Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka Hajiya ta karaso ko zama batayi ba ta fara surfa bala'i,sai da ta zage kowa tas,sannan tace duk ranar da wani ya kuma dukana koda Ammy ce bata yafe ba, tace ma yaya Farooq ya biyota gida, ta fice daga gidan.
Haka Ammy ta dafa ruwan zafi ruwan zafi ta Gasa mun jiki,sannan nasha ruwan Lipton da paracetamol na kwanta.basan ya aka kare ba tsakanin Hajiya da yaya Farooq,na ga dai da safe Ummy ta hada kaya ta tafi kano da sunan yaji(abun kunya tsofai2 da ita).









*Fateeyzah* πŸ–ŠπŸ–Š




*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*( _Burunmu mu fad'akar, mu nishad'antar, mu wa'azantar da al'umma)_*



*GIDAN NAGOGGO*🏨

*_A true life story_*


*_Written by fateeyzah_*😍😍


*_Wannan page din Nakune_ HIKIMA WRITERS _Allah ya kara basira da daukaka_*



*Bismillahir rahmanir rahim*


_Page_ 0⃣9⃣&1⃣0⃣

Haka su Alhaji suka tafi suka bar Yaya Farooq,saboda bashi da manyan kayan da zai saka, kasancewa duk kayansa Jeans ne da T_shirt ne.

Kwana biyu na dauka ina jinyar jikina saboda ba karamar illa Yaya Farooq yamin ba,godiyar Allah ma weekends ne babu school.

Sai da Ummy tayi sati daya tukunna Mahaifinta ya dawo da ita,don ba yanda Ammy batayi da Alhaji ba akan yayo bikonta,shikuma ya dage bazai jeba tunda bashi yace ta tafi ba, ita ta tafi da kanta,gaskiya a cikin satin da Ummy tayi bata gidan ba karamin wata yawa mukayi ba,su kuma 'ya'yanta ina lura duk a takure suke.

Bayan Wata biyu,Yaya Farooq ya samu soja ya tafi,a lokacin ba karamin dadi naji ba don na lura duk cikin yaran Ummy yafi kowa tsanata,A dai dai lokacine kuma Tasi'u ya samu admission a A.B.U zaria(Tasi'u kani yake wurin Alhaji don da Babanshi da kakanmu Alh Akilu 'Ya'yan mata suke),anan Gidan Hajiya Kaka aka Bashi daki,kasancewa duk 'yan uwan da yazo karatu daga Kudan Gidan Hajiya Kaka suke zama har su gama,daki guda ake ware musu kusa da dakin Aunty Amina(inba ku mantaba itace babbar 'ya wurin Alhaji kuma ita ke auren Babban d'an Hajiyar Sokoto,Yaya Kabeer,kasance wa auren Zumunci ne sai Alhaji ya basu daki anan gidan Hajiya),shima nan Tasi'u ya zauna, wanda ni nake kaimai abinci Don Alhaji yace kwanonshi yana dakin Ammy ne.


A wannan shekarar abubuwa sun faru da yawa,ciki harda aurar dasu Aunty Asma'u,Aunty Fatima da Aunty Khadija,wanda Aunty Asma'u ta auri Suleiman(Yaron Alhaji ne da yake jamai Trailer Zuwa Lagos),aka kaita dan gaba da Gidanmi don nan Mijinta ya gina gida,Aunty Fatima kuwa ta auri Salihu,shikuma yana aiki ne a Embassy na Egypt,Ita kuma Anguwan k'aya aka kaita kafin su wuce can Egypt din,Aunty Khadija kuma auren zumunci aka mata da Yaya Al'amin ('yan Hajiyar Sokoto)can Sokoto aka ajiyeta Gidan Hajiya.

Bayan Bikinsu ne kuma da Wata Biyu,Allah yayi wa Hajiya Kaka rasuwa(Allah ya jikanta),Rasuwarta ta girgiza mu especially 'yan dakinmu da'ya'yan Hajiyar Sokoto(duk ita ta rikesu,su biyar,har aurensu),aka raba gado,kowa ya watse.

Bayan wasu watanni aka yi passing out don Yaya Farooq,wanda ya fito da mikamin second Lieutenant,Anyi POP da sati biyu aka daura mishi aure da Aunty Zeenatu,shi ma dai auren zumunci ne don da Babanta da Alhaji cousin ne,wannan bikin ne akayi biki da ba a taba yi a *GIDAN NAGOGGO* ba,don sai da akayi event kusan hudu da kuma crossing of sword,tukunna aka dauko Amarya daga Kaduna aka kawo ta nan Gidan Hajiya Kaka(ta gaban gidan Alhaji ya fitar mai da part dinsa kuma yace ya mallakamai wurin).


Haka rayuwa taci gaba da tafiya watarana Farin ciki ko bakin ciki,wanda bakin cikin yafi yawa.Acikin Shekarun nan an hayayyafa sannan anyi Rashi,wanda har da Alhaji Kaka da Allah ya mai rasuwa.

Acikin shekarar da na gama School,Abubuwa marasa kyau sun faru,daga ciki akwai Rikicin da ya faru tsakanin mijin Aunty Asma'u da Alhaji,inda Alhaji yace yana cutarshi bai kawo mai balance da yawa,shi kuma yace motor na bashi matsala,kudin na Tafiya a gyaran motor,Haka Alhaji ya rufe idoshi ya karta mai rashin mutunci kamar ba Sirikinshi ba,kuma daga baya ya karbe motarsa,Dalilin haka har auren Aunty Asma'u ya kusa mutuwa,Allah dai ya taimaka suka samu masalah.
Yaya Al'amin Mijin Aunty Khadija kuma ya kara aure,inda suka yi ta samun matsala tsakaninsu,har dai ya saketa,ita kuma ta aje mai Jariri dan wata biyu ta tawo Gida,ba tare da Alhaji ya tsaya yabi ba'asi ba yace ta fitar mai gida Bashii bata,kuma yace in Yaya Al'amin ya maida ita gidanshi,shima sun raba Hanya kuma sai ya tsine mata, ya kuma hana a bata d'anta haka Alhaji ya raba Jariri d'an wata biyu,haka tattara ta koma Dagin Mahaifiyarta.
A shekarar ne kuma Tasi'u ya gama degree ya tafi services,ni kuma na ci gaba da zaman gida,saboda Alhaji baya bari mu shiga university sai munyi aure,shima sai mijinki ya barki.Haka na kara wata shekara a gida ba tare da na samu miji ba,don Alhaji ba bari yake in fita ba.

Bayan Tasi'u ya gama service ne ya samu aiki a wani filling station a Lagos,wanda aka bashi matsayin manager,a lokacine Sarki (sarkin kudan) yace yazo gidan mu ya zabi mata,yana zuwa aka tura mu wurinshi ni da Halima muka gaisheshi,bayan ya tafi ne yaje ya sanar da sarki ya zabeni,shikuma ya Sanar da Alhaji,nan ko Halima tayi ta murna don dama ita da wanda take so,nan muka fara soyayya da Tasi'u ba a dauki dogon lokaci ba aka daura mani aure dashi,Halima kuma da Salis saurayinta.
Nan Alhaji yace tunda ba dani zai tafi Lagos ba, ba sai ya kama hayaba,nan muma ya bamu daki a gidan Hajiya Kaka.




Ya zaman zai kasance tsakaninmu:
Aunty Amina
Yaya Farooq(abokin fadana)
Ga kuma ni Bahijjah.
Karku manta dukkanmu 'ya'yan Alhaji NAGOGGO ne,sai mun hadu a next page.







*Comment*
*Vote*
*Like*
*Share*






*Fateeyzah* πŸ–Š



*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_(Burinmu mu fad'akar,mu nishad'antar,mu wa'azantar da al'umma)_*


*GIDAN NAGOGGO*🏨
*_( A true life story)_*



*_Written by fateeyzah*😍_

_Bismillahir rahmanir rahim_

*_Page_* 1⃣1⃣


Tunda aka daura aurena na tsinci kaina a cikin farin cikin samu FREEDOM,ta wani 'bangaren ina bakin cikin rabuwa da Ammy da Kannina.
Ammy ko tana can bedroom tana Kukan tausayina,don a ganinta ba a rabu da bukar bane an samu habu,domin an aurar da nine,amma har yanxu ban bar *GIDAN* *NAGOGGO* ba.

Karfe hudu nayi Alhaji ya umurci su Yaya Amina a fara shirya Amare domin karfe biyar yake so kowacce ya danka ma mijinta(yana daga cikin Al'adar *GIDAN* *NAGOGGO*,duk yarinyar da aka ma aure Alhaji dakanshi zai kai ki dakin miji,zai hadaki da kanniki maza sune 'yan rakiya).

Bayan an gama shiryamu ne aka fara kaimu wurin Ummy don yi mana fada,daga nan kuma aka wuce damu dakin Ammy,nan ma dai fadan ta mana,sannan aka wuce damu palourn Alhaji,gyaran murya Alhaji yayi tare da kiran sunanmu"Halima,Bahijja"bai jira amsawarmu ba yaci gaba"Allah ya kawo mu yau na sauke nauyinku da ya rataya akaina,ba wata doguwar magana zanyi ba,don nasan duk abunda zan fadi,iyayenku mata da 'yan uwa sun fada muku,abinda zan tunatar daku kusan Gidan nan ba a yaji(barkonoπŸ€ͺ),duk abunda ya hada ku da mazagenku Ku ringa hakuri ba wai ku kwaso 'kafa ku tawo gida,don bazan dauka ba,sannan ke Bahijja(ya nuno ni da yatsa)ki kiyayeni wallahi in naji ance kiyi ma Amina ko Zeenatu wata rashin kunya wallahi zanyi mummunar sa'ba miki,kibar ganin wai yanxu da aurenki,zan iya zuwa har dakinki in zane ki,don Amina ya isa ta haifeki,kina da shekara biyu a duniya aka mata aure,don haka ki kiyaye,ku tashi muje Allah ya muku Albarka,yasa ku shiga dakin miji a sa'a.

Halima muka fara kaiwa gidan ta dake Tudun wada kasancewa ita ce karama,muna zuwa Alhaji ya kira mijinta a waya,ya damka mai matarshi,sannan muka juyo muka dawo,Alhaji da kanshi ya rike mun hannu ya kaini har cikin dakina,sannan ya tafi ya barni,bude idona nayi na kare ma dakin kallo,ba laifi,Dakin ya tsaru.Gab da Sallar magariba sai ga su Aunty mamy, Aunty Amina,Aunty Zeena da Aunty Asma'u sunzo,suka kara gyara dakin,sannan suka sani inyi wanka, in dauro Alwala,anan ne nace musu banda tsarki sai zuwa gobe zanyi wanka,Nan Aunty Mamy ta kwashe da tariya tare da fadin "lallai bahijjah kina ruwa".haka dai suka karasa gyaran daki tare
da mun 'yan nasihohi,suka mana bankwana ni da su Aunty Amina suka tafi.

Bayan sallar Isha'i Aunty Amina da Aunty Zeena suka mun sallama kawacce tayi dakinta.
Sai wurin karfe tara tukunna Tasi'u ya shigo,sai ya umurceni da in tashi muyi nafila,ina dan nokewa na Sanar dashi ban da tsarki,muka dan yi ciye ciyen mu muka kwanta.
Washe gari na wuni ina ta karban baki 'yan ganin amarya,wurin la'asar na yi tsarki,a daren ranar Tasi'u ya maidani cikakkiyar mace,wayewar garin ranar kuma yayi mini kyautar gold half set(half set shine dankunne,da sarka) kirar Dubai.

Zamana da Tasi'u sai dai san barka saboda bai rageni da komai ba yana kokarin kyautatamin dai dai gwargwado,yana gudun bacin raina.
Haka kuma zamana da Aunty Amina shima banda matsala haka 'ya'yanta na girmamani,don wani zubin har tunani nake yanda Aunty Amina take jana a jiki,amma ni duk da haka na kasa sakin jiki da ita saboda tun can dama ba wani sabo a tsakaninmu,saboda duk da muna Anguwa daya bata cika zuwa gida ba,kasancewarta nurse ce yawanci a Asibiti take wuni.
Ta bangaren Aunty Zeena ma banda matsala,saboda ita mutumce mai hakuri da kawaici,ni dama tunanina ko da zan samu matsalah,wai wuce ta Yaya Farooq ba,amma sai naci sa'a a week din da akayi bikinmu akayi masa transfer ya koma Ilorin da aiki.

A ranar da muka cika sati biyar da aurenmu,Tasi'u ya fara shirin komawa bakin aiki,Don washe gari da daddare yake so ya wuce,karfe takwas ya umurceni da in shirya muje mu gaida Alhaji,aiko nayi ta murna don nayi kewar Ammyna don ma muna waya,cikin shigarmu ta alfarma muka kama hanyar zuwa gidan,direct parlourn Alhaji muka wuce,nan muka tarar da shi da Ummy,bayan mun gaisa,Tasi'u yake sanar da shi yazo mushi sallamane ,nan Alhaji ya sa mana albarka,daganan dakin Ammyna muka wuce,muna shiga na rungumeta ina murnar ganinta,sannan suka gaisa da Tasi'u,nan ma dai albarkar aka samana tare da mai fatan sauka Lafiya, tukunna muka taso muka tawo,bayan dawowarmu gidane ya shirya ya tafi Kudan.

Wajen karfe biyu sai ga Aunty Mamy da Aunty hauwa sunzo nan muka hadu dakin Aunty Amina (kasancewa night duty gare ta ranar)mukayi ta hira,cikin hirar ne Aunty Mamy ke tambayata wai anya ba ciki gareni ba,nayi saurin ce mata ni banda komai,sai ta kuma tambayata yaushe rabona da menstruation nace mata tun lokacin bikina,anan Aunty Amina tasa mana baki tare da fadin ai ita tun last week ta lura cikine dani,nan dai suka hadu su uku sukayi ta zugani kar in yarda in haihu da wuri,su bana ganin su basu da yara da yawa(Aunty Amina nada yara hudu,Aunty Hauwah uku,sai Aunty Mamy nada daya),nan da har na hau kai na zauna,nan Aunty Amina tace tana da Maganin da zata bani cikin ya zube tunda tasan bai wuce 4 weeks ba,a lokacin duk na manta kiyayyar da suke nuna mana mu da mahaifiyarmu,don gani nake banda masoya irin su(kar ku ga laifina,alokacin shekarata 18),nan Aunty Amina ta tambayeni yaushe Tasi'u zai dawo nace mata sai dare,tace ai ya isa cikin ya zube lokacin,haka tabani kwayar nan guda biyu tace in Hadiya da ruwa,take ko na sha magani.

Har kusan 2hours ba labari,nan dai su Aunty Mamy suka tafi suka barmu cikin jiran tsammani,in takaice muku har bayan isha babu bayani.
Wurin karfe tara sai ga Tasi'u ya dawo,nan dai nayi ma Aunty Amina sallama na nufi daki,gabana na dukan uku uku don ko girki banyiba,Allah ya taimakeni karin in kirkiri karyar da zanyi yace in dafo mai Lipton don bazai iya cin abinciba.

Around 10pm muna kwance sai naji wani azababban ciwon mara ya taso mun tun ina dauriya dai har na fara ihu,nan Tasi'u ya rikice yana tambayata mai ya sameni,kafin in bashi amsa sai ga jini na bin kafafuna.







Don jin ya zata kaya,sai mun hadu a next page.



*Comment*
*Vote*
*Like*
*Share*









*Fateeyzah* ✍



*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*



*GIDAN NAGOGGO*🏨
*_(A true life story)_*



*_Written by fateeyzah*😍_

_Wannan page din nakune masoyen *GIDAN* *NAGOGGO* a duk inda kuke,nagode da kaunar da kuke nuna ma novel dinnan._

_Bismillahir rahmanir rahim_


*_Page_* 1⃣2⃣


Ganin jinin na bin kafata yasa Tasi'u ya kara rikicewa,ihun dana kuma saki ne ya dawo dashi hayyacinsa,daukan key din motar yayi tare da sunkuta ta yayi waje dani,sa key yayi ya bude motar ya kwantar dani a back seat ,shiga driver seat yayi ya figi motar a guje,Da taimakon Allah muka isa ABUTH dake Tudun wada saboda reckless driving da yayi,yana parking ya kuma sunkuta ta da gudu ya shiga cikin Asibitin dani,da gudu nurses sukakarbeni a hannushi,daganan kuma ban san abunda ya faru ba sai farkawa nayi naganni daure da drip a hannuna,ga cikina ya na min wani matsiyacin ciwo,gefen damana kuma Tasi'u ne a zaune,wanda kallonshi da nayi sai da na shiga cikin firgice,don fuskarshi da idon shi yayi wani irin da alamun yasha kuka,juyin da cikina yayi shiyasani fasa ihu,da sauri ya juyo gareni,irin kallon daya watsa min shiyasa na manta da ciwon dana ke ciki,don in idona bai min karya tsanata na gani a idon Tasi'u.

Har gari ya waye,yana zaune a inda yake bai kuma kallon bangaren da nake ba ballantana insa
ran zai mun magana,ni kuma na kasa mai magana saboda wani tsoronsa da ya shigeni.

Sai around 7,tukunna naga ya tashi yana jan kafa ya fada toilet din dakin, sai da yayi kusan minti biyar tukunna ya fito da alamar alwala yayi,fita yayi daga dakin.
Zafin dana ji a hannuna ya dawo dani daga gajeran tunanin da na shiga,drip din dake hannuna ne ya kare har ya fara dawowa da jini,yunkirin tashi nayi amma na kasa.

Turo kofa akayi aka shigo,Tasi'u ne da doctor,da sauri suka karaso wurina ganin yanda jinine ke dawo cikin cedar,cire min drip din yayi tare da"sorry madam,bamu zo da wuriba".kada kai kawai nayi.
Wurin karfe takwas sai ga Aunty Asma'u tazo,lokacinne kuma naji Tasi'u yake mata sallama zai je ya dadi.
Tunda na kwanta Asibiti ba wanda yazo agidan sai Aunty Zeena,shima bata dadeba ta tafi,naso tambayar Aunty Asma'u datake jinyata Amma itama ba fuska,Tasi'u ko a Asibitin yake Wuni amma ko magana bata shi ya tsakaninmu don ko na masa bai amsawa.

Sai da na kwana biyar A Asibiti sannan akayi discharging dina,direct GIDAN Alhaji aka wuce dani,dakin Ammyna Auto Asma'u ta kaini nayi wanka,sannan muka je parlourn Alhaji wanda duk yaran gidan,masu aure,da marasa shi duk suna parlourn,ina hada ido da Ammy ta sakar mun harara,saurin dauke kaina nayi tare dajin wani takaici ya rufeni,har na samu wuri na zauna ba wanda yamun magana sai ido da kowa ya zuba min,Aunty Amina na hango zaune a gefe tayi tsiru tsiru,duk alamun rashin kwanciyar hankali ya bayyana a fuskarta.

Mun kusa minti goma da zama sai ga Alhaji da Tasi'u sun shigo,samun wuri sukayi suka zauna,sannan Alhaji ya dago Fuska a hade ya yaficeni da hannu,take cikina ya kada haka na tashi jikina a sanyaye,ina zuwa na tsugunna a gabanshi,baiyi wani jinkiri ba ya tsinkeni da mari ........






More comment,more typing





*Comment*
*Vote*
*Like*
*Share*






*Fateeyzah* ✍



*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*


*GIDAN NAGOGGO*🏨
*_(A true life story_)*


*_Written by fateeyzah_*😍😍


Wannan page din naki ne,Aminiyar kwarai,sahibata,is easiest to cut my hand than to loose u as a friend, *SOPHIE* *MUHAMMAD* *BUBA*πŸ‘©β€β€β€πŸ‘©πŸ‘©β€β€β€πŸ‘© (The potential banker and the financial analyst),Allah ya barmu tare har *CBN*(insha Allah),Allah kuma ya nuna min auranki da *ABDULJABBAR*❀

*Fateeyzah* *novel* *group* inaji dadin addu'ar ku ako da yaushe,ina godiyaπŸ™.

_Bismillahir rahmanir rahim_

*_Page_*1⃣3⃣.

Marin da yamun sai da yayi sanadiyar dauke war jinaπŸ‘‚ na wasu dakika alokacin da jina ya dawone,na tsinci Alhaji na magana cikin matsinancin fushi"wai bahijja yaushe zakiyi hankaline,wace irin dakikiya ce ke,duka duka shekarunki goma sha takwas a duniya amma har kin iya shan magani don ki zubar ciki(duka ' yan parlourn suka dau salati don yawancinsu basu sasan dalilin da Alhaji ya kira wannan meeting din gaggawar ba)sai da parlourn yayi shiru tukunna,sai nan Alhaji ya cigaba da bambami wanda ayanxu bazan iya tuna wa duka ba,ranar na sha zagi don Allah komawa yayi kamai wani bamaguje,sai da ya gaji don kansa sannan ya umurci Tasi'u yabani key din dakina in tashi in tafi don yana son magana dasu,haka na karfi key na tashi na fita hawaye na bin idona,haka na kama hanyar gida ba tare dana damu da kallon da mutane ke bina dashi ba.

Ina shiga gida na hadu da Aunty Zeena ta fito part dinta,ganin yanayin da nake ciki yasata karasowa da sauri tana tambaya ta mai ya faru,amma nakasa bude baki in bata amsa haka ta jani har part dinmu ta karfi key din hannuna ta budemin dakin muka shiga ta zaunar da ni akan two seater,direct fridge dina Ta nufa ta dauko min maltina mai sanyi ta bude min ta kafa min abaki,batare da bata lokaci ba na shanye tas,sai databari na dan wuta,sannan ta kuma tambaya ta mai ya faru,kwashe duk abinda ya faru nayi na fada mata tun daga maganin da Aunty Amina ta bani har abunda ya faru a gidan Alhaji,nan ta hau salati tare da fadin lallai biri yayi kama da mutum,saurin kallonta nayi tare da tambayar mai ya faru?.
Gyara murya tare da fadin"ana sauran kwana biyu ki kwanta a Asibiti naji Aunty Amina na waya tanan bayan window bedroom dina tana cewa kamar ma ciki gare ki,bansan dai da wanda take wayaba amma nadai ji ta ambato sunanki ina kyautata zato indai bada Aunty Hauwah take waya ba to da mamy ne takeyi,to tunda naga su Mamy sunzo nidai jikina bai
bani ba banzo dakin bane saboda Aunty Hauwah kinsan na samu matsala da ita saboda salma lokacin bikinki"?
Nace "ai ban sani ba"
Tace"abunda ya faru shine yaya Farooq ne ya dinko mana dogayen riguna na shadda ni da salma,sai ya kasance dankwali daya ne shine sai na dauki dan kwalin sai ya kasance na salma ba dan kwali,kinsan namiji da yakai mata kayan sai Ummy ta tambayeshi ina dankwalin,sai ya ce mata wai guda daya ne kuma na dauka,to bansan yanda akayi ba sai ga salma tazo wai in bata dankwali,ni kuma na ce bazan bada ba,shine fa ta fara fadamin bakaken maganganu,ni kuma naga bazan jura ba na mareta,to bayan ta tafi ne sai ga Aunty Hauwah tazo wai rama mata mari,nan fa muka fara cacar baki sai ga daddyn Abdul(Yaya Farooq) ya shigo shine fa da yaji abunda ya faru ya bata rashin gaskiya".
Na numfasa tare da fadin"Allah ya kyauta,ni yanxu matsalata Yaya Tasi'u,bansan yanda zan bullo mai ba don fushi yake dani sosai,saboda tunda na farfado a Asibiti bai mun magana ba"na karashe magana tare da goge hawayen da ya sulalo daga idona.

"Daurewa zakiyi ki kaskantar da kanki ki basa hakuri amma kar ki yarda yasan da sa hannun Aunty Amina a wannan lamarin saboda in ya sani abun zai fi kamari"cewar Aunty Zeena.

Nace"zanyi kokari Allah ya daurani kanshi"
Tace" amin,amma Bahijjah ina mamakin Aunty Amina,ban taba tunanin zata aikata haka ba,shiyasa Aunty Hanna tace min inyi taka tsantsan da ita don green snake ce under the green grass,duk ita take kitsa musu duk iskancin da sukeyi"
Nace "Allah ya kyauta nima dai nayi saurin sakin jiki dasu"
Tace"gaskiya kam,bari in kawo miki,Abinci don nasan baki ciba"fita yayi daga dakin.

Sai da tayi minti biyar sanna ta kawo mun abinci tare da fadin"kici kisha magani,bari inje inshirya su Abdul zasu tafi islamiyya hudu tayi".

Sai da naci Abincin, nasha magani,sannan na wuce Kitchen don in dafa ruwan wanka,ina tsugunne sai ga Aunty Amina tayi shigo,motsin ta danaji ne yasa ni dago kai,muna hada ido ta watsa mun harara sannan ta bude dakinta ta shiga.

Anan na zauna har ruwan yayi zafi na juye nashiga nayi wanka.
Bayan na fito wanka ne ina zaune ina shafa mai sai ga kiran Ammy ya shigo ta phone dina,cikin sanyi jiki receiving tare da sallama,na gaisheta ta amsa tare damun ya jiki,sannan tayi gyaran murya tare da cewa"Bahijjah na kira ne ki fadamin gaskiyar abunda ya faru don zuciyata taki amincewa ke kika zubar da cikin sunna,saboda nasan baki da wayewar da har zaki aikata haka".
Nan na kwashe duk abunda ya faru na fada mata,salati tayi tare da fadin"Amma Amina bata kyautaba,girman ta baida amfani,ita da ya kamata ta tsawata miki,Amma ita ta aikata haka,Allah shi kyauta kuma banaso Tasi'u yaji maganar nan saboda duk lalacewa dai 'yar uwarkice".
Nace"insha Allahu Ammy bazai jiba".nan dai tamin sallama tare da jamun kunne akan Aunty Amina.

Juyowar da zanyi kawai muka hada ido da Tasi'u,yanda naga idonshi ya kada yayi jane ya tabbbatar mun da ya gama jin maganarmu da Ammy,take naji gabana ya fadi,juyawa naga yayi cikin tsananin fushi ya fice daga dakin,hankalina naji ya tashi don bansan hukunci da zai yanke ba.
Ji nayi yana ta kwada ma Aunty Amina kira tare da bugun kofar dakinta.




Don jin yanda zata kaya a *GIDAN* *NAGOGGO* sai ku jira next page.


More comment,more typing



*Comment*
*Like*
*Share*
*Vote*










*_Fateeyzah_*✍




*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*



*GIDAN NAGOGGO*🏨
*_(A true life story)_*

*_Written_ _by_ _fateeyzah_* 😍😍


*_Jinjina gareki 'yar GIDAN DC,Hauwah A Abba(mrs Mur)Allah ya bar kauna_*❀.

_Bismillahir rahmanir rahim_

*_Page_* 1⃣4⃣ *_to_* 1⃣5⃣

Jin kiran da yake mata ne yasa gabana ya fadi, ban tsaya dogon tunaniba na yi hanyar fita dakin, fitowa ta yayi daiΒ² da bude kofarta, tsaye tayi tare da watsa mai hararara hade da cewa"wai kai Tasi'u me ke damunka ne kake ta kwala mini kira sai kace wani mahaukaci, kaje kaji da abinda mahaukaciyar matarka ta yimaka, ba kazo ka sauke fushinka akaina ba,ai bani na kashe zoman ba,rataya aka ban"ta karashe maganar tana yamutsa Fuska.

Gyara tsayuwarsa yayi tare da yamutsa fuska yace"ba wannan ya kawo niba,nazo ne in miki gargadi hade da kashedi ki fita daga harkar matata, don naji abunda kikayi na bata magani ta zubar min da ciki,to wallahi ki shiga taitayinki,in ba haka ba zan nuna miki true color dina, don naga Alamar baki da mutunci,(ya tsaigaita da magana for 3seconds,sannan yaci gaba)kuma daga yau na yanke alakar da ke tsakaninku".
Yana gama fadin haka yazo ya wuce ta gefena ya shige daki,niko ina tsaye kamar mutum mutumi,don na kasa ko motsi,ita ko Aunty Amina jikinta a tsanyaye taja tsaki ta shige dakinta hade da turo kofa,haka naja kafata hade da dafa bango na shige daki.

Direct Bedroom na nufa don ina kyautata zaton acan zan sameshi,ina shiga na ganshi zaune a gaban mirror dafe da kanshi,wurin shi na nufa gwiwata a tsanyaye na zube a gabanshi tare da kai hannuna kafarshi,ban zata ba naji saukar mari a kumatuna, saurin sakin kafarshi nayi don ji nayi duniyar na juya min don tun da nake ba a taba min marin daya shigeni ba irin wannan,saboda masifar shigata da yayi na kasa kuka sai sauke ajiyar zuciya nake,ganin yana kokarin mikewa yasa naja baya da sauri,ji nayi ya damkoni,da sauki kulle idona ina jiran saukar wani marin,sai jinayi yayi hugging dina hade da fashewa da kuka,nima kukan na saka tare da kankameshi,haka mukayi tayi babu mai lallashi.(Allah sarki Bahijja yanxu kika fara kuka😭😭😭).

Sai da mukayi kukan mu muka gaji tukunna muka kwanta kowa na sakin ajiyar zuciya,anan bacci ya daukemu wanda sai kiran sallar magariba ne ya tashemu(kasancewa jikin gidanmu akwai masallaci),tashi yayi ya fita ba tare da ya tanka munba.

Sai wurin karfe Tara ya dawo hannunshi dauke da takeaway wanda ledan ke dauke da tambarin chicken republic,yana ajiyewa ya kuma fita sai gashi da plate da fork,fridge ya bude ya dauko maltina guda biyu yazo ya ajiye akan center Table,takeaway ya bude hade da juyewa a plate gasasshiyar kaza ce wadda taji hadi,haka ya ringa yaga ya na samun a baki hade da maltina sai da nace mai na koshi, tukunna ya fara cin nashi.
Sai da ya gama ya tattara kayan yakai kitchen hade da daura ruwan wanka aka gas,tukunna ya dawo daki ya kunna TV hade da kamo tashar Mbc Action yana kallo,zuwa nayi na durkusa a gabanshi tare da kamo kannunshi na rike ina zubar da hawaye hade da fadin"Yaya Tasi'u bansan da wata irin kalma

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment