Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hado kayana, ina cikin hadawa Aunty Asma'u ta shigo tace inje Yaya Baffa na kirana, cikin sanyin jiki na bita zuwa parlour, ina zuwa na samu wuri na zauna sannan Yaya Baffa ya fara magana cikin bacin rai "Bahijjah ganin mu da kikayi munzo, Alhaji ne yayi umurni akan muzo mu tafi dake Saboda Asma'u tazo mana da maganar Tasi'u ya sake ki,Hakika dukkanmu ranmu ya baci akan abunda ya faru,duk da a baya mu muka nemi daya sake ki,amma ya nuna mana yana son matarsa,ko yanxu abinda ya bata mana ran baiwuce yadda Ammy ta fada mana irin wulakancin da ya miki hade da hanaki abinci da yayi,Amma kuma yanxu Alhaji ya kuma kiranmu akan mubarki anan ki haihu, inyaso inkin yi arba'in sai ki ijiyemai 'yarshi ko 'yanshi ki koma gida".

Nan naji gabana ya fadi in ijiye dana kuma, ai abunda bazai taba yiwuwa ba kenan in bar dana ko'yata mai kwana arba'in a duniya, ina kokarin magana ne Aunty Asma'u ta girgiza min kai, ma'ana kar ince koma.Anna Yaya baffa ya tambayeni in bashi Account number na, ina bashi yayi mini tranfern dubu dari yace inje in sayi abinda nake bukata in kuma akwai wata matsalar in kirashi a waya, ina ji ina gani suka tafi suka ganni.

Haka naci gaba da rainon cikina cikin kulawar 'yan uwana da Humaira, tsakanina da Tasi'u kuwa sai dai ido ban shiga harkarshi nima bai shiga tawa, su Ihsan kuma bai dawo dasu ba.

Bayan wata uku na haifo dana da taimakon unguwar zoman da Humaira ta kira mun a bayan layinmu, duk wanda yaga yaron sai ya yabashi,a ranar ne kuma Allah ya dauki ran Alhajin Tasi'u.

Haka 'yan uwa sukayi ta kirana suna min barka hade da gaisuwa, sati na zagayowa aka rada ma yaro suna ibrahim khaleel,ba wani taro akayiba ,amma duk 'yan gidanmu da surukan gidan sunzo illa 'yan dakin Ummy, ba laifi an tara mana kaya ni da khaleel, Tasi'u ko khaleel kadai yai ma kaya niko ko kyale bai min ba.

Nayi arba'in da kwana daya sai ga Yaya Baffa yazo wai Alhaji yace in ajiye ma Tasi'u danshi in bishi mu tafi gida.

Please manage.





Shin Bahijjah zata ijiye danta ta tafi ko zata zabi danta akan Alhaji?

Sai mun hadu a next page.








*_Fateeyzah_*✍





*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
_*(home of peace,joint of entertainment,to educate and enlighten our readers)*_



*GIDAN NAGOGGO*🏨
*_( A true life story)_*



_*Written by fateeyzah*_😍😍


*Godiya gare ku real Fateeyzah novel group,ina jin dadin comment dinku ako da yaushe especially maman Abdulaziz,Aisha jibril(Aj),yar Asalee da sauran members ina yinku.*




*Da masu kirana,da masu text ina yinku,naga tsakonninku na gode da nunamin kulawa da kukayi.*


*Hafsat .s.bello(maman fadila) thanks for the visit,gskiya na ga alama ke babbar fan ce ta GIDAN NAGOGGO, ina godiya*


*Aisha jibril(Aj)thanks for the call,Allah kara zumunci.*

*Sis Zuby Allah ya kara sauki,yasa kaffarane*


*_Bismillahir rahmanir rahim_*



*_Page3⃣1⃣to3⃣5⃣_*

Take naji hankalina na tashi,don kwata² na manta da maganar Alhaji na in na haihu zan barmai yaron, tsawar da Yaya baffa ya daka munne ya dawo dani daga gajeran tunanin dana tafi tare da fadin "don Allah Yaya Baffa kayi hakuri, bazan iya barin khaleel ba in tafi,don Allah ka taimakeni ka rokon min Alhaji ya barni da dana"na karashe maganar ina zubar da wasu zaffaffun hawaye.

Wata harara ya banka min tare da fadin "wai ke Bahijjah wata irin kafaffiyar yarinya ce,duk wulakancin da Tasi'u ya miki ba ki gani ba,amma har yanxu kina nan nanike da dansa,mufa gata muke so mu miki amma kinki ganewa, kinsan ko daya sake ki sai da muka sha artabu da Alhaji kafin ya bari muka zo wurinki,amma kike nema ki watsa mana kasa a ido".

Dago kaina nayi a karan farko na kalleshi tare da fadin"wani irin gata ne wannan nasan rabani da d'ana mai kwana arba'in da biyu a duniya, wanda ta dalilinsa na samu kaina a cikin halin dana ke ciki,ta dalilinsa na rasa ubansa da yayyinsa, a yanxu in ka cire Ammy ba wanda nakema son da nake ma khaleel a duniya, don haka in baza ka iya yimin taimakon dazan kasance da d'anaba ka tafi ka barni kawai"na karashe magana cikin daga murya.

Yanayin yanda nayi magana da hargagi da kuka yasa jikinsa yayi sanyi tare da fadin "Bahijjah kinsan halin Alhaji, inya zartar da hukunci ba wanda ya isa ya saba, Bahijjah duk irin rashin jituwar dake tsakanin 'yan dakinmu da naku baki ji bakin cikin damuka tsinci kanmu ba da mukaji sakin da Tasi'u ya miki, wannan ne dalilin dayasa mukayi confronting din Alhaji lokacin da abun ya faru, dakar muka shawo kanshi akan muje mu dauko ki amma da sharadi inkin haihu da zaran kinyi arba'in zaki maida mishi danshi, wanda daga baya kuma ya canza shawara akan abarki anan, in kinyi arba'in din kya ijiye yaron ki dawo gida, a yanxu basan yanda zan tunkari Alhaji akan ya barki ki koma gida da..... "Ringing din wayar shine ta katse mai magana, cikin sauri yayi receiving din wayar tare da sata a speaker, muryar Alhaji ne ta doki kunnena wanda dalilin haka yasa 'yan hanjin cikina kadawa, Yaya Baffa ne yayi mai sallama tare da fadin" an wuni lafiya Alhaji"

Daga can bangaren Alhaji ya amsa tare da fadin " lafiya lau Baffa, kun tawo ne Saboda kunake jira, don inason zuwa ta'aziya".

Saida Yaya Baffa ya kalleni, tunkunne ya kwashe duk yadda mukayi ya sanar da Alhaji, nan fa Alhaji ya fara bambami, nan dai ya ringa bala'i, sannan daga karshe yace ma Yaya Baffa ya taho ya kyaleni sannan ya shaidamin kar in sake in tako gidanshi batare dana maida dannan ba.

Inaji ina gani Yaya Baffa ya tafi tare da cemun in mai kwatancen Gidan granny zaije ya sanar da ita in yaso sai in koma wurinta da zama kafin su samo mafita.

Bayan fitarshi da awa biyu sai ga kiran Ammy inda take fadin mu Yaya Baffa ya kirata ya fada mata komai,sun yanke hukunci zan koma Gidan Granny da zama, don haka gobe Aunty Asma'u zatazo ta rakani Gidan, nan dai tayi mini nasiha tare da fadin wannan karan zata kai karar Alhaji wurin Hajiyar Sokoto don ta gaji da irin abinda ya kemun.

Bayan na gama waya d Ammy ne kuma sai ga kiran Yaya Baffa inda yace min in turo account number na, take ko na tura wanda anan yamin transfer dubu dari, kiranshi nayi don in mai godiya anan yake cemin ya turamin ne don in samu sana'ar yi, nan dai shima yamin nasiha sannan muka yi sallama.

Nan na zauna inata mamakin Yaya Baffa,don dai nasan da ba haka yakeba, don shima nuna mana tsana yake kiri kiri, ina cikin wannan tunanin sai ga Humaira ta shigo nan dai na fada mata yanda mukayi da su Yaya t Baffa,nan da muka fara kukan rabuwar.

Wurin karfe takwas na dare,sai ga Tasi'u ya shigo ya hada kayanshi dana yara da duk abinda yasan mallakinsane yayi ta futa dasu,sai daya gama sannan ya miko min key tare da fadin in na kwashe kayana na kulle ma masu gida dakinsu,bai jira cewata ba yasa kai ya fita ya barni da tunani.

Ina zaune a inda yabar ni,ina ta juya maganarsa acikin kwakwalwata, don na kasa fahimtar inda ya dosa, sai ga Humaira ta shigo cikin sauri tana kwala min kira, ganina zaune a parlour yasata karasowa wurina cikin hanzari tare da cewa" Maman Iman kinji abunda na jiyo kuwa(na girgiza mata kai)wai sauran sati uku bikin Daddynsu Iman".

Bakina na rawa nace mata"da gaske Humaira ko dai jita² kikaji kan cewa zai yi aure"

"Wallahi da gaskene don mai gidana ya fada mawa, na ma manta, yaufa ya tare a sabon gidanshi tare dasu Iman da ummanshi", take naji cikina ya fara juyawa,nan danan naji wani zazzabi yana son rufeni,ban san har yanxu akwai son Tasi'u a raina ba sai da naji maganar aurensa, sannan gidan dana zabi plan da kaina shine wata zata shiga bani ba,nan dai naji wani irin kishi ya rufeni, ganin halin da nake ciki yasa Humaira tafara lallashina tare da min nasihohi,sannan ta tashi ta fita.

Daukar waya nayi nakira Ammy tana dauka na sa mata kuka tare da fada mata abinda naji daga bakin humaira.

Gyaran murya tayi tare da cemin"Bahijjah mun riga mun sami wannan labarin, Alhaji ne yace kar a fadamiki, don tunda Tasi'u ya sakeki da sati biyu aka samasa rana da wata yarinya anan kaduna,don ko su Iman ba kudan ya kaisu ba suna nan gidansu amaryarsa"

Cikin rawar murya nace" Ammy duk kunsani kuka kasa sanar dani?, a ganina Ammy koda Alhaji yace kar a fadamin ai ke bai dace ki'ki sanar daniba"

Cikin sanyin jiki Ammy tace"Bahijjah kiyi hakuri don sanar da ke baida amfani, mutuwar auranki bakaramin rikici yaja a dangiba wanda yaja rarrabuwar kawunansu, a ranar da kika sanar dani Tasi'u ya sakeki, saina kasa sanar da Alhaji don nasan duk abunda zai biyo baya ba mai dadiba ne, sai na yanke shawarar kiran Baffa na fadamai wanda cikin tashin hankali ya hado kannisa suka samu Alhaji suka fada mai, cikin bacin rai yace shi ba ruwansa, dakyar suka shawo kan Alhaji inda ya yadda su Baffa su daukoki, bayan tawowarsu wurinki ne sai Alhaji ya dauki waya ya kira Babban Tasi'u ya sanar dashi abunda ya faru, amma budar bakin shi sai yace ya sani, don shi farin ciki ma yake Tasi'u ya rabu dake saboda wai Tasi'u yace rikemai riga kikayi kikace in ya cika cikin uwarshi da ubanshi ya sakeki, shine shi kuma ya sakeki, haka dai yaci mutuncin Alhaji a waya, wannan dalilin ne Alhaji yace a bari ki haihu anan,don bazaki kawo mai jinin Tasi'u gida ba, wallahi bahijja ko da mahaifin Tasi'u ya rasu muka je gaisuwa bakiga irin wulakancin da 'yan gidan suka mana ciki kuwa har da ummanshi, wannan dalilin ne yasa Alhaji cewa ki ijiye khaleel ki dawo gida, don dacan ya sake shawara akan in kinyi arba'in ki dawo gida da khaleel inyaso inkin yayeshi kya maida shi".

Cikin kuwa nace"Ammy tabbasa biri yayi kama da mutum don tunda Tasi'u ya sakeni wani dag gidansu bai taba kirana ba, don ko lokacin da Alhajinsu ya rasu da na kirasu nayi musu gaisuwa yanda suka amsa mini kamar akwai wani abu, ni kuma sai na dauka mutuwarce ta taba su,Ammy ayau na tabbatar da Alhaji abunda yayi shine daidai, don haka zan ijiyemai danshi in dawo gida tunda dai abun rashin mutunci ne".



Ya kuke gani,shin Ammy zata yadda Bahijjah ta ajiye danta mai kwana arba'in da biyu a duniya ta koma gidan Alhaji?




_Sorry fans insha Allah daga next page zamu dawo cikin labari don jin yadda auren Bahijjah na biyu zai kasance._




*Comment*
*Like*
*Vote*
*Share*


*Fateeyzah*✍





*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_(home of peace, joint of entertainment and to educate and enlighten our readers)_*




*GIDAN NAGOGGO*🏨
*_(A true life story)_*


*_Written by fateeyzah_*

*Ta'aziya*
*Inalillahi wa inna illayyir raji'un.*

_Ina mika ta'aziyata zuwa ga ummu salma daya daga cikin member na_ *HIKIMA* *WRITERS* *ASSOCIATION* , _na_ _rashin danta(naeem),wanda ya rasu ranar kamar haka 11/04/2020,muna rokon Allah ya jikanshi,ya gafarta masa yasa masu ceton mune,ameen._




*_Bismillahir rahmanir rahim_*




*_Page3⃣6⃣to4⃣0⃣_*


"Kul Bahijjah, ki dena fadin zaki ijiye mai dansa, kina ganin abinda ya faru da zubaida sakamakon rabata da danta da Alhaji yayi dan wata biyu,ranar kakarta t kawota gurin Alhaji take fadamai, yanxu haka Asibitin mahaukata ake karbat mata magani, don doctors sunce tunanin 'yayanta yasa kwakwalwarta ta tabu, don haka ki barshi da Allah duk abunda yayi, yai ma kansa, sannan na san ki da kulafacin 'ya'ya don Allah kicire 'ya'yan nan aranki, sannan karkiga garinku daya kiyi ta daukar kafa kina zuwa gidan, don bansan abunda za ayi ta kananan magannanu akai, sannan kinsan irin gidan dazaki koma zama, don haka ki kama bakinki, ba ruwanki da gulma da tsegumi irin na family house"haka dai Ammy tayi tamin nasiha sannan mukayi sallama.

Washegarin ranar, wurin karfe goma na safe sai ga Aunty Asma'u tazo, nan muka samo Almajirai suka tayamu kwashe kaya sannan muka rankaya har da Humaira sai dan bushiya Gidan Granny.

Daki guda aka waremun a shiyar Granny,inda anan akasa mun kayana,suka gyara min daki kamat wata amarya,sannan bayan la'asar suka tafi suka barni,wanda munci kuka da kyar Granny ta rabamu(lol 🤪su Bahijjah masu idon kuka)
.
Kudin da Yaya Baffa ya bani,shine na dauka na siya keken dinki hade da materials,na fara dinka gowns mai kamar jallabiya inasa stones,sannan ina dinka kimono,kasancewa dan bushiya akwai gidan masu kudi, Sai ya zamana ina ciniki sosai don da kaina nake shiga gida² ina masu talla.

A bangaren zamana a gidan,banda wata matsala da kowa,ban shiga shirgin kowa ,in mun hadu a tsakar gida kuwa gaisuwa ke shiga tsakanin mu,in ko ban fito ba sai mu dade basu sani a ido ba.

Su Iman kuwa, so biyu ina zuwa dubasu, nan na tarar yara sunyi kyau sunyi bul² kamar 'ya'yan turawa don Amayar Daddynsu na kula dasu kuma Tasi'u yanxu kudi ya zauna mai sosai don dakaga irin dukiyar da aka sama gidan kasan mai gidan ya jiku da naira, ko da naje nasamu tarban mutunci a wurinshi da kuma Amaryarshi mai suna Sumayya don har mukai exchanging din number sukace zasu ringa kawo mun su,aiko so biyu suna zuwa sumin yini ranar da ba makaranta.

Gidan Alhaji ko so uku ina zuwa,wanda so biyu ya barni na shiga shima sai da nakai khaleel Gidan Aunty Asma'u,ana ukun ne yace indai bazan maida khaleel ba kar in kuma shigo min gida, haka nayita kuka tukunna nabar Gidan na koma Gidan Aunty Asma'u na kwana, washe gari kuma na koma kaduna, wanda ina zuwa kuma na tarar da abin tashin hankali, barayi sun shiga dakina sun dauke min keken dinki da naira dubu ashirin,take hankalina ya tashi haka akayita min jaje, faruwar haka na shiga cikin wani hali, wanda ya zamana komai sai an taimaka min dashi saboda rashin sana'a, yau da gobe sai Allah, ganin suma masu taimakona sun fara gajiy yasa na fara sa'kar hannu,ba laifi ina ciniki, da haka rayuwa taci gaba, yau da dadi gobe akasin haka.

A lokacin dana cika shekara daya a Gidan granny,sai autan su Ammy yazo zaiyi aure, kuma dakin danake da dakinshi yakeso ya hadama Amaryarsa, hakan yasa na koma dakin Granny, kayan dakina kuma aka kai ajiya makota. Gani haka yasa na kira Ammy a kan maganarmu ta baya da tace zata yima Hajiyar Sokoto magana, shine tace in bari in hajiyar tazo bikin Yaya sadeeq da za ayi zata mata magana.

Haka dai na cigaba da zama a gidan Granny cikin hakuri don ji na nakeyi a takure, don abinci ma sai an kawo ma Granny daga wurin 'ya'yanta sannan nake sami inci sabanin da kafin a sace mun keke girkina nakeyi daban.

Anyi bikin Yaya sadeeq lfy,inda sai danayi danasanin zuwa don duk inda nabi su Aunty Mamy nuna ni suke suna ga
bazawarar gidansu, washe garin bikin da sassafe nabar gidan don banason Alhaji ya ganni saboda baison nazoba.

Biki da sati daya Yaya Arsala(dan Hajiyar Sokoto) ya kirani awaya yace in shirya in tafi sokoto, nan ko nayi ta murna don nasan ko ba komai zanci in koshi.

*SOKOTO*

kamar yanda na fadi Hajiyar sokoto yaya take wurin Alhaji su biyu kadai ne awurin Hajiya Kaka, farkon auranta tayine a Kudan inda ta haifi Yaya Kabeer(mijin Aunty Amina) daganan sai suka rabu da mijin tayi aure a sokoto ,mijinta shahararren mai kudi ne kuma mai sarauta,wanda a farkon auransu lagos a ka kaita saboda acan yake kasuwanci tana da yara takwas dashi, Aunty Atika,Yaya Arsala, Aunty huzaima, Aunty zainab, Aunty Aisha, Yaya Alamin(wanda Aunty zubaida ta aura kafin su rabu), Aunty shafa'atu da Aunty zuhura dukkansu sunyi aure sun hayayyafa don akalla hajiya nada jikoki hamsin da hudu, ban taba ganin family masu zumunci irinsuba dasu da 'ya'yansu kansu a hade yake, family ne da kowannensu yakeji da naira don duk cikinsu ba mai auran talaka, kuma kowanne business sukeyi sosai ba matan ba,ba mazan ba, hakan yasa kowa yake ji da kanshi a cikinsu.

Mijin hajiya Alhaji sammani kafin ya mutu yabar dukiya da yawa bacin gidaje,da gonaki har kuma tsabar kudi, hajiya na zaune ne a Gidan Alhaji Arsala, don tunda ta gama aurarwa ya zamana ita kadai ce a gida,sai ya sai wani karamin fili dake gefen gidanshi ya gina mata 3bedroom flat,sai ya zamana in kinshigo gate din gidan part dinta na hannun dama na Yaya Arsala na hannun hagu dashi da matarshi da 'ya'yanshi shida biyu mata, hudu maza.

Tunda nake ba a taba karramani irin yanda akamin a sokoto, ina zuwa na tarar da an waremin daki daya a part din hajiya an zuba min set din italian bed,ga plasma tv, Ac, center carpet da sauran kayan bedroom.

Zamana a Sokoto,zama ne mai cike da FREEDOM inci,insha abunda nakeso duk wani jin dadin rayuwa na sameshi a sokoto nan danan ni da khaleel hasken mu ya fito muk kara wani kyau don duk wanda yasan mu shekara daya baya zuwa yanxu yasan mun canza, anan ma na cigaba da sakata ina samun kudin kashewa, banda wata damuw don ko duk Gidan mu daga Ammy sai 'yan dakinmu suka san ina Sokoto,don Yaya Arsala ne yace kar a fadama Alhaji don yasan zai iya hanani Zuwa.

Watana you a Sokoto akayi karamar sallah,mun samu kaya dani da khaleel sosai, don ni ina da kala goma, khaleel na da shabiyu, don duk cikin 'ya'yan hajiya kowa sai da yamini kayan sallah,anyi sallah da kwana biyu sai ga Yaya Farooq yazo gaida Hajiya aiko nan yayita mamakin ganina, ni kuwa tsurewa nayi don nasan dole zai fada ma Alhaji.

Anyi sallah da sati biyu na yaye khaleel,sannan na daukeshi na kaishi kaduna na mika ma ubansa daga nan na wuce zaria, ina zuwa Alhaji yace in wuce in bashi wuri in koma inda na fito tunda sanda yace in bar yaron banji maganarsa ba, sannan wai don na rainashi da munafunci irin na Ammy dani na dauki kafa na koma sokoto ba tare da mun sanar maiba haka ina kuka nabar gidan,don bakinciki ko Gidan Aunty Asma'u banjeba na wuce park na hau motar Sokoto.

Tunda na dawo daga sokoto ko hajiya ta shiga gyarani don kullun addu'arta insamu miji anan inyi aure ko na samu kwanciyar hankali.

Satina biyu da dawowa daga zaria sai ga Aunty zubaida tazo wadda kallo daya zaka mata kasan kwakwalwar tata da matsala,nan dai hajiya tayi ta neman mata magani don abin nata kamar asiri saboda wani zubin lafiya wani zubin cuta.

Ana cikin hakane kuma kawu Muhammadu ya kirani yake sanar dani dakin da akasa kayana ya fadi,sundai kwashe kayan amma duk wasu sun fashe, dana sanar da Yaya Arsala sai yace in shirya in tafi in duba kayana, dazan wuce sai ya hadani da Aunty zubaida in kaita wurin mai magani da ya samu nan kaduna.

Bayan naje na duba kayana wanda duk wani kayan kitchen dina da kujera sun lalace,kayan gado kawai na tsira dashi, daganan nan kuma muka nufi gurin mai magani da Aunty Zubaida.
Bayan mai magani yayi mata tambayoyi yace mun aljanu aka turo mata,kuma ba shiganta sukayiba,shafenta sukeyi,sannan wani dan uwa na jikine yasa a tura mata, sannan makaryinsa sai dai a maida ma wanda ya turota........kakakarakara,asirin wasu ya kusa tonuwa.









*Comment*
*Like*
*Vote*
*Share*




*Fateeyzah*✍









*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_(home of peace,joint of entertainment,to educate and enlighten our readers)_*


*GIDAN NAGOGGO*🏨
*_(A true life story)_*


*_Written by fateeyzah_*😍😍


*_Bismillahir rahmanir rahim_*


*_Page4⃣1⃣to4⃣5⃣_*

Daukar waya nayi na kira Yaya Arsala na sanar dashi abunda mai magani ya fadi, sai yace adai yimata magani amma kar ace za a maida ma wani tunda yace cikin 'yan uwane, anan dai malam yace maganin na sati biyu, hakan yasa Yaya Arsala yace in zauna harsai angama maganin sai mu dawo tare.

Kwana na biyar a kaduna na shirya na tafi ganinsu Iman, tarba akamin ta mutunci kamar yanda aka saba, kuma naji dadin yanda sumayya take kula dasu especially khaleel dana ga ya zamo wani kato kuma ya dada wayo(rainan madara🤪), suma su Iman da ka gansu kasan suna jin dadin zaman gidan,nayi mamakin yanda yaron bai manta dani ba don yana ganina ya taho da gwarancinsa yana cewa yummy(mummy), wannan karan harta umma ta sakarmun fuska don haka tayi ta jana da hira, nan dai na basu chocolate din dana saimusu na dawo Gidan Granny cike da kewarsu.

Washe garin ranar da naje wurinsu Iman sai ga kiran Tasi'u, ina dauka muka gaisa yake tambayara ashe nazo kaduna, nace mai kwanana shida kenan, nan dai yayi ta jana da surutu, tun ina biye mai har na gaji nayi mashi sallama.

Bayan kwana uku,ranar na tashi da kewar yarana , hakan yasa na daidaici lokacin tashinsu break na shirya na tafi school dinsu, nan dai na gansu mukayita hira tare da daukar hoto, harsai da aka kada bell na komawa class tunkunna nabarsu suna daga min hannu,nima ina daga musu.

_(😭😭 rabuwar aure wallahi bata da dadi,especially in akwai yara a tsakani,sai yara su taso kamar marayu gasu dai suna da iyaye duka,amma rashin iyayen a wuri daya matsala ne duk yanda wata zata kula miki da 'ya'ya ba kamar yanda ke zaki kula dasu ki basu tarbiyya ba,inma aka hadu da mai rikon mara kirki sai tayi ta azabtar da yaran, amma kuma wani auren rabuwarshi shinr maslaha kamar wannan na Bahijjah mai cika da matsaloli wanda har takai babu ganin girma da mutunci tsakaninsu, Allah ya tsare ya kara dangana, hakuri da soyayyya tsakanin ma'aurata ya shiya mana 'ya'yanmu,shiriya ta tafarkin addinin musulunci,Ameen)_

Ina tafiya ina kokarin maida kwallar dake shirin futowa,kiran sunana da akayine yasa ni saurin juyowa,Yaya Mahmood na gani(yaya Mahmood cousins yake wurina, amma dangantakarsu tafi kusa da Tasi'u), nan dai na karasa muka gaisa sannan ya tambayeni hala su Iman nazo gani na amsamai da eh,nan dai yayi tamin fada na zubar da zumunci tunda na rabu da Tasi'u ko kira banayi a gaisa nan dai nayi ta kawo excuses, sannan muka yi sallama muka rabu.

_(Haka mutane suke,su suke zubar da zumunci amma insun ganka suyita borin kunya wai bakason zumunci🤔)_


Bayan kwana biyu, ina zaune ina shafa ma Aunty Zubaida magani, kawai sai ga kiran Alhaji ya shigo wayata, take gabana ya yanke ya fadi, don nidai a wurina kiran Alhaji ba Alkhairi bane a wurina, sai da wayar ta kusa katsewa tukunna na dauka cikin rawar na dauka tare da karawa a kunne hade da sallama, ya amsa sallamar tawa tare da fadin "uban mai ya kaiki kaduna?" yayi mini tambayar hade da hargagi.

Cikin rawar baki nace"naje kai Aunty Zubaida wurin mai magani ne daga nan kuma na duba kayana da akace ginin dakin ya fadi"

Cikin daga murya yace"Bahijjah yaushe kika fara karya?, kuma karyar ma kirasa wa zakiyi mawa sai ni"

Cikin sanyin jiki nace" wallahi Alhaji ba karya namaka ba,kafi kowa sanin ko yankani za'ayi indai na........"bai bari na karasa maganaba ya yanke kiran.

Haka ranar na wuni suku²,don duk iya tunani na na kasa tuna laifin dana yi ma Alhaji.

An gama yima Aunty Zubaida magani,inda abin nata yadanyi sauki, kwana biyu muka kara muka kama hanyar Sokoto.


Bayan mun huta tukunna Hajiya da Yaya Arsala suka kirani palour,jin kiran sai da gabana ya fadi don nasan ba lafiya ba, ina zuwa yay Arsala ya fara magana cikin bacin rai"Bahijjah kinsan maganganu da tijara da kika jama na cikin dangi kuwa?".

Jikina na karkarwa nace "A'ah".

Yace"maganganu nata yawo cikin dangi akan kinje kin samu Tasi'u kina kuka akan ya maida ke dakinki, hakan yasa yace muki bazai maida kiba don Allah yace inkin koma bashi bake, Amma wai sai kikayi hugging dinshi kika ce wai ya maida ke zaki zauna dashi yabar maganar Alhaji,shine yanxu muka kiraki muji gaskiyar magana don na kasa gasgata haka".

Cikin matukar razana na zayyane musu abunda ya faru, ina fadi ina kuka,don tunda nake ba'a taba mun irin wannan sharrinba.

Take Yaya Arsala ya kira Alhaji ya zayyane mai abunda ya faru, nan

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment