Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana kallan Ibtisam.
Goggo a fusace tace "Bakaji nace ka fita ba?"
Juyawa yai kamar zan sa ihu ya fita daga falan, a kofar falan yaja ya tsaya fuskarsa kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa.
Kanwar Abba cikin hanzari ta dau waya ta kirashi, ta sanar dashi yazo gida yanzun nan dan ba lafiya.
Bilkisu kam kawai hawaye ta shiga yi, da sauri taja kekenta ta koma daki, sauka tai ta dan dafa kago ta zauna sannan taja bargo ta lulube kanta, a hankali wani wahalalen kuka ya kwace mata. Me ke faruwa? Taya ango zaizo yace ba amarya yakeso ba kanwarta yakeso? Bayan an daura musu aure? Wannan wani irin bala'i ne?

*******
Umma a fusace ta dago Ibtisam ta girgizata iya karfinta tace "kin dawo hayyacinki ko sai na miki tsinanen duka?"
Idanunta ne kawai suka fara cicikowa, haryanzu jikinta bai dawo da karkarwa ba. Umma ta kalleta tace "Meke faruwa? Umar ke yake so ko me?"
Bakinta ne ya hau rawa ta rasa ta ina zata fara magana, wani wawan mari taji an wanketa dashi, ta rike kuncinsa anan fa hawaye suka gangaro mata, bakinta na rawa tace "Umma nasan yana sona amma na dauka ya hakura dani ne zai auri Yaya tunda Abba ne yamai magana."
Saketa Umma tai iya karfinta hakan yasa Ibty ta dan fadi kasa, jiki a sanyaye Umma ta zauna akan kujera dabas, nan fa aka fara kananan maganganu, dayawa suka hau Ibty da masifa ai laifinta ne, hawaye kawai Ibtisam takeyibta dukunkune.
Abba ne ya shigo shi dasu Kawu, tundaga hanyar shiga sukaga Umar, yana tsaye fuskarsa haryanzu ba alamar saukowa.
Kawu kam fuskarsa kawai ya shafa dan yasan kwanan zancen.
Abba ya kalli Umar yace "Umar kai kuma nan ka taho anata nemanka a dau hotuna?"
Mamaki ne ya kama Abba ganin ko amsamai baiyi ba, daga ciki kanwarsa ta fito da sauri cikin ahin gulma tace " Yaya shigo shigo."
Shiga yai ganin yanda kowa yai cirko cirko yasa yaji gabanshi yadan fadi, dama gashi ya baro can da takaicin fasa motar Aminu da akai.
Zama yai yace "Meke faruwa?"
Nan ta zayyanemai abinda ya faru, tashin hankalin da ba'a misaltawa, Inalilahi wa ina ilaihi raji'un abinda Abba kawai yake cewa kenan.
Kallan Umar yai yamai alama ya shigo.
Umar ya shigo ya zauna daga gefe, Abba yace "Umar meyasa baka fadamin Ibtisam kake so ba?"
Umar ya kalleshi yace "Ni dakace 'yarka ita kadai na kawo shiyasa banyi tunanin wani abu ba na amince."
Kawu ya kalleshi yace "Wannan laifinka ne ko ma menene ya kamata ka tsaya kaji sunan yarinyar kafin ka amince."
Umar ya kalli Kawu yace "Ni dai yanzu koma menene bai dameni ba Kawu, Ibtisam matatace dole wanda ya aureta ya bani takardarta na aureta, ni ma zan saki Bilkisu dama ban dauketa a matsa............"
Bugun dayaji a kafadarsa baisa ya juya ba, Goggo cikin kunar rai tace "Umar bakada hankali ne? Mutumin daya rikeka ya maka gata kake fadawa zaka saki 'yarsa sannan yasa a saki daya 'yar tashi ya baka?"
Umar ya kalli Ibtisam yace "Ko ma menene sai dai ku fada amma Allah ba wanda ya isa yai zaman aure da ita inba ni ba."
Yanzu kam Abba ya tabbatar Umar baya tunani, ya kuma tabbatar inya bar Ibtisam yaran nan zai iya ja musu bala'i.
Dakewa Abba yai yace "Koma menene ya riga ya faru, in har bakasan Bilkisu wannan daban sai dai auran Ibtisam da Aminu baka isa ka kashe shi ba, da ba yanzu zata tare ba amma yanzu bazan barta ko kwana daya ta kara a gidan nan ba, gidan mijinta zata tafi, aure shiri ne na Allah, da ace Aminu ba mijinta bane da auran nan bazai taba yiwu ba."
Umar ya kalli Abba yace "Allah Abba bamai fitar da ita ya kaita gidan wani in ba ni ba."
Baki Abba ya bude yace "Umar? Ni kake fadawa haka?"
Ran Kawu yai matukar baci yace "Tashi ka fita daga nan ka koma bangarenka."
Umar ya kalli Kawu yanaji kamar zaiyi hauka yace "Inhar tabar gidan nan duk abinda ya biyo baya kar wanda yaga laifina."
Yana kaiwa nan ya mike ya fita, kanwar Abba tace "Anya Umar baya shaye shaye? Na dauka baya magana sosai yau me idona yake gani?"
Abba kam salati kawai yakeyi tashin hankalin da ya tsinci kansa a ciki ko sanda akace Bilkisu tanada sikila bai ji ba.
Ibtisam kam kuma take iya ranta, Umma bata ko bi ta kanta ba ta wuce daki gun Bilkisu, Abba ne ya kalleta yace "jeki hada kayanki da kaina zan kaiki gidansu Aminu, ki zauna a gidan mijinki gobe duk yanda za'ai za'azo a miki jere."
Kasa tashi tai, Iman tazo ta dagata tanata kuka haka suka hau sama.
Umar kam a daki kayansa shima ya hau hadawa zuwa zaiyi ya dau Ibtisam su wuce kauye bazai iya wannan rainin hankalin ba.

Nace ikon Allah sai kallo🤔 wayaga karfin hali barawo da sallama?


Ayusher Ce🏌🏻‍♀�?
2/4/22, 11:10 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
      (.........In Between)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

*Last Free Page🤸🏻‍♀�?*

*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA 500 TA*  *Ya samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

+447894142004

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

Page 10😘


  Iman ta kama hannun Ibtisam wacce ta mike tana kuka, sama suka wuce nan Iman ta shiga hada mata kayanta, meyasa kowa ke neman daurawa Ibtisam laifi? Bayan kana gani kasan sanda Umar ke mata bana hankali bane? Da alama itama neman kwatar kanta takeyi. Tana hada mata kaya itama hawaye na zubo mata dan yanda Ibtisam ke kuka duk mai tausayi sai ya tausaya mata.
Abba ne ya turo akan Ibtisam tai sauri ta fito, haka suka fito da ita tana tafe tana kuka, dakin Bilkisu ta shiga, Umma ta gani rungume da Bilkisu tana kuka, karasawa tai ta zube a kasa jikin gadan da suke tana kuka tana kiran sunan Umma.
Fuskar Umma a daure sosai ta kalleta tace "Ke kuma kukan me kike? Naji ita tanada hujjar kuka ke fa?"
Kai Ibtisam ta girgiza tace "Umma wlh ba'a san raina bane naki fada muku, har daki na biyoki ina san na sanar dake, sannan lokacin da kuka fara maganar hadin nan kai tsaye na tambayeku dan ni nasan akwai wani abin, amma alokacin kukace inata tambaya ai shi ya fara amincewa, shiyasa na dauka ya hakura dani ne, ita kanta Yaya har daki na biyota na tambayeta ta nunamin ita ke san Ya Umar? Umma ya kukeso nayi? Menene laifina????" Abinda ta fada kenan ta sa wani irin kuka, duk da jikin Umma yayi sanyi ta kuma tuno tabbas duk abinnan data fada ya faru amma haryanzu bata sauko daga bacin kan laifin Ibtisam bane.
Kanta ta kauda wanda hakan ya kara daga hankalin Ibtisam, kanwar Abba ce ta shigo ta fito da ita tana kuka tana ba Umma hakuri tasata a motar Abba.

