda ba Iklas yake so.

Haba baby Iklas rannan naje gidanku akace kun bar unguwar ina ta nemanki,nasha wahala wlh ko sunana fa Baku sani ba,pls ki bani numberki kinji.ya kalli Omar Wanda ya gama hasala.sannu malam, baby wannan yayanki ne?naga kuna kama dashi.Iklas murmushi tayi ta fara magana,

Asmabaffa

ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

85-90


By
Asmabaffa



KUJI DADINKU READERS.


Sannu ya gida? Yayana ne mana,mun manta an rabu ko sunanka bamu tambaya ba,washe baki yayi Suna na IBRAHIM ZAKARI ana ce min IBZZY BOY.daria ta kusa kwacewa Iklas yanda yace Ibzzy boy har da daga hannu kamar masu wakar raps.shi a dole nigger.
Omar yaso yayi maganinsa amma ganin kwata kwata ibzzy irin banzayen mazan nan ne sai ya shareshi,Iklas harda jin haushin Omar baya kishinta dan bai San matarsa bace ita.

Waya ta dauko da niyyar karbar number Ibzzy sabi da taji haushin Omar ba ko kishinta,fisge wayar Omar yayi tare da sa yatsa daya a dan chakurkurin kirjin Ibzzy ya tunkudashi baya sai da Ibzzy ya kusa faduwa,da masifa Ibzzy ya tasowa Omar dole sai ya ci mutuncin Omar, daukeshi da wani zazzafan mari Omar yayi Wanda yasa Ibzzy dafe kumatu ba shiri,kafin ya dago Omar har ya finciki hannun Iklas kamar tsinke kawai janta yakeyi har mota ya jefata,driver kuwa yaja a kabar Ibzzy da kumatu kumbure,a fili ya furta kai wlh saina ci uwar guy nan sai naga ubansa dan babarsa.

Gida suka koma a compound suka ci karo da Abdallah zai fita da Sauri yazo wajen Iklas wacce ke kukan masifar da Omar ya zazzaga mata kan Ibzzy.da sauri Abdallah ya kai hannu da niyar sharewa Iklas hawaye Omar ya bige hannunsa,bai gane ba ya kara yunkurowa zai rukota Omar ya shiga tsakani da Sauri ya tsaya a tsakiya,
Ya kare Abdallah kar ya taba Iklas,gocewa Abdallah yayi ya zame ya nufi Iklas anty wa ya Saki kuka kara kai hannu yayi,Omar ya jawo rigarsa baya kiiiiiiii ya dawo dashi baya,
Abdallah sarkin naci kara komawa yayi shima Omar cikin zafin nama ya cakuma Abdallah ya turashi baya yana zan mareka wlh,to yaya kuka fa take, cike da masifa Omar yace ina ruwanka ko huruminka ne ban son shishigi...wuce kasan inda dare ya maka.sum sum Abdallah yayi gaba abinsa yana kallon Iklas,an hanashi lallashinta.

Janta Omar yayi suka wuce wajen Mama... kallon Iklas tayi taga alamar tayi kuka,lfy Iklas me ya sameki?tana shesheka cike da shagwaba tace ba ya Omar bane dan kawai wani ya sanni munyi magana shine ya dinga min bala'i harda murdemin kunne wai zai cire min kunne, dadi Mama taji ganin Omar zai fara son Iklas fa,hmm nace Mama batasan zaman da sukeyi da Iklas ba su kashe su rufe.
Lallashinta Mama tayi tare da balbale Omar da fada,Omar kuwa kememe yaki karbar laifinsa Mama muna tafiyafa ta kama magana da wani dan ta raina min hankali ni ina sauri zasu tsaya bata min lokaci idan zancen takeso yazo gidan mana zasu shiga rayuwata harda cewa wai ni yayanta ne..to ba hanani karbar number sa kayi ba,kinji ko Mama dan karyane fa wai zata karbi number sa, to koma ki karbo mana yanzu tunda baki da hankali
Sai da ka bari muka dawo da ka barni mana tun acan cewar Iklas,gajia Mama tayi da cacan bakinsu tace dan Allah Ku je part dinsa kuyi can ni kun cika min kunne na rasa me gaskia cikinku.

Da sauri Omar yace ni Karta zo min room,tabe baki Iklas tayi to me zanci da room din naka ko kace Nazo bazanzo ba tun yaushe na daina kulaka ma,ae naji cewa Oga Sir, yazo zai wuce amma saida ya matso jikin Iklas ya take mata yatsa daya.ihu ta fasa Mama tace maganinki kenan Babana muguntar tsiya gareshi in kika bashi haushi,ki dinga kyaleshi kishinki yakeyi fa ke baki gane ba.
Karki yarda ki fada masa ke matarsa ce kinji ko,kai ta daga,idan ya warke kuma zaki koma schl sosai taji dadi wai zata koma schl,wayyo aikin gomnatinta.

Umma Rahina ce tasa yarta Naja aikin kan tasan yanda za ayi ta shige jikin Iklas sosai har ta jawo musu ita ta dinga shiga part dinsu,kuma ta gargadi su Sadiya su daina nuna mata tsana a fili,ta hakane zasu samu nasara..Sadiya tafi kowa tsanar Omar kawai jiran lokaci take ta kaddamar masa ba tare da kowa ya gane ba.

Ibzzy Boy ya cika da haushin Omar marinsa da yayi,kuma bazai daina son Iklas ba dole ya nemi gidan da suka koma yaje can,domin so yake ko ma ta halin kaka shi dai ya auri Iklas.wasu manyan kawensa mata da suke masa kawalcin mata JALILA WANKAN TSINKE da FATI GOCEWA ya kira ya shaida musu komai wankan tsinke tace haba Ibzzy kar ka ba damu mana kai da kake kullum matane frnds dinka amma ka kasa da wannan kucakar,

Fati gocewa tace ka bari kawai zamu je wajen LAWISA ICEN KABARI harda LADI PIJO wlh sai mun shawo kan wannan yarinyar ba gaggawa a nutse zamu wayar da ita dole ka aureta ita din banza dan uwarta ko da ubanta take kwana wace ita ta kara narko wasu manyan zagi.nan suka taru Ibzzy sai barin kudi yake musu.

Saleem ya kira wayar Ummi ta bashi address din gidan su Omar zai kawo musu ziyara sannan zai ga Iklas dinsa.sai dadi yake ji.har ya matsu Sunday tazo.

Sahar taji labarin Omar yayi budurwa nan ta fara bala'i wlh bai isa ba yana warkewa zan koma gidansa dole na tara dukiya nayi tafiyata,ko wacece bata isa ta rabi Omar ba,kuma ko ya aureta sai na koreta kuma sai ya saketa wlh,kai zan iya hallakata nan Sahar take ta bala'i a Office.wannan alkawarin sahar kenan itama.

Iklas ce tazo sanye da yar wata Riga da kadan ta wuce gwiwa me dogon hannu ce red kanta ba dankwali sai gashi yarab,tunowa tayi bata bawa Omar magani ba tunda sukayi fada ga dare yayi.da tayi fushi dashi amma yanzu ta hakura zata je room dinsa duk da yace karta kara zuwa masa.
A hankali da sallama ta shiga dakin nishin Omar kawai ta jiyo,kan sofa ta ganshi kwance amma dai tunda aka fara maganin suna ganin sauki,da dane da tuni Omar ya Dade da suma,

Karasawa tayi ta dakko maganin wajensa taje ta zauna gefensa kadan ta dago kansa sai sannu take masa yau da yake baya cikin hayyacinsa ba gardama yasha maganin,
Addua ta dinga tofa masa tana sannu kaji ya Omar tare da kara harde yatsunsu waje daya.
A hankali ya dawo normal yau Iklas tsokanarsa taso yi dan haka zamewa tayi ta kwanta cinyarsa,haushi ya kama Omar yarinya ba kamun kai,ta gama lalacewa a dalilin talla.
A ransa kuwa ji yake kamar su zauna haka har abada, zuciyarsa ta gayamasa kai bafa muharramakar ba ce kaji tsoron Allah don yana ganinku,ai da sauri Omar ya daga cinyarsa ya hantsilo kan Iklas ya mikar da kafarsa,
Magagin baccin karya tayi ta wani taho luuuu ta fada jikinsa,zameta yayi daga jikinsa,hannunta daya ta dauka ta wani jefa luuuu kan cinyar Omar,wata zuciya ce tazowa Omar ya dauki hannun Iklas yayi wancakali dashi tare da mikewa ya shige toilet.

Iklas kuwa daria taitayi amma kuma sai taji dadin hakan ta rasa me takeji haka tare da ita kuma bata ji a wani namiji sai Omar kadai.musamman da ta fada jikinsa sai taji wani ni'ima ta shigeta kamar ta karayi,tunani tayi tace ai kuwa tunda naji dadi saina dinga daneshi wlh,
Wata zuciyaar tace zai rainaki,can kuma a fili tace to mene ma wai tunda mijinane sai na dinga masa wayo.
Ai a islamiyya dama malam yace mana idan mace ta taba mijinta ladane,a radio har wanka akace idan kunyi sunna ce.
Tab bazan iya wanka gaban Sir ba,murmushi tayi tace kai wlh a wandonsa watarana ina hango sandar girmansa tayi katoto da yawa zureriya bazan iya kallonta ba.shuru Iklas tayi ta fara tunani ai kuwa sau da dama nasha tabota by mistake uhmmm maza wlh yan iskane.
Ya Omar Sam bai taba nunawa ko a fuska yaji wani abuba.Allah shiryeka Sir da gani nasan maita zaiyi.ita Kadai take zancenta har Omar ya fito daga wanka.

Daure da towel yana tsane jikinsa kamshin sabulun wankansa ya cika mata hanci.tunda Omar ya fito Iklas ta kura masa ido wuri daya take ta kallo a jikinsa,kawai joystick din Omar take karewa kallo ta cikin towel a dole sai ta gano adadin girmanta.
Omar yana kallonta shi kam ya sallamawa Iklas ya kyaleta abin nata yafi karfinsa amma akwai time zaiyi maganin marar kunya.

Hakawai yaji Iklas ta tuntsire da daria a fili tace yau mun shiga uku mu mata.tsaki Omar yaja tare da maka mata harara.janye idonta tayi ta nutsu ta koma kallon kyan diri da skin na Omar,ciwonsa ya fara tashi yajiyo Iklas sama sama tace Allah me baiwa.
Da Sauri ya dakko kayan baccinsa har zaisa yaji an karbe kayan a hannusa yasan Iklas ce,bako damuwa ta fara shafa masa man zaitun na magani.

Mugun sha'awarta ce ta kara taso masa, ga shigar da tayi ta mata kyau ta janye hankalinsa. Har ta gama jikinsa har rawa yake sandar girma ta harba, Iklas kuwa ta samu abin daria sai kare wa joystick kallo takeyi tana murmushi hakan ma a boye takeyi kar ya kamata,Iklas ita kawai abar maza daria take bata,don akwai sanda ta leko daga gidansu taga wani Arne na fitsari a tsaye sai da ta tsaya ta kalle masa sandar girma tsab tana daria.

Har yan ball idan taga zasu wuce sabo da wandonsu ana ganinta suma saita sa musu ido tayi ta sheka daria.
Mikewa tayi da niyyar tafiya ji tayi Omar ya jawota tare da dorata saman bed dinsa,ya hau bed din shima cike da sha'awarta,ido ta zaro tana ina ina.....wlh....uhm...uhm tana yarfe hannu Omar Wanda ya mata rumfa tana tsakiyarsa,..nifa....ba...fa...daria nayiwa abakarba...kawai kawata na tuno.
Kayi hakuri ni indai a gabanka ne nama daina daria gaba daya.ba tare da Omar ya furta komaiba ya fara kokarin cire mata kaya, kuka ta fara da yace abinda kikewa dariar ai zan baki.
Sosai ta saki kuka na rantse da Allah bazan karaba I promise u,ni ban taba gani ba dan Allah ka yafemin,daria ta ba Omar sai da yayi murmushi sannan ya sauketa kasa.

Tambayarta yayi kinyi wanka da sauri tace yes.bed chair ya nuna mata to maza kwanta can,a'a dakin Ummi zanje ni, OK to bari na baki abin da sauri ta koma ta kwanta inda yace.

Hakikanin gaskia Omar baisan me Iklas kewa daria ba,ita ta fallasa kanta da ta kama rantse rantse dama kuma yayi zargin hakan saboda yaga inda idonta ke kallo.
Wasu rantsatsun kayan baccin maza yasa rigar kalar singlet wandon Short ne guntu farare kal,turare ya fesa kala wurin 4.sannan ya kwanta tare da adduoi.
Iklas tuni bacci ya dauketa.yau ikon Allah Omar baiyi ciwo ba har suka tashi lfy,sai mugun mafarkin da yake yawan yi.

Iklas da murna ta fadawa Ummi,kowa yaji dadi.yau kuma Sunday yau saleem zai zo wajen su Iklas. Omar na dakin Mama Iklas ta rude sai shige da fice takeyi a kitchen,Duk abinda takeyi Omar na lura da ita,ya gama Dana mata tarkonsa.







Asmabaffa

ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

90-95

By
Asmabaffa


Iklas sai da tayi girki kala 3 lafiyayyu da kayan sha ta hadawa saleem,Omar fitowa yayi cike da kasaita ya hango Iklas tana waya,dai dai bayanta ya tsaya kamar zai shige jinkinta mika wuya yayi tare da Dora kansa a dokin wuyanta yana kara kunnensa jikin wayar yaji me suke magana akai,
Iklas tana jinsa ta shareshi taci gaba da wayarta duk inda ta sa kafa sai Omar yasa dole yaji da wa takewa me take cewa, Saleem ne ya mata waya cewar yana hanya.

Da gudu ta zille ta shiga dakin Ummi tare da fadawa toilet,wanka da sallar la'asar tayi sannan ta hau shafe shafenta,tasa wani lace red and pink,tasha kyau,kwalli da powder ta shafa sai jambaki shike nan tayi kyau,turare ma iya body spray ta shafa.sabo da tasan yanzu tana da sure,

Takalmi pink,gyale pink Ummi yazo bari na shigo dashi yana waje,to Iklas ki kula kisanfa da auren wani kanki ban son shashanci,haba Ummi ki daina bata bakinki nasan fa me nakeyi.
Tana fita taga Omar a compound lallai Omar yaji sauki yaushe da zai iya zama shi kadai haka,
Shima Omar yasha wani narkakken yadi yayi kyau sai da Iklas ta kalleshi da yawa,shi kuwa Omar ba karamin kyau da girma yaga Iklas tayi ba,sai kallonta yake kamar ya hadiyeta.

Bayan sun gama kalle juna Iklas ta fara tafiya,tunowa Omar yayi fa wajen Saleem zata je,a hankali cike da isa da takama kamar bazai magana ba ya mata alama da hannu tazo.
Zuwa tayi ya Omar gani,kallon tsab yayi mata sannan yace je ki kawo min ruwa ,komawa tayi ta kawo masa,ta juya yace saura ki dauko furata a fridge,kai ya Omar bako fa mukayi,haka tana kunkuni taje ta kawo masa, da kyar ya kyaketa ta fita domin shigo da Saleem Wanda ya gaji da tsaiwa a waje tunda taxi ta saukeshi yake jiran Iklas.

Saleem ya dau wankansa na talakawa ba laifi,Omar bakin ciki kamar ya mutu ganin Iklas ta jera tare da wani,da kyar ya samu ya danne zuciyarsa,a mutunce Saleem suka gaisa da Omar,Iklas cikin palon Mama ta kaishi,sun gaisa da Ummi harda hira haka Mama ma,sun yaba da hankalin Saleem.
Dan haka Mama ta tambayeshi matakin da ya tsaya a schl,yace N.C.E gareshi tace in ya samu time yazo zata bashi manager a gidan gonarta,sai ya samu kudin cin abinci sannan ya biyawa kansa schl.sai godiya da murna yakeyi.

Bayan ya danci girkin Iklas wajen gidan suka fita shi da Ita suna ta hira,Omar tuni ya koma room dinsa jikinsa yayi sanyi lekensu kawai ya fara yi ta window bazai iya jurewa ba,ruwan da Iklas ta kawo masa ya daga ta saitin kan Iklas ta window ya shararo musu ruwan,kafin su matsa juice din sa ya dauka ya watso musu,kafin su kalli wajen da aka jikasu Omar ya Dade da barin wajen,sun rasa waye ya musu haka,duk jikinsu ya baci Saleem yace maybe Wanda ya zuba bai San muna wajen ba,
Hira sukaci gaba Omar sai zirga zirga yakeyi ya rasa me zai musu ma.palon Mama ya koma ya kama yin abu irin na ciwonsa wai ciwonsa ya tashi,da gudu Suhaila ta fadawa Iklas ba shiri Iklas ta sallami Saleem ya tafi gida cike da jin haushi baiyi wata hira da Iklas ba kuma yau ya shirya fada mata sakon zuciyarsa.

Iklas na shiga palon Omar ya mike yana wani narkewa ya janye Iklas zuwa part dinsa, suma su Suhaila sunyi Mama ki kwarai ganin Omar na numfarfashi amma lokaci daya ya mike garau.
Mama basu San me akeyi ba suna daki.Iklas hankali tashe ta bishi har room dinsa sai wani lallabashi takeyi,a sofa suka zauna sai nishin karya yake tare da cewa mutuwa zanyi,da kyar idan zan tashi,wasiyata......sai nushi....a firgice Iklas tace dan Allah ka daina fadin haka Sir,no ni nasan me nakeji Iklas, fashewa da kuka Iklas tayi,ya ci gaba ban San dalili... ba.... sai.... naji bana son ganin.... mace da namiji.... tare.... ko wace Dana gansu sai ciwona ya dawo sabo.
Yaya to ai kuma gani ni da kai,wasu nace miki ba mu ba,Ashe bakya kauna na warke ban sani ba..... gashi nan kin kula wani ciwona ya tashi,tausayinsa Iklas taji to indai hakane bazan kara kula kowa ba,yawwa ko kefe idan kuma ba kyaso na rayu to....haba ya Omar ka daina fadin haka ai na daina ma baza ka mutu ba da izinin Allah.
Har Saleem bazan kara tsayawa dashi ba sai dai in dasu Ummi a wajen. dadi Omar yaji yayiwa Iklas wayo wani sanyi yaji a ransa.Ashe kinaso kiyi aikin Gomnati? zabura Iklas tayi tare da yake hakoranta masu matukar kyau da haske Allah Sir da gaske zanyi aikin Gomnati?kai ya daga mata yasan yanda take kaunar aikin Gomnati da wannan zai mata wayo.shi kam sai yanzu ya tuno ma Gomnati ce fa da kanta.

Ci gaba yayi da indai kin min biyayya duk

2 Comments On MA'AIKACIYAR GWAMNATI
avatar
abubakar-adam

10 months ago

Reply

Perfect

avatar
abubakar-adam

10 months ago

Reply

Perfect

Please Login or Register in order to submit comment