Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Alhaji yace abar maganar zai zo da babbar sallah.

Anyi sallah da kwana biyu su Alhaji suka zo Sokoto, bayan sun ci abinci sun huta aka fara meeting wanda duk akaina akayisa,nan dai aka maida magana akamana sulhu da Alhaji(dani da Aunty Zubaida)nan dai Alhaji
yace ya hakura sannan yace kowa ya zama shaida ko bayan ransa na koma Gidan Tasi'u bai yafemun ba.

Kwanan su biyu tukunna yace mu shirya yatafi damu don canma zaria meeting din zamuje muyi.

A ranar da muka dawo ba karamin farinciki na tsinci kaina ba saboda ko ba komai ranar na shiga gidan Alhaji batare daya koreni ba, kwana mukayi muna hira da Ammy don rabon da mu zauna muyi hira batare da wata fargaba ba shekara goma kenan.

Washe gari,Alhaji ya hada meeting wanda duk wani dan gidan sai daya halatta, nan dai Alhaji yayi mana nasiha tare da nuna mana muhimmancin zumunci, da alama dai mazan jikunansu sunyi sanyi don har gafarar Ammy suka roka sabanin matan da sai wani cika suke yi suna batsewa.

Satina daya a zaria na fara shirin komawa Sokoto,ba yadda Ammy bata yi daniba akan in bari akwai buki a gidan Aunty jummai dake katsina(kanwar Alhaji dasuke uba daya ita zata aurar da danta)amma naki,don gaba daya dan zaman gidan da nayi naji zaria ta fitarmun a rai,haka na shirya kayana na koma Sokoto.

Daga nan Sokoto ma Aunty shafa ce kadai taje bikin, itama kwananta biyu ta dawo.

Ina kwance da dadddare sai ga kira ya shigo wayata,ganin number ba suna yasa naki daga wayar, sai da aka kira so uku tukunna nayi picking, muryar babban magidancine ya bugu kunnena, jin hakan yasa na gaisheshi cikin girmamawa, bayan mun gaisa tukunna yayi gyaren muya tare da fadin"Bahijjah nasan baki gane mai magana ba,sunana Alhaji Suleiman,ina zaune ne a garin kano,inada mata biyu da yara hudu, ban taba ganinkiba amma na karfi number ki a wurin kawunki ne Alqasim da yake kano, abunda ya faru shina naje biki katsina ne kasancewa Mamar Aunty Jummai kanwa take a wurin babana,to anan naga 'ya'yanki kakarsu taje da su bikin,to gaskiya yaron sun bani sha'awa anan na tambayi Aunty umma(kanwar Aunty Jummai) yaron waye,anan dai ta bani labarin ki da abunda ya faru dake ba,gaskiya anan naji na kamu da sonki, ban yi nauyin bakiba na fada mata ina sonki, anan dai ta fada ma Alqasim da mijinta sabitu kasancewa sabitun yaya nane uban mu daya, shine sai Alqasim ya bani numberki"ya karashe magana cikin sanyi murya.

Nan na rasa bakin magana don jin maganarshi nayi kamar saukar aradu,sai da yayi gyaran murya sannan na dawo daga guntun tunanin da na tafi tare da cewa"ya za ayi baka ganniba amma kace kan sona?, don kaga 'ya'yana bai zama hujjar daza ka amince dani ba.

Ajiyar zuciya yayi tare da fadin"ina nan zuwa Sokoto sati mai zuwa saboda akwai wani abokina senator dazai kara aure, in nazo zan karaso wurinki".




Hmm ya kuke ganin,don da alama Bahijjah ta samo babban fish,abokin senator fa🤔.








Sorry for the errors ban yi editing ba.









*Comment*
*Like*
*Vote*
*Share*









*_Fateeyzah_* ✍









[4/17, 12:47 AM] ~Fateeyzah✍✍: *© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)_*


*GIDAN NAGOGGO*🏨
*_(A true life story)_*



*_Written by fateeyzah_*😍😍



*_Bismillahir rahmanir rahim_*


*_Page4⃣6⃣to5⃣0⃣_*


Haka dai mukayi sallama dashi, yabarni inata sake² don ban dauki maganarshi da wani muhimmanci ba,don a ganina daga gani 'ya'yana kawai batare da ya ganniba sai yace yana sona.

Washe gari kuma sai ga Aunty Umma ta kirani,bayan mun gaisa again dai maganar Suleiman tayi mini,tare da gargadina kar in basu kunya don suna son nuna ma Tasi'u da magoya bayanshi nafi karfinshi da har zai min sharri wai naje ina kuka ya maidani, bayan mun gama magana da ita ta umurceni da in kaima Hajiya wayar, nan dai nakai ma Hajiya wayar, bansan yanda suka Kare ba ,don ina bata wayar na juyo dakina ita kuma Hajiyar bata cemin komai ba.

Tunda ga ranar Suleiman kullun sai ya kirani so hudu, tun ban saki jiki da shiba,har nazo na yi,Suleiman namijine da ya iya tattali don yadda yake nuna min so bazakiyi tunanin ya ajiye mata biyu ba har da yara hudu.

A cikin satin nan nayi wani irin sabo dashi, wanda nake ji kamar mun yi shekaru tare, don wani irin zafaffan so nake masa wanda nima bansan lokacin daya shigeni ba, don a wannan lokacin na tabbatar da son dana yima Tasi'u kadan ne akan wanda nake yi ma Suleiman.

Week na zagayowa kamar yanda yayi alkawari sai gashi yazo,kallo daya zaka masa kasan akwai 'yan gidan rana(naira),wanda yasha shaddar shi gezna sai kyalli takeyi,chocolate color ne gashi giant,duk inda ake neman namiji, Suleiman yakai har ya wuce, nan dai na sauke shi a falon hajiya sannan na fara kawo mai su snacks da abinci dana tanada donshi,sai daya cika cikinsa sannan ya shiga ya gaida hajiya da Aunty suwaiba(matar yaya Arsala)sannan muka dawo parlour muka dasa hira, duk da yawancin hirar shi yakeyi don ni daga eh sai a'ah.

A dan zaman da mukayi na fahimci Suleiman mutum ne mai saukin kai, ga sanin ya kamata nan dai ya tabbatar mun shifa da gaske yake,don in so samune in aka tashi saka rana a saka wata daya, haka dai mukayi ta hira har Yaya Arsala ya dawo suka gaisa nan ya sanar da Yaya Arsala yanaso ya turo iyayensa amma kafin nan yanaso inje inyi HIV da Genotypes test nan dai nan dai Yaya Arsala ya amsa mai da zanyi kuma shima yanaso yayi bincik, inyaso in ya kammala ya turashi wurin Alhaji, anan dai sukayi sallama dashi.

Dawo wa gurina yayi mukayi sallam, ya kirgo 30k ya bani tare da fadin ga kudin hira Kya sa kati, nan dai nayi godiya tukunna namai rakiya ya tafi don jirgin karfe hudu zai bi zuwa kano.

Bayan sati daya naje nayo test inda result ya fito HIV Negative, Genotypes kuma AA, nan nayi snapping na tura masa shima ya turo min nashi wanda the same thing ne da nawa.

Bayan sati biyu yaya Arsala ya gama bincike sannan ya kira Alhaji ya sanar dashi nan dai Alhaji yace ya waliyi na, amma aje Kudan a daura aure, nan dai ya tsayar da ranar sati biyar.

Suleiman dubu dari uku ya bani in hada lefe, sannan danace mai zanje kaduna in gyara kayana ya bani dubu hamsin(wanda nayi karya nacema Yaya Baffa dubu goma ne)naki fada mai gaskiyane sabodah nasan sai ya fada ma su Aunty Amina.

Bayan nanne ya zamana in nakira Alhaji bai daukar wayata,ni kuma danaga baya dauka sai na dena kiransa.

Biki yana sauran sati uku shine na shiryo don in gyara kayana,wanda na biya gidan Alhaji yayi mini koron kare batare da nasan abunda nayi masa ba.




*BACK TO STORY*

Nauyayyar ajiyar zuciya na saki yare da goge hawayen dake idona, jin an tada kiran sallar magariba ne yasa na mike da sauki na fito,a kofar daki na taradda Granny na alwala kallona tayi tare da fadin "sannu hakima,sai yanxu kika tashi daga baccin asara, ai da niyata inna gama alwala inje in tashe ki da ruwan sanyi"ta karashe magana tana miko min butar hannunta.

Karfa butar nayi yare da fadin"ni ba bacci nayiba,tunanin rayuwar gidanmu nayi".

Tabe fuska granny tayi tare da fadin"rayuwar gidanku har abin tunawa ce, ai wannan mai hancin kamar biro itace matsalar gidanku,amma da *NAGOGGO* zai gane daya bincike rayuwar gidanshi"ta karashe magana tana shiga daki.

Inayi sallah isha'i naci abinci nayi shirin bacci na haye gadon Granny na kwanta,kamar jira yake sai ga kiran Suleiman, nan dai muka gaisa sannan yake cewa "wai darling har yau baki tambaye ni inda zan ijiyeki".

Lumshe ido nayi tare da fadin"indai zan zauna tare da kai, ko daji ka ajiyeni ba damu wata bane"

Murmushi yayi tare da fadin"wannan dadadan kalaman naki,shi yasa nake karaa sonki, Bahijjah zan hadaku keda matata ta biyune kasancewa no wacce cikin matana gidanta daban, to ke kinga yanda aurenmu yazo a kurarran lokaci babu time din gina miki naki gidan amma insha Allah kema zan miki naki daban, sannan kinyinmu babban laifii,hakan kuma yaja na fara tunani baki damu da lamarinaba"

Bakina na rawa kuma cikin sigar shagwaba nace"haba sweetheart me nayi maka,don Allah kayi hakuri".

Cikin sanyin murya yace"duk lokacin da muka dauka tare baki taba tambayata sana'ata ba kuma nasan baki sani ba"

A kunyace nace"sorry sweetheart, amma ni a tunanina tun ran farko da muka hadu kai ya kamata ka sanar dani".

"Gaskiya ne abunda kika fada gimbiyaata,to nidai sana'ata itace siyar da GOLD".

Cikin jin kunya nace"Allah sarki,Allah ya bada sa'a".

Haka dai muka cigaba da hirar mu sai wurin goma muka yi sallama.

Ina shirin kwanciya kuma sai ga text ya shigo,ina dubawa sai na ga number Tasi'u ne cikin sauri na bude sai gani nayi ya rubutu _wallahi_ _Bahijjah baki isa kiyi aure ba indai ina raye,ba wani dan akuya daya isa ya shigarmun gonata,dan haka mu zuba ni dake shege ka fasa._
Wallahi nayi nan kafin 'yan Bahijjah team su fasa ma Tasi'u kai,azo ace dani a ciki💪🏃‍♀️🏃‍♀️.


*Comment*
*Like*
*Vote*
*Share*






*_Fateeyzah_*✍
[4/18, 8:00 PM] ~Fateeyzah✍✍:









*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_(home of peace, joint of entertainment and to educate and enlighten our readers)_*



*GIDAN NAGOGGO*🏨
*_(A true life story)_*


*_Written by fateeyzah_*😍😍



*_Bismillahir rahmanir rahim_*

*_Page5⃣1⃣to5⃣5⃣_*



Ina gama karanta text din shi na tuntsire da dariya 🤣🤣don a tunani na sanda Tasi'u yayi typing din text din kamar kwakwalwarshi ta juya, ban tsaya wani tunani ba na kashe wayata na kwanta don na riga na fitar da Tasi'u da duk wata matsalarshi a raina, don a yanxu na riga nayi mai nisa,yarana kuma kullun bana fashin addu'a akansu, Allah ya rayasu, ya shiryasu a tafarkin addinin musulunci.

Washe gari da safe, wurin karfe goma na bude inda aka ajiye kayana,duk kayan sun lalace duk gara ta cisu,kallonsu nake nama rasa ta inda zan fara,shawara kawai na yanke a zuciyata akan kudin da Suleiman ya bani na lefe inyi amfani dashi in canza gado,saboda yaya Arsala shi yace zai mun kujeru, ina tsaye inata tsake² sai ga kiran Aunty Aisha a wayata, bayan na dauka muka gaisa take cemun inbar gyaran gadon don sunyi magana da yaya Al'amin zai canza min gado,nan naji wani farin ciki ya lullubeni, tsakanina da 'ya'yan Hajiyar Sokoto sai dai addu'a don sunyi mini abunda ko wadanda muke uba daya sun kasa yiminshi, nan dai na koma na sanar da Granny, ita ma tayi murna tare da sa musu Albarka.

Haka na kira Aunty Asma'u na sanar da ita, sannan nakira Ammy, bayan na sanar da ita itama ta tayani murna sannan tace "Bahijjah Baffa yazo ya bama Alhaji hakuri, ya amsa ya hakura, amma yau da safe yace min ince miki kafin ki wuce Sokoto ki biyo ta zaria yana nemanki".

Cikin rikicewa nace "Ammy Mai kuma nayi?"

Ta amsa da"nima bansani ba,abinda dai yace kenan"

Cikin sanyin jiki na sanar da ita text din da Tasi'u yamin, nan dai Ammy ta kuma kwantarmun da hankali tare da nuna min in dogara da Allah ba abunda ya isa yamun.

Kamar jiya,yauma bayan nagama waya da Suleiman sai ga text din Tasi'u, ina budewa sai naga ya rubuta:
_(Bahijjah don ke aka yini,haka nima don ni aka yiki, don Allah Bahijjah karki aure wannan jakin mutumin, na miki alkawarin zan maida ke dakinki tare da Alkawarin rayuwa mai inganci, rayuwa ta jin dadi, ki taimaka ki dawo ki rungumi yaranki)._

Wannan karan text dinshi ya daga mun hankali tare da tambayar kaina wai mai Tasi'u yake nema a gurina, duk abinda yayi min bai isheshi ba sai ya kuma dasa mun wani bakin cikin, ganin bani da mai ban amsar tambayata yasa na kwanta, wanda sai wurin karfe biyun dare bacci ya daukeni.

Sha biyu dai² na shiga Gidan Alhaji wanda direct palourn shi na wuce, nan na tarar da shi da Ummy a parlourn,bayan na zauna muka gaisa, duk suka amsamin fuska ba yabo ba fallasa, take jikina yayi sanyi, don dama zuciyata tun jiya take bani akwai wani abu da ya faru, daukar waya yayu ya kara a kunne, an sai da yayi kamar sakon biyar tukunna yace kisa meni a parlour.

Bayan mintina kadan sai ga Ammy ta shigo da sallama, samun wuri tayi ta zauna tare da fadin"sannuku da hutawa".
Umm

Ummy ce kawai ta amsa sabanin Alhaji da daga kai kawai yayi tare da gyaran murya" Abinda yasa na taraku shine jiya da daddare ina zaune a parlour nan sai ga sarki da Tasi'u sunzo, bayan mun gaisa da sarki shine ya fadamin musassbabin zuwanshi wai Tasi'u ne yaje yana tamai kuka akan shi baisan sanda ya saki Bahijjah ba, a taimaka a dawo mai da matarsa yana sonta, jin abinda sarki ya fadine ya tunzurani nafara fad'a amma kuma sai ya dakatar dani akan mu tsaya mu saurareshi, nan dai Tasi'u yafara bamu labari wai yaje karatu da akeyi ne tsakanin magariba da isha'i sai malamun yafara karatu akan sihiri, daganan sai yafara karanto ayoyin da suke karya sihirin, wai daganan sai kanshi ya fara juyamai, daganan baisan inda kanshi yakeba, sai farkawa yayi ya ganshi a kwance a gaban malamin daga nanne kuma malamin ya fada mai abunda ya faru wai Aljanu aka turo mai amma sun samu su fitar dasu, sannan ya fadamai Aljannun sunce turo su akayi su shiga jikinsa don su raba aurenku, wanda ke ma akwai asirin a jikinki wanda zaisa Tasi'u ya tsane ki, daga karshe dai har kuka rabu, sannan zaman da sukayi a jikinsa sun taba masha kwayoyinsa na haihuwa" Alhaji ya karashe magana hade da goge zufar da ta tsattsafo mai.

Dukkanmu damuke parlourn kasa magana mukayi, sai zufa datake ta tsattsafo mana, ni kuwa har da wani firgice daya shigeni.

Alhaji ne ya ci gaba da cewa"malamin yace akai Bahijjah don yayi mata rukiyya,sannan ko za a samu na jikinta su fadi wanda yayi musu wannan aikin".

Take Ummy ta zaro ido,zufa nata keto mata.



Pls manage




Not edited




*Comment*
*Like*
*Vote*
*Share*






*Fateeyzah*✍






*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)*



*GIDAN NAGOGGO*🏨
*_(A true life story)_*


*_Written by fateeyzah_*😍😍


*_I dedicated this novel to my late father(Alh Babangida N.T.C)who die on 23rd August 2014, may his soul rest in peace._*


*_Bismillahir rahmanir rahim_*

*_Page5⃣6⃣to6⃣0⃣_*





Cikin kidima Ummy tace "yanxu in aka yi rukiyyar zasu fadi wanda ya turo su".

Cikin mamakin tambayar ta yasa gaba daya muka kalleta, lura da tayi hankalinmu ya koma kanta ne yasa tayi saurin cewa"Allah ya baki lafiya Bahijjah,Allah ya saka muki", gaba dayan mu muka amsa da "Ameen"

Alhajine ne ya mike hade da fadin" Amina sai ki shirya kayan ki kema don gobe in Tasi'u yazo dake zamu tafi, daga nan sai ki dan kwana biyu wurin Goggo tunda kin dau lokaci bakije ba"

Cike da murna Ammy ta amsa da "nagode Alhaji,Allah ya kara tsahon shekaru".

Amsa wa yayi da "Amin"sannan ya shige bedroom dinshi.

Nan muka tashi muka bar Ummy wanda tayi nisa cikin tunani don bata san sanda muka fita ba.

Yini ranar hirar mukayi tayi da Ammy, wanda yawancinta ta bata gidanmu ce kawai ba har da ta matsalolin family dinmu gaba daya, duk yanda naso Ammy ta tsaya muyi magana akan aljanun da akace an turo min da asirin da aka yomin taki, don dana kawo maganar take Zamora wanda bansan dalili ba.

Wayewar ranar bakwai tayi ma Tasi'u a gidanmu bayan gaishe² muka kama hanya wanda Tasi'u ne ke driving, sai Alhaji a gefenshi, sannan nida Ammy a baya,don Alhaji ya hana a sanar da sauran yaran Gidan, saboda yace a bari dai muje mu dawo, yana ta satar kallona ta mirror, damun hada ido sai ya dauke kai don na lura yanxu Tasi'u kamar kunya ta yake.

Muna isa kaduna, direct gidan malamin dake Malali muka wuce, bayan mun isa, Tasi'u ya kira malamin a waya don neman iso, muna tsaye sai gashi ya fito, bayan mun gaisa yayi mana iso cikin gida inda ya sauke mu a wani Babban parlour da aka lailayeshi da brown carpet sai wata cabinet a wata kusurwa dake shake da manyan Qur'anai da sauran littafan Addini.

Bayan mun zauna Tasi'u ya yi masa bayani kamar haka"Allah ya gafarta malam wannan ce tsohuwar matata da muka yi magana dakai kwana uku da suka wuce, wadannan kuma iyayentane" ya karasa magana yana nuna Alhaji da Ammy.

Sai da malam ya kalleni for some minutes, sannan ya maida kallonsa kan Ammy daga bisani yayi gyaran murya tare da cewa" Alhaji da Tasi'u ina tunanin zaku dan bamu waje" yayi magana yana kallonsu.

Nan dai Alhaji ya amsa mai da"toh,babu damuwa"

Bayan fitarsu Alhaji, malam ya umurceni da inbashi tarihin aurena da Tasi'u, aiko nan na fara bashi wanda kafin in gama na wanke fuskata da hawaye wanda Ammy take tayani.

Gyara zama yayi tare da fadin" gaskiya zan fada muku kuna da matsala dukkanku,don ke(ya nuna Ammy da yatsa) dadadden asiri ne a jikinki wanda karya shi lokaci daya zai yi wuya, sanna ke (ya nuno ni da yatsa)Aljana ne aka turo miki kamar yanda aka turo ma Tasi'u wanda shi harda Asiri aka hada mai wanda kuma asirin yafi tasiri a jikinshi, sakamakon rashin maida hankali akan ibada da azkar, bayan na karya asiri jikinshi ne na mai rukiyya inda Aljananin yake sanar dani dashi data jikinki tare aka turo su, kasancewa shi ya tsani aljanar jikinki ita kuma tana sonshi, wannan ne yasa aka turashi jikin Tasi'u don yasa mai kiyayyarki acikin zuciya, wannan ne yayi musabbabin rabuwar ku wanda kuma Allah yasa zaman aurenku ya kare".

Kafin ya gama maganar nan gaba daya hawaye ya wanke mana fuska, Ammy ce tayi karfin halin cewa" Allah gafarta malam, ko sun fadi wanda ya turo su"

"Tabbas shi Aljanin ya fadi uwar gidankine ta turo su, naki fadama Tasi'u ne saboda na fison in gama yi ma ita Bahijjah rukiya itama, don ko asirin da ke jikinki ita tayi shi"ya karashe magana yana nuno Ammy.

Cikin kidima muka hada baki muna salati,sai da muka kwashi mintina sannan Ammy tabude baki tace"don Allah malam ina neman wata alfarma na karka fada ma Alhaji ko Tasi'u wanda yayi wannan abun don nasan wannan maganar ba karamin tashin alkali zata jaba, ni na barta da Allah, Allah ya saka mana, don insha Allahu da sannu zata girbe abinda ta shuka".

Malam ya amsa"da insha Allahu baza suji wannan maganar ba,wannan dalilin ne yasa nace su bamu wuri, don na saba samun irin wannan case din naku, yanxu ke zan hada miki magunguna da ruwan magarya, indai kina amfani dashi da izinin Allah komai zai warware, sannan ke Bahijjah zamu miki rukiyya kema insha Allahu komai zai daidaita, yanxu bari in kirasu su shigo ayi a gabansu"ya karashe magana ya na kokarin tashi".

Bayan su Alhaji sun shigo ya nuna musu toilet din dake parlourn a kan su shiga su dauro Alwala, da ya bayan daya mukayo Alwala,sannan malam ya ibi wani ruwa daga cikin wata jarka ya watsa min akai, sannan ya bama Ammy wani turare ta shaka mun, tunda ta shakamun bansan inda kaina yake ba.

Wurin la'asar na tashi na ganni akan gadon Granny, kokarin tashi nayi amma na kasa don jinayi duk jikina kamar an mini duka, jin muryar Ammy da nayi daga falo yasa na fara kwala mata kira" Ammy, Ammy".

Cikin hanzari ta shigo dakin Granny na biye da ita, kokarin tada ni tayi tare da fadin "sannu Bahijjah, Goggo dan Allah miko min maganin da malam yace inta tashi a shafa mata"

Cikin sauri Grand ta fita sai gashi ta dawo da wata kwalba ta mikia ma Ammy, karfa tayi ta shafa mun tare da jero mun sannu, bayan ta shafamun da kusan minti biyar sai gashi inata zufa daganan kuma sai naji jikina ya canza take naji wani karfi yazo min, ganin haka yasa fara'ar fuskar Ammy ta karu.

Kwana biyu na kara a kaduna sannan na shirya komawa saboda inaso in biya zaria in kwana daya kafin in wuce sokoto, kafin in tafi sai da Ammy ta kuma jamin kunne akan kar in sake ko Aunty Asma'u in fada mata abinda ya faru.

Bayan na kuma warwarewa nasamu nayi wanka hade da rama sallolin da ake bina.


Ina sauka a zaria direct gidan Alhaji na nufa,wanda bayan gaishe², Alhaji ya nemi ganina cikin sirri a bedroom nashi, bayan na shiga na samu wuri na zauna tukunna ya gyaran murya yace"abunda yasa nace ina son ganinki ba komai bane illa in nemi yafiyarki akan abubuwan dana yi muki, hakika Bahijjah ban miki adalci a matsayina na mahaifinki don nasan na cutar dake, so da yawa sai nayi miki abu amma daga baya kuma sai abin ya zo ya dameni, Amma daga yanxu insha Allahu kin dena zubar da hawaye saboda ni" ya karashe magana cikin sanyin murya.



Cikin karayar zuciya wanda duk wanda yaji muryata yasan dauriya kawai nake nace" na yafe maka Alhaji,amma nima don Allah ina neman yafiyarka, don nima na saba maka na tsallake duk wata magana taka".

Yace"Bahijjah ba komai Allah ya yafe mana gaba daya, abu na gaba kuma shine Tasi'u yazo mini da wata magana akan yanaso a maida auranku, to amma sai na nuna masa yanxu haka da sa ranar wani akanki, to dayake a gaban sarki mukayi sai yace a bari aji ta bakinki ,in zaki koma gidan Tasi'u ne ki rike yaranki sai aba ma shi Suleiman hakuri, inkuma Suleiman din kika zaba shi kenan don dai wannan karan bazan miki doleba kamar wancan karan".



To Bahijjah fans sai ku zabar mata miji a karo na biyu tunda Alhaji ya baku zabi😍.



Ina Suleiman fans banda son kai,haka kuma Tasi'u fans.


Insha Allah saura page daya na gama novel dinnan saboda azumi ya gabato.



*Comment*
*Like*
*Vote*
*Share*





*_Fateeyzah_*✍


*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_(home of peace,joint of entertainment,to educate and enlighten our readers)_*



*GIDAN NAGOGGO*🏨
*_(A true life story)_*



*_Written by fateeyzah_*😍😍




*_Page 6⃣1⃣to7️⃣0⃣_*


Cikin tsarkewar murya nace"don Allah Alhaji kayi hakuri da abinda zan fadi, na zabi auran Suleiman akan komawa Gidan Daddynsu Iman, don ko na koma zan ringa kallonshi da irin wulakancin da yamun duk da ba a hayyacinsa yayi ba, sannan su Iman sunyi dace da uwar riko, don nasan sumayya na kula dasu dai² gwargwado".

(Lol🤪 duk kun bude kunne kuji zabin Bahijjah, to dai ta zabi naku nikuma ta ajiye nawa my Tasi'u😢😢).

Cikin sanyin jiki Alhaji yace"Allah yasa haka shi yafi zama Alkhairi, su kuma yaran Allah ya shiryasu".

Cikin jin kunya na amsa da"Amin".

"Ina zuwa Bahijjah"Alhaji ya fada tare da mikewa ya nufi drawer da ke dakin, bayan 'yan mintoci kuma ya nufo ni da kudi a hannushi, mika min yayi tare da fadin" Bahijjah ga gudunmawata nan a matsayina na mahaifinki, kije ki sayi abinda baki da dashi, sannan zan kira 'yan sokoto in musu godiya don Ammynki ta fada mun sunyi miki kayan daki".

Cike da murna na karfa tare da fadin "nagode Alhaji, Allah yasaka da alkhairi ya kara girma.

Fuskarshi cike da fara'a yace "Amin Bahijjah,Allah yayi miki albarka, yaushe zaki wuce Sokoto?"

Ina mirmushi nace" Amin Alhaji, gobe zan wuce".

Ya mike tare da fadin" Allah shi kaimu,bari in tafi masallaci naji an fara kira" ya karashe magana yana fita.

Bayan nabar dakin Alhaji, Gidan Aunty Asma'u na wuce don magana nacina na kosa inje in fada mata yanda mukayi da Alhaji, da sallama na shiga Gidan, da gudu Aunty Asma'u tazo ta hugging dina tare da fadin" wallahi yanxu nake zuci² kiranki" ta fadi fuskarta cike da fara'a.

Nace" gani nan nazo ai, nima bakina cike yake da magana, wallahi Aunty Asma'u yau ji nake kamar an mini kyautar Aljanna, wai yau ni Alhaji ya nemi yafiyata har da samun Albarka, wanda tun dana taso nayi Wayau ban taba jin wata kalma mai dadi da Alhaji ya jefeni da ita ba" na karashe magana cikin zubar da wasu zafaffun hawaye.

Idon Aunty Asma'u cike da kwalla tace" Bahijjah ba kuka zamuyi ba, godewa Allah zamuyi don nima jiya Alhaji har gidan nan yazo ya nemi yafiyarmu nida baban Amira, Ammy ma tace ya nemi yafiyarta, kinga wannan

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment