Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kikaji? Kiyi hakuri gobe kya tahomin dashi skul to, shikenan?�?
Dariya tai da alama ta sauko nan sukaci gaba da hira wanda rabinshi na Umar ne, itakam Ainah sai kara bata shawara take akan tasan yanda tai ta yakice wannan abin.

********

Yarane ‘yan kanana guda biyu mata ‘yan shekara biyar, kallo daya zaka musu kasan yan biyu ne wato tagwaye saboda kamaninsu da tsayinsu, sanye suke da riga doguwa ta lace sunyi kyau sosai, abin sha’awa.
Da gudu suka taho suka rungume Aminu wanda yadan motsa lebe kadan sam babu fara’a a fuskarsa, in da sabo sun saba, cikin zakin baki daya tace “Dady ka taho mana da chocolate?�?
Kallan wacce tai maganar yai yace “Islam na dauka na fada miki banasan shan zakin nan? Nace zan siyo sau daya a sati ba kullum ba. Okay?�?
Ya karasa maganar yana mika ma dayar ledar hannunsa “Ilham kaiwa Hajiya maganinta.�?
Abinda yace kenan ya wuce dakinsa, dakin Hajiya suka shiga tana zaune tana irga kudi, tanajinsu ta maida kasan pillow da sauri ta kwanta a kan gado tana wani fitarda numfashi, da gudu suka fada kanta.
Ta shafi kansu tace “Ilham kin fadawa Dady dinki ina kwance ba lafiya haryanzu?�?
Da sauri ta rufe baki tace “namanta Hajiya, bari na je na fadamai.�?
Rikota tai tace “bashi kya fadamai anjima.�?
Magani ta mika mata, ta amsa tai dan shiru alamar tunani sai kuma ta baza tagumi ta mike dakyar ta kwaso kaya daga cikin drawer tana kokarin sawa a akwati, Islam tace “Hajiya ina zaki?�?
Tadan shafi kanta tace “Islam kinga Ummy batasan na cigaba da zama anan, shiyasa nake jiran babanku yazo dan na samu na mai sallama……�?
Ai basu tsaya jin karshe ba suka rushe da kuka, fitowa sukai daga dakin sunata kuka Islam harda zunduma ihu, da sauri ya fito daga dakinshi jin kukan da suke rusawa, suna ganinshi suka karaso suka rike rigarsa Ilham tace “Dady dan Allah karku kori Hajiya! Ka roki Ummy tabar mana ita.�?
Islam ma tana kuka tace “Dady inta tafi wazai dinga mana wanka? Yana shiryamu yana mana abinci?�?
Idanu yadan runtse kadan yace “Ya isa hakanan, ba inda zataje zan mata magana yanzu.�?
Fuskarsu suka share suka hau murna harda tsale.
Bangaren Hajiya ya nufa wanda dan karamin corridor ne tsakaninsu, tana zaune ta saka hoton Na’imah a gaba, gefe kuma kayayakin da taketa hadawa ne a gefe, sallama yai ya shiga ciki.
Hajiya tana ganinshi ta ajiye hoton tana share kwalla, jikinsa ne ya sake wani irin sanyi jikinsa yai ya zauna a kasa tare da lankwashe kafa yace “Hajiya meyasa kike haka dan Allah? Da jikinki zakiji ko kuma da tunani?�?
Cikin muryar kuka tace “Aminu yazanyi? Rashin Na’imah a kullum dawomin yake sabo? Barin gidan nan shine abinda ya cancanta, taya zakai aure ina gidan nan? Na fahimci dalilin Ummynka nasan taga na bar gidan, haka zakaci gaba da zama? Kaifa d’anane bazanzo abinda zai ma ila ba a rayuwa.�?
Ajiyar zuciya yai yace “Wai dan Allah menene na tilastawa sai nayi aure? Nace ba yanzu ba dan Allah Hajiya ku barni tukuna.�?
Tace “Aminu bafa zai yiwu ba, shekara biyar? Ai Ummynka tayi hakuri, dan Allah kabi umarninta.�?
Shiru yai shikansa ya gaji da batawa Ummy raj akan maganar aure, Hajiya bata auno abinda zaice ba sai jitai yace “Naji zan yiwa Ummy magana ta samo yarinyar data kwanta mata, amma wannan bazai sa ki bar gidan nan ba, ke amanace a gareni, zan kuma kula dake har karshen rayuwata.�?
Gabanta ne ya fadi, tadan hadiyi wani abu tare da yin yake tace “Nagode Aminu daka fahimceni.�?
Mikewa yai ya bar dakin, yana fita ta dafa kanta, itafa ba auransa bane matsalarta, matar da za’a kawo wacce zata hanata jin dadi ne bazata yarda ba, haka kawai yaran da ‘yarta ta taimaka gun bunkasar arzikinsa wata can tazo ta mori jin dadi ta barsu? In ‘yarta bataji dadin daya kamata taji ba ita da jikokinta dolene suji, kauye kuma ta barshi kenan har abada.

*******

Duk yanda Ibtisam taso tai bacci ta kasa, wannan bala’i dame yai kama? Mikewa tai ta sauko daga kan gado, sauka kasa tai inda dakin yayarsu yake wacce Allah ya jarabceta da ciwo na sickle cell, mahaifinsu fa mahaifiyarsu basu san As da AS bane harsai bayan an haifeta, da harsun so hakura da haihuwar sai Allah ya kawo cikin Ibtisam, damuwa da tashin hankali ya bayyana a gunsu suna tsoron kar su sake samun SS sai dai cikin godiyar Allah ita sai aka samu mai lafiya, daga nan sukace sun hakura, sai dai zuciya dasan abu yasa Umma ta sake rokar Abba akan su gwada na karshe, Alhamdulila Iman itama tazo da lafiya daga nan suka hakura balle a lokacin damuwa da rashin lafiyar Bilkisu ya damesu, kusan koda yaushe suna asibiti, wannan ciwo ya taba kafarta daya wanda tafiya take wahalar da ita, dole sai keken guragu aka nemar mata.
Bude dakin tai a hankali ta shiga ta kwanta a bayanta, tana tsananin san yayarnan, idanunta ta rufe tana tattaro idea din abinda ya kamata tai wanda zai rabata da wannan jarabar.

*********
Washegari…�?.

Yauma sanye take da abaya sai dai yau mayafin kanta brown ne kalar jakarta, tunda dadewa ya hanata yawo da mayafi, bata isa ko kofar gida ta fito da mayafi ba, da hijab yasa ta dinga sawa dan har dinko mata dogaye yai tace ita kuma bazata sa hijab kullum ba, nan sukai ta fada a karshe dai ya hakura da abaya.

Cikin murna ta tari adaidaita sahu ganin yau bai biyota ba, lalai yau tayi sa’a, tana shiga adaidaita kawai taganshi ya shigo.
Jitai kamar an kwara mata ruwan xafi, kai ta kauda gefe suka fara tafiya, ba wanda yace wa wani kala. Kallan mai adaidaitar yai cikin masifa yace “Inka sake kallanta ta madubi wlh sai na faffasa maka jiki, wannan ai iskancin banza ne.�?
Baki mai adaida ya bude yace “bawan Allah nida adaidaita ta akan me za’a hanani kallan madubi?�?
Cikin bacin rai yace “Ka sake kaga yanda ake hauka wallahi daga kai har adaidaitar sai na muku ila.�?
Ibtisam ta sa hannu a saman goshinta itakam anya mutumin nan baya shaye shaye? Ko dai yanada tabin hankali ne? Wannan wani irin jaraba da masifa ne? Suna isa makaranta ta sauka bata ko mai magana ba tai ciki, sai dayaga ta wuce sannan shima ya wuce.
Motar datasha gabanta ne yasa tadan matsa kadan, tana kallan motar, glass din motar aka zuge ta gefe ta kalli motar, a daidainan idanunta suka sauka akan matashin dake zaune akan kujerar bayan mota, hannunsa dauke da jarida ya sa medical glasses fari a idanunsa, jitai ance “Yaya bari na sauka anan, zamu wuce da kawata.�?
Ganin Ainah yasa ta saki murmushi sannan ta gane Ya Aminu ne, a hankali tace “Ina kwana?�?
Kalan sakan daya ya mata kawai yace “Lafiya.�?
Ainah na fita Mamman yaja motar suka tafi, kallanta tai tace “Can na hango chewing gum dinki yana lekenki yaga ko aji kika wuce.�?
Tsaki tai tace “Yau dakar sa’a kikai Ya Aminu ya kawoki?�?
Tadan yi huci suka fara tafiya tace “gida yazo yiwa Ummy magana danaga zai wuce na rokeshi ya saukeni, dakyar ya amince sai da Baffah yasa baki.�?
Tadan girgiza kai, Ainah tadan daga mata gira tace “nafa taho miki dashi.�?
Ibtisam ta saki fuska tace “Thank you Ainah kinsan ko breakfast banba? Wai ina sauri dan na gudu kafin ya fito?



