Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba yasa tace "muje amma ba dadewa zanyi ba kar Umma ta fara cigiyata."
Dadi ne ya kama Ainah, nan tayiwa Mamman waya akan yazo ya dauketa.
Tare suka fito suna tafe suna hira, Ainah na bata labarin wani saurayi dayace yana santa.
Ibty tana dariya tace "Amma dai ba soyayya zakiyi da mate dinki ba ko?"
Ainah tadan dafata tace "Hajiya soyayya nace zanyi ba aure ba, dan chilling da rage dare."
Mota suka shiga sunata hira da shewa, Ibtisam jinta tai kamar ba ita ba, yau wace rana? Wai itace take tafe gidan kawa hankali a kwance?
  Sun isa tafkeken gidan da tun daga waje zai baka sha'awa, gida biyu ne a hade iri daya kana gani kasan tare aka ginasu, gidan Baffa nesaya Ummy ce a ciki daya kuma kishiyarta.
Na farkon suka shiga yai parking suka fito, hannunta Ainah ta riko duk sai zumudi take, suna shiga ko sallama batai ba tai ba ta fara kwallawa Ummy kira.
Ummy wacce ke kitchen ta fito tana cewa "Ainah nikam dan Allah sai yaushe zakiyi hankali? Ko sallamarki banji ba sai kiran sunana da kike kamar wacce kika ban ajiya." Tana kaiwa nan ta karaso cikin falan, Ummy ce ta kalli Ibtisam wacce tai saurin tsugunawa har kasa tana gaisheta. Cikin sakin fuska sosai ta amsa, Ainah tana dariya ta matso kusa da Ummy tace "Canka Ummy, wacece?"
Kallanta ta sakeyi tace "Yawanci dai kawayen da ke zuwa nasan sunan su wannan ban taba ganinta ba, sai dai tabbas na taba ganin hotonta, ko Ibtisam ce?"
Kasa Ibty tai da kanta tana murmushi tare da wasa da yatsun hannunta. Ainah tana dariya tace "Bingo! Ummy wallahi in kika shiga exam hall tsaf zaki fito da A."
Alamun duka takai mata ta kauce da sauri, Ummy tace "Ibtisam lale marhaban mutuniyar sinasir."
Kunya ce ta rufeta tai kasa dakai tanaji kamar ta nutse, Ummy tai dariya tace "Duk sanda akai sinasir sai Ainah tace "Wayyo mutumin Ibty."
Dan murmushi tai nan suka dan sake gaisawa Ummy sai sake binta da kallo take, haka kawai kaunar yarinyar ta shigeta, ita macece wacce takesan taga yaro da kunya abinda yai karanci kenan a gun 'yan matan zamani, har suka shiga dakin Ainah idanunta nakan Ibtisam haka kawai ta samu kanta dayin murmushin jin dadi.
Da sauri naga ta girgiza kai tace "Lalai Asma'u kin iya san kai, yanzu harkin farawa Aminu sha'awar yarinyarnan? Karfa ki manta sa'ar Ainah ce? Danki kuwa yayi aure harda yara biyu."
 
****
Sallar la'asar sukai suka zauna sukaci abinci, bayan sun gama ne suka zauna suna hira, Ibtisam tana kallan picture album din da Ainah ta kawo mata.
Kallan family picture dinsu tai wanda kana gani xakasan da biki akayishi, tace "Nasan ki nasan Ummy, nasan Ya Aminu, wadannan fa?"
Ainah yadan nuna picture din amaryar tace "Itace marigayiya" kallanta sosai Ibty tai tare da mata addu'a a zuciyarta, Ainah ta nuna mata saurayin dake gefen Aminu tace "wannan shine maibin Yaya sunanshi Abbas yana karatu a Canada, sai wannan daga shi sai ni shi kuma yana NYSC"
Ibty tai murmushi tace "Sai ke auta mace."
Gira ta daga mata tace "'yar budurwa ba? Yar lele."
Dariya sukai, Ibty ta kurawa matar Ya Aminu ido lalai sun dace dan dukanninsh farare ne kuma dogaye.
Kofa aka turo da karfi ana ihu da kiran sunan Ainah, da sauri ta mike ta rugume kyawawan yaran guda biyu a jikinta tare da manna musu kiss tace "Saukar yaushe?"
Islam cikin zakin murya tace "Mun taso daga islamiya mukai ta rokar Dady a waya akan ya bari a kawomu, shine yace muzo ya zo ya daukemu."
Kallan Ibtisam sukai wacce ta kura musu ido cikin sha'awa, Islam tace "Wacece ke?"
Ibty tai murmushi tace "Kawar Aunty?"
Gaisheta sukai Islam ta matso tadan taba dimple din Ibtisman tace " Aunty kawar Aunty nima ina san wannan abin kisamin dan Allah."
Gaba daya dariya sukasa, Ilham tace "taya zata saka miki?"
Tadan matso kusa da ita sosai tace "kinji Aunty kawar Aunty?"
Dariya Ibty tai tace "To shikenan, rufe ido."
Da sauri ta rufe idanta, Ibty tadan dangwali kuncinta tace "bude kika na sa miki."
Cikin zumudi ta tafi madubi ganin bakomai yasa ta turo baki tana shirin kuka, da sauri Ibtisma ta matso tace "Kiyi hakuri kinji, wannan halitace bayanda zanyi na saka miki, kinga kamar ke kinaga ke fara ce nifa?"
Ta girgiza kai, tace "to in nace ki maidani fara zaki iya?"
Da sauri ta sake girgiza kai, tace "to kingani, halittar Allah ba'a canzata, ko?"
Kai ta daga alamar gamsuwa.
Ummy da ke jikin kusa da dakin, jin motsinsu Islam ta taho taji muryarsu a dakin Ainah zata shiga taji Ibty na ma Islam bayani, wani irin kaunar ta ce ta kara shigar ta anya itakam basai dai ace tayi san kai ba? Da alama Allah ne ya kawo mata Ibtisam saboda ya riga ya rubuta, in ta duba yau Aminu ya yarda da auran nan, sannan yarinyar da bata taba zuwa gidanta ba yau tazo, agoggo ta kalla tana fatan Allah yasa karta tafi harsai Aminu yazo dan ta tabbatar yana hanyar tasowa daga aiki.
Islam ce ta rungume Ibty tace "Aunty kawar Aunty muma kizo gidanmu ki zama kawata nima, kinji?"
Dariya tai tace "To shikenan."
Mikewa tai ta kalli Ainah tace "Kinga bari na wuce gida dukda nacewa Umma zanzo na gaida Ummy banasan magrib tayi ina nan"
Ainah tace "Ni hakan ma nagode ai yau bakiji yanda nakeji ba."
Tare suka fito suka nufi falan Ummy wacce tasa waya a gaba tana kiran Aminu dan yai sauri yazo.
Suna shiga falan yana dagawa, cikin sauri tace "Aminu ka kusa isowa?"
Yace "Eh Ummy nan da minti biyar zan iso."
Kashe wayar tai tana dan murmushi, kallan Ainah tai da Ibtisam wacce ke tsugune a kasa tace "Ibtisam har zaki wuce?"
Tace "Eh Ummy banasan magrib tayi ban isa gida ba."
Cikin jin dadi tace "Bakomai, bari nazo."
Mikewa tak ta shiga daki ta dauko turare guda uku masu tsada da kamshi tasa a leda tare da kallan agoggo, zama tai a bakin gado tana fatan Allah yasa abinda ke faruwa alkairi ne a garesu, itakam ji take hadin nan hadine daga Allah.
Sai dataji alamar ana tura gate sannan ta fito daga daki, mika mata leda tai suka fito tare, shi kuma daidai nan ya fito daga mota.
Ibtisam tana ganinshi ta koma daya bangaren gefen Ainah, tare da sauke kanta kasa.
Ummy ce ta amsa gaisuwar da yake mata tace "Aminu dan taimaka ka sauke kawar Ainah gida mana? Magrib ta kawo kai."
Mamaki ne ya kamashi dan tunda yake Ummy inba kawayenta ba bata taba cewa ya sauke wata ba, cikin mamaki yace " Maman ya sauke ta mana."
Tace "Aikenshi zanyi yanzu kuma aiken na sauri ne banasan ya dau lokaci bai dawo ba."
Wannan amsar ta bashi mamaki matuka yace "Ummy su fita tare ya sauketa sai ya wuce aiken ko?"
Tace "Ni dai nace ka sauketa ko?"
Kamar zai sake magana sai ya fasa, Ainah kam baki kawai ta bude tana kallan Ummy dan ita kanta bata taba ganin haka ba.
Ibty kam hankalinta ya tashin jawo Ainah tai tace "Ainah taimakamin dan Allah kafin Ya Umar ya fasa muku mota."
Zaro ido Ainah tai dan sam ta manta dashi, tana kokarin magana taji Ummy tace "Ibtisam shiga kinji."
Kallan gaban motar da Ummy ta bude mata tai, gabanta sai dukan uku uku yake, harta hangosu a police station Ya Aminu ya kai karar Umar.
Idanu ta runtse, muryar Ummy ce ta katseta tace "Ibtisam shiga mana."
Haka ta shiga ta zauna duk a tsorace, kallanta yai sosai yanzu kam ya gane ta itace ta dazun nan.



Ayusher Ce🏌🏻‍♀�?
2/4/22, 11:07 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
(.........In Between)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

*Free Page*


*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA KUDINSA TA*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*

*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.

Page 5

Gaba daya Ibty ji take kamar an kwara mata ruwan sanyi, ta takure daga gefen mota kai kace satota akai.
Haka kawai ta samu kanta da farayin lazimi tana addu'a akan Allah ya tsaresu da ganin Umar dan itakam ta kasa auno abinda zai biyo baya.
Aminu ne ya shiga wajen tuki yana mamakin wannan abu, shikanshi ba kasafai yake tuki ba amma yau Ummy tana sashi ya tuka kawar kanwarsa? Yarinya karama? Fuskarsa a daure kamar yanda ya saba ya zauna sannan ya kunna mota.
Ummy kam kallansu take cikin tsananin sha'awa, ganin ya zuge glass din motar yasa ta kalli Ainah tace "Wuce ciki ko?" Nan ta juya ita kanta fargabar abinda zai faru take ga tasan Yayanta sarai shima baya barin ta kwana ga babban abinda ya tsana raini.
Shiru ne ya bayyana a cikin motar sai karar radio wanda ake gabatar da shirye shirye.
Ibty ta daure cikin dakiya tace "Ya Aminu ina wuni?"
"Lafiya." Kawai yace bai sake magana ba, ganin haka yasa itama taja nata baki tai gum.
Sun hau kan titi can yadan kalleta ta gefe, ta wani takure kamar wacce ke jin sanyi, kansa yamaida kan titi ba tare da ya tanka taba.
Bakinta na dan rawa take cewa "Nan zamuyi"
An kusa zuwa layin gidansu taji wayarta tana kara, garin saurin dauka yasa ta fadi inda kafafunta suke, kasa tai da sauri tana kokarin daukowa ji kake kum ta make goshinta, da sauri tasa hannu tana dan murza gun dan taji zafin buguwar.
Aminu ya kalleta tare da girgiza kai, dauka tai ganin sunan Umar yasa gabanta ya sake faduwa, dagowa tai tana san mai magana taga harsun wuce layin gidan, da sauri tace " Ya Aminu can ne layin gidan ban kula munzo nan ba."
Kwana yai da motar kafin yace "Kin tabbatar dai lafiyarki kalau ko?"
Mamaki ya kamata tace "Eh, me ka gani?"
Inane layin? Abinda yace kenan ta rasa ta inda zata sake tambayarsa me yake nufi da lafiyarta kalau? Kwarjini yake mata haka ta hadiye maganarta.
Suna isa titin gidansu tace "Yaya Mun iso." Magana tai ba tare da ta kalli jikin gidan da suke ba, itadai fatanta kawai ta sauka kafin Umar ya gansu.
Kallan makeken gidan dayake jikinsa yai sannan ya sauketa, nan ta mai godiya ta fita, ga mamakinsa gani yai ta fara tafiya. Ya girgiza kai cikin takaici yace "Bansan meke damun wasu yaran ba, yanzu menene na karyar gida?" Kallanta ya sake yi da yake ta titin zaibi kawai ya mike titin.
Tun daga dan nesa Umar dake tsaye a waje yanata safa da marwa ya hangota, a guje ya nufo inda take, Aminu dake cikin mota yana kallan sanda ya isa gunta, jan motarsa yai ya wuce.
Umar yana dan haki yace "Ibtyna ina kika shiga? So kike damuwarki tasamin hawan jini?"
Juyawa tai taga Ya Aminu ya wuce hakan yasata sauke wata nannauyiyar ajiyar zuciya, sannan ta kalleshi tace "Gidansu Ainah naje." Hannu ya dunkule kamar zaiyi masifa dan har tadan kauda ido tana jiran ya fara zazzagowa, sai jitai yace "Kunyi magana da Abba?"
Kallan mamaki tamai tace "Name?"
Bakinsa duk yaki rufuwa yace "ki shiga gida zai fada miki, sannan ni da sassafe zan wuce Karaye zanje gunsu Kawu mu fara shirye shirye."
Kallansa take sosai dan tabbas akwai abinda ke faruwa haka kawai Umar bazai ganta ta dawo yanzu ya kyaleta ba, gani tai ya sake matsowa kokarin rike hannunta yake da sauri ta sa hannunta a bayanta.
Murmushi yai tare da dan dukan daya hannunsa yana dan dariya yace " Ibty kiyi hakuri, na matsu na matsu na ganki a kusa dani ne, dan Allah kimin alkawari."
Bai jira amsarta ba yace "inhar kika tashi school gida kawai zaki dinga dawowa, sannan kimin alkawari namiji inhar ba Abba bane bazaki amsa ko gaisuwarsa ba, ko sallama ne ki amsa a ranki.�?
Wani murmushin takaici tai tace "Yaya wai dan Allah nikam ka taba kamani ina bin maza? Ko abin banza ne? Ni na kasa gane wannan rashin yarda da zargin daga inda ta fito, wannan wani irin kishi ne? Sallama wannan bazan amsa ba?�?
Fuska ya daure sosai yace "Alkawarin ne bazaki iya ba ko kuwa hakura da magana da mazan ne bazaki iya ba? Na tabbatar yanzu ma dakika je yawo kin kula wani namiji ko ba haka ba?"
Ya Allah! Ka ceceni daga wannan masifar. Abinda kawai ta fada a ranta kenan.
Umar ya kara matsowa, ganin a waje suke tana tsoron abinda zaije ya dawo yasa tai saurin bin gefe ta fara tafiya, suna shiga gate yasa hannu ya rikota iya karfinsa, yace "Alkawari nace kimin ko?"
Ajiyar zuciya tai tace "Inkaje ba goben zaka dawo ba? In ka dawo ka cigaba da kula da abinda nake aikatawa."
A fusace ya bude baki zaiyi magana sai kuma ya fasa saketa yai da sauri, yana kokarin yiwa kansa fada dan tunda an kusa aure gani yake yadan kara kai zuciyarsa nesa.
Ganin ya kasa magana kawai tai saurin wucewa ciki, harzai bita sai kuma ya shafi bayan kansa yana dariya, "To ai ka bari suje su tattauna da Abba ko?"
Wani tsalen dadi yai tabbas shikam yau burinsa ya cika lalai duk duniya bayaji akwai wanda yakaishi farinciki.
Bayan gidan inda dakinsa yake ya nufa ya fada kan gado ya jawo pillow ya rungume tare da rufe ido, can ya lula lambun soyayya wai gashinan shida Ibty anyi aure ta kwantar da kanta akan kirjinsa tanamai kukan shagwaba wai karya fita aiki batasan tai missing dinsa.
Shi kuma dadi ya kamashi ya turo kansa ya fara sumbatarta, tana dan dariya tana sake rungumeshi.
A zahiri kuwa Umar ya dage sai makawa pillow kiss yakeyi ba kakautawa duk ya gama sudar jikin pillow din. Idanunsa ya bude wanda sukai jaa da wata muguwar sha'awa, kallan pillow din yai kawai ya kwashe da dariya tare da sake rungume shi lalai za'asha soyayya bayan aure, sannan shifa karatun nan ajiyeshi zatai haka kawai ciwon zuciya da damuwa bazasu kashehi ba. Kallanta kawai yake bari dai ai auran shida kanshi zai yakici karatun nan.

********

Ibty tana shiga ta tadda falan su Abba duk suna zaune da alama abinci ya gamaci yasa a kirasu Iman.
Gaishesu tai sannan ta zauna tana sanarda Umma gaisuwar Ummy.
Abba ya kalleta cikin mamaki yace “Yau me ya samu Ibtisam harda zuwa gidan kawa?�?
Dariya tai tana sadda kai kasa, murmushi sukai yace “Dama magana nakeso muyi ko ince sanar daku nakeso nayi.�?
Kallan juna sukai ita da Iman sannan suka kalli Bilkisu wacce ta sadda kanta kasa da alama ita tasan me za’ace.
Abba yana murmushi yace “Yayarku za’ayiwa aure nan da sati biyu, karamin gidan can da ke jikin namu na samu na siya, zan fashe katangar dan ya zama kamar gida daya, ba lafiya ne da ita ba tana bukatar kulawarmu gaba daya.�?
Gaba daya mamaki ne ya kama Ibty da Iman a iya saninsu yayarsu batada saurayi meke faruwa?
Abba ne ya katse tunaninsu yana murmushi yace “Mijin na gida ne dan ‘yar gida zanyi da Umar…�?..�?
Jin kalmar tai a cikin kanta bata san sanda tace “Abba? Wani Umar din?�?
Umma tace “Umar dai mana na gidan nan.�?
Kai ta girgiza da sauri tace “Abba a’a dan Allah a’a, Ya Umar bazai yadda ya auri Yaya ba.�?
Dariya taga Abba yasa sosai mamaki ya kara kamata, jitai yace “To ai shi na fara fadawa kuma shi ya fara yadda.�?
Idanu ta zaro cikin matukar mamakin wannan lamari, Umar din ya yarda?
Kallan yayarsu tai tace “Abba ita Yayanfa?�?
Umma tadan bigeta kadan tace “Yau Ibty lafiyarki kalau kuwa? Keda bakya tambaya yau kece kike ta tambaya ba gaira ba dalili? Itama ta amince.�?
Itakam gaba daya ta kasa gane abinda ke faruwa, haka suka mike ta dawo daki ta zauna a bakin gado turus, ta kasa tunanin komai sai sake dawo mata kawai abinda ke faruwa yakeyi.
Wayarta ta dauko a jaka kamar zata kira Umar sai kuma tamai text tace “Ya Umar me kake shirin yi da amincewa dakai?�? Gogewa tai kawai ta mike ta fara safa da marwa a daki, daga baya ta fito tai alwala tai sallar magrib sannan ta sauka kasa ta nufi dakin Yayarta.
Tana zaune tana cin abinci dayan hannunta tana daddana waya, Ibty ta shiga ta zauna a bakin gado tace “Yaya da gaske kin amince? Kinsan halin Ya Umar kuwa?�?
Bilkisu ta harareta tace “Ibtisam meke damunki ne wai? Ya Umar fa a gidan nan ya taso, sannan ganin banida lafiya ne yasa nake kokarin boye abinda ke raina, amma maganar gaskiya na dade ina san Ya Umar, har addu’a nake Allah ya yayemin kaunarsa a raina.�?
Gaba daya Ibty jitai kamar an tsayar da komai na jikinta daga aiki, muryar Yaya taji tana cewa “Ina sanshi iya raina, ganin halin da lalurar da nake dashi yasa nake kokarin danne wa, shiyasa sanda Umma ta fadamin naji kuma ya amince na samu kaina cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa.�?
Kasa ko magana tai haka ta mike jiki ba laka ta nufi dakinta ta zauna a bakin gado ta baza tagumi.
Yau meke faruwa? Me take ji haka? Sam ta manta Umar yace mata gobe zaiyi tafiya da sassafe jira take safiya tai ta sameshi baki da baki taji me yake shirin yi?

************

Ummy kam ta gama yanke shawara dan Abba yana shigowa dakyar ta jira ya gama cin abinci, ta sanar dashi abinda ke faruwa. Mamaki ne ya kamashi jin yarinyar sa’ar Ainah ce. Yace �? Yanzu Asma’u bakya tunanin hakan bai dace ba? In Ainah ta kawo namiji mai yara biyu tace tanaso zaki amince?�?
Tace “Alhaji nima nayi wannan tunanin, sai dai zamanin da muke ciki ba wani abin bane, sannan hadin nan fa ba na dole zanyi ba, zamu fara tambayar iyayenta in har sun amince sannan zamu tura Aminu yaje gidansu, inaji a jikina alkairi ne a tattare da abin nan.�?
Murmushi sosai yai yace “Shikenan Allah ya wuce mana gaba, tunda dai Aminu ya amince da kowa kika zabamai ina ganin komai zaizo da sauki.�?
Ta kalleshi tace “Da zafizafi akan daki kirji, yaushe zaka samu ka gana da mahaifin yarinyar? Tunda karatu take kaga sai ta karasa a dakinta�?
Kallanta yai kafin yai dan dariya yace “Wai abin ba jira haka? Gaggawa fa aikin shedan ne.�?
Tace “Tsoro nake kar waccen matar ta kara shiga tsakanin lamarin auransa, sannan ina tsoron kar a kara canzamai ra’ayi.�?
Kai Baffa yadan girgiza yace “Asma’u adaina mumunan zato wancan Allah ne baiyi ba, in wannan rabanshi ne sai kiga komai ya tafi daidai. Yanzu ki bari gobe zansa ai bincike akan yarinyar zuwa jibi ko gata sai naje na samu mahaifinta da kaina yanda inhar bazaj yiwu ba kinga a ajiye maganar ma kafin ‘yan uwa suji.�?
Cikin gamsuwa tace “Shikenan Alhaji, Allah ya wuce mana gaba.�?
Da kanta Ummy cikin dabara ta amso kwatancen gidansu Ibtisam agun Ainah, sannan tace intaje makaranta ta amso mata number wayar Abba.
Mamaki ya kama Ainah tace “Ummy me zakiyi da number babanta?�?
‘Yar harara Ummy ta maka mata tace “So nake na hada Baffanki da Abbanta abokantaka dan yarinyar ta kwantamin.�?
Dariya Ainah tai tace “Ummy kema ki zama kawaye da Ummanta kinji?�?
Kai ta daga alamar to sannan tace “inkin amso number ma samu daga baya muje gidan, shikenan?�?
Dadi ya kara rufe Ainah tace “To Ummyna�?

*******

Ibty kam da wuri ta shirya ta fito waje tana jiran Umar, ganin har lokacin tafiyarta ya wuce bai fito ba yasa ta nufi bangarensa, tana zuwa taga an garkame kofar da kwado, goshinta tadan rike tana tuno ashe fa tafiya zaiyi yau.
Dole ko waya tamai taji me ke faruwa, dan itakam bazata taba bari a cuci yayarta ba. Tafi kowa sanin Umar tasan babu macen da zata iya hakuri dashi, balle Yaya da batada lafiya haka kawai bakin cikinsa yaja mata ciwon zuciya.



********

Acan gidan Aminu kuwa Hajiya duk ta matsu tanaso taji meke faruwa da maganar auran dayace zaiyi, gashi ta rasa ta inda zataji labari, dama dabara takeyi ya kira Ainah cikin bugar ciki taji komai to wannan karan itama Ainan tace mata batasan komai ba, da alama Ainah ta girma ba kamar da ba da take kanenayeta da dadin baki.
Haka kawai hankalinta ya kasa kwanciya, dole ko gun Ummy taje cikin dabara ai zataji in har da wani abin a kasa.



********
Nace yau naji mata😒? In akwai menene naki a ciki?🤔




Ayusher Ce🏌🏻‍♀�?
2/4/22, 11:08 - Ummi Tandama😇: 💫 IBTISAM...... 💫
(.........In Between)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀�?*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

*Free Page*


*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA 500 TA*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

+447894142004

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730


Page 6

  Lecturer dinsu yana fita ta kamo hannun Ainah suka fita waje, a bakin wani dandamali dake gefen hall din suka zauna, Ainah ta kalleta tare da daukan wayarta tace "Ibty bani number Abbanki plz, Ummy kesan hadasu zumunta da Baffa."
Cikin jin dadi tace "Allah sarki amma naji dadi, nan ta bata number Abba, ita kuma ta turawa Ummy." Kallan Ibty tai wacce tai shiru da alama tunanin abinda zatace mata takeyi, hannu tasa tadan bigi kafadarta tace "Tell me, meke faruwa?"
Juyowa tai ta kalleta sosai, tasa hannu ta kamo hannun Ainah tace "Ainah bansan meke faruwa ba, jiya da daddare bayan na dawo daga gidanku Abba ya sanar dani wai zaiyi hadin aure tsakanin Yaya da Ya Umar."
Cikin matukar mamaki Ainah tace "What?"
Ibty tadan girgiza kai kafin tace "Bansan meke faruwa ba, kwakwalwata ta kasa tunanin komai, kuma abin mamakin wai Ya Umar shi ya fara yarda da wannan hadin. Gashi itama Yayan sanshi take ashe bansani ba."
Ainah kanta tadan kama alamar damuwa tace "Yau naga ikon Allah! Kin tambayi Ya Umar din?" Tace "Yayi tafiya kauyensu, so nake yanzu ko in an tashi ma kirashi a waya naji meke faruwa."
Yanzun ma shiru Ainah tai da alama batasan me zatace ba itama, Ibty ta sake kallanta tace "Ainah kodai na samu Umma na sanar da ita halin Ya Umar? Tsoro nake kar a dalilina Yaya ta shiga cikin kangin rayuwa, gashi ita ba lafiya ba dame zataji?" Tai maganar cikin rauni da alama kuka ke neman kamata.
Ainah ta jinjina kai alamar gamsuwa tace "ina ganin ki sanar da itan gaskiya, duk da dai ina tunanin wani abu, kodai ya amince da Yaya ne saboda yaga batada lafiya? Ina take zuwa? Yanada wani hali ne bayan kishi da wannan zargin?"
Ibty tai shiru kafin ta girgiza kai alamar a'a tace, "A iya sanina wannan halin ne nashi mara kyau banda shi yanada kirki ga taimako."
Ainah tace "to ko shiyasa ya hakura dake? Yana ganin gwara Yaya wacce zata zauna a gida kullum? Hankalinsa a kwance?"
Alamar tunani ta tafi kafin tace "Ko?"
Kai ga jinjina tace "Nidai haka nake gani, inba haka ba meyasa yanda yake haukar sanki zai yadda ya auri Ya Billy?"
Wannan maganar ita ta gamsar da Ibty ta kuma sa aranta lalai haka ne dalili da alama ya hakura da ita ne shiyasa jiya bai rufeta da masifa ba dayaga taje gidansu Ainah. Amma alkawarin dayace ta dauka fa? Kodan dai ya saba ne? Haka taita sake sake a ranta har suka koma class.

********

Kiran Baffa ne yasa Ummy ta dan gyara zamanta tare da kara wayar a kunnenta tace "Alhaji har ka kirashi?"
"Asma'u kin tabbatar number nan itace ta Baban yarinyar?"
Cikin mamakin kalamansa tace "Eh Ainah tana turomin na tura maka ai."
"Number Audu mai kwari ne fa? Kina san cemin 'yarsa ce kenan?"
Mikewa tai zaune sosai tace "Audu dai Audu abokinka da kuka hadu a Saudia?"


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment