Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

arziki,mama turaruka,atamfa kala biyu,baffa 20k ya bata,sultan ma 10k ya bata,ta fito tsakar gidan kenan iyayin iklas ya kaita ta dinga zagaya compound tana ta daukan selfie,har jikin motoci,tana haka ta kai garden,yaran haj rahina ta hango birjik a garden.

Lallabawa tayi taji Suna ta gulmar su Omar suna zancen asiri,bata karasa ji ba sukayi karo da Aisha,kallonta Aisha tayi take taji ta tsani iklas,ga bakin cikin kyau da taga iklas ta fisu kaf,tayi imani wannan tafi omar ma kyau,

Kwalar iklas Aisha taci ke gidan ubanwa zaki,?gidan ubanki cewar iklas,ai tuni su sadiya ma suka karaso wajen,iklas taga tabbas zaneta zasuyi,da sauri tace kuyi hakuri Ku saurareni, wajen sadiya aka aiko ni,sadiya cike da bala'i tace gani lfy,karewa sadiya kallo tayi tana tuno maganganun suleim yanda sadiya ta tsanesu ta tsani yaya Omar.a kan me za a zagi oga wlh ba a isa ba kunji iklas da karfin Halifax.

Gajiya sadiya tayi ta dakawa iklas tsawa ke karki raina mana hankali fa,duka iklas ta makawa sadiya a kirji,ba tare da sadiya tayi tsammani ba,,tana juyowa ta dullukawa Aisha dundu ji kake dummmmm ta arce da uban gudu, gateman sunga komai,su kansu dadi suka ji,domin su aisha sun gallabesu,tana zuwa gate cike da murna suka wangale mata kofa tace na gode da karfi ta ci gaba da gudu,saida tayi nisa da gidan sannan ta Shiga taxi sai gida.

Su sadia kuwa sunyi suman tsaye,Aisha tace billahillazi duk ranar Dana hadu da yarinyar nan....wlh.....hmm...sai na kusa zare mata numfashi. Sadiya kasa magana tayi tsabar bacin rai,yarinya karama ta kwada mata duka haka.

Taxi na tsayawa ta wuce gida sai daria takeyi hade da haki kamar tayi gasar tsere.oga Omar yana kwance a Palo bacci ya fara daukansa dan ya gaji da jiran dawowar iklas,dariarta ya jiyo ya fito waje sanye da wata dakakkiyar gezna milk color,yasha kyau,

Fuska tamke kamar kullum ya kalli iklas ke lfy,kusa dashi tazo tana tuntsira daria hannunsa ta kamo,yarrrr omar yaji bai San sanda ya fisge hannunsa ba,kara sakalo hannunsa tayi ta jawoshi tsakar gidan tana murmushi ta shimfida musu tabarma,kaka ummi tana kallonsu domin fitowarta kenan zata je makwafta,murmushin manya tayi tasan iklas bata fiye tsoron maza ba ta saba da gogayya dasu,tayi talla a kwalta,ga unguwarsu hausawa kadan ne,dole mutum ya tashi haka,danma iklas kwai tarbiya, sallama ta yi musu ta tafi gidan suna makwafta zasuyi aikin abinci sai dare zata dawo,

Suhaila ce itama tayi sallama ta dawo daga islaamiyya,oyoyo beauty cewar omar dadi suhaila taji tace sannu da gida yaya omar,ta wucewarta dakinsu,

Iklas kuwa kalonta ta mayar gefen omar,sir dole kasha lbr yau,nan iklas ta kwashe komai ta fada masa,sannan ta nuna masa video da ta musu,omar harda kwalla ganin mama da yan uwansa abin sha'awa, yayinda iklas ta bashi daria sabo da shirmen da ta dinga yi a gidansu,kamar irin yar gida,omarma ji yayi hankalinsa ya kwanta ya kara samun nutsuwa.

Kinyi kokari yan mata cewar omar,iklas kuwa cinyar omar ta dafa kasan me nake wa daria,zame cinyarsa omar yayi,ita kuwa iklas kallon omar takeyi kaamar jininta,kamar dan uwanta,kuma ita bada wata manufa take taba jikinsa ba,ga kuma unguwarsu sun saba da hakan sabo da yaren da suke unguwarsu,wannan ba komai bane wajensu.

Wai pls oga sir su waye sadiya ne?kar ki kara ce min wani oga ko sir,sunana omar..sorry to ya omar,ina jinki suna ta zaginka da su mama har zance asiri sukeyi,ban gama ji ba mukayi fada.fada kuma?cewar omar,sisters dinane fa,shekewa da daria iklas tayi ta manta ta sake riko hannun omar daya,kash wannan zata kasheni wlh batasan yanayin Dana ke shiga ba a zuci yayi maganar,daya hannnun yasa ya cire hannun iklas a jikinsa,ji yayi hannunta kamar Auduga dan laushi.

Video ta kunna masa fadansu da su sadiya omar kanshi yasha dariar abin,sau 2 yana kalla,drama queen dama sun zaneki,tab ai wlh basu isa ba,wannan sadiyan me siri siri kafa kamar ta sauro,wasu zagada zagada dasu,tab Allah gidanku ya omar rida ridan tsofaffine ciki hhhh kaga wata me kwalliyar aljanu kuwa,baki ya bige mata sannan tayi shuru,kayan da ta samo ta nuna masa.

Yana gani yace kinji dadinki,wayarta ya karba ya dinga kallon pics din iklas a cikingidansu,sai daria yakeyi,mikewa tayi zata kwace wayarta ta fara jin haushin dariar da yake mata,hanata yayi tana kokarin kwacewa ta kasa,sai haki takeyi,

Zuwa tayi da iya karfinta zata makalkaleshi da sauri ya mike tsaye ya matsa kamar irin yaga wuta zata konashi,bai son ta haddasa masa masifar da take jawo masa da zarar ta rabi jikinsa,

Pics yaci gaba da kalla har yazo kan nata da sultan,gani yayi kafadan sultan tana gogan ta iklas,wani takaicin iklas yakeji,zuciyansa ce yaji ta baci,ga wani kishi daya taso masa,wato ma yanda take taba shi haka takewa kowa,ai kuwa sai yayi maganinta,sai ta daina shashancin taba jikin ko wanne namiji.

Kara kalla yayi yaga wato pics dinsu da sultan har kala 3.bai San sanda ya kwarankwatsa wayar da kasa ba,sai da tayi warka warka,tayi raga raga.tsaki yaja cike da bacin rai ya ficewarsa daga gidan baki daya.

Abinda Omar bai taba yi ba kenan,tunda ya dawo gidan su iklas bai taba gigin fita ba sabo da tsoron yanayin lafiyarsa.

Iklas tayi matukar firgita kamar me aljanu,daga yi masa abin arziki ya zama tsiya

Tsoro taji kar ummi ta dawo ta tadda Omar ya bar gidan,tasan yanda ummi ke kaunar omar,gashi bata San me yasa ya dawo gidansu da zama ba,,duk irin arziki da Allah ya musu,yanke shawara tayi gwara fa tabi bayansa ta dawo dashi.da gudu ta bi bayansa kamar zata tashi sama.

Titin layinsu ta mike a 80 tunda uwarta ta kawota duniya bata taba yin gudu irin wannan ba,sai tareta matasa keyi suna gomanti gomnati,iklas amma ina Sam bata ji bata gani,

Wani uban lungu ta shawo kwana,wata majalasa ce guda ta maza,sun hango gomanti na sheka gudu,wani cikinsu tace hey weyting?iklas tana gudu tace ba lfy ta wucesu fuuuuu...suna gani haka suma suka kwasa da gudu suka rufa mata baya.

Tazo dai dai jikin wani shago taji an riketa caraf da mugun karfi,ido 4 sukayi da omar,da karfi tazo zata rungumeshi tana murmushi hade da Jan numfashi,gocewa yayi da sauri ya matsa ta rungumi iska,

Kunya taji ganin namiji yafita kamewa da taka tsantsan.



Ayi min afwa idan an samu matsala readers dan Adam ajizine.


Ina ji dake MAMAN SULTAN.


Asmabaffa
[27/03, 17:48] Hassan Atk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

30-35

By
Asmahbaffa


Masoyana masu karanta wannan novel duk inda kuke a kasar nan ga gaisuwata na sauke muku mota mota,kwando kwando.ina jinjina Allah kara nisan kwana me amfani da karfin ido.ayi min afwa kwana biyu banyi posting ba.



Me hali baya fasawa fuskar nan kamar Wanda akace mama ta rasu! haka take a daure,tunda omar yabar gidan su iklas gabansa ya kara faduwa,gaba daya tsoro da fargarba ne ya shigeshi Wanda bai San dalili ba,tuni yaji ciwonsa ya fara dawo masa,yayi niyyar kiran driver sa domin ya gwada zuwa gida wajen mama,amma me yana fitowa daga gidan hankalinsa ya tashi,ji yake kamar ana hura masa wuta a jikinsa,gaba daya ya fita a tunaninsa,ji yayi yana neman sumewa shine ya tsaya dai dai jikin shagon da ya hango iklas na famfara gudu,cikin zafin nama ya riketa dan tabbas ya San nemansa ta fito yi,gashi magriba ma tayi,

Iklas kuwa tunda taji kunyar gocewa da omar yayi dan kar ta rungumeshi, ido ta kafa masa,nan ta hango jikin omar na rawa kaf kaf kamar mazari,ga gumi na keto masa duk da cewar ba a Dade da dauke ruwan sama ba,kara kura masa ido tayi nan fa ya fara dafe kirji yana cije lips kamar zai fadi,idonsa sai wani lumshewa sukeyi,tsoro ne ya kamata,sir....ya omar wai lafiyarka kuwa?

Hannu ta kai zata kama hannunsa ya boye hannun,fuska ta daure itama ta fisgo hannun nasa tare da cewa! muje gida ya omar baka da lfy,rike take dashi gam,shi kuwa ba musu ya bita,suka jera abin sha'awa kowannensu na ji da kansa wajen baiwa.

Duk inda suka ratsa sai an kallesu an kara kalla,duk sun haske unguwar,kowa nuna gomnati yakeyi suna ai bro dinta ne yazo,me kudi ne,gashi nan gomnati ta daina talla,ta zama yer gayu,maganganu kala kala.

Gida suka karaso lokacin Omar ya fara nishi ma zai fadi kasa,da sallama suka shiga,yana zura kafarsa daya cikin gidan yaji wani azababbiyar niima da kwanciyar hankali,take yaji gaba daya ciwonsa ya yaye lokaci daya...a ransa ya furta lallai wannan gidan ni'ima ne,

Bayan sallar isha kaka ummi ta dawo daga unguwa,yanzu most of d time omar ke wa suhaila assignment, yau ma hakane shi yayi mata homework,

misalin karfe 1 na dare iklas ta farka,hanklinta ya kasa kwanciya tana tunanin ya omar karfa ko bashi da lfy,

Mika da hamma tayi ta kama shagwaba tana ummi fitsari ki rakani,farkawar ummi keda wuya ta fara masifa ba inda zani da tsohon Daren nan,ke kenan fitsari da zawo,dama haka iklas ke so,ficewa tayi sadaf sadaf da sanda ta murda dakin omar,a zaune ta ganshi yayi tagumi a gefen bed,dago kansa yayi yasan dama sai ita,

A tsorace ta karasa kusa dashi sir omar bacci ka kasa yi ne?harara ya watsa mata,ki daina zuwa wajena da dare ko ba komai sabo da gudun zargi,ba kya jin magana,ki daina sani magana fa tam,baki ta turo kai ya omar Allah baka San a ma gwaninta ba,me zanyi ma ina tunanin ko baka da lfy ne that's y na leko ka,OK tnx as u can see am fine sai ki tafi.

A shagwabe tana buga kafa to kayi bacci mana,dan ta tafi kawai sai omar ya kwanta a bed din,kafin ya mike kafarsa ta karasa ta hada leg nasa wuri daya ta mikar masa dasu,blanket taja ta rufa masa,a.c ta kara karfinta kana ta kashe masa light,ta fice zuwa dakinsu,da rarrafe ta shiga dan kar kaka taji tafiyarta, kwantawa tayi ta bar omar da tunaninta, yanda ta iya kula da mutum , wai bata ma auri mutum ba kenan ina ga ta aureshi.lallai mijinta ya more,sahar dinsa ya tuno wacce ko kallon arziki bata yi masa bare ta gyara masa kwanciya,wai a haka ta waye kuma yar boko,ga me talla nayin abinda ta gagara yi.

3days later omar yasa an kawowa suhaila sweet da snacks,wayoyinsa duka a flymode suke yana buga game a Palo,yayin da suhaila da ummi suka tafi kasuwa,iklas ta tafi kai kayan siyarwarsu makwafta,Omar bacci ne ya daukeshi a Palo,nan ya shiga mugayen mafarkansa kamar kullum,ya hada zufa,sai nishi yakeyi,iklas ce ta dawo da Sauri ta fada palon,tsugunawa tayi kasan kujerar da omar ke kwance,addua ta shiga tofa masa,falaq da nas,fatiha,ayatulkursiyyu,amanarrasulu,can taga ya daina mafarkin,dadi taji tace kai Ashe zan iya rukiyya ma in na dage,

Omar ne ya bude idonsa cike da bacci,tashi yayi zaune, a hankali ya bude idonsa tare da aza su kan kyakyawar fuskar iklas jinjina kai yayi,a ransa yana fadin wannan yarinya tana da nacin tsiya,ruwa ta dauko masa da sauri,a ransa yace ikon Allah kaga shishigi.

A gabansa ta tsugunaa tare da kallonsa cike da tausayawa, Jim kadan tace pls sir ka fada mana abinda ke damunka,inma baza ka fada min ba ka sanarwa ummi,in kuma baka son ummi ta sani ka fada min zan boye ma sirrinka,

Maybe zamu iya baka shawara,bai dace ka zauna haka ba,in kuma kaki to zan fadawa ummi mafarkan danaga kanayi da kuma time din Dana ganka a bakin shago,

Ido kawai ya zubamata yana kallonta har ta gama.Hannun iklas ya riko da hannu biyu ya zaunar da ita a kujera,kinyi alkawari in na fada miki baza ki fadawa kowa ba?da sauri iklas tace ae wlh sai in kai kace na fada,I mean sai da yardarka.Good muje tsakar gida to sai na fada miki,cike da zumudi tayi waje.

Farar kujera ta mika masa ya zauna itama haka,har sun dauki kusan 20mnt amma omar ya kasa bude baki yace komai,a zuciyarsa har ga Allah yana so ya fadawa wani matsalarsa ko zai bashi shawara amma ya kasa,daga lokacin da yayi niyyar sanarwa wani sai ya kasa furtawa.

Gajia iklas tayi da zama ta kirashi cike da sanyin murya,ya omar kayi shuru,kallonta ya kara yi ba tare da yace komai ba,sunyi wurin 30mnt amma yaki magana

Da kyar da sidin goshi ya cije ya furta bani da lfy a jikina,kamar ya?cewar iklas shuru yayi mata,haka ta hakura ta kyaleshi tunda ya kasa cewa komai,ita kuma bata gane me yake nufi ba.

Har ta mike zata wuce sai ta fasa ta dawo ta zauna inda ta tashi,tana zama ya zuba mata ido daga bisani yace zan fada miki next time not know,

Zuciyar omar kuwa ko ya yi niyyar fadi sai yaji a cikin ransa ana gargadinsa,zuciyarsa na tafarfasa,bakinsa yayi nauyi sai ya kasa fada.

Ya schl yanzu aji nawa kike?cewar omar dan kawai ya canja zance.suna hira su ummi suka dawo,ummi sai Murna takeyi ganin iklas tare da yaron kirki umaru.

Bangaren sahar kuwa duniya take tsikara da tsinke,babu ta inda bata cokalar duniya,ta manta ma da aure a kanta.
Mama da baffa sun yanke hukuncin zuwa gidan su sahar domin yin bikonta.

IKLAS na gidansu yau Sunday haka kawai taji yau ta tashi da masifa,ji tayi duniyar ta mata zafi,kamar ta kunnawa kanta wuta,kowa ta tsaneshi,magana kadan sai ta balbale mutum da masifa,

Ita kanta ta rasa dalili, mamakin kanta takeyi,omar na kallonta yanda takewa ummi da suhaila,da safe ma sai da ta Zane suhaila akan kallon film.iklas tana kwance ta baje a tabarma tsakar gida,omar na gyarawa suhaila farce yayinda ummi ke kitchen,haka kawai sukaji iklas a ta fashe da kuka wiwi. Kuka take sharba sosai tsakaninta da Allah,Har shidewa takeyi.

Kallonta omar yayi da sauri ke kumafa?lfy kikewa mutane kuka,da ganinta yasan akwai matsala,ummi kuwa fada ta kamayi me yasa zaka saurareta umaru tunda ta zama shashasha ba sai tayi ba,yarinyar nan tun safe take bala'i! haka kawai ki dauki halayyar banza da wofi,wlh bazan laminci iskanci ba.

Omar bai so fadan kaka ummi ba sai yaji haushi danme zatayiwa iklas fada,ai ruwa baya tsami banza tunda iklas tana da juria haka kawai baza tayi kuka ba

A fili yace ummi ki kyaleta maybe tana da damua ne,pls ya fada da kalar tausayi,hmm ai dama nasan kai umaru baka ganin laifinta biye mata kakeyi shi yasa take kara shagwaba.murmushi yayi ba tare da yace komai ba,sai gomnati da ya kafe da ido wacce take ta sheshekar kuka harma da jingina kanta ki?? Jikin bango tana ta yi.

Ranar haka ta kwana tana kunci da bakin ciki,washe gari Monday haka ma taje schl kowa cin ubansa takeyi ba mutunci...

11:30am dai dai suna class taji kamar danshi a kasanta ita kanta ji takeyi kamar acikin ruwa ta zauna,mikewa tayi tsaye ,Ai firgita tayi sosai,tabbas shine! jini ne,wato abinda takejin lbr period, ta fara itama,abin yazo kanta.

Kunya taji yau kam ba zaman schl dole ta tafi gida,hijab din wata Christian da bata sawa ta ara, ta daura saman rigarta ta rufe wurin daya bata mata uniform.

Omar zaune a Palo yana danna computer sanye cikin jallabiyya yar ubansu fara sai kamshi yakeyi,sumansa tayi yawa sosai sabo da ya jima baije an rage masa ita ba,sai ya kara kyau musamman da baya fita sai ya kara haske da sheki.

Ummi na gefensa suna ta labari,iklas ce ta shigo ko sallama babu ta wuce su ummi da omar fuuuuuuuu kamar zata tashi sama,su har sun tsoratama suna tunanin ko lfy.

Minti 2 tsakani ta kara fitowa daga room dinsu wannan karan har gudu ta hada dashi,waje tayi kofar gida wani shago ta shiga,pad ta siyo ta kara dawowa ta wuce su ummi,sai gata ta fito da Riga,da wasu tarkace a Leda,toilet ta fada karaf...... kararaf ta rufe kofar,suna jinta tana ta kwaramniya da botiki da ruwa.




Asmabaffa
[27/03, 17:48] Hassan Atk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

35-40


By
Asmahbaffa



Ta kai wurin 1hr a toilet sannan ta fito,mikewa omar yayi ya leka ta window ya hango iklas tana shanya kaya,daure take da zani da hijab a jikinta,

Omar ganin iklas ta wanke uniform dinta ya sashi nazari ko lfy?amma dole sai ya tambayeta yaji meke faruwa da ita, Shanyar ta gama ta shigo palon da sallama, kaka ummi ce ta amsa tare da kallon iklas sama da kasa,ke kuma lfy?me ya sameki?

Kunya ce ta lullube iklas sai take ganin kamar kowa ya gane halin da take ciki,sai wani matse kafafu takeyi,su ummi fa sun kasa ganewa,wai me ya sameki ne iklas?ni yar nan na shigesu,

Umaru tayani figa uwar kishiya ta zama kaza,iklas kuwa daki tayi wucewarta ta bar ummi na sallallami,shiryawa tayi cikin dangalalliyar sabuwar doguwar rigarta fara me digon ja,rigar ma da kadan ta wuce gwiwarta,irin kayan da iklas tafi so kenan,

Turare ta shafa yau sosai a jikinta kamshi kawai takeyi ta ko ina,batayiwa kowa magana ba ta wuce kitchen,tea ta hada me kauri ta dawo Palo kusa da omar ta zauna a 3seater da yake zaune yana danna system.

Iklas Sam ta kasa zama,sai taji kamar period zai bata mata kayanta,shi yasa minti biyu uku sai ta mike tsaye ta waiga ta kalli bayanta,sai ta wayance kamar za tayi mika,

Omar ta gefen ido yake kallonta,ya kasa gano matsalar iklas yau,ummi kuwa tun tana masifa har ta kyale iklas.tsakar gida ta koma ta zauna a farar kujera ita kadai,wai nufinta ko da zata baci to ita kadai zata gani,

Ta kasa sakewa Sam ta takure waje daya yau ko akwalar wayarta ta kasa dauka bare tayi danne danne,Ummi ce ta kalli omar....umaru dan Allah jeka wurin yarinyar can kaji meke damunta,tunda naga ni baza ta fada min ba, watakil in anyi dace kai ta fada maka,

Sai da omar ya dauki 5mnt sannan ya fito waje ya nufi inda iklas ke zaune,ta hada kai da gwiwa sai hawaye takeyi tare da kallon gabas ta daga kai sama tana addua,fadi takeyi Allah ka yayemin wannan abun daya sameni,

Idan taji zubowar period zuuuuuu sai tace wayyyoooo Allah na,ta kara daga hannu tana ta zuba addua kan Allah ya yaye mata.tsawa omar ya daka mata! lfy kiki dami mutane,shuru tayi tana kwalla idonta yayi jajir,dake fa nake karki bari raina ya baci..

Kallonsa tayi amma kunya ta hanata fada masa meke damunta,kujera shima ya jawo ya zauna,suna zaune kowa yayi shuru,omar sai latsa wayarsa yakeyi,sun kai kusan 2hrs iklas ta mike ta shiga daki,fitowa tayi dauke da bakar Leda da abubuwa a ciki ta shige toilet,

Nan ma ta Dade sannan ta fito,ledace kulle a hannunta zata jefa a dustbin,fisge ledar omar yayi yana kokarin dubawa,ai iklas kukan kura tayi hade da kurma ihu ta makalkale omar,wayoo ledata dan girman Allah kar ka bude min,dan Allah kayi hakuri,gani tayi da gaske budewa zaiyi,kuka ta sa masa sosai tana rokonsa,pls ya omar karka bude min,

Omar kam ko kulata baiyi ba sai bala'in da ta haddasa masa a cikin jikinsa sanadiyyar Makalkaleshi da iklas tayi,amma ya rantse sai ya gani me take boye musu,ledar ya bude pad din da iklas ta cire ya gani,ai da Sauri ya rufe idonsa ya jefa mata ledar da sauri,

Iklas kam fashewa tayi da kukan takaici tare da zabgawa omar harara,4eye sukayi yaga yanda iklas ke harararsa,kallonta yayi ya saki shu'umin murmushin sa me rikita yan mata,

Ki harareni da kyau kazamar banza dama nasan bazai wuce wannan ba,kinbi kin damu mutane da kuka da masifa,wurin da ta shanya panties ya kalla jiba duk kin baza mana wannan a gida salon wasu su shigo sugane size naki.tun dare bai miki ba ki kwashesu daga nan ki kaisu can baya.

Omar Ya kai kofar Palo zai shiga ya juyo ! ki tabbatar kin wanke mana toilet neat kar na shiga na shaki dirtyn ki.kallon omar iklas tayi hade da sakin kuka da karfin tsiya tana shure shure,

Kaka ummi ce ta fito da Sauri jin kukan iklas, shima Omar tsayawa yayi ya fasa shiga dakin,umaru lfy?cewar ummi,hmm ummi girma ne fa ya kama jikarki, bata da lfy period ne cewar omar ko kunya bai ji ba.

Dogon tsaki ummi taja shine kika hanamu jin dadin rayuwa ja'ira tashi kar cikon kunzugun naki ya goce ki baci.

Daria Omar yayi ya faki idon ummi yawa iklas gwalo,daria da kuka iklas keyi, yanda Omar yayi gwalon shi ya bata daria kamar wani tom.

Baffa da mama ne suka kama hanyar gidan su sahar domin yin bikonta tunda yanzu sun San dansu yana nan lfy,an musu tarba ta ban girma,maman sahar tunda taji biko sukazo ta daure fuska,cika take tana batsewa,dady Baban sahar kuwa fada da masifa ya fara,ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,gaskia alhaji mohd ka raina mana hankali,billahilazim badan kai abokina bane da sai nayi kararka,kuma dan naka ya daawo ya sakar min yata,na gaji da azabtar da ita da kukeyi,ita kadai Allah ya mallakamin sannan Ku dinga min wasa da ita,fafafafaffa maganganu marasa dadi Baban sahar ke yi, haka baffa ya Shiga bada hakuri da Neman sulhu amma Sam maman sahar ta janye mijinta suka shige room suka bar su mama zaune.haka dole suka dawo gida,cike da takaicin wulakancin da iyayen sahar suka yi musu.ba komai duniace cewar mama.


Haj rahina burinta ya kasa cika,ta kori Omar daga gida domin ta kwashi naira a wajen alhaji mohd amma hakanta ya kasa cimma ruwa,domin baffa ya daina Sakar mata fuska ma,bare ma ta samu dama,ta rasa ta wacce hanya zata bullo masa domin so take ta yashi rabonta tunda wuri.sabo da haka ta kara Neman haj bilki kawarta domin ta bata shawara.


Naja na hango a kitchen ita da wata me aikinsu sai dungurewa yarinya kai takeyi tana zaginta ta uwa ta uba,duk yan uwan na kallo ba Wanda yayi magana har umman tasu haj rahina,yar aikin gajiya tayi tace dan Allah ki daina zagar min iyaye,kafin kace me naja ta ebo soyayyen man gyada akan gas ta watsawa yar aikin,tare da kunduma ashar,

Ihu sosai takeyi tana kuka tare da Neman agaji,rankwashi

2 Comments On MA'AIKACIYAR GWAMNATI
avatar
abubakar-adam

10 months ago

Reply

Perfect

avatar
abubakar-adam

10 months ago

Reply

Perfect

Please Login or Register in order to submit comment