Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zanyi amfani wurin baka hakuri ba,amma don Allah ina rokon ka ka yafe mini ko na samu sassauci acikin Zuciyata ba,domin wallah fushinka a gareni zai iya sa in shiga halin da yafi wanda na tsinci kaina kaina yanxu a ciki,wallahi nayi nadama ji nake na tsani kaina tunda har zan iya saba ma mahaliccina,sannan kuma na yaudari mijina wurin zubar mai da jininshi"na karashe magana hade da fashewa da kuka.

Hannu yasa ya sharemin hawaye tare da sauke numfashi yana fadin"komai ya wuce Bahijjah amma ki sani abinda kikayi ya fara sani shakku akan kina sona kuwa,don da kina sona da baki yadda an baki maganin da kika zubar min da jinina ba,amma innayi la'akari da auren hadi aka mana,sai inga kamar an miki dolene wurin aurena,saboda tun kafin auremu ban taba ji kin bude baki kin fada min kalmar I LOVE YOU a bakiba koda bata kai ZUCIYA ba"

Nayi saurin cewa"Wallahi yaya ina sonka,sharrin shedan ne kawai hade da zugin su Aunty".

Yace.shikenan ya wuce sai ki kiyaye gaba sannan ki dukufa wurin rokon Allah yafiyar abinda kika aikata,sanna daga yau bake ba Aunty Amina ban yadda ki ringa shiga dakinta ba ko wata magana ta hadaku mai tsawo,abunda na yarje miki shine yimata sallama ko gaisuwa".

Nace.insha Allah zaka sameni da bin umurninka".

Kamoni yayi yai hugging dina tare da fadin"shikenan Allah ya miki Albarka,amma ya kamata a canza mun suna daga Yaya ya koma Sweetheart ko baby,tunda yau dai an tabbatar mun da ana sona".

Sunne kai nayi ina dariya,a wannan daren yaya Tasi'u (aw😷sweetheart) ya nuna mini soyayya don hatta wanka sai da yamin kafin mu kwanta.
Sai da ya kara kwana biyu tukunna ya koma Lagos ya barni da kewa.

Tunda ga abunda ya faru,sai ya zamana ko na gaida Aunty Amina bata amsawa ,yaranta ma basa shiga harkata,sai ya kasance ina zaman kadaici a gidan don itama Aunty Zeena ta samu admission a A.B.U,yaran Aunty Amina kuma in suka tafi school tun safe sai yamma.
Da naga zaman ya fara isata sai na fara zuwa gidan Alhaji in a rage wuni,nan ma a rana ta hudu Alhaji ya koroni yace na cika yawo,bayan nan Kuma su Aliyu suka fara zuwa suna tayani hira in sun dawo makaranta,nan kuma Aunty Amina tace in sunzo wai suna mata rashin kunya basu gaisheta,daga nan Alhaji ya hanasu zuwa.




Bayan shekara biyar,A lokacin inada 'ya'ya biyu duka mata, Amina(Iman) da maryam(Ilham) da kuma cikin na uku.

A lokacin da cikina ya kai wata takwas ne mai afkuwa ta afku, abinda ya faru shine ana sauran kwana biyu sallah Daddyn su Iman ya dawo daga Lagos, sai na dafamai ruwan wanka na kai bathroom,nashiga daki in dauko sabulu, kawai ina fitowa sai naga Aunty Amina ta zubar da ruwan ta jefo min bucket dina waje, ni kuma naga bazan iya daurewa ba sai na tambayeta dalilinta nayin haka, budar bakinta kawai sai ta cemun gani tayi wanda aka kai ruwan dominshi ba gidan ubanshi bane, ni kuma kawai da abun ya bata mun rai sai nace mata shima naga wannan mai jan GOLF(Mijinta) din ba gidan ubansa bane, ina fadin haka na shige kitchen domin in kara dafa wani ruwan, kawai sai jinayi an rufeni da duka da wata zabgegiyar bulala, ihun dana kwala shi ya fito da Daddyn su Iman, yana fitowa yaga abunda yake faruwa bai yi wata² ba ya tsinketa da mari, shikuma dai² Yaya Farooq ya fito shi da Aunty Zeena, yana karasowa baiyi wata² ba ya tsinke Daddyn sun Iman, nan suka kaure da dambe, kasancewa training din soja daban yake haka, haka Yaya Farooq yaringa kwala Daddyn su Iman da kasa,ganin yana niyyar yin kisa yasa na fita GIDAN da gudu ina neman taimako,ina fita nayi kicibus da Alhaji zai shiga masallaci,ganin yanayin yanda na futo ne yasashi tambayata lafiya, kasa bashi amsa nayi,sai dai nuna mai cikin gida nayi da hannu,a dai² lokacin ne mukaji an saki wani ihu, da gudu muka karasa cikin gida,muna zuwa na tarar da Daddyn su Iman a kwance baya motsi da gudu na karasa wurinshi ina jijjigashi ina kuka,amma kwata² bai motsa ba nan na kwala ihu tare da faduwa kasa tim........

Alqur'an na gaji da typing🤪




*Comment*
*Like*
*Vote*
*Share*











*_Fateeyzah_*✍




*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*


*GIDAN NAGOGGO*🏨
*_(A true life story)_*


*Written by fateeyzah*😍😍

*_Jinjina gareki sharifat niamey,Allah yabar kauna❤_*


*_Allah ina rokonka ka*_ *_kara daukaka*_ *HIKIMA WRITERS* *ASSOCIATION* , *_ka_* *_karemu daga sharrin mahassada_*.


*_Bismillahir rahmanir rahim_*


*_Page_* *_1⃣6⃣to2⃣0⃣_*



Tunda na fadi bana cikin hayyacina sai washe garin ranar na farka na ganni a Asibiti, shafa cikina danayi ne naji ba komai yasa hankalina tashi, nayita kokarin mikewa amma na kasa.

Nakai kusan minti goma da farkawa amma ba wanda ya shigo dakin, hakan yasa ni cikin tunani, don zuciyata cike take da tambayoyi, wanda na rasa wanda zai amsamin.

Turo Kofan da akayine yasa ni maida hankalina wurin don ganin mai shigowa,ganinsu Aunty Asma'u da Daddynsu Iman ne yasa wani farin ciki ya lullubeni, don ganinshi danayine ya tabbatar mun yana raye, karasowa wurina sukayi tare da tambayata ya jiki, a hankali na amsa idona akanshi Saboda ganin fuskarshi da bandeji, ganin haka yasa Aunty Asma'u ta juya tafita, ganin fitar tane yasa shi karasowa bakin gadon ya zauna.

Kallonshi nayi hade da tambayarshi me ya samu cikin jikina,anan yake fadamin kasancewa wurin faduwa cikina Yaya bugu,shine aka min C.S aka ciremin babyn,amma sun sata a Incubator (kwalba) saboda watanta bakwai ne da sati biyu.


*_A gurguje_*

Satina hudu a Asibiti tukunna aka sallamoni da ni da Jaririyata wadda taci sunan mamar Daddynsu wato rukayya(ruhaima), duk cikar dakin Ummy ba wanda yazo dubani, haka ma dana dawo,Su Aunty Hanna ne kawai da Aunty Fatima suka zo dubani,amma Aunty Amina ko lekowa batayi ba domin ta min barka sabanin haihuwar su Ilham da duk da bama magana tana min barka,Ammyna ma bata zo ba sai dai ta sanar dani Alhaji ne ya hanata Zuwa.

Kwananmu biyu da dawo wa Alhaji yazo gidan,a lokacin Daddyn Iman na nan, dukkanmu ya tara mu a dakin Yaya Farooq,anan ya yanke hukuncin akan Daddynsu Iman ya dena shigo mai gida,Amma ni bazai iya cewa in bar gida ba,sai dai in zai ganni,ya ringa zuwa bakin GIDAN ya kirani,in kuma ya na ganin ba haka ba ya tattara ni yaje ya kama min haya,sannan ya min kashedu in zan je Gidanshi kar in yadda in shigo mai da Jinin Tasi'u,hakanan Alh ya kakkabe Rigarshi ya kara gaba,ba tare da ya saurari ban hakurin da muke yiba.

Aunty Amina ko kamar ta zuba ruwa a kasa tasha na wannan hukuncin da Alh ya yanke,sabanin Yaya Farooq da jikinsa yayi sanyi.

Haka Daddynsu Iman ya shirya kayansa tare da diremin ATM card dinsa ya wuce Kudan tare da min Alkawarin zaije yayi shawara da Iyayensa don samun mana mafita.

Bayan tafiyarshi da kwana biyu ya kirani ya sanar dani zai wuce lagos,don sunyi shawara da iyayenshi akan ya barni anan kafin ya karasa gininshi (kasancewa yana gini a kaduna).

A wannan zaman da nayi ba karamin bakin ciki nake kunsa ba,don Aunty Amina bata da aiki sai na yada min da habaici, saukin tama Iman ta girma,don da ita nake hira in bata je school ba.

Ruhaima nada wata hudu akayi bikin Yaya Ibrahim da ya auro matarshi daga Abuja,bikin ba karamin kashe kudi akayi ba,inda har mutanen unguwa suka fara tambayar aikin da Yaya Ibrahim din yakeyi,anan naji Aunty Hanna na cewa wai Yaya Aminu ne ya daukeshi suna hakar Gold,nan ma sai da suka yita sakin habaici na sunyi mana fintinkau bamu da yanda zamuyi,shima dai Alhaji ya bashi Gida anan unguwar.

Bayan bikin ne da sati uku, Daddynsu Iman ya kirani akan in shirya kayan mu don zai zo ya tafi damu kasancewa ya samu scholarship na yin M.sc a Dubai kuma damu zai tafi don harda Gida aka bashi acan.

A ranar ne kuma *GIDAN* *NAGOGGO* suka tashi da wani tashin hankali inda aka kama Yaya Ibrahim dalilin satar motar da yayi ta wasu 'yan India da suke yi ma Yaya Aminu Aiki, wanda kafin wani lokaci maganar ta zagaye unguwa,ranar dai su Ummy sun shiga tashin hankali ni kuwa ko a kwalar rigata,don a ganina Alhakinmu ne ya fara kamasu,don ko Jaje ban ma kowa cikinsu ba,anan dai su Alhaji,Yaya Baffa da Yaya Farooq sukayita ciku² har sai da suka fito dashi, sannan Alhaji ba wani mataki da ya dauka akan hakan,sai ma fushi dayayi akan abunda Yaya Aminu yayi na kama Yaya Ibrahim din da yasa akayi.

Wani satin na zagayowa, Daddynsu Iman yazo ya kwashe mu kuka tafi Kudan,kwanan mu biyu anan muka wuce lagos inda zamu yi sati biyu kafin mu wuce Dubai.

Satin mu daya sai ga kiran Yaya Farooq,ina dauka ya fara duramin zagi akan tunda na zabi mijina akan su in zo in kwashe kayana daga Gidan,bai jira cewa naba ya kashe wayar, hankalina ba karamin tashi yayi ba da jin zancensa,dialing din Number Yaya Farooq nayi amma yayi rejecting,nan na fashe da kuka,sai da naci kukana na gaji sannan na yanke Hukuncin kiran Aunty Asma'u.

Bayan na kira Aunty Asma'u ne take sanar dani yanxu suka gama meeting a kaina anan Gidan Alhaji,ana take fadinmin wai sarki ne da Mahaifin Tasi'u suka zo bama Alhaji Hakuri akan matsalar dasuka samu da Tasi'u,shine bayan sun gama tattaunawa ya dauki waya ya kira Tasi'u yace mai ya samu lokaci kafin mu tafi Dubai yazo a musu sulhi da Alhaji,shine shi kuma baisan wayar a speaker take ba yace wai ai a share Alhaji da 'ya'yansa duk munafikai ne(wannan shine ruguntsimi), anan Alhaji yace to ya sakanmai 'yarsa,shine yace ai tun da abin ya faru yaso sakina,amma na roke shi ya rufamin asiri kar ya sakeni saboda bazan iya zaman Gidan Alhaji ba.

Tana gama min wanna bayanin naji zufa tana keto min,na rasa a inda zan sa kaina,don Alhaji shima sai da ya kirani yace kar in kuma zuwa mai Gida in dai akwai Auren Tasi'u a kaina.

Ruguntsimi kenan🤔,
Shin Bahijjah zata bi maganar ko kuma zata bi Tasi'u domin tafiya Dubai?.

Amshoshin tambayar nan zata zo a page na gaba,wanda anan ne zamu ci gaba da Asalin labarin.


Ayi hakuri da Errors saboda banyi Editing ba.



Kar ku manta comment dinking,shine karfin gwiwa ta.







*Comment*
*Like*
*Vote*
*Share*







*Fateeyzah* ✍



*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*


*GIDAN NAGOGGO*🏨
*_(A true life story)_*



*_Written by fateeyzah_*😍😍

*GIDAN NAGOGGO FANS*
*Mmn Abdoulaziz*
*Queen candy*
*Hassinat Muhammad*
*Fadiey*
*Rabi'atu Y*
*Sharifat niamey*
*Saudah*
*Fa'iza Auwal*
' *yar Asalee*
*Zainab zee*
*Fatima imilan*
*Maman farhiyya*
*Munlex*
*Hafsat s bello(maman fadila)*
*Meerah*
*Adizatou zanna*
*Ummu farha*
*Amina Sufi usman*
*Maman safwan*
*Nazma*
*Maryam*
*Zabba'u Abdulrahman*
*Mrs Annur*
*Mrs Yarima*
*Maman Deeja*
*Aisha jibril(Aj)*
*Innah sharrif* , *da sauran wadanda baku ji sunanku(sorry sai next page) dukkanku barka da jumma'a,ina jin dadin comment dinku,ina godiya.*

*jinjina gareku 'ya'yana fadila,khaleefa,Affan Allah ya raya minnku*



*_Bismillahir rahmanir rahim_*


*_Page2⃣1⃣to2⃣5⃣_*

A ranar haka na wuni cikin tashin hankali,don ko girkin dare na kasa daurawa, sai dai cornflakes na hada ma su Iman suka sha sannan sukayi bacci, niko ko ruwa na kasa sawa a bakina , haka nayi ta zaman jiran Tasi'u ya dawo saboda nata kiran phone dinshi amma baya dauka daga baya ma sai ya kashe wayar.

Sai wurin karfe sha biyu tukunna ya shigo gida alokacin har na fara gyangyadi don karar rufe kofar shi ne ya tasheni, kallon da na watsa mai ya sa jikinshi sanyi da jan kafa ya karaso wurina hade da fadin"bahijjah mai ya faru, tunda nake da ke ban taba ganin kin min mafificin wannan kallon ba".

Na kalleshi fuskata cike tab da hawaye nace"dole kace haka mana, tunda kasan abun da kayi,haba Daddynsu Iman koda Alhaji sa wuka yake yana yankan naman jikinka ai bai kamaci zagi a wurinka, ko ba ka aurena ai akwai dangantaka ta jini, amma wai har kai zaka iya bude baki ka kira Alhaji munafiki, aiko kaga ka cancanki wannan kallon daga gare ni " na karashe magana ina goge hawayen dake fuskata.

Riko hannuna yayi tare da fadin"wallahi Bahijjah ba abunda ya faru kenan ba, nasan dai Alhajinmu ya kirani yace mun shi da sarki sunzo sun samu Alhaji sun bashi hakuri akan abunda ya faru, shine Alhaji yace yana bukatar inzo saboda akwai maganar da yake so yayi a gabana shine fa nacemai bazan samu zuwa ba saboda ina shirye shiryen tafiyar mune, to kinji yanda muka yi dasu,kawai kuma sai ga Yaya Baffa ya kirani yanata zagina wai na zagi Alhaji, tunda bansan mutunci ba in sakeki, ni kuma nace mai ina sonki ne shi yasa ban sakeki ba, amma da bana sanki da ba mu kai wannan lokacin a tare ba".

Ajiyar zuciya na saki tare da fadin"kar kaga laifina hatta Aunty Asma'u abunda ta fada min kenan, amma me yasa da na kira wayarka ba ka dauka ba daga baya kuma ka kashe wayar gabaki daya"na karashe da tambayarsa.

Sakin hannuna yayi sannan yace"wallahi sanda kika kirani ina meeting ne kasancewa yau nayi handing din komai ga sabon manager da aka kawo".

Hausawa nace wa tsakanin miji da mata sai Allah,a wannan dare muka shirya da ni da Tasi'u don ni aganina abunda ya fada min shine gaskiya sabanin abunda Alhaji da sauran ' yan uwana suka ce.

Sati na zagayowa,jirgin mu ya tashi zuwa Babban birnin Dubai wato Abu Dabi city, zaman mu a Dubai zama ne mai cike da FREEDOM hade da jin dadi,banda wani tashin hankali ko fargaba, don duk na manta da wani tashin hankali a Nigeria,don daga Ammy sai Aunty Asma'u kawai nake waya don nasan ko na kira Alhaji dauka zaiyi ba.

Kasance wa in Daddynsu Iman ya tafi school sai yamma yake dawowa,sai ya neman ma Iman da Ilham school acan,inda akasa Iman a nursery two,Ilham kuma a pre nursery,ni kuma sai ya neman mu wani school na fashion designers, wanda anan na koyi yanda ake dinka jallabiya da veil.

Shekara mu daya da wata biyu acan muka tattaro muka dawo Nigeria inda muka sauka a Lagos,kwanan mu biyu muka yo Arewa inda Daddynsu ya ijiyemu a zaria shi ya wuce kudan.

Wurin karfe biyar keke napep ya sauke mu a bakin gate din Gidan Alhaji,nan na nemu Almajirai suka daukar mun trolleys dina suka shigan mun dasu gidan,ni kuma na biyar mai keke napep kudinsa na kama hannun yarana muka shiga ciki.

Muna kusa kai Gidan,naga Almajiran da na bama kayana na tsaye a farfajiyar Gidan,gefe daya kuma ga Alhaji,Ummy,Ammy da wasu daga cikin yaran Gidan a tsaye,ganin irin kallon da Alhaji yake watsamin ne yasa na kasa ci gaba da tawo wa,nuna ni yayi da dan yatsa tare da fadin "kar ki kuskura ki karaso wurinnan in baso kike na bata miki rai ba,ai dama an fadamun kin dawo,shiyasa na kasa na tsare don nasan dole zakizo, toh ki bude kunnan ki kiji wallahi bazaki shigo mun gida da auren Tasi'u akanki ba, inkin ga na kuma bari kin shigo gidannan to kinzo min da takardar sakine,don haka na baki minti buyu ki tattara kayanki da yaranki ku bar min Gida kuma kar ki sake inji kinje wani gidan dan uwa, sannan kayan dakinki na baki nan da sati daya kizo ki kwashe in ba haka zan zubar dasu a waje,kinji dai na fada miki"

San ya juya ga 'yan gidan tare da fadin" ku kuma ku wuce muje",haka ya tasa su a gaba suka shige cikin falonsa,ina gani Ammy idon ta cike da hawaye tana waiwayoni har suka shige.

Haka ina kuka muka fito Gidan inda nasamu keke napep na muka shiga, sannan na sallami almajiran na umurci Driver da ya kani motor park.

Muna hanya Ammy ta kirani tana kuka tana ban hakuri sannan ta ja mun kunne akan kar in sake in ce zan kashe aurena,don ko na dawo Gida bazan iya jin dadin zaman Gidan ba,don ita ma saboda Kannena take zaune, haka tayi ta bani shawarwari da nasiha, sannan muka ajiye waya.

Muna karasowa motor park na sallami mai keke napep na kama yarana muka hau motar Kudan,minkai minti goma sannan motar ta cika muka tashi,a hanya ma Aunty Asma'u ta kirani ta ringa bani hakuri tare damun kashedin kar in sake in kashe aurena.

Sai bayan magriba muka iya kudan,muna sauka na samu Almajirai suka daumin kayana muka kama hanyar Gidansu Tasi'u kasancewa babu nisa daga inda aka saukemu.

Muna isa, mukaci karo da Tasi'u a kofar Gida, da mamaki ya tare mu, ya amshi kayanmu kayanmu sannan na sallami Almajirai muka wuce cikin Gida,yana ijiye kayanmu ya fita domin yin sallar magariba,mu kuma muka shige dakin mahaifiyarsa(umma).

Bayan munyi sallah hade da cin abinci sannan Alhajinsu ya kirani zuwa falonshi,nan na tarar da Tasi'u da umma da Alhaji, bayan na gaisheda Alhaji sannan ya tambayeni abunda ya faru na tawo kudan bacin Tasi'u yace ya barni a zaria, nan na kwashe duk abunda ya faru na fadamai,nan ko ya fara fada ya dauki waya ya kira Alhaji, yana dauka ya fara surfa mai masifa kamar haka"wai kai *NAGOGGO* wani irin zuciya gare kane,an bak hakuri amma kaki hakura, ko Allah ana mai laifi kuma atuba, ballantana kai, to wallahi ka guje randa Allah zai kama ka saboda hakkin yarinyar nan kaji na fada maka,kuma insha Allahu auren Bahijjah da Tasi'u har mutuwa" yana kaiwa nan ya kashe wayar bai jira amsarshi ba.


Nan Alhaji ya shiga yi mini nasiha tare da kwantar min da hankali,sannan yace min zasuyi shawara da Tasi'u suji inda zamu zauna,ranar dai sai kusan asuba nayi bacci.

Kwanan mu biyu a Kudan,Tasi'u yazo ya sameni da murna yake cemin ya samu aiki a NNPC nanan Kaduna,nan mukai ta murna nan yace mun gobe zai je don sun kirashi,washegari ko yayi sammako ya tafi kaduna.
Sai bayan magariba ya dawo,bayan ya yi sallah yaci abinci yake cemin sunce ranar monday zai fara aiki saboda haka yayi shawara da Alhajinsu akan sai kama mana haya a kaduna kafin ya gama nashi ginin,nanko naji farinciki ya rufeni, don ko ba komai kafi sakata ka wala anaka dakin.

Acikin sati naje na kwashe kayana a Gidan Alhaji, tukunna muka wuce kaduna inda ya kama mana haya a Kinkinau, gida ne mai dauke da Flat biyu kowanne flat yanada 2bedrooms, kitchen, toilet da store.

A farkon zaman mu, muna zaune ba tare da wata matsala ba,haka ma makociyata wacce take dayan flat din itama bata da matsala.

Matsalar dana fara facing daga Tasi'u shined dana samu ciki, sai ya nemi in zubar da cikin wai saboda shi yara uku sun isheshi, ni kuma naki yadda,nan fa yafara min rashin mutunci hade da gori, sai ya kunle store ya tafi da mukullinshi sai dai makociyata ta bani,su Iman dama ya sasu a makaranta insuka tafi tun safe sai la'asar sai ya zamana in yaje daukosu sai ya biya dasu ta restaurant suci abinci,da daddare kuma sai ya dafa musu indome ko ya siyo musu snack su ci nikuwa bai damuba, haka ya raba daki dani ya zamana yana kwana da 'ya'yansa.


Ranar da bazan manta da itaba,itace ranar wata babbar salla alokacin cikina wata shidda, sai na sami Tasi'u don in tunatar dashi hakkina daya danne,aiko na ya balbaleni da masifa har da cemun dama halin 'yan gidan mune rashin kunya ni kuma da abun ya ban haushi sai nace mai ai munfi 'yan gidansu da suke maneman mata,aiko nan ya tsinke ni da mari yaci gaba da zagina nima ina ramawa,aiko da ya gaji sai naga ya shiga daki sai gashi ya fito da farar takarda ya mikomin........
'ka'ka'kara 'kara, sai mun hadu a next page.



Kuyi hakuri na gaji banyi Editing ba.






*Comment*
*Like*
*Vote*
*Share*






*_Fateeyzah_*✍




*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*( _Home of peace,joint of entertainment,to educate and enlighten our readers)_*



*GIDAN NAGOGGO*🏨
*_(A true life story)_*


*_Written by fateeyzah_*😍😍




*_Bismillahir rahmanir rahim_*



*_Page2⃣6⃣to3⃣0⃣_*

Mika min takardar yayi tare da fadin "gashinan sai a kara gaba,ki tafi gidan masu tarbiya wadanda basa neman mata"yana gama fadin haka ya dauki key din motar shi ya fita.

Take kukan da nakeyi na nemeshi na rasa, jinayi kamar in hadiye zuciya in mutum, aranar na tabbatar da namiji badan goyo bane duk wanda ta maidashi uba zata mutu marainiya, a ranar na kuma tabbatar da namiji ko service din MTN ya fishi guarantee, sannan alokacin nadama ta kamani na yanda na fifita mijina akan ubana, na zabi in zauna da mijina akan mahaifina,a wannan lokacin nayi danasani da naki bin maganar Alhaji,aganina duk wulakancin da yamini da hana ni abinci bai isheni ba har sai daya hada ni da saki a lokacin danafi bukatarsa,sannan nayi danasani na rashin sanar da Ammy da Aunty Asma'u halin da na ke ciki, don ko Granny da muke gari daya karya na mata nace cikin yazo mun da matsala shi yasa bana zuwa gaisheta wanda kuma saboda rashin kudin mota ne dalilin, ita kuma ba kafa ba ballantana tazo.

Nakai kusan awa biyu a inda ya tafi yabarni,ba komai nake tunani ba sai rashin sanin abin yi,da rashin sani wanda zan fada ma maganar nan,ganin shigowar Humaira (makociyata) ne ya bani kwarin gwiwar tashi na nufeta nayi hugging dinta sannan na fashe da kuka, cikin rikicewa take tambayata mai ya faru ,kasa bata amsa nayi sai zame jikina danayi daga jikinta na nufi inda na tashi na dauko takardar na mika mata, karba tayi cikin mutuwar jiki ta warware takaddar,cikin sanyin jiki tace "inalillahi wa'inaillahir raji'un maman Iman saki har biyu", cikin azama na karfi takardar daga hannunta na kai duba cikin takardar ba komai na fahimta acikin takardar ba sai layi biyu da na iya kai duba na kai wati inda ya rubuta
_Ni Tasi'u Ibrahim Kudan na saki matata Bahijjah Ahmad Nagoggo saki biyu_...........nan naji wani irin jiri ya debe ni da sauri na dafe hannu kujera ana Humaira ta karaso wurina ta taimaka min na zauna.

Mun kai minti talatin ba tare da mun furta komai ba don kowannan mu yayi nisa cikin tunani, humaira ta fara janne shirun tare da fadin"Maman Ihsan ya kamata ace kin sanar da gida halin da ake ciki"

Sai da na dau dan lokaci tukunna nace "haka ne humaira amma kinfi kowa sanin halin dana ke ciki,ni wayata babu ko sisi".
"Bari in dauko wayata akwai credit"ta karashe maganar tana ficewa.

Cikin minti biyar sai gashi ta dawo ta mikamin wayar tare da juyawa ta fita, jikina na rawa haka na fara dialing din Number Ammy sai da tayi ringing so uku tukunna ta dauka tare da yin sallama, cikin Muryar kuka na fara magana"Ammy ya sakeni ba tare da nayi mai komai ba".
Salati tayi tare da fadin"Bahijjah kikace ya sakeki?, mai kika masa?, dama baku zaman lafiya ne kika boyemu?,oh ni Amina wani irin abune wannan ka saki matar ka ranar sallah".
Jin wadannan tambayoyi daga bakin Ammy yasa hankalina yakuma tashi, nan na zayyane mata abunda ya faru tun daga daukar cikina har zuwa sakin daya mini, nan Ammy ta kuma zabga salati tare da fadin"Bahijjah kina da hankali kuwa,duk wadannan abun na faruwa amma kika kasa sanar da kowa".

Nace"Ammy don Allah kiyi hakuri wallahi banson ya zamana ko yaushe ni nake daga miki hankali,kuma kinga kema kina ji da kanki, ga matsalar nan gidan, shiyasa naga bai kamata in kara miki wata damuwar ba"

"To yanxu ina su Iman din" Ammy ta tambaya

Nace"inaga ya kaisu Kudan ne,saboda naga ya hada musu kaya".

"Bari yanxu xan kira Asma'u muji yanda za a yi, don gaskiya bansan yanda zan tunkari Alhaji da wannan maganar" haka mukai sallama da Ammy na kashe wayar.

Can wurin karfe biyar na ranar sai ga sallamar Yaya Baffa,Yaya Farooq da Aunty Asma'u, suna shigowa Yaya Baffa ya umurceni da intashi in hada kayana inzo mu wuce, cikin rawar jiki na shiga daki dan

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment