Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dominsa ya tashi ya tafi ba tare da yaci abincin ba.
Mikewa tai tace “Ya Aminu ko na zuba maka?�?
Kai ya girgiza alamar a’a sannan ya dan bude kular?�?, fried rice ce tasha hanta, ya zuba dan kadan a plate sannan ya zuba hadin salad din a gefe, bai dauke pepper chicken din ba yadan ci kadan sannan ya ajiye plate din, mikewa yai yace “Zai wuce.�?
Ta mike itama tana kokarin sanar da Umma zai tafi, tana kokarin shiga dakin taji yace “Ki sanar dani daga yau zuwa gobe inhar kin janye maganar auren, in kin kasa musu magana ni zan sanar dasu.�?
Ta kalleshi tace “In fadawa Ainah?�?
“Ainah kuma?�?
Tace “Banida numberka bansan ta yanda zan fada maka ba.�?
Hannu yasa a aljihunsa ya dauko wayarsa ya mika mata, a hankali ta tako tazo inda yake ta amshi wayar.
Hotonshi ne shida Aunty Na’imah a jikin alan wayar, da alama daga jikin hoton takarda aka dau hoton, murmushi tai sannan ta saka number tai dialling sannan ta kashe ta mikamai.
Kallansa tai a gabanta taga ya rubuta “Kawar Ainah.�?
Samun kanta tai dacewa “Sunana Ibtisam.�?
Kai ya daga bayan yasa wayar a aljihu yace “Na sani.�?
Juyawa tai ta kira Umma aranta tace “Ai sai ka canza kasa sunana.�? Umma ce ta fito nan sukai sallama, yaba Iman dubu biyar, sannan bayan ya fito mota ya ciro ledar da Ummy ta bashi yaba Iman yace “Ki ba yayarki inji Ummy.�?
Nan ya juya ya tafi yana mamakin wannan lamari…�?.
Ita kanta Ibty daki ta wuce ta fada kan gado tana mamakin wannan abu, tana ganin kiran Ainah amma ta kasa dauka yau kam batasan da wacce zatai gulmar ba dan bata isa tayi da Ainah ba da alama ma Ummy bata sanar da ita komai ba.

********

Ganin yanda Abba ke ta murna yasa Ibty ta kasa cewa a’a kuma harga Allah dama bata tsani Ya Aminu ba, bata sanshi kuma bata tsaneshi ba.
Shikam Aminu sai jira yake yaga text dinta ko kiranta akan ta fasa ya mata girma sai dai haryau babu ko flashing dinta.
Shi kuma yana ganin yayi girman da bazai kira yarinya karama yana tambayarta ra’ayinta akanshi ba.
Ganin yanda Ummy keta shirin hada lefe yasa duk ya rasa abin yi, gashi duk wannan abin da ake haryau Ainah bata sani ba.

******
Ibty kam a skul duk yanda Ainah ke binta akan ta bata labari taki, har ta gaji ta daina tambayarta.

*******
Yau tafiyar Umar kwana biyar, a yau kuma Ummy ta sake turo Aminu yazo zance da daddare, sannan su kuma gobe suke sa ran kai kayan lefen da suka hada cikin gaggawa.
Umar ya gaji da kauyen nan ko ince ya gaji da rashin Ibty, da safe ya shirya tsaf yana san tahowa, yana shiga dakin mahaifiyarsa ya tadda ita a kwance ba lafiya, ashe tun daren jiya take amai da gudawa. Wannan lamari yasa dole ya fasa tafiya a wannan ranar, haka suka kira likita yazo ya daura mata drip a cikin gida.

*******
Ummy yau ta samu kanta da samun shawarar data kara kwantar da hankalinta, Baffa na shigowa bayan yaci abinci sunyi sallah tace “me kake tunani in muka katangewa matar can bangarenta? In har bazamu iya korarta daga gidan ba ai zamu iya raba gidan da take ciki da inda Aminu da Ibtisam zasu zauna.�?
Baffa dadin wannan shawarar ya kamashi yace “Ya akai wannan shawarar bata taba gifta mana ba?�?
Ummy tace “Da alama alkairi ne yake binmu a wannan auren haka kawai daren jiya wannan shawara tazomin, ku katangeta a fitar mata da kofarta ta waje, duk masifa da bala’inta ai sai ta shiga cikin gidansu ko? Kuma duk rashin hankalinta bazata dinga afka musu gida ba, dan dama Aminu bai bari tana shigar mai gida ba kaga in taga an barta ita kadai zata gaji tabar gida, balle in taga Aminu yana rayuwar farinciki da matarsa.�?
Wannan shawara ta musu dadi, Baffa ya sanar da Aminu kuma shima bai musa ba dan shi dama damuwarsa bazai iya barinta bane, alkawari ya dauka yana ganin hakkinsa ce ya kula da ita.

*******
Ibty tayi zugum a daki tana tunanin yanda zasu kwashe yau da daddare in Aminu yazo, gashi Umar ya isheta da kira, number number, kwanciyar hankalinta kawai ta kashe wayarta gaba daya, dan batasan me zatace mai ba bayan an riga anba yayarta shi, sannan tana sa ran tunda dai Yaya ba fita take ba Umar zai kula da ita…�?..


Hmmm


Ayusher Ce🏌🏻‍♀�?
2/4/22, 11:09 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
(.........In Between)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

*Free Page*

Ki hanzarta ki mallaki naki dan Free Pages sun kusa karewa🤸🏻‍♀�?

*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA 500 TA* *Ya samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

+447894142004

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730


Page 8

Yau ankai laifi duk da ba'ai karya ba amma kaya kam anyisu masu kyau da tsada, Yayar Ummy da kanwar Baffa ne suka kai, a cewarsu tunda abin na gaggawane basu samu damar yin gayyata ba, sai dai a zahiri sunyi haka ne dan kar labari yakaiwa Hajiya, haka kawai ta tashi taga ana gini a gidanta, tasan sarai abinda Ummy ke shirinyi sai dai a ganin ta a banza, dafarko dai su Ilham a gunta suke, a kuma gunta suke kwana, duk wani abu na Ummy sai dai tayi ga gama gida ne duk duniyar nan bataga mai rabata dashi ba, ita kadai tasan wahalar datasha a kauye bayan auranta ya mutu, har mayya sai da akacemata, yanzu kuwa da Allah ya kwaceta gani take bamai sake maidata gidan jiya.

*****
Ibty tana zaune da daddare suna ta kallan kayan dasu Iman ke dagawa, jiya akace Aminu zaizo saidai har dare bai zo ba karshe dai Abba aka kira aka sanar dashi aiki yadan rikeshi dole ya tafi Abuja, amma yau inya dawo nan zai fara zuwa.
Itadai tana zaune tana kallansu sam ji take kamar bada gaske bane, wai ita ce za'a a daurawa aure nanda sati daya, to dama haka ake auren a gurguje? Duk da ance ba tarewa zatai ba amma a kalla ko 'yar waya sa dingayi da wanda zata auran, sai dai har yau ko Hi bai kara hadasu ba. Gashi tanasan yiwa Ainah gulma ba dama.
Yaran makotarsu ne yai sallama cikin mamakin ganinsa bayan isha ba tare da sunji an kwankwasa ba, Umma tace "Sani kofar a bude take?"
Ya daga kai yace "Ina turawa naga ta bude."
Da sauri Umma ta kalli Iman tace "Kece karshen shigowa kina tafe kina latse latsen wayar taki hala kika manta baki rufe ba? Kindai fi kowa sanin halinsa kasar nan tamu take ciki, ka rufe gida ma ya aka kare bare ka bar gida a bude.
Cikin sanyin murya tace "Umma yahkuri."
Sani ya kalli Ibtisam yace "Ana sallama dake a waje."
Kallansa tai ta nuna kanta dan jin abin tai wani banbarakwai tace "Ni?" Ya daga kai yace "Eh wai inji Yayan kawarki."
Da sauri Umma ta wurga mata wani kallo tace "Waye yake sallama? Bayan an riga an bada ke?"
Cikin dan shagwaba tace "To ai shine yayan kawar tawa." Ta mike tai daki cikin takaicin wannan abu, meye zai wani ce yayan kawarta? Harta dau powder zatadan shafa kawainta ajiye ta zari hijab ta zunbula ranta duk a bace. Tana kokarin fita Iman tace "A haka zaki?"
Bata ko tankata ba ta fito, Umma tadan guntse dariyarta kafin tace "In borin Ibty ya tashi ai sai a hankali, gwara yasan halinta tun yanzu."
Dariya sukasa dukansu suka cigaba da kallan kaya.
******
Yana zaune a cikin mota ta karasa jikin motar daga gefe ta tsaya ba tare da tace komai ba, shi kuma yana zaune a mota ya kurawa hoton Na'ima ido a hankali ya maida wayar ya ajiye yana duba agoggon hannunsa, kodai yaran baikai sakon bane? Gashi ya gaji dan daga Abuja yake ko gida bai je ba Ummy ta takura sai ya fara biyowa nan.
Fitowa yai da niyyar sake aiken wani yaran, mamaki ne ya kamashi ganinta tsaye daga gefe ta jingina da jikin motar tana kallan mutanen dake wucewa.
Maida kofar yai ya rufe sannan yai dan gyaran murya irinta manta, kallansa tai cikin dan dakewa tace "Ina wuni?" Cikin mamaki haryanzu yake kallanta yace "Lafiya kalau me kike a tsaye anan?"
Cikin dan kunkune tai magana hakan yasa yace "Me kikace?"
Ta girgiza kai alamar bakomai, ko zaginshi tai? Abinda yazo mai kenan, lalai Ummy tana neman jawomai raini shifa sam kunyar ma tsayawa yake da yarinya karama haka.
Shiru sukai kai kace zancen kurame akazo, to wai me zaice? Shifa sam baisan me zai cewa yarinya ba.
Itakam Ibty itama shiru tai tana tunanin ko zai sake tambayarta meyasa ta tsaya anan, dan yanzu kam so take ta daure ta fadamai dalilin.
Ganin shirun yaki karewa yasa yace “Akwai wani abu da zakiyi da biki ne?�?
Kallansa tai kafin ta girgiza kai alamar a’a tace “Komai cikin sauri akeyi sai dai in zan tare.�?
Ya jinjina kai yace “Inda wani abin sai ki sanar dani na baki kudi.�? Yai maganar yana mika mata envelope yace “kiyi amfani da wannan yanzu.�? Ta kalleshi bata amsa ba cikin girmamawa tace “Ni Allah ba abinda zanyi da kudi, in ina bukata zan fada maka.�?
Kafeta yai da ido haka kawai ko tanasan rama abinda ya mata ko tanasan maida mai murtani inta kalli idansa sai taji ta kasa, hannu tasa ta amsa sannan tace “Nagode.�?
Bai amsa ba sai cewa yai “Inba wani abin ni zan wuce.�?
Matsawa tai daga jikin motar yana kokarin shiga tace “Sai yaushe Ainah zata sani?�?
Kallanta yai ta sauke kanta kasa yace “Sanda Ummy ta sanar da ita, na dauka saboda kawancenku zaki sanar da ita.�?
A hankali tace “Gani nai bata sani ba bankuma san meyasa ba’a sanar da ita ba, sai naga kamar banida hurumin fada mata.�?
Shiru yai yana kallanta, wanda har tadan tsargu ta dago ta kalleshi, bai taba tunanin jin magana ta hankali agun yarinya karama haka ba.
Murmushi yai yace “Zan wuce.�?
Kai ta daga sannan tace “Agaida su Ilham.�?
Juyawa tai ta shiga ciki duk haushin kanta ya isheta, haka za’ai zaman auren bata iya magana daga ta kalleshi? Oh itakam wannan shine gaba kura baya damusa, sai dai duk da haka auranshi yafi mata na Umar.

********
Umar kam a kauye duk yabi ya daga hankalinsa ga kwanan nan tsabar missing din Ibtisam ko gyangyadi yai sai yayi mafarkinta, abin takaici numberta kawai ya hadace sai number Abba shi kuma sunyi waya a wayar Kawunsa, yanzu Abba sirikinsa ne bai isa ya tambayeshi Ibty ba.
Duk abin duniya ya dameshi ga jikin Goggonsa yaki warwarewa, shi so yai ya tafi a haka amma Yayanshi ya hanashi yana ganin taya zai tafi bayan mahaifiyarsa ba lafiya?
Umar har wata rama yai na rashin Ibtisam ya mata text yayi kiran har ya rasa kuma abinyi, yanzu kam kawai jiran sanda zasu barshi ya taho yake dan shikam gaba daya komai ya fita a kansa, hira wannan basanyi yakeyi ba.

******
Akwana a tashi asarar mai rai, Abba ya samu ya kammala gyaran bangaren da Bilkisu zata zauna, ya kuma fara shirye shiryen kayan dakin Ibty dan a san ransa in akai ta tare bayan wata daya ko sati uku dan baisan ai aure yarinya ta dade sosai a gida balle ita da take karatu.
Gidansu Umma har an cicika ‘yan uwa yau tun safe suka bayyana, shima Umar yau da safe ya iso dan baya azahar ne daurin auren, Abba yasa an mai dinki ya kuma amso mai, tun a hanya Umar duk ya susuce yanaji kamar yai tsale ya ganshi a gidan, suna isa ya fara kokarin cusa kanshi cikin gidan sai dai abin haushi gidan ya cika da mata anata hidima, ta ina zai nemo Ibty? Gashi sai tsokanaraa ake wai ango ango wai basu yarda yaga amarya ba yanzu sai ya jura sai an daura, haka ya fito kunya duk ta kamashi to shi gaskiya ana daura aure a bashi matarsa su tare tunda dai abin haka ne.
Wanka yai a bangarensa yayansa sai tsokanarsa yake, ya dauko dakakiyar farar shaddar da Abba ya dinka mai ya saka, ya saka babbar rigar nan fa ya fito cas dashi.
A’a ango kasha kamshi inji Ayusher🤩

*******

Acan gidansu Ummy kuwa suma yau yayunta sunzo da kannenta, haka kannen Baffa, batai gayya ba su kadai ta sanar tana ganin a bari in zata tare mutane saji burinta dai a daura auren in dai an daura to komai ya wadatar.
Ainah yau tasha mamaki bayan asuba da Ummy ta sanar da ita za’ai auran Aminu sai dai bata fada kata da wacece ba, duk da haka tayi murna saboda ita kanta tanasan taga Yaya Aminu yayi aure.
Baffa yasha manyan kanya hakama Aminu yasha fararen kaya, yayi kyau matuka, Ummy kam ta kasa rufe baki sai addu’a take zubgamai.
Haka suka fito suka shiga mota, yan uwan Baffa su daga can zasu wuce, Aminu dama shi ba abokai gareshi ba balle yai gayya, kuma shi a ganinsa ma da kunya yace zai auri yarinya sa’ar Ainah.

*******
Masallacin ya cika sosai da mutane, anan Umar yaji labarin auren mutum biyu za’ai, bayan zuwansu Aminunya kure mai kallo yana mamakin mutum irinsa babban mutum haka dan kana kallansa zakasan kudi ya zauna mai, shi kuwa ya rasa wacce yakeso sai Bilkisu? To ko dai yanada wata lalular ne a boye? Inba haka ba baiga wani dalili ba.
Hannu ya mikawa Aminu sukai musabaha yana mai kallan tausayi tare da zargin abinda ke damunsa a boye.
Aminu kam bai tsaya wani kallan Umar ba balle yasan wanene shi suna gaisawa ya wuce ya cigaba da gaisawa da mutane, Umar yana jiyo wani mutum abokin Abba yana cewa “Wannan ne mijin Ibtisam din?�?
Umar ya matso yana murmushi, gani yai mutumin na kallan Aminu, tsaki yadanja yace “matsalar a hada auranka da wasu kenan sai mutane su fara kuskuren fuskokinku.�?
Nufar mutumin yai da niyar mai magana, yayansa ya dafashi yace “Kai kuma rashin hakurin na menene? In an daura ai zai ganka ko?�?
Haka suka shiga cikin masallaci nan fa aka fara addu’oi, gaba daya Umar ji yake kamar a mafarki lalai wannan rana tafi ko wace rana mahimmanci a tattare dashi, yau zai cika burinsa na auran masoyiyarsa abin begensa abin kuma alfaharinsa.
Sam baiji sanda akace an daura auran Umar da Bilkisu, Aminu da Ibtisam ba, gaba daya kunnensa shidai ya jiyomai Umar da Ibtisam.
Yayansa ne ya dan dafa cinyarsa cikin rada yace “Meke faruwa? Naji ance Umar da Bilkisu?�?
Umar ya bude idanunsa yace “Kai wallahi inaji ka fara tsufa ina nan naji ance Umar da Ibtisam kai mai kake tunani?
Da sauri yace “Ba haka akace ba wlh na tabbatar ji nai ance Umar da Bilkisu.�?
Tsaki yadan yi yace “Kai dalla banasan zancen banza ranar farinciki na. Kunnenka yak ta jiye maka karya.�?
Shikam Kawun Umar gaba daya shima jikinsa ne yai sanyi dan tabbas ba haka Umar yace mai ba, meke faruwa? Taya za’a hada dansa da nakashashiya?
Mutane anata musabaha ana rarraba goro, nansu Umar suka fito dan daukan hotona, abokansa da suka taho daga kauye suka kwashe mai da dariya daya ya dafashi yace “Ha’a na Ibtisam bada kanka a sare kaje gida kace ya fadi, kace da Ibtisam za’ai ya akai ka kare da gurguwa? Wancan babban guy din ya maka dan kafa?�?
Kansa ne yaji yayi wani gingiringin, kallansu yai idanunsa suka dan kada suka fara jaa yace “Banasan hauka da rashin hankali uban wa kake cewa ya auri wata?�?
Kallansa sukai, dayan yana dariya yace “to ko limamin ne yai kuskure? Dan dai aure da Bilkisu aka daurama.�?
A zuciye yakai mai wani wawan naushi ya cakumeshi yana neman sake naushinsa, yayansa ne ya riko hannunsa da sauri ganin mutane harsun fara nufo gun, janshi yai bayan masallacin dashi.
Umar sai huci yake cikin kunar rai yace “Bani dan Allah na fasawa yaran nan jiki banasan dakikanci da jahilci.�?
Cikin tausayi yake kallansa yanzu kam ya tabbatar abinda yaji gaskiya ne kenan Umar da Bilkisu aka daura mai, lalai in Umar yasan maganar nan gaskiya ne baisan me zai faru a masallacin nan ba dan tabbas Umar bazai taba barin abin nan ba dan zuwansa kauyen nan kowa ya fahimci mugun san da yake yiwa Ibtisam…�?


Hmmmm nikam Ayusher a guje nabar masallacin dan nasan in Umar yasani harni za’a yiwa illa haka kawai baza’a karyamin dan kafar da nake ji da ita ba…�?


Ayusher Ce🏌🏻‍♀�?
2/4/22, 11:10 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
(.........In Between)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

*Free Page*

Ki hanzarta ki mallaki naki dan Free Pages sun kusa karewa🤸🏻‍♀�?

*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA 500 TA* *Ya samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

+447894142004

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

Page 9

Girgizashi yai yace "Umar ka dawo da hankalinka nan, kai baka tambayi yarinyar da aka ce an baka bane? Koni magana ta gaskiya kunnena abinda yajimin kenan auran Umar da Bilkisu."
Fizge jikinshi yai yana huci ya nunashi da yatsa yace "Yaya Naziru karka batamin rai wallahi in raina ya baci ba abinda bazan iya aikatawa ba, uban waye zai sani auran wata a duniya inba Ibtisam ba Yarinyarnan mata tace tun farko kuma wlh duk wanda ya nemi shiga tsakanina da ita zan iya mai ila."
Shi kanshi Naziru ya tsorata da yanda Umar ke magana, a tsorace ya sakeshi yana kallan yanda yake wani huci, Umar ya kalleshi yace "Bari naje gun Abba ko shi limamin sai ya sanar dani meke faruwa."
Naziru kam ya fahimci lalai akwai matsala da sauri ya juya ya nufi inda Kawunsa yake cikin mutane, shikanshi Kawun jikinsa duk yai sanyi kawai dai yana yake ne cikin mutane amma yasan tabbas akwai matsala. Yana hango Naziru ya nufoshi da sauri yace "Ina Umar?"
Naziru jiki a sanyaye yace "Ya tafi neman Abba ko Liman."
Shafar fuskarsa Kawun yai yace "kafin yaran nan ya sa mutane sumana kallan mahaukatan kauye kajashi ya bat gun nan."
Cikin damuwa Naziru yace "Matsalar yaki tsayawa ya saurareni, bansan ya zanyi ba Kawu."
Da sauri Kawun ya shiga neman Umar a cikin mutanen, masallacin ya nufa dan yafi kokontan can zaije, yana shiga kuwa ya hangoshi a tsaye da alama mutanen dake durkushe kusa da limamin, da sauri Kawu yasa hannu ya rikoshi suka fito.
Umar gaba daya ya firgice yace "Kawu tambayar liman nake san yi me yasa yace ya bada auran Bilkisu gareni? In ma kuskure yai ya dawo ya kira mutane a sake daura aure."
Kawun ya jashi can gefe yace "Umar bansan meya faru ba tsakaninka da uban rikonka, sai dai tabbas shi Bilkisu ya baka, sai dai in kaine baka tsaya ka fahimceshi ba, bayan an daura aure dakanshi a masallaci yace "Yaya nikam Umar ya gamamin komai tunda ya amince da auran Bilkisu."
Rai a bace ya nuna kansa yace "Ni? Wlh cutata akai ni ban taba kawo auran nakashashiya ba, Kawu Allah cutata yai, bakuma zan yarda ba, duk bala'in da za'ai sai dai ayi amma ba wanda ya isa ya rabani da Ibtisam."
Baiko tsaya jin me Kawu zaice ba ya wuce ya fara tafiya ransa na wani irin kuna, motar da su Aminu ya kalla wacce yaganshi dazu ya iso a ciki, a kufule ya dau dutse ya kalli gefe da gefe ganin gun ba mutane kawai ya buga gaban motar iya karfinsa sannan ya wuce. Karar glass din motar da mutane sukaji ne yasa suka juya, shikam adaidaita ya tara kawai ya shiga.
Ganibyai mai adaidaitar baya sauri cikin bacin raj yace "Kai Dalla malam kajani da sauri wannan tafiyar kamar wani dan koyo? In kasan baka iya ba uban wa yace ka fara sana'ar?"
Wannan magana ta batawa mai adaidaita rai gashi shima dama ba hakuri gareshi ba, parking yai a gefen titi yace "Kai bansan hauka da iskancin, tashi sama kake so nai ko me? In shaye shaye kai kaje can ka sau........" Ai Umar ya gama kaiwa wuya cakumo kwalarsa yai ya daga hannu yana neman kaimai duka, shima mutumin ya cakumo wuyan Umar, ganin baisan bata lokaci yasa ya sakeshi rai a bace ya fito ya tari wata, gaba daya huci kawai yakeyi.

********
Gida kam ya cika sosai da mutane anata hidimar yin abinci an sauke wasu ana daura wasu, a daki kam Ibty tana zaune ita da kawayenta 'yan uwa sukaji ana guda ana cewa an daura, sanye take da wani hadaden lace wanda Abba ya dinka musu ita da Yaya Bilkisu iri daya, sunyi kyau iya kyau ga dinkin ya karbesu, Iman dama ta iya makeup ita ta zane musu fuskarsu, sunyi kyau sosai abinsu.
Bilkisu tana kasa cikin mutane su kuma suna sama anata hira, itakam sam batajin dadi haka kawai takejin jikinta kamar mai zazzabi, Ainah ce ta kirata dagawa tai tare da dan matsawa gefe tace "Ainah!"
Ai Ainah bata amsa ba tace "Ibty yau naga abinda ya hanani sukuni, wai yau ake daura auran yayana amma ba wanda ya fadamin?"
Dan idanta Ibty ta runtse tace "Ainah maganar gaskiya......."
"Ibty kinsan abin dariyar? Sunanku daya da amaryar."
Yawun bakinta ta hadiya tace "Ainah wai nice amaryar."
Ainah bata fahimci me take nufi ba tace "Kece me?"
Kiran da aka kwalla ma Ibtisam ne yasa tace "Zan kiraki anjima" bata jira me zatace ba ta kashe wayar, fitowa tai daga dakin, kanwar Umma ce ta kalleta tace "ki sauko mai hoto yazo."
Kai ta daga sannan ta koma ta dauko mayafin kayan sannan ta sauko, sun tsaya kenan ana shi shiryawa za'a dau hoto tundaga wajen harabar gidan sukaji ana kwallawa Ibtisam kira cikin kakkausar murya, gabanta ne ya yanke yai wani irin faduwa balle dataji muryar Umar, me yake yi hakan? Ta dauka dai yanzu komai ya wuce ko?
Kafafunta ne suka dan fara rawa jin yanda yake kiranta kai tsaye kuma kana ji kasan muryar bacin rai ce.
Gaba daya mutanen falan mamaki ne ya kamasu, Umma ta mike cikin mamaki tace "Umar lafiya kuwa?"
Suna kokarin fitowa ya shigo cikin falan, ya cire babbar rigar ya rike a hannunsa, bai damu da taron mutanen dake falan ba ciki kuwa harda mahaifiyarsa, idanunsa kawai ya sauke kan Ibtisam yace "Ibty meke faruwa?"
Kallansa tai gaba daya ta kasa magana sai rawa da jikinta kawai yakeyi, takowa yai yazo inda take yanayinsa ya canza sosai cikin tsawa yace "Meke faruwa nace?"
Baya tadanyi gaba daya jikinta ya kasa daina rawa, cikin fada mahaifiyarsa tace "Umar me kakeyi hakan? Bakaganin manya ne? Ko sallama da gaisuwa bakai ba kazo ka tsareta kamar 'yar cikinka."
Kallan Goggon yai ji yake kamar yai ihu, wani mugun kallo ya zabgawa Bilkisu sannan ya kalli Ibtisam yace "Wuce muje ki fadawa Abba dani za'a daura miki aure kafin ranki ya baci a cikin gidan nan."
Jin wannan kalmar yasa gaba daya matan dake gun suka sauke salati, Umma cikin tsananin mamaki tace "Mene? Umar me kake cewa?"
Ibty kam zubewa tai a kasa kawai jikinta na rawa, ta kasa ko magana balle hawaye.
Umar ya kalli Umma yace "Ibtisam nake so kuma ita tafi kowa sanin tsawon lokacin dana dauka ina santa akan me za'a dauramin aure da Bilkisu?"
Nan fa falo ya kara rincabewa gaba daya kowa yahau salati ana kallan ikon Allah, yau meke faruwa a gidan nan? Umma kam ta kasa ko magana sai kallan Umar da takeyi.
Shikam ko a jikinsa ya kalli Ibtisam yace "Bakiji nace ki tashi ba?" Yai maganar yana kokarin fizgota, cikin tsawa mahaifiyarsa tace "Kaci gidanku Umar, mu zakayiwa diban albarka? Ka fita daga nan ko sai na sharara maka mari? Hankaline bakada shi ko tunani ne bakadashi?"
Kallan Goggo yai kawai ya dunkule hannu, ya fara huci

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment