Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗin kawai take hankali kwance dan securites ne zagaye da ita suna gadinta har ta gama sannan suka kama hanya suka nufo gida.........





Tunda ya fara maganar take kallonsa with mouth agape tarasa ma me zata ce masa, ta rasa farin ciki take ko akasin haka. Ganin yanda ta yi shuru yasa ya ce


"Ko akwai matsala ne?"


Girgiza kai ta yi ta ce" kawai dai ina tausayin yarinyar ne kwata-kwata shekarunta sha biyar kaga kuwa akwai ƙalubale zamanta cikin kishiyoyi har uku kuma dukkansu babu wacce batayi degree ba kaga kuwa dole naji tausayin Aneeserh"


Kamo hannunta ya yi ya ce "ki tayata da addu'a kawai" ta ce" in sha Allah, amma shi Aliyun yaushe zai dawo?"

"Maybe gobe" ya furta yana kallon dramar da ake haskawa a Arewa24.....




Ana kiran sallar magrib a masallacin gidan suka shigo, kai tsaye ɗakinta ta nufa dan bataga Mommy parlon ba, bayan ta idar da sallar ta ɗauki al-qur'ani ta fara karantawa har akayi kiran sallar isha'i....



Kallonta Mommy take har ta idar da sallar sannan ta ce" shine bakizo kin faɗamin kun dawo ba ko?" sunkuyar da kanta ta yi sai kuma ta ce


"Daman naga kina sallane shiyasa " harararta Mommy ta yi ta ce

"Babu wani kawai dai bakison sakin jikinki har yanzu" turo baki ta yi amma ba tace komai ba, miƙewa Mommy ta yi ta ce

"Maid zatazo ta jera miki kayan naki" gyaɗa mata kai ta yi har takai bakin ƙofa sai kuma ta ce


" nd ki fito yanzu" sannan tayi waje......



Kwanciya tayi kan gadon tana tunaninta as usual har kuma bacci ɓarawo ya saceta.....




*ANEESERH*



~Paid 500₦~

*WACCA TA SHIRYA BIYA SAI KI BIYA TA WANNAN DETAILS👇*


*Account Name: Hauwa lawan.*
*Account Number: 9086030007.*
*Bank Name: Opay digital service.*

*Sannan sai ki turo evidence of payment ta waɗan nan Countacts_08081129487 or 09086030007.*


*ANEESERH.*
BY:
*N $ N.*

*Ep. FIVE*


*DREAM!!!*


Da gudu ta fito daga Bedroom ɗin jikin ta sanye cikin Expensive princely gown fuskarta wadace da make-up, hannunta dake riƙe da tsadadiyar wayarta, yatsun suna bada sauti mai daɗi sakamakon awarwaraye da take sanye da su.


Dariya kawai take yi tana kuma ƙara gudu faɗi take.



"Yehhhh!! Nayi ma Yaya Farouq wayo na rigasa ƙari sawa tarbar Abba!."


Tayi maganar tana daka tsalle cike da farin ciki ta ɗafale saman jikin mahaifin nasu da Dawowar sa daga Austaraliya ke nan Jerin gwanin motocin sa suka shigo Gidan da fitowarsa ta basa kyakkyawar runguma.






Daidai lokacin kuma shima Farouq da ya biyo bayan ta ya fito daga palon, tsayawa ya yi yana haki daidai entrance, Hannu yakai yana goge Cake da ta shafe masa fuska da shi har tayi masa wayo ta rigasa tarbar Abba.






"Allah Abba wannan Yarinyar ta ka sai ana haɗawa da Addu'a fa, wannan shegen wayo haka ga gudu kamar wacce taci ƙafan kare."







Dariya Abba da Ummi suka yi lokacin da suka zazzauna saman Royal sofa dake palon haɗaɗɗen gaske bayan sun shiga..





"HHhH ai Yarinta ne zata dena. But amma fa kayi kyau da wannan cake na fuskar ka kamata ya yi muyi pictures a hakan..."





