Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*PAGE 4*




*MAZA KUJI TSORAN ALLAH LOKACIN DA KAKE NEMAN MACE KOMAI TACE TANA SO SAIKA MATA, WANI ABUN MA BATA TAMBAYA KAKE MATA, IN ANYI AURE DUK HIDIMAR DA KAKE MATA SAIKA DAINA, KUMA BAWAI DAN BAKA DA HALIN YI DIN BANE, IN BAKA KYAUTATA MA IYALINKA BA WA ZAKA KYAUTATAMA, SAI KAJE KANA FAD'A AI BATA KWALLIYA BATA MAKA ABU KAMAN DA KAFIN KA AURETA, HMMM TAYA ZATA MAKA KWALLIYA TAYU KUD'IN POWDER DINMA BAKA BATA, KO KUD'IN KITSO A INA KAKE SON TA SAMI KUD'I TAYI??? DA LOKACIN DA TAKE GIDANSU TANA DA KYAU KOMAI NATA ABUN SHA'AWA AMMA KA AURETA KA MAIDATA TSOHUWAR KARFI DA YAJI, BABU KUD'IN LALLE, BALLE NA TURARE😫 HABA MAZA MAI YASA KUKE HAKA?? IN KAJE GIDAN ABOKIN KA YA BAKA ABINCI MAI DAD'I SAI KAZO KANA ZAGIN MATARKA BATA IYA GIRKI BA, BAYAN KAINE BAKA BATA KUD'IN CEFANE WANDA ZAI IYA HAR AYI MAI DAD'IN BA, WLH KUJI TSORAN ALLAH MAZA MASU IRIN WANNAN HALIN DAKA RANAN DA AKA BAKA ITA A MATSAYIN MATARKA KOMAI NATA YA RATAYA AKAN KA, ABUNDA MUTUM YAKE GANIN BA KOMAI BANE ZAI IYA KAISHI GA HALAKA, IN KANA DA HALI KA FARANTA MA MATARKA YANDA INTA FITO ZA'A CE MATAR WANCAN NE SABODA AN GANTA FES, AMMA IN AKA GANTA SABANIN HAKA ZAGINKA ZA'AYI TUNDA ANSAN KANA DASHI PLZ MAZA KU GYARA DOMIN ALLAH ZAI TAMBAYEKU TUNDA KANA DA HALI DAMA BABU NE SAI AYI HAKURI*






Kallonshi tayi cikin tsoro tare da fad'in Yarima plz ka barshi Kawu nane yake kira, so yake Inba ma Abba, wayan Abba ne ya sami matsala in an kira yana ji amma ba'a jinshi, inna d'auka nace bana gida zai iya zuwa har gidan ya sami Abba da Umma yayi musu fad'a akan Mai yasa zasu dinga bari Ina fita da yamma, kuma yanzu inna shiga Gida Umma bazata Bari in fita ba, dan yanzu tana tunanin ina d'akin makwabciyan mune.....

Yarima Aliyu ajiyan zuciya ya sauke, lallai Zainab gidansu gidan tarbiya ne, sabanin yanzu da iyaye suke sakin y'ay'ansu suna abunda suka ga dama, har ma wasu zaku ga kaman su suke juya nasu iyayen sai abunda sukace iyayen nasu keyi..... Amma a fili sai yace Mata my princess na fad'a miki tun Farko ai ki bani dama inga Abba kinki, yanzu Idan yazo ya gammu ya kike so inyi???

Cikin sanyin murya tace bazanji dad'i ba, domin na tabbata Abba zaiyi fushi Sosai, amma Yarima tunda harna yarda yau kazo gidanmu hakan ya kamata ya nuna cewa Ina son Kaga Abba din.....

Wani irin murmushi Yarima ya saki cikin jin dad'i tare da furta Kalman Alhamdullilah cikin ranshi, domin wannan maganan da Zainab tayi mishi yasa shi cikin farin ciki Sosai..... Kallonta yayi cikin ido tare da fad'in my princess kin tabbata kina son inga Abba.???

Ganin bazata iya juran kallon cikin idonshi ba yasa ta kawar dakai gefe tare da fad'in eh Ina so ka ganshi, domin hakan ya kamata Ayi tun Farko

Murmushi yayi tare da fad'in zan iya ganinshi yau?

Tace eh amma sai dai ka tura wani yaje ya maka sallama dashi duk da ban tunanin ya dawo amma kuma hala ya dawo din dan lokacin dawowarsa yayi .....

Dariya Yarima yayi tare da fad'in am joking bazan iya zuwa ni d'aya ba, but zuwa jibi Zanzo da Usman da wasu friends dina sai mu ganshi mu nemi izinin zuwa zance Kafin manya su shiga

Murmushi tayi tare da fad'in Allah ya taimaka

Ya amsa da Ameen, tare da fad'in where is my promise?

Kallonshi tayi taga shima ita yake kallo da sauri ta kawar da kanta gefe tare da sakin murmushi sannan tace wani promise??

Yace abunda ya faru wajan Walima.

Dariya tayi wanda ya kara mata kyau sannan tace Yarima ban samu daman d'aukan komai ba saboda jama'a Wlh kunya duk ta hanani gashi mune masu saukan..... Amma munyi hoto a gida da kawaye na Wanda mukai saukan tare

Yace OK Nasan duk kinfi yin kyau

Tace a'a tare da danna wayarta tace na tura maka ta whatsapp

Murmushi yayi ya d'auko wayanshi ya fara dannawa, yace my princess duka sun sa nikaf Kema Aida kinsa ko so kike ayi ta kallemin ke

Dariya tayi tace a cikin gida nefa babu Mai kallo na sai Kai ta karasa maganan tare da rufe fuska

Murmushi yayi tare da fad'in my princess yunwa nake ji banci komai ba tunda safe.....

Da sauri ta kalleshi tare da fad'in mai zakaci in kawo ma? Yarima taya zaka zauna har yanzu bakaci komai ba ulcer zai kamaka plz mai zaka ci??

Murmushi yayi cikin jin dad'i domin ganin yanda ta nuna kulawanta akanshi, ya tabbatar mishi da cewa tana sonshi Sosai......

Katse mishi tunani tayi da fad'in Yarima ko in kawo maka tea kasha Kafin in dafa maka wani abu??

Yace a'ah ki barshi zanje Inci abinci yanzu

Shuru tayi tana d'an nazari can tace ko in kira habib yaje ya kawo ma wani abu kaci?

Hannunta ya koma tare da ri'ke mata su duka biyun yace my princess karki damu zanje wani waje Inci, ko zaki raka ni?

Da sauri tace eh muje Kafin Abba yasa Umma ta kirani a d'akin da take tunanin ina ciki inya dawo Kar yasa a kirani yaga bana nan koda yake Nasan ma ya dawo ganin habib Nasan bazai damu daya ganni ba.

Murmushi yayi yace Nop Bari inje alone banso Ayi miki fad'a my princess

Tace Yarima plz muje kaci abinci habib na nan bari in kirashi sai muje tare zance ma Abba zani maraban jos In kwana bazai hana ba sai muje kaci

Yarima yace ok my princess

Fita tayi ta shiga cikin gidan Jim kad'an sai gata ita da habib da abbanta na Bariki Sun fito daka gani ya fito raka habib dinne a yanda Yarima ya fahimta kenan🤣 har bakin titi ya rakasu sannan ya dawo ya shiga gidan yarima yana kallonshi cikin ranshi yace wannan daka gani Dattijo ne yana yin kamalan shi ya nuna ma Yarima hakan🤣🤣🤣 kai ana abu a duniya sai yasa akace sometimes abunda ka gani bashi bane gaskiya......

Yarima tada motar yayi shima ya nufa titi bai gansu ba kiran Zainab dinne yasa ya dauki waya tare da fad'in my princess where are you?

Tace muna gaba wajan NDA Abba saida muka shiga mota ya koma shine muka sauka a nda

Yarima yace ok ga ninan zuwa, Yarima juyawa yayi ya nufi nda din ya d'aukesu ta shiga gaba habib kuma baya, Yarima ya kalleta yace Ina zaki kaini Inci abinci??

Ido ta d'an zaro tare da fad'in ni Ina na sani tunda ba zuwa nake ba

Habib dake Bayan motar yana jinsu cikin ranshi yace bariki ko y'ar iska ke inane baki Sani ba cikin garin kaduna yanda kuka san map din garin ne a kanta amma yanzu tana wani nuna ita ta Allah ce..... 🤣

Yarima wani babban restaurant ya faka motarshi wajan yayi mugun had'uwa gashi babu irin tarkacen mutane a wajan, daka ganin alama wajan ba kowa ke zuwa ba sai y'an gayu na gaske, private waje suka zauna, shidai habib cewa yayi cikin mutane zai zauna danya dinga ganin masu shiga da fita

Bariki tace muje tare mana

Yace ke barni in zauna nan ko zanyi kasuwa

Bariki dai dariya tayi sannan ta nufi ciki inda Yarima yake domin yace baya son su zauna inda akwai mutum ko d'aya dan baya son ana kallon mishi ita.......

Yarima ya fad'a abunda za'a bashi bariki kam tace ta koshi Yarima yace dole taci wani abu, babu yanda ta iya tasa a kawo mata snack dan a koshe take shima takeaway tace tana so, yarima yace abar snack din in Sun tashi fita zata zaba abunda take so.

Wajan 15 mnt aka kawo ma Yarima abinci lokacin ana ta kiran sallah magrib tashi yayi ya Kalli bariki tare da fad'in bari inyi sallah.

Tace OK tare da kallon Wanda ya kawo abincin tace maida kayan inya dawo sai kayi warming din abincin ka kawo.

Mutumin yace ok ma, Yarima bai tafi ba saida yaga mutumin ya fita dan ya Lura dashi yanda yake kallon zainab kaman yana son yi mata magana.....

Yarima Aliyu na fita kam saiga mutumin ya dawo da sauri yana fad'in ma plz I need to talk to you.

Bariki tace lafiya maiya faru?

Yace ma ance in amso phone number d'inki ne

Tace what? Are you mad da aurena inzo da mijina kazo kace min in baka phone number dina get lost frm hare Kafin mijina ya dawo ya ganka

Mutumin yace sorry ma Nima na fad'a mishi kina da aure saboda irin shigarki amma yace babu damuwa koda kina da aure in amso mishi number d'inki

Bariki tace Waye zan iya ganinshi??

Yace let me go and ask him in yace in kawo ki sai kizo

Bariki tace ok yana tafiya saiga Yarima ya dawo Allah yasa bai ganshi ba

Bariki tashi tayi tare da fad'in har an idar kiran mutumin tayi da baiyi nisa ba yazo tace Kawo Mai abincin

Yace OK ma

Bai dad'e ba saiga abincin ya kawo, Yarima coffee ya fara sha sannan ya kalli bariki yace my princess feed me plz

Dariya tayi tare da fad'in feed ur self u r not a baby

Yarima kallonta yayi tare da fad'in oh really? Ni baby dinki ne

Ido ta rufe alaman jin kunya

Hannunshi yasa yana kokarin cire mata hannunta da tasa ta rufe fuskanta ..... Muryan Wanda ya kawo abincin ne yazo yana fad'in ma he said that you can come he is waiting for you......




*Plz kuyi ma my hrt addu'a Allah ya bata lfya my princess my queen phareejay, Allah yasa kaffara ne🙏🙏😫😫*



*kuyi manage plz Nima ba wani lfya gareni ba Nayi muku ne dan kusa my hrt a addu'a plz 🙏🙏*





*plz ku dinga hakuri da typing error banda tym din editing*




~MARYAM OBAM~
*BARIKI NA FITO*




*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*WWW.Maryamobamnovels.com*


*Wattpad @maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*




*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*




*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*




*BOOK 2*


*PAGE 5*




*Y'AR UWA KOMAI MUJINKI YAYI MIKI AMSA KIYI GODIYA TARE DA NUNA FARIN CIKIN KI DUK KANKANTAR ABUN KARKI RAINA, DOMIN YAU IDAN MIJINKI YA KAWO MIKI PURE WATER YAGA KINA TA MURNA TOH GOBE SWAN WATER ZAI KAWO MIKI YAGA WANI IRIN MURNA ZA KIYI, BABU ABUNDA NAMIJI YA TSANA KAMAN YAGA YA KU'KE YAYI MIKI ABU AMMA KI NUNA MISHI HALIN KO IN KULA, Y'AR UWA IN KINA MA MIJI HAKA WLH KO YANA DASHI BAZAI DINGA YI MIKI BA ZAICE BAKYA GODEWA IN YAYI MIKI GWARA KAR YAYI KI ZAGESHI DA HUJJA, NAMIJI YANA DA SAUKI IN KIN IYA TAFIYAR DASHI DUK DA NASAN WASU MAZAN KOYA KA MUSU🙆🙆 BASU CANZAWA, AMMA ANA CEWA IN KASAN HALIN MUTUN SAI KASAN YANDA ZAKA ZAUNA DASHI, RAYUWAR AURE DUKA HAKURI NE IN KINCE MIJINKI YAYI MIKI KAZA, TOH WATA ITA NATA MIJIN YAYI MATA ABUNDA YAFI NAKI MUNI KUMA HAKA TAKE ZAMA DASHI BABU YANDA ZA TAYI, AURE BAUTA NE KUMA DUK ABUNDA AKACE BAUTA TOH SAI ANJURE DAN HAKA MATA KUYI TA HAKURI DUK MAI HAKURI YANA TARE DA ALLAH, SANNAN WUYA BAYA TABA DAUREWA HAKA JIN DAD'I DAN HAKA HAKURI DAI SHINE ZAMAN DUNIYA*





Yarima cire hannunshi daka fuskanta yayi idonshi ya sauka akan yaron, ganin irin kallon da yake Mai yasa yaron Ya daburce.....

Tare da fad'in sir aikoni akayi na fad'a mata shine tace zata taga Waye, shine yace ince taz.....

Bariki ta Katse shi da fad'in ya isa haka, kallon Yarima tayi wanda fuskanshi ke d'aure alaman bacin rai tace Yarima na yazo yace in bashi number dina shine..... Labarin abunda ya faru ta bashi....

Yarima Aliyu baiyi magana ba sai d'aukan wayarshi da yayi ya danyi danne danne sannan yasa a kunne yana fad'in ina restaurant dinka kazo yanzu coz ina sauri, yana fad'in haka ya ajiye wayar.... Ganin haka mutumin daya kawo abincin ya zube a k'asa ya fara ro'kan yarima danya tabbata Mai wajan ya kira, yace plz sir forgive me Wlh Aiko ni akayi saida nace bazan zoba matar aurece, amma yace dole sai Naje ko yasa Mai wajan ya koreni, sir In baka yarda ba kazo muje ka ganshi....

Tashi Yarima Aliyu yayi yace muje.....

Da sauri ya tashi ya shiga gaba amma suna zuwa wajan da yace mutumin na ciki suka ga wayam, babu kowa.

Yarima Aliyu ya kalli mutumin yace yana Ina?

Mutumin yace sir Wlh a nan yake sai dai in fita yayi, hakuri yaita bama Yarima.... Bariki tace Yarima kayi hakuri kazo muje.....

Jan hannun bariki yayi sukai waje Bayan ya biya kud'in tare da cema habib dake zaune ta waje muje.....

Bayan sun shiga mota Yarima tuki yake cikin bacin rai domin shi gaba d'aya laifin Zainab din ya gani damme zata tsaya Tana magana dashi har tace tana son ganin mutumin yanzu inda ban dawo ba zuwa za tayi..... Wani irin gudu ya saki....

Habib dake baya yace cikin ranshi Kar yaje ya kasheni ina cin gajiyar kuruciyata da sauri yace Yarima zan sauka a kawo zan amsa sa'ko...

Yarima yace ok suna zuwa kawo Yarima ya faka habib ya fita tare da fad'in a gayas haka kawai aje a kashe ni ban shirya ba...... 🤣🤣

Yarima bai tsaya ba sai maraban jos, da yake yau sati mutane nata kaiwa da komawa cikin shigar banza, Yarima shidai ya rasa mai yasa baya son wannan anguwar shi inda so samu ne baya son tana zuwa kwata kwata domin anguwar bata Mai ba, ga motoci dake ta shigowa waima damma ba tanan bane Layin da bariki take ba......

Bariki kallon Yarima tayi da fuskanshi babu alaman wasa..... Tace haba Yarima kofa abincin baka ciba, aiya kam......

Yace ya isa Zainab plz, ban son dogon magana, sauka kije zan tafi.....

Kallon mamaki take mishi ganin yanda yake mata magana duk da hakan ya bata tsoro amma saita dake tace haba Yarima, wannan fushin fah, karka manta kazo tayani murna ne bai kamata ka sani cikin damuwa ba

Shuru yayi ba tare da yace Mata komai ba, a tunaninta ya sauko ne, dan haka tace yanzu Mai zaka ci in n.....

Ya dakatar da ita da fad'in Zainab plz leave my car....

Tace Yarima Mai.....

Yace I said leave my car plz

Hawaye ne ya fara zubo mata, garin yayi duhu, baya ganin hawayen da takeyi jin Tana sheshekar kuka yasa ya gane kuka takeyi..... Bud'e motar yayi ya fita domin bazai iya sauraranta Tana kuka ba uwa uba kuma abunda tayi ya bata mishi rai, a duniya babu abunda ya tsana kaman yaga ana taba abunda yake so, wanda yake ganin kaman Zainab din ta raina shine tunda har tayi magana da wani ya tabbata inda bai dawo ba zata iya sauraranshi tunda harta yarda Tana son ganinshi din, wata zuciyar tace amma tayi maka bayani.... D'an tsaki taja tare da nufa masallacin dake kusa da wajan dan yin sallah isha'i da ake kira......

Bariki kam tana cikin motar tana kuka, wanda ba kukan komai take ba saina tausayin kanta, musamman abunda taga ya faru yau, jiba yanda Yarima yayi fushi har yake nuna kishinshi a fili, tabbas Idan Yarima yasan wacece ni ban tunanin zai ragamin ko kad'an, lokaci d'aya taji kanta ya fara mata ciwo, lallai Ina son Yarima bana tunanin zan iya rayuwa ba tare dashi ba, sonshi yasa na daina aikata zina sonshi yasa na daina aikata abunda Nayi niya dan inga na kuntata ma iyayena, wani sabon kuka ta kuma saki.....

Yarima ne ya shigo cikin motar jin Tana kuka Sosai yasa yaji jikinshi yayi sanyi, duk da ranshi har yanzu a bace yake, domin Yarima namiji ne mai mugun kishi ya wuce duk yanda Mai karatu yake zato..... Janyota yayi jikinshi tare da fad'in plz stop it, bana son jin kukanki, Zainab Ina fushi dake inda kin San yanda nake sonki da kuma kishin ki da Idan wani namiji yazo inda kike zaki nuna mishi ke kurma ce, yanda ma bazaiji sautin muryanki ba, inda banzo a time ba only god knows what will happen......

Bariki cikin kuka tace Yarima Wlh abunda na fad'a maka gaskiya ne, nace mishi ya fad'a ma mutumin inason ganinshi tunda nace ni matar aurece yace duk da haka a bashi number dina, nayi hakan ne in kazo muje tare dakai amma badan wani ab........

Yarima Aliyu yace ya isa haka mubar maganan yanzu kije gida ki huta, Nasan yau Kin gaji Sosai....

Cikin sanyin murya tace toh amma Yarima baka ci abinci ba??

Yace don't worry, zanci in naje gida....

Kai ta d'aga alaman Toh, tare da fad'in Yarima hope u trust what I said? Nd ina fatan ka hakura?

Yace Zainab plz nace mubar maganan go and rest, muje in raka ki bud'e kofar motar yayi....

Ganin ya fita itama ta bud'e kofar motar ta fito har kofar gidan da tace mishi na y'an uwanta ne ya rakata saida ya Bari ta shiga ciki sannan ya dawo ya shiga motarshi yayi gaba cikin gudu

Bariki kam tana ganin ya wuce ya fito danta nufi inda take, tafiya take tana tunani domin ita bata yarda Yarima ya hakura ba, dan inda ya hakura da baiyi reaction haka ba, lallai Yarima yana da kishi, duk ranan da yasan wacece ni ban tunanin zai zauna dani a matsayin matarshi koda ya aureni..... Wata zuciyar tace mata kin manta gidan sarauta basa saki, sai an Kama Ka da laifi biyu? Bata san lokacin da tayi murmushi ba wannan tunanin da tayi shi yasa taji karfin giwa tare da kara d'aura dammaran rufe sirrinta har sai ta auri Yarima dan tana sonshi kuma tasan indai ya sani Bayan aure bazai saketa ba tunda ba'a saki...... Yarima Aliyu na tabbata kai mutumin kirki ne, soyayarka a gareni gaskiya ce kaman yanda nima nake maka, Idan na tuna abunda ya faru dani Ina takaici, tabbas Yarima ni Nasan baka dace dani ba, kafi karfina domin irin rayuwar mu ba d'aya bace, duk shirin da nakeyi na auranka Inayi ne kawai amma bawai dason raina ba, ina ganin kaman zan cuceka ne Sonka yasa na zama mai son kaina, ban taba tunanin duk duniya akwai wanda zan boyema halin da nake ciki ba tunda har iyayena sun sani kuma sun kasa yin komai akai, duk da ransu yana baci amma babu yanda za suyi domin burina in rama abunda sukai min na rashin d'aukan kaddaran daya fad'amin...... Jin ana mata magana yasa ta waiga

Driver din alh madu ne yake mata magana, yace sannu hjy tun dazu nazo ai inata jiranki, mai gida yace ya kira baki d'aga waya ba, gashi hjy babba wayanshi shima baya d'aga wa.

Bariki tace Indai wajan hjy babba kazo yana filin rawa Nasan zaka iya dubashi a can , Tana fad'in haka tayi gaba ......

Binta driver din yayi yana fad'in a'ah Wajanki nazo oga yace inzo in d'auko ki sai yasa nazo.......

Bariki tace kaje kace Mai nace bazan zo ba, and kuma daka rana irin tayau karya kara kirana domin ni yanzu Allah ya shiryar dani na daina wannan banzan rayuwar aure zanyi

Driver din alh madu yace Kai Alhmdlh Wlh naji dad'i Sosai, dama Wlh tunda na ganki naji Ina takaicin wannan rayuwar da kikeyi gaki yarinya karama amma babu daman inyi magana karki fad'ama oga ya koreni, wlh Ina takaicin wannan abunda yakeyi Wlh sai muje garin abuja muyi wata biyu uku amma baije yaga iyalanshi ba, sai dai wancan macen tazo wancan tazo ta sameshi a guest house dinshi, ni Kece ma naga yana bi kina Mai wulakanci, gashi mutum ya girma Mai yakon yabi Allah yaita istigfari amma shi ina kullum hanyar bata ita yake bi

Bariki tace Allah dai ya shirya, nidai ka fad'a mishi sa'ko na, Tana fad'in haka tayi gaba

Driver din alh madu yace Kai Alhmdlh Wlh naji dad'i Sosai, yanzu kam zani in fad'ama wannan tsohon banzan sa'kon yarinyar nan





*********
Yarima Aliyu saboda gudun da yayi kaman zai tashi sama 20mnt ne ya kaishi Zaria, Allah ya taimakeshi ya sauka lafiya, domin gudun fitan rai yayi yana tuki yana tuna abunda wanna yaron yazo yana cewa *he said that you can come he is waiting for you* Yarima Aliyu Wanda yaga Abun a matsayin kaman Zainab ta raina shine dan taga yana Sonta da yawa tsaki yaja tareda shiga gefenshi inda yaga gimbiya zinatu a falo tana zaune tana danna waya tasha wata doguwar riga y'ar kanti yayi mata kyau Sosai, kauda idonshi yayi daka kanta kaman bai ganta ba...

Tashi tayi da sauri ta nufeshi tare da rungume shi tana fad'in Yarima inata kiranka baka d'auka ba, tun dazu nake cikin damuwa tare da fargaban Allah yasa lfya

D'an janyeta yayi daka jikinshi tare da fad'in plz allow me to go and rest ,gaba yayi abunshi

Gimbiya zinatu binshi tayi da ido alaman Mai yake nufi, kodai ya gano gaskiyan al'amarin ne? Kai a'a bazai taba ganewa ba domin jinin daya gani zai sa ya tabbatar da ita budurwace, kafada ta d'aga alaman shiya sani Nasan wani wajan ne aka bata mishi rai, chatting dinta taci gaba dayi ita da gimbiya Amina.

Yarima kam yana shiga bedroom dinshi wanka yayi tare dasa jallabiya, ya fito yaga gimbiya nata danne danne dan tsaki yaja mara sauti yakan yi mamaki Idan yaga mutum yana bama waya muhimmanci fiye da komai, danya Lura da gimbiya zinatu Tana son bama waya lokacinta Sosai, dinning ya nufa dan yayi dinner....

Gimbiya ganin ya zauna akan dinning yasa ta tashi ta danna wani abu saiga kuyangi nan sun shigo, sun San abunda za suyi dan haka shi suka farayi zuba ma Yarima abinci, Bayan sun gama suka bar wajan, Yarima Fara ci yayi amma baya jin dad'in abincin dan ranshi a bace yake, yau princess dinshi ta bata mishi rai Sosai, gimbiya zinatu zama tayi itama akan dinning din tare da kura mishi ido tana kallon yanda yake cin abinci kaman baya son ci...... D'ago kai yayi yaga tana kallonshi a hankali yace stop starring at me like that,

Gimbiya zinatu tace in ban kalleka ba wa zan kalla?

Yarima shuru yayi ba tare daya kuma cewa komai ba, ya rasa mai yasa yake tantama akanta Sosai, abunda yasa har yanzu yake ganin kaman akwai wani abu tare da gimbiya zinatu shine lokacin da yayi sex da ita bai San sanda ya fara ba,hakan yana nuna mishi baya cikin hayyacinshi, yaga Abun kaman mafarki har yake ce mata ita ba virgin bace, abun daya d'aure mishi kai kuma shine yanda ya farka yaga jini a jikinta alaman she is virgin, wannan Abun yana d'aure ma Yarima kai, ido ya d'an lumshe lallai gimbiya she is a virgin Inba virgin bace taya zanga blood? Bai kamata Ina tantama akanta ba, I have to believe in what I see, tunda if she is not a virgin bazanga blood ba, duk da Nasan bako wace mace bace take zubar da jinin budurci kuma budurwa ce, but da yake Allah yana son nuna min sai gashi ita gimbiya Tana d'aya daka cikin masu zubar da jini a daren farkon su, sabanin wasu matan dasu baya zuban musu kuma suma virgin ne, ba lallai bane Idan jini bai zuba ba ace mace ba budurwa bace, wata baya zuba wata yana zuba, shi budurci ba daka jini yake ba, yanda kaji cikin mace Idan ka shiga zaka jishi a matse tun daka farko har ciki, wannan shine budurwa, wacce kuma ba budurwa ba koda tayi matsi ana ganewa, domin wajan ne zai matse cikin kuma yana shiga yaji kaman ya fad'a rami, dan haka y'an mata ku daina rud'an kanku kuce AI akwai magani

Please Login or Register in order to submit comment