Ayusher Ce🏌🏻‍♀�?
2/4/22, 11:06 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
      (.........In Between)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

*Free Page*


*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA KUDINSA TA*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*

*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.

Page 3

Suna shiga class Ainah ta ajiye kayanta tace “Ibty ina zuwa.�? Ko minti biyu da fita batai ba wayarta data bari a kusa da Ibtisam ta fara kara, kallan wayar tai ganin My bro a jikin allan wayar dauke da hotonsa yasa ta kara kallan wayar da sauri, tare da wawaigawa ko zata hangota, ganin wayar na kokarin katsewa yasa ta daga tare da karawa a kunnenta, haka kawai ta samu kanta da kasa magana.
Aminu yanaji an daga yace “Ki fito ki dau wallet dinki, kin barshi a mota in kuma bakya bukata na wuce.�? Tana kokarin mai magana taji an kashe wayar.
Kallan wayar tai cikin mamaki tace “Ikon Allah sai kallo, ai ka bari kaji amsarta kafin ka kashe wayar ko?�?
Mikewa tai ta fito waje rike da wayar Ainah sai dai sam bata hangota ba, zuciyarta ce ta bata gwara kawai taje ta amso dan da alama Ya Aminun nan bashida hakuri.
Tayi tafiya maidan yawa kafin ta hango motar dazu, karasawa tai a hankali tadan kwankwasa glass din motar, cikin mamaki yake kallanta, shifa matsalar yaran zamani yana bashi mamaki, sam mata yanzu basuda kamun kai.
Bai sauke glass din ba sai kallanta da ya sakeyi tana tsaye tana jira, sake kwankwasawa tai, cikin kulluwa da takaicin halin matan yanzu, yarinyar da batafi kanwarsa ba tana neman mai mota ya kulata, kai yadan girgiza dan ya saba fuskantar wannan takaicin, ransa a bace ya sauke glass din.
Bai jira tace wani abu ba kawai ya hau magana cikin bacin rai �? Motar kice? Ko kuwa mai motar dan uwanki ne?�?
Zati da girman shekarunsa yasa Ibtisam tai shiru haka kawai shakkarsa ta kamata, dan Aminu nada kwarjini da cikar zati balle gashi babba, bakinta nadan rawa tace “Ya Aminu wallet……�?
Jin ta kira sunansa yasa ya kara kallanta cikin mamaki yace “Ikon Allah! You even know my name?�?
Tadan sake motsa baki kokarin maida glass din ya farayi cikin hanzari tasa hannunta a saman, kallanta yai cikin matukar mamaki, yanzu kam kallan da yake mata na kyamar rashin kamun kai ne, yace “Me kike hakan?�?
Hannunta ta zare da sauri idanunta sundan ciciko tace “Ya Aminu ni kawar Ainah ce, wallet dinta nazo amsar mata tadan fita ne.�? Ta dan kunna wayar Ainah dake hannunta tana nunamai.
Tsananin kunya da haushin abinda ya aikata ne yasa ya kalleta, lalai idansa ne ya rufe tabbas muryarta ce dazu wacce ta gaisheshi. Burin kunya da kokarin danne laifinsa ya fara yi yace , “Oh! Why didn’t you said it earlier?�? Yai maganar yana miko mata wallet din.
Amsa tai kafin tace, “Ina na samu damar magana? Ka rufeni da fada?�? Abinda tace kenan ta juya ta fara tafiya, baki ya dan bude kadan tare da komawa ya zauna sosai yace “Mamman kaga sanda na rufeta da fada?�?
Mamman ya shafi kansa yace “Yallabai ai tana zuwa baka bata damar magana ba ka hau fada�?
Ya dan kalli wajen window inda take tafiya yace “Amma dai ba bakinta na rufe bako? Kawai dai bataso yin magana bane.�?
Mamman yadan guntse dariyarsa dan karyai laifi.
Ya kara kallanta daga yanda take tafiya ya tabbatar zaginsa takeyi, in ba zagi ba rashin kunya take na abinda ya mata.
Kanshi ya kawar daga kallan gun a ransa yace me yasa tana zuwa bata sanar da kanta ba? Su yaran yanzu sai kwarewa gun neman magana.

Itakam Ibtisam tana tafe tana mita, �? Su manyan nan sai suyi abu suki daukan laifinsu, insukai abu sai su nuna ba laifi sukai ba. Ai sai ya bata hakuri amma tsinanen san girma irin na mutane da san rike girmansu bazai taba bari ya bata ba.�?
Aji ta shiga lokacin har lecturer dinsu ya shigo, kusa da Ainah ta zauna ta ajiye mata wallet da wayarta, cikin muryar rada tace “Ina kikaje?�?
Harararta tai tace “Gun Yayanki mai masifa.�?
Dan zaro ido tai batasan sanda tadan daga murya ba tace “Ya Aminu?�?
Ganin kallan da aka mata yasa ta gyara zaman ta da sauri tare da guntse baki, Ibty ta harareta tare da mata alama datai shiru.
Ai Ainah ta kasa hakuri tace “Ya akai kika ga Yaya? Bayan ya tafi?�? Cikin maganar rada ta nuna wallet dinta tace “Abinda kika manta ya dawo ya baki.�?
Ganin ana kallansu yasa Ainah tai kasa dakai tace “Allah ya taimakeshi Umar bai ganshi ba da an rotsawa Yayana mota. Baiji ba bai gani ba.�?
Wata muguwar harara Ibty ta maka mata, nan suka maida hankali gun abinda akeyi.

*********

Dattijon da ya shigo kalla tare da amsa sallarmarsa, fuskarta a sake take sosai, tun safe take jiranshi ya iso dan jiya ba a gidanta ya kwana ba sai yanzu ya samu zuwa. Babbar rigarsa ya cire yace “Asma’u kodai zaki fadi abinda ke ranki ne kafin na zauna? Dan naga alama kin matsu.�?
Dan dariya tai tace “Alhaji dazu da safe Aminu yazo.�?
Cikin fara’a yace “Ai ni nasan abin dama ya shafi Aminu, to meya ce miki?�?
Ta dan matso kusa dashi tace “Alhaji ya amince, yace in nemar masa matar da hankalina ya kwanta da ita, ko wacece bai damu ba wai indai zan bar mahaifiyar Na’ima ta cigaba da zama a gidan.�?
Dariya sosai yai yace “kice farin cikinki ya rabu biyu. To yanzu me kike tunani?�? Yai maganar tare da zama akan kujera.
Ta zauna itama tare dayin murmushi tace �? Bari yai auran kaga, ko sati bazan barta tai ba zan tattarata ta koma garinsu, ai ba a garin maguzawa muke ba, wannan jaraba ta isheni.�?
Yace “Wato dai kinsamu daidai dake, shiyasa fadan nan naku ke ban dariya.�?
Fuska tadan daure tace “Me kake nufi?�?
Yace �? Duba ki gani, ke kin nace sai ta tafi ita ta nace sai ta zauna, kunsa Aminu a tsakiya ke kiyi amfani da matsayin ki na uwa ita tai amfani da ‘yarta dayake masifar so da ‘ya’yansa.�?
Kwafa tai tace “Duk nacin ta dai inyai aure sai ta bar gidan, kasan Allah ko hawan jinin da take cewa tanadashi ni ban yarda ba, nifa komai na matarnan gani nake karya ne.�?
Baffa yai shiru yana kallan Ummy, tacigaba “Naji ‘yan uwanta na kauye sun koreta bayan rasuwar mijinta, amma menene dalili? Ai halin mutum wani sa’in shike sa a kyamace shi.�?
Ta dan kauda kai tana murmushin takaici kafin tace “Ni duk na rasa ma ta ina zan fara nemomai mata.�?
Baffa ya girgiza kai yace “Rashin bacci yazo.�?
Ta fahimceshi sarai dan duk sanda ta fara nemawa Aminu mace to fa bacci dakyar takeyi ta dinga juyi kenan tana tufka da warwarewa.

********

Yi tai kamar bata ganshi ba ta cigaba da tafiyarta, tsabar tasan nacinshi yau dakanta tawa su Ainah sallama.
Tana tafe ya matso kusa da ita yace “Ya makarantar?�?
Cikin dauriya tace “Lafiya kalau.�?
Shiru sukai suna tafiya tana kallan abokan saurayin jiya suna nunashi suna gulma, itakam wannan masifar ta isheta, wannan wani irin bala’i ne.
Dakewa tai tace “Yaya wai dan Allah bazaka dinga zama a kasuwa ba? In Abba ya tambayeka me zakace?�?
Adaidaita ya tare yana cewa, �? Inhar kinaso hankali na ya kwanta to ki amince na fadawa Abba maganar aure na dake, ai alkawarin da kikasa na miki yanzu yaci ace kin bari kowa ya sani.�?
Aranta tace “Ai da’a sani gwara ka kamani kaitamin duka dan ni da in aureka gwara nai ta zama a haka.�?
Jin tayi shiru yasa ya kalleta cikin fada yace “Kwanan nan na gaji da kin maidamun magana da kikeyi, sai na miki magana amma sai kiyi kamar bakiji me nake cewa ba.�?
Kallansa tai tace “Ya Umar na rokeka da Allah ka barni nai karatu salin alin, koma menene in mun hadu a gida ma tattauna ka taimakeni ka barni na shaki iska a makaranta.�?
Isowar mai adaidaita ne yasa ta fara kokarin shiga cikin tsawa ya kalleta ya kalli mak adaidaitr yace “Barnan.�?
Tsaki mai adaidaitar yai tare da cewa “Aikin banza kawai.�?
Umar ya maida kallansa gun Ibtisam yace “Me kike nufi da kalamanki? Kinasan cewa na hanaki shakkar iska ko me?�?
Saman goshinta ta shafa tace “Magana wannan ta fahimta bamu isa muyi ba, ta ina zaman aure zai yiwu a haka?�?
Ai kamar ta kara ingizoshi ya hau fada “Me kike san cewa? Ibtisam na dauka jiya na gargadeki ko?�? Ya nunata da yatsa yace “Last warning zan miki, inhar kika kara fadamin magana makamancin wannan ki tabbatar zaki ganni a gaban Abba, kin kuma fi kowa sanin Abba bazai taba hanani auranki ba.�?
Idanunta ne suka ciciko da kwalla, matsawa yai ya tari adaidai yana shiga ta juya ta koma cikin makaranta, sauka yai ya fara bin bayanta yana kiranta.
Bata ko tsaya ba balle yasa ran zata waigo ta kalleshi, gudu yadan sa ya sha gabanta da sauri yace “Ibty meye hakan?�?
Tace “Na manta akwai lesson din da zamuyi yanzu, zan kira Umma na fada mata.�?
Agoggon hannunsa ya kalla yace “Amma yau dama 3 kike gama lectures.�?
Ta kalleshi sosai tace “In kai ba mahaifina bane na rokeka da Allah ka kyaleni, lesson zamuyi da kawayena, kuma Abba bai hanani ba.�? Ji yake kamar ya cafko hannunta sai dai cikin makaranta suke gashi mutane sai wucewa sukeyi.
Hannunsa kawai ya dunkule ya zabga mata wani irin kallo idanunsa sun kada sosai sunyi jaaa. Wayarsa da tun dazu take vibrating ya dauko ya kara a kunne ba tare da ya duba mai kiran ba, jin muryar Abba yasa ya gyara muryarsa da sauri tare da sake gaisheshi.
Abba yace “Umar wai kana ina? Meyasa baka zama a shagon ka? Jiya nazo bakanan yau ma haka, ina kake zuwa?�?
Bayan kansa ya sosa yace “Abba naje wani guri ne yanzun nan zan dawo.�?
Da sauri ya juya ya fita daga makarantar zuciyarsa kamar zata fashe yana tafe yana tunanin ga Ibtisam can da wannan saurayin na jiya yana koya mata karatu suna tuntsira dariya.
Idanunsa ya rufe ya dunkule hannu kai kace zai tafi dambe…�?..


********

Mamaki ne ya kama su Ainah ganin Ibtisam ta shigo ajin da suke karatu, zama tai a kusa dasu tare da dafe goshinta.
Cikin tsananin mamaki a tare suka ce “Yau mafarki muke ko me?�?
Tsaki taja kawai ta kwantar da kanta akan desk din kujerar da take, Ainah ce ta dafata tace “Ibty Allah ki fadawa Ummanki wannan wani irin bala’i ne? Shi bai bar mazan dake sanki sun kulaki ba shi kuma ba mijin aure ba, na tabbatar akwai mazan dake sanki amma ganin ki kullum da wannan mutumin yasa suka hakura.�?
Hawaye ne ya zubo mata tace “Zan fadawa Umma in har bata yarda da abinda nace ba wallahi Ainah zan kawo koma wanene ko ni da kaina zan nemo zan nemo wani na kawo gida a aura min shi na rabu da wannan bala’in, bacci wannan banayi sosai, in zauna a falo gun iyayena ai hira ban iyawa saboda yana gida yai ta bina da kallo kamar zai cinyeni, ni kenan a daki kamar mayya, a hakan ma ba bari na yai ba wani sa’in sai dai kawai naga mutum a kaina. Wannan wani irin bala’i ne? Tunda nake bantaba daukan wannan abin da sunan so ba hauka na daukeshi………�?
Yanda take zubar da kwalla ne yasa duk jikinsu yai sanyi, Ainah ta dan jawota jikinta alamar lalashi…�?.


Ayusher Ce🏌🏻‍♀�?
2/4/22, 11:06 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
(.........In Between)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

*Free Page*


*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA KUDINSA TA*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*

*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.

Page 4

 
Haka ya isa kasuwa duk zuciyarshi ba dadi, yayi ta kiran Ibtisam video call taki dagawa. A dan karamin shagonsa wanda Abba ya bude mai yake saida atamfofi da shadda yaga Abban a zaune da alama jiransa yakeyi, yaran dake kula da shagon yana zaune shima suna dan hira.
Dakyar ya daure ya boye bacin ran dake fuskarsa ya sake gaida Abba tare da bashi hakuri akan fitar dayai.
Kafadarsa Abba ya dafa ya kalli yaran shagon yace "Kaje shagona kaci abinci kafin mu gama tattaunawa." Nan yai musu sallama ya fita. Umar ya zauna daga gefe wajen kaya, Abba yai shiru yana kallansa, yau ya yanke hukuncin akan su tattauna abinda ya dade yana ayyanawa a ransa, babban dalilin dayasa shi dauko Umar daga kauye gun Yayansa, dalilin dayasa ya kula dashi kamar dan cikinsa harya bude mai shagonsa. Dan ajiyar zuciya yai kadan irin ta manya yace "Umar banaso muyi maganarnan a gida, nafiso muyita tsakaninmu yanda inhar abin ba me yiwu wa bane mu bine shi tsakaninmu ba tare da ya taba zumuncin mu ba."
Yanda Abba yai maganar cikin kakkausar murya ne yasa shi tattara hankalinsa ya maidashi gun Abban.
Murmushi yadanyi yace "Aure nakeso na hadaka da 'yata."
Wayyo dadi! Shikenan burina ya cika, abinda kawai yazowa Umar kenan, baisan sanda kwalla ta cikamai ido ba, tsugunawa kasa yai yana kokarin boye tsantsan farincikin dake ransa, yace "Abba! Nagode nagode nagode....."
Mamaki ya kama Abba ganin bai tsaya yaji ko wacece ba, lalai Umar ya tabbatarmai a matsayin uba ya daukeshi kenan baima damu da ko wacece ba burinsa kawai ya faranta mai rai. Kaunar Umar ta kara ratsashi ya dan matsamai kafads alamar farinciki yace "Nagode sosai Umar, in ba damuwa gobe ka shirya kaje kauye gun mahaifinka, zan kirashi na sanar dashi kaima saikaje ku tattauna kafin mu fara shirye shirye."
A ransa yace ai yanzu zai iyayin tafiya wani gun yabar Ibty dan saboda tsaro ko garinsu yaje baya kwana yake dawowa ji yake kamar inya tafi kafin ya dawo wani ya kwace ta, yanzu kam wata nanauyan ajiyar zuciya ya saki ji yake kamar ya saki kara saboda murna da farinciki.
Abba kam dadi ya nashi sukuni kai tsaye gida ya wuce.
Kallanta ya tsaya yi tana zaune akan kekenta tanata ninke kaya da alama wanki akai suka bushe take ninkewa, hamdala yai dan babban tashin hankalinsa a koda yaushe ya zaiyi ya farantawa Bilkisu rai, tun Umar na shekara sha takwas yasa aka dau jinjnsa aka gwada tunda yaga AA yake ta jiran wannan lokacin dan dama da zuciya biyu ya dauko Umar.
Sallama yai ta juya cikin sanyinta tare da murmushi, ta amsa tana kallansa cikin jin dadi, shigowa yai yace "Uwata aiki kike?"
Ta dan birgo keken cikin sakin fuska tace "Abbana sannu da dawowa."
Yana murmushi yace "Ina Umman taki?"
Ta nuna daki tace "Ta shiga yin sallah." Wucewa yai ciki bayan ya mika mata ledar kayan marmari daya taho dasu a leda, Abba yanada kudi sai dai shi bashi da sakin kudi sosai, a cewarsa dan kasuwa baya almabazaranci, kusan komai da akw bukata na gida shi da kanshi yake siyowa. Umma bata damu ba dan duk wani da suke bukata yana kawowa.
Gana zaune tana lazimi ya shiga dakin cikin nishadi ya zauna abakin gado yace "Hadiza! Burinmu ya kusa cika."
Waigowa tai ta kalleshi tafi kowa sanin burin su guda daya ne, cikin jin dadi tace "Kamai magana?"
Ya jinjina kai alamar eh yace "Inhar na aurar da Umar ga Bilkisu nasan ko bayan raina komai zai tafi daidai, Ibtisam tasan ciwon kanta, lafiyayya ce sannan tana kaunar yayarta sosai, Iman duk da yarinyar dake kanta tana jin maganar Bilkisu, Umar zai kula dasu sai kuma nema musu miji na gari.
Umma juyawa tai tare dayin sujjada tana godewa Allah.

*******

Sam yau batasan komawa gida, Ainah tai ta nacin akan tazo suje gida tagaida Ummy, dan sun dade tare tun secondary school suke kawaye, nacin Umar da bibiyar Ibty yasa ko sha'awar zuwa gaida Ummy bata tabayi ba.
Yau kam ganin ta samu pass tana ganin ba lalai ya kara barinta

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment