Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mishi zaki ganshi sai ki watsa min kasa a ido kisa ya dinga min kallon karaman mace, da mutunci na kisa ya daina gani.

Bariki tace naji Toh zan ganshi saboda ke amma fah Indai dan yazo ne yasa wannan karaman ayabar tasa cikin gindina karma ya fara.

Hjy babba yace oh ni zata lalatani Kinga Bari inyi gaba tunda sauran mutunci na, gaba yayi yana rangwada.

Bariki dariya tayi can kuma tayi shuru tace gobe alhamis jibi jumma'a alh madu zai zo jibi, gobe Ya kamata inga Yarima, Tana shiga d'akinta ta doka ma habib kira tare da fad'in kawata zo d'akina dan Allah tare da kashe wayan.

Ba'a wani dad'e ba saiga habib yazo yana fad'in lafiya wannan kiran kaman na kashe miki wani.

Bariki tsaki tayi tare da fad'in kawata kina da matsala

Habib tabe baki yayi tare da fad'in tsaka ma da tayi Allah tsine Mata yayi.

Bariki tace Ka dai ji dashi.

Tashi yayi tare da ri'ke kugu yace bariki Wlh kina kaini bango zan miki tujara a cikin d'akin nan, yana maganan ne tare da hararan bariki

Bariki tace sorry kawata zauna kiji abunda yasa na kiraki,

Zama yyi tare da fad'in wlh bariki Kar ki bari in miki tujara dan banda mutunci, akan wani dalili zaki dinga had'ani da y'an maza Ina mace na.

Bariki tace Kedai baki da hakuri

Yace zawo ne ni.

Tace ni bari kiji kiran da nayi miki akan maganan Yarima ne, ina son gobe mu had'u a wani Gida zamu hadu?

Habib yace ah Allah sarki kice dan mutunci, karki damu kawai goben ki bashi dama zan shirya komai

Tace an gama, message tayi ma Yarima tare da fad'in gobe insha Allah zamu hadu da yamma.

Habib yace bariki harna kosa goben yayi ki ganshi kiga yanda ya had'u kai inama ni yace yake so Aida na aureshi da yaga yanda ake zuba soyayya🤣🤣

Bariki dariya take Sosai har tanayin kasa dan dariya...... 🤣🤣🤣🤣🤣










~MARYAM OBAM~

*BARIKI NA FITO*




*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*WWW.Maryamobamnovels.com*


*Wattpad @maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*




*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*




*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*




*PAGE 14*



*PLZ KUYI HAKURI DA TYPING ERROR, BANI DA LOKACIN EDITING, NASAN KUNA GANEWA*






Ganin bariki na dariya.

Habib yace miye kike dariya haka? Naga kin samu dama kina son wasa dashi, wlh dani yace yana So da yaga yanda ake zuba soyayya, baki ga yanda ya had'u ba, kai akwai y'an maza kyawawa fah, kaman yanda muma muke jerin kyawawan Mata.

Bariki taci dariya Sosai, sannan ta tsagaita tace yanzu miye Abun yi?

Yace kawai ki zama ready goben, zamu wani Gida saiki fito daka cikin gidan kaman nan ne gidan y'an uwan naku.

Bariki dariya ta saki tare da fad'in Kai kawata kanki naja fah Sosai.

Habib yace Toh an fad'a miki nita wasa ce, wai mai kika kawo mana ne? Yunwa nake ji wlh.

Bariki tace tea nake son sha, Bari in had'a mana.

Habib tabe baki yayi tare da fad'in sai kace wasu 'konannu, Musha tea da wannan daran, bada niba sa lallan kaza.

Bariki tace toh mai kake so? Ni tea din kawai garan indomie nama ta Kare.

Habib yace tashi za kiyi muje wajan mai shayi ya soya mana indomie da kwai.

Tace Kai kawata kije ki siyo mana Wlh na gaji, ni zan fara shan tea Kafin ki kawo indomie din dan Wlh bazan iya jira ba, wani irin shegen yunwa nake ji, kaman hanji na zasu fita.

Tashi habib yayi tare da fad'in kyaji dashi yanzu inda wani tsohon kwarto zai kiraki ai nasan tashi za kiyi ki tafi.

Bariki mi'ka ma habib kud'i tayi tare da fad'in zani mana da gudu Indai ayabarsa tamin, ki siyo mana da kaza.

Habib yace oh Ina mace santaleliyan budurwa zani siyan nama, salan kisa su kwa'kuleni.

Bariki tashi tayi tasa ruwa a heater tare da fad'in dan Allah kije ki dawo.

Fita yayi yana fad'in sabon salon iskanci, sai kace Nina aikeki kije tama d'id'i.

Bariki had'a tea tayi tana sha, jin karan wayanta yasa ta d'auka taga Yarima ne, da sauri ta danna tare da sawa a kunne.

Sallama tayi cikin sanyin murya.

Amsawa yayi tare da fad'in Barka da dare, hope baki Fara bacci ba na tada ki?

Tace a'a bacci tun yanzu, karatu ma nakeyi yanzu Ina shirin in ajiye qur'ani sai ga kiranka.

Yarima murmushi yayi cikin jin dad'i domin duk Sanda zaiyi magana da Zainab dinshi wato bariki sai yaji tana abun islamiya abun addini dai, yace yanzu naga message dinki, so gobe around 2 zaki ganni.

Tace Allah uban giji ya nuna mana goben lafiya.

Ya amsa da Ameen, tare da fad'in ta ina gidan yake?

Tace karka damu Idan kazo bakin titi ka kirani zansa habib ya kawo ku dan ban san yanda zan maka kwatance ba.

Yace ok babu damuwa gimbiya Zainab

Dariya tayi tace Yarima niba Mai sarauta ba amma kaban sarauta.

Yace mijinki ai mai sarauta ne, Kinga Kema sarauniya ce koh?

Uhm kawai tace alaman taji kunya..... Nocking aka fara Mata,

Yarima jin kaman ana nocking yace ba'ki kikai cikin daren nan?

Tace ba'ki kuma ina tunanin mum ce, take nocking Bari in gani.

Yarima yace ok take care tare da kashe wayan.

Tashi tayi ta bud'e kofar.

Habib yace bud'e kofar ma sai an batamin lokaci?

Tsaki tayi tare da fad'in waya nake kin zo kina buga kofa kaman nayi sata.

Habib tabe baki yayi tare da ajiye ledan kayan daya siyo, yace kyaji dashi, bud'e ledan yayi ya d'auko indomie ya fara ci.

Ita kam bariki Naman ta d'auka tana ci tare da fad'in Yarima na yanzu ya kira.

Habib dariya yayi yace amma bariki Keko y'ar duniya har wani suna kika samai Wai Yarima na.

Bariki tace eh mana Yarima na Mai son ustaziya

Dariya suka saki Sosai

Sannan habib yace ai Wlh har na kosa goben yayi ku had'u ku tattauna inga yanda zata kaya.

Bariki murmushi tayi tare da fad'in Nasan muddin na fad'a Mai gskya koni wacece Zaima gudu ne, dan bazan bari ma muyi nisa ba.

Habib yace amma dai Keko anyi mara wayau, akan wani dalili zaki fad'a Mai koke wacece?

Bariki tace kawata ban son in cutar dashi in.....

Habib ya Katse bariki da fad'in ya isa dan Allah ni Kinga saida safe kiyi duk abunda ya dace tashi yayi ya fita yana gantsaro duwawu.

Bariki rufe kofarta tayi tare da fad'in shege kana son in cuta mutum, kai ai saika aureshi, Bayan ta gama abunda take ta kwanta abunta.





***********
Hjy Umaima tunda ta shiga d'aki ta tsure Sosai dakyar nutsuwa ta dawo mata tare da fad'in yau na d'auko ruwan dafa kaina, oh Allah ya soni na tsallake Rijiya da baya, wannan kyan nata ai dole aljanu su shigeta, kasa fita tayi dan tsoro ranan ko bacci ta kasa, tana tsaye wajan window da safe taga bariki ta fita, tana ganin haka ta kira security tace karsu bari yarinyar nan data fita yanzu ta kara shigowa.

Suka amsa da ok ma.

Kiran Hjy habiba tayi tare da fad'in kawata jiya naga bala'i yarinyar nan dana tawo da ita ashe aljanu gareta, baki ga yanda tamin ba Wlh nayi mugun tsorata.

Hjy habiba tace Innalillahi, ya kuka kaya?

Labarin abunda ya faru hjy Umaima ta bata.

Hjy habiba tace Allah ya kyauta ga yarinya kyakyawa, toh amma sai naga kaman y'ar hannu ce, kawai dai Nasan an sami matsala ne aljanunta suka tashi, amma bari in tambayi daughter na, tashi tayi ta nufi falo inda haulat ke zaune tana breakfast, tace haulat Wai bariki kawarki tana da aljanu ne?

Haulat dariya tayi tare da fad'in injiwa?

Hjy habiba ta bata Labarin abunda hjy Umaima ta fad'a mata.

Haulat taci dariya Sosai sannan tace bariki ko y'ar iska, toh Wlh bata da komai, nidai Ina tunanin bata lesbians dan zama na da ita ban taba ganinta tayi ba, ita kawai barta da bin mazanta.

Hjy habiba tace kenan tayi ma Hjy Umaima hakan ne danta kwaci kanta, Allah ya kyauta itama Hjy Umaima ta cika jaraban tsiya Wlh tana da y'an mata kala Kala, amma daka taga wasu ta dinga rawan jiki kenan Allah ya kara mata Kinga aita had'u da cikakkiyar y'ar bariki tayi maganinta ta rage zari ai yanzu....

Haulat ganin hjy habiba nata surfa bala'i yasa ta tashi ta nufeta tare da saka bakinta cikin na hjy habiba ta Fara tsotsa sunyi wajan minti biyar sannan haulat ta cire bakinta cikin na hjy habiba tace mumy wannan fad'an fah haka?

Hjy habiba data fara tsumuwa tace Wlh baby raina ne ya baci ta cika kwashe kwashe, tace muje d'aki daughter sha'awar ki nake Sosai haulat tace muje mum tun daka nan suka fara she'ke ayarsu.





********
Habib ne bakin titi daka gani yana jiran wasu ne, sai faman tabe fuska yake da baki a dan dole shiga mace, yana nan tsaye yaga jerin motoci har biyar kobai tambaya ba yasan Yarima Aliyu ne, gyara tsayuwa yayi da kyau yana d'an murmushi, dai dai inda habib din yake motar da Yarima Aliyu ke ciki ta tsaya, glass din motar aka bud'e driver din Yarima ya gani d'aure fuska habib yayi tare da fad'in mai ba'kin hali.

driver din murmushi kawai yayi tare da fad'in kaje motar gaba danka nuna mana gidan.

Habib bai kuma cewa komai ba yayi gaba aka bud'e Mai motar ya shiga, dai dai kofar wani Gida suka karasa gidan ginin kasa kana ganin gidan kasan basu da karfi.

Idon Yarima ya sauka a kofar gidan, gaba d'aya yaji jikinshi yayi sanyi da ganin gidan, tare da fad'in my princess bata dace da zama a nan ba, Sosai yaji tausayinta tare da kara Sonta.

Bayan sun tsaya habib ya fita ya nufi motar Yarima inda driver din Yarima ya fito ya bud'e Mai, habib shiga cikin motar yayi a gaba ya zauna dan Yarima yana baya, kallon Yarima yayi yana wani murmushi tare da fad'in Barka da zuwa Bari inje in kirata.

Yarima amsawa yayi da yauwa, da fatan kana lafiya?

Habib har wani fari yake da ido yace eh ranka ya dad'e, tare da bud'e motar ya fita, kallon driver din Yarima dake tsaye yayi ya banka mai harara tare da fad'in munafuki.

Yarima Aliyu yana mota yana kallonsu ya rasa mai yasa baya son habib, kodan yana hulda da wacce yake so ne oho, kuma ya tabbata badan uwanta bane....

Yana cikin wannan tunanin ya hangota ta fito ita da habib cikin hijab, idon Yarima na kanta yana kallon kyakyawan fuskanta duk da batai makeup ba dan dama ita ba ma'abociyar yin kwalliya bace, Yarima Aliyu kallonta yake har suka karaso inda yake

habib ya bud'e mata motar alaman ta shiga.

dan cijewa tayi alaman bazata iya shiga ciki ba.

Habib yace Zainab kiyi hakuri ki shiga yanzu kawu zai dawo, kuma Kinga ba mutunci bane ku tsaya a waje koh?

Shiga tayi ta zauna gabanta taji ya fad'i da taga Yarima, wani irin mugun kwarjini taga yayi mata, zuciyarta ta Fara buga mata da karfi, duk kallonshi da takeyi ta gefen ido takeyi.....

Yarima Aliyu yace tsarki ya tabbata ga Allah da yayi wannan halittar.

Kanta tayi kasa dashi tana wasa da y'an yatsun hannunta alaman kunya, tace Barka da zuwa, ina wuni.

Yarima idonshi na kanta yana kallon bakinta yanda take magana cikin nutsuwa yace lafiya kalau my princess, d'an shuru yayi yana kallonta wani irin sonta yaji yana fusganshi... A hankali ya kira sunanta da zainab

D'ago dakai tayi suka had'a ido da sauri tayi kasa da kanta.

Murmushi yayi tare da fad'i cikin ranshi tana da kunya Sosai, yace Zainab da farko dai sunana Aliyu mu biyar ne wajan dad dina nine namiji guda d'aya da iyayena keda shi, zainab na dad'e Ina sonki tun ina secondary school....

Da sauri ta d'ago ta kalleshi domin abunda yace ya bata mamaki Sosai, Anya Yarima bai sanni ba kuwa?....

Katse mata tunani yayi da fadin tun ina skul nake ganinki cikin mafarkina tun ban d'aukan abun da muhimmanci harna Fara d'auka har takai ta kawo na Fara zana hotan jikin ki, dan ban taba ganin Fuskanki ba, domin kina zuwa min cikin duhu ko kuma kizo min sanye da nikabi, danna wayanshi yayi yace kalla ki gani.....

D'ago dakai tayi tare da kallon wayan gabanta taji ya fad'i nuna mata hotan yake amma duk babu fuskanta akai sannan duk colour din hijab din duk tana dasu, harda wani farin hijab Wanda take dashi Mai leshi a wajan kan, tana kallo tana mamaki ya fara nuna mata Wanda akwai fuskanta akai, da sauri ta kalleshi ganin idonshi na kanta yasa tayi kasa dakai sannan tace duka duk Kalan hijjabai nane, abun yaban mamaki.

Yarima yace Zainab Nayi imani had'uwa na dake had'in Allah ne, tun sanda nake mafarkin ki nake ta fama da sonki tare da burin ganinki, sau d'aya na ganki a bakin hanya na tabbata Kece domin da jikin ki na ganeki.

Bariki tace hakane Abun yaban mamaki

Yarima Aliyu yace ba'a mamaki da ikon Allah Zainab, ina son in San koke wacece.

Bariki shuru tayi ga gabanta dake ta faman fad'i...... Muje zuwa muji bariki gaskiya zata fad'ama Yarima Aliyu ko akasin haka......










~MARYAM OBAM~


*BARIKI NA FITO*




*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*WWW.Maryamobamnovels.com*


*Wattpad @maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*




*MARUBUCIYAR*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*11)MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*AND NOW.... BARIKI NA FITO*




*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*




*PAGE 15*






Jin tayi shuru yasa Yarima Aliyu fad'in, lafiya kuwa?

'kago murmushi tayi tare da fad'in sunana Zainab musa haifaffiyar garin kaduna, gidan mu yana u/kanawa mahaifina yana sana'ar rini, duk da bashi da karfi ya bamu tarbiya dai dai gwargwado sannan har yau yana kokari wajan bamu tarbiya, mahaifina Talaka ne amma yana da Kawa zuci, zaiyi abunda wani mai kud'in ma bazai iyayi ba, mu biyu iyayena suka mallaka sai yasa duk wani burinsu da kudirunsu yake kammu nida dan uwana, wajan ganin mun sami rayuwa mai in ganci kuma Alhmdlh tunda yau saukan mu ranan sati mai zuwa insha Allah zan haddace al'qur'ani Mai girma, shi yayana mai suna Saddiq ya dad'e da sauke al'qur'ani, sannan fannin boko inada matakin secondary domin mahaifina bazai Bari Inci gaba da karatu a gidansa ba sai gidan mijina, wannan dai shine labari na.

Yarima murmushi yayi sannan yace y'an Zaria ne kenan ku?

Gabanta taji ya fad'i dan in tace su y'an Zaria ne toh a wace anguwan? Kai a'a da sauri tace a'a mahaifina dan Kano ne domin a can aka haifeshi, tun yana dan shekara Goma sha biyu ya dawo kaduna shida iyayensa har Allah ya musu rasuwa inda mahaifina ya fara buga buga har yakai da yayi aure aka haifemu a garin kaduna, toh Kaga inda aka haifa mutum toh nan ne garinsa.

Murmushi Yarima Aliyu yayi tare da fad'in hakane,. Yace Zainab naji dad'i Sosai da naji tariyin ki, babban abunda ya kara burgeni daya kasance princess dita maddaciyan al'qur'ani ce, Allah yasa ya amfana al'umma

Tace Allahumma Ameen Yarima na..... Shuru tayi domin jin Kalman daya fito daka bakinta....

Yarima da sauri ya kalleta domin irin Sunan take kiranshi cikin mafarkin shi, yace Zainab plz say it again

Jin tayi shuru kanta na kasa yasa ya kamo hannunta da take wasa dashi ya ri'ke hannun duka biyu tare da fad'in plz say it again plz.

Ri'ke mata hannu da yayi yasa komai dake jikinta ya tsaya wannan ne karo na farko da namiji ya taba, taba mata jiki taji wani abu, danko mazan da take iskanci dasu bawai tana jin wani abu bane kawai tana dai yine, amma shi Yarima hannunta ya ri'ke yasa tana jin wani abu tun daka tsakiyar kanta Kar kasan kafanta, kokarin Fara Jan hannunta tayi daka nashi, amma ta kasa.

Murmushi yayi tare da fad'in sai kin fad'a min abunda nace zan sake ki, a hankali tace Yarima na, ido ya lumshe cikin jin dad'i tare da wani kara jin Sonta har cikin ranshi.

Muryanta da yaji tana fad'in plz ka sake min hannu shine ya dawo dashi daka duniyar tunanin daya fad'a, ido ya bud'e tare da d'auko wani Leda, ciro wani karamin kwali yayi anyi raping dinshi, bud'ewa yayi ya d'auko wani diamond ring, saka mata yayi a hannunta das ya shige kaman an gwada, yace this ring is my heart, ina fatan zaki ri'ke min shi dakyau?

Murmushi tayi tare da saka hannunta a kafanta tana kallon zoban mai shegen kyau Wanda Yarima Aliyu ya kira da zuciyar shi ce.

Ganin idonta nakan zoban tana kallo kobai kara cewa komai ba yasan ya samu shiga.

A hankali tace Yarima wannan ring din bai dace dani ba, hawaye ne ya fara zuban Mata Sosai

Ganin haka hankalin Yarima Aliyu ya tashi Sosai tare da fad'in Zainab mai yasa kika fad'i haka?

Cikin kuka tace Yarima ni dakai bamu dace ba baka dace dani ba kafi karfina ba Irina ta dace dakai ba nasan in.....

Dakatar da ita yayi tare da fad'in ya isa haka zainab. Tissue ya d'auko ya fara goge mata hawayen da takeyi yace kalla yanda kika batamin Fuskanki da hawaye, yana maganan ne yana kallon ta, yace Zainab shi so babu ruwanshi dako Waye mutum, Zainab ina sonki dagaske bada wasa ba, tun Kafin in ganki nake sonki tun cikin mafarki na, bana tunanin akwai abunda zai saka in daina sonki, zainab yau had'uwa na dake da nayi na fuskanci abubuwa da dama, kina da addini kin fito gidan mutunci iya wannan ya isheni, zainab duk irin yanda nake son matar da zan aura ta kasance kina dashi, ina da kishin abunda nake so, ina son mace Mai suturta jikinta Wanda ke gashi ko a cikin mafarki na da hijab kike zuwa har a zahiri ma da hijab na ganki, wannan abubuwan ya isa duk wani namiji yayi burin samunki a matsayin matar auransa kuma Uwar y'ay'ansa, I don't care ko daka ina kika fito ke nake so bawai wani abuba, inda kin San yanda nake jinki a raina da baki tunanin wani abuba so plz karki kara fad'in ni dake bamu dace ba, d'an matsawa yayi kusa da ita yace kalleni kiga bamu dace ba? Ganin taki d'ago kai yasa yayi murmushi yace ban taba ganin couple din da suka dace ba kaman ni dake.

Bata san lokacin da dariya ya sakar mata ba domin maganan shi ya bata dariya.

Ganin tayi dariya shima yayi murmushi tare da fad'in yauwa na saki dariya am happy now.

Murmushi tayi tare da fad'in babu kyau son Kai, ai bakai zaka fad'a ba wani ne zai fad'a yace mun dace ko bamu dace ba.

Murmushi yayi tare da fad'in Toh Kema ya akayi kika san bamu dace ba?

Kanta na kasa tace saboda naga haka dinne.

Shima yace nima na fad'i hakan ne dan Ina ganin mun dace

Murmushi tayi

Sunanta ya kira yace Zainab Ina son fad'a miki magana Mai muhimmanci.

Gabanta taji ya fad'i, amma saita daure tace inaji.

Yace biki na ranan Friday din nan rana ita yau.

Dam taji gabanta ya fad'i Wanda bata san dalili ba tare da kallonshi da sauri ganin Sun had'a ido domin shima ita yake kallo yasa tayi kasa dakai.

Yace Zainab iyaye na sun sha bani mata amma naki yarda burina kullum in ganki dan muyi aure sai yasa bana yarda da duk wani zabin iyayena, mahaifina ya gaji da zama na haka babu mata, musamman daya kasance nine d'ansa namiji guda d'aya yana bukatan ganin jikansa, sai yasa ya yanke bani auran y'ar sarkin katsina gimbiya zinatu, bayan na amince da auran domin ko ban amince ba dole Ayi tunda mahaifina bada wasa yake ba, kawai sai na ganki keda wancan guy din ya nuna mata habib dake waje yana hararan driver dinshi, Zainab na fad'a miki wannan maganan ne saboda ina sonki ban son boye miki komai dake tare dani , ina son Kema ki fad'amin abunda kike ji a game dani.

Bariki kanta na kasa tunda Yarima ya Mata maganan auranshi rana ita yau, ta shiga damuwa wanda ta rasa dalili, ganin yayi shuru ita yake saurara yasa tace ina son ka bani lokaci kad'an inyi tunani akai

Yace Zainab when no one's around but you and me. A lokacin zaki iya tunanin mai kike ji a kaina. Kiran sunanta yayi cikin wani irin murya

d'ago dakai tayi suka had'a ido da sauri ta sauke idonta ta rasa mai yasa bata iya kallonshi gabanta faduwa yakeyi Sosai, jin hannunshi tayi akan nata.....

Yace my princess zan baki lokaci amma fah bamai yawa ba, kwana biyu kawai na baki kiyi tunani akai na Zanzo inji amsa daka gareki.

Kasa motsi tayi sai gabanta dake faman dukan uku uku, Mai yasa na kasa fad'a mishi abunda Nayi niya Mai yasa bana jinshi kaman sauran mazan da nake hulda dasu? Mai yasa ya banbanta dasu? Ga hannuna a ri'ke da nashi amma na kasa yin abunda nayi niya ido ta lumshe domin ta rasa amsan wannan tambayan nata .

Ganin tayi shuru yasa yace my princess karki manta kwana biyu na baki Zanzo inji daka gareki jibi kenan, sannan Saturday shine ranan waliman ki koh?

Kai ta d'aga alaman eh.

Yace Allah ya nuna mana ranan, jin kiran sallah la'asar yasa yace bari muyi sallah sai mu kama hanya.

Tace toh Bari a kawo maka ruwa, bud'e motar tayi ta fita cikin gidan ta shiga da sauri habib yabi bayanta..

Tana ganin habib tace yauwa Kai ma Yarima ruwa yayi alwala, amsa yayi ya fita tare da kaima yarima ruwan

Sannan ya koma ciki, inda ya sami bariki na sallah itama, zama yayi yana jira ta idar, Bayan ta gama.

Habib yace ya kukayi?

tace Kai baka je masallacin ba, d'aure fuska yayi tare da fad'in in banda rashin mutunci kin taba ganin mace a masallaci? Gskya banso.

Bariki tace Allah ya shirya, jin wayanta yayi kara alaman sa'ko ya shigo yasa ta duba taga Yarima ne yayi mata message *come out my princess* murmushi tayi tare da tashi ta d'auko jakarta ta fesa turare sannan ta fita, motar ta bud'e ta shiga inda ta ganshi zaune yana waya taji yana fad'in lil yanzu zan dawo nace kuyi komai keda usman Kafin in dawo, kashe wayan yayi sannan ya kalli bariki

Yace my princess zan tafi, sai nake ji kaman mu tafi tare.

Murmushi tayi tare da fad'in in lokacin hakan yayi zamu..... Da sauri tayi shuru dan maganan da taji tana niyan fad'a

Ganin tayi shuru yasa Yarima Aliyu yayi murmushi tare da fad'in ina ji karasa abunda kikai niya.

Hannunta tasa a fuska alaman jin kunya

Yarima dariya yayi Sosai abunda bai taba yima wani ko Wata ba sai yau, d'auko wani card yayi ya bata tare da fad'in plz in kin shiga Gida ki turomin Abokina habib

Tace toh har zata fita ya kira sunanta waigowa tayi

Yace Zainab Waye habib a wajan ki?

Tace d'an uwana nane yaron kanwar mama nane.

Yarima yace ok na gane I love you

Dariya tayi tare da fita da sauri tayi cikin gida.

Ko minti biyu batayi da shiga ba saiga habib yazo, yarima wani Leda ya bashi babba tare da fad'in kaba ma my princess wannan, wata karaman Leda ya d'auko tare da bama habib yace ga naka.

Habib amsa yayi yana ta godiya sannan ya fita

Su Yarima hanya suka kama yana kallon gidan da zainab dinshi take har suka wuce.

Koda habib ya shiga gida bama bariki sa'kon da Yarima ya bata yayi, bud'e nashi yayi yaga agogo Mai shegen tsada da kud'i dubu d'ari biyu ihu ya saki tare da fad'in oh wannan koh dan arziki. Ganin bariki tayi shuru kaman mai tunani yasa yace bariki lafiya kuwa?

Please Login or Register in order to submit comment