Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

babban ni'ima ce daga Allah".

Nan dai na nuna mata kudin da Alhaji ya bani, itama tayi ta murna tare da yima Alhaji addu'a sannan tace zata kirashi Tayi masa godiya koda muka irga kudin naira dubu hamsin muka gani.

Nan dai na taya ta mukayi girki sannan na mata sallama na nufi Gidan Yaya Baffa.

Bayan gaishe gaishe, yaya Baffa ya kawo dubu dari biyu ya bani yace ga gudummawar da suka hadamun nan, cikin farin ciki na masa godiya sannan yamana sallama nida Aunty Hanna ya fita.

Bayan fitarsa kuma muka dasa hira da Aunty hanna inda take fadinmin wai su Aunty Amina sunce bazasu bada komai ba da sunan gudun mawa, tunda ai farko sunyi meeting akan bazasu bani komai ba, amma Yaya Baffa yaje matarshi ta zugo shi don haka bazasu bada komai ba.

Cike da mamaki nace "yanzu to dubu dari biyun nan wa ya bada"

Gyaran murya tayi tare da fadin"Farooq yabada dubu hamsin,sai honey yabada dari, sauran dubu hamsin din Kuma da Asma'u,fatima da halima suka bada, sai matar Ibrahim da ta Baki food flask, zeena ta baki tukunya, sannan fatima ta kara miki da bedsheets".

Fuskata dauke da murmushi nace"Allah ya saka musu da Alkhairi ya kara budi, kinga can ma Yaya Arsala ya yimini gado, yaya Al'amin kuma kujeru".

"Ai na ma mantane ban miki murna ba don honey ya fada mini, su Aunty Amina su kuma na lura bakin ciki ke damunsu" ta karashe magana fuskarta cike da damuwa.

Nace"su suka sani, ni yanxu banda lokacinsu"

Nan dai muka shigaba da hira,da natashi tafiya ta hado mun kayan dana samu gudun mawa, sannan ta bani zanin gadon data saimuni.

Ina komawa, direct parlourn Alhaji na wuce na nuna masa kayan da kudin, nan yayi ta sa Albarka, sannan yace in nuna ma Ummy ta gani na ansa mai da toh, amma ban nuna mata don Aunty Hanna tayi mini kashedin kar in sake in nuna mata don zanja ma wadanda suka bani magana.

Dakin Ammy na shiga na ajiye kayan sannan na nufi gidan Yaya Ibrahim don inma matarshi godiya, daga nan na shiga Gidan yaya sadeeq muka gaisa da matarshi , itama da zan fito ta bani wani jug hade da cups dinshi, daga nan nayi wurin Aunty zeena.

Ina shiga nayi kicibus da Aunty Amina zata fita ko kallonta ban yiba na wuce ta, ita kuma ta bini da tsaki.

Aunty Zeena da murna ta tare ni tare da fadin "maman Iman kece".

Na amsa"da nice Aunty zeena" nan dai muka gaisa tare da mata godiyar tukunyar da tabani.

"Bahijjah ba godiya tsakanin mu,ke dai Allah sanya Alkhairi ya bada zaman lafiya"cewar Aunty zeena.

Nace"amin, dama inaso in karbi number Yaya Farooq in mai godiya kudin daya bada".

Aunty Zeena ta gyara zama tare da fadin"Bahijjah kar kiji komai, kuma dama yace in neman mai yafiyarki akan abubuwan daya miki a can baya, don wai kunyarki yake ji, shi yasa bai kiraki ba".

Nace "ba komai Aunty, zan kira shi"

Nan dai muka dan taba hira, sannan na karfi number Yaya Farooq na kuma komawa Gidan Aunty Asma'u, wanda ban dawo gidan Alhaji ba sai dare, na leka dakin Alhaji na masa sai da safe, daganan kuma na leka wurinsu Aliyu sannan na wuce dakin Ammy ko kallon part din Ummy ban yiba don har ga Allah ba karamun tsanarta nake ji a raina ba.

Ina gama waya da Suleiman bacci ya daukeni saboda ba karamin gajiya nayiba yau, da safe ma sai dana makara don banyi sallar asuba ba sai karfe shidda da rabi, wurin karfe takwas na gama shirya wa, sannan na dauki wayata na kira Ammy, tana dauka nace" Asslamu alaikum, Ammy ina kwana?"

Daga can bangaren Ammy ta amsa da"wa'alaikumussalam, lfy lau bahijja badai har kin shirya ba".

Na amsa da na shiya, amma sai karfe goma zan wuce, dama nakira ne in fada miki yaya Baffa ya bani dubu dari biyu gudunmawar da suka tara, Alhaji kuma ya bani dubu hamsin, Aunty Hanna bedsheet, Aunty zeena tukunya, Aunty Rukayya food flask sai matar yaya sadeek da ta bani jug, sannan Aunty Fatima ta bani bedsheets".

Ammy cikin murna tace "Alhamdulillah Bahijjah kinga riban hakuri ko?, ubangiji Allah ya saka musu da Alkhairi ya kuma hada kanku, ya kareku daga sharrin makiya".

Cikin jin dadi na amsa da "Amin Ammy", nan dai mukayi sallama na kashe wayana.

Haka na kira Yaya Farooq,Aunty Fatima da Halima na yi musu godiya.

Wurin karfe takwas sai ga breakfast Ummy ta aiko salma dashi(first in history), karfa nayi tare da godiya, ina ganin fitarta na samu leda baka na zuba nasa a jakata, don niyyata in na fita insa a kwata, don da inci abincin ummy gwara na kwana da yunwa.

Wurin karfe tara da rabi na dauki kayana na kulle ma Ammy dakinta, sannan na shiga dakin Ummy na gaisheta tare da mata sallama, sannan na wuce part din Alhaji shima mukayi sallama tare da bashi keyn part din Ammy yana ta samun albarka, ina fitowa harabar gidan na ga Aliyu yana kokarin hawa lifan dinshi, tsaida shi nayi tare da umurtarshi ya a jiyeni Gidan Aunty Asma'u, bayan ya ajiyeni mukayi sallama na kawo dubu goma na bashi nace ya dauki dubu biyar yabama su Abdullah da Taheer su raba dubu biyar, godiya yamun tare damun addu'ar sauka lafiya.

Ina shiga muka gaisa da Aunty Asma'u sannan nace" maman Amira ga dubu hamsin ki ijewa Ammy inta dawo ta siya abinda bata da shi" na karashe magana ina mika mata kudin.

Bata fuska tayi tare da fadin"Bahijjah baza ayi haka ba ke da kike da hidima a gabanki, in bamu kara muki ba ai baza mu karba a wurinki ba".

Bata fuska nayi tare da fadin"don Allah ki karfa, wallahi yanxu haka kusan dubu dari shida gareni, kuma kinga abinda zan siya ba wasu masu yawa bane, tunda duk an riga an gama siyansu, kinga ita kuma Ammy ko gas a saimata don naga da gawayi take girki".

Gyara zama Aunty Asma'u tayi tare da cewa "shikenan bahijja tunda kince akwai kudi a hannunki,kuma dama nayi niyar saimata gas din ko karamar cylinder ne, ko itama ta huta, don tunda gas din gidannan ya lalace Alhaji yasa aka futa dashi nayi ta son in siyan mata, amma kuma sai Aunty Hanna tace Yaya Baffa yace zai siya, to sai dai daya tashi sai ya siyan ma Ummy, sai da muke magana da Aunty hanna tace wai Ummyn ce ta hana ya siya har da Ammy".

Tabe baki nayi tare da cewa ita ta sani, kayi da kyau ma ya ka kare ballantana bakayi ba" na karashe magana ina kokarin tashi.

Aunty Asma'u itama tashi tayi tare da fadin"Allah dai ya kyauta".

Na amsa da"Amin, ni dai na wuce".

"To Allah ya kiyaye hanya ki gaida su Hajiya, sai mun hadu a kano"cewar Aunty Asma'u.

Na ams da"Amin zasuji".

Ina fita na bude jakata na fito da bakar ledar dana zuba abincin wurin ummy na jefa a kwata na wuce abuna.


*Sokoto*

Tunda na koma Sokoto ban zauna ba don kullun muna hanyar kasuwa dasu Aunty Zuhura, duk wani abu da nasan ba'a siya ba especially kitchen equipment na siyesu, sannan na siya set din akwatina mai guda hudu, sannan na sayi kaya kala goma sha biyar na bada dinki.

Bangaren hajiya kuma, ta dinka mun kaya kala goma wanda duk kayan bamai arha.

'ya'yan hajiya kuma mata su suka siyarmun blanket 2,TV, reciever, center carpet,gas cooker ,bedsheets 5, da tukwane biyar.

Garaah ko wadda sukayi mini ko aurena na farko ba ayi min ba.

Sosai Hajiya dasu Aunty shafa suka tsima ni da magungunan karin ni'ima.

Biki na sauran sati daya Suleiman ya samu matsala da matarsa ta biyu, inda abun har ya kai da saki, har cikin raina banji dadin haka ba dukda an sanarmun masifaffiyace ta karshe, kuma da da ita zai hada mu.

biki sauran kwana biyu, aka wuce da kayana kano, wanda washe gari kuma mukayi mota uku daga Sokoto mukayi kano, don hajiya kawai aka bari a gida.

*KANO*

Direct gidan Aunty Aisha muka wuce inda na tarad da su Aunty Asma'u,Aunty Hanna da Aunty zeena, sai manyan 'ya'yan hajiya su Aunty huwaila da Aunty Atika har sun iso, nan dai mukaci abinci, muka yi sallah sannan aka fara aikace², ni kuma aka kiramun mai lalle aka fara muni.


Washe gari, karfe shadaya aka daura auran a Kudan, auren da Alhaji shi ya bada da kansa batare daya wakilta kowa ba.

Ana daura aure ,fateeyzah tazo ta tsantsaramun kwalliya wadda ta dace da fuskata.

_(Fateeyzah makeover for_ _u at affordable price)_

Ana gama min makeup sai ga kiran sumayya ya shigo, ina picking naji tana kuka tana fadin" maman Iman don Allah Daddynsu Iman yake son magana dake, satinmu daya kenan a asibiti sakamakon hawan jini dayayi masa mugun kamu".

Nan naji hankalina ya tashi don nasan ciwon bazai rasa nasaba da kin komawa gidanshi da nayiba, don dana koma sokoto Ammy tace yazo yana ta kuka, cikin sanyin jiki nace "bashi wayar sumayya"

Cikin murya irin ta marasa lafiya ya fara fadin" Bahijjah nasa sumayya ta kira kine in roke ki gafarar abunda nayi miki, wallahi Bahijjah ba a hayyacina na aikata miki haka ba, don Allah ki taimaka min ki yafemun" ya karashe magana cikin karayar zuciya.
Cikin mutuwar jiki nace" yaya Tasi'u na yafe maka,don Allah nima in cikin zamanmu akwai abunda na maka ka yafemun "

Cikin sanyin murya ya amsa da"na yafemiki Bahijjah, Allah kuma ya sanya Alkhairi ya bada zaman lafiya"

Kasa amsa mai nayi saboda wani kuka da yazomini, kashe wayar nayi tare da kifa kaina a cinya ina kuka, don gani nayi ban kyauta ma Tasi'u ba.

Karfe hudu su Aunty Ateeka suka tafi gyara mini gida.

Bayan magriba kuma motocin daukata suka iso, haka aka futo dani ina kuka sai kace wata budurwa aka wuce dani gidana dake nassarawa g.r.a, gidanne na alfarma wanda ke dauke da flat biyu, kowanne flat akwai parlour daya, bedroom biyu,dinning sai kitchen da store.

Su yaya Arsala ba kananan furnitures suka Samun ba, don da bed dina da kujeru duka Royal furniture aka samun, kitchen dina kuwa ko wata budurwar albarka.

Karfe tara su Aunty Asma'u suka juya bayan sun gama min nasihohi.

*A gurguje*

Zamana da Suleiman, zama ne naso da mutumta juna, zamane na kwanciyar hankali, haka ita ma uwargidansa banda matsala da ita don macece mai sanyin hali.

Satina biyu a gidan Suleiman ya siyan mini dinning table da fridge, sannan ya bani naira dubu dari inyi jali, wanda na hada da kudin hannuna na sari kaya na tura ma Aunty Asma'u ta ringa saida muni.

Matsalar dana dan fuskanta a Gidan Suleiman, shine matsalar matarshi da suka rabu, wanda ta ringa turomin da bakaken maganganu tare da alwashin sai taga bayana tunda na rabata da mijinta, ba karamin tsorata nayi da maganganunta ba amma daga baya na dage da addu'a da tsayuwar dare, wanda ko da ta yimini wata muguntar kanta take komawa.

Sannan ina yawan tunanin su Iman amma daga karshe sai na hakura ina binsu da addu'a.

*Bayan shekara biyu*

Abubuwa sun faru da yawa, ciki kuwa harda haihuwar 'yan biyu da nayi mace da namiji wanda aka sa masu suna Muhammad da Fatima.

Asirin dake jikin Ammy kuwa duk ya karye wanda yazama kaikayi koma kan mashekiya, don Alhaji gaba daya yanxu ya fita hanyar Ummy wadda abu ya mata yawa yanxu don salma tayi aure biyu kenan cikin shekara daya, wanda yanxu haka zawarci takeyi.

Aunty Amina kuwa yanxu duniya ta juya mata, don d'an aikin da take fafa dashi an koreta, sai dai abinda miji ya kawo ya bata, don shima mijin ba karfi gareshi.

Aunty Mamy kuwa itama dai duk daya suke da Aunty Amina don shima mijinta an koreshi daga aiki sai dan buga².

Aunty Hauwah kuwa ita mijinta kishiya yayi mata da sa'ar 'yarta ta uku, sannan sati daya kenan da mukaje bikin babbar 'yarta inda aure ya mutu washe garin bikin saboda ango yazo ya musu karyar kudi suka dauki yarinya suka bashi wanda daga karshe akazo ba dakin da za a saka amarya, shikuma uban amarya yace a sakar mai 'ya.

Muko rayuwarmu yanxu sai dai muce Alhamdulillah don irin daukakar da muka samu, don yanxu Aliyu ya sa mu aiki a refinery, Abdullah kuwa yana aikine a ministry of finance, Taheer kuma sannan shekarar ya samu admission a A.B.U inda yake karanta medicine.

Bangaren Aunty Asma'u kuwa yanxu mijinta trailer shi uku, sannan itama tana samu a business din da mukeyi ni da ita.

Zuminci mai karfine tsakanina da yaya Tasi'u, don har gida yake kawomun su Iman hutu, sannan ya sami sauki don sumayya ta haifi 'yarta mace wanda taci sunana sai dai yarinyar Abnormal ce.

*GIDAN NAGOGGO* kuwa yanxu sai son barka don in ka cire su Aunty Amina zumunci muke yi sosai har da surukan gidan.

Alhaji kuwa a kunlin addu'ace da sai Albarka ke shiga tsakaninmu, Ammy kuwa yanxu itace 'yar gaban goshin Alhaji.



*ALHAMDULILLAH !*
*ALHAMDULILLAH*

Anan na kawo karshen littafina mai sunan *GIDAN NAGOGGO* , ina rokon Allah ya yafemun kuskuren dake cikin wannan littafi.

Jinjina garekuu

*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*REAL FATEEYZAH NOVEL*
*REAL FA'EEZAH NOVEL*
*MUM IRFAAN NOVEL*
*OUM RAMADAN FANS CLUB*
*WUTA DA AUDUGA FANS*
*KUNDIN HIKIMA WRITERS*
ina godiya daa irin kaunar da kuka nunamin, sai mun hadu bayan sallah a sabon littafina mai suna *DOCTOR* *ZAHRAH* 💉💊,Allah yasa ayi Azumi lafiya.





*Comment*
*Like*
*Vote*
*Share*


*Fatima Zahra Muhammadu sani*
*(Fateeyzah)* ✍



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment