Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

domin na kiyaye."






Ya yi maganar bil-haƙƙi yana juyo da Kallon sa gareta, tare da bata gaba ɗaya hankalinsa.





Shiru tayi dan bata da abin faɗa domin wannan ƙaramin ƙanin nasu da ya kasance Namiji ɗaya tilo gidan su, sauran duka mata ne su uku sai kuma shi, sosai suka sha fama da shi, tun Yana Yaro domin bayaji ko kaɗan kuma har girman sa gashi yaƙi ya yi Aure babu kalar naci da basuyi masa ba amma yaƙi, daga ƙarshe ma ya bar musu ƙasar, gashi kuma yanzu ya yi musu Dawowar ba za ta kuma ya fara da gidan ta, dama kuma Rayuwarsa yafi yi a gidan wurin ta muddun yana ƙasar.




*Aneeserh p.o.v.*


Da shigarta Bedroom nata da ya gaji da haɗuwa wanka tayi sannan ta buɗe leda ta ɗauki cake guda, ta zauna gefan Bed tana ci, sosai ta ci har sai da taji cikin ta ya cika da kayan zaƙi sannan ta Bari, kwanciya tayi saman Bed Kamar da wasa har Bacci Ya yi gaba da ita......




*Tofah ga fa Jay ya bayyana a bazata, 😸😸 sannan Hydar yaƙi ya bayyana kansa mu san shi, 🌝🌚 to ai hi ke nan.*🤸🤸



~Paid 500₦~

*WACCA TA SHIRYA BIYA SAI KI BIYA TA WANNAN DETAILS👇*


*Account Name: Hauwa lawan.*
*Account Number: 9086030007.*
*Bank Name: Opay digital service.*

*Sannan sai ki turo evidence of payment ta waɗan nan Countacts_08081129487 or 0810 660 8363.*



https://chat.whatsapp.com/GGPVCQ6ozk64RL5o2dARsT


*ANEESERH*


*💥Aneeserh Just The Beginning.*💥



*Story $ Writing By:*✍️📚


*N $ N.*


*🔥Nanameera $ Nainarh KD.🔥*

______________

*This page is last of free page's.🧏*


_________

*Idan kin shirya biya 500₦ only ki biya ta nan Details ɗin 👇.*
_______________
9086030007
Hauwa lawan
Opay or
8106608363
Hauwa lawan
Palmpay
_______________
Evidence
09121033575
Or
07085212808
Via WhatsApp Only.


*Ep-10.*

Wajejen ƙarfe sha ɗaya jirgin ya yi landing a filin jirgi na garin abuja, fitowa ya yi cikin tafiyarsa ta cikakkun maza dan adire yake sosai, da sauri wasu guards suka zo suka buɗe masa ƙofa ya shige suka kama hanya. Fitowarta kenan cikin wata riga doguwa fara ƙal da'ita sosai rigar ta kama jikinta dan irin silky riga ce, baya tayi jin ta buge wani abu kamar dutse, waro idanunta ta yi ganin wani babban mutum dan yafi yaya Farooq ɗinta nesa ba kusa ba, gashi wani irin murɗaɗen jikine dashi kana ganinsa kaga zam soja, fari ne sosai kuma asalin kyakkyawa dan yafi kamada half-caste ɗin nan yana da manyan idanuwa kamar zasu fito su zageka, kana ganinsa kasan ajebo ne iya ajebo dan yanda fatarsa ke glowing kaɗai zai tabbatar maka da haka. Da gudu ta koma cikin gidan tana kiran

"Mommy!! Mommy!! Mommy!!"

Da sauri Mommy ta fito daga kitchen tana kallonta da tsoro ta ce

"Aneeserh lpy?"

Kasa magana ta yi sai nishi take tana nuna mata waje, daidai nan Aliyu ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, murmushi Mommy ta yi tana kallonsa ta ce "oyoyo Aliy sai yau?" cikin sassarfa yazo ya shige jikinta yana sakin ajiyar zuciya ya ce "i miss you so much Mommy" shafa kansa tayi ta ce" nima haka son" zame jikinsa ya yi sai asannan ya kalli Aneeserh da take ta kallonsa kamar ta samu tv, zama ya yi kan royal sofa ɗin parlon yana sakin ajiyar zuciya akaro na babu adadi

"Safeena ki zauna mana"

Mommy ta faɗa tana kallon matashiyar budurwar wacce bazata shige shekaru 22 ba, zama ta yi tana kallon Mommy ta ce" Mommy ina kwana?" murmushi ɗauke a fuskar Mommy ta ce "lpy lao Safeena ya gida?" "Alhamdulillah ina Daddy?" kallon Aneeserh ta keyi ta ce" ya fita ɗazu wai naji ya ce za suje kano maybe zuwa la'asar ya dawo" tashi Aneeserh ta yi tana kalle-kalle Mommy ta ce "Aneeserh ga yayanki fa" da sauri ta sake kallonsa jin ance wai yayanta, kasancewar da baƙin glasses a idanunsa yasa bata gane ba ko shima kallonta ya ke

"Ina kwana?"

Ta faɗa a ɗan rikice, ba tareda ya kalleta ba ya ce "lpy y kk?" "Alhamdulillah" ta furta sannan ta bi bayan Mommy kitchen.



Murmushi Mommy ta yi ta ce "meyasa ɗazu kika tsorata ne dear?" waro idanunta ta yi ta ce "Mommy ganinsa nayi kamar dodo wlh irin wadannan mutanen waɗanda suke wristling a Mbc max ne" dariya Mommy ta yi tana kallonta ta ce" Allah ya shiryamin ke Aneeserh toh yayanki ne sunan sa Aliyu waccen kuma matarsa ce"


"Mommy batajin tsoronsa?"

Girgiza kai Mommy ta yi tana jinjina yarintar Aneeserh ta ce" daman mata najin tsoron mijinta Aneeserh?" da sauri ta ce" wannan ai sai ya zaneta baki ganshi ba jibgege" murmushi ta yi ta ce "yanzu idan akace shine mijinki sai kiji tsoransa?" dafe ƙirji ta yi ta ce

"Wlh Mommy sai na mutu saboda tsoro yanzu mafa banason ganinsa gani nake kamar zai dakeni" fitowa Mommy tayi daga kitchen ɗin bayan ta gama bawa maids din instructions da sauri Aneeserh ta haye sama kamar zata waɗi saboda kada su sake haɗa ido da Aliyu.



Aliyu ne zaune gefen gadon ɗakin yayi shuru, zama ta yi kusada shi tana kallonsa ta ce" G.A lafiya?" kallonta ya yi sai kuma ya miƙe kamar zai shiga toilet sannan ya ce

"Nothing"

Ajiyar zuciya ta sauke dan daman ta san halinsa kenan, Aliyu bashida ɗaukan raini kuma bashida rashin mutunci amma mutum ne irin kaifi ɗayan nan idan ya ce zai yi abu tofa babu wanda ya isa ya hanashi haka idan ya ce bazai yiba babu wanda ya isa ya saka shi, sannan kuma akwai shi da izza kodan ya kasance jinin sarauta ne ga kuma mulki da mahaifinsa keyi???? bashida shiga harkar mutane da yawa amma idan ya sanka zai mutuntaka, kowa na wajen aikinsa sonsa yake kasancewar mai kyawawan ɗabi'u uwa uba kuma addini dan bashida flaws a wannan ɓangaren babban abinda ya fiso a rayuwarsa shine mahaifinsa yana matuƙar jinsa a ransa kamar yanda shima Daddy yake matuƙar sonsa ba kowane lokaci yake kula mutane ba kuma ba kowane irin mutane yake mu'amala da suba, wannan kenan daga cikin halayen General Aliyu Muhd Baira A.K.A G.A.





Da sauri ta buɗe idanunta tana kallon agogon gefenta dafe ƙirji ta yi ta ce" wayyo Allah na ya akayi nayi bacci haka it's almost magrib banyi sallah ba, tashi ta yi ta shige toilet dan ɗauro alwala. A gurguje ta shirya tayi sallah sannan ta fito cikin wata abaya ash colour ta ɗaura veil ɗinta akanta ta shafa lip gloose a bakinta, sosai ta yi kyau masha Allah dan sai ta ƙara zama wata budurwa da'ita.




Zaune ta samesu suna ɗan taɓa hira sai wani shagwaɓe fuska yake kamar Baby tsayawa ta yi tana kallon ikon Allah lokaci ɗaya kuma Abbanta ya faɗo mata



"Shalele lafiya kike kuka?"


Sai a sannan ta taɓa fuskarta taji danshin hawaye dan batasan ma ta fara kuka ba, da hannu ya yi mata alama da tazo ai kuwa ta ƙaraso zata tsuguna ya zaunar da ita kan cinyarsa yana share mata hawayen fuskarta da hannunsa ya ce


"Ke dawa shalele?"

Girgiza kai tayi sai kuma ta fashe da kuka, kuka take mai tsuma zuciyar duk wani mai sauraro dan kukan daga ƙasan zuciyarta yake fitowa, bai hanata ba sai shafa mata bayanta da ya dunga yi har kusan 10mins sannan ta fara sauke ajiuar zuciya tana shashsheƙa a hankali



"Yanzu faɗamin mene ne ya saka ki kuka?"


"Daddy Abbana, Ummin, yaya Farooq ɗina yaushe zan sake ganinsu Daddy?"


Rasa abunda zai faɗa mata ya yi ya tsurawa kyakkyawar fuskarta irinta fulani ido ba zaice ga abinda yake tunani ba amma tabbas yana matuƙar tausayin Aneeserh yau da ace Farooq ko ɗaya daga cikinsu bai mutu ba to da tabbas zataji sauƙi amma ace duka family ɗinka ka rasa su abun isn't easy.



Shikam Aliyu kallonsu kawai yake dan baisan inda wannan yarinya t samu ba, kallonta Daddy ya yi ya ce

"Shalele!" ɗago kanta ta yi ta ce"na'am Daddy" numfasawa ya yi sannan ya riƙo haɓarta yana kallonta ya ce


"Daga yau ki ɗauka ni ne Daddynki, shikuma wannan ki ɗauka shine Abbanki kinji, duk abinda uba yakewa ƴarsa to Aliyu zai miki shi Shalele understood?" ya ƙare maganar yana nuna mata Aliyu.



Da ɗan firgice a tareda ita ta ce

"Abbana wannan?"

Murmushi Daddy ya yi sannan ya gyaɗa mata kai, a hankali ta sauka daga jikin Daddy ta ce "zani wajen Mommy" okey ya ce mata sannan ta shige.



Kallon Daddy ya yi ya ce "Dad wannan ƴar daga ina?" ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce " zan baka labarin komai son ka bari sai gobe"


"Why not today Daddy?"

Tashi Daddy ya yi ya ce" gobe Uncles ɗinka zasu zo tom za'a faɗa maka yanda zaka fahimta" daga haka ya fara taka stairs ɗin.


Ɗaga kafaɗa Aliyu ya yi irin abun bai damesa ba sannan ya miƙe a nutse ya fara tafiya torward direction ɗin fita daga parlon.



Zaune yake kusada wani ƙaramin swimming fool yana kallon ruwan da yake gwanin ban sha'awa, ajikinsa yaji ana kallonsa ai kuwa ya juya karaf idanunsa ya shiga cikin nata, cikin hanzari ta zuwa amma kafin tayi taku ɗaya yazo gabanta, hannunsa yasa ya kamota aikuwa ta fashe da kuka tana haɗe hannayenta guri guda ta ce


"Dan Allah dan Annabi kayi haƙuri wlh bazan ƙaraba na rantse" shuru ya mata kuma har sannan tana riƙe a hannunsa, sake fashewa ta yi da kuka tana kare idanunta ganin yana kallonta ta ce" wlh banaso kana kallona kamar dodo" waro idanunsa ya yi yana kallonta wato shine ma dodon?? Kwafa ya yi kawai sannan ya koma ya zauna kan kujerar har sannan tana hannunsa.



Iyaka rikicewa Aneeserh ta rikice dan Alah ya gani idan da abunda tafi tsoro a rayuwarta bai shige soldier ba shiyasama ɗazu ta tashi tabar wajensa da ƙaryar wajen Mommy zata je, tun tana koke-kokenta har ta gaji tayi shuru tana kallon inda yake kallo



"what's your name?"

Kallonsa ta yi sai kuma.ta ce " Aneeserh"

Yana kallonta shima ya ce" daga ina kike kuma me ya kawo ki gidan nan?" turo baki ta yi ta ce


"irin wannan tambaya haka nima bansani ba" da sauri ya kalleta yaga ta ɗauke kanta tana ƙunƙuni wanda kuma daman ɗabi'arta ce, girgiza kansa ya yi sannan ya sake ta


"Tashi ki tafi"

Ya furta ba tareda ya kalleta ba, da sauri kuwa ta miƙe har tana tuntuɓe wajen shigewa ta ƙofar sa ta fito.




*ANEESERH*.



*ANEESERH*


*💥Aneeserh Just The Beginning.*💥



*Story $ Writing By:*✍️📚


*N $ N.*


*💫Nanameera $ Nainarh KD.💫*




*EP. ELEVEN*




```WASHE GARI```


Cike da magagi ta kuma kai hannu tana laluba saman mattress ɗin tare da saka ran taɓosa, sai dai jin alamar babu kowa ne yasa ta buɗe idanunta masu cike da Bacci ta ware su saman Bed ɗin, da sauri ta tashi zaune, saukowa tayi daga saman Bed ɗin tuna a'ina suke yasa ba tare da damuwar rashin ganin sa ba, ta shiga bathroom domin ɗauro alwalar Sallahr Asuba da bata samu tayi ba tun lokacin da G.A ya tashe ta sai yanzu.





"Barka da safiya Mommy na ina fatan na sameku lafiya jiya bamu samu mun gaisa sosai dake ba."


Ƙayataccen Murmushi Hajiya Aisha tayi tana shafa kansa mai cike da tarin suma take faɗin.


"Lafiya Qlau muke Hydar da fatan kun kwana lafiya?."


"Lafiya Qlau Alhamdulillah."


"Masha Allah, ina ita Safeena ɗin take kodai ta koma Bacci ne?."


Shiru ya yi na 'yan sakanni sannan ya bata amsa da faɗin.


"Tana part ɗin mu ina ga ta koma ɗin ne."



"Okay Tohm amma me yasa banga kazo tare da sauran Matan naka ba, Humaira da Yasmeen fatan dai kuna zaune lafiya gaba ɗaya."


Tambayar tayi masa cike da kulawa idanunta akan tilon ɗan nata tausayin sa fal zuciyarta.






A hankali ya miƙe tsaye zura hannayen sa ya yi cikin trouser pocket nasa, sannan ya ƙari sa kusa da window na Bedroom ɗin idanunsa ya lumshe tsawon sakanni sannan ya bata amsa da cewa.



"Duka suna lafiya sai dai basu damu dani ko magana ta ba, ita Humaira bata dawo Nijeriya ba, ta wuce Asturaliya wurin iyayen ta, ita kuma Yasmeen tana Kano a halin yanzu. Safeena ita ce ta biyo ni, kuma muke tare da ita"





Ajiyar zuciya ta sauke ɓoyayyiya tana kuma tausayawa halin da yake ciki mata har uku cikin su kuma babu wata da tasan menene ma Auren yake nufi gaba ɗaya. Ko wacce sha'anin gabanta kawai take yi babu ruwanta da wani Aure dake kanta.



Sanin da tayi ci gaba da maganar ma ɓacin rai zai haddasa masa kuma abin da bataso ke nan, yasa ta canza maganar tare da faɗin.


"Nace kuwa kaje kira da His Excellency ya yi maka jiya naji kamar ya ce ka same sa?."



Huro iskar dake cike da bakinsa waje ya yi, idanun suna sauyawa daga rinewa da suka fara lokaci guda.


"Ban tafi ba."


"Me yasa."


"Haka Kawai naji kamar babu Alkhairi a nema na da yake yi kuma ya ce Uncle Bashir suna nan tafe Kinga kuwa akwai ayar tambaya a lamarin."



"Amma ina ga da kaje ɗin kaji koma Menene Kamar zai fi ko?."


"Okay."


Ya faɗa a taƙaice.


Hajiya Aisha tana shirin ƙara Magana ke nan, aka turo ƙofar aka shigo.


Juyawa suka yi gaba ɗaya domin ganin ko wani mahaluki ne.



Shigowa Bedroom ɗin tayi tamkar wacce aka jefo ta babu ko sallama Kallabi a hannunta take faɗin.


"Wato Mommy shi ne ma kika manta dani ko tashi na bakizo ba, to ma nayi fushi."


Tayi maganar cike da shagwaɓa ba tare da ta lura da shi dake tsaye bakin window ba, shi kuwa zuba ma ta idanu ya yi yana kallon ta da nazarin ta ba tare da ya ce Komai ba.




"Oh am sorry Dear ɗokin Dawowar Hydar ne yasa na sha'afa gaba ɗaya."



Turo baki tayi tare da kifa kanta saman lap's na Hajiya Aisha Bayan ta ƙari sa wurin ta tare tana faɗin.


"Chabb wannan mai ƙirar dodan nin Allah jiya dana fara ganinsa na zata wannan Lion ne da ake haskawa a Tv ne fa, bakiga yadda yake tafiya bane a wani hakimce gashi jikin sa a murɗe ta ko'ina kamar kamar....."


Wani irin zaro ido tayi waje cike da tashin hankali da yasa babu shiri ta miƙe daga jikin Hajiya Aisha sakamakon Four eyes da suka haɗa da shi, yunƙurin ficewa daga Bedroom ɗin tayi gaba ɗaya, sai dai ko kafin ta kai ga ƙofa taku ɗaya ya yi ya damƙo ta, ta dawo faɗa saman faffaɗan ƙirjin sa.


Cike da mugunta ya saɓata a kafaɗar sa ba tare da ya ce Komai ba.


Ihu ta fara tana roƙon sa da ya sauke ta, sai dai da alama bashi da niyyar hakan, cizo da yaƙu shi ta fara masa amma ko'a jikin sa, sadaƙarwa tayi ta fara basa haƙuri harda hawayen ta.


"Hydar sauke ta mana ƙanwar ka ce fa, Yarinta ke damun ta ba Komai ba."




Sauke ta ya yi ƙasa Aikuwa bata jira Komai ba ta ruga da gudu har da haɗa hanya ta bar Bedroom ɗin.


"Huh kaga ka tsoratar da ita ko, ya yi maka kyau."


"Mommy hakan ne ya kamata da ita ai."

Ya yi maganar yana sakin Murmushin mugunta.

Ya lura Yarinyar Akwai tsokanar tsiya sai shegen tsoro.

Shiru Mommy tayi ba ta kuma cewa Komai ba. Tunanin ta gaba ɗaya ya koma ne kan yadda za'ai Aneeserh ta iya Rayuwa da Hydar ne As Matar sa kuma cikin kishiyoyi har uku gaskiya lamarin kamar da wuya.




*Kano, Nigeria.*


*G.R.A*


Gidan ya haɗu sosai kuma katafaren gida ne wanda ba'a ko'ina ake samun gida mai kyau da tsaruwa kalar sa ba, daga ko'ina na gidan securities ne birjik suna gudanar da aikin tsaron Gidan kamar ko yaushe dama kuma Gidan baya rabuwa da masu tsaron sa ko da yaushe.



Jin da tayi knocking ɗin da ake ta faman bugawa daga palon ya yi yawa ne, yasa cike da kasala da gajiya ta kawar da laptop dake Gaban ta gefe sannan ta miƙe tsaye a kasalan ce ta fito daga Bedroom ɗin ta ƙari sa ƙofar palon ta buɗe.



"Oh Sabeera kune ashe. Ku shigo ciki please."



Tayi maganar tana kallon su fuskarta cike da Murmushin farin ciki na Ganin su, tafawa suka yi cike da farin cikin sake Ganin juna bayan sun zazzauna a haɗaɗɗen palon saman lumtsa lumtsan kujerun alfarma dake zagaye da Palon.





"Wai amma Suhaila ta ya ya securities suka bari kuka shigo ciki?."


Tayi musu tambayar lokacin da ta dure musu faffaɗan Tray dake cike da kayan qwalam gaban su saman Center table.


Su biyu ne 'Yan matan da bazasu haure shekaru Ashirin da bakwai ba, suka tafa cike da salon bariki da jin kalar tambayar da tayi musu ɗaya cikin su da alama ita ce Suhaila ɗin ta ce.



"HHhH Yasmeen ke nan Kamar kin manta su waye mu ko, waɗannan ƙananan balagaggun salo ɗaya ya rikita su suka bamu hanya cikin fita hayyaci ba tare da sun sani ba."



Kuma tuntsire wa da dariya suka yi suna tafawa ɗayar ita ma ta ce.


"Yasmeen ya kamata Ku canza securities na gidan gaba ɗaya domin za'a iya haɗa baki da su wata Rana a ga bayan ku wallahi shawara ce wannan."






Dariya Matar Gidan wacca suka kira da Yasmeen tayi tana zama saman Sofa ta ce.






Babu Ruwana su wallahi Aliyu da ya kawo su shi keda ikon sallamar su duk lokacin da ya so bawai Ni ba.



"Ke kika sani dai da bakya jin shawara ko kaɗan, wai amma nace ina shi General ɗin yake ina ce jiya kuka dawo ƙasar kodai shi bai dawo ba ne?."


Sabeera ce tayi ma ta tambayar cike da son Sanin Komai.


Taɓe baki tayi cike da rashin wayo ta Gyara zama tana zayyano musu yadda suka kwashe da shi akan ya yi, ya yi da ita ta bisa Abuja su gaishe da Iyayen sa sannan su dawo Kano ɗin amma taƙi ta taho Kano kai tsaye.


Sai da ta gaba faɗa musu Komai har ƙin ɗaukar Wayarta da ya yi yau da ta kira sa, sannan suka tafa suna faɗin gwara da tayi hakan wallahi domin da hakan ne kawai zata ɗa ga darajar ta wurin surukan ta.



Fira suka ci gaba da kwasa suna bugun ruwan cikin ta tana basu Labarin Komai dake tsakanin ta da mijinta Aliyu har kalar Rayuwar aure da suke gudanar wa.

Yasmeen ke nan 'Ya wurin Alhaji Isah Sambo Ministan harkokin waje na Nijeriya, ita ce 'Yar sa ɗaya tilo a duniya, shekarun ta Ashirin da bakwai zata shiga da takwas ta taso cikin gata da sangarta ta Iyaye domin babu abin da nema ta rasa, lokacin da ta kammala University nata ne ƙasar America bayan ta dawo aka ɗaura Aurenta da General Aliyu, sam Yasmeen bata da wayo kwata kwata a Rayuwarta, Sabeera da Suhaila sune kaɗai ƙawayen ta domin batada tara ƙawaye barka tai dukkan su anan Kano suke Kuma tare suka yi Karatu acan America acan ne ma suka haɗu har Kammala karatunsu kuma suke tare yanzu sai dai bada zuciya ɗaya suke zaune da Yasmeen amma sam ta kasa fahimtar Hakan.






* Sydney. Australia.*



Kallon ta ta kuma yi a karo na babu adadi sannan cike da ɓacin rai ta kira Sunanta bata jira ta amsa ta ci gaba da faɗin.


"Humaira!! Kina da hankali kuwa yaushe Ilimin ki da tunanin ki gaba ɗaya suka bar ƙwaƙwalwar ki da har zaki zo nan ɗugui-ɗugui har Austaraliya ki bar mijin ki a can Nijeriya kuma ma ba tare da san Ransa kika zo ba, yanzu yanzu ki shirya ki koma Nijeriya kafin na sassaɓa miki kamanni a Gidan nan, don na lura kwata baki da hankali a rayuwa."


Turo baki tayi cike da shagwaɓa tana shirin magana, takai hannu zata bige bakin, da sauri ta matsa gefe cike da tashin hankali ta ce.


"Hajiya mana!! nifa babu inda zan koma don na gaji da wannan Auren da ya ƙi ci yaƙi cinye wa wallahi."


Jin abin da 'Yar nata ta faɗa ne yasa Hajiya Khareema sassauta Murya ta ce.

"Haba mana Humaira ta 'Yar Albarka wai kin manta burin mune kiyi haƙuri ki koma mana lokacin kaɗan ya rage da zaki rabu da wannan Auren domin nima ba ƙaunar sa nake ba."



"Ni dai gaskiya na gaji kawai ki faɗa min menene shiri da kika shirya muji."

Humaira tayi maganar a sangar ce cike da rashin ta ido tana kuma turo baki.


Ƙara ƙasa da murya tayi ta ce.


"Matso da kunnen ki kiji Abin domin sirri ne."


Cikin sauri ta matsa kusa domin jin koma menene.

Sun daɗe sosai suna ƙus-ƙus da tattaunawa akan lamarin.

Sannan daga bisani Humaira ta fara shirin komawa Nijeriya ko zuwa marece ta gama shiri Mahaifiyar ta ta da ƙaninta suka rakata Airport domin dawowa Nijeriya.....



*WANNAN KE NAN.*




*ANEESERH*


*💥Aneeserh Just The Beginning.*💥



*Story $ Writing By:*✍️📚


*N $ N.*


*🔥💫Nanameera $ Nainarh KD.🔥💫*



*EP-Twelve*



Kallonsa Mommy ta yi ta ce" wai Aliyu me kake jira baka je kiranba?"

Murmushi ɗauke a fuskarsa yake cewa" calm down Mommy yanzu fa zan tafi" harararsa ta yi ta ce" karma ka tafi kaida shi" bai ce komai ba ya juya zai fita, da sauri ta koma baya tana kalle kalle hankalinta tashe ta ce " dan Allah kayi haƙuri wlh ban kula ba" hannunsa yasa ya ture ta sannan ya shige batareda ya ce komai ba, ajiyar zuciya ta sauke tana hamdala aranta dan ita babu wanda take tsoro agidan nan sama dashi.


"Aneeserh kinje kiran Daddyn?"

Gyaɗa mata kai tayi tana lumshe ido bayan ta kwanta kan royal bed ɗin Mommyn ta ce" cewa yayi naje anjima zai kirani" okay Mommy ta ce sannan ta miƙe ta fita.



Zaune ya tadda ƙannen mahaifinnasa su biyu sai Daddy na uku suna ɗan taɓaa hira, cikin ladabi ya gaishe su sannan ya zauna ƙasa kan carpet ya ce" Daddy gani" gyara zama Daddy ya yi sannan ya ce


"Daman akwai wata magana da nakeso zamuyi dakai kuma tanada muhimmanci sosai maganar saboda haka ka nutsu kaji abunda zamu faɗa" kansa ƙasa ya ce "in sha Allah"


Uncle Bashir ne y ce"Aliyu kasan kasan ɗan uwanmu Ahmad wanda ya rasu shida matarsa few months ago?" girgiza kai ya yi ya ce" A'a bansani ba"


"Tom shiɗin ɗan uwanmu ne na kusa bana nesa ba kawai yanayin rayuwane yasa bamu mu'amala dashi sosai har ku baku sanshi ba, wannan yarinya da kake gani Aneeserh ƴarsa ce ɗan uwanta ya yi hatsari tare da iyayen sai ita kaɗai ta rage, saboda haka ku kaga ya dace mu sake ƙulla wani zumuncin a tsakaninmu shiyasa muka aura maka ita lokacin da ta dawo gidan nan da zama"


Da wani irin expression yake kallon Uncle B with mouth agape wane irin aure aka masa da wa kuma?????


Ganin yanda ya yi ne yasa Uncle Nasir ya ce" munyi hakane saboda ka kula da rayuwarta Aliyu ka ɗauketa matsayin ƙanwarka kayi mata abinda iyayenta zasu yi mata ka kula da rayuwarta fiyeda kowa Aliyu dan Allah"


Tsabar takaici ya kasa magana sai binsu yake da kallo Daddy ya ce

"Kayi shuru ana yi maka magana"

"Daddy meyasa zaku yimin haka please?, ya zanyi da waccen ƴar ƙaramar yarinyar wacce da Allah ya bani haihuwa da wuri ya ci ace na haifi kamarta haba Daddy?, sau huɗu fa kenan ban taɓa auran mace sabida ina sonta ba kawai kuna aura min matane saboda ban samu haihuwa ba kuna nuna kamar baku yarda da ƙaddara ba, amma ni mezanyi da yarinya kamarta matsayin mata?? Asake duba lamarin nan please"


Murmushi Daddy ya yi yana kallon ƴan uwan nasa ya ce" bana faɗa muku ba Aliyu bazai karɓeta matsayin mata ba? Yanzu gashi nan kowa ya gani da idanunsa ni kuma bazan maka dole ba har ka dinga gani kamar ba'ason yarinyar ne yasa aka aura maka saboda haka kana iya sakinta yanzu"



Uncle Bashir ne ya ce" bafa za'ayi haka ba dole zai zauna da ita yake zama da ƴaƴan wasu ma bare kuma ƴar uwarsa kodan maraicinta ai ya ci ace kaji tausayinta ka ɗauketa matsayin ƴarka"


Shuru Aliyu yayi bai ce komai ba amma tabbas this time around bazai yarda da irin abunda ake masa akan aure ba,kallon Uncle Nasir ya yi wanda shine kaɗai yasan zai goyi da bayansa ya ce

"Please Father kace abar wannan maganar wlh banida intention ɗin yin aure anan kusa please Father"


Murmushi Uncle N ya yi ya ce

"Karka damu Aliyu na tabbata zakayi farin ciki da abinda muka aikata kayi haƙuri ka ɗauka hakanne mafi Alkhairinka"


Shuru Aliyu ya yi ransa duk a dagule murmushin ƙarfin hali Daddy ya yi ya ce" banason aja maganar nan da tsayi Aliyu zaka zauna da Aneeserh matsayin mata ko A'a?"


Da sauri ya kalleshi sai kuma ya sunkuyar da kansa ya ce"sorry Daddy gaskiya bazan iyaba saboda tamin ƙanƙanta"


"maganar nan ta shige yanzu kawai ka furta ka saketa shikenan daman ba idda zata yi ba"


Zai yi magana Uncle N ya ce

"Ba haka za'ayi ba yaya, tunda yarinyar nan tana

Please Login or Register in order to submit comment