Abba ya yi maganar cike da zolaya yana dariya.





"Yehh kuma wallahi Abba Gaskiya ka faɗa kamata ya yi muyi pictures a hakan kodan Tarihi gaba bamusan wanene gawan fari ba, koda dai bana fatan ku rigani tafiya ku barni."




"Lalle Yarinya kince wani abu amma ki rubuta ki a je sai na rama nima."




"Oho dai yanzu dai ku tashi muyi pictures ba sai an jira photographer ba."



"Au wai da gaske kukeyi ne?."


Farouq ya tambaya da mamaki Ganin yadda suka mimmiƙe ɗin.





Hanyar Dining ya yi domin ya samu ya wanke cake ɗin a Tap.


Lura da hakan yasa Aneeserh cikin sauri ta sha gaban sa, ya yi yunƙurin canza hanya ta kuma shan gaban sa ita da Abba da Ummi nan suka shiga ƴar tsere cikin palon Kamar wasu Yara sun biyewa Aneeserh sai faman zagaye Palon sukeyi wai a dole ba zasu bari ya wanke fuskar ba sai sun yi pictures da shi a Hakan.......



*NOW*




Wuntsilowar da tayi tun daga saman mattress ɗin ne, har ƙasan tiles, yasa ta farka a firgice tabi ta haɗa uban gumi Tamkar wacce aka watsama Ruwa a duka jikinta.





Waige waige ta fara yi tana ya ye Blanket da take ƙudundune ciki, tunanin ina ne nan kuma take, sannan kuma ina su Abba da Yaya Farouq ɗin ta da Ummi suke, waye ya kawo ta nan, kodai har sun dawo ne bata sani ba???...






Kuka ne taji ya suɓuce ma ta sosai lokacin da ta tuna Komai ya dawo kwakwalwarta, kewar iyayenta da Yayan cike fal da zuciyarta ta miƙe tsaye tana tangaɗi Kamar wacce ta sha giya, take zagaye Bedroom ɗin cikin rashin abin yi da tashin hankali hawaye na ma ta zirara a idanunta, takai hannu ta toshe bakinta, lokacin da ta ƙari sa gaban Akwatin ta da aka zo dasu, ta ciro wani frame na pictures nasu ita da Ahalin ta Abba, Ummi, Yaya Farouq, sun yi kyau sosai Ranar da ta cika fifteen years a Duniya suka yi shi.


Kuka take sosai tun daga ƙasan ran ta, haƙoranta har ƙara suke badawa suna haɗewa wuri guda saboda tsananin kuka da take yi, a hankali bakinta take furta.


"Wayyo Allah na Abba na Ummi, Yaya Farouq, Please ku dawo gareni, bazan iya jure rashin ku ba, wayyo ni Rayuwa ta Aneeserh wannan wacce kalar ƙaddara ce???."






Zubewa tayi a ƙasa ita ba suma tayi ba kuma bata dena hawaye ba, gunin ban tausayi, ta daɗe sosai a hakan sannan can knocking ƙofar da taji ne yasa tayi saurin sha re hawayen ta, a tunanin ta Hajiya Aisha ce, da sauri ta mayar da Frame ɗin cikin Akwatin, sannan da hanzari ta shige Bathroom ta wanke gaba ɗaya fuskarta.




Ta fito ta ƙari sa sannan ta buɗe ƙofar tana yunkurin ƙaƙalo Murmushi na yake saman kyakkyawar fuskar ta.


Sai dai Ganin wacce take a ƙofar ne yasa, ta matsa gefe ba tare da ta ce da ita komai ba, ta koma ciki ta zauna gefen Bed tana wasa da finger's nata.


"Am Maa!! Her Excellency ce dama ta ce...."


