Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciki yayi yana tabawa yace wannan ai sai takai ma mutum har cibiya

Bariki tace zo kisa mu gani

Habib yace wai miye haka ne? Naga ke burinki kiga tsiraicina? Toh niba haka nake ba, nono ne kina dashi ina dashi hq gareki shike garan, kowa yaga nasa mana, in banda sabon salon iskanci mutum saiya dinga harin na wani.

Bariki dariya tayi tace toh miye dan naga abun y'ar uwata mace, Aiba komai bane

Habib ya ri'ke kugu yace oh ni habiba yau naga takai na, bariki Wlh in baki fita hanyar tsiraicina ba zan Karta miki guguwan iskancin dake kaina.

Bariki tace oho dai koma dai miye in an isa a bud'e in gani

Habib yace bariki kodai Kema kin Fara neman mata ne? Naga kin d'age sai Kinga tsiraicina, toh inma kin Fara ni bana haka dan bana cin mata ni sai maza inji ayaba tana shiga tana fita

Bariki tace ta ina zata shiga tare da sakin dariya

Habib yace bariki Wlh zan Karta miki rashin mutuncin dake kaina yanzu,

Tace yakuri kawata, gobe yarima zai zo zamu gidan nan

Yace an gama kice mijinki zai zo gobe tare da sakin gud'a

Bariki tace au har ya zama mijina?

Habib yace insha Allah ai wannan a rubuce yake

Wani irin murmushi ta saki cikin jin dad'i Wanda bata san tayi ba, tace taya zan aureshi ba tare da wani matsala ba?

Habib yace Aina fad'a miki dattawa zamu samu, masu ruwan mutunci su zauna a matsayin iyayenki, Kinga Idan akai haka an wuce mataki na farko sannan sai a sami gida a anguwan kanawa irin dai na Talakawa a matsayin nan ne gidan ku.

Bariki tace toh Idan akai bincike fah? Kasan fah dole suyi bincike Wlh ban son a sami matsala

Habib yace ah da naga ni d'aya nake wannan Abun yanzu harda ke, gskya Yarima ya mamaye zuciyarki, karki damu nasan koda za'ayi bincike ta wajan sarkin anguwan za'ayi zan shirya komai

Bariki murmushi tayi tace Allah yasa Kar Abu ya kwabe dan Ina tsoro naga wannan Yariman kaman zaiyi bin kwakwafi.

Habib yace ai koma dai miye karki damu ni zan shirya komai Indai da kud'i ai an wuce wajan

Bariki tace hakane

Habib yace yau bazaki rawan bane?

Tace Wlh babu inda zani Kar in fita Yarima ya kirani.

Habib yace ah toh ni bari inje in dan karkad'a duwawu in girgije inji dad'in rayuwa, fita yayi

Ganin ya fita bariki yasa ta rufe kofarta tare da d'auko wayarta ta danna taga har yanzu Yarima bai kira ba, tunani ne Kala Kala suka cika ta tare da tambayan kanta kodai wani abu ne?

Kwanciya tayi dan tana fashin sallah, tunanin maganan habib take da yake ce mata soyayyan Yarima ya kamata, ido ta lumshe tana tuna haduwanta da Yarima murmushi taita saki lokaci d'aya tace gskya Yarima ya had'u, amma hakan bashi bane yake nuni da ina sonshi ba, toh mai yasa kika damu dashi Sosai haka duk wannan maganan tana yinta ne cikin zuciyarta. Jin karan wayanta alaman kira yasa ta tashi da sauri ta d'auka...

Ganin Sunan Hon salis yasa ta saki tsaki dan a zaton ta Yariman ta ne, sai kuma taga akasin haka

Har wayan ya tsinke bata d'auka ba, wani kiran ne ya kuma shigowa, d'auka tayi tare da fad'in hello

Yace bariki manya, bariki ganinki sai anyi Sa'a inma an ganki sai kinso ki zauna.

Murmushi tayi Mai kama da Ya'ke tace ya akayi?

Yace lafiya just call to say hi

Tace nagode ya abuja hope komai lafiya?

Yace lafiya sai dai I miss dat ur sexy body nd ur swt hq

Murmushi tayi tare da fad'in dama Nasan kiran kenan

Yace Toh bariki Kece ai saida haka, kin San Allah ya miki baiwa Sosai, kullum Indai mutum zai ciki ruwa zuba yake baki da bushewan hq kina da ni'ima Sosai gskya Kinji dad'i kyanshi ai mutum ya sameki ya killace ki waje d'aya, yaita cinki shi d'aya

Murmushi tayi tare da fad'in bariki ba haka take ba, inda ina bukatar hakan da baka cini ba.

Yace hakane, yaushe zan ganki ne?

Tace yaushe nabar abuja? Kai Hon salis kaima fah kana da jaraba

Yace haba bariki kina zuwa fah kika wuce kema kin San banji wani dad'i Sosai ba, inda so samu ne mu zauna harna sati d'aya ko biyu Ina baki ayaba Kinga ai in kika min haka zan gamsu Sosai

Tace uhm Toh yanzu dai zan kwanta inna samu lokaci Zanzo.

Yace godiya nake sai na jiki tare da kashe wayan

Bariki shuru shuru Yarima bai kirata ba, abun ya d'aure Mata kai tayi mugun shiga damuwa kodai an gayama Yarima wani abu ne? Kai Anya kuwa? Mai yasa Bai d'auki wayata ba Mai yasa bai kuma kirani ba? Anya ba'a sami wasu y'an iskan da suka fad'ama Yarima ko ita wacece ba? Inko hakanne tasan Yarima har abada ya barta tashi tayi ta Fara sintiri a d'aki kaman wata soja Mai parade, mai yasa ban fad'a mishi koni wacece ba tun Farko Mai yasa na mishi karya? Gaba d'aya ta kasa sukuni sai kaiwa da komawa takeyi.

Jin karan wayanta tayi alaman sa'ko ya shigo dan haka da sauri ta d'auka taga Yarima ne ga abunda yace.....


Baby are you still awake?

Da sauri tayi mishi reply da yes am awake.

Ko minti d'aya ba'ayi ba sai ga kiran yarima ya shigo wayan ta, da sauri ta d'auka tare dayin sallama

Amsawa yayi da fad'in my princess sorry u call me bana kusa

Wani irin kishi taji hala yana can wajan wacce zai aura, wata zuciyar ce tace Aiba a nan take ba ajiyan zuciya ta sauke tare da fad'in eyya babu komai, tace ya shirye shiryen biki

Murmushi yayi yace Alhmdlh muna tayi, Kema ya kamata kizo ki tayani

Ranta taji yana mata zafi, wato shi har murna yake zaiyi aure, harda wani inzo in taya shi, Toni miye matsayi na a......

Katse mata tunani yayi da fad'in ya naji kinyi shuru, hope lafiya?

Tace uhm Ina jinka

Yace OK ya shirye shiryen Walima? Ina fatan kin Fara inviting friends dinki koh?

Tace a'a ai kace in jira kazo mu tsara komai, dama ina jira ne kazo muyi magana ni nafi son a fasa Walima din I...

Yace OK as you wish good night, naga kaman u r tired so go nd rest gobe zan aiko miki da sa'ko tunda bakya son yin Walima din so basai nazo ba take care yana fad'in haka ya kashe wayan....

Bariki sororo tayi tana kallon wayan tana mamaki, mai Yarima ke nufi kodai yayi fushi ne?????










~MARYAM OBAM~
*BARIKI NA FITO*




*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*WWW.Maryamobamnovels.com*


*Wattpad @maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*




*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*




*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAUWA A USMAN*
*JIDDERH*
~kawata Ina matukar yinki Sosai da Sosai wannan page din duka naki ne kiyi yanda kika ga dama dashi much love my fwnd~



*PAGE 21*







Bariki ce zaune idonta duk sun kumbura alaman taci kuka, sannan kallo d'aya zaka mata ka gane tana bukatar bacci Sosai, amma saboda damuwa yasa kwata kwata bata ji, domin burinta shine anjima Yarima yazo, ta fad'a mishi komai taga yanda zasu kaya, wani hawaye ne ya silalo mata Mai zafi, tunawa da mafarkin da tayi jiya tayi wanda tsoro ya kamata take ganin kuma kaman hakan ne zai faru inta fad'a mishi, kaita girgiza alaman bazan iya juran rasaka ba Yarima, tashi tayi dakyar tayi toilet dan tayi wanka ko zata ji dad'i tun tana toilet take jin nocking sauri tayi ta gama wankan ta fito daka ita sai towel ta nufi kofar Tana fad'in Waye ne?

Muryan hjy babba ne yace nice

Bud'e kofar bariki tayi tana fad'in hjyta wannan uban nocking haka kaman zaki ballamin kofar

Hjy babba yace kedai bariki kin iya iskanci dama kina jin.... Bai karasa ba yayi shuru yana kallon fuskanta hannu ya fara tafawa tare da fad'in mai zan gani haka?

Tace maika gani?

Yace kodai alh madu ne ya kuma marinki? Ji yanda Fuskanki yayi sintin kaman biredi bugun k'ato.

Bariki tace Wlh babu abunda ya faru kawai bacci ne da Banyi ba, shi yasa fuskan ta kumbura.

Hjy babba tabe baki yayi tare da fad'in baki kwana wajan alh madu din ba kenan?

Tace ko d'aya ban kwana ba, tunda period nake inna zauna uban Mai zan masa....

Hjy babba yace kyasha masa ayaba mana

Bariki dariyar da batai niya ba tayi tare da fad'in wace ayaban zansha? Dariya ta kuma saki tare da fad'in dan Allah hjyta kibar maza suyi magana alh madu ai baida ayaba sai tsinke Abu yanda kasan ayaban yara, ni Wlh matarshi ma take ban tausayi, koya take dashi oho.

Hjy babba yace haka zatai ta cinye kayanta tana jin dad'i AI abincin wani guban wani.

Bariki tace tab aiko Indai ayaban alh madu ne toh Wlh babu mace Mai lafiya da zata ji dad'inta hjyta Kinga ayaban ne kuwa? Niko damai zanyi miki kwatance..... Dariya bariki ta saki tace Wlh Kaga karamin yatsa ta? Toh da kad'an ayaban alh madu ya fishi.

Dariya Hjy babba ya saki tare da fad'in na shiga uku Nayi gamo, kice ba banza ba kike gudunsa?

Bariki tace Ashe kin gane gashi babu y'an shafe shafe da tsotse tsotse sai dai kawai ya kamo y'ar ayabarsa yasa yanda kasan ya sami kayan wanki dan iskan tsoho

Dariya Hjy babba yayi yace ah toh wannan ai iskanci ne, taya yasan sarai abunshi karami ne,, kuma bazai dinga shafaki da tsotse kiba sai kawai ya Saka miki ayaba gskya da sake an Kama ango da Uwar amarya.

Bariki dariya tayi tare da cewa Toh hjyta ai na dad'e Ina fad'a miki ni yanzu aure ma zanyi in huta

Hjy babba salati ya saki tare da tafa hannu yace bariki aure dai?

Tace shifa

Yace keda alh madu din?

Tsaki tayi tace koma da Waye zaki ji hjyta lokaci nayi

Hjy babba yace adai gama rufa rufa din zai fito kuma zamu ji.

Bariki tace toh sai a Bari lokacin yayi......

Habib ne ya fad'o d'akin ganin hjy babba da bariki suna fira, yace wace wainar kuke toyawa ne haka kuke k'asa k'asa da murya

Hjy babba ya kalli habib yace Wlh dad'i na dake habiba kin cika zargi, shikenan babu daman aga mutane suna fira sai a fara zargin su.

Tabe baki habib yayi tare da gwale kafa ya zauna yana fad'in kwaji dashi, kallon bariki yayi wacce fuska take a kumbure ga ido yayi ja, yace Mai zan gani dambe kikayi da wani?

Tace Ya'ki Nayi ba dambe ba.

Habib yace ah daka tambaya? Ke kika sani ina Fata dai kin San yau kina da ba'ko saiki tashi ki shirya muje inda zamu tun Kafin lokaci ya kure, ni Mai kika dafa ne yunwa nake ji wlh.

Tace ban dafa komai ba, nima saida kayi m.....

Yace dakata Mlm ban son iskanci miye wani kayi? Mai ya had'ani da wannan Kalman ina mace

Bariki tace Kai Allah ya kyauta

Habib da hjy babba suka amsa da Ameen

Habib yace dan Allah tashi kisa kaya mu fita daka nan maci abinci dan y'ay'an hanjina har kugi suke

Kaya ta d'auka tayi toilet tasa sannan ta d'auki Wanda zata canza anjima tasa a akwati karami suka fita

Bayan sun fita Hjy babba yaga mota sabuwa fil tana walkiya yace oh ji wannan motar Mai Kyau

Bariki kallon motar tayi ita harga Allah ma ta manta da ita.... Tace Alh madu ya bani ita jiya.....

Hjy babba yace shine baki fad'a mana ba amma dai baki da hali

Tace ni nama manta da ita Wlh sai yanzu dana ganta na tuna

Habib yace bariki Anya Kema baki Fara d'an taba shaye shayen nan ba? Taya zaki ce kin manta da motar da aka baki?

Tabe baki tayi tare da fad'in saboda ban d'auki kyautar da wani muhimmanci ba S.......

Hjy babba ne ya Katseta da fad'in amma dai gaskiya bariki baki da mutunci, wannan motar Mai Kyau matrix cefa, gata Sabuwa fil da ita, mutumin nan yana sonki amma kina mishi tsiya....

Tace hjyta yanzu saboda yaban mota kike wannan abun? Bayan kin San matsalan.

Tabe baki hjy babba yayi tare da fad'in Indai da kud'i ai sai Ayi hakuri haka....

Bariki tace bashi bane damuwa ta, hjyta inna dawo za muyi magana...... Gaba sukayi ita da habib

Habib yace bariki Wai wani tsohon ne ya baki mota kike kushewa?

Tace wani Sanata ne, mai karamin ayaba kaman na jarirai yaban.

Habib yace na shiga uku Nayi gamo karamin ayaba? Kuma kaman na jarirai Toh ya yake cinki da ita?oh ni habiba

Bariki tace ci kodai gogawa dan banjinta ako ina

Habib yace tunda ya baki mota ai Kinji dad'i yanzu dai kin San yakamata kiyi taka tsan tsan dan Kar Yarima ya gane wani abu, in kuma sanatan zaki aura Toh yana kaiwa nan ya sake shewa tare da fad'in sai kuje kuyi ta goge juna, tunda baida abun kwarai

Bariki duka takai ma habib tare da fad'in Rufamin asiri, in aureshi ince ma mutane Nayi me? Wai dana bani miji babu kayan harka

Habib ya saki shewa tare da fad'in shi Yarima yana dashi?

Duka takai ma habib tare da fad'in ban son iskanci

Habib yace karki kassarani, ai gaskiya ne shi yana dashi Mai girma ko ya Kar sai Kinje kiga wacce bata Kai ta jarirai ba

D'aure fuska tayi tare da fad'in habib Wlh ka daina dan ban son ana kushe min Yarima I.......

Habib yace ke zance ma ki daina miye kuma wani habib Toh Waye habib din? Taya zaki dinga kirana da Sunan maza Ina mace karki kuma in ba zaki cemin habiba Toh ki bari ban son iskanci yana maganan ne yana bud'e hanci alaman yayi fushi

Bariki gaba tayi tana fad'in ni Nayi gaba in Kaga dama ka zauna a nan

Binta yayi yana fad'in Wai bariki Mai kike nufi dani ne wai? Kalleni sama da k'asa miye a jikin ki wanda babu a nawa?

Dariyan da bariki batai niya ba ta saki tare da fad'in taya zan sani tunda kaya Sun boye muje kowa yayi tsirara sai a gani

Habib yace Aini ba y'ar iska bace in zaki zo muje kizo muje dan zaki iya ganin yarima ya fad'o koda yaushe

Gaba sukayi Dan zuwa gidan y'an uwan bariki na karya😹





********
Karfe hudu da wasu mintinoni motocin Yarima suka tsaya a kofar gidan su zainab wato bariki, message ya Mata tare da fad'in ina kofar gida

Bariki dake kwance akan tabarma taji wayanta yayi kara, d'auka tayi ta duba ganin sa'kon Wanda tun dazu take jira yasa ta tashi da sauri ta kara feshe jikinta da turare tare da shafa powder, fita tayi

Tunda ta fito idonshi ke kanta harta karaso matsowa yayi ya bud'e Mata kofar ta ciki

Tana kokarin bud'ewa taga an bud'e murmushi tayi sannan ta shiga da sallama tare da rufo kofar dan AC a kunne yake

Amsawa Yarima yayi tare da fad'in maiya sameki? Kina ciwon ido ne?

Kai ta girgiza alaman a'a

Yace Toh maiya sami idonki naga kaman sun kumbura? Ko kuma kikayi?

Tace Yarima wani mafarki nayi Wanda Yaban tsoro cikin mafarkin Wai nida kai muna fad'a har kace bazaka aureni ba saboda an fad'a maka mugayen Abu a Kai na kum........

Hannunta ya ri'ke Wanda yasa tayi shuru daka abunda tayi niyan fad'a, yace my princess bana tunanin akwai abunda wani zaice a kanki in fasa auranki Abu d'aya za kiyi wanda ko a masarautar mu babban laifi ne kuma yana d'aya daka cikin laifin Wanda Idan ka aikata dole kabar masarautar shine zina, wannan abun ne kad'ai zaki aikata na fasa auranki domin ni namiji ne mai kishi Sosai ina da kishin abunda nake so, wanda na tabbata ke bakya d'aya daka cikin masu aikata alfasha sai yasa a kullum nake kara sonki, ban kasance mazina ciba sai yasa a kullum nake ro'kan Allah ya bani mace tagari wacce ta tsare kanta daka rudin zamani

Wani hawaye ne ya silalo daka fuskan bariki wanda bata san sun zubo ba .....

Jin hannun Yarima tayi akan fuskanta yana share mata hawayen tare da fad'in baby maiya faru?? Ki daina wani tunani ina tare dake nazo jin amsa kona karbu Ashe an dad'e dayin accepting dina.

Murmushi tayi cikin sanyin jiki ba tare da tace komai ba, domin gaba d'aya maganan Yarima yasa ta fita hayyacinta tare da neman hanyan mafita, tabbas Idan Yarima yasan ita wacece bazai taba auranta ba, kenan mafarkinta gaskiya ne?.....

Katse mata tunani yayi da fad'in my princess tell me Mai kike ji a kaina?

Murmushi tayi tare da fad'in ai kace ka sami amsa

Yace eh but Ina son in kara tabbatarwa

Tace Yarima tabbatarwa ya wuce yardan da nayi za muyi aure Tana maganan ne tana rufe fuska alaman kunya take ji

Matsawa yayi kusa da kunnenta ya fara mata magana cikin rad 'a tare da fad'in I need my kiss...

Tana jin haka tayi saurin matsar da kunnenta Tana fad'in zan koma Gida

Murmushi yayi tare da fad'in yau babu inda zani har sai anyi min abunda nake so, sannan kema kina nan babu inda zaki

Tace Yarima ko gaisawa ba muyi ba.

Murmushi yayi dan yasan Tana son su canza zancen ne sai yasa tace basu gaisa ba , yace oh hakane fah bamu gaisa ba

Tace eh Ina wuni? Da fatan kazo lafiya

Murmushi yayi tare da fad'in lafiya qalau, toh mun gaisa yanzu koh?

Tace eh cikin murmushi

Yace Toh am waiting for it

Tace what???

Yace kiss

Ido ta lumshe ba tare da tace komai ba, wani irin son Yarima yake fusganta sai yau ta kara tabbatarwa da tana sonshi tunda ta ganshi taji wani irin sonshi na fusganta

Shima haka ta gefenshi wani irin sonta yake ji har cikin ranshi ji yake kaman ya tafi da ita ace yau mallakinshi ce da yafi kowa murna, daya nuna mata so Wanda bazata taba samun wanda zai Mata shiba, amma dai a kwana a tashi burinshi insha Allah zai ciki, ya tsara musu abubuwa da dama shida ita ya tanadar mata soyayya tsantsa Wanda zai nuna mata inya mallaketa

Bariki ido ta bud'e ta kalleshi ta gefen ido taga ita yake kallo, da sauri ta kara lumshe ido, tare da tunanin abubuwa da dama, lallai Idan Yarima yasan wacece ni Toh daka ranan na rasa shi, maiya kamata inyi? Hawaye ne ya silalo mata a fuska......

Janyota yayi jikinsa tare da share mata hawayen yace mai yake damunki ne yau my princess?

Tunda ya janyota jikinshi ya saka mata kanta a kirjinshi ta lumshe ido domin gaba d'aya jikinta ya mutu ga kamshin turarenshi dake dad'a tayar mata da hankali, yau ce rana ta farko da namiji ya Mata haka taji har tana sha'awa da sauri ta Fara kokarin Jan jikinta daka nashi amma saiya kara manneta dakyau

Ta gefen Yarima kam shima jinshi yake wani iri, ya rasa wani irin so yake mata, kwata kwata baya son ganinta cikin damuwa ko kad'an baya son yin nesa da ita akan dole yake tafiya ya barta, yau ne rana na farko daya kosa ayi bakinshi da gimbiya zinatu dan Ayi maganan auranshi da zainab dinshi....

Bariki ce ta katse shi da fad'in Yarima wayanka na wuta kaman ana kira.

D'aukan wayan yayi yaga gimbiya zinatu ce, murmushi yayi tare da d'auka har yanzu bariki na manne dashi yaki sakinta. Yace gimbiya Barka da yamma... Yana maganan ne yana Satan kallon bariki dake manne a jikinsa ban San mai gimbiya tace mishi ba naji yana fad'in saura kwana nawa a kawo ki kaman jibi ne koh? Tunda anan za'ayi komai.....

Bariki dake kwance a kirjinshi taja jikinta da karfi har wayan tayi kasa ta silale daka hannunshi, kallonta yake tayi yanda yaga ta murtuke fuska abun yaso ya bashi dariya amma saiya dake dama da biyu yayi hakan, wayan yake kokarin d'auka bariki kuma tana kokarin bud'e kofar, hannunta ya ri'ke Bayan ya d'auko wayan kashe wayan yayi gaba d'aya, ya kalli zainab dinshi yace Ina zaki?

Tace zani gida in d'auko Abu ne tunda naga kana waya

Yace Toh yanzu na gama

Tace ina zuwa yanzu zan dawo

Yace OK tare da sakar mata hannu,

Fita tayi tana shiga cikin gidan ta fashe da kuka, yanzu dan wacce zai aura ta kirashi nake wannan kishin shifa Idan yaji na bayar da mutunci na ga wasu mazan ya zaiyi? Kuka ta kuma saki Sosai tare da fargaban abunda zai faru in Yarima yaji wannan zancen.......











~MARYAM OBAM~
*BARIKI NA FITO*




*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*WWW.Maryamobamnovels.com*


*Wattpad @maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*




*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*




*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*




*PAGE 22*







Kuka tayi Mai isarta, sannan ta wanke fuskanta tare da shafa powder dan Kar Yarima ya gane, saida ta tsaya ta seta kanta sannan ta fita.....

Tunda ta fito yake kallon fuskanta wanda dama tunda ta shiga idonshi nakan kofar gidan, tun Kafin ta karaso ya gane tayi kuka domin idonta yayi ja, dan farar mace Indai tayi kuka sai an gane dan fuskanta zata canza tayi ja ja......

Isowarta ne yasa tunanin da yake ya kawar

Bayan ta bud'e motar ta shiga da sallama muryanta a dashe....

Amsawa yayi tare da fad'in my princess yau kwata kwata na rasa gane maike damunki? Mai yasa kikai kuka da kika shiga ciki?

Gabanta taji ya fad'i ya akai yasan nayi kuka toh kodai ya biyoni ciki ne kai Anya a'a Toh y......

Katse mata tunani yayi tare da kiran sunanta da zainab

Da sauri ta d'ago ta kalleshi dan tasan magana zai Mata Wanda yake bukatan hankalinta tunda ya kirata da sunanta....

Yace I don't know why yau kaman you are not happy, plz Idan kina da wani matsala ko damuwa let me know, ban son kiji shakkan fad'amin wani abu da kike bukata ko kunya, plz tell me maike damunki?

Muryanta na rawa tace Yarima Ina son inyi maka wata tambaya, ina son Kuma ka bani amsa...

Murmushi yayi tare da fad'in go ahead....

Tace kasan al'amarin aure yana da abubuwa da dama, yau Idan akace mutum zaiyi aure sai ayita kushe shi, ko kuma azo ana ya'da Labarin karya akan mutum yan.....

Dakatar da ita yayi da fad'in enough my princess it seem like wannan mafarkin da kikayi yasa kike wannan maganan, na fad'a miki zina ne kawai zaki aikata in fasa aurenki..... Bayan haka banga abunda zaki aikata ba ince na fasa auranki ba, sannan ina so ki sani sonda nake miki ba Wanda wani zaizo ya fad'a magana akanki bane in yarda I trust you nasan bazaki taba bani kunya ba

A hankali tace in fah wani yazo yace maka ni karuwa ce ya Z........

Yace ya isa haka ya isa yana maganan ne cikin jin haushin abunda tace, yace karki kara danganta kanki da wannan Kalman infact ma ban son ki karamin wannan maganan plz..... Let change the topic

Shuru tayi ba tare da tace komai ba, Satan kallon Yarima tayi wanda taga gaba d'aya yana yinshi ya canza alaman ranshi a jagule yake.....

Katse mata tunani yayi tare da fad'in Zainab kinsa naji babu dad'i, mai yasa zaki damu da mafarkin da kikayi haka har kike zargin wani abu? Har kike dan ganta kanki da wannan mummunan Kalman, Zainab duk Wanda ya kiraki da wannan Kalman sai Nayi karanshi dan ba haka kike ba, I trust you more than my self, ina jin kaman na sanki tun tuni karki manta tun a mafarki na Fara ganinki ban taba ganin Fuskanki ba a mafarki ba

Please Login or Register in order to submit comment