Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sun fito suna tsaye da Ma'u yaya Farooq yazo, murmushi ta yi ta ce " sai Monday yayana ya zo " Ma'u ta ce " muje na gaisa dashi" ok tace sannan suka nufi inda ya yi parking...






Ganin su biyu yasa ya sauke glass ɗin motar, suna zuwa Aneeserh ta ce " yaya ga seatmate ɗina nan Asma'u ku gaisa " Ma'u ta ce " ina wuni " murmushi ɗauke a fuskarsa ya ce " lafiya lao ya karatun?" ta ce "alhamdulillah" ya ce " masha Allah, Allah ya taimaka " Ameen ta ce sannan sukai sallama da Aneeserh ta koma su kuma suka tafi.....





Bayan sunyi nisa ta ce " yaya kasan me wannan ƙawartawa ta ce mini?" girgiza kai ya yi ya ce " A'a sai kin faɗa " murmushi ta yi tana wasada fingers ɗinta ta ce " wai cewa tayi tana sonka inama ta aureka " haɗe rai ya yi ya ce " keee ina wasa dake?" girgiza kai ta yi ya ce" idan kika sake yimin irin wannan maganar sena fasa bakinki" turo baki ta yi ta ce " toni ba saƙo aka baniba zaka dinga yimin faɗa " a fusace ya tsaida motar ya juyo ya na kallonta ya ce "




Ya ce" wlh saina kwaɗa miki mari idan kika sakemim irin wannan maganar " fashewa ta yi da kuka amma bata sake cemasa komai har suka je gida, suna shiga ko gama parking bata tsaya yayi ba taɓude motar tayi waje girgiza kai ya yi sannan ya gyara parking ɗin ya sakko shima. Zaune ya tadda ita gaban Abba sai rusa kuka take kamar wacce akawa wani mugun abu, zama ya yi aikuwa Abba ya rufeshi da faɗa shikam saboda mamaki ma kasa rufe bakinsa yayi jin abubuwan data faɗawa Abban, sukuyar da kansa ya yi bai ce komaiba har Abba ya gama faɗan sannan ya ce"sorry Abba" shuru Abba ya yi yana kallonta ya ce" tashi kije ki cire kayanki" toh ta ce sannan ta tashi ta shiga ɗakinta shima tashi ya yi ya wuce nasa ɗakin ransa a ɓace. Bayan sun shiga Ummi ta kalleshi ta ce" amma kasan halinta sarai ba baka saniba kasan babu yanda za'ayi Farooq ya daketa haka kawai ko wani abun tayi masa bazai daketa ba bare kuma haka kawai" Ajiyar zuciya ya sauke yana shan ruwan gabansa sannan ya ce" nasani itama ai kinsan halinta idan wani abun ya sameta fa?, kinsan lalurarta shiyasa ai nasan babu abunda ya yi mata" sakar baki Ummi ta yi ta ce" saboda kada wani abun yasameta yasa ka zauna kana yimasa faɗa irin haka kuma faɗanma a gabanta?, to Allah ya kyauta" ta tashi ta koma kitchen dan duba abunda take.



Tundaga ranar bai sake kaita makaranta ba dan ko ganinsa cikin gidan batayi kuma ta damu sosai dan Allah ya gani tana son yayanta, yaukam saturday suna kitchen itada Ummi suna girki ta ce"Ummina wai ina yaya Farooq?" harararta Ummi ta yi ta ce.




"Yaya Farooq ɗin da kikasa babanku yay taima faɗa?."



Kwaɓe fuska ta yi ta ce"please Ummi yana ina wallahi so nake na ganshi" kallonta Ummi ta yi ganin yanda ta shagwaɓe fuska ta ce"yaje Abuja" ta ce" amma shine ba'a faɗaminba kuma nima inaso naje fa" banza Ummi ta mata ta cigaba da abunda take aikuwa ta kumbura kamar ta fashe ta juya ta fita a kitchen ɗin, Zaune ta tadda shi yana danna wayarsa da gudu ta tafi ta rungumeshi tana cewa"yayaaaa" dariya ya yi kawai ta ɗago ta kalleshi ta ce.



"Yaya shi ne kayi tafiyar ka, ka barni ko?."


Kumatunta yaja ya ce, "I'm sorry kinji"

Kitso ta fara masa da gemu kamar yadda ta saba indai suna zaune, kwaɓe fuska ya yi yana riƙe hannun nata ya ce.


"Ki yiwa Allah ki daina yimin wallahi da zafi."🥲




Turo baki ta yi tana faɗin"Dan ma zan maka kitso.."


Langwaɓar da kai ya yi ya ce"to na yafe basai an yimin ba" tashi ta yi a jikinsa ta ce"shikenan babu ruwa na dakai" jawota ya yi ya ce" Allah ya baki haƙuri kinji, jeki ɗaki na tawo miki da abun daɗi" tashi tayi da gudu tashiga ɗakinsa, ta ɗauko sannan ta fito. Zama tayi ƙasan kujera zata buɗe ya ce" no ni zaki bawa ai" babu musu ta miƙa masa ya kalleta yana murmushi ya ce"closed your eyes" waro ido ta yi sai kuma a hankali ta rufe idanun nata ya ce"karki kuskura ki buɗe sai na ce miki" gyaɗa masa kai kawai tayi, a hankali ya kalleta ya ce.



"Now opened it."


A hankali ta buɗe idanun nata tana kallonsa, ya yi murmushi, ta kalla gabansa, ai batasan lokacin da ta fasa wata uwar ƙara ba, ta rungumesa tana wujijjigashi tana dariya ta ce.



"Yayana i Love you wallahi har na manta yau birthday ɗina, thank you so much Yayana."


Dariya shima ya yi yana cewa.



"Happy birthday to you.."


Ummi ce ta fito dan ta ɗauka wani abun ne ya faru, sai kuma taga suna ta dariya girgiza kai kawai ta yi ta koma, ya miƙo ma ta wuƙar ta karɓa ya riƙe hannunta yana ma ta waƙa har ta yanka cake ɗin ta saka masa a baki shima ya bata, sannan ta gutsura ta yi kitchen da saurinta, duk yadda Ummi tayi akan ta kyaleta ki tayi har sai da ta bata cake ɗin, sannan ta fito suka zauna ya dinga yi musu hotona suna dariya abin su.








Yau tashi suka yi zasuyi tafiya lokacin kuma ya yi daidai da lokacin da su Aneeserh suke jarrabawa a school.


Zama tayi gefen Abba tana kallonsa ta ce.


"Abba Dan Allah ku tafi dani wallahi idan muka dawo za'amun make-up ɗin jarrabawar."



Murmushi Abba ya yi ya ce.
"No Aneeserh kiyi zaman ki kinji, nayi miki alƙawarin idan kun gama exams da kaina zan kaiki wajen Uncle naki His excellency kinji, amma yanzu kiyi tafiyar ki makaranta."

Hawaye ne ya kawo idanunta ta ce "Amma Abba ni dawa zan zauna a gidan?."
Ya ce "bafa daɗewa zamuyi ba gobe zamu dawo kinji na sanki jaruma ce zaki iya zama."

Goge hawayen fuskarta ta yi ta ce.
"Toh Abba harda Yaya Farooq?."

Murmushi Abba ya yi ya ce.
"Eh mana kema na ce miki zan kai ki"


Shiru tayi bata kuma cewa komai ba, ya kamo hannunta ya riƙe ya ce.
"Sorry baby kiyi karatu da kyau zan siyo maki chocolates da sweet da yawa."



Rungumeshi ta yi batace komai ba.

Ƙarfe biyu suka gama shiri dan tafiya ta rakosu har parking lot, Abba na kallonta ya ce.
"Banda wasa kinji?."
Ɗa ga masa kai kawai tayi Ummi ta rungumeta, ta ce "Bafa zama zamuyi ba karkiji tsoro."

"Toh."


Kawai ta ce sannan ta kalli Yaya Farooq kafin ta ce komai ya yi ma ta murmushi ya ce.
"Sai mun dawo lil sis."
Ya shige mota dan idan har tashi za'a bi baza'a tafi abar Yarinyar da bata wuce 15yrs ita kaɗai ba, kawai dan babu yadda zaiyi ne yasa.
Kallonsu ta dunga yi har suka shiga mota tana ɗaga musu hannu suma suna ɗago ma ta a haka har suka fice daga gidan, ita kuma ta koma ciki.



Washe gari da safe ta tashi ta dafa abinci ta zuba a flask sannan ta ɗau jakarta zata fito akayi kiran wayarta, ɗauka tayi ganin sunan Abba ta yi murmushi sannan ta ɗaga wayar, bayan ta gaisheshi ta ce.


"Abba yaushe zaku dawo?."
Ya ce
"Idan kin dawo daga school zaki tarar da mu a gida kinji baby?."


Murmushi tayi ta ce.
"Tom Abba Allah ya dawo daku lafiya."
Ya amsa ma ta da, "Ameen Aneeserh ki tafi karki makara."

"Okay."

Ta ce sannan ya katse wayar ta ajiye ta fito driver ya tafi kaita school.



*Wannan shi ne abin da ya faru kuma sanadin mutuwar iyayenta da kuma Yayanta wanda kuma shi ne mafarin ƙaddarar ANEESERH kudai ku biyo dan jin yanda labarin ANEESERH zai kasance da kuma ƙalubalen da yake cikin rayuwarta.*



*PRESENT*....
*CI GABAN LABARI*...


✨✨```ANEESERH```✨✨

*Queen Of Squad With Nkd's 🤙*



*Ep. Three*



*PRESENT*....
*CI GABAN LABARI*..



Dogon numfashi His Excellency yaja idanun sa akan Aneeserh cike da yake da tausayin ta, Yarinya ƙarama cikin shekarun ta da bata haura 14 to 15 yrs ba, tayi rashin iyayen ta da Yayan farouq, gaskiya dole mutum ya tausaya ma ta komai dakiyarsa kuwa.



"Aneeserh ki daure kinji ɗiyata insha Allah zuwa anjima Jirgin mu zai ɗa ga zuwa Abuja acan zaki ci gaba da gudanar da Rayuwar ki, ina fatan ki fara sabuwar Rayuwa mai cike da farin ciki."


Shiru tayi masa kamar bazata ce da shi komai ba, sannan ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin.

"Uncle wai yanzu fa shikenan bazan ƙara ganin Yaya Farouq na ba, balle har nayi masa tsokanar dana saba muyi nishaɗi, shikenan Abba na yafi bazai dawo gareni ba, bazai dinga yimin faɗa da nasiha ba, idan ina wani abu da bai dace ba, Allah Sarki ni na cika marainiya a yau babu Ummi da zan tayata girki, wayyo Uncle Zuciyata zafi take yimin sosai Uncle ji nake kamar nima na bisu kawai na huta."


Cikin sauri His Excellency ya rungumota a ƙirjin sa ganin yadda tayi maganar idanunta suna lumshewa, tayi baya zata faɗi daga zaune da take saman gadon jinyar.


Lumshe ido tayi yayin da take tuna siffofin iyayenta Abban ta mai ƙaunar ta Ummi Yaya Farouq ɗin ta duk sun tafi sun barta ita ɗaya a Duniya.



____________
A hankali ta buɗe fararen idanunta ta sauke su a window na private jet. da suke zaune ciki ita da Uncle nata da Matar sa Hajiya Aisha.



Aneeserh mai yawan surutu barkwanci neman tsiwa yau gata so silent Kuma a cikin jirgi ba tare da Abba da Yaya Farouq ɗin ta a gefe ba, hawaye ne taji ya zubo ma ta, da dabara ta goge dan bataso Uncle nata da matar sa su gani.

Jin gine kanta tayi gefen kafaɗun Her Excellency tana lumshe ido.


Murmushi Hajiya Aisha tayi sannan ta gyara ma ta ta kwantar da ita saman lap's nata.




A haka dai shiru har Jirgin su ya yi landing a babban filin saukar jirgi na Garin Abuja.



Securities na musamman suka tar be su a Airport, sannan suka shishshiga tsalatsalan motocin guda biyar jeras suka bar Airport suna jiniya, yayin da Aneeserh take maƙale jikin Her Excellency duk wata iri take jin kanta.






***


Koda isarsu Government House of President na Nijeriya gaba ɗaya, tsararren gida na gani na faɗa na nunawa a television, suka sama tarba mai kyau daga ma'aikatan gidan maza da mata cikin uniform white and sky purple color, masu aikin girke-girke sun ɗaura Apron saman kayan jikin, dukkanin su jere zagaye da motocin fuskokinsu ɗauke da walwala na dawowar His Excellency da matar sa Hajiya Aisha mutanen kirki cikin ƙoshin Lafiya.





Nan ba tare da wani ɓata lokaci ba, suka fiffito Aneeserh tana rungume da Hajiya Aisha idanunta a lumshe sam taƙi bari tayi nesa da ita.


A haka har suka shiga katafaren main palo na gidan ƙamshi kawai ke tashi ta ko'ina na palon gyare yake tsaf tsaf.






"No, Bacci zan yi, ki kaini Bedroom ne Auntie."




Aneeserh tayi maganar idanunta a lumshe lokacin da Her Excellency take ƙoƙarin a je ta saman Royal sofa dake zagaye da Palon.


Ajiyar zuciya ta sauke zuciyarta cike fal da tausayin ta, sannan ta nufa upstairs da Aneeserh rungume da kafaɗar ta.



Shimfiɗe ta tayi saman Bed Like a Little girl sannan ta ja ma ta Blanket ta lulluɓe ta, tana shafa sumar kanta dake baje saman goshin ta.




"Ohya Sleep, kina buƙatar hutu kiyi bacci kinji?, And please ba Auntie zaki ke kira na ba, da Mommy nake so daga yau ki rinƙa kirana, okay!?."



Buɗe lumtsatsun idanunta dake cike da gajiya da kuma Bacci tayi ta sauke su saman kyakkyawar fuskar matar bafulatana da ita.






"Okay, Mommy Insha Allah, amma zan iya tambayar ki kuwa?."





"Ina sauraren ki Shalele."


Murmushi Aneeserh tayi a karon farko har sai da fararen haƙoran ta suka bayyana Yaya Farouq ne yake kiran ta da wannan sunan.
Faɗar haka da Hajiya Aisha tayi saita tuno ma ta da Yayan ta, sai dai tun kafin Murmushin nata yaje ko'ina tayi saurin gimtse fuska idanunta tana tara kwalla tunawa da tayi yanzu ita kaɗai ce a Duniyar ta ba tare da Yaya Farouq abin ƙaunar ta ba, da Ummi da Abba ba.








Cikin taɓe fuska na shagwaɓa alamar kuka ta kalle Her Excellency da rawar jiki da murya take faɗin.

"Mommy! Menene zan dinga yi wanda ba zai saka na manta da Iyaye na ba?."



Kwallar tausayin ta cike da idanunta Allah Sarki har ta ɗauki dan gana ta sakawa ranta.


"Aneeserh saboda Mene kika yimin wannan tambayar?."



"Saboda Ina Son Ummi na sosai ina son Abba da Yaya Farouq nawa Komai nayi masa baya duka na koda ya yi fushi dani baya taɓa dena siyomin chocolate Ina ƙaunar su sosai bana son na manta da su har abada a Rayuwata."


Ƙaunar Yarinyar ne ya daɗa shiga ran Hajiya Aisha.


Ta kamo ta ta zaunar da ita saman mattress ɗin sannan ta a je mayafin kanta gefen gadon, ta kwantar da kan Aneeserh saman lap's nata tana shafa ma ta sumar kanta mai yawan gaske take faɗin.





"Ki dinga musu Addu'a duk lokacin da kikayi sallah kinji, wannan ɗaya ne daga cikin abubuwan da zan faɗa miki ki dinga yi saboda ki dinga tunawa da su forever."








"Sallah!! Wayyo banyi sallah ba Abba zai dakeni wayyo ni Yaya Farouq."





Aneeserh tayi maganar da sauri tana sauka daga saman Bed ɗin da sauri ta nufa hanyar bathroom take faɗin hakan.





Sai dai chak taja ta tsaya ƙafafuwan ta suka ma ta nauyi sosai tuna cewa ashe Abba da yake ma ta faɗa idan batayi Sallah akan lokaci ba, bashi a Duniyar."


Slowly Hawaye ya wanke ma ta fuska, cikin sanyin jiki ta juya ta kalla Hajiya Aisha da tayi ma ta Tsuru da ido tana kallon ta cike da tausayin ta, Tabbas ta ɗauki aniyar riƙe Aneeserh tsakani da Allah ta bata lokacin ta, wurin bata tarbiyya mai kyau Kamar yadda iyayenta zasu bata.


Ba tare da Aneeserh ta ce da ita komai ba, ta juya ta shige cikin Bathroom ɗin cikin sanyi jiki.



Alwala ta ɗauro duk wani motsi da zatayi sai ta tuna Rayuwarta da Ahalin ta Rayuwa mai daɗi mai cike da farin ciki mara adadi mai tsayawa a rai.




Fitowa tayi daga bathroom ɗin bayan ta kammala alwalar sannan ita ma Hajiya Aisha ta shiga tayi Alwala ta fito suka yi Sallahr la'asar da aka kira basu samu sun yi ba sai yanzu.




Duk wani motsin Aneeserh akan idon Hajiya Aisha yake gudana tana lura da yadda ta zubawa Bedroom ɗin idanu tana kalla bayan sun idar da Sallahr.



"Bedroom ɗin da kayan cikin sa sun yi miki ko kuwa a canza bakyason kalar su?."






Da sauri kuma a firgice Aneeserh ta kalla Hajiya Aisha da tayi ma ta tambayar tana kallon ta Murmushi ɗauke a fuskarta.






Ƙasa tayi da idon ta tana wasa da Diamond ring dake hannunta wanda Yayan ta Farouq ya bata Ranar Birthday nata ta ce.




"Kalar ruwan ɗakin kala ne mai kyau wanda matasan Ƴan Mata masu kamar shekaruna suke so wato sky purple color, sannan ɗakin ya haɗu sosai, domin ko ɗiyar president albarka."






"HHhH to ai kece ɗiyar President ɗin, ko kin manta wanene Uncle ɗin naki President of Nijeriya ne guda, kinga ke nan kece ɗiyar President ɗin, dama kuma ɗa ɗaya garemu, shi kaɗai Ubangiji ya nufa da zamu haifa, sai dai yanzu kun zama biyu, dan ina fatan ki ɗauke mu Ni da Uncle ɗin ki, Iyaye a gareki Shalele, nayi Alƙawarin kula dake daga yau kuma yanzu har Ranar da zanga Auren ki."😅



Murmushi Aneeserh tayi tana rufe fuska domin Hajiya Aisha ta bata kunya sosai.





Ita ma Hajiya Aisha Murmushin tayi dama Burin ta ke nan Aneeserh ta saki jikinta ta saba da su sannan ta ɗauke su Iyaye a gare ta..



Hajiya Aisha bata bar Aneeserh ba har sai da ta tabbatar da ta rage ma ta kaɗan daga cikin damuwa da take ciki sannan ta fito daga Bedroom ɗin ta bar Aneeserh tayi Bacci ta huta.


A palo ta tarar da mijin nata zaune da alama ita yake jira dama.


"Sorry Habibi kasan sabuwar ɗiyar tamu sai da lallashi da kuma bata lokaci yadda ya kamata, don tana cikin kewa sosai wanda bana tunanin zata fita daga wannan hali a wannan lokacin."



"Masha Allah. Babu Komai Jannat karki damu, na gode miki sosai da nuna kulawa ga ɗiyar ɗan uwana, ina fatan kulawar ki a gare ta ya ɗaure har abada ki mayar da ita Tamkar ɗiyarki ta cikin ki."


Zama tayi gefen sa saman 3sieter da yake kai ta kamo hannun sa ta haɗa da nata.


"Insha Allah Habibi nayi alƙawarin kula da Aneeserh duk rintsi duk wuya a duk yadda take zan kula da ita na bata tarbiyya kamar ɗiya ta ta cikina wacce ban samu ba, sai yanzu wato Aneeserh."



"Kai Amma naji daɗi sosai Jannat very proud of you."


Murmushi tayi na jindaɗin alfahari da ita da mijinta abin ƙaunar ta yake yi ta kwanta jikinsa sanin su kaɗai ne cikin Palon babu mai shigowa.


"Yauwa kaga yanzu sai mu zuba ido sosai akan abin da take so da kuma wanda bata so, yadda zamu fi janta jiki, ta manta duk wani abu mummuna a Rayuwar ta, farin ciki ya gauraye Insha Allah gobe ko jibi Ni da kaina zan aje duk wani aiki da yake a office na bawa ɗiya ta kulawa mu tafi yawo da ita mu zagaye Abuja gaba ɗaya nasan hakan zai taimaka sosai wurin rage ma ta kewa."



"Kai Masha Allah amma fa naji daɗi sosai kuma insha Allah dani za'ayi wannan yawon Ubangiji ya kaimu."


Amsa wa tayi da Ameen, sannan cikin nutsuwa irin na manya da kuma fahimtar juna dake tsakanin su suka ci gaba da tattaunawa akan yadda zasu ɓullo wa al'amarin Aneeserh...




*Wannan ke nan kaɗan ko nace mafari daga cikin wannan Zazzafar labari mai suna ANEESERH Insha Allah idan mabiya kukayi juriya na biyo wannan labari gaba ɗaya zamuji yadda rayuwar Aneeserh zai kasance yanzu dai ga Aneeserh a Abuja gidan Uncle nata Mister President ko ya ya zamanta zata kasance???...*



*💥Aneeserh Just The Beginning.*💥


~Paid 500₦~

*WACCA TA SHIRYA BIYA SAI KI BIYA TA WANNAN DETAILS👇*


*Account Name: Hauwa lawan.*
*Account Number: 9086030007.*
*Bank Name: Opay digital service.*

*Sannan sai ki turo evidence of payment ta waɗan nan Countacts_08081129487 or 09086030007.*



*MU TARA A NEXT PAGE DOMIN SANIN YADDA ZATA KASANCE.*😇🤸

*ANEESERH.*

*Story $ Writing By:*✍️📚


*N $ N.*




Ep- Four.




Wajejen la'asar ta farka daga bacci, a hankali take buɗe lumsassun idanunta tana sake ƙarema ɗakin nata kallo wai yau ita Aneeserh ce zaune cikin garin Abuja ba tareda Abba, Ummi Yaya Farooq ba anya kuwa ba mafarki take ba?, ganin batada mai bata amsa yasa ta tashi tana tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a jiki ta shige banɗakin....

Zaune ta tadda Mommy tana danna wayarta tana ganinta ta sakar mata murmushi tana ajiye wayar hannunta ta ce
"Kintashi daga baccin?"
Gyaɗa mata kai Aneeserh tayi dan har sannan bata wani saki jiki da'itaba, ganin ta tsaya yasa Mommy ta ce "ba sallah zakiyi ba?" tana wasada fingers nata ta ce "Eh sallah zanyi " girgiza kai Mommy ta yi ta ce "ok idan kin idar ina jiranki a parlona" tom kawai ta ce sannan Mommy ta fita ita kuma ta bita da kallo.....

Ahankali ta tura ƙofar parlon kamar wata mara gaskiya, babu kowa cikinsa sai wani daddaɗan ƙamshi dake tashi a parlon iyaka haɗuwa parlon ya haɗu, zama tayi kan ɗaya daga cikin royal sofa ɗin dake parlon ta lumshe idanunta. Fitowa Mommy tayi ta kalleta ganin yanda ta rufe ido sosai takejin yarinyar a cikin ranta, ta zauna gefenta tana sake ƙare mata kallo, Aneeserh asalin kyakkyawa ce tun daga kan idanunta yanda suke a rufe gata da long eyelashers masha Allah, hancinta dogone sosai kuma ɗan ƙarami abin sha'awa, sai ɗan ƙaramin bakinta wanda yake jajur dashi koda yaushe saboda yawan tsotseshi da takeyi. Murmushi Mommy ta yi ta ce
"Masha Allah"
Buɗe idanunta ta yi tana kallonta sai kuma ta kwaɓe fuska ta ce
"Why are u looking at me like that?"
Murmushi Mommy ta yi ta ce" ina sake kallon kine saboda kada watarana na kasa gane ki sweetheart" murmushi Aneeserh tayi wanda iyakarsa lips ɗinta ta ce" ina Daddy?" sosai Mommy taji daɗi aranta jin sunan da takira his excel..ta ce
"Yana office dear, kici abinci sai muyi hira sosai" daga haka ta dana wata ƙararrawa not too long wata maid tashigo ta sunkuya cikin girmamawa ta ce " gani maa"
"Ki je ki haɗowa dear abinci, but abu mara nauyi haka" sunkuyarda kanta ta yi ta ce "okay maa" sannan ta juya ta fita.....

Ajiye spoon ɗin tayi Mommy ta kalleta ta ce" mene?"
Kwaɓe fuska ta yi ta ce "i'm full " haɗe rai Mommy ta yi ta ɗauki spoon ɗin ta ɗebi pepper ɗin offals ɗin takai bakinta, shagwaɓe fuska ta yi ta ce kamar zatayi kuka
"Wlh Mommy na ƙoshi anjima zanci"
"Promise?" Mommy ta faɗa. Gyaɗa mata kai ta yi alamar Eh sannan Mommy ta ajiye ta ce "Allah ya kaimu anjiman"......


Banda ƙarar spoons babu abinda kakeji a parlon, juya abincin kawai take amma ta kasa kaishi bakinta lura da haka ya yi ya ce

"Aneeserh meyasa baki cin abincin?"

Sunkuyar da kanta kawai tayi batace komai ba ya yi mata alama da tazo da hannunsa. Tashi tayi ta kowa kujerar kusada shi ta zauna yana kallonta ya ɗebi abinci ya ce "haaaa" kasa yimasa musu tayi a hankali ta buɗe bakin ya zuba mata abinci, haka ya dunga feeding nata har ta ƙoshi sannan ya rabu da'ita, yana kallon Mommy ya ce " Jannat ya kamata zuwa gobe akaita ta zaɓi kayan sakawa, nd gobe Bashir zai zo " ta ce "okay, in sha Allah " ya ce "good"........

Da sassafe ta farka kasancewar ta saba da tashin wuri a gida amma babu abin yi agidan nan dan komai anriga anyi, gani abun take kamar ba gaske ba yau itace irin wannan lokacin bata kitchen kuma badan lokacin makaranta yayi ba, wasu zafafan hawaye taji sun zubo mata ta ce "Allah ya jiƙanku da rahma, Allah ya gafarta muku"..Kwanciya ta kuma yi kan royal bed ɗin nata tana cigaba da tunanin rayuwarta ta baya da kuma wacce ta sameta yanzu.......


Ƙarfe biyar saura Mommy ta shigo ɗakin tana kallonta ta ce "yawwa Aneeserh please duk abinda kika san zaki buƙata ki ɗauko dan Allah" murmushi ta yi ta ce "amma Mommy zan siyo chocolates da biscuit!" dariya Mommy ta yi ta ce" duk abinda kikeso ki siya dear ke ko duka shopping mall ɗin kikeso zaki samu" rufe fuskarta ta yi tana dariya dan sai asannan take jin kunyar abunda ta faɗa, girgiza kai Mommy ta yi sannan takama hannunta suka fita......


Har takusa kaiwa ƙofa ta ce "Au!, na manta kije kiyiwa Daddy sallama yana parlonsa uncle ɗinki ma yazo" toh kawai ta ce sannan ta kama hanyar parlon......




Da sallama tashiga parlon kanta a ƙasa, murmushi Daddy ya yi ta tsuguna gefensa tana kallon baƙin dake zaune a parlon ta ce

"Ina yini"


Cikin sakin fuska suka amsa mata sannan ta kalli Daddy ta ce

"Daddy daman zanje shopping ne shine Mommy ta ce nazo na faɗa maka" shafa kanta yayi ya ce "ok tom adawo lpia dear" tashi tayi ta juya ta fita tana tafiya a nutse kamar ba itaba.......




Ya ce" nikam yaya sai nake ganin kamar a aurawa Aliyu yarinyar nan ko Allah zaisa a dace"


Shuru his excellency ya yi sai kuma ya ce

"Amma meyasa ?"

"saboda yarinyar tana da hankali kuma yarinya ce duk yanda yakeson ta kasance haka zata masa"


Uncle Nasir ne ya ce "Bashir kazo da magana nima kuma wlh tunda na ganta naji sha'awar ya aureta" murmushi kawai Daddy ya yi yana kallon ƙannen nasa. Shuru suka yi dan sun rigada sunsan halin ɗan uwan nasu akwai kafiya masha Allah.......



"Shikenan na amince"


Da sauri suka kalleshi domin ba su yi tunanin haka daga gareshi ba Uncle Bashir ne ya ce" Masha Allah kawai abinda za'ayi a ɗaura auren yanzu tunda duk zamu iya wakiltarsu"


Waro ido Daddy ya yi sai ya ce" kamar ana yaƙi?" murmushi sukai atare Uncle Nasir ya ce

"Ai wannan ɗinma yaƙin ne kawai a ɗaura yanzu"



Babu yanda ya iya da ƴan uwan nasa aka ɗaura auren Aneeserh da kuma ɗan gidan president Aliyu wanda bamusan ko wane ba ko waye Aliyun??????.




Ɗaukan duk abinda taga ya yi mata cikin shopping mall

Please Login or Register in order to submit comment