Tun kafin ta ƙari sa faɗar abin da ke bakinta tayi saurin dakatar da ita, ta hanyar yi ma ta nuni da gefe wurin da tulin abubuwan da ta kwaso a shopping Mall da ta fita suke, kaya ne kala kala tun Daga kan na sakawa a jiki tufafi, biscuits chocolate cake babu abin da babu.


Shiru maid ɗin tayi sannan ta ƙari sa wurin ta fara abin da ya kamata.


"And she's call you.."



"Okay, where is her?."


"She's in main Palo in Downstairs.."



"Okay, Thanks."



Ta furta sannan ta miƙe tsaye ta kuma Gyara fuskar ta, kar a gane tayi kuka sannan ta fice, koda ta sauka Down babu kowa Palo, tunani tayi akan ƙilama tana kitchen, hakan ne yasa ta nufa kitchen ɗin kai tsaye.




"Oh, My Son, I don't like this playing with my heart da kakeyi fa, Now Tell me, Yaushe ne zaka dawo?, and tell me the truth..."


Shiru tayi tana sauraren abin da yake faɗa.


Yayin da Aneeserh da ta shiga kitchen ta tarar da Hajiya Aisha tana wayar, kuma da alamu da yaron ta ne, yasa taja gefe tana jira ta kammala.



*IN BRIEFLY*



Haka Rayuwar Aneeserh ta ci gaba da tafiya cikin gidan Gwamnati Na President of Nijeriya, Kuma uncle nata da ya kasance Yayan Mahaifin ta mai rahusawa.

Ba'ace tana jin daɗi na zama gidan ba, sannan baza'ace bata jin daɗi ba, saboda bata nema Komai ta rasa ba, komai ta tambaya, kai tun kafin tayi tambayar ma ake ma ta, sosai Her Excellency take jan Aneeserh a jiki tana bata kulawa da ya dace, shima His Excellency ba'a barsa a baya ba, duk da cewa ayyuka suna masa yawa, amma sosai shima yake bawa Aneeserh lokacin sa.



Aneeserh zaman ta a gidan Uncle nata tana gudanar da rayuwa Normal babu wani walwala mai yawa a ciki.







Lokuta da dama idan ta zauna da Hajiya Aisha da take kira da Mommy, yawancin fira da Hajiya Aisha take ma ta akan ɗan ta Hydar ne, sosai Aneeserh ta kula da ba ƙaramin ƙauna Mommy takewa Hydar ba, da ita Aneeserh ɗin bata san shi ba, kuma bata taɓa Ganin sa ba.




Tun Aneeserh bata damu da zancen sa ba, har ta fara saka ayar tambayar ta akan sa, Ganin Kullum Hajiya Aisha idan tana waya da shi lokacin da suke tare babu tambayar da take masa, sai Yaushe zai dawo Nijeriya, aikin sa ke nan ja ma ta rai.

Tambayar Aneeserh anan ita ce, wai shin to yana ina ne, kuma wanene shi ma gaba ɗaya sannan yana wata ƙasa ce questions dai Like this sune cike zuciyarta.



Wasu lokutan har ta wurin Maids na gidan tana samun labari akan sa, anan ne ma take ji, wai shiɗin soja ne, kuma matsayin Likita yake cikin su, babban muƙami.


Sosai ta shiga tsoro jin cewa Soja ne shiɗin, a Rayuwar ta babu irin mutane da ta ke tsoro a Duniya sama da Soja........




```GA DAI ANEESERH NAN TANA GUDANAR DA RAYUWARTA BA TARE DATA SAN CEWA AN ƊAURA MA TA AURE DA MUTUMIN DA BATA SANI BA, BATA KUMA TAƁA GANINSA BA, SANNAN KUMA WANDA TAKE MATUƘAR TSORON AIKIN SA WATO SOLDIER, KO TA ZATA KAYA?????```


```TOHM A TARA NEXT PAGE 😸```



💞💞*ANEESERH*💞💞

💥*The Beginning*💥


*🔥💫Nanameera $ Nainarh KD.🔥💫*

~Paid 500₦~

*WACCA TA SHIRYA BIYA SAI KI BIYA TA WANNAN DETAILS👇*


*Account Name: Hauwa lawan.*
*Account Number: 9086030007.*
*Bank Name: Opay digital service.*

*Sannan sai ki turo evidence of payment ta waɗan nan Countacts_08081129487 or 0810 660 8363.*



*ANEESERH*

*💥Aneeserh Just The Beginning.*💥


~Paid Book~

*😻🔥Wai shin baku da labarin cewa free page's Aneeserh suna daf da ƙarewa 🙀 kuyi gaggautawar yin payment domin wannan tafiyar Zazzafa karya kasance ba tare da ku ba. Don't Miss It Dearest Sister's.🔥😻*



*Story $ Writing By:*✍️📚
*N $ N.*
*💫Nanameera $ Nainarh KD.💫*





*EP. Six-Seven.*

Yau Saturday dan haka da wuri ta tashi tayi wanka sannan ta shirya cikin wata abaya peach colour wacce tayi matuƙar amsar jikinta, saida tagama shiryawa tsaf sannan ta sauko ƙasa.........

Babu kowa a parlon hakan yasa tayi zamanta ta kunna tv tana aikin kallo, nikam nace daman su Aneeserh ansami waje. "Ai ya cemin zuwa tuesday zai dawo" Mommy ta faɗa lokacin da suke fitowa itada his excel., zama sukayi kan royal cusuion ɗin parlon da murmushi a fuskarsu, sunkuyawa ta yi ta ce" Daddy good morning, Mommy good morning" "morning dear" suka faɗa atare Daddy ne ya ce" kallo ki keyi?" murmushi ta yi sannan ta ɗaga masa kai, kallonta Mommy ta yi ta ce" ai kin kusa komawa makaranta in sha Allah" dariya tayi dan daman burinta kenan tana kallon Mommy ta ce" Mommy yaushe?"
"Sai Aliyu ya dawo" shuru ta yi dan har ta fara gajiya da maganarsa a gidan, maids ne suka fara shigowa suna jere kayan breakfast ɗin har suka gama sannan suka fita su kuma suka nufi dinning area ɗin dan fara cin abincin..............


Wajejen la'asar tana zaune duk gidan ya gundureta, Mommy ta shigo hannunta ɗauke da plate wanda akayi sliccing pineapple da apple aciki. Zama tayi gefenta kasancewar akan kujera 3seater take ta dafata, kallonta ta yi ita kuma ta yi murmushi ta ce

"Kin gaji ko daugher?" murmushi kawai tayi amma ba tace komai ba, ta ce" ga fruit nan kisha kinji zanje gidan wata friend ɗita" kallonta tayi har zatayi magana sai kuma tayi shuru ganin haka yasa Mommy ta ce" ko zaki bini?" gyaɗa mata kai tayi dan daman abinda zata tambayata kenan. Ta ce" ok tom jeki shirya sai muje" tashi tayi ta wuce ɗakinta dan sanza kayan kamar yarda Mommy ta ce mata................

Wani irin babban gidane sosai kuma ya haɗu iya haɗuwa, sai kallonsa take dan tunda ta shigo abuja banda gidan president bataga wanda ya kaishi kyau ba..........


Da murmushi ta ce"oyoyo yau kece agidan?" dariya ta yi tana zama ta ce" tunda ke kin kasa zuwa ni gani nazo ai" girgiza kai Hajiya Zainab ta yi ta ce"wlh ba haka bane your excel kinsan Ayrah batajin daɗi shine abinda ya hanani fita wlh" "Allah sarki kece jikin ne?" ta ce" wlh kam abunnata ne kamar tasamu sauƙi kamar kuma bazata warkeba, ɗazu mijinnata ya bar gidan nan wai cewa ya yi azubar da cikin kawai" da mamaki Mommy ta ce" amma dai baku yarda ba ciki ai lokaci ne da Allah yabasu daman duk wata mace ai dole zatayi laulayi saidai wata tayi mai zafi wata kuma da sauƙi" ajiyar zuciya ta sauke ta ce" wlh nima abinda nace masa kenan duk yabi ya damu", murmushi Mommy ta yi ta ce" kawai rabuwa zaki yi dashi Allah ya bata lafiya" Ameen ta amsa dashi sannan ta kalli Aneeserh ta ce" Hajiya ina kika samo budurwar ƴa?" kallon Aneeserh Mommy ta yi tana murmushi ta ce".wlh ƴa nayi daga kano, Aneeserh tafi ɗaki kiyi kwanciyarki" da sauri ta tashi dan daman ta gaji da zaman parlon.....


Bayan tashiga ta kalli Hajiya Zainab sannan ta ce" matar Aliyu ce" da mamaki ta ce" wata matar kuma?, anya kuwa abun baiyi yawa ba?" girgiza kai Mommy ta yi ta ce" ƴar ɗan'uwansa ce toh iyayenta ne suka yi hatsari sunzo wajensa bayan sun koma a hanya sukayi hatsari duka suka mutu, toh shine ya ɗauko yarinyar ya tawo da'ita, shine fa aka aurawa Aliyu ita wai ko za'a dace" jinjina kai Hajiya Zainab tayi alamar gamsuwa sannan ta ce" toh Allah yasa hakane mafi alkhairi Allah kuma ya kawo zuri'a tagari" Ameen suka amsa dukansu............





Sai bayan magrib sannan suka dawo gida duk tagaji kodan daɗewa da tayi bata fitaba?. Tana shiga ɗakinta ta waɗa banɗakin dan yin wanka ............




Suna gama cin abincin Daddy ya kalleta ya ce" Aneeserh!" "na'am" ta amsa masa da hannu ya yi mata alama da tazo ta taso ta zauna gefensa dan haka ya koyar da'ita. Kamo hannunta ya yi ya ce" Aneeserh zan faɗa miki wata magana inaso ki kula da'ita sannan ki riƙeta kinji" gyaɗa masa kai ta yi ya ɗora da faɗin

"Nasan kinaji ana cewa Aliyu ko?, to ba kowa bane Aliyu face ɗana kuma shine kaɗai ɗan da Allah yabani, yana da mata guda uku duka kuma suna zaune lafiya dashi, Aƙalla Aliyu zai kai shekaru 35yrs a duniya kuma ya yi auren fari tun yana ɗan shekara 28 amma har zuwa wannan lokacin Allah bai bashi haihuwa ba wanda kuma duk ya damemu duka, inaso idan ya dawo ki ɗaukesa matsayin Abbanki kamar yanda kika ɗaukeni domin wajensa zaki cigaba da zama saboda ki samu ki ƙarasa secondary school ɗinki idan yaso daga baya zaki iya dawowa wajenmu kinji" shiru ta yi sai kuma ta ta ce" in sha Allah Daddy zanyi kamar yanda kace Allah ya dawo dashi lafiya" sosai yaji daɗin furucinta bashi kaɗai ba harda Mommy dan basu ɗauka zata amince da sauƙi ba, ita kuma tayi hakane kodan ta samu damar komawa kano cikin ƙawayenta.............


Ganin dare nayi yasa Daddy ya ce" tashi kije ki kwanta dare ya fara" kwaɓe fuska ta yi ta ce" Daddy zan kalli film ɗin happy New year ƙarfe goma a mbc bollywood" murmushi ya yi ya ce" bazaki ji bacci ba dear?" gyaɗa masa kai tayi ya ce" tom shikenan Allah ya kaimu" ta ce "Ameen" sannan suka cigaba da ɗan taɓa hira...........




Yaukam makara tayi dan jiya sai wajen ƙarfe 12pm sannan ta kwanta bayan ta ɗan taɓa chat da ƙawayenta, tana gama shiryawa ta sake naɗewa a gado saboda wani bacci da keji. Da sallama ta shigo bedroom ɗin ganin har kusan ƙarfe 11am amma bata fitaba, hangarta tayi tana kwance sai baccinta take hankali kwance, murmushi Mommy ta yi sannan ta kashe mata a.c ɗin ɗakin saboda ana sanyi ba laifi sannan ta juya ta fita..........



Da sauri ta miƙe tana kallon agogon gefenta ta ce" nashiga uku ya akayi nayi bacci mai nauyi haka" sannan ta tashi da gudu yashiga banɗaki dan sake yin wanka...........



Fitowa tayi cikin wata doguwar riga ta atampa maroon colour anmata ɗinkin A-shaped ta zauna das a jikinta, lip gloose kawai ta shafa abakinta sai eye pencil data saka a idanunta amma tayi wani sihirtaccen kyau mara hayaniya...........


Zama tayi gefen Mommy da take ta murmushi tun fitowarta ta ce" masha Allah shalele kinyi kyau sosai abinki" dariya Aneeserh ta yi ta ce" Mommy good morning" kwaikwayar maganarta Mommy tayi ta ce" Mommy goood morning" ai kuwa ta fashe da dariya tana kallonta ta ce

"Daman kin iya irin magana ta?" dariya itama ta yi ta ce" baki gani nayiba dear na iya sosai" shuru tayi dan babu abinda ta tuna sai sanda yaya Farooq zai kaita makaranta ahanya ta kira sunansa shima ya kira irin yanda Mommy tayi yanzu, nan da nan hawaye ya kawo fuskarta. Lura da hakan yasa Mommy ta ce" lafiya dai shalele?" tana goge hawayenta ta ce" Mommy yaya Farooq na tuna shine yake yimin irin abinda kika yimin yanzu"rungumeta Mommy ta yi ta ce" kiyi haƙuri Aneeserh Allah ubangiji ya jiƙansu da rahama" ta ce "Ameen".............





Ana idarda Sallar la'asar ta shigo ɗakin Mommy time ɗin tana zaune tana danna wayarta ganinta yasa ta ajiye ta ce" naga kinyi kwalliya dear?" sunkuyar da kanta ta yi sai kuma ta ce" Mommy daman chocolates ɗina ne suka ƙare" murmushi Mommy ta yi ta ce" ok yanzu zaki fita siyowa ne?" ta gyaɗa mata kai, tashi Mommy tayi ta ɗauko mata ATM card ɗinta sannan ta ce" gashi nan duk abinda kike so ki siya kinji, amma karki daɗe".


Murmushi ta yi ta ce"tom Mommy nagode sosai saina dawo" ta ce" tom Allah ya dawo dake lpia" na ce" Ameen"..........



*Nikam burina naga wannan Aliyun da aketa faɗarsa ko ya yake ohhho?*
*Kudai ku biyo mu cikin book ɗin Aneeserh*



~Paid 500₦~

*WACCA TA SHIRYA BIYA SAI KI BIYA TA WANNAN DETAILS👇*


*Account Name: Hauwa lawan.*
*Account Number: 9086030007.*
*Bank Name: Opay digital service.*

*Sannan sai ki turo evidence of payment ta waɗan nan Countacts_08081129487 or 0810 660 8363.*


EP_8_9.
~Paid Book 500₦~
*ANEESERH.*

*Free Page na kusa da na ƙarshe 😹.*


*💥Aneeserh Just The Beginning.*💥



*Story $ Writing By:*✍️📚


*N $ N.*


*🔥💫Nanameera $ Nainarh KD.🔥💫*



EP. Eight-Nine.








Tunani Hajiya Aisha tayi lokaci guda ta canza shawara, kallon Aneeserh da ta kusa ƙofa tayi.




"Babyna tsaya kawai na rakaki mu tafi tare dama ba kince kina so ki zagaye Birnin Abuja ki buɗe ido ba?".

Juyowa Aneeserh tayi fuskarta ɗauke da ƙayataccen Murmushi ta amsa ma ta da faɗin.



"Yeah Mommy please muje?."





"Okay karki tohm Karki damu yau zamu yawata ko'ina da ina."





Hajiya Aisha tayi maganar tana Murmushi tana son Yarinyar Sosai wasu lokutan abin har mamaki yake bata.



Cikin ƙankanin lokaci ta shirya tsaf cikin rantsatsiyar lace milk color sama sama ta saka make-up artist nata Saima tayi mata Make-up ita ma Aneeserh aka kuma tsantsare ta da make-up tamkar wata bride.


"Oh Mommy sai kace zamu tafi wurin Birthday Party wannan make-up haka...*


Aneeserh tayi maganar cike da shagwaɓa tana juyo da fuskarta tana fuskantar Hajiya Aisha bayan Saima ta kammala ma ta make-up.


"Wow Masha Allah, kai kai Baby Aneeserh dama haka kike da wannan uban kyau haka sai kace Queen Of Beauty Gaskiya bazan yarda ba har sai mun yi Pictures fa, lallai Hydar ya yi dace da wannan zuƙe ƙe kiya haka..."



Hajiya Aisha ta ƙari sa maganar ƙasa ƙasa ba tare da ta bari Aneeserh taji ba.


Sai dai kaf Aneeserh taji abin da ta faɗa, but confusing kawai ta shiga bata gane Komai ba.



"Common Saima ƙari so ta nan ki kafta mana pictures ko kala uku da wannan Glam Babyn tawa mana."


Hajiya Aisha tayi maganar cike da nishaɗi fuskarta cike da wadataccen walwala.




Murmushi Saima tayi ita kanta ta yaba da Irin kyau da Aneeserh tayi.



Sosai suka sha pictures kala kala mai kyau da mara kyau cike da farin ciki suke.




"Yauwa barima na nuna Miki Pictures na Yayan ki Hydar da yake ta jamin rai zai dawo zai dawo amma shiru tun ina saka rai har na fara karaya."


Hajiya Aisha tayi maganar ne bayan sun fito daga Bedroom sun nufo Down suna taka Stairs.



"Eyya, wata ƙila wani abun ne ya riƙe sa Mommy kinsan fa yanayin aikin nasu."


Aneeserh tayi maganar Kamar wacce tasan wani abu dangane da Aikin soja.



"To ya zanyi yana yimin iya yi ne, saboda a tunanin sa shi kaɗai ne Baisan cewa na sama 'Ya ba da daɗewa ko kewar sa ma na dena."


Dariya Aneeserh tayi ba Tare da ta kuma cewa Komai ba.



"Oh Dam it, oh Allah Ni Aisha naga Ikon Allah...."



Her Excellency tayi maganar tana riƙe baki. Ganin yadda Wayarta da ta juya bayan ta lalubo picture na Hydar zata nunawa Aneeserh kamar an tankaɗe wayar daga hannunta haka wayar ta goje ta faɗa ƙasa Glass ta yi tatsa tatsa.


"Oh am so sorry Mommy saboda Ni Gashi Wayar ta farfashe."



Aneeserh tayi maganar idanunta rau rai kwalla cike Tabb tana shirin fashewa da kuka.




"No ba laifin ki bane dama haka Ubangiji ya ƙaddara, karki damu yanzu muje daga nan sai na nema wata Kafin a sake kawomin kalar samfurin ta."


"Tohm."


Aneeserh ta faɗa a gajarce, ba tare da ta saki fuskarta ba.



Wasu lokutan dole sai ana ma ta uzuri kodan halin da take ciki.







****
Sosai suka sha yawo cikin Garin Abuja suka yawata lungu da saƙo Aneeserh ta sha kallo Sosai duk da cewa ba karon ta na farko da zuwa Abuja ba ke nan.




Sosai Aneeserh ta jido Chocolate cake biscuits shawarma kamar hauka a cewar Hajiya Aisha ta ɗauka duka abin da take so. Bata da wata matsala.







Aneeserh tanajin daɗin Zama a gidan Uncle nata President of Nijeriya Sosai. Domin kulawa ta musamman His Excellency da Hajiya Aisha suke bata Fiye da wasu Iyayen ke bawa Yaran su.



Koda gama yawace yawace da suka sha sun kwaso gajiya sosai domin har wurin Salon na manyan yara masu ji da Dukiya Hajiya Aisha takai Aneeserh aka ma ta mai kyau.




"Jay Kuma anan Nijeriya gida na, to Yaushe ke nan ya dawo ƙasar?."


Kallon Hajiya Aisha da idanunta ke kan tsalatsalan motoci da suke pake gefe kuma take wannan maganar, Aneeserh tayi tana nazari akan abin da taji ta ce da kuma tunanin wanene kuma Jay?.....




Sai dai bata ce Komai ba, kamar yadda ita ma Hajiya Aisha ba ta kuma magana ba, har suka shiga tsararren palon kai tsaye Bedroom Aneeserh ta wuce bayan ta gaisar da mutum da suka shigo suka tarar a Dining hakimce yana Kai Loma.







A gajiye take sosai shiyasa bata tsaya ba, kuma sannan a wannan lokacin bata cika son Hayaniya ba.








"Jay! Yaushe ka dawo Nijeriya ne ban sani ba, sannan ina ne ka tafi babu ko waya, wato ka girma ka manta da Irin walahar da muka sha akan ko???."




Juyowa Matashin Mutumin da ba zai haura 40 years ba a Duniya ba, Ya yi yana kallon Yayar ta sa sannan ya ce ma ta.




"Gajiya nayi da ƙorafin ku akan Rashin Aure da Banyi ba, shi ne kawai na shiga Yankin Turawa domin lalubo muku ita....."



Cike da mamaki ta katse sa cikin hangame baki Galala tana kallon sa, da kyar maganar ma ta fito daga bakinta.




"Ita wa ke nan????."



"Ah ah ita Matar Auren mana..."


Ya bata amsa tsakani da Allah, yana bawa Saima da ya tsareta dole a Dining ɗin tana masa hidima a dole, umarni da ta zuba masa juice dake jug a cup.


"Jay!!!."


"Na'am!! Yes it's my name. Kune fa kukace kuna Buƙatar suruka daga gareni, shi ne na tafi samota, sai dai ba'a samu ba."



Ɓoyayyiyar Ajiyar zuciya ta sauke jin abin da ya faɗa, sai dai tun kafin ta gama sauke numfashin ta kuma zaro ido waje, jin abin da ya ci gaba da faɗa.


"Sai dai yanzu na samu waccan kyakkyawar Sweet 18 daga ina kuma kuka samota, kawai ki Aura min ita, kinga shikenan."



"Subhanallah ya Ubangiji waccan da ka gani tare dani matar Hydar ce a yanzu kuma 'Yar ƙanin His Excel... Da suka yi Hatsari da matar sa suka rasu..."



Hajiya Aisha tayi maganar cikin suɓutar baki, duk saboda jin abin da ya faɗa da tayi.


Umarni ta bawa Saima da ta bar wurin.




"Okay!! No problem na bar masa ita, kawai saboda ya kasance jinin ki ne, sannan ki Aura min wannan Yarinyar kawai don naga alamar zatayi biyayya."







"Ya Salam Jay!! Kana wahalar dani fa, ita Saima da kake gani ba House maid bace, make-up artist ce Kuma kwararriya domin ta fannin tayi karatu."








"Okay!! Ki ce idan na Aureta na huta raka ta wurin Make-up ke nan, ina sauraren ki faɗa min wasu abubuwa akan ta

Please Login or Register in order to submit comment