******
Umar kam a daki ya gama hada kayansa tsaf, cikin bacin rai ya kalli hoton frame din Abba dake makale a dakin wanda suka dauka tare, a kufule ya dau hoton ya makashi da kasa iya karfinsa sannan ya dauko jakarsa yana neman fitowa.
Da sauri Naziru ya maida kofar ya danne iya karfinsa daga waje.
A fusace Umar yace "Naziru kasan Allah in har baka bude kofar nan a duk abinda ya biyo baya karkaga laifina? Wlh zan iya tada gidannan da abinda ke cikinsa."
Naziru ya kara danne kofar iya karfinsa yace "Da alama ka fara haukacewa, ka kuma nunawa duniya kamar yanda aka daukemu 'yan kauye duk zaman birnin da zamuyi bazamu kile ba, banda rashin d'a da tunani mutumin daya rikeka kake neman ruguza rayuwar 'ya'yansa?"
Cikin tsawa yace "In ya rikeni shine ya halliceni? Ko kuwa ni daya nunamin rashin d'a'a anga laifinsa? Ko kuwa ni ba mutum bane?"
Nan fa kokawa ta shiga dan Umar iya karfinsa yake sakawa, daga waje shima Naziru iya nasa karfin yake sakawa, cikin tashin sa'a Naziru yai baya hakan yasa Umar fitowa cikin tsananin karfi.
Wani mugun kallao ya zabgamai sannan ya nunashi da yatsa yace "Inhar kai dan uwanane na jini to ka tabbatar ka kyaleni dan wlh duk mai kokarin rabani da Ibtisam to yana daga cikin makiyana." Yai magana yana rataya jakarsa, mamaki ne ya kamashi dan yana fitowa harabar yaga motar Abba na fita, ai kuwa idanunsa suka leko mai Ibtisam a zaune a bayan mota, sakar jakar yai ya biyo motar da gudu iya karfinsa, Kawunsa da ke kokarin maida gate ne ya bugamai wani kallo yace "Wallahi in har ka kuskura ka fita daga kofar gidan nan to ka shirya fuskantar bacin raina, akan wannan haukar taka zan iya sallamaka."
Turus yaja ya tsaya idanunsa suka canza launi, ya kalli Kawu yace "Kawu inhar su sun manta da farinciki na kai a matsayinka na mahaifi bai kamata ka bi bayana ba?"
Banzan kallo Kawu yamai yace "Inbi bayanka akan hauka? So hauka ne akace maka? Ko kuwa akanka aka fara so? Ko kuma akanka aka fara rasa abinda mutum ke so? Banda hauka da rashin hankali ka kalli mahaifin daya rikeka kace wai zaka saki 'yarsa yasa shima a saki daya 'yar kuma wai ya baka? Tunda nake a rayuwata ban taba ji bayani wanda yake tattare da rashin tunani da hauka ba irin wannan, ko mu dake kauye bamu shigo birni ba munsan wannan hauka da rashin tunani ne."
Huci kawai Umar yakeyi ya dunkule hannunsa yanaji kamar ya naushi gate din gidan, tabbas wlh sai dai suyi abinda zasuyi amma Ibtisam bazai taba barinta ya kwana da wani kato ba inba shiba.
Kokarin fita ya farayi, Kawu ya matso ya wanka mai mari iya karfinsa sannan yace "Wallahi in baka wuce daga nan ba sai jikinka ya fadama."
Babu alamar wucewa a tattare dashi sai dai ya daina kokarin fita, ko gizau baiyi ba da marin dan yana ganin halin da zuciyarsa ke ciki ya ninka wannan marin, a ransa yace "Ai ko tsakar dare ne zan je na dauko matata dan wlh in har wannan sokon namijin yasa hannu ya taba Ibty to lalai za'ai kisan kai a daren yau." A fusace ya juya bangarensa.


*******
Abba kam yana fita cikin karfi yaja motar dan ya hango sanda Umar ya fara tahowa, tafiya sosai yai sannan yaja gefen titi ya tsaya, hannunsa biyu yasa ya shafi fuskarsa wannan wani irin bala'i ne?
Kukan Ibtisam ne yasa ya dan sauke ajiyar zuciya yace "Ibtisam meyasa baki sanar dani halin da ake ciki ba? Da alama wannan halin na Umar ba yau ya fara shi ba."
Dagowa tai tana kuka tace "Abba bansan ya zanyi nasanar dakai ba, yaran nan dan yayanka ne wanda duk duniya ku biyu kuka rage, ka yadda da Ya Umar sama damu, Abba ban isa ko shiga cikin kawaye nai ba, sallama wannan ban isa na amsawa namiji ba, Abba tunda na fara makaranta shi ke kaini shike zuwa daukana wai duk dan karna kula kowa." Ta share hawayenta tace "ko adaidaita na shiga ban isa nai ko murmushi ba sai yace mai adaidaitan nake wa murmushi, haka rayuwata take cikin ukuba saboda shi, jin ya amince zai auri Yaya wlh na dauka hakura yai dani yana ganin ai Yaya batada lafiya tana zaman gida, duk da haka naje na sanar da Umma ta katseni, Abba bansan ya zanyi da rayuwata ba." Kuka ne yaci karfinta, gaba daya tausayinta ya kamashi. Fita yai daga cikin motar, ya kira Baffa.
Suna zaune suna cin abinci shida Aminu a gidan Ummy, dan yau ranar farinciki ce a garesu matuka, Kanin Aminu ma daga Singapo yace gobe zai taho.
Wayar Baffa ce tai kara, ya ajiye cokalin hannunsa sannan yazarota daga cikin aljihunsa. Ganin Abba ne yasa ya kara yana cewa "Sirikina baka gaji da ganina bane?"
Abba yai dan yake yace "Sulaiman ina cikin wani hali ne, wanda nake neman alfarma a gunka."
Jin haka yasa Baffa yadan mike ya maida hankali sosai kan wayar yace "Meke faruwa?"
Abba yai dan murmushin takaici yace "Ya Aminu? Ya akaji da asarar da aka mai dazu?"
Baffa yace "Haba bakomai, tsautsayi ne ai da alama yara ne basu kula ba suka buga mai." A ran Abba yace "Yanzu kam inada yakinin Umar ne."
A fili ya daure yace "So nake Ibtisam ta tare gidan mijinta, yau ta kwana a haka gobe insha Allahu za'a zo ai jere duk inda jibi take an kammala, wani uzuri ne babba ya taso wanda dole ta kwana gidan mijinta ayau din nan."
Sosai wannan kalamai na Abba sunbashi mamaki sai dai tunda yaji bai fadamai dalili kai tsaye ba ya tabbatar akwai wani babban dalilin daya hanashi.
Kallan Amini yai wanda yake cin abincinsa hankali a kwance, gashi basu gama katange Hajiyarcan ba, menene mafita?
Daurewa yai yace "Shikenan yanzu ka kawota gida na, in ma tafiyar ne sai su wuce ita da mijinta, ai dama a musulunce ba ace sai anyi gayya gun kai amarya ba."
Ajiyar zuciya Abba yai yace "Nagode sosai! Insha Allahu zan iso yanzun nan."
Wayar ya kashe Baffa ya fito daga falo ya nufi dakinsa sannan ya kira Ummy a waya. Bata jima ba ta shigo cikin fara'a tace "Alhaji! Ina cikin bakin ma baza'a barni ba?"
Zama yai a bakin gado sannan ya mata nuni data zauna kusa dashi. Kallansa take harta zauna kafin ya kwashe abinda ke faruwa ya sanar da ita.
Tayi mamaki kwarai kafin tace "in har hakane ina ganin Aminu ya dau matarsa su kwana a hotel, suje can suyi kwana uku har a kammala yi mata jeren, kafin nan an gama raba gidan."
"Hotel kuma? Da haka a kawota nan gidan mana."
Ummy ta girgiza kai tace "Dama inata tunanin yanda za'ai a basu dama su fahimci junansu, komai anyishi cikin sauri, Aminu nada yara, duk da agun Hajiya suke kwana amma agunshi suke, daga auranta za'a sata kula da yara? Ya za'ai su samu damar zama su biyu? In kawosu guna suyi sati ne? Duk wadannan tunanin sun cabemin wanda jin hakan yamin daidai, nan gidan ma in an kawota taya zasu zauna su biyu?" Tadan sauke ajiyar zuciya tace "Ga mutane a gidan nan me kake tunanin za'ace in aka ganta?"
Baffa yai shiru alamar tunani, tabbas yanzu ya gane me take nufi.
Sansanyan murmushi yai yace "Asma'u shiyasa a koda yaushe nake alfahari dake, na kuma tabbatar barin Hajiya ba laifinki bane, kinyi iya yinki fin karfinmu tai, wanda na tabbatar Allah yana tare damu."
Falo Baffa ya dawo ya sanar da Aminu wannan hukuncin, mamaki ne matuka ya bayyana a fuskarshi yace "Dama can abinda Ummy ta tsara kenan ko?"
Ummy ta hade fuska tace "Dama can haka nai niyya na tabbatar in na sanar dakai ne bazaka yarda ba, shiyasa nace a bari sai bayan an daura muku aure."
Shiru yai shifa bawai auran ba wannan takurar da za'a dinga bulomai dasu ya tsana, yanzu fisabillilahi nan akacemai ba yanzu zata tare ba, yanzu kuma anzomai da maganar wani hotel? Kamar wanda bashida gida?
Ummy ce ta katseshi tace "Ka tashi ka dau motar Baffanka yanzu za'a kawota ka amsheta ku wuce abinku, in kaje gida dauko kayanka basai ta shiga ciki ba kaje kai kadai ka kwaso ku wuce."
Mamakin yanda Ummy ta daure fuska sosai tana jawabi yake, lalai wannan shine a dakeka a hanaka kuka.
Haka ya fito duk ransa a bace, motar Baffa ya dauka, daga ciki Baffa yamai waya yace "yaje waje sun iso."
Haka ya wuce ya gaida Abba sannan ta fito ta shiga mota, kayanta tasa a baya ta zauna a gaba. Itakam ko a novel bata taba karanta amarya mara gata irinta ba, ace an kawota babu wani farinciki, uwarta ko kallan arziki bata mata ba.
Kanta kawai tasa akan cinyoyinta tana kuka, tana a haka Aminu ya shigo.
Idanunsa yadan runtse dan ya tsani kuka sam, dakewa yai yaja mota suka nufi gidansa, a waje yai parking ya shiga ya dauko jaka ya zuba kaya duk ransa a bace, wannan wani irin lamari ne? Ko auren soyayya sukai ai gida ya kamata a kawota amma wai wani hotel kamar a film sun tafi honeymoon?
Cikin bacin rai ya gama hada kaya ya fito yaja mota.
A Bristol Palace yai parking sannan ya kalleta, haryanzu kuka take, ya daure yace "Zanshiga nai check in."
Bata amsa ba shima bai jira amsarta ba, sai daya gama komai sannan ya dawo ya kalleta yace "Muje."
Dagowa tai duk fuskarta hawaye, gabanta ne ya fadi ganinsu a hotel, me zasuyi anan? Kallansa tai tana neman magana sai dai jitai batada bakin magana.
Aminu ya dau tissue ya mika mata yace "Goge fuskarki kafin mutane su dauka satoki nai."
Ansa tai ta goge fuskarta sannan ta fito sam ta manta da jakarta.
Aminu ya kalli jakar lalai wannan yarinyar, badai da saninta tabarmai jakar ya daukar mata ba?
Kallanta yai kamar zai mata magana sai kuma ya fasa, dauka yai sannan yai gaba, wuceta yai ta bi bayansa.
Babban daki ya kama musu, ta zauna akan kujera, ko sallah batai ba, mikewa tai ta kalli falan ba kowa sai ita, nufar daki tai da niyar tai alwala shi kuma daidainan ya cire manyan kayansa yana sanye da vest da wandan shaddar, kokarin yin wanka da alwala yakeyi.
Idanu ta zaro da sauri ta koma falo, bakijta nadan rawa tace "Yahkuri."
Aminu kam da sauri ya maida kayansa sannan ya zauna akan gado cikin dakewa yace "Shigo ko ba toilet zaki ba?"
Shiga tai kanta a kasa wai dan karta kalleshi, tana kokarin kuma kanta da bango taji yace "Me kikeyi hakan?"
Tsayawa tai sannan ta kalleshi da sauri, ganin saura kiris ta make kanta yasa ta sake kallansa tace "Yahkuri na dauka baka gama shiryawa bane."
Tai maganar tare da wucewa toilet da sauri, alwala tai sannan ta fito ta koma falo tai sallah, ya dade akan sallaya tana kuka tana kaiwa Allah kukanta, shikam Aminu duk kunnensa ya gaji dajin wannan kukan, wai haka amaren yanzu suke? Shi ko dan suna kaunar junansu da Na'ima ne? Dan kuka kadan tai, wannan anya ko abinci ma taci?
Yadan kauda kai ai wannan ra’ayinta ne. Harya gama abinda yake ya kwanta bata shigo ba, yanzu ya daina jin sheshekar kukanta.
Ibty kam tun tana kuka har bacci ya dauketa, dan ta rasa yanda zatai gashi Abba ya kwace wayarta yace “Ko an sai mata waya karta kira kowa saishi, itakam tanasan tasan halinda su Umma kw ciki. A haka bacci ya dauketa a durkushe.
Tun Aminu na lissafi hardai ya kasa kwantar da hankali ya mike, falon ya fito a zaune take inda tai salla ta hada kai da gwiwa, kallanta yai sannan a fili yace “Ba dole bacci ya daukeki ba, kinata kuka kamar ba gobe, kinfi awa hudu kina abu daya.
Kamar zai juya sai kuma tausayin kwanciyar datai yadan kamashi, ko ya sata a daki shi ya kwanta anan?
Hannu yasa yadan tabata yace “Tashi ki koma daki.�?
Sam bataji ba saboda nannauyan baccin daya tafi da ita, dan tabata ya sake yi da dan karfi, ita kuma daidainan tayi mafarkin Umar na janta a daji tana turjewa.
Cikin firgici ta rike hannun Aminu iya karfinta tana wani irin kuka, tana cewa “Kayi hakuri dan Allah! Na tuba!�?
Yanda ta matsemai hannu da kalamanta ne yasa yadan sunkuyo hannu yasa yadan daga kanta yace “Tashi!�?
Bude ido tai gabanta na faduwa, ta zubasu akanshi, wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata, mamaki ya kamashi yace “Sakemin hannu ko?�?
Kallan hannun tai sannan ta sakeshi da sauri, ya dan gyara zamanta, mikewa yai cikin dakewa yace “Ki wuce ciki ki kwanta, in kuma kinajin yunwa a kawo miki abinci.�?
Kai kawai ta girgiza sannan ta mike a hankali tace “Nagode Ya Aminu, banajin yunwa.�?
Abinda tace kenan ta wuce ciki, kafada yadan daga kadan sannan ya zauna ya jawo wayars ayana dube dube, kallan dakin yai yace “Tunda batajin yunwa ai tasan cikinta.�?

**********

Umar kam ya gama saitawa ta yanda zai je gida ya sato Ibtisam, ya kuma samu abokansa biyu wadanda zasu taimaka mai, sai dai abin tambayar “Inane gidan?�? Taya zaisan gidan? Wannan abu yasa sun rasa yanda zasuyi shi kuma yasha alwashin bazai kwana ba sai da Ibty…�?.



*******
Wayyo🤭 Kinaso kisan yanda rayuwar Aminu da Ibty zasu kasance? Ga kuma Hajiya a gefen hagu? Sannan ga Umar a gefen dama?
Yi maza ki mallaki naki domin free pages sun kare😔


Ayusher Ce🏌🏻‍♀�?
2/4/22, 11:11 - Ummi Tandama😇: 💫 IB💫
      (.........In Between)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*
*Dan Allah in baki siya ba karki karanta, kudi kalilan zaki biya ki samu wannan garabasar*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment