Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sadiya ta zuba mata sannan a wulakance suka dauketa zuwa hospital daga nan suka maidata kauyensu.

Yau kwanan iklas 1 tana period yau Sam kasa zuwa schl tayi,omar kuwa wani new sim card yasa ya kira yaronsa hade da bashi umarnin kawo pad ,iklas na zaune taga an shigo da pad da yawan gaske,kamar Zara bude shago.

Godiya tayiwa omar,ki daina godemin fatana ki wanke mana toilet sosai.Baki ta cuno cike da shagwaba haba sir kasan fa kai yaya nane sai kana bani kunya,ai kasan dama ni ke gyara gidan ko,?

Kafe iklas da kallo omar yayi,in tana shagwabar nan birgeshi takeyi,shi a kanta ya San shagwaba na yiwa mata kyau sosai,lalacewa yayi wajen kallon iklas na zuba masa shagwaba.da kyar ya jawo nutsuwarsa ya mannata jikinsa tare da cewa hope kin iya wankan musuluncin dai ko?daria iklas tayi ya omar bafa a asarar kudin tara in fadama babu kalar da ban sani ba ehe,

Lumshe ido yayi wani nishadi da dadi ya tashi a sararin samaniya a dirga a zuciarsa tsabar iya fadan OMAR da iklas tayi,a dunia yana son yaji iklas tace masa omar ji yake kamar sunansa yafi na kowa dadi a dunia,

Ya omar kazo yau da yamma muje yawo kaga kai baka fita,kai kawai ya daga mata dan ta kara kashe masa jiki,ta tsinka masa jijiyoyin jikinsa jin ya omar again daga bakin iklas,


Karfe biyar iklas ta fito sanye da wata arniyar super atamfa dinkin riga me coler da dogon hannu Riga da skert,bata daura dankwaki ba gyale ta yada,ta sha kyau pose ta dauka pink kalar atamfar takalmi ma same color,

Numfashinta ne ya dauke ganin omar sanye da 3quater arsh da riga T-shirt milk color sai rubutu da pink ansa defence da babban baki,yayi kyau sosai ummi sukayiwa sallama,omar na fargaba da tsoron fita sabo da lafiyarsa.

Iklas kuwa ta nace sai ta kaishi yawo,sun fita iklas ta ga wata sabuwar mota dal arsh color,mota ta alfarma ta fita kunya ta nunawa a gari,zagawa Omar yayi ya shige mazaunin driver,itama ta shiga gaba,suka fasa gari,ko Nisa basuyi ba ciwon omar ya fara motsawa,iklas ma ta kula da hakan,to shi wannan meke damunsa haka cewar iklas a ranta,

Ciwon karfi yakeyi sosai har driving yana nema ya gagareshi,iklas ta tausaya masa ganin yanda ya fita a hayyacinsa lokaci daya,hannunsa daya ta kamo ta rike gam cikin nata,sabo da haka ya gangare kasa da hannu daya yake driving har yayi parking gefen titi,

Duk ac dake motar omar gumine ke keto masa,iklas du ta tsorata ta rude tausayin Omar takeji sosai,hannunsa ta kara damkewa tare da goge masa gumi da handkerchief tana tofa masa addua,

A hankali yaji sauki amma da zarar iklas ta zare hannunta cikin nasa sai ya fara jin ciwon zai dawo,kawai sai yaja hannunta har kan sitiyarin ya hade da nasa ya ci gaba da driving,har sukaje city wani tsadajjen wurin shakatawa ya kaisu,na manyan yara kowa ka gani wajen to karshene wajen rike doller.

Iklas yar kallo ta zama,hannunta cikin nasa ko ina birge mutane sukeyi sai kallonsu akeyi,da yawa sun zata ango da amarya ne,iklas har wani gadara da yanga takeyi ita a dole babbar yarinya,omar na kallonta ta gefen ido daria yakeyi a ransa kawai,

Dan zagawa yayi da ita,maza kowa kallon iklas yakeyi sabo da baiwar kyanta,harma da wasu matan amma su omar yafi yi musu kyau,baya son ciwonsa ya tashi that's y kawai ya musu take away,wannan karon iklas hannunta ta gwiwar hannun omar ya sakaloshi, istigifari yayi wai a bisa lalura ya rike hannunta,

Sunzo jikin mota zasu shiga kenan motar sultan Frnd din omar ta danno kai,omar na Jan motarsa sultan shi kuma ya parker a wurin,tabbas sultan yaga omar amma gani yakeyi kamar shi kamar ba shi ba,kai tabbas wancan omar ne cewar sultan,amma yayi mamaki da yaga kamar yarinyar nan da taje gidan su Omar takai sakon takarda,kai sultan kansa ya kulle,to omar da mace?aure yayi?to meke faruwa da Omar haka,amma kuma kamar me tallan kwai ce tare da omar.duk sultan ke zancen zuci.

Yasan idan ma yabi bayansu yanzu sun bace masa,da ganin kalar motar ma da tsadarta gata sabuwa yasan sai omar,shine keyin too match da kayansa da mota most of d time,kuma shi ke yawan order new cars don kawai ya hau yaji dadinsa.

Bangaren Omar kuwa yaga shigowar sultan,yaso ya masa magana amma sai yaji ya kasa,bazai iya ba,katon shopping mall ya tsaya sukayi siyayya da yawa stl hannunsu na damke da juna,nan ma wani cikin yaran sadiya yan daba yaga omar,amma kwokwanto yakeyi kamar yanda sultan yayi,

Suna karasawa gida sun kwashe kayan da suka siyo tas,Omar ya kira yaronsa yace ka dauke motar mutumin ya fasa amfani da ita.bazai siya ba,yaro shi ya zata Omar business sukeyi.bai San oganne da kansa ba.ya musu haka ne dan karma su San inda yake.kowanne ya Kira tsarashi yakeyi.

Omar da iklas mamaki kowannensu keyi tare da tunani to me yasa idan Omar na gidansu su iklas baya ciwon,me yasa da suka fita ciwonsa ya tashi amma tana rikeshi ya warke,idan ya saki hannunta sai ciwo ya dawo,tofa readers koma mene zamu ji nan gaba.

Omar kullum yana yin mugayen mafarkansa,washe gari iklas ta dawo daga schl suka shigo gidan tare da Frnd dinta dan unguwansu wato saleem,zai kai 32yrs kusan made din Omar ne,

Ummi ya gaida tare da mikawa omar hannu,da kyar Omar ya mika masa hannun,tsakar gida suka koma shi da iklas suna ta hira suna daria,ummi ta shige room,bakin ciki omar keji a ransa ganin saleem da iklas tare,

Kujerar dake jikin window ya dawo yana jin me suke cewar dama burinsa kenan,ruwan jarka Omar ya dauka ya bude,ta window ya zuro robar dama iklas da saleem suna saitin window,kwara musu ruwan omar yayi a Kansu,.






Asmabaffa

Godiya dubu readers.
[27/03, 17:48] Hassan Atk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

40-45

By
Asmabaffa



Ruwa kawai iklas da saleem sukaji a jikinsu,kara shararo ruwan yayi tas ya juyeshi jikin saleem da iklas,da sauri suka mike tsaye,omar na jikin window yana zabga harara,ya omar ka jikamu fa da ruwa cewar iklas,so what ni nace ku zauna jikin window,nazo zan zubar da ruwa ni na kula da akwai mutane nan?

Amma ya omar jibafa yanda ka jika saleem,sorry saleem hannu ta kai zata karkadewa saleem rigarsa,wata uwar tsawa omar ya bugawa iklas...wlh wlh if u dear touch that guy yau jikinki sai ya fada miki,saleem kallon omar kawai yakeyi yana tunanin to me yayiwa wannan mutumin? Daga zuwa wajen iklas.

Kallonsa iklas tayi haba ya omar me nayi ma kana daga cikin room kawai ka leko ta window sai fada kake mana,ok bakiyi komai bama ko...ki taba jikinsa ki gani ke na rantse da Allah yau Indai hannunki yakai jikin wannan sai na zaneki tas a gidan nan.

Malam pls ka tafiyarka ka daina zuwa wajenta an mata miji a kauye,daga yau ka kiyaye...ni wlh ba wani miji da akamin cewar iklas,omar ne ya fito waje ransa bakikirin,yana fitowa iklas ta fada toilet da gudu ta banko kofar,

Saleem takaici ya kamashi ya bar gidan yayi ficewarsa,omar kuwa jikin toilet yaje gwara ma ki fito kafi na bude toilet din ta karfi na kamoki,daria iklas tayi naki na bude kuma ka balla kofar mu gani,abinda kai baka da karfi,wani karfine da kai,amma kika gudu me yasa baki tsaya ba,ai ni wanka zanyi shi yasa kaga na shiga toilet.

Murmushi Omar yayi,na kyaleki yarinya tunda matsoraciya ce ke,ka jira na fito ka gani mana...cewar iklas,sai da ta tabbatar omar ya shiga daki ta fito sadaf sadaf,suhaila ce tace anty kiyi min gugar kayana,ke baki isa ba bani da lokaci unguwa zanje yau.

Kije ummi ta miki,shiryawa iklas tayi cikin tsadajjiyar shaddarta para kal da dinki light blue kalar zaren,takalmi da jaka da mayafi du light blue,fitowa tayi omar ta gani a Palo wajensa taje ya omar zanje unguwa anjima kadan zan dawo,

Ke kullum wai in baki fita ba Sam bakya jin dadine?no sir kawai dai wannan fitar me muhimmanci ce,to muje tare mana cewar omar,ni bazani da kai ba ciwonka ya tashi haka kawai,rannan hannuna har zafi ya min tsabar rikewar da ka masa,

Sallama tayiwa omar tayi tafiyarta,direct gidan su omar naga ta tsayar da me taxi,masu gadi suna ganinta suka su bude mata ta shige,tana shiga sukayi ido 4 da Aisha,ai Aisha tana tabbatarwa ganinta ta koma part dinsu,yau ta fasa fita sai tayiwa yatinyar nan dukan kawo wuka,

Tana shiga ta sanarwa sauran sis nata,shegiya Allah ya kawota zata ci ubanta yau wlh,sadiya kuwa wata sandar karfe ta dakko.tana Ashe yau za ayi daukan rai,kwanan wata zai kare,naja jeki waje ki jira tana fitowa ki mana flashing.

Ita kuwa iklas part din maman omar ta wuce,hannu bibiyu suka tarbeta,yau iklas an sami waje har kitchen ita ta taya mama girki,wajen 5:30 tayiwa mama sallama ta fito domin tafiya gida,

Tazo tsakiyar gidan su sadiya suka zagayeta kafin kace me sun rufe ta da duka,sai da suka farfasawa iklas jiki,da kyar mama da masu gadi suka kwaceta,

Hhhh Allah sarki iklas da kyar take motsi ko ina jini,fuskarta ce kawai take normal,hospital mama tasa driver ya kaisu ita da iklas,dressing akayi mata,mama tayi tayi iklas ta bari su kaita gida amma taki yarda,dole suka kyaleta ta shiga taxi ta tafi gida,omar da ummi hankalinsu ya tashi ganin ba iklas ba labarinta,har dare shuru,Omar sai tsaki yakeyi ya kasa zaune ya kasa tsaye,sai duba agogo yakeyi,

Shaddar iklas ta baci da jinin dukan su sadiya,sannan gashi period din da takeyi shima garin fadan pad ta goce,duk ya bata mata jiki,tana dingishi hade da nishi ta rarrafa ta shiga gidan,su ummi ta gani tsaye a tsakar gida hankalinsu tashe,da gani ita suke jira,tana shiga da sauri suka tareta,

Rushewa da kuka iklas tayi,tana ta kuka me ban tausayi,jikinta suka gani duk rauni,omar ne ya riko hannunta,accident kikayi? cewar omar ,cikin sheshekar kuka iklas tace wash...was...wasu suka dakeni,sai ta kara sakin kuka,

Su waye?wanne yan iskanne suka Dakar min jikata marainiyar Allah ummi ke fadi,wasu ne ummi,idan kin sansu ki fada min cewar omar,ni ban sansu ba kawai sunce na zagesu wai,omar kuwa Sam bai yarda da zancen iklas ba.ummi kuwa yarda tayi tace Allah zai saka miki,muje kiyi wanka ki gasa jikin.

Ruwan zafi ummi ta hada mata kana tayi wanka,tana daga cikin toilet ta kwalawa ummi kira,ummi kuwa bata kusa sai omar dake zaune a kujera,me kike so a miki ummi sallah takeyi,pls sir wata Leda zaka dauko min a room kan bed dina,dakin su iklas ya shiga ya dauko ledar wacce ba komai bane ciki face pant da pad,tsaki ya ja karbi kayan kazantarki malama,hannu ta miko ta window ta karba,omar kam hannun nata ya bi da kallo,yanda suke masu matukar kyau ga ruwa jiki sunyi fresh fari tas, shirya kanta tayi, tea omar ya hada mata ta sha,duk abinda sukeyi ummi tana sallah tana kallonsu tare da jin dadi, suhaila harda kukan tausayin iklas.

Gomnati sai kuka takeyi tana yarfe hannu abin nata harda shagwaba ya koma,omar kuwa tausayi ta bashi har wani lallabata yakeyi duk zatonta zafin ciwo ne,kukan nata jinsa yake har ransa.

Haka sukayi fama da iklas har ta warke,kamar kullum iklas ta fito daga schl a gefen titi wata mota dalleliya ta parker a saitin iklas,sauke glass kasa akaayi,ba kowa bane face sultan,yazo wucewa ya hango wata kamar ummi da taje wajen maman omar,wacce ya gani da omar yana kokwanto,

Gaisawa sukayi ummi kike ko?yea ya gida ya aiki?cewar iklas dan ta San sultan,ahmmmm...kamar ke na gani da omar rannan a garden kingdom ko?da mamaki iklas ta nuna Sam bata San waye Omar ba,ta manta ma da wani omar,wanne omarfa?frnd dina mana Wanda ya baki envelop ki kaiwa mamansa.ohhhhh na tuna dama sunansa omar?ai na manta ma,pls ya koma gida kuwa,

Au dama bake na gani tare dashi ba,gaskia ba ni bace,maybe wata ce,ok pls kin taba yin sana'ar talla?cewar sultan.mene kuma talla ban gane ba.it's OK bari naje na gode fa,sultan yaja motarsa yayi gaba abinsa.

Da sauri iklas ta sha kwana,ko nisa batayi ba wasu Igbo suka parker sukayi mata lift,har taki shiga motar saboda yan iska ne a unguwar,sabo da kar sultan ya ganota ta shige motar ba tare da tunanin komai ba,

Joseph ne ya dawo baya kusa da iklas India shi kuma nmandi ya ci gaba da tukinsa,ga hanya kusa amma sai suka canja suka dauki ta nesa wacce za a Dade ba a zo layin su iklas ba,

Sai shawagi sukeyi da ita a mota,Joseph ne ya matsa jikin iklas,ta kara matsawa,har suka kai karshen bangon murfin motar,

Iklas sai hakuri take basu tana rokon su sauketa amma ina,tuni Joseph ya fara shafa cinyoyinta,kuka ta saka musu,amma sai daria sukeyi mata tare da kara kwakwumeta,manne jikinta tayi waje daya yayinda shi kuma ya sutale hijab dinta,wow this girl fine woooo,omoh see her hair like arabs girl,

Kirjinta ya fara kokarin shafawa ta tsala ihu, make bakinta yayi,a take ya fashe yana jini har hancinta,tafiya sukeyi har sukazo gidan su iklas basu gane cewar gidansu bane,omar ya leko kofar gida yana jiran suhaila ta kawo masa recharge card daya aiketa ta siyo masa,

Iklas ya hango a bayan motar wasu kuma mutumin taba jikinta yakeyi,iklas kuwa tana ganin gidansu ta kwala ihu tana Neman agaji, su Joseph tabbas sun ga alama zata tona musu asiri,gashi ta makale jikinta ko kirjinta ya kasa latsowa,haushi yaji ya fesa mata mari ya taka birki kuuuuu,ta fito kuwa da gudu suka ja motarsu da gudun tsiya.

Suka bar unguwar,Omar kam ya gama tsorata da lamarin iklas, ya rasa ma tantancewa me yakeji a zuciarsa, wanne kalar bakin ciki ne yake ji ya kasa ganewa.

Hannun suhaila ya ja sukayi cikin gida, kallo daya yayiwa iklas ya dauke kai,baki duk jini da hanci,a waje ta tsaya ta goge jinin sabo da ummi,

Wanka tayi da sallah taci abinci,sai istigifari iklas keyi a ranta, duk da tasan bata da laifi amma ai ganganci tayi tasan yan iskane amma ta shiga motarsu,

Ba abinda ya dameta irin kallon da Omar ya mata,haka kawai taji ta shiga damua,gashi ko magana yaki yi bare ta samu damar wanke kanta,yanzu zai mata kallon yar iska.kunyarsa take ji sosai,duk tayi wani sukuku da ita,ummi har tambayarta tayi ko lfy?amma tace normal take gajia ce.

9:30pm washe gari kowa ya tashi banda Omar, yau ba schl Saturday, ummi ce ta umarci iklas da taje ta Kira Omar suyi break,kwance ta sameshi sai marfakansa yakeyi, tashinsa ta fara yi.a tsorace ya tashi zaune daga shi sai boxers, tsoro ne ya kamashi sosai kan mafarkin da yayi,bai San sanda a rungume iklas ba,yana shakar kamshin wuyanta tare da sakin ajiyar zucia



Asmabaffa
[27/03, 17:48] Hassan Atk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

45-50

By
Asmabaffa



Na gode masoyana Allah karo karfin ido.



Kiciniyar kwace kanta takeyi amma ya mata rungumar karfi,da kyar ta fara zamewa cikin magagin bacci omar yace 2nmt pls.....tsayawa tayi cak tare da lafewa ita dama iklas ta Dade da son ta jita a kirjin omar,bata San me yasa ba kuma ta rasa dalilin da yasa jikin omar ke birgeta.sun dauki minti biyar haka omar ya dawo normal,jinsa yayi manne jikin mace ai bai San sanda fancakalar da iklas daga jikinsa ba,sai da ta fado kasa daga bed din.

Masifa ya fara IKLAS karo na farko da Omar ya kira sunan iklas,wani zirrrrrrrr taji lokacin da omar ya furta iklas,kallonsa tayi tare da tsilli tsilli da ido tana Sosa gashi,me ya kawoki dakin nan,mikewa yayi idonsa jajir ya damki kunnenta,kara ta saki kadan,ba kyajin magana ko iklas,am I ur mate? Ke bakya banbance tsakanin maza da mata,bayan yan iskan da suka saukeki dazu kinga bance miki komai ba shine zaki sauke iskancinki kaina ko?

Ina ina ta fara ....to wai...wai ba kaine ka janyoni jikinka ba kuma ka rokeni kan na tsaya,har hawaye kayi fa wai kar na tafi,kuma kace kai dadinka kake ji,kukan karya ta fara yi,kuma ni taimaka maka nayi,daga taimak....shut up tashi ki fita mayyata kar ki kuma zuwa min room kije kiyi raping dina,ki samin kazamin jikinki duk dazu wasu gardawa sun gama goga jikinsu a naki.

Kuka ta saka masa harda rufe ido da hannu,dama nasan yar iska zaka na kallona,na rantse da Allah billahillazi la'ila ha illahuwa Allah daya ragemin hanya sukayi shine suke kokarin tabani sir.

Kaga Allah kallo wurin da suka dinga marina akan naki yarda ai kaga jinin ma ko,ni ban wani gani ba ke dai kawai kin lalace jikin maza kike so,in auren kike so ayi miki mana,har kayan daki zan miki, cewar omar

Iklas tsalle tayi ta make kafada Allah kiyaye na haihu na ragwaje,ai nasan ma yanda kake ji dani baza ka bari amin auren wuri ba,tunda kai kaka tana jin maganarka.

Igbo za a aura miki tunda su kike biyewa suna lagudaki.hawaye ta fara, wlh sir na fada ma ni ba yar iska bace,Omar yasan gaskia kawai maganinta yake son yi sabo da ta daina ganganci.

rike haba iklas tayi kamar gaske tace ohh sir wai kai wanne mai kake shafawa ne?mene kuma?hmmm jikinka Allah ya Omar kamar flour baka ji ba.daria ce ta kwacewa omar,ga iklas tayi wani zaman cin tuwo a kasa, banza omar ya mata.

Minti 1 iklas tace yaya?kinga get out,kofa ya bude mata tare da kamo hannunta ya tankada keyarta waje ya rufe kofar,sai da ta kusa faduwa kasa,tunawa tayi bata fadi kiran da ummi tace tawa Omar ba,jikin kofar ta Dora kanta ya Omar kazo inji ummi muyi break,tsaki yaja ke kinfa isheni kije zanzo wanka zanyi...ok.

Kamshin omar da suka ji shi ya basu tabbacin fitowarsa wani danyen yadi ne sanye jikinsa light blue,har kasa ya gaida ummi,umaru wannan kwalliya haka kamar me zuwa zance?amshe zancen iklas tayi haba ummi ke ba dama mutum yayi kwalliya sai kice zance zai je to shi ya omar wa yake da ita,ina yake fita Da har zaiyi wata budurwa, to uwar shishigi ki bari umaru ya bani amsata mana,

Murmushi omar ya saki ummi bikon matata zanje,tayi yaji sabo da rashin ganina da batayi.sallallami ummi ta fara yanzu umaru kana da mata amma baka fada min ba,ayi hakuri ummi,yanzu ma so nake iklas ta rakani can.dole kaje ai baka kyauta ba umaru.

Da karfi iklas tace bazanje ba kaje kai kadai ina ruwana da wata matarka,ni nasa ka aureta,zamana takeyi,kai ta shafa can kaje da wata badai ni ba.cike da masifa ta mike zata shige daki,omar kuwa daria kawai yakeyi kadan kadan wannan masifa ta iklas da takeyi,riko hannunta yayi tunda bazaki ba suhaila jeki shirya ki rakani,

Tana zaune suhaila ta fito sanye cikin English wears Riga da wando masu kyau,ummi ta gyara mata gashinta,wuce iklas tazo yi iklas kuwa kafa tasa wa suhaila ta shatile kafarta ta fadi kasa,kuka ta fashe dashi me karfin gaske,rufe iklas da masifa ummi tayi.

Omar da ummi ne suka lallasheta da kyar,gani tayi da gaske tafiya zasuyi,fuuuu tazo ta wuce su tare da bangaje omar,mota ta gani rantsatsiya a waje, omar na danna remote ya bude iklas ta balle murfin gaban motar ta shige,

Shi kuwa omar murna yayi a ransa dama haka yakeso,a baya ya zaunar da suhaila shima ya shiga.yasan idan ba iklas tafiyar baza ta yiwu ba saboda definitely ciwonsa zai tashi,amma idan iklas na kusa ya riketa sai ya warke

Tafiya sukeyi sun fara shiga abuja city iklas kawai kumburi takeyi kamar zata ce wayyo na shiga uku na lalace

Tunda suka fara tafiya omar ciwonsa ya fara tashi kawai zufa yakeyi ya rasa inda zai sa kansa, ba shiri ya sadada hannunsa ya riko hannun iklas,da karfi cike da masifa ta fisge hannunta,naga Wanda zaka rike ai yau.

Omar ta kansa yakeyi kawai shi yasan me yake ji,suhaila ce dake bayan mota ta mikowa omar hannu gashi ya omar ni ka rike nawa hannun ka kyale na anty.iklas juyawa tayi a fusace ta zubawa suhaila rankwashi ta make hannun wai ni sa'arki ce,ina ruwanki da shi,ba a son hannun naki to.

Omar na nishi da kyar yake tukin motar kallon iklas yayi idonsa yayi jajir,ki daina dukanta ke iskancin da kikeyi a garin nan wa ke dukanki,kunya iklas taji tace to a kyale maganar kana fama da kanka,hannunta ta miko masa ungo gashi ka rike na taimakamaka.yatsunsu ya sarkafe wuri daya yaci gaba da driving,5mnt omar ya dawo garau dashi,yayinda iklas da shi suka shiga wani hali na shauki kowannensu ji yake jininsa na masa wani yammmm.....yammmm.

Wani katafaren barbing saloon Wanda yake hade maza da mata omar ya parker,mata maza birjik ciki ana gyaran gashi,matan manya da yaran manya,da manyan masu kudi sune a cikinsa,turawa ne masu aiki a ciki.gurin ya hadu kamar a turai,

Fitowa yayi sakale da hannun iklas kamar chewgum,tafiya sukeyi cike da izza,iklas ta raina kanta kyaune kadai ya ceceta,dan duk tafi matan ciki kyau nesa ba kusa ba,sai kallonsu akeyi,suhaila na kusa da ya omar.bangaren mata ya fara kaisu yana zaune,iklas ta karbe daya hannun ta mika masa daya hannun gashi rike wannan dayan ya samu ya huta.

Kujera aka ba omar yana zaune gaban iklas hannunsa rike da nata haka akayi mata gyaran gashi aka gama,suhaila ma an mata,sunyi matukar yin kyau,su Kansu masu saloon din sunyi jinjina.

Wurin maza suka koma wannan karan iklas aka bawa kujera ta zauna gaban omar rike da hannunsa,masifu kawai take ji a jikinta na kamar sha'awa amma ta rasa gane mene take ji.

Omar kuwa a cikin jininsa yake jin bala'in sha'awar iklas wacce bai taba ji ba,amma haka ya daure ya cije.tunda aka fara gyarawa Omar suma iklas ta fara turbine fuska,idan ta kalli Omar sai ta tabe baki,wlh ka cuci kanka

2 Comments On MA'AIKACIYAR GWAMNATI
avatar
abubakar-adam

10 months ago

Reply

Perfect

avatar
abubakar-adam

10 months ago

Reply

Perfect

Please Login or Register in order to submit comment