Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yace "Shifa, na gama saka number kawai sunanshi ya bayyana a jikin wayata, sannan address din gidan ma ai gidanshi ne."
"Ikon Allah! To ko kasan ma yarinyar? Tunda naga kana zuwa shima yana zuwa."
Baffa ya jinjina kai yace "Yaranshi uku mata, daya kinsan batada lfy, sai ta tsakiyan wacce nake zatan itace dan sa'ar Ainah ce."
Ummy tai murmushi tace "Da alama wannan hadin daga Allah yake, sannan itace matar da muka dade muna fatan Aminu ya samu."
Baffa yai dan shiru kafin yace "Ki bari dai mu hadu dashi muyi magana, kar inje an mata miji."
Kai ta jinjina sannan tace "Dan Allah yanda kukai ka kirani ka sanar dani dan damuwa bazata barni na kwantar da hankali na ba."
Dariya yadanyi yace "In matarsa ce komai zaizo da sauki in kuma ba matarsa bace sai kiyi hakuri tunda dai kinsan wani baya auran matar wani."
Kashe wayar yai kai tsaye ya kira Abba, shikam yana zaune a babban shagonsa yanata lissafin kudin da zai kashe na kayan daki, da gyaran gidan da akeyi. Ganin sunan Sulaiman a jikin alan wayarsa yasa ya dauka cikin fara'a yace "Lalai ka tari numfashi na, ina san kiranka na sanar dakai babban al'amari ashe kai zaka riga kirana."
Baffa yai dariya yace "Kana shago? Inaso zanzo yanzu mu tattauna akwai maganar da nake so muyi."
Abba yace "ina shago in kuma kana ganin ni nazo office dinka to?"
Baffa yai saurin cewa "A'a ai ni na fara cewa zanzo ko?"
Suna dariya sukai sallama akan Baffa zaizo nan da minti ashirin.

Haka ya wuce kai tsaye zuwa kasuwa yana tafe yana tuno haduwarsu a saudia da yanda suka zama abokai, dakin Abba na kusa dana Baffa a hotel dinsu, komai tare suka yishi, ko sarin kaya da Abba zaiyi shi ya rakashi sukaje, bayan sun dawo sun cigaba da zumuncinsu, duk dadai zumuncin maza sai lokaci zuwa lokaci amma duk da haka suna kokarin haduwa.
Abba cikin tsananin murna ya tarbeshi ya zauna akan kujera yana kallan katan shagon, wasu laces ya kalla yace "Da alama ya kamata kafin na tafi na saiwa Uwar gida da Amarya tsarabar zuwa kasuwa."
Abba yana dariya yace "In baka siya ba ma duk sanda naje gidanka zaiyi gulmar kazo bakasainmusu komai ba."
A tare sukai dariya kafin Baffa yace "Me kake san kirana ka fadamin?"
Abba ya fadada murmushinsa yace "Sulaiman nan din shirin auran 'yata nakeyi, ina sa ran nan da sati biyu a daura, tunda 'yar gida zanyi a hankali a karasa gyara da wasu abubuwan."
Jikin Baffa ne yai sanyi a ransa yace "Ba rabanmu bace."
Abba ne ya katsemai tunaninsa yace "Kasan Umar ai ko? Yaron da na rike? Wanda yake zaune da a shagon nan?"
Baffa yace "Umar? Na ganeshi ko ba yaran yayanka ba?"
Cikin jin dadi yace "shi! Shine zan hadasu da Bilkisu."
Fuskar Baffa ce ta bayyana da fara'a yace "Kai masha Allah! Amma na tayaka murna, ita ta tsakiyar fa?" Da saninsa yaki fadan sunan Ibtisam saboda yana san tabbatarwa kansa itace wacce Ummy ke magana.
Abba yana murmushi yace "Ibtisam?" Baffa fara'arsa ya fadada yace "Eh!"
Kai yadan girgiza yace "A'a sai fatan Allah ya kawo nagari."
Baffa yadan gyara zamansa yace "Audu bansan ya zaka dauki abin ba, na kuma san Aminuna ya mata girma amma me kake ganin in muka hadasu aure?"
Abba yai dan shiru kafin ya kalleshi yace "Aminu?"
Baffa ya daga kai, Abba ya danyi dariya wacce ta dan kwantar da hankalin Baffa yace "Aminu dai Aminu?"
Tambayar tadansa jikin Baffa yin sanyi, jiyai yace "Sulaiman kasan yanda nake san hada zuri'a dakai? Balle Aminu wanda a koda yaushe nake kainar hankali da nutsuwarsa, tunda na ganshi nasan lalai kayi dacen d'a ga tausayinsa da nake daka sanar dani rasuwar matarsa da halin da ya shiga na rashinta."
Baffa dadi ne yasa ya rasa abin cewa sai hanun Abba kawai daya kamo.
Abba cikin jin dadi yace "Da alama kwanciyar hankali ce tazomin, ban taba tunanin Umar zai yarda kai tsaye da auran Bilkisu ba gashi ya yarda sannan ban taba kawo Ibtisam zata samu miji kamar Aminu nan kusa ba sai gashi ta samu. Sulaiman Allah ne kadai yasan dadin da nakeji."
Baffa dadi ya kamashi yace "Amma kana ganin yarinyar zata amince?"
Cikin sauri ya daga kansa alamar eh yace "Ibtisam yarinyace mai biyayya da hakuri, ban taba ganinta da ko saurayi ba, ita ba zuwa gidan kawaye take ba, batada rawar kai irin na yaran zamani, na tabbatar bazata taba kin namiji kamar Aminu ba."
Hamdala Baffa ya fara ji yake dadi duk ya rufeshi, Abba ya kalleshi yace "In har na sanar da ita ta amince ka kuma sanar da Aminu shima ya amince me kake gani in muka daura musu aure tare a ranar da za'a daura na Umar? Banasan sai an gama a sake taso mutane wani auran, amma in anyi auran sai ta jira a gida kafin na gama hada kayan daki da sauransu."
Baffa cikin tsananin gamsuwa yace "Kai amma naji dadi, hakan yayi sosai wannan abu yamin dadin da bansan me zan ce ba. Ji nake kamar a mafarki"
Lamarin ya musu dadi nan suka zauna sunata tattaunawa cikin nishadi da farinciki.

******
Ummy kam duk hankalinta yaki kwanciya sai kallan wayarta takeyi, tunanin yanda zatai ta kori waccen matar inhar abin ya tabbata takeyi, ta tabbatar matarnan magani ta musu dan duk sanda ta yunkuro zata mata korar kare daga taje gidan sai ta kasa, wannan bala'i ya isheta mutane sai zaginsu ake aka magana akan wannan rashin tunanin, 'yan uwanta sunyi fada harsun gaji kowa ya zuba masu ido, gashi Aminu sam abin bai damunshi itakam ta rasa ta inda zata shawo kan wannan bala'i da masifar.
Kamar daga sama taji sallamarta, gabanta ne ya fadi tai saurin fara addu'a a cikin ranta tana neman tsari daga sharrin wannan matar.
Juyowa tai bayan ta gama addu'oin sannan ta kalleta tadanyi yake tace "Yau kece a gidan? Na dauka baki da lafiya tunda inata aikawa kizo kin kasa zuwa."
Hajiya tai dan murmushi ta zauna akan kujera kai kace mutuniyar kwarai tace "Asma’u ai kya bari mu gaisa dai ko?"
Ummy ta koma ta zauna akan kujera nan suka gaisa, kallanta tai tace “Kwanaki dana miki magana kikace zaki wuce a satin, ko?�?
Kallan Ummy tai sosai, wanda har ranta ya fara baci, gani tai ta saki murmushi wanda ya kara dagawa Ummy hankali.
Tace “Aminu bai sanar dake bane? Har kayana na hada shine ya hanani tafiya?�?
Yanda ta yiwa Ummy maganar haka kawai ta samu kanta da kasa cewa wani abin, sai tsananin faduwar gaba kawai da Ummy ta fara fuskanta. Addu’a ta fara cikin sauri.
Hajiya ta sake murmushi tace “Sannan kinsan ni na saka Aminu ya amince da auran da kike san yimai ko?�?
Ummy kam duk yanda taso ta daure ta mata magana ta kasa, yawun bakinta ta hadiya ta daure sosai tace “Ba maganar aure ba, Yanzu yaushe zaki tafi? Wai dan Allah bakya jin kunyar zama a gidan sirikinki? Ni tunda nake ko a labarai ban taba jin wannan abin ba, mu ba a garin maguzawa ba bare garin gala galu? Ai na tabbatar kudin da kike tarawa ya isheki yanzu haka nan.�? Dakyar Ummy ta daure tai wadannan kalaman dan ji take zuciyarta kamar zata fito saboda bugawar da take.
Murmushi ta sake yi tace “To ya kikeso nayi? Ni kaina yanzu so nake na tafi. Danki ne ya dage sai na zauna, in ke baki daukeni a matsayin wani abu ba shi a matsayin uwa ko ince sama da matsayinki ya daukeni.�?
Kallanta kawai Ummy take cikin tsananin mamaki, Hajiya ganin tabbas Ummy bata samu matar da zata aurawa Aminu ba dan yanda ta watsa mata maganganu ta tabbatar da ta maida mata murtani yasa ta mike tace “Dama dai gaisheki nazo yi bari na wuce zan dauko jikokina.�?
Fita tai ba tare da ta sake neman jin ta bakin Ummy ba.
Tana fita ta kalli gidan tace “Daga ke har Aminu a tafin hannuna kuke.�?
Ummy kam harta fita gabanta bai daina faduwa ba, wayarta ce tai kara cikin tsoro da firgici ta dauko wayar dakyar ta danna ta kara a kunnenta.
Baffa cikin jin dadi ya sanar da ita abinda ke faruwa, hamdala ta shiga yi sannan tace “Alhaji karka fadawa kowa maganar auran nan dan Allah, shi kanshi Aminu zan ce karya sanar da kowa, in aka daura auran koma menene aji.�?
Yasan tanada dalilinta na fadar haka, shi kanshi abin na damunshi ya rasa me yasa suka kasa korar matarnan, sannan duk matar da Aminu zai aura sai wani tangarda ya taso.

*********

Umar kam can cikin zumudinshi a motar haya, yana kwance ya rufe ido yana hango ana shafa fatihar auransa da Ibty bai san an sace masa wayarsa ba, sam bai kula ba harsai da ya isa kauyensu, takaici ya isheshi gashi yanasan ya kirata video call dan har ya fara missing dinta.

A kauye kuwa ya sanar da kowa maganar auransa da Ibtisam. Murna kam kowa ya shiga tayashi dan Ibtisam irin matan nan ne masu ban sha’awa da birgewa.
Kawunsa yace ai kuwa anan kauyensu zai zauna kafin aure dan tunda ya koma birni shekara sama da goma kenan bai taba zuwa ya kwana ba, sun kuma tabbatar yanzu in yai aure shikenan sai dai yazo ya wuce.
Bai musa ba dan yanzu ji yake rayuwar sa tana cikin kan hanyar da yake so, yace zaiyi sati daya inyaso sai ya koma ana saura sati daya biki.
Rashin wayarsa ya dagamai hankali, haka ya ari wayar abokansa yai ta kiranta ita kuma taki dauka, dan ita sam bata daukan number da bata sani ba, ganin Umar bai kirata ba yasa ta tabbatar da lalai yanzu ya juya akalarsa zuwa kan Yayarta, sai dai duk da haka zata sanar da Umma halinsa.

Umar kullum ya kwanta bashida aiki sai mafarkin yana saduwa da Ibtisam shikenan da yin wanka, wannan sha’awa data tasomai kwanan nan ta isheshi, lalai in akai aure zai kwashi gara dan tabbas a rana sai ya sauke sha’awarsa iya san ransa, shi ji yake sau hudu ma bazai gamsar dashi ba. Wani irin mugun santa yakeji bai taba yini bai ganta ba lalai sati dayan nan sai ya jure in ba haka ba tabbas za’a tashi cikin dare a nemeshi a rasa, matsalar daya yayiwa mahaifansa alkawarin zama harna sati daya.

Nikam nace Hmmmm😆 su sha’awa manya…�?

*******
A hankali ta sauko daga saman dakinsu ta kwankwasa kofar dakin Umma, daga ciki ta amsa tare da bata izini, a tunaninta Abba bai dawo ba dan bataji alamun motarsa ba, tana bude kofa ta ganshi a zaune yana shan tea.
Gaisheshi tai sannan ta tsuguna, ita datazo yiwa Umma zancen Umar yanzu kam ina zata iya a gaban Abba?
Abba cikin jin dadi yace “Ibtisam dama yanzu zan sa a kiraki.�?
Kallansa tai a ranta tace “Shikenan Ya Umar ya canza ya dawo yace ita yake so�? Idanunta tadan sadda kasa takaicin duniya ya isheta.
Abba cikin jin dadi yace “Akwai bako da zakiyi gobe in Allah ya kaimu, naga gobe asabar kina gida ko?�?
Kallansa tai a hankali tace “Eh ina gida Abba, amma wani bakon?�?
Ya dan sake shan tea din yace “Yaran abokina ne bazaki gane babanshi ba amma sau biyu yana zuwa gidan nan, daya kun gaisa lokacin daya kuma kina makaranta yazo. Dazu Ummanki ke fadamin dan na dauka ma kinsanshi sosai tace bazaki ganeshi ba.�?
Bata ce komai ba sai daga kai kawai datai tana mamakin wani yaran abokin?
Abba ya sake murmushi yace �? Ibtisam ki kalli abin nan da fuska mai kyau, wannan hadin ina matukar sanshi ina kuma fatan kema zaki soshi. A koda yaushe burin iyaye bai wuce su aurar dasu gidan da zasu samu kwanciyar hankali da nutsuwa ba.�?
Kanta yana kasa a hankali tace “Hakane Abba.�?
Jin kalamanta yasa Abba ya mike ya shiga toilet yana murmushi shi dama yasan bazai samu matsala daga gunta ba.
Umma cikin jin dadi tace “Ibty ko akwai wanda kikeso? Naga bamu tambayeki ba.�?
Da sauri ta girgiza kai alamar a’a, Umma tai murmushi tace “Ya taba aure amma matarsa ta rasu, sannan yanada yara biyu mata ‘yan biyu ne shekararsu biyar.�?
Kallan Umma tai tace “Yara?�?
Umma ta daga kai alamar eh tace “Bakyasan mai yara?�?
Kai ya girgiza alamar a’a itakam ai koma wanene indai zai barta da rayuwarta ya barta tai karatunta zata amince, sannan in har zai rabata da kusa da Umar dan ta tabbatar barinta gidan shine zai sa ya maida hankali gun kula da yayarta.
Umma ta dan dafata tace “Allah ya muku albarka, yau cikin farinciki nake, ban taba tunanin auranki zaizo nan kusa ba.�?
Kunya ta kama Ibty ta mike da sauri ta wuce daki.

Tana shiga wata number na sake kiranta, kashe wayartai gaba daya ta zauna a bakin gado tana tunani, tunda take bata taba kula wani saurayi ba da sunan so saboda takurar Umar, gobe ko me zatace? Sannan gobe dole ta sanar da Umma tunda yau bata samu dama ba.


Ayusher Ce🏌🏻‍♀�?
2/4/22, 11:08 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
      (.........In Between)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

*Free Page*

Ki hanzarta ki mallaki naki dan Free Pages sun kusa karewa🤸🏻‍♀�?

*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA 500 TA*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

+447894142004

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730


Page 7

Washegari......

Tun bayan Ummy tayi sallar asuba ta zauna akan sallaya tana addu'oi itakam tasan Allah ne kadai zai kwacesu ya kuma kwaci Aminu daga wannan bala'in, mutanen unguwa sai zundensu akeyi zagi kuwa da yada habaici har bataso ta shiga taro. Dadinta daya mijinta nada hali sai dai a dinga yada mata habaici, kishiyarta kam cin mutumcin da take mata akan wannan abu ya isheta, addu'a kawai take Allah yasa wannan karan Aminu ya samu abokiyar rayuwa kuma ya basu ikon korar matarnan data zame musu bala'i da masifa......
****
  Itakam Ibtisam bayan sun gama gyaran gida itada Iman, tana shiga daki zatai wanka Iman ta biyota tana dariyar gulma, fuska ta daure tace "Meye hakan zakizo ki sani agaba kina dariya?"
Iman ta kalli dakin tace "Kai duniya tamin dadi, yanzu dai saman nan ni kadai zan zauna, injuye can in murguda can, bamai sa min ido."
Harara Ibty ta maka mata tace "Dadinta kema mace ce ki gama murgude murguden a hankadaki kema gidan miji."
Iman ta dan turo baki tace "Ni Autar Umma ce bazata ba kowa ni ba. Ko mijin nake so sai dai ya biyoni."
Tsaki Ibty taja tace "Sanda za'a cilaki gidansa ki tabbatar kin sake maimaita kalaman nan."
Baki Iman ta murguda mata tace "Allah yasa in kin tashi ganin miji ki ganshi dan lukuti mumuna wanda inya danneki bazaki iya......" Dukan da Ibty ta kawo mata ne yasa ta fita a guje tana cewa "Ki kasa ko motsi."
Kwafa tai tace "Yarinyarnan ta mugun rainani wlh."
Wayarta ce ta fara kara, kallan wayar tai harta katse, wanka ta shiga haka tai wanka tanata tunanin ko ya zataga bakon? In kuma ta Iman ne taga jibgegen namiji fa? Kallan dan siririn jikinta tai tace "shikenan mai makon na gudarwa Umar sai na samu mai kakaryani." Ajiyar zuciya tai na tausayin kanta, can kuma tace "in kuma shima masifaffen kishi da zargi gareshi fa?" Haka ta gama wankan tana saka da kwancewa.
Daya daga cikin sabbabin kayanta ta dauka ta saka, material ne an mata gown dark blue ya mata kyau sosai da sosai, zama tai a bakin gado ta dau wayarta ta turawa Ainah text "Ainah akwai labari anjima."
Ai tana ajiye wayar sai ga kiran Ainah, dariya tasa ta daga tace "Kai jama'a wato ke dai bakyasan a barki cikin duhu."
Cikin zumudi Ainah tace "Ya akai? Fesamin dan Allah."
Dariya tai tace "Ki bark sai anjima in yazo ya tafi sai muyi gulmar da hujja." Ido Ainah ta zaro ta zauna digirgir akan gado tace "Wanene zaizo?"
Cikin dan kunya Ibty tace "Abba jiya yace min yau zanyi bako, bansan wanene ba tukuna." Wata 'yar kara Ainah tasa na nishadi tace "Kai amma naji dadi, Ibty ai daga kinga ya miki kiyi wuf kuce gobe a dayra muku aure, dan nikam fargabar dawowar jarababem can nake."
Dariya sosai Ibty tai tace "Dan ni na kawo rashin hankali duniya daga ganin namiji yau sai ince gobe ya zo ya aureni? To ko tallan kaina nake ai sai haka."
Baki Ainah tadan rufe tace "Na zake dayawa?"
"Zakewar gaske ma." Sako ne ya sake shigowa wayar ta nan sukai sallama tana dubawa taga ansa "Ibty nine Umar ki daga muyi magana, wayata aka sace."
Idanu ta zaro gabanta yai wani irin faduwa, kashe wayar tai da sauri sannan ta sauka kasa, dole ta sanar da Umma abinda ke faruwa yanzun nan.
A falo taga Yaya Billy sunata kara gyagyara gida ita da Iman, tausayinta ne ya kamata ta dan matso tace "Yaya dan Allah ki bar gyaran nan ki huta."
Murmushi ta mata tace "Ki barni hankalina yafi kwanciya in nai, in na auri Ya Umar ke zaki dinga zuwa kina min gyara?"
Shiru tai tana kallanta, cikin mamaki tace "Yaya Bilkisu wai da gaske san da kike mai haryakai kina auno zamanku tare?"
Dan gefen kanta tadan buga kadan tace "Ke wai meyasa kika damu da san da nake mai? Ibty maganar gaskiya ada na hakura amma a yanzu ji nake kamar dashi kadai zan iya rayuwar aure, Yaya shi kadai na sani, zuciyata shi takeso, inaji kamar inba shi ba to ni da aure har abada."
Dariya sosai Iman ta kwashe dashi tana tafi tace "Lalai Yaya bansan kin rika agun kalamai ba."
Ibty ta maka mata harara, sannan ta nufi dakin Umma.
Umma tana zaune tana gyara fuskarta a madubi da alama itama wanka tai, kallan Ibty tai cikin jin dadin shigarta yasa tace "yanzu nake tunani Allah yasa kinyi shiga mai kyau."
Zama tai a bakin gado cikin kunya, Umma tace "Munyi waya da Abbanki yace nan da minti ashirin zai iso, duk da nasan basai na fada miki ba amma ki bashi girmansa a matsayinsa na babba."
Kai ta daga a hankali sannan tace "Umma dama maganar Ya Umar da Yaya Bilkisu ce, nikam........"
Katseta tai tace "Kiji da abinda ke gabanki ba maganar nan ba, su sun amince da junansu bansan me yasa ke kika damu ba, Ibty wannan shine babban burin mu nida mahaifinki dan haka ki cire komai a ranki ki rungumi abinda muke so kuma suma suke so."
Jikinta ne yai sanyi a hankali ta daga kai alamar to sannan ta mike jiki a sanyaye ta fito daga dakin.
Sama ta koma tai sallar azahar ganin lokacinta yayi sannan tadan yi kwaliya sama sama dan dama bata iya heavy makeup ba amma ta iya daidai nata wanda kuma yake kara mata kyau.

********
Sanye yake da farin yadi mai tsada, kana iya hango vest din jikinsa ta cikin yadin, sanye yake da hula dark brown kalar takalminsa, yayi kyau kwarai da gaske ga sajen ya kara fito da zatinsa da girmansa.
Motar ya maida ya rufe yana tunanin yaushe rabanshi dayazo zance? Wannan karan kuma Ummy wata samo? Sai murna take kamar ance yaune auransa, shikam yana mamakin yanda Ummy ke san taga yayi aure.
A hankali ya karasa jikin kofar gidan sannan ya kwankwasa, daga can ciki Iman ta fito sanye da mayafi karami, dama tun dazu take gadi wai a dole ita zata fara ganinshi.
Bude kofar tai, Aminu cikin mamaki ya kalleta amma dai ba wannan 'yar ficikar bace bako? Katseshi tai da cewa "Sannu da zuwa."
Kai ya daga mata kafin yace "Yauwa."
Shiga yai sannan tai gaba yabita a baya, kofa ta budemai na falo ya shiga. Kamshin turaren wuta ne ya fara dukan hancinsa, a hankali yadan lumshe ido, sallama yak ta amsa sannan ya shiga ya zauna akan kujera, Iman ta wuce dakin Umma. Tana shiga tace "Umma! Yaya! Ya iso ya iso."
Bata jira me zasuce ba tace "Ammafa ya hadu sai dai Allah babba ne sosai dan cikin sajen daya tara harda furfura."
Yatsa Umma ta nuna ta dashi tace "Kinga ki fita idona, koma menene ki tabbatar kin nutsu bansan tsinanen rawar kan nan."
Umma ce ta fito da sauri yadan sauka daga kan kujerar ya gaisheta, cikin fara'a tace "Aminu ya Ummyn taka?" Cikin girmamawa yace "Tana gaisheku."
Komawa ciki tai, sannan Bilkisu ta fito suka gaisa itama, tausayin yanda take akan keken guragu ne yadan kamashi, nan Iman ta kawomai juice da ruwa sannan tahau sama ta kira Ibty wacce tun farkon jin muryarsa suna gaisawa da Umma taji gabanta ya fara dukan uku uku.
Iman ta shigo tana zolayarta, itadai batace komai ba.
Mayafinta ta dauka ta koma gaban madubi ta zauna tana dan maida ajiyar zuciya, dariya Iman ta saki tace "Ibty karfa kije saboda rikicewa maimakon kice ina wuni kice ina kwana."
Bata tanka ta ba sai data gama sauke hucin ajiyar zuciyarta sannan ta fito, a hankali ta sauko kasa ta zauna daga can gefen bakin kujera, a hankali cikin dauriya tace "Ina wu..........."
Idanunta ne ya sauka akanshi, shima cikin tsananin mamaki yake kallanta, kif kif tai da ido kafin tace "Ya Aminu?"
Kansa yadan karkatar kadan sannan yadan sa hannu ya gyara zaman farin glasses din dake kan fuskarsa, murmushi yai yace "Kamar kawar Ainah ko?"
Kai ta daga cikin mamaki sannan tace "Kaine bakon?"
Kunya duk ta rufeshi amma lalai Ummy, ta rasa da wacce zata hadashi sai kawar Ainah? Kasa magana yai itama tai kum ta kasa cewa komai.
Can dai ganin zaman nasu bamai cewa komai yasa tace "Amma Ainah bata sani ba ko? Naga munyi waya batace komai ba."
Kallanta yai sosai yace "Ke saurin me kikeyi?"
Fuskarta dauke da mamaki tace "Saurin me?"
Ya kalleta sosai yace "Yarinyarki dake meyasa kike neman auran namijin da ya taba aure har yake da yara biyu?"
Kai ta girgiza da sauri tace "Ba sauri nake ba, Abba ne yace zanyi bako."
Ya dan hade hannayensa yace "Baki tambayi girman bakon ba?"
A hankali ta daga kai kafin tace "Umma tacemin kanada yara."
"And?"
"Nace to."
"To kawai? Ya tambayeta yana kallanta."
Kai ta daga alamar eh, sun sake yin shiru kafin yace "Yanzu sai ki sanar dasu na miki tsufa."
Tai saurin cewa "Ya Aminu sai dai kai ka sanar dasu Ummy ni bazan iya cewa Abba a'a ba……�?
Kallan mamaki ya mata hakan yasa ta kasa karasa abinda take shirin cewa, yace "Baki damu da rayuwar ki bane? Taya yarinyarki dake zaki auri namiji babba wanda a kalla na baki shekara kusan sha takwas zuwa ashirin, sannan kizo ki fara kuka da yaran da ba naki ba? A shekarunki?"
Haushi yadan fara kamata, duk da ba so take ba itama amma sai wani zancen yarinta da shekarunki yakeyi kamar irin 'yar shekara goman nan.
Kamar zata maida mai murtani sai kuma ta kasa dan tana shakkarsa sosai balle yanzu daya tattara hankalinsa kanta.
Kanta kawai tai kasa dashi tana wasa da hannunta, shikam ko Ainah bayaji zai bari ta auri sa’ansa, mesu Ummy ke tunani?
Shiru falon yai, a hankali tadan mike ta shiga kitchen dan kawomai abincin da aka shirya dominsa, kusa dashi ta dan turo centre table din sannan ta ajiye.
Tana kokarin mikewa yace “Badai sanda kikaje gida kinsan abinda ake ciki ba?�?
Kallansa tai idanunta suka dan canza tace “Allah bansani ba.�?
Yace “To Meyasa ranar kikace na ajiyeki a gidan da ba naku ba?�?
Da sauri ta kalleshi sai a lokacin ta tuna, cikin wani yanayi tace “Gani nai ga bakin hanya yafi sauki.�?
“Saurayin da na gani yana jiranki fa?�?
Gabanta ne ya fadi ta kalleshi kafin ta tattaro dauriyarta tace “Yaya nane, a gidan nan yake.�?
Kai ya jinjina alamar gamsuwa, dan ya dauka ko auren dole ake shirin mata bayan tanada wanda takeso.
Mikewa tai a hankali ta koma ta zauna, haryanzu bata dawo daidai ba, Aminu ya kalli abincin a zahirin gaskiya ya koshi kuma yana ganin ba dadi an shirya abu

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment