Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta tafi kasar ghana akwai wani aiki za suyi..ok kawai yace ya koma gidan mamansa,abinda Omar bai sani ba sahar ta kara lalacewa sai matan manyan alhazawa take kulawa Wanda suke da naira,wata kawarta hajiya talatu matar wani gomnace ita ta bawa sahar shawarar tunda kullum a hanya take ga mijinta ba wani shiri sukeyi ba kuma sahar akwai tsananin sha'awa kawai tunda tana da kudi a hannu ga maza nan samari yara sai ta zaba tunda yanzu matasa sun zama kwadayayyu kudi suke nema ta ko wacce hanya komai kudi,to ta mori dukiyarta ta samu wasu suna biya mata bukatarta tana biyan kudi.amma ta daina zubar da ajinta wurin omar mijinta tunda shi baya taba nemanta itama ta daina kai kanta.wa'iyazu billah mai makon muyi kokari mu gyara halinmu sai mu kara dilmiyewa mu jefa kanmu halaka wacce har ka mutu kana da na sani.Allah shiryamu gaba daya.dan yanzu wannan ya zama ruwan dare wurin wasu matayen musamman masu naira

Mama na room dinta tana shafa magani a kafafunta da suke mata ciwo omar ya shigo da sallama,da fara'a ta amsa masa babanmu ina ka shiga ne haka ban ganka ba,maganin ya karba ya karasa shafa mata,ina gida mama ga office ba sauki,omar kenan na dauka ma ko suruka ta biyu ka samo min,murmushi yayi mama aure tun yanzu zan kara aure,ina zan kai matan dayar ma da za a yagemin ita so nakeyi,daria mama tayi omar sai hakuri dan kawai ba auren so aka maka bane kuma matar taka ba ayi dace ba shi yasa ka fadi haka,

Mama kinji yanzu na dawo gida wai ta bawa yan aiki sako a fada min ta wuce Ghana,duk yawon da takeyi kasar nan bai isheta ba mama.mama ma ranta ya baci da jin abinda sahar tayi,ka bari zanwa baffanku magana a waya sai aje gidansu a sanar da iyayenta tunda ta Gagari kowa,ni ma zan kirata a waya,mama ki kyaleta pls kar tazo tana miki rashin kunya kin San bazan kyale ba.ya isa omar dole a fada mata gaskia.to mama ba matsala.ledar da iklas ta bashi ya mikawa mama,ledar kaka ummi ma ya mika mata gashi mama sunce a baki kuma suna gaisheki,murmushi tayi na gode Allah saka,amma banana wannan su waye suka bani bazan bude ba sai ka fada min,ohh mama wannan red din na kaka ummi ne wannan kuma na jikarta iklas,

Murmushi mama tayi tana jin dadi tana fatan abinda tayi tunani ya zama gaske,a fili tace ban ganesu ba ai...uhm..uhm yana Sosa kai yace aikine ya hadamu gidan gona.kyaleshi mama tayi, tace angode kaga mutanen kirki bari mu gani mene ciki.

Ledar iklas ta fara budewa wata katuwar farar roba ce mai murfi shake take tam da dambun naman kaza iklas yinsa tayi musamman sabo da suhaila na sonsa ganin omar yasa ta canja idea ta juye masa duka me uban yawa ta bawa mamansa.mama taji dadi sosai,ta bude ledar ummi kayan kamshi ne da sauran abubuwan miya busassu.mama sai murna takeyi omar har mamakin murnar mama yayii,babana ya kamata ka kawo min su na gansu ko ka kaini gidansu,ba yanzu ba mama to allah kaimu koma yaushene.kasan bana cin maiko sabo da ulcer ta,kadan zan iba ni da su abdullah.dauki wannan kaje dakinka dashi..da kyar ya karbi na robar wai a dole bayacin girkin yara,amma ya dauke ya wuce room dashi yana bata rai da muzurai.

Sadiya na hango sai masifa take zazzagawa tana dura ashar a compound din gidan,duk wani ma'aikata sunyi luf suna jinta,suleim na hango da uniform jikinta tsugune a gaban sadiya tana faman bata hakuri,anty sadiya kiyi hakuri ban San takadar tana da amfani ba shi yasa Dana gani na yaga na zuba a dustbin,

Wani lafiyayyan mari sadiya ta kwadawa suleim Allah sarki yar yarinya sai ga shatin hannun sadiya radede a fuskarta,kuka ta tsala hade da dafe kumatunta,gashinta sadiya ta ja da karfi dan uwarki baki San darajar takarda ba,gadon tsiya ba laifinki bane uwarku ba ilmi ne da ita ba jahila ce shi yasa Baku San darajar takarda ba,tsabar masifar da sadiya keyi ko kula da motar omar wacce ta shigo har ya parker bata sani ba,hankada suleim tayi ta tintsira ta bige kanta da bakinta,wani gigitaccen kuka ta fasa,omar Wanda yana kallon abinda ke faruwa ransa ya baci,idonsa yayi jajir,zuciya ta tashi,karasowa yayi wajen ya ware hannu ya dinga zubawa sadiya mari,tun tana tsaye sai da takai kasa,belt din wandonsa ya zare ya fara zabgarta gashi ya riketa ram sai daya zaneta tas jikinta duk ya fashe,a hakan ma dan mama ta fito ta rikeshi ne,duk yan gidan suna wurin suna kallo,kafin kace me su Aisha naja sun kama zage zage suma,sannan suka kira baffa da ummansu dake Russia suka fadi karya da gaskia.

Nanfa hajiya rahina ta haukacewa baffan su omar,wlh bazan yarda ko a dauki mataki ko na dauka da kaina,an Dade ana zalinta ni da yarana Sam bazan yarda wlh,akan haka sai dai in ka sakeni amma billahillazi bazan yarda ya kashe min yara ba.tsawa baffa ya daka mata ki saurara min shashashar banza,duka kannensa ne yana da damar hukuntasu,nasan dole omar yana da dalilinsa me karfi,yaran naki bansan halinsu bane an fada miki, marasa tarbiya omar ne wakili na yana da daman yanke komai a gidana.kuma wlh tun kafin na koma ki fada musu dukkansu su fito da miji,na gaji da zubar min da mutunci da sukeyi a unguwa..... Wai wai ai rahina kururuwa ta sa da gunjin kuka,baffa kuwa gidan ya bari.


Asmahbaffa na godiya gareku masoya readers,masu commenting idan nayi posting kunfi kowa birgeni, domin kuna bani kwarin gwiwar typing, na tabbatar kuna jin dadinsa.
[17/03, 21:45] Hadiza Sani Fbk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

10-15

By
Asmabaffa.



Pls readers a dinga kula ana amfani da sakon da muke isarwa me kyau,marar kyau ayi watsi dasu, bukatata kenan,kuskuren da mukayi Allah yafe mana kuma readers ayi mana afwa.Allah tsarkake mana zucuyoyinmu,a dinga rula sakonni nake isarwa ko wanne page lol na gode muku yan readers dina ina ji daku.kunyi male male araina.

Tunda baffa ya fita taki daina kuka sosai take sheka kuka an Zane first daughter dinta me irin halinta sadiya,sai da ta koshi da kuka daga bisani ta jawo wayarta,ta kira haj bilki babbar kawarta tas ta kwashe zance ta fada mata,lallai yaron nan kwai tsinane tambadadde cewar haj bilki,rahina tace shi yasa na fada miki kije min wurin babban malaminki na kasar Mali ayita ta kare,na gaji da tsinannun mutanen nan,akan wannan zan iya dawowa Nigeria muje tare bilki ki rakani,duk wanda na sani nawa malaman ba kudin da ban kasheba abu shuru,nasan naki manyan shegu ne,daga bangaren haj.bilki baki ta tabe daga bisani taji dadi a ranta tana adduar insha'allah bazaiyi aiki ba,yar iska wai ke mijinki me kudi har yanga kike mana kin fimu kudi,ga yaranki masu aikin gomnati,ai sai na miki sanadiyar barin gidan alhaji mohd wlh,hauka nake na yarda ki samu daula ke kadai,Baki San yanda nake miki bakin cikin auren alhaji mohd ba,dan yafi mijina kudi...

Haj rahinace ta katsewa bilki mugun tunanin dake ranta tana ta hello....hello....inajinki network ne wlh rahina,kina jina ki kwantar da hankalinki ni danake babbar kawarki ai dole zanje kasar Mali ko dan ke,ki bar komai hannuna,ammafa sai kin turo isassun kudi,babu matsala wannan cewar rahina,kuma dole sai mun haada da tuggunmu na mata.kin san yanzu sunfi tsafi aiki wajen maza,wasu maganganu haj bilki ta tsarawa haj rahina wanda koni banji me suke cewa ba readers.

Suna katse wayar haj rahina tace shegiya haj bilki tasan takan duniya....banza marar wayo yar matsiyata kina taimakamin na samu abinda nake buri ko kawa nafi karfin nayi dake,jahilar banza yaushe ma inba dole ba zan tsaya ko kusa dani ki raba,iyakarki primary schl.nan umma rahina ta kwashe da daria,a karshe tace har a bada bilki sai dai ki zama baiwata ba kawa ba.haj bilki kuwa tsaki taja tace shashasha naci banza,kudinki zan cinye na Gina kaina,ta zata shawarar Dana bata zata bulle,hhhhh lallai alhaji mohd zai saki dattijuwar banza zaki gane wace bilki.

Kunji fa readers ko wacce cin amanar ko wacce takeyi,kuma wannan cin amanar ya zama ruwan dare tsakanin kawaye musamman mata,kowacce bata son yar uwarta taci gaba hassada,ga mugun nufi wannan ya zama ruwan dare a rayuwarmu ta yanzu,taya zamu ga dai dai wannan ya jefi wannan ,wannan ya jefi wannan.Allah ka tsarkake mana zuciyoyoyinmu.

Bangaren su oga omar kuwa abin nasa yaci tura,da kyar mama ta janyeshi suka dauki suleim,family doctor mama ta kira yawa suleim dressing,abdallah harda kuka an jiwa kanwarsa ciwo,omar kuwa jikinsa sai rawa yake ran maza ya bacifa readers,dama can ya gaji da halin kannen nasa,sharesu kawai yakeyi amma komai da sukewa mama da kannensa ya sani kyalewa yakeyi dan a zauna lfy,amma tunda haka suka zaba zaiyi maganinsu idan basu nutsu ba.sadiya kuwa sai ihu takeyi jiki ya kumbura,sun hadu a kanta su Aisha suna ta Gasa mata jiki yayinda suke ta zage zagensu iri iri,sadiya kuwa jinsu kawai takeyi dan Allah ne kadai yasan irin matakin da zata dauka kan su omar da uwarsa,dan tayi alkawari ko zata mutu,ko zata karar da salary dinta sai ta kulla musu bala'i,yanzu ta fara ta daina jiran ummansu yanzu itama ta zauna da kafafunta daram sai taga karshen omar da wanda ya rabeshi gaba daya...ruwan zafin da Aisha ta danna mata a gefen wuya shi ya dai daita tunaninta ta saki kara da ihu hade da cewa Aisha zanci uwarki kasheni zakiyi.tana ta ciccijewa sabo da azaba..ni kuwa nace heeee..na fece daga wurin,

Omar bakin ciki ya cunkushe masa zucia,haushin gidan yakeji gaba daya,mikewa yayi ya bar gidan gaba daya,har ya dauki hanyar office din sultan ya fasa ya canja hanya,dan yasan idan yaje wurin sultan bacin rai zai kara masa,da gudu na bishi readers na tafi gulma....lol.mayenta layin su iklas na ganshi gheto area yana Jan motar a slow yau 6days rabonsa da gidan,a tsakiyar layin gefen titi ya hangota tana magana da wasu maza igbo su biyu,sanye take cikin uniform 1:30 da alama daga schl take,

Wani bakin ciki ne ya kara mamaye cuciyar oga omar,ya kwaso bakin ciki yaci karo da wani,haka kawai ya tsinci kansa cike da bacin rai ganin iklas da wasu kucakan maza Igbo,tana ta surutunta hankali kwance.omar na karasowa wajen ya danna wani horn da karfi wanda ya janyo hankalin kowa dake wurin suka zubawa shegiyar azababbiyar motarsa na mujiya,cikinsu harda iklas me dafaffen kwai,glass ya sauke sukayi 4 eye da iklas,alama ya mata tazo sallama tayiwa mazan Igbo bye Emma a gwarance suka ce gomnati gomnati murmushi iklas tayi tare da mikawa Emma hannu suka tafa hade da cewa NO BE SMALL THINGS WOOO,Dayan Dennis yace,ur first salary is my share,nanfa gomnati tace,never mind A NO DEY CARRY LAST MY BRO,daria sukayi dukansu sannan ta daga hannu tana WE GO RUNNERM,U ASEY DEY NOOOOW.ta nufi motar omar kafin ta karasa wani bahaushe saleem yace gomnati sai kinci da biro hannu ta daga masa tare da bude gaban motar ta shiga,ta glass ta leko da kanta tace saleem salary na farko da kasonka ciki,fisgar motar omar yayi ji kake gwaf kan iklas ya bigi gaban motar,birki yaci kyaaaaa....ta koma da baya jagwaf...kafin ta nutsu ya kara fincikar motar ta kuma gwaraf da kanta a jikin glass,kuka ta kece dashi yanda zafi ya hadata ta ko ina.cisgar motar omar ya karayi kamar zasu kifa,ina gefe nace Allah tsare na cikinta Dana kan hanya,kuka iklas takeyi musamman da goshinta wani katon kululu ya fito,parking yayi kofar gidansu,da Sauri iklas ta fita dan ta ga mutuwa with her own koro koro eye,tana fita omar ya sauke glass ji mana....juyowa iklas tayi, u hv to be very careful banda sauki ina gargadinki ki tausayawa lafiyarki kiyi abinda ya dace kunnena yaji da wanda idona zai gani,zan dawo next time hukunci yana nan zaki karba dai dai da ke cewar omar tare da figar motarsa ya bar layin gaba daya cike da jin tsananin haushin iklas,shi kadai ya rasa ma ina zaije ya huta,wani katafaren guest house dinsa ya nufa dake gwagwalada,da ma'aikata da komai a gidan so very neat.

Iklas kam ta Dade a tsaye tana tunanin to ita wai me tayi masa,mene hadinta dashi da haka kawai zai tsaneta,ya dauki karan tsana ya Dora mata..tsaki taja tana mulmula ciwonta ta wuce gida tana kunkuni za a kasheta a banza.

Ummi ce ta tsare iklas da tambayar me ya sameta a goshi,fada mukayi a schl ummi Da wata,shine ta buga min kai da chair nima na fasa nata da dutse.kin kyauta iklas Allah taimaka cewar ummi,shashasha matsa ko na makeki wacce bata San ta girma ba,bari Allah ya kawo min yaron albarka umaru na fada masa tunda naga kinfi jin fadan sa.

To wai ummi ni me nake mikine dazaki dinga hadani da wani azzalumi bare can,bamu hada dangi dashi ba amma har kinfi sonsa akanmu...ummi ce ta maketa da gudu ta mike ta wuce toilet,sallah tayi,wanka da cin abinci,mikewa tayi ta kwanta tana tunani kala kala wanda yafi yawa akan omar.tana tunaninsa kuma sai taji ranta yayi fari,ji tayi gwara tayi tunanin oga fiye Dana schl,ita kadai idan tayi tunanin schl sai tace no sai tayi na omar,sai ta saki murmushi tare da cewa kai ni kwai banza,mene abun tunashi,me ma zanyi dashi,ina Sam mijina yafi wancan ogan kyau ma,

Maman omar ce ta kira wayar sahar sai da tayi mata 5 missed calls bata daga ba,after 40min sahar ta kira back tasan Maman mijinta ce tana da number amma sai tace hello who is on the line pls?,who am I speaking with? Shuru mama tayi tana jin sahar na turancinta ta gane me take fada amma baza ta iya mayar mata da turanci ba domin abdallah yana koya mata sosai shi yasa tana ji sai dai baza ta iya mayar da magana da turanci da tsayi ba.

Sahar Maman omar CE...ohh mama ya gida ya aiki,lfy alhmdllh,sahar dama naji tafiyar da kikayi ne shine naga rashin dacewar hakan,bai....din din din mama taji an datse wayar,kira ta karayi ringing daya taji wata ta dauka tana ta watso turanci tabbas tasan sahar ce ta bada wayar dan a ci mata fuska.mama taji zafin abin sosai amma bata fadawa kowa ba,da kanta ta shirya driver ya kaita har gidan su sahar ta sanarwa iyayenta duk abinda ke faruwa,Maman sahar tabe baki tayi to ai sahar yarinya ce hajia,dole Ku dau hakuri,mu yarmu gaskia banga wani abu da takeyi ba,ya kuke abu kamar muna kauye,zamani ya canja balle ma sahar yar boko ce tana aiki babba dole sai tayi tafiye tafiye.

Baban sahar kuwa gyaran murya yayi am hajiya za a mata fada kar Ku damu,yarinya kuma sai hakuri domin dole tayi aiki,kuma ita yar dangi ce dole sai da ziyarar yan uwa,aikinta kuma gaskia baza tayi wasa dashi ba dan yanzu rayuwa planning akeyi,amma tunda kunce tayi laifi kar Ku damu za a mata fada.haka mama ta dawo tana jimamin halayen iyayen sahar da sahar din kanta.ko omar bata fada masa ba.

Sadiya tayi shige shige ta samo yan daban ta inda ta basu kwangilaar a sassara mata omar,in ta yiyuwa su hallakashi nan da 3wks,kudinta kaf da ta Tara na albashi shekara da shekaru ta basu.

Ita kuwa hajiya rahina ta ajiye shawarar da haj. Bilki ta bata sai nan da wani lokaci zata fara hada makircinsu,yanzu wata kawarta hajia magajiya ta hada da wani shahararren malamin bokanta ta sanar masa so takeyi kawai omar ya bar gidan ubansa da kafarsa.yayinda haj bilki ta samu kudin da rahina ta tura mata na bokan kasar Mali ta bude makeken wajen saloon dinta dama ta gama ginawa rashin kudin siyen kayan ciki ya jawo ta kasa budewa,

1wk da faruwar hakan Omar ya fara jin baya son Sam yaje gidansu,haka gidansa ma bai son zama ciki dole yake zama,mama kanta taga omar ya rage zuwa wajenta,sai ta dauka ko sahar ta gyara halinta ne sun shirya,har tana murna,omar sabo da mama yake daurewa watarana ya shiga gidan,dan in ya dauki hanyar gidan ji yake kamar za a zare masa rai,ga wani mugun bakin ciki da faduwar gaba,haka the same da gidansa,steal guest house nasa ma hakan take,ya canja gidaje da dama nasu amma hakan yakeji,hotel ya koma da zama yafi jin sauki,office kuwa bashi da ikon zuwa.duk wani harkar kula da dukiyar baffa sai wani manager su me amana ya dora akan komai ba wasa

Kuma salisu manager ya kafa ya tsare kan komai,shi yasa baffa yake ganin komai normal,sadiya yaranta sun bazama Neman Omar.amma Sam sun kasa gane inda yake kwata kwata,yayinda Omar ya hada kayansa ya tare a hotel,hakanma kullum tsoratashi akeyi,ga muggan mafarkai,a firgice yake kullum,ya rame,kullum kwakwalwarsa a tunani take ina zai je yaji dadi,ya samu peace of mind,

Omar gashi ya kasa fadawa kowa halin dayake ciki,yayi niyyar sanarwa sultan da mama sai yaji bakinsa yayi nauyi,ita kanta mama taga omar kwata kwata baya hayyacinsa,ko sun tambaya sai yace office ne,kuma sai su Dade basu Ganshi da idonsu ba,abin ya dami mama da sultan,mama ta sanarwa baffa yace suyi masa addua kawai ko da wani abun a ransa da yake damunsa wanda bamu sani ba,

Yaran sadiya sai Neman omar suke su aikashi garin da ba a dawowa,amma abu ya fassakara,sadiya sai masifa takeyi an kasa cika mata burinta,yayin da omar ya kara boye kansa a hotel yana karbar masifu a jikinsa,

Dan yanzu Sam ya bacewa ganin su mama,ya kashe wayoyinsa,an rasa inda ya shige,yanzu ko bacci baya iyayi da kyar yakeyin sallah ma,amma addua ta gagareshi,ko Quran ya dauka tofa faduwa yake ya sume,idan addua zaiyi sai bakin yaki motsawa,kawai gaba daya ya yanke shawarar barin hotel din ko garin abuja duka,

Wani tunani yazo masa ransa take ya tattara trolley dinsa ya shiga taxi har kofar gidan su iklas,cike da izza ya tura gate din yana shiga gidan yaji mugun nutsuwa ta shigeshi,hankalinsa ya dawo jikinsa,ga wani ni'ima hade da nishadi a cikin zuciarsa,tofa readers,wani hanin ga Allah baiwa,haj rahina tsafinta yaci Ashe gata Allah yayiwa omar,domin yaran sadiya sun kara nemo wasu manyan yan daba duk Inda suka San wurin kashe naira na yan Hutu,na masu kudi sunje sunje amma Sam ba Omar ba labarinsa,shi yasa komai kaga ya sameka na kaddara Allah yafika sanin dalili,sonka yake.


Sallama yayi gidan su iklas,kaka ummi ya iske ita kadai tana kulla citta a Leda,iklas tasha baccin rana ta mike ta fito kenan tana mika hade da yin hamma,vest ce jikinta pink da skert dogo me roba.wuf ta koma daki da sauri,ummi kuwa baki ta washe tana tarbar oga umaru,a tabarmar da ummi take nan ya zauna gefenta.




Ku kara shiri readers yanzu za a fara.



Asmabaffa
[17/03, 21:45] Hadiza Sani Fbk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

15-20



By
Asmahbaffa



Ina godiya masoyana masu karatu,ban San wanne irin farin ciki ma zan nuna ba yanda kuke kara min karfin gwiwa.tsakanina da Ku sai addua.


Tunda omar ya zauna gefen kaka ummi suka gaisa bai kara magana ba,Sam ya rasa me zai ce mata,ummi kuwa ta fuskanci umaru matsalace dashi babba,tun daga yanayinsa ta gane gashi ya dan rame ya kara haske,gashi harda trolley dinsa kamar dan gudun hijira,

Kallonsa ummi tayi a nutse kana tace umaru iceko dai lfy?naga kamar kana da damua,omar kamar zaiyi kuka amma bazai iya fadan matsalar sa ba,uhm...uhm...ummi kawai ina cikin Matsala akan lafiyar jikina,nan ne kadai Dana shigo naji nutsuwa,ban San me ya sameni ba,kawai ki tayani da addua ummi,

Kallon omar ummi tayi tabbas iyaka gaskiarsa yayi maganar,ta tabbatar akwai Matsala tattare da omar,gashi kowa yasan babansa a kasar nan kuma da alama suma basu San matsalar dan Nasu ba,


To umaru me kake so ayi?ina
kaje haka?ummi ko ina ya gagareni zama,nan gidan kadai naji na samu nutsuwa,jinjina lamarin ummi tayi amma har yau bata gano matsalar omar ba,dan kar ta takura masa da tambaya ta kyaleshi sai nan gaba idan ya kara samun nutsuwa,

Umaru zaka zauna damu kafin komai ya daidai tane?cewar ummi cike da murna ya daga mata kai,murmushi ummi tayi ko ba komai gidansu zai kara armashi samun namiji tsayayye cikinsu,duk hirar nan da sukayi iklas tana labe jikin labile ta zuro kanta waje,sai da taji komai,a ranta tace to shi me ya sameshi,sai kuma ta tuno yanzu room din da take kwanciya shi za a bawa wannan ogan,

Ta gama planning dinta an rusa mata,yanzu wajen ummi da suhaila zata koma da kwana,daki daya zasu ruguntsuma,abin haushi cewar iklas a ranta.

Omar tunaninsa ya canja state ko ya koma wata kasar amma sabo da baffa ya ce dole ya kula da harkokinsa ba inda zaije,ummi ce ta kwalawa iklas kira,wuf ta yo waje gani ummi jeki kwashe kayanki a dakinki umaru zai zauna zuwa wani lokaci,kallonsa tayi shima kuwa ya dago da kansa sukayi 4eye,Wani sanyi iklas taji a ruhinta,idonta ta janye ta gaisar dashi,yau ya dan sakar mata ba laifi,kayanta ta kwashe tas,ta kara gyara room din sai kamshin ni'ima,daga bisani ta kai masa karamar akwatinsa ciki,alwala yayi yau a nutse yayi sallar azahar da la'asar duk a gidan,

Suhaila kuwa murna take ta tayi dan gayu zai kwana gidansu,zasu dinga shan sweet,shi yasa ta makale kusa da omar.

Abinci iklas iklas ta kawo masa ita tayi girkin kasancewar yau ba islamiyya,tuwon danyar shinkafa miyar egusi,da dan namansu na talaka,rabon da omar ya ci abinci a nutse haka har ya manta,iklas wani table da chair dinta ta jawo ta zauna kai ita fa bata yarda ba ma'aikaciyar gomnati ce,shi yasa in tana kai tana lissafinta wani dadi take ji,kanta kara girma yake sai ta dinga hangota kamar a office,

Tunda omar ya fara cin abinci yake satar kallon shirmen iklas,sai yanga takeyi tana ta faman rubutu,sai da ta gama karatun schl ta jawo jotter lissafinta ta fara,har yi take tana kwankwasa tsinin Biro a dole babbar ma'aikaciyace,

Ummi na gefe suna kallonta,har gumi ta hada sabo da lissafi,readers duk lissafin nan da iklas keyi bai wuce kan karuwar omar da suka samu a gidan ba,dole komai yanzu na ci dashi za ayi lissafi,shi yasa take ta tarawa da ebewa,ummi ce tayi murmushi su kuruci dangin hauka,in kin gama sai ki tashi ki hadawa umaru ruwan wanka.

Ba tare da ta dago kanta ba tace ok,sai da ta dauki lokaci me tsawo sannan ta gama ta kalli agogon dake sakale a hannunta sannan ta mike ta maida littafin palo cikin drower ta dawo,sai da omar yayi wanka sannan ya shiga dakin da aka saukeshi,gaba daya jinsa yake a takure,zafi ya dameshi,ala dole

2 Comments On MA'AIKACIYAR GWAMNATI
avatar
abubakar-adam

10 months ago

Reply

Perfect

avatar
abubakar-adam

10 months ago

Reply

Perfect

Please Login or Register in order to submit comment