Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

IBTISAM......
(.........In Between)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

*Free Page*

*Na Kudine ki Bada 500 ki cafki garabasar novel bakwai da program Uku*

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin kai....
Daga gareshi muka zo gareshi zamu koma, Allah ya bani ikon rubuta abinda zai amfani jama'a ya kuma tsareni da rubuta abinda zai gurbata al'umar ma'aiki Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi Wa Salam....(Ameen)


*mg's skincare*

Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaranjiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare duk wnd yy using set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali😘just start placing ur orders dearies DNT be left behind
Available product👇
Herbal whitening black soap:3k
Beauty kit:11k
Blacksoap/molato whitening soap: 3500
Bridal kit:20k
Muna maraba da masu siyan daya ko sari
Chat
08062991549
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩
Then @mgs skincare gat you covered 💯
Now is time to glow😍
Pamper ur skin🦵
Shine like bride👰🏻‍♀
Glow🧖‍♀�?

💯 tested nd trusted🤝
Guarantee

Sannan munada frames masu kyau shima siyan daya ko sari 07046881166
08062991549

Sannan gamai bukatan abinci, cakes,meatpie,samosa nd spring rolls, traditional juices nabiki shima yy hanzari yy mgn 08062991549
Mungode🤝

Shafi na Farko. 🤸🏼‍♂�?

     KANO STATE (BUK NEW SITES)

  Sanye take da doguwar rigar abaya, ta yane kanta da mayafi dark purple, hannunta dauke da handbag irin babbarnan, wacce ke cike da litattafai, kafarta wani flat shoe ne kalar mayafinta. Doguwa ce sai dai ba irin cancan ba, fatarta ba mai haske bace haka kuma bamai duhu bane, batada jiki dan a koda yaushe Mamanta fada take mata akan rashin maida hankali gun cin abinci, tana ganin kamar shi yasata rama.
Gefenta kawayenta ne wanda da alama tare suka fito daga lectures, suna tafe ana hira ana dan shewa, suna kokarin shan kwana tai trus taja ta tsaya tare da kurawa wani bangare daga can nesa kallo da idanunta. Runtse idanunta tai a kuma take yanayin fuskarta ya canza, kallan gun sukai suka kalleta sai suka sheke da dariya a tare harda tafa hannu. Fuskarta a daure tace "Dalla dariyar ku kuma ta menene?" Wacce ke kusa da ita tace "Ibtisam anya mutumin can ba ya wadudu kikamai ba? Mutum kamar mara aikinyi sai bibiyarki?" Dan karamin tsaki taja tace "Ainah bansan iskanci, dadinta dai yayana ne in ma da biyu kikai maganar."
Dayar ta sa dariya tace "Wannan ko cikinku daya ai cewa zamuyi bashida lafiya balle kiri-kiri duk munsan sanki yakeyi." A ranta tace ni wannan soyayyar tun kafin ma aje ko ina ta isheni. A fili kuwa kallansu tai kawai tai dan murmushin yake, dan batasan ma me zata kuma ce musu ba.
Fara tafiya sukai tare da daga mata hannu alamar bye-bye, itama dan daga musu tai tace "Sai gobe in Allah ya kaimu."
A hankali ta fara takawa zuwa inda yake sam fuskarta babu fara'a, hannunta yadan daga ya rike jakar dake kafadarta, hakan yasa dan saman hanunta ya fito.
Shikam tunda ta taho ya kafe ta da ido yana jin wani azabar santa na sake ratsashi, idanunsa ne yakai kan hannunta sake waje, a take ya daura fuska tamau, harta karaso gun bai dauke ido daga kanta ba.
Cikin dan sanyayen murmushi wanda kana gani zaka fahimci bai kai zuci ba tace "Yaya ina wuni?" Kallanta kawai yake ya kasa amsawa, itakam wannan kallan na bala'in kular da ita, can ta daure ta sake cewa "Yaya!"
Cikin daurewar fuska ya juya ya kalli gefe da gefe ganin ba namijin dake kallanta yasa yadanyi ajiyar zuciya yace "Ba ba kiga hannunki a waje ba?"
Kallan hannun tai sannan ta saukeshi wani abu ya kara tokare mata magogwaro.
Fuskarsa haryanzu a daure yace "Na na na siyo miki hijabai kinki sakawa yanzu ina amfani haka?"
Bata tankashi ba dan batasan ranta ya baci yanzun nan.

Murmushi ya mata ganin yanda ta kawar da kanta yace " Kun kun fito lafiya?" Kai tadan daga kafin su fara tafiya a tare, ba wanda yai maganar sai tafiya kawai da sukeyi, can ta daure tace "Yaya nikam me yasa kullum kake jirana? Baka tsoron randa Abba yaji ya maka fada? Yace baka maida hankali kan aikinka?"
Tafi kowa sanin halinsa magana baya yinta mai tsayi sai azabar zuciya kamar me. Cikin dan maganarsa mai dan in-ina kadan yace " Ib Ibtisam hankalina ba-baya kwanciya in ba zuwa nai na rakaki gida da kaina ba."
Wannan abu itakam ya isheta, da batasanshi ba wlh da tuni sun hau sama sun fado, ace namiji tunkafin ya aureka yabi ya takurawa rayuwarka? Matsalar daya dan uwanta ne tana tunanin abinda zaije ya dawo, dan a yanda yake ba abinda bazai iya aikatawa ba in ta wulakantashi.
Sun dan yi tafiya kadan, suka iso gate din makaranta, daga baya taji ana kwalla mata kira, kafin ta juya shiya fara juyawa, fuskarnan tasa a daure kai kace makiyinsa ya hango. Juyawa tai tadan fara komawa kadan tana kallan saurayin dake gudu yana neman tarosu.
Dan hannu ta daga mai kadan alamar ya tafi a hankali, nan ya karaso yana hakki fuskarsa dauke da dariya yace "Book dinki." Yai maganar yana mika mata, ta amsa tana dan murmusawa tace "gudun duk na menene? Ka jira gobe ka bani mana?"
Dan bayan kansa ya dan sosa yace "Ban isa ba, kin ban aran note dinki ai dole na dawo dashi da wuri dan a sake bani aro nan gaba."
Zata sake magana ya kalli saurayin da ya hade fuska a bayansu kamar mai shirin dambe harda dunkule hannu, yace "Hmmm! Wannan saurayin naki har tsoro yake ban, ji yanda yake kallona kamar wanda nake kokarin kwace masa ke." Bata kalleshi ba tace " Nagode! Sai gobe."
Ta juya ta fara tafiya, tana isowa inda yake ta kalleshi tace "Yaya mu wuce?" Ai kamar ta taboshi nan fa ya fara zabga mata masifa kamar zai daketa, "Ke baki da aiki sai yiwa maza dariya? Sannan uban wa ya hanashi yin note? Bama wannan ba meyasa bazai ari littafin a gun namiji dan uwansa ba? Kina irin wannan ta ina zan yarda dake? Ta ina zan kwantar da hankalina? Ni wannan makarantar ta isheni sam ta hanani sukuni kullum tunanina me kikeyi? Da wani namijin kike magana, haba! Ni na gaji wallahi da kin aureni kafin ki fara bazan ma soma barinki ba."
Baki kawai ta bude tana kallansa, yau kam ankaita makura, ko mahaifinta bai taba tsareta yana watso mata tambayoyi haka ba, wato da alama wannan in akai auren ma bazai barta ta gama karatunta ba.
Cikin matukar kunar rai tace "Yaya ni na tilasta ka soni? Ko kuwa rokanka nai? Akan me soyayyarka zata nemi haukatani? Ka hanani sukuni, kawaye wannan bana zama dasu muyi magana, kullum kana tsare dani, biki wannan ko ziyarar kawayena ban isa nai ba sai dai ka tasani a gaba kamar 'yarka, taya mahaifina bai tsawalawa rayuwata ba saurayin da ba mijina ba zai takuramin? Wannan ko na aureka zargi ma bazai bar auranmu yai kargo ba........."
"NI KIKE WA MAGANA HAKA?"
Yanda ya daka mata tsawa ne yasa ta kasa cigaba da magana. Kallansa tai yau itama takai iya wuya tace "Dan Allah ka saukakemin wannan soyayyar na gaji haka nan, wannan ko auranka nake zan nemi ka sauwakemin balle....."
Abinda ta fada kenan ta fara tafiya, tana mita, "Haka kawai? Wannan wani irin masifa ne? So ya zama hauka, gaba daya rayuwata an lalatata banda zabin kaina ko ra'ayina?"
Shikam yana tsaye a gun ya dunkule hannunsa, saurayin daya kawo mata book dazu ya kalla, wanda yake ta tafiyarsa, da gudu ya bi bayansa, shikam tafiya yake baimasan ana binshi ba.
Ibtisam ganin shirin yayi yawa yasa tadan juya dan ta tabbatar ba lafiya ba, idanu ta zaro ganinshi daf da yaran dazu, kafin ta gama tunani ya kaiwa yaran wani wawan duka wanda yasashi faduwa a kasa.
A rikice ta fara sauri sauri gudu gudu tana kwalla mai kira ai shikam baisan tanayi ba dukan saurayin kawai yake, ganin yanda ake makarsa yasa yaran ya fara kokarin kwatar kansa.
Mutane sun fara taruwa a gun maza sunata kokarin rabasu. Karasowa tai takaici kawai yasata zubar da kwalla cikin murya ta kunar rai tace "Ya Umar ka bari nace! Na rokeka da Allah." Tai maganar cikin dan daga murya, kallanta yai yana wani huci, ganin tana kuka yasashi sakar yaran ya nufota da sauri yace "Ibtisam menene kike kuka?" Yai magana duk a rikice kallansa tai ji take kamar taita zunduma ihu, juyawa tai kawai ta fara tafiya tana tafe tana share hawayenta.
Binta ya farayi da sauri yanaji saurayin nan na zabgamai Allah ya isa amma baibi ta kanshi ba, tana fita daga school din ta tari adaidaita, cikin sauri ta shiga shima ya shiga duk ya rikice, tafiya suka fara yanasan yi mata magana bayaso mai adaidaita yaji, haka yai shiru yanata maimaita kalamanta na rabuwa data furta mai ba shakka ko za'a mutu a dawo ba wanda ya isa ya rabashi da Ibtisam, ai ko wani ne yai gigin auranta to lalai ya shirya sakinta dan wallahi sai yasa an saketa ya auri abarsa, ko ubanta daya haifeta bai isa ya hanashi auranta ba, tashi ce ita kadai bayaji zai iya rabuwa da ita ba kuma yajin duk duniya akwai wanda ya isa rabasu.

**************
Tsaye take a cikin kitchen, gefenta mata ne guda uku suketa zuzuba waina, sinasir, panke a cikin takeaway suna rufewa.
Kallansu tai tace "Ankusa gamawa kuwa?"
Daya daga cikin masu zuzuba abincin wacce da alama tadan girmi ragowar tace "Ummy ankusa insha Allah!"
Wacce ta kira da Ummy tai dan sansanyan murmushi tace "ina ganin kafin a gama zubawa a fara fita da wadannan ko?"
Matar tace "To shikenan, bari Zulaiha ta fara fita dasu."
Kai Ummy ta girgiza da sauri tace "A'a kuyi aikinku bari Ainah tazo ta fita dasu." Tai maganar tare da juyawa, dan murmushi sukai tabbas suna jin dadin aiki da matarnan a koda yaushe girmamasu take tana basu darajarsu duk kuwa da kasancewarsu 'yan aiki.
Ummy kam daki ta nufa, ta tura kofar tare da sallama.
Ainah tana kwance akan makeken gadanta tana ta daddana waya, dawowarta daga makaranta kenan ta baje akan gado tana chatting.
"Ki ajiye aminiyar taki kizo kiyi aiki."
Juyowa tai tare da ajiye wayar tana dan dariya tace "Kai Ummy yaushe waya ta zama aminiyata?"
"Inba aminiyarki ba mecece? Ki zauna a falo ayi hira dake ma baso kike ba, yau kinfi kowa sanin ranar mecece amma kin shige daki kinata dane danen da kika saba."
Dan ido ta zaro kadan tare da mikewa ta yayo hijabi ta zura tace "Ummy wlh na manta sam, hankalina ya tafi....."
Dan kai ta girgiza tace "Taso ki fita da abincin sadakarnan Mamman yana jira a mota."
Da sauri ta nufo Ummy kafin tace "Ikon Allah sai kallo yanzu wai har Aunty Na'ima tayi shekara biyar da rasuwa?"
Kai kawai Ummy ta daga jiki a sanyaye, Ainah ce ta fita tana gyara hijabin ta.
Fitowa daga dakin Ummy tai sannan ta nufi fallan Abba gaba daya jikinta a sanyaye.
Daga bakin kofar falan ta tsurawa wanda yake zaune akan sallaya ido, matashi ne wanda a kalla yakai shekara talatin da tara sanye yake da farar jallabiya yana zaune akan sallaya yana jan carbi, fari ne dan kana ganin Ummy zakasan ita yayo saboda kalarsu da kamaninsu, ya dan tara kasumba a fuskarsa wanda ta kara nuna girman shekarunsa, gefensa Qur'ani ne da alama ya gama karantawa ne, shiru tai tana kallansa a hankali taji kwalla sun taru a idanunta.
Tana neman juyawa taji ance "Ummy?"
Kallansa tai tare da sakar mai murmushi sannan ta shiga cikin falan.
Zama tai akan kujera tace "Gashican ana zuba abincin a mota, Mamman ne zai kai ko tare zaku wuce?"
Yace "Tare zamu wuce dan Hajiya batajin dadi zan sai mata magani na tafi mata dashi."
Dan yanayinta ne ya canza wato dan ta tura mata sako jiya akan tanasan magana da ita shine yau tace batada lafiya?
A fili ta daure tace "Aminu haka zamu cigaba da zama? Sai yaushe ne zaka sallami matarnan ta koma garinsu? Sai yaushe ne zaka sake aure? Ka nemawa 'ya'yanka guda biyu uwar dazata maye gurbin mahaifiyarsu?"
Yanayin sa ne yadan canza, bata damu ba dan raban da ko murmushi ta gani a fuskar Aminu tun randa matarsa Na'imah tabar duniya tayi tayi ya dawo yanda yake amma inaa abin yaci tura, ta hadashi da mata dayawa sai dai Allah baiyi ba dan babu wacce ta kwantamai. Babbar matsalarta kuma Hajiya wato uwar matarsa data rasu, wacce ke zaune a gidan tun bayan auransa da Na'imah tayi tayi ya maidata kauye garinsu amma yaki, ko kuma tace matar taki dan ta tabbatar itace take karyar ciwo dan karya tabar gidan.
Muryar Aminu ce ta katse mata tunaninta "Ummy dan Allah ki bar maganar Hajiya, matarnan amana ce a gareni ni nake rike da ita tun auranmu da Na'imah taya yanzu zance tabar gidan? Matarnan fa ba lafiya gareta ba?"
Dan ajiyar zuciya tai cikin kulawa tace "Aminu baka fahimceni ba, ni nace ta dawo gurina ta zauna, ko ka nema mata karamin gida ta zauna, dole sai a gidanka? Wace matar ce zata yarda ta aureka bayan tasan zama zatai da uwar matarka? Ko uwar miji ce mata ba so suke ba inaga matar da basuda hadi da ita? Ni na kasa gane wannan masifa, in kai ka kasa sallamarta ita bazatai hankali tabar gidan ba? Ita kadaice zata iya rike yaranka ko me?"
Ganin yanda ran Ummy yadan fara baci yasa yace "Ummy dan Allah mubar maganarnan, matarnan zaman jikokinta takeyi ki barta dan Allah ta kula dasu."
Abinda take yaki dashi shekara biyar ta tabbatar bazai warware yau kadai ba, sai dai tabbas sai ta sa matarnan tabar gidan, dan bata taba ganin inda akai wannan kwamacalar ba, in shi yana ganin ta zama dolensa ita ai tanada hankalin da zatasan abinda ya kamata in har kuma ba wani abin take sakawa a ranta ba.
Duk sa a boys quarters take itadai san bata yarda da wannan zaman ba.

********

Suna sauka daga kan adaidaita tai saurin shigewa gida, biyota yai yana kiran sunanta batako amsa ba tai ciki da sauri.
Falo ta shiga da sallama, karar bude kofa yasa ta kalli gun tare da sakin fuska, da dan sauri ta karaso ta rungume budurwar dake kan keken guragu. Tace "Sisi na."
Murmushi tai tare da cewa "Ki hau sama akwai tsarabar da Iman ta shirya miki."
Idanu ta zaro dan ta tabbatar kayanta ta taba, da gudu ta hau sama hartana neman faduwa ta bankade kofar dakin da karfi batai ko sallama ba.
Baki ta bude tana kallan Iman dake ta daukan hotuna da kayanta, kayan ta kalla akan gado gaba daya sabbabin kayanta data dinka na salla an watsar dasu alamar ansa ancire.
Cikin ihu tace "Wallahi yau sai naga mai kwatarki....."
Iman tana ganinta ta sake wayar ta fara kokarin guduwa, aifa nan Ibtisam ta rufa tana kokarin kamata, da gudu ta fito daga dakin tana kwallawa Ummansu kira, tana saukowa falo taga Umar ta boye a bayanshi tace "Yaya taimakeni wayyo shikenan yau za'ai layya dani." Tana magana tana hakki....
Ibtisam ce ta sauko a sukwane nan fa suka cigaba da guje guje a falo itakam budurwar dake kan keken guragu tana zaune sai dariya take.
Umar kam ji yake kamar ya kamo Ibtisam ya rungumeta saboda tsananin so..... Ba shakka duk randa ya aureta sata zaiyi a gaba yai ta kallo dan shikam baisan irin so da kaunar da yake mata ba.



Ayusher Ce🏌🏻‍♀�?
2/4/22, 11:06 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
      (.........In Between)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

*Free Page*

*Na Kudine ki Bada 500 ki cafki garabasar novel bakwai da program Uku*

*Shafi na Biyu.*

Umma ce ta fito daga daki, ko karasowa cikin falan batai ba Iman ta ruga a guje ta boye a bayanta, Ibtisam ta biya da gudu tana, "Wallahi Umma yau wannan autar taki sai ta gamu dani."
Umma ta kalli Iman ta baya sannan tace "Yahkuri Ibty na kinsan kanwar taki akwai tsokana, karki biyeta kinji? Ke ai mai hakuri ce.�?
Tsayawa tai tare da hararar Iman kamar zatai kuka tace "Allah Umma shiyasa takemin haka, taga duk sanda kika sa baki bana iya yi mata komai."
Cikin murmushi Umma tace "Nan gaba in ta kuma dakaina zan zane miki ita kinji?"
Juyowa Ibtisam tai a take suka hada ido da Umar wanda ya kafeta da ido yana kallo kai kace xai lashe ta, dauke kai tai da sauri ta hau sama tana yan kunkunin abinda Iman ta mata.
Umma ta kalli Iman ta kamo kunnenta daya tace "Na dauka na hanaki daukarwa Ibty kaya?"
'Yar kara tai tace "Nadaina Ummana."
Umar ne ya kalli sama yace "Umma bari na amso sakona agun Ibtisam, da alama tahau dashi sama."
Tana kokarin cemai ai basai ya hau ba ya bari Iman ta amsomai ko a kira Ibty ta kawomai kawai taga harya haye, itakam halinsa na bata mamaki, duk da a gidan ya taso ya kamata yasan shifa saurayine su kuma 'yan mata ne, inda yayi yanzu ai bai kamata ba.
Umar kai tsaye ya tura kofar dakinsu Ibtisam, tana ta ninke kayanta sam bata kawo shi bane ta dauka Iman ce, dan har ta mita, “Allah Iman kinyi na karshe ya isa hakanan kuma.�?
Jin ansa key a kofar dakin yasa ta juyo da sauri, cikin tsananin faduwar gaba ta kalleshi bakinta nadan rawa tace "Ya Umar meye hakan?"
Takowa yai zuwa inda take idanunsa duk sun canza, hannu yasa ya dagota iya karfinsa, jikinta ne ya fara rawa tace "Me kakeyi hakan?"
Jikin bango ya kaita ya matse hannunta biyu wanda zafi da zugi sukasa tadan runtse ido kadan, cikin kakkausar murya yace "Me kikace dazu a makaranta?"
Wani irin bugawa zuciyarta take da karfi tace "Ya Umar wai dan Allah ana so dole ne? wannan wace irin soyayya ce? Dan Allah na rokeka da Allah ka......."
Hannu ya daga kamar zai wanka mata mari ne yasa tai dif, idanunta ta runtse da karfin gaske, jikinta ya kara daukan rawa, sauke hannu yai sannan ya nunata da yatsa yace "Wallahi inkikai gaggawar sake furtamin wannan kalmar ki shirya fuskantar tashin hankali a rayuwarki, na sanar dake ba yau ba bakuma jiya ba, ke tawa ce ni kadai duk duniya ba wanda ya isa ya rabamu. Aurena dake wajibi ne yanda kike sallah biyar a rana haka aurena yazama wajibi, ko da wasa karki kuskura ki karamin maganar nan wannan umarni ne na baki." Yana kaiwa nan ya saketa ya juya ya fita daga dakin tare da banko kofar da tsananin karfi.
Haryanzu jikinta bai dawo daidai ba, tsugunawa kawai tai ta fara wasu hawaye masu tsananin zafi da kuna, itakam ya zatai ta kwace kanta daga wannan bala'in da masifar? Ko zuwa zatai tace Abba ya mata aure da wanda yake so? Dan aure ne kawai zai sa wannan mahaukacin ya kyaleta. Da sauri ta girgiza kai in kuma Abba ya zaba mata Umar fa? In ta fadi abinda yake mata ba lalai su Abba su yarda ba dan Abba ya yarda dashi dari bisa dari kuma batasan adalilinta Abba ya rabu da yayanshi wanda shikadai Allah ya barmai a duniya, duk ‘yan uwansa sun rasu daga shi sai mahaifin Umar. Fuskarta ta shafa tana kokarin mikewa wayarta tai kara.
Idanunta cike da hawaye ta jawo wayar tare da zama a bakin gado, ganin sunan Ainah a alan wayar ne yasa ta dan share kwallarta cikin sanyin murya tace "Ainah!"
Daga can bangaren Ainah cikin zumudi tace "Ibty albishir?" Bata jira me zatace ba tacigaba "Anyi mutumin naki a gidanmu yau, in kawo miki?"
Murmushin yake tai tace "Oh ni Ainah yanzu haka kawai dan ni na kawo san sinasir duniya sai ai abinci a gidanku ki taso ki kawomin?�?

Dariya Ainah tai tace "Ke dai me ya dameki? Sannan sinasir din sadaka ne, yau matar Ya Aminu ta cika shekara biyar da rasuwa.�?
Cikin sanyin jiki tace “Oh ikon Allah! Yaushe yaushe kika kawomin na shekara hudunta a makaranta?�?
Ainah tace “Duniyar ce gudu kawai take, yanzu tunda kinji na sadaka ne in kawo miki?�?
Kai ta girgiza tace “Ki barshi dan Allah, nima jiya naci a gida.�?
Yanayin maganar Ainah ne ya canza da alama taji ba dadi tace “Shikenan.�?
Kamar zata kashe Ibtisam tai saurin cewa “Haushi

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment