Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*



*GIDAN NAGOGGO* 🏨


This is my first novel.




*A true life story*

*Written by fateeyzah 🥰🥰*

Bismillahir rahmanir rahim.


Page0⃣1⃣




Tsawar da naji shi ya dakatar dani da bude dakin Ammy na.
"wallahi Bahijja in kika shiga dakin nan sai na bata miki rai,Uban mai kika zo yi mini a gida,ki tashi ki koma inda kika fito,tunda baki daukeni a bakina komai ba "cewar Alhaji kenan.
Take naji wata wata fargaba ta ziyarceni,wai yaushe zan fara samun kwanciyar hankali da maslaha tsakanina da Mahaifina,maganar Ammy tace ta tsinke min dan gajeran tunanin da na shiga wacce take tambaya abunda ke faruwa.
Alhaji ne ya fara magana cikin fushi "Amina ki juya ki koma ciki, in ba so kike fushin wannan mara kunyar ya shafeki ba,in kuma ba haka ba wallahi zanyi mummunar saba miki".
Da sauri na juya domin fita daga gidan don ganin Ammy na ta juya tana hawaye,ji nayi na tsani kaina,don tun ina Yarinya har girmana ta dalilina Ammyna ke zubar da hawaye.
Daga gefen gidan na tsaya ina kokarin tsaida hawayena da tunanin mafita.
Yanke hukunci nayi kawai akan na tunkari gidan Yaya Baffa wanda shine Babba a mazan gidan,don ina tunanin duk da 'Yan Uba nake dashi zai iya taimakona ya rokan mun Alhaji duk da wannan karan bansan laifin da nayiba.

Achaba na tare na hau tare da fada mai Anguwan dazai kaini,cikin 10minutes muka isa gidan saboda bamu da nisa,kasancewa Alhaji yana Banzazzau shikuma Yaya Baffa yana filin Mallawa,sallamar dan Achaba nayi na karasa nayI knocking din gidan,after some seconds Gateman yazo ya budemin tare da mun sannu da zuwa na kutsa kai harabar gidan.
Gida ne wanda ya amsa sunansa wanda kallo daya kayi ma gidan kasan mai gidan ya jiku da naira,hanyar da zata sa dani da main door din gidan na nufa,zuciyata na bugawa kamar zata tsago ta fito saboda shima bansan irin karban da zaya min ba.



More comment,more typing.

Yaya zata kaya tsakanin Bahijja da Yaya Baffa.





*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*



*GIDAN NAGOGGO* 🏨


*A true life story*

*Written by* *fateeyzah** 🥰🥰


Bismillahir rahmanir rahim .




Page0⃣2⃣


....Knocking din main door din nayi ,sai da nayi some seconds tukunna aka bude min kofar,Murmushi tamin tare da cewa "Bahijjah ce,sannu da zuwa,yaushe a Garin" dukka ta min wannan tambayar a lokaci daya.
Nima na maida mata da martanin murmushi tare da cewa"Nice Aunty Hanna,yau nazo".
"Karaso ciki mana"cewar Aunty Hanna.
Shiga cikin parlour nayi tare da kulle kofar,nan danan ta cika mini gaba da Snack da Drinks,tukunna ta zauna muka kuma gaisawa tare da tambayarta ina Yara.
Tace "Sun tafi school.
sannan tace "kici Snacks din mana"
Nace "Aunty Hanna bazan iya cin komai ba,don Allah Yaya nanan"?
Ta amsa min da"Yana nan bari inyi masa magana amma don Allah Bahijjah ki daure ki danci Snack din ko kadan ne".
Na amsa da "to Aunty"
Tashi tayi ta nufi ciki,ni kuma nasa Hannu na dauki Samosa daya na fara ci,ji nayi kamar ina cin magani.

Sun dau lokaci Basu fito ba,don har na fara gundura da zaman,sai gashi Sun fito dukkansu fuska ba yabo ba fallasa,nan da nan nasha jinin jikina,na zamo daga one sitter da nake zaune na gaisheshi,Ya amsa fuska a hade kamar hadari,sannan na koma na zauna,suma suka zauna a 2sitter dake facing din inda nake zaune.
Gyaran murya Yayi tare da tambaya ta"me ke tafe dake"?
Muryata a sanyaye nace "Yaya nazo ne don Allah ka taimake ka rokan min afuwa a gurin Alhaji Don naje ya koreni,kuma ni bansan mai nayi mai ba wannan lokacin "na kara she tare da kokarin maida kwallar dake barazanar saukomin.
Ya tambayeni "Bahijjah kikace baki son mai kikayi ma Alhaji ba"?
Na amsa da gyada kana sama.
Yace" alhaji Yace tunda kika koma Sokoto baki taba kiranshi kin gaishe shiba har maganar auren nan naki da ya taso,baki kira kin sanar dashi ba sai da Yaya Arsala ya kira shi ya fada mai,kuma Tace yana ji kuna waya da Ammy,amma shi kin maida shi Makiyinki,yanxu watan ki nawa da komawar ki Sokoto amma ko so daya baki taba kiranshi ba,yanxu tsakaninki da
Allah Bahijjah kin
kyauta?,yanda fa Ammy keda hakki a kanki haka Alhaji shima yana da hakki a kanki".

Kaina a duke nace"Yaya nasan nayi laifi amma wallahi Yaya ko na kirashi baya dauka,so uku ina kiranshi bai daukaba,shi yasa ni kuma ban kuma kiransa
ba,saboda na dauka bai bukatar gaisuwar tawa".

Kara gyaran murya yayi tare da cewa"look Bahijja ni kwata kwata ban ganin laifinku,na Ammy nake gani,amma zan sami Alhaji muyi magana,yanxu dai mai ya kawo ki garinnan,ina zaton yau saura 3weeks bikinki?"ya karashe da tambayata.
Nace"Kaduna zan wuce,in gyara kayan bed dina"
Yace"to da kike maganar gyaran kayan bed
kina da kudi ne?"
"eh,angon ya ban 10k saboda in gyaran kayan"
Anan Aunty Hanna ta saka baki tare da cewa«Honey,ni a ganina da Bahijja tabar maganar gyaran gadonnan kawai ka canza mata sababbin gado,tunda wancan auren nata shekara 10,kaga sun tsufa da yawa"
Yace"A,ah Sweety kibarta taje ta gyara kayanta,tunda tazo da niyyar gyarawa"sannan ya juyo gareni tare da cewa"Bahijja kije ki gyara kayanki,zan sami sauran 'yan uwa muyi maganar gudunmawar da za a hada miki ".ya karashe tare da mikewa yana kallon Aunty Hanna sannan yace Sweety ni na dita,in zata tafi ki duba drawerta ki bata 2k tayi transport"
Bai jira cewarmu ba yasa kai ya fita,sai da mukaji fitar motor dinshi sannan Aunty Hanna ta juyo tare da cewa"Bahijjah kiyi hakuri da rayuwa wata rana sai labari".



Fateeyzah



*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*


*GIDAN NAGOGGO* 🏨


*A true life story*

*Written by fateeyzah* 🥰🥰


Bismillahir rahmanir rahim


Page0⃣3⃣







Nace "to Aunty nagode,kuma muna nan muna kai kukanmu wurin Allah,Allah ya kawo mana dauki a wannan rayuwar ta gidanmu,wallahi Aunty Hanna ban damuwa da kaina akan yanda nake damuwa da mutum biyu wato Ammyna da Aunty Zubaida,kina gani yanxu Aunty Zubaida abin nata kamar hauka amma duk da haka Alhaji yaki dena fushi da ita,kuma yace idan Baban Fadila ya maida ita gidanshi,wai bashi ba Baban Fadila".
"aini Bahijja ban ganin laifin Alhaji sai na Ummeey da yaranta Mata,wallahi wadannan ba Allah a ransu,shi yasa nake fadin ma Honey ya bar yadda da kananan maganganunsu amma yaki,kiri_kiri sun tsare ko inna acikin gidan suna gidan aurensu amma kunnansu na gidan Alhaji,duk su suke hada fitina,shiyasa ranar da muka yi da Mamy na wanke ta tsab wai naje gidan Alhaji ta fara min hayagaga wai in fita daga gidan tunda ba gidan Ubana bane,ni kuwa nace mata ai tasan nawa gidan Uban yafi nasu,don baza ma a hada gidanmu da nasu ba,wai fa duk abinda ya kawo fitinar sunce wai Alhaji ya karbi dukiyarshi a wurin Honey saboda wai da kudin yake Almubazaranci wai yana kashemun".
Nace"ai mu Aunty 'Yan dakinmu duk abinda yake faruwa a gidannan bama sani,kina ganin Asma'u da take kusa da gidan ma Alhaji ya hana ta zuwa wai sai bayan 3month saboda wai 'yan dakinmu muke hada fitina a gidan,tsakani da Allah ga Mamy nan da kullin tana gidan da ita da Mijinta da 'Yarta amma su ba a hanasu zuwaba sai mu".
Aunty tayi gyaran murya tare da fadin"kedai Bahijja mubar maganar nan Allah ya shiryesu,don ni ina fada ma Honey abun kunya ne a wurinsu ace kamar gidan Alhaji Nagoggo,ana Samun wannan matsalar.yanxu wai a ina za ayi bikin tunda Alhaji yace badai gidanshi ba kuma kinga Dokoto tayi nisa".
Nace"Mun yanke shawara zamuyi biki ne a Kano gidan Aunty Aisha tunda kin ga nan zan zauna".
"Ok,yanxu abunda za ayi in kinje Kaduna kin dawo ki biyo tanan ki karbi bedsheets a matsayin gudunmawa ta don
nasan ba bari za a yi inje bikin ba".
"shi kenan Aunty na gode,Allah ya kara budi".
Tace "amin,ina zuwa".
Tashi tayi ta Shiga daki,sai da tayi like 3minute tukunna ta fito ta mika min kudi tare da cewa "Ga 12k nan,2k kudin da Honey yace in baki na transport,10k kuma ki kara a kudin gyaran bed".
Take naji kuka ya tawo min na mike tsaye tare da rungumeta ina kuka tare da mata godiya.
Itama kukan ne yazo mata tare da cewa"Allah ya tona asirin wanda ya raba Bahijja da Alhaji,yanxu Bahijja akan 12k kike kuka,sai kace wadda aka bata millions".
Nace"Aunty ba komai ya sani kuka ba,sai alamarin Ubangiji dana tuna,wai yau nice na ke murna akan 12k,abunda lokacin da nake auren Tasi'u nafi karfinsa,sai dai ni in
bada,lallai na yadda duniya juyi juyi wanda ya dauketa da fadi yana tattare da wahala,Allah dai yasa mu dace".
Tace Amin Bahijjah.
Mikewa nayi tare da saba jakata Nace Aunty ni xan wuce dai na dawo a gaishemin dasu Baby,ta amsa da za su ji,Rakiya ta yimini har main door tukunna muka kuma sallama ta juya,ni kuma na fice gidan,Achaba na hau wanda zaikaini Agoro Motor Park don in shiga Motar Kaduna.





Wacece bahijja?

Pls manage

🖊fateeyzah


*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*



*GIDAN NAGOGGO* 🏨




*A true life story*

*Written by*
*fateeyzah* 🥰🥰


Bismillahir rahmanir rahim


Page0⃣4⃣



Tafiyar one hour ta kaini garin Kaduna,inda Driver ya saukemu a Kawo,nan na samu Napep din da zata kaini gidan Kakata dake Unguwar dan Bushira,tafiyar 30minutes mukayi,inda Mai Bapep ya saukeni a kofar Gidan,na biyashi kudinshi na karasa cikin gida.
Babban gida ne,wanda kallo daya zakamai kasan masu gidan suna fama da rashi,gidan cike yake da 'Yan uwan Ammyna daga Yayyinta zuwa Kannita kuma kowanne da Iyalanshi,akalla Mutanen gidan zasu kai dari(100),bayan gaishe gaishe tare da taya ni muryar auren da zanyi,direct dakin Kakata na wuce wacce muke kiranta da Granny,shiga nayi ina mata wasa irin ta Kaka da Jika,bayan mun gaisa,nayi wanka hade da salla sannan na zauna cin Abincin da aka kawo min daga dakin Matar Kawu Muhammadu.

Hira muka dasa ni da Granny wadda yawancinta hiran gidanmu ne da halin da Ammyna take ciki,anan na bata labarin abinda ya faru dana je gida da gidan Yaya Baffa da naje.
Aikuwa nan ta bude baki tayi ta surfa balla'i,saboda Granny irin mutanen nan ne da basu daukar wargi,sai da ya koma ni nake bata hakuri sannan tayi shiru saboda zaka dauka dani take fadan.
Can kuma kamar an tsikare ta tace"ni wallahi badon Amina ta wuce zaman gida ba da sai na raba Aurensu da NAGOGGO,tunda kwata kwata naga alamar wannan Matar tashi mai hanci kamar bututu👃(lol😃irin hancin Sophie ta)ta gama Mallake shi,in banda kaddarar Allah da rabon Haihuwarki data Kanninki da munsani sanda ya taba sakinta bamu bari ta koma ba (kaji Granny da tonon asiri,irin haka har yanda aka nemi auren Mahaifiyarka sai an fadin maka)amma kana naka ne Allah na nashi gashinan har tsufa abu yaki daidaita".
Nace"don Allah Granny kibar maimaita maganar nan,wallahi in hadda ce ya isa na haddace wannan karatun dakike fadamun tun zaman da nayi a gidan nan".na karashe maganar tare da tashi na shige bedroom dinta,inajinta Taci gaba da sababi.
Gado mai runfa na samu na haye tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya,'Ya'yana ne suka fado min arai ko yanxu ya suke,oho,don nadau Alkawarin bazan kuma zuwa ganinsu ba tunda last zuwan danayi sai da Tasi'u ya bini da sharri(anya ko Bahijja zaki iya yanke alakarki da ta Yaranki).
Nan danan naji kwakwalwata ta fara tariyo min abubuwan da suka wuce har .....


Manage


Insha Allah next page zamu ji wacece Bahijja?



*Fateeyzah🖊*



*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*


*GIDAN NAGOGGO* 🏨


*A true life story* .

*Written by fateeyzah* 😍😍


Bismillahir rahmanir rahim.

Page0⃣5⃣



*FLASH BACK*

Mahaifina da ne ga Alhaji Akilu kudan,wato sarkin kudan na wancen lokacin,mahaifiyarsa Hajiya Atika wacce suke kira da Goggo ita ce mata ta farko a wurin mai martaba sarkin kudan.
Hajiya Atika 'ya'yanta biyu a gidan wato mahaifyana Alh Ahmad NAGOGGO da yayarsa Hajiya Hajara wadda nake wurinta a sokoto, a lokacin Mahaifina na da shekara daya Allah ya kaddara rabuwarsu wanda har yau da basu a duniya babu wanda yasan dalilin rabuwar aurensu,sannan Alhaji Akilu ya auri matansa biyu wato Dayyiba(Umma,wacce ita kadai ce take da dai a yanxu), da Amaryarsa Zulai(Mama) wanda suka haifammai 'ya'ya kusan sha shidda, ba lallai bane in iya lissafo su tunda ba wani zumunci mukeyi dasu ba duk da sun kasance 'yan uba suke da Babana,duba da irin yadda zumunci ya kasance a yanxu.
Bayan rabuwar kakata Hajiya Atika da Kakana,sai ta dauki Babana wanda suke cema NAGOGGO (sunan NAGOGGO ya samo asaline da yanda a unguwarsu masu suna Ahmad suna da yawa, shine ake kiransa da Ahmad din Goggo wanda daga baya suka maida sunan Nagoggo,Wanda har sunansa Ahmad ya bace Mutane suka koma kiransa Nagoggo),ta daukeshi ta dawo garin zaria dashi wurin iyayenta tabar Hajiya Hajara a kudan.

Tabama ma Babana tarbiya dai dai gwargwado saboda Hajiya Atika irin mutanan nanne masu fadin gaskiya,wanda komin girmanka sai ta fadin maka,Mace ce mai tsauri wanda ko cikin Dangi kowa yana shakkarta,Babana nada shekara biyar a duniya tayi aure anan zaria ta tafi da Babana gidan Mijinta, kasancewa shi baya haihuwa sai ya zamana ya rike Babana kamar danshi.anan zaria yayi primary school daga nan bai ci gaba ba,duba da yadda mutanen da suka dauki karatun boko,daganan ya fara bin kanin Mai Martaba legos,wanda wannan ne musabbabin arzikinsa.

Matar Mahaifina ta farko ita ce Hajiya Maryam,wadda ya auro daga k
Kano,daka ganta kaga bafulatana, fara ce tas,ita keda manyan yara a gidan,yaranta sha daya,mata hudu maza shidda,Amina,Hauwa,Akilu(Baffa),Faruq,Atika (Mamy),Ibrahim,Aminu,Jafar,Auwal,Salma,Ahmad(Abba).Hajiya Maryam Mace ce mai son kanta,kwata kwata batason wani ya rabesu,bayan ita Alhaji ya auri kusan Mata biyar amma basu dadewa suke fita saboda ta kasan kasa take azabtar dasu,wadanda suka dade a gidan sune wadanda suka haifi 'ya'ya
biyu2,Amina wacce ta haifi yara biyu, Fatima da Zubaida,sai Huwaila da ta haifi Halima da Bello.


Mahaifiyata itace Matar Babana ta shida a jerin Matan da ya aura,ita a Bazawara ya Aureta,tanada yara biyu a gidan da ta bari,Zainab da Mustapha, Haifaffiyar garin zaria ce,don daga baya su Granny suka koma cikin garin kaduna.
Mu biyar ne yaranta a wurin Babana,Asma'u itace Babba,wanda bayan haihuwar Asma'u sai da suka rabu da Babana,ta koma gidan b'Babansu Aunty Zainab,chan ma auren yaki tunkunna ta dawo gidan Babana,bayan dawowarta ne ta haifeni(ni Bahijja,Aliyu,Abdullahi,Taheer.
Mahaifiya Allah yayota mai hakuri don yanda ake takurata a gidan Babana abun ba a magana,duk wani cigabanta Alhaji ya dakusheshi,tun muna kanana bama fahimta har muka girma muka fahimci Mahaifiyar mu itace bora agidan mukuma 'Ya'yan bora.





Pls ur comment is needed.



Fateeyzah



🖊*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*



*GIDAN NAGOGGO* 🏨


*A true life story*

*Written by fateeyzah*😍😍



Wannan page din nakine *MUM IRFAAN*Allah ya baki abunda kike nema DUNIYA da LAHIRA,Amin.



Bismillahir rahmanir rahim
Page0⃣6⃣


Duk wani hakki namu an take shi a gidannan,don ko Almajirin gidan an fi daukarshi da daraja fiye damu,a hakan ma ana raga mana ne saboda hajiya kaka(Hajiya Atika ),saboda tana kokarin nuna ma Alhaji abunda yake yi bai daceba,kasancewa bayan rasuwar mijinta Alhaji ya gina mata gida nan kusa da gidanmu ta dawo,ya saka mata 'yan haya duk da akwai jikoki('ya'yan 'yarta hajiyan sokoto).
Su kuwa sauran yaran da iyayensu basu gidan,suma Alhaji ya rarrabasu,Aunty fatima da Bello ya bama Hajiya kaka,Aunty khadija kuma ya bama Hajiyan sokoto sai Halima da take wurin mamarta.
Bayan ammy ta haifi aliyu ne ta samu teaching a wata private school,amma daga baya sai da Alhaji yasan hanyar da yabi ya hana ta teaching din,abunda ya faru shine, ummy ta kawo kararta wurin Alhaji akan wai tana barin mata yara da yunwa,hakan ya kawo musu rashin jituwa,har sai da hajiya kaka ta sasantasu tace kowa ta ringa girkinta daban,daga baya kuma yace wai sai dai ta zaba ko teaching ko aurenta,saboda kullin tana fita ana kalle mai mata,haka ammy ta hakura tabar teaching ya koma sai dai abinda ya kawo ya bata,don ko sana'a a cikin gida ya hanata.
A wannan lokacin kuma an aurar da mata uku a gidan mu duk daga dakin ummy,wato Amina(ta auri babban dan Hajiyan sokoto), Hauwah da mamy, dukkansu duk sun hayayyafa.
A lokacin da nake da shekara sha biyu yayi dai dai da ina j.s.s one a kayi bikin yaya Baffa da Aunty hanna wacce ta kasance diyar aminin Alhaji,a lokacin ne kuma komai na gidan mu ya kara tabarbarewa dalilin Alhaji ya dauki dukiyarsa gaba daya ya damka ma yaya Baffa don yaci gaba da juyawa,a dai dai lokacin kuma Tasi'u ya shigo rayuwar gidanmu,wanda dalilinsa na tsinci kaina a wanna rayuwar da nake ciki.






*Comment*
*Share*
*Vote*


*Fateeyzah*




*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*



*GIDAN NAGOGGO*🏨


*A true life story*

*Written by fateeyzah*😍😍

Bismillahir rahmanir rahim



Page0⃣7⃣&0⃣8⃣


A wannan shekaran na taso da wani irin hatsabibanci,duk nabi na addabi kowa a gidan, don duk wanda yayi ma Ammyna rashin mutunci ni ma sai na yi masa, don har Alhaji ban raga mawa, hakan ya jawo mun tsana a wurin 'yan gidan especially Yayyina maza da yayyina mata da sukayi aure,Don duk wacce tazo tayi ma Ammyna rashin kunya, nima kafin ta tafi sai na yi mata wanda yafi nata,hakan ba karamin duka yake jawo mun ba musamman wurin Alhaji da Yaya Farooq wanda shine ya kasance babba a gidan bayan auren Yaya Baffa.Duk sanda ko ake dukana Ammyna da Asma'u zasu shiga daki suyi ta kuka, saboda yanda suke zage karfi su dakeni zaka dauka wani Gardi suke duka,haka zasu min likis, amma haka bashi zai hana in ka ma Ammyna ko Asma'u da kannina wani abun ni ma in karta maka nawa Rashin Mutunci.

Aikuwa wata rana fada ya hada Ammyna da Ummy, sai Yaya Farooq ya shiga ma Ummy yayi ta zagin Ammyna,a lokacin da abun ya faru ina school,ina dawowa na kira Almajirinmu na tambaye shi mai ya faru da bana nan,don naga idon Ammy yayi jawur alamun taci kuka,aiko ya kwashe ya fadamun(dama indai na dawo naga Ammyna a wani yanayi, Almajirinmu nake tambaya don nasan ita ko Asma'u baza su sanar dani ba, saboda sanin bana yafiya).

A Hankali na shiga part din Mazan gidan,nan na hango Yaya Farooq yana wanki,ga Radion shi a gefe yana shan disco,wata bishiya na samu na make ina kallonsa,lura da nayi Manyan kaya yake Wankewa ya tunasar dani washegari zasu je Nadin Sarauta Kudan(kakana yayi murabus ya bama Kanninsa saboda rashin lafiyar da yake fama da shi da kuma maida Aurensa da Za ayi da Hajiya Kaka),Aiko nan farin ciki ya rufeni don na samu hanyar da zan Rama ma Ammyna zagin da yayi mata,Shigowar Yaya Ibrahim ne ta katse mun tunani,inaji ya na cema Yaya Farooq wai sabon kaya ne yake wankewa,shi kuma ya bashi amsa da Kyamar kayan yake yi Saboda ya dade a wurin Tailor,dariya Kawai Yaya Ibrahim yayi ya ajiye Bucket ya fita,Ina nan make har Yaya Farooq ya gama wankinshi ya shanya ya fita, sai dana kara kamar 5minutes sannan na fito daga maboyata,kitchen na nufa direct naje na dauko Almakashi,Wurin kayansa na nufa na ciro su a Igiya na samu kayan nan na yankasu kuci2 da Almakashi na zubar mai a wurin na kama gabana,dakinmu na nufa nayi kwanciyata a Gadon Ammy nayi baccina.
Cikin bacci naji an kwada min mari wanda zafinshi ya sani sakin fitsarin da ban shiryaba,haka ya jani ya fita dani harabar gidan ya jefar dani gaban kayan dana yanka,daka mun tsawa yayi tare da tambayata wa ya yanka kayannan ya karashe tambayar yana nuna min kayan dake gabana,bakina na rawa na amsa mai da ni ce,saboda wani tsoronshi da ya dirar mu a zuciya ban shiryaba,zare belt yayi ya shiga jibgata,ni Kuma ina ihu,ihuna ne yayi raising din Alarm din da kowa sai da fito har da Ammyna dake Kitchen,duk taron yawan gidanmu an rasa mai kwata ta a wurin Yaya Farooq,haka ya ringa jibgata sai da yaga na dena motsi tukunna ya yarda belt din,da gudu Ammy da Asma'u sukayo kaina suna girgizani,amma ina ba labari,Ammy ce ta kwala ihu tare da Fadin "shikenan Farooq ka kashe min ita,wallahi bazan yarda ba,ke Asma'u miko min Hijab dina in kaita wurin Hajiya".da gudu Asma'u ta shiga daki ta dauko mata Hijabi ta saka,haka ta ciccibeni ta goya ni a bayanta tayi hanyar gate din gidan,tana fita suka ci karo da Alhaji ya dawo daga masallaci,ko kallonsa batayi ba ta rabashi ta wuce,shi kuma ganina goye a bayanta ga Asma'u na binmu yasa shi rufa mana baya.

A kusan tare muka shiga gidan Hajiya tawa,kukan da ammy take yine yasa Hajiya fitowa da sauri zani a hannu tana tambayar lafiya,shimfideni tayi tare da fadin "shike nan Farooq ya kashemun ita",salati Hajiya ta dauka tare da fadin"garin yaya?", babu wanda ya bata amsa tsakanin Alhaji,ammy da Asma'u,ganin baza ta samu amsa bane yasa ta maida hankalinta kaina,ganin alamun suma nayi yasa ta shiga daki da hanzari ta debo ruwa a fridge ta zo ta watsamin,sauke ajiyar zuciya nayi hade da fashewa da kuka,rungume ni Ammy tayi a jikinta itama tana kuka,ba wanda yace hanamu,sai da muka yi shiru don kanmu,sannan Hajiya ta nemi sanin dalili,nan Asma'u ta fada mata abunda ta sani,juyo wa tayi ta tambayen mai nayi masa nan na kwashe na fada mata,aiko nan ta hau sirfamin zagi sai da tayi mai isarta sannan ta koma kan Alhaji,shima ta zageshi tas,sannan tace mu tashi muje Gida gatanan zuwa itama,da taimakon Ammy na mike don duk jikina a fashe yake,don na daku.

Isarmu gida mu ka tarar da duk ' yan gidan a harabar gida,kallonsu kawai zakayi kasan suna cikin tashin hankali,ganin shigowarmu yasa duk sukayo kanmu har da uban gayyar(Yaya Farooq),duk jikinsu a sanyaye,suna mana magana amma ba wanda muka tanka,ana cikin

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment