Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mijin Aisha ma Nasihar iyaye data Omar sun jawo ya nutsu ya canja hali,sai kiba da kyau da su Sadiya suka karayi. Kullum sai sun Sawa Omar albarka, har Baffa da Umma Rahina suka fadawa abinda Omar yayi musu,haka Mama har Godiya suka Mata.

Iklas ta shiga damuwa akan Khairat tana shigewa mijinta tayi hakuri tayi kawaici ta gaji haka.musamman da taga Omar na biye mata,shima Omar Haushin Iklas yakeji yaga kamar ta daina sonsa bata kishinsa,tana ganin yanda Khairat ke manne masa amma bata nuna komai,shi kuma kara yake mata kawai,baya ga haka da tuni ya kwadawa Khairat maruka yanda take zama tana goga masa kafardarta a tasa, tana taba jikinsa ko ta rike hannunsa in tana masa magana.ga shi kullum shigar banza takeyi a gidan ko kunyar su Baffa bata ji.
Kamar kullum yau Omar da Iklas suna zaune a palon Mama sun baje suna cin abinci Khairat ta fito taci kwalliya ta matse cikin Riga yar fingila da wando sai kamshi takeyi, wajen Omar ta nufa tare da zama kusa dashi tana gugan jikinsa, ran Gomnati yayi mummunan baci

Kishi ya tashi dama ta gaji da halin Khairat,Iklas wani azababben kishine ke azalzalarta kwakwalwarta ta dau zafi, zuciyarta tafasa kawai takeyi,Omar ya ga halin da Iklas ta shiga amma yace me yasa tun farko bata dakatar da abinba.
Iklas tana so taga Omar ya matsa amma taga cin abincinsa ma kawai yakeyi. Iklas a ranta tace kut inama ina da lafiya da billahillazi sai nayiwa matar nan abinda ko a mafarki baza tayi sha'awar zuwa Nigeria ba,amma zanyi maganinta, maganin shege sai dan banza.
Gani tayi Khairat ta zuba lemo a glass cup za ta kai bakin Omar,cikin Zafin Nama Iklas tasa hannu ta fisge cup din tare da watsawa Khairat lemon a fuska, ta mike tsaye tare da nunata da yatsa a tsawace tace get out before I scatter your skull into peaces, dama ga su da tsoro Da Sauri Khairat ta fice,Omar zaiyi magana Iklas ta daga masa hannu ya Isheka ya Ishe.....bata karasa ba mararta ta mirde,ta kulle tare da zamgewa da cakudewa. Rawa jikinta ya fara Kar kar kar....... Gumi ne kawai yake keto mata,wani azababben ciwo taji Wanda ko a labari,,films,da mafarki bata taba sani ba,mararta ta dafe ta daddage iya karfinta cikin siriyar Muryarta ta tsandara Ihun daya fito dasu Mama da Ummi daga kitchen a guje.
Sulalewa kasa tayi tana kuka wayyo Allah na Ku taimaka min,a kaini asibiti na mutu acan,tuni Omar yana kanta shima hawaye yazo masa yana tunanin idan ya rasa Iklas tasa ta kare.

Iklas ta rike Omar kam yana kiyi addua pls yanzu za a tafi asibiti,tana kuka ta fara La'ila ha illalla la'ilaha ilallah taana rerawa ita kadai yanda zakuru sukeyi kawai kirjinne da bata duka,tuni su Ummi sunyi waje kiran driver,Mama na hada kayan haihuwa,
Suna cikin mota tana cinyar Omar kwance su Mama a gefe,Ummi tace dan Allah Iklas ki rufemana baki haka akanki aka fara haihuwa,Omar shafawa Gomnati marar yakeyi yana lallashi tare da tofa mata addua.

Ciwon ne ya lafa mata suna mota driver na tsala gudu, mikewa zaune Iklas tayi tana goge gumi tana wash naji salama,suna shiga asibitin ciwon ya dawo yafi na da,cije baki Iklas tayi tana Bala'i.....Bala'i....gashi......nan.....Omar sai hawaye yakeyi yanda Iklas ta haukace gaba daya gashin kanta kamar daga bakin kura ya fito,yanzu bata ma San me take cewa ba,kuka takeyi tana nishi tana Ku miko min danwake na kwandala,abani ko dan malelene,haka aka turata a gadon asibiti har dakin da aka kwantar da ita,patients da malaman asibitin kowa dariya sukeyi da tausayin Iklas yanda take fadan abu barkatai.

Ummi ce ta kalleta tace yar bantan Uba taji wahala, Mama tace sannu yanzu Likita zaizo, Iklas ta Kalli Mama ta fara tooooooo.......yayi sauri yazo yamin Allura ta kwandala. Shi kansa Omar ta bashi dariya dannewa yayi.

Ummi ce tsuguna a jikin gadon ai kuwa Iklas Neman abin rikewa takeyi ta tugewa Ummi dan kwali ta jefar,da Sauri Ummi ta matsa ta dauki abinta tana daurawa tace harda ciremin dankwali?Iklas tana cijewa tace idan....dan kwalin na kwandala ne to a bani......lallai.... Nace a bani.
Nurses da likitoci sunzo sunce Kaine mijinta? Da sauri Iklas tace yana ina bakin mugu azzalimi,ta fashe da wani irin kuka me karya zuciya.Omar hankalinsa ya kara tashi gashi kusa da Iklas hannunta cikin nasa amma take nemansa bata ganeba.




AsmaBaffa

Ku kwashe min da tafi readers.


Tnx all nayi delay ban cika alkawari ba, amin afwa nima ko ta kwandala ce.ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

190-195



By
AsmaBaffa





Ciwon daya taso ne gadan gadan yasa Iklas ta daina kuka sai muzurai da cijewa kawai kuka ya gagara,likitoci sun bazu a kan Iklas yayinda Gomnati ke sambatu karfinta ya kusa karewa a hankali tace doctor kayi min Allurar guba tunda dai haihuwar nan baza ta zo ba,Omar ya rude addua kawai yake tofa mata,
Iklas tace Ku fadawa mijina ya yafemin bazan warke ba,irin wannan ciwon nasan sai dai na tafiya lahira,Omar ne ya rungumeta yana hawaye am sorry wifey insha'allah zaki tashi,kan Omar ta shafa tace kamar Omar dina,nine matata Honey dinki ne,kayiwa Mama biyayya sosai,idan baka bita ba dole kaci wutar jahannama,domin bakusan Haihuwa ba.
Sakinsa tayi,likita yace ya basu waje ga wani sabon ciwon daya taso mata,Ummi tace kiyi fa a Hankali Iklas Maza suna jinki, da karfi tace Maza? Maza basu San Haihuwa ba....wayyo Maza basu San Haihuwa ba.
Likita ne yace su Ummi su fita duka zasuyi Aiki,Omar yace bazai yuwu namiji ya duba masa mata ba,dole suka kawo mace da mata nurses,harda shahararriyar nurse din nan Subby,Maman waleeda ma anyi mata Transfer Hospital din ita ce ta karbi haihuwa da gaggawa,Subby ta Daura drip,Hajiya Jamila,Jamila Sule duk a asibitin suke aiki sai kaiwa da kawowa sukeyi wurin Iklas,

Tun safe ake abu daya Har yamma Iklas bata haihu ba,bakar azaba take sha kawai,Subby tayi gumi sosai,Iklas kuwa da taji shuru sai tace kuji na fada muku bazan Haihu ba kawai kuyi min Allurar guba,Omar ya rasa Inda zai sa kansa,Sallah sai da yayi rafkannuwa da yawa,
Babbar likita King ita ta zo ta kawo wasu dabaru cikin Ikon Allah 5pm kan yaro ya danno kai,Iklass ido yayi jajir yayo waje,ansata nishi ana fush,babu bakin magana ya mutu murus,nishi ake ta sata suna taimakawa,Rabin Rabin jikin Baby yayo waje aka taimaka ya fito du da komai a hannun Subby,
Zukeken Namiji ta santalo me kama da Ubansa,lafiyayye katon gaske, yaro na fitowa Iklas ta sume, sai da tayi 5mnt ta farfado,nan akayi mata Allurai kala kala,nan danan nurses suka gyara yaro tsab,sannan aka fara yiwa Iklas aikin fito da jinin cikinta tas,tare da gyarata ta Huta sosai sannan Ummi ta shigo ta taimaka mata a bayi tayi wanka sosai ta gasa mata ko ina nan ma Gomnati harda kukan ruwan zafi,kafin su fito room din sai kamshine ke tashi,abinka da private hospital me tsadar gaske kai ka rantse Hotel ne,baza kace a asibiti kake ba,Iklas ita kadai ce a room din ba a hada mutane room daya,kowa da nasa.

An canja bedsheet ma sabo,tana fitowa suka fada toilet ma'aikata suka gyara shima,kamshin dadi ne kawai ke ratsa ko ina,
Iklas ta hana a fadawa Omar ta haihu wai sai ta shirya,a cikin jakar kayan haihuwa harda body lotion da su turare,da man gashi da handdrier,wata nurse da tazo domin sauran sun tafi,tace lallai haihuwar fari ce wannan shiri haka.

Aikuwa Iklas ta busar da gashinta da hand drier ta tajeshi tsab ta shafeshi da man gashi me kamshi,da turaren gashi ma aka shafa,tea ta sha me kaurin gaske,sannan taci kaji da sakwara miyar egusi,Omar kuwa tuni Subby ta fada masa ta Haihu lfy amma ance ya jira za a kirashi,ai kudi ya zaro wanda bai san yawansu ba ya bawa Subby yar Albishir,sauran nurses ma kawai kudi yake ta fella musu,

har yau shuru,har yayi Sallar isha yana jira,Iklas zama tayi ta shafa body lotion dinta me arnen kamshi,
Ta sa Wani Sabon dinkin doguwar rigar material black and milk yayi mugun mata kyau,sama ya dame kasa ya bude,Gomnati fa ta gaji amma haka ta dage tana kwance ta shafa powder ta,ta sa red jambaki,kamar ba ita ta haihu ba,
Dagwas da ita tana kwance Ummi ta mika mata turaruka ta shafa wasu ta fesa wasu,kamshi takeyi na fitar hankali,jariri kuwa tuni Mama ta goge masa jiki da zaitun bayan ya dan dade akayi masa wanka tas dashi aka shafa masa lotion irin na jarirai masu matukar tsada da kamshi Omar ne ya siyosu tun cikin Iklas na 7mnths,kaya masu kauri da pampers aka sa masa suma kayan sai da Mama ta shafa musu turare kafin a sa masa

Yaro gwanin sha'awa,sai da komai ya zama normal sannan a hankali Iklas tace Ummi a kira min ya Omar, Mama sabo da Murna duk ta kira mutane ta sanar musu,Iklas ma haka,Omar kuwa bai kira kowa ba yafi so yaga Halin da matarsa ke ciki.
Yana zaune Ummi baki har kunne tace shigo Umaru,ai Omar ya Riga Ummi shiga dakin,mamakine ya cikashi,bai zaci haka zaiga Iklas ba.shi gani yayi ma ta kara kyau,sai yar ramar wahala da tayi kadan,ga kamshi da take zubawa,tuni Mama da Ummi sunyi waje sun basu waje,Omar ya rungume Iklas murna ta hanashi sukuni,sannu my sweet heart,kinsha wahala,har mamakin Murnar Omar tayi.
Kisses ya dinga manna mata tako ina,kamar zai cinyeta sai sinsinar kamshinta yake tayi kamar zai zauce,yaron dake gefe ya dauka yayi masa Addua sosai sai kallon sa yakeyi ba kifta ido,zama yayi gefen Iklas yaron na jikinsa Kara kallon yaron yayi ya kalli Iklas tare da cewa amma wannan yaron na Kwandala ne ko?dariya sukayi gaba dayansu,tana dukan Omar a baya cike da shagwaba,

Sai kunyar abubuwan dayi takeji a gaban mutane,yaro ya dara alamar Neman Nono,wifey nono za a bawa intestine tunda kince a bashi hanji,murmushi tayi tana shagwaba tace ni... Sai..na huta bacci nakeji,ki bashi mana yasha sai kiyi baccin, a'a ruwan nono bai zo ba fa,a bashi zam zam yasha kawai,dole Omar ya bashi Zam zam.ita kuma tana ta baccinta.

Sai da ta kwashe 8hrs tana bacci,Omar har yaje gida yayi sabon wanka ya dawo,Mama tace Tunda kinci abinci yanzu ki bashi yasha mana kinga har ya fara kuka,a bari na kara yin wanka Mama, wanka tayi ta canja wata shigar ta lace Riga da skert cib ita,kamar dazu haka ta kara hadewa,

Yaro sai kukan yunwa yakeyi,Omar ya shigo room din me ya sameshi haka?Ummi ta bata fuska gata nan taki bashi nono, daga tace wancen sai tace wannan,Mama ce tayi waje tana amsa wayar Baffa,cike da Fushi Iklas ta kalli Ummi ni... Nifa.. Nonona zubewa zaiyi ya lalace,kuma mijina fa?salati Ummi tayi,Omar kuwa dadi yaji ana ji dashi,ya zauna gefenta da sigar lallashi yana Haba wifey ai duk daya ne ni da shi,kinga shima yasha Nima a boye min nawa,bazai yi komai ba in dai ana kula dashi,

Tana kunkuni ta dauki Baby ta saka Hijab ta boye sannan ta fara bashi,yana zuka tace wayyo Allah,Omar yace mene rada masa tayi a kunne tana cije lips wannan da zafi wahala yake bani ba irin naka yakeyi ba,dole ayi masa fada,murmushi Omar yayi yace yes ai ni na musamman ne kalar nawa daban,,Iklas tace cikin rada shi yasa nace kar a bashi gudan jini ko heart a kaishi wajen madaciya,ko hanji.

Haka ne my love,Ummi ce tace munafukan banza aikinku kenan,ke harda boye nono kar a gani ko,Iklas tace ae Ummi abina me daraja ne,nufinki in dinga kwayeshi gaban kowa nasan muhimmancinsa.

Ke ni kar ki isheni da Surutun tsiya dazu kika gama kururwa da kuka,sambatu ba Wanda baki ba kin samu kanki yanzu kin ishe mu,Omar waya yake ta kira cike da zumudi an haifar masa a bouncing Baby Boy,
Mama tace kar a sallamesu sai gobe Iklas tayi bacci ta huta.

Ibzzy Boy yan sanda sun masa jina jina yayi nadamar halinsa,yayin da ya shiga taitayinsa,da kyar aka karbeshi.ya tafi cike da nadamar rayuwarsa ta baya,sai Istigifari yakeyi.
Sadiya ta samu kiran gaggawa daga Office dinsu tana zuwa aka mika mata takardar sallama daga wajen aikinsu,saboda taci bashinsu masu matukar yawa na company taki biya,Sadiya tayi nadamar irin karyar da suka shirya a bikinsu domin da kudin ta ranta ta kara,
Tayi kuka ta gode Allah,tana Oh nasan wannan hukuncina nake karba sanadiyyar abubuwan da nayiwa su Ya Omar,ya zama dole na fada musu abinda muka shuka.
Aisha kuwa yarta da ta Haifa yanzu an gano tana da sickle cell,wato cutar sikila,kullum a hospital suke suna kashe kudi,basu da kwanciyar hankali.

Dama shi laifi in kayi watarana ma sai ka shiryu ka daina sannan a fara jefo ma kaddarori,to su Sadiya karba tasu sukeyi tako Ina,addua kawai sukeyi,sun tabbas hakkin Mama,dasu Omar ne yake binsu,
Dan yanzu haka Sadiya hawan jini ya shigeta,an dorata akan magani.Hajia Rahina da kawarta Hajia Binta sun shirya zasu je ayi musu wata addua wurin malam ,saboda abinda ke fadowa Kansu na masifa.
Suna hanyar Nijar wasu yan fashi suka taresu a mota suka karbe kudaden tare da yi misu fyade sannan suka harbesu a kafafu da Hannu,driver kuwa basu kulashi ba ganin shi talaka ne,shine ya buga waya ya fadawa Baffa yayin da saura 4days sunan Baby na Omar.haka aka kwasosu ranga ranga rai a hannun Allah.

Asibiti aka wuce dasu ,a wulakance,rai a hannun Allah,dama ita duniya dai dai take da kowa,mutum yayi ta shuka tsiyarsa,rana daya Allah ya maidashi ba kowa bane,kyashi,hassada,bakin ciki,gulma,cin amana ta ko ina sunyi yawa a alummarmu ga jarabar son abin duniya,kowa burinshi yaga yafi kowa.Allah kyauta.

Sahar kuwa an gaji an dawo da ita gida,ta fige,ta yage,tayi baki,kai ba Wanda ke gane Sahar yanzu ta dawo kamar kwarangwal,tsoron zuwa dubiyaa akeyi ma,malamai sai aiki sukeyi a kanta ba dare ba rana.dama duk wani iskanci da mutum keyi lafiya ce tayi masa waya,yau gashi halin da suka fada.
Muji tsoron Allah don yanzu tun a duniya ake karbar saka mako.

Bayan an sallami su Iklas,suna gida an cika ana zuwa barka kungiya kungiya,Omar yana dakin da aka bawa Iklas kullum yana tsakiyar Bed shi yake mika jariri,Mama ce take korarsa amma ya nace a room din.
Masu ganin jariri sunyi saukin zuwa,Baffa yazo Room din Iklas ya daukeshi cike da farin ciki,sai addua yake zuba ma jaririn.Iklas yanda take daukan wanka kamar zata party kullum,kai kace bata haihu ba,kullum sabon kayan da Omar ya dinka mata wajen set 20 dasu take cakarewa.kamshi na gaske ke fita a ko ina na jikinta,haka Baby ma kana gani kaga yan gayu ne iyayensa.
Kullum Ummi ke yiwa Iklas wanka ta gasata sosai,ita kuma Iklas anayin wankan tana kuka,tun kafin ma aje wankan take fara kuka.
Me gyaran jiki ta biya kudi ake mata kullum,sai kace zatayi bikin aure,
Khairat suna nan suma sunga jariri,ganin Iklas na busy ta kara likewa Omar,Iklas kuwa hankalinta na kan mijinta tana kallon abinda Khairat keyi.
Angel kawar Iklas ce tazo ganin jariri tace Gomnati ya haihuwar?kallonta Iklas tayi tace keeeeeee Marododo kenan,kinji azaba wlh kubi uwarku na fada miki ki dage da yiwa mamanki biyayya,sai yanzu naga muhimmanci uwa,ke ni yanzu da Mahaifiyata tana da rai ai da taga biyayyar da bata taba gani ba.
Duk inda ake tunanin ciwon ya wuce tunanin me tunani,duk inda zan miki bayani baza ki ganeba Angel,ki bari sai kinyi kya ji.
Wani duhu duhu na dinga gani,ke nifa ban San sanda na koma ganin Hoton kwandala a idona ba,Angel tace kwandala?abinda ba wani amfani ake dasu ba yanzu amma kika ga pic din kwandala,Iklas ta gyara zama tace to wlh kwandala na dinga gani a cikin idona kawai,sai kuma naga danwake da danmalele,ke harda dankwali Ashe na Ummi ne.

Kinga da dan nan ya fito wani duhu na gani duf sai naga wani kwan fitila yayi flashing wall wal,kinsan irin fitilar da can da tsofaffi suke durawa kerosine?Angel tace yeah tace to irinta fa na gani Dana fara farfadowa,Ashe kwan nepa ne.Angel sai dariya take mata.

Omar ne ya shigo da jariri ya mikawa Iklas lokacin Angel tana sallah,zama yayi zai fito da nono ya bawa jariri Da sauri Iklas ta dafe Rigarta miko min Hijab,ke wifey kawarki ce kawai a room dinfa kuma sallah takeyi,ae ni dai ka dauko min,dakko mata yayi tasa ta fara bawa jaririn nono, Omar dage hijab din yayi ya shige shima ya kwanta a cinyarta,Jariri na shan nono Omar na kan cinyar Iklas tana shafa masa gashinsa.
Da dare Iklas ta fesa wanka ita da jariri ta sashi gaba cikin haske ta kura masa ido kurrrrrrrrr ko kiftawa batayi,har Ummi ta shigo bata San ta shigo ba,tana ta kallon Baby tana murmushi ita kadai,afili ta fara maganganunta Kai yanzu Allah ni na haifeka?kato dakai amma ka fito ta wannan yar kafar kofa?kalleka me kyau,gaskia Ina sonka,ina sonka,nafi kowa kaunarka a duniya,Allah raya min kai,ka zama dan albarka,dagashi tayi sama tana ta kissing dinsa ta ko ina ba ji ba gani,Ummi ce ta katseta ina jin dai Aljanu sun shigeki ko?Murmushi Iklas tayi tare da kwantar da yaron,Ummi Allah dan Boy din nan yayi kyau da yawa,kalli hancinsa irin na honey. Ummi wai kamar ni amma ina da haka,gaskia na samu abokina,rufemin baki sakarar banza cewar Ummi.

Shi Omar yanda Iklas ke chake gayu ne yake birgeshi,ta haihu kullum busy amma tana kula da kanta,shi gani yakeyi har tafi da kafin ta haihu daukan wanka da komai da komai.
Kasancewar Hajiya Rahina na asibiti Iklas batayi taron suna ba,yaro yaci Sunan Baban Iklas wato Abubakar suna kiransa Prince,raguna 2 da katon Sa Omar ya yankawa Iklas.

Gomnati so takeyi kawai ayi Suna tayi maganin Khairat.

Baffa sunje asibiti kowa da kowa na family Suna Gaban Haj Rahina wacce take rai a hannun Allah.kuka sukeyi ita da Binta, Binta tana ki yafemin kawata naci amanarki,Ita kuma Haj Rahina tana ke ki rabu dani Binta tsinaniya,so take ta ce Allah na tuba ka yafemin maimakon haka sai zafin ciwon yasa ta koma fadin Alhaji Mohd Inshaa'Allahu......insha'Allahu,sai ta koma cewa nashiga uku mun godewa Allah mun yabi Annabi. Sai rerawa takeyi da wanka.

Bangaren Sahar kuwa ta dan samu sauki amma ta haukace domin duk namijin da ta gani ko yaro ko Babba,ko karami ko babantane da taga da Namiji sai ta bude masa zaninta gabanta ya fito fatsar tace Malam Zaka siya?

Babanta yasa an kulleta a daki na musamman, ammma ko Daddy ta gani sai ta bude masa tace Daddy Na siyarwa ne fa,kan haka wata rana Daddy yayi mata dukan tsiya ya farfasa mata jiki.yana ta kuka shi da Mummy tare da Nadama.
Omar ba abinda ke damunsa irin sha'awar Iklas, wankan da takeyi shike kara rura masa wutar sonta da sha'awarta, ya gama gama sawa Iklas ido, tare da Dana mata tarkonsa ba tare da ta ganeba.burinsa ya samu Iklas ta fara Sallah,bazai iya zama cikin wahalaba ace har sai tayi arba'in. Ga shigar da takeyi me Jan Hankali. Iklas kuma yanda taji wahalar haihuwa tace baza ta kara yarda da Omar ba sai tayi 3mnths ta murmure, kuma hakan ma sai an mata family planning.



AsmaBaffanku ce readers. Tnx all for d comments.ayi min Afwa da typing error ba time ne.ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

195-200



By
AsmaBaffa



Haj Rahina tana sambatun wahala tace Alhaji Mohd ka yafemin,ina Omar a nemo min shi na masa laifi na jefa masa cuta,Mama ki yafe min,tana nishi taci gaba ni...ni....nice....na..je....wajen...boka...ya sawa Omar cutar da ya bar gida kwata kwata,kuma....kuma...na jefa masa lalaura da dama Wanda bai sameshi ba,Nan dai ta tonawa kanta asiri kaf,
Ita kuma Haj Binta tace ni...kuma...kece zaki yafemin Rahina....naci...amarnarki...kin bani kudi...naje wajen....boka...amma na naki zuwa....na dinga shuka miki karya....na cinye miki kudi...na gina kaina.....sabo....sabo da Bana so kici gaba.
Haj.Rahina ce ta fashe da kuka tace wa Binta ke annamimiya ba take nakeyi ba....ki kyaleni inji da kaina...kowa yana gabansu both family Binta da Rahina sai kuka sukeyi.Omar da Iklas sun shigo suma,nan take Omar yace kanku kuka yiwa na yafe.....da sauri Iklas ta rufe masa baki,cike da shagwaba ta rada masa a kunne Allah ni baza ka yafe musu ba,da ace da hali ma gwara a karasa datse musu kafafunsu

No wifey cewar Omar,to shike nan a datse musu hannu ko daya ne,kuma baza a yafe musu ba masu shirka,suka cucemu mijina yayi ta shan Wahalar kuka nima aka sani kuka
Na dinga tausauyin Omar Ina kuka to kukan da suka sani bazan yafe ba.
Omar ne dauke da prince a kafada ya karasa jikin Bed din yace sannu Allah Baku lfy,da sauri Haj Rahina tace ka yafemin da yarana mun zalinceka,na yafe muku komai wlh,Mama ma ta yafe,Baffa kuwa tunda yaji lafazin Rahina ya fuce cike da takaici
Su Sadiya sun cika wajen da kuka ba ji ba gani suma suna rokon a yafe musu.

Iklas tace honey na gaji kasan fa yau 2 days da yin suna ni na gaji kazo mu tafi gida,Ummi ce ta harari Iklas,Mama tace kuje Omar tunda ka yafe ba matsala ,ni zan zauna dasu tare da Ummi.

Baffa anyi anyi yaki ya yafe musu da kyar Mama ta lallabashi sannan yace ya yafe musu,Omar mota ya budewa Iklas ta shiga shima ya shiga yau shine driver prince yana Bayan mota a kwance,Iklas ce ta kalli Omar da harara tare da dauke kai,hannunta ya riko yana mirzawa lfy ke kuma?me nayi ake hararata.Kaine ai Honey ragon maza kawai,daga anyi Abu sai zuciyarka tayi Rauni ka yafe musu,yanzu mene abin yafe musu

2 Comments On MA'AIKACIYAR GWAMNATI
avatar
abubakar-adam

10 months ago

Reply

Perfect

avatar
abubakar-adam

10 months ago

Reply

Perfect

Please Login or Register in order to